Yadda ake Hada Sabulu na Musamman na Gyaran Fuska


YADDA AKE HADA SABULU NA MUSAMMAN DOMIN GYARAN FATA DA GYARAN FUSKA DA KUMA HADIN DILKA. 

1) DOMIN KYAWUN FUSKA

     A samu

1 . Garin zogale

2 . Farar albasa

3 .Sabulun ghana 

4 . Sabulun Dettol

5 . Sabulun salo


Yadda za a hada. 

Ki samu sabulun ghana dana   salo dai dai kai daya sai ki samu dettol shima kamar guda 2 sannan sai ki sami garin zogale cokali 2 sai albasa manya guda 2 duk sai ki hada su a turmi ki kirbe su sannan sai ki juye a roba mai murfi zaki dunga wanke fuskarki da shi yanada kyau sosai  yana magance kurajen fuska. 


2) HADIN DILKA

1 . Dilka da sukari

2 . Lemon tsami

3 . Man zogale

4 . Turaren Du'aul jannah 


   Yadda za a hada:-

Zaki zuba duk kayan a cikin ruwa sai ki sa wuta amma kadan  har sai  ya tafasa yayi kumfa sai ki sauke idan ya huce kirinka dangwala  kina shafawa a ko ina a jikinki, ki bari ya bushe, zai fara murmushewa da kansa sai ki karasa murje shi sai kiyi wanka da ruwan dumi, fatarki zatayi kyau

3) SABULU NA MUSAMMAN

  A samu:-

 

10 Best Dating Apps 2024 - Abokiyar Hira Hausa Novels
 

1 . Madarar turari

2 . Lalle da dilka 

3 . Ganyen magarya

4 . Kur kur 

5 . Dudu osun da Detol

6 . Sabulun ghana

'A hadasu wuri daya a daka su a turmi mai kyau su hadi jiki sosai sai ki runga wanka da shi.

Kada ku manta da Following Page dina ta hanyar danna bulun Rubutun dake kasa 👇👇

Domin Kallon yadda ake Haɗawa(Video)

https://vm.tiktok.com/ZM2DBuT7k/

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post