Daga Alƙalamin Boss Bature🔥🌹
COURTROOM, FEDERAL HIGH COURT
BABBAR KOTUN TARAYYA
A ranar da za'a yi zaman shiri'ar Elders kar ku so ku ga yadda jama'a suka dadda6e babbar kotun tarayya, ta ko'ina zauren kotun ya cika maƙil da ƴan jarida, da kuma human rights activists) masu fafutukar kare hakkin ɗan adam) ƴan majalissa da ministoci, gwamnoni da sauran manyan ƴan siyasa da masu ruwa da tsaki a ƙasa. Wasu daga cikin iyalan Elders sun hallara, kuma abun ƙayatarwar, gaba ɗaya an buƙaci a zo da fursinonin kurkukun ƙaddara da suka rage. Ba'a ta6a yin shari'ar da ta ja hankalin duniya ba irin wannan, saboda kowa jiran ta yake yi, idon duniya ne akan kotun tarayyar Abuja, kowa ya ƙagara da ya ji hukuncin da za a yanke masu, sa'ilin da Isod Agents suke shigowa cikin zauren kotu tare da Elders sun yi masu ƙawanya, baka iya ganin fuskokinsu saboda an yi masu alfarmar rufe fuskar su da mask, amma idanunsu a buɗe suke.
Alƙalin da zai yi shari'ar babban mutunne dattijo, Justice Salahuddeen Muhammad tsohon abokin baba Obie ne, yana a zaune kan kujerarsa, cikin shigar sa ta alƙalai, idanunsa sanye da farin glass.
Bangaren Prosecutors gaba ɗaya sun hallara kowan nan su yana zaune kan kujerar sa, ga uban case files na kurkukun ƙaddara a gaban su suna duddubawa.
Dangin baba Obie sun fi kowa shiga tashin hankali da damuwa.
Lokacin da Justice Salahuddeen ya fara magana kotun ta yi tsit kamar mutuwa ta gifta, ko sautin tari baka ji saboda kowa burinsa ya ji me alƙalin ya ke cewa..
"This court is now in session..." Ya faɗa a nutse tare da kallon al'ummar dake cikin kotun, umarni ya ba court registrar na ya yi announcing shari'ar da za a saurara, bayan ya miƙe ya soma karantowa kamar haka,
"The case before us today is that of the Federal Republic of Nigeria and Mr. Obinna Chimaobi wanda kowa ya fi sani da dattijon arziƙi, Alhaji Musa Wadata former president of our country, Ifeanyichukwu Lucas, Ja'afar Falgore wanda aka fi sani da Ɗan Iya......"
Gaba ɗaya saida ya zayyana sunayen su, kafin alƙali ya buƙaci da a fiddo su gaban kotu, gaba ɗaya idanu suka koma kan su, kunyar duniya ta kama su, sun muzanta sosai, duk suka kasa haɗa idanunsu da na kowa bayan da aka buɗe fuskokinsu, hannayensu da ƙafafuwansu gaba ɗaya ɗaure suke da sarƙa, kamar dabbobi da ƙyar suke ɗangyasa ƙafafunsu. Har suka ƙarasa da su inda za su tsaya wato cikin dock, ba su ɗago da ido sun dubi al'umar da ke a cikin kotun ba, iyalin baba Obie sun shiga matsananciyar damuwa, hankalinsu na kan mahaifinsu tun lokacin da aka shigo da su suke ta kallon shi idanunsu cike da ƙwallar baƙin ciki, gaba ɗaya zuciyoyinsu a cike suke da zullumi da fargaba, haka ma sauran iyalan elders da suke a cikin kotun baƙin ciki ne ƙumshe cikin zukatansu. A duniya kenan ina ga ranar tonan asiri ta lahira.
Bayan an fiddo su aka fara announcing of appearance, in da prosecutor ya miƙe cikin natsuwa, bayan ya yi kalamin girmamawa ga alƙali ya soma bayyana kan shi tare da sunan shi, ya ɗaura da faɗin, "...On my humble appearance is for the prosecution." Bayan ya gama ya koma ya zauna, wani ma ya miƙe bayan ya gyara rigar shi ta lauyoyi ya fara bayanin kan shi kamar yadda wanccan ya yi, ya ɗaura shima da faɗin, "...My humble appearance is for the defendants. (lauyan waɗanda ake ƙara) Haka duk suka rinƙa tashi suna gabatar da kawunan su.
Bayan sun kammala prosecution counsel (Lauyan da ya yi filing case ɗin daga hukumar Isod) ya sake miƙewa ya bayyana charges da ke gare su tare da ranar da aka shigar, ya ɗaura da faɗin, "...The defendants are accused of dark magic cult, human sacrifices, kidnapping, torture, murder, and human trafficking."
("Waɗanda ake tuhuma, ana tuhumar su da laifin baƙin sihiri, sadaukarwar mutane, garkuwa da mutane, azabtarwa, kisan kai, da fataucin mutane.") Bayan ya gama zayyana laifukan da ake tuhumar su da su ya buƙaci da a karanta ma masu laifin charges ɗin don su amsa, bayan alƙali ya bada damar hakan court registrar ya miƙe idonshi akan elders ya ce masu ga abubuwan da ake ƙarar su akai su saurara don su ji, he reads the charges to them openly, da turanci ya zayyana masu kamar yadda ake magana a cikin kotun, amman duk da haka bayan ya gama sai da ya tambaye su sun ji abun da ya karanta ko akwai wanda bai fahimta ba bai jin yaren da aka faɗi da shi, wasu daga ciki ne suka jinjina kai alamar sun fahimta, yayin da wasu sukai shiru ba tare da sun ɗago kai ba, sanin su su waye kuma an san suna fahimtar yaren da ake magana da shi ya sa aka ci gaba,
Prosecution Counsel ya sake miƙewa cikin nutsuwa ya soma kora jawabi dangane da kurkukun ƙaddara, bai yi kuskuren ko da harafi ɗaya ba, komai da Elders suke aikatawa a gidan kurkukun ƙaddara da irin azabtarwar da suke yi wa fursinoni saida ya zayyana su tiryan tiryan...."
Kowa da ke a kotun ya nutsu yana sauraron shi, idanun mutane suka cuccuko da ƙwalla saboda tausayin prisoners da ya kama zuciyoyinsu, shi kan shi alƙalin farin ruwa ne kwance a cikin idanun shi.
Kowa ya shiga tashin hankali da firgici, mutane sai girgiza kai suke wasu har da matse ƙwalla.
Elders kuwa cikinsu ya ɗuri ruwa, sai zazzare idanu suke yi, cikin tashin hankali da kunyar duniya..
Bayan da me gabatar da ƙara ya ƙarasa zayyana komai da kuma hujjoji da shaidu..
A ƙarshe ya ce, "We urge the court to impose the maximum penalty for these heinous crimes."
(Muna roƙon kotu da ta zartar da mafi girman hukunci kan waɗannan munanan laifukun) Ya koma ya zauna a mazauninsa.
Jinjina kai Alƙali Salahudeen ya yi tare da numfasawa cikin murya mai kaushi ya furta, "Thank you, Br. Nawaz."
Maida duban shi ya yi kan elders ya ce sun ji laifukan da ake tuhumar su da aikatawa sun amince? Farko duk shiru suka yi idanun mutanen kotun na akan su, kowa na su ya ji mi za su ce, Baba Obie ne ya fara jinjina kan shi tare da furta ya amince, duk sauran ma suka yi hakan, amman abun mamaki Musa nunawa ya yi bai amince ba, fuska a murtuke rabinta an rufe da bandeji ya ce yasan ya ta6a yin sadaukarwa don biyan buƙatun shi, kuma duk yaran da ya sadaukar jinin shi ne, don haka ƙazafi ne aka yi mashi shi bai aikata sauran laifukan ba kuma shi baya a cikin elders, jin abun da ya ce yasa Pravin a ruɗe shima ya ce sadaukarwa kawai ya ta6a yi bai aikata sauran laifukan ba baya a cikin elders, bayan da farko ya jinjina kai alamar ya amince, Ɗan-iya na so shima ya musa tuhumar da ake mashi amman ba dama don yasan iya gawar Anah da aka tono ta isa hujja akan shi, duk da halin damuwa da Chief Owais yake a ciki sai da ya ɗan yi murmushin takaici ganin yadda suke son naɗe tabarmar kunya da hauka,
Jin haka ya sa alƙalin maida duban shi kan lauya masu ƙara ya ce mashi ya ji abun da suka ce na basu amince ba, miƙewa ya yi ya ce in an bashi dama zai gabatar da hujjoji alƙalin ya ce an bashi, lauyan ya buƙaci a fiddo da prisoners gaban kotu, bayan sun fito gaba ɗaya sun tsaya a cikin witness stand lauyan ya je gaban su a nutse ya fara yi masu tambayoyi game da kurkukun kaddara da abubuwan da ake aikatawa, gaba ɗaya sai da suka faɗi komai da ake aikatawa, bayan ya gama yi masu tambayoyi ya gabatar ma da kotun hotunan kurkukun ƙaddara da aka ɗauka lokacin da su Owais suka kai farmaki na biyu, bayan su ya ƙara gabatar ma kotun da wasu shaidu wanda suka samu daga wurin Baba Obie ciki harda vediotape na elders da su kan su basu san da shi ba da kuma list na sunayen su da bayanan su, harda hotunan abubuwan da aka samu a gidajensu da aka je bincike.
Bayan ya gama gabatar ma da kotu duk hujjojin, alƙali ya maida duban shi kan lauyoyi masu kare waɗanda ake tuhuma ya ce, "Defenses, do you have any statements to make?"
Farko duk shiru suka yi kafin wani ya miƙe ya gabatar da kan shi a matsayin lauya mai kare Alhaji Musa (Dama kafin a zauna zaman shari'a, waɗanda ake tuhuma da laifi suna da hakkin ɗaukar lauyoyi da za su kare su), Ya fara bayani da cewa sam bai gamsu da hujjojin da aka gabatar akan alhaji Musa ba saboda za a iya yi mashi ƙazafi tun da shi babban mutum ne ɗan siyasa dole bai rasa maƙiya masu son ganin bayan shi, kuma duk hujjojin da aka bayar basu isa su gamsar da ya aikata sauran laifukan da ya ce bai aikata ba tun da yanzu muna a lokacin technology duk za a iya ƙagar su, har prisoners ya tambaya kan ko lokacin da suke a kurkukun sun san su waye elders duk suka amsa da basu sani ba, ya ce ko wannan ma hujja ce da zata sa kotu ta yarda ba lalle yana cikin su ba, bayan ya gama jawabin shi ya roƙi kotu da ta yi nazari sosai kada ta amince da hujjojin da aka bayar kafin ya koma ya zauna, hannu chief Owais ya kai ya ruƙe ha6ar shi, a ranshi yana mai mamakin wani alƙawari Alhaji Musa ya yi ma lauyan da har ya iya yin wannan ƙarfin halin.
Bayan lauyan masu ƙara ya sake miƙewa ya buƙaci da a bashi dama zai ƙara gabatar da wasu hujjojin alƙali ya bashi, Unaisah ya buƙaci ta fito, bayan ta tsaya a wurin da aka tanada ya fara yi mata tambayoyi kan ko tasan alhaji Musa, aikuwa kaman tana jira nan ta shiga kora jawabi tun daga kan zuwan Unaizah kurkukun ƙaddara da yadda ta mutu da wasiƙar da ta bata da diary ɗinta mai ɗauke da hotunan su har da shi, daga ƙarshe ta yi bayanin yadda ya sace su ita da Batool ya sake maida su kurkukun kaddara don cika ƙudirin shi na zamowa shugaba inda har ta yi nasarar watsa mashi acid ta kuma buga mashi zarto a kafaɗa, bayan ta gama lauyan ya yi ƙarin bayani tare da nuna ma alƙali ciwukan da Unaisah ta ji ma alhaji Musa, daga baya ya gabatar ma kotu da wasiƙar tare da diary ɗin Unaizah. Bayan alƙali ya gama duba su ya tambayi lauya mai kare Alhaji Musa ko akwai abun da zai ce, miƙewa ya yi ya ce duk abun da Unaisah ta faɗa zasu iya zamowa ba gaskiya ba shirya mata aka yi amman yana son a bashi dama ya yi mata tambayoyi alƙali ya ce an bashi, tun da ya tsaya a gabanta ta wani murtuke fuska, tambayoyi ya fara yi mata kan yadda ta ce alhaji Musa ya sace su ya maida su kurkuku, duk tambayar da ya yi mata sai ta bashi amsa,
"Kin ce bayan ya maida ku kurkukun, ya sanar da ke kudirin shi na son kashe ki sannan kuma ya cire zuciyar ƴar'uwarki, a ƙarshe kuma kika yi nasarar watsa mashi acid kika kuma raunata mashi kafaɗa, duk yana mi har kika samu damar da ke kika aiwatar masa da hakan ba tare da shi ya aiwatar da ƙudirin na shi a kan ki ba?" Wani kallo ta jefa mashi tana tura baki tare da hura hanci ta ce, "Allah ne bai nufa zai cutar da ni ba duk da ya samu damar hakan, kuma dama Allah Yana yiwa azzalumi jinkiri har zuwa ranar da idan ya kama shi ba zai iya ku6uce masa ba, haka na sanar da shi a lokacin, to a ranar dama Allah ya ƙaddara dubun shi zata cika, dama na sanar da shi idan muka roƙi Allah ba kai tsaye yake taimakon mu ba don shi ba a ganin shi sai dai ya yi mana hanyar da taimakon shi zai iso gare mu, a lokacin na ce mashi in sha Allah zai ga yadda addu'ar wanda aka zalunta take tasiri har ya yi nasara akan wanda ya zalunce shi, amman sai ya ƙalubalanci hakan da na faɗa ya ce wai zai jira ya ga ta yadda taimakon Allah zai iso gare mu, nasan Allah ne ya nuna masa ishara shine dalilin da ya sa ya jinkirta aikata abun da ya yi niyya a gare mu." Ba ƙaramin burge mutane ta yi ba yadda ta kora mashi jawabin, mutane suka shiga jinjina kai wasu da murmushi akan fuskokin su.
Ƙarshe lauyan ya ƙaryata cewa Alhaji Musa ya aikata masu hakan ya ce duk sashi faɗi ne, ba yadda za ai ya samu dama irin haka amman ya kasa aiwatar masu da kudirin shi har ita ta yi nasara akan shi, in ma da gaske ne hakan ya faru da su to akwai yuwuwar bata a cikin hayyacinta ne ta ruɗe har ta kasa tantance wanda ya aikata masu hakan, yana rufe baki a tsiwace ta ce,
"Ina a cikin hayyacina! Na yi rayuwa a cikin kurkukun ƙaddara na tsawon lokaci, tun ina da shekara 11 na tsinci kaina a kurkukun, ba irin tashin hankalin da ban gani ba, an yanka mutum an feɗe gaba na, an yi mani wankan jini! Na ga abubuwan tashin hankalin da sun isa su saka ni in haukace amman hakan bai faru da ni ba, sai wannan ne zai sa in fita hayyacina har in kasa gane wanda ya aikata mini? Wannan azzalumin shine ya sadaukar da ni a kurkukun, kuma shine ya yi ma mahaifiyata asiri a ranar da ta haife ni ta tafi ta bar ni tsawon shekaru ba a san in da take ba saboda tasan wani sirrin shi da ya danganci kurkukun ƙaddara, shine kuma ya yi ma Uncle ɗina Shureim tare da makwabciyar su asiri saboda ta ce bata son shi Uncle ɗina take so sannan kuma yana jin haushin mahaifinta Sheikh Imam. Shi Elder ne! Duk abun da aka zayyana yana aikatawa wallahi..." Kuka ne ya ƙwace mata ta duƙar da kanta, duk da yadda ta yi maganar da tsawa har tana nuna Alhaji Musan da hannu ya sa6a ma dokar kotun amma alƙalin ya kasa dakatar da ita, gaba ɗaya kotun ta karaɗe da hayaniyar mutane, ƙarfin halinta ya matuƙar burge mutane, kuma ta ba mutane tausayi, hatta alƙalin ma ta bashi tausayi, umarnin a mayar da ita wurin zamanta alƙalin ya bada, kusan a tare Benazir da Owais da Shureim harda kakanninta da ƴan uwanta prisoners duk suka miƙe don su tarbe ta, kotu fa ta harmutse da hayaniya, har saida alƙalin ya bubbuga gavel ɗinsa tare da ambaton, "Order, order!" Sannan kotun ta daidaita, daga haka alƙalin ya sanar da kotu zata tafi hutu na ɗan wani lokacin kafin a dawo a ci gaba da sauraran shari'ar.
Bayan wa'adin da alƙalin ya ɗauka ya ƙare aka dawo zaman ci gaba da sauraran shari'ar. A lokacin lauyan masu ƙara ya buƙaci Benazir, Batool, Shuraim, Ummi da kuma Sheikh Imam duk suka fito ya yi masu tambayoyi, duk suka amsa mashi saidai ba komai da ya faru da su suka faɗi ba sun bar wasu abubuwan matsayin sirri, haka shima lauyan dake kare Alhaji Musa ya yi masu tambayoyin ba kamar Batool ya fi yi mata tambayoyi game da komawar su kurkuku, a lokacin har saida alƙali ya buƙaci a gabatar masa Dr Mark, Chief Owais ne ya yi ma kotu bayanin cewa ya gudu amman suna akan binciko shi za su samo shi su kawo shi kotu shima da sauran likitocin dake da sa hannu a case ɗin.
Ƙarshe dai sai da aka ƙure lauyan alhaji Musa saboda tarin hujjojin da aka gabatar a gaban kotu waɗanda ke nuna yana aikata duk laifukan kuma yana cikin elders, tun kan a dawo kan Pravin ya tabbatar ma kotu yana cikin elders don yasan shima za a samu hujjojin da zasu tabbatar da shi ba kamar da ya ga harda vedio recording ɗin alhaji Musa na cikin Cell ɗin hukumar Isod aka kunna ma alƙalin in da wasu maganganun da ya yi suka tabbatar da laifukan da ake tuhumar shi, ya san shima sun yi maganganun da Owais shiyasa ya saduda, amma ya ce ma alƙalin wllh Baba Obie ne ya yaudare shi ya saka shi cikin su ba da son ran shi ba.
Bayan sauraran tarin hujjojin lauya mai ƙara, alƙali ya tambayi lauyoyi masu kare waɗanda ake tuhuma kan ko suna da sauran abun da za su ce,
Gaba ɗaya wutar su ta ɗauke, saboda basu da wani ƙwarin gwiwa ko hujjar da zasu iya kare su, gashi akwai masu son su nemawa dattijon arziƙi sassauci saboda da yawansu mutanan da suke mutunci da shi ne, da ƙyar wani bayerabe daga cikin su ya yi ƙarfin halin miƙewa ya ce,
"Your Honor, while we acknowledge the severity of the crimes committed, we urge the court to consider the defendants ages, health, and social status. We request leniency in sentencing."
(Ya mai girma mai shari'a, yayin da muka amince da girman laifuffukan da suka aikata, muna roƙon kotu da ta yi la'akari da shekarun waɗanda ake tuhuma, da lafiyar su, da kuma matsayin su na zamantakewa. Muna neman a sassauta hukunci) Ya faɗa tare da komawa ya zauna.
Bayan nazarin da Alƙali ya yi, ya ɗan numfasa na wani lokaci, kafin ya ɗago ya dubi ilahirin mutanen dake a kotun.
Cikin kakkausar murya ya furta.
"I have reviewed the evidences presented in this case, and I find the defendants guilty on all counts, The crimes committed are among the most heinous and reprehensible imaginable..." Karanto hukuncin da kundin tsarin dokokin ƙasa ya tanada ga dukkan laifukan ya yi kafin ya dunƙule hukuncin da kotu ta yanke masu ya ce,"The court hereby, sentences each of the defendants to, Life Imprisonment without the possibility of parole (ɗaurin rai da rai batare da sakin layi ba) a cikin kurkukun ƙarƙashin ƙasa."
Sallallamin da jikokin Obie ke yi ne ya cika kotun, ba ka jin sautin komai sai na, Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un.!
Gaban Elders ya shiga faɗuwa cikin firgici da kiɗima suke ƙara zazzare jajayen idanunsu, ganin yadda reshe ya juye da mujiya, abun da suke yi ma wasu yau sune za a yi mawa, kurkukun ƙarƙashin ƙasa da alƙali ya faɗa wani kurman kurkuku ne saboda tsaronsa da uƙubarsa ya sa mutane suke yi masa laƙabi da kurkukun azaba, saboda mawuyacin abu ne mutun ya zarce watanni batare da zafin jail ɗin ya lahanta fatar sa ba, ƙuntatarsa kamar ƙabari, baka ganin kowa babu haske cikin duhu, ɗan hasken da za'a iya samu na wasu hudoji ne guda uku da ke a saman jail ɗin, dai dai da wanda zai kawo maka abinci ba zaka gansa ba, ta wata ƙaramar ƙofa da ke a jikin ƙofar jail ɗin su ke zuro maka kwanan abinci, kai kanka ba zaka san an kawo maka abinci ba, in har ba ka jiyo motsin buɗe ƙaramar ƙofar ba, daga kai sai halin ka a cikin jail ɗin nan, ba shige ba fuce, da yawa waɗanda ake kaiwa cikin kurkukun miyagun ƴan ta'adda ne masu haɗarin gaske, kamar Elders ɗin dai.
Alƙali bai dakata ba ya ɗaura da cewa, "Dukiyar su da suka mallaka ta haramtacciyar hanya, Kotu ta mallakawa waɗanda abin ya shafa.." Ya faɗa yana kallon bangaren da fursinonin Kurkukun Ƙaddara suke a zazzaune kan kujeru sun yi shiru sun nabba'a, fuskokinsu ɗauke da murmushin farin ciki, kamar su zuba ruwa ƙasa su sha, sun ji daɗin hukuncin da aka yankewa Elders, ransu fari tass, ba don Dg ya gargaɗe su akan su nutsu ba in an shiga zaman shari'ar, da ba abun da zai hana su fasa ihun murna.
"Ƙadarorinsu da suka mallaka ba bisa ƙa'ida ba, za a yi gwanjon su, abun da aka samu gwamnati zata yiwa ƙasa amfani da su..."
Alƙali Salahudeen bai dakata ba, ya ci gaba da cewa, "Bayan haka kotu ta soke duk wata daraja da muƙami na su, bugu da ƙari, kotu ta bayar da umarnin a saka sunayen su a cikin rajistar masu aikata laifuka ta ƙasa!"
Alƙali Salahudeen yana kai ƙarshen maganar shi, ya damƙi gavel ɗin gefensa mai kama da metal hammer ya buga da ƙarfi saman table ɗin gabansa,
(shari'a ta ƙare) Zauren kotu ya harmutse da hayaniyar al'umma, masu kuka suna yi, masu murna suna yi, masu 6acin rai suna yi, kowa da abun da ya dame sa.
Prison Officers tare da Soldiers ne suka tasa ƙeyar Elders suka fito da su harabar kotun, mutane daddabe da su, ƴan Jarida sai neman tattaunawa suke yi da iyalansu sun ƙi basu haɗin kai saboda tashin hankalin da suke a ciki.
A wata ƙatuwar Prison Van za a shiga da su, wasu har sun fara shiga, Musa yana ta gurnani yana tirjewa kamar 6auna, bai aune ba, ya tsinkayi muryar hajiya Sarah a kunnansa. "Ba na ta6a faɗa maka ba? In har akwai mai cutar wani tsakanin ni da kai Allah zai yi masa sakayya..." A firgice ya waigo yana fitar da hucin 6acin rai.
Tana a tsaye ta sanya baƙar abaya da niƙab.
A hankali ta zame niƙab ɗinta, ta watsa mashi kallon ƙasƙanci. "Hakkin Unaizah ne ke bibiyarka, la'ananne... "
Ta faɗa tare da tofa mashi kakin majina saman fuskar shi, ya yi wata zabura kamar zai cafkota sojoji suka rurruƙe shi, tare da ingiza shi cikin motar kamar dabba sai waiwayonta yake yi cikin ƙunci da baƙin ciki.
Yana tsaka da waiwayon ta, ya hango hajiya Layla a bayanta bakinta washe kamar wadda ta tsinci haƙori, ɗaga mashi hannu ta yi, "Allah ya raka taki gona Musa, Allah ya ƙara nauyin ƙasa, sai mun haɗu a filin hisabi na lahira.."
Ta ƙyalƙyace da dariya, wani irin baƙin ciki ne ya ziyarce shi kamar ya haɗiyi zuciya.
"Ina maka fatan sauka ƙabari lafiya, kar ka wani damu zan ci gaba da kula da mommyna.."
A ɗimauce ya kai idonsa ga Omar, yana tsaye bayan Chief Owais, wlh kwata kwata bai lura da su ba a kotun saboda bai ɗaga idonsa ya dubi kowa ba ashe duk sun hallara.
Unexpected ya tsinkayi muryar Sheikh Imam Malik a cikin kunnansa. "Musa ina tayaka murnar kar6ar sakamakon zunubin ka na duniya.. "
Cikin 6acin rai ya wurga idanunsa gurin da Imam Malik ya ke, gabansa ne ya faɗi ganin Ummi da Shureim sun saka Imam Malik tsakiya, daga gefen su Batool da Unaisah ne tare da Benazir, sai faman washe baki suke yi.
Ya Ilahi! Kamar ya fasa ihu yake ji saboda baƙin cikin da ya turnuƙe zuciyarsa, yana ƙoƙarin buɗe baki ya yi magana Isod soldiers suka turmuƙa kan shege bayan motar, suna juyo kururuwar baƙin cikin da ya ke saki.
Daidai Lokacin da Isod soldiers suka fito da baba Obie suna ƙoƙarin shigar da shi bayan motar, ƴa'ƴansa da jikokinsa suka kewaye shi, suna ta kuka kamar ran su zai fita.
Ya dinga bin su da kallo ɗaya bayan ɗaya, cikin karyewar zuciya, kallon bankwana yake musu, saboda ya san ba zai sake ganinsu ba, wannan tafiyar bata dawowa bace ta mutuwa ce.
Babu Saratu a cikinsu, a gida suka kulle ta a ɗaki, Momma ma bata halarci kotun ba, da wasu daga cikin jokokinsa.
Da raunannun idanunsa ya dubi ƴa'ƴansa cikin sanyin murya ya ce, "Ku yafe min, yawancin yaran da nake sadaukarwa na ku ne, wataƙil idan kuka yafe mini in samu salama a cikin Zuciyata"
A tare suka haɗa baki gurin furta, "Zamu yafe maka, amma ka fara amsa buƙatar mu, ka musulunta baba, muma shi kaɗai ne fatan mu, ko mun samu mu dinga saka ka a addu'ar mu."
Girgiza kanshi ya yi zafafan hawaye na sintiri kan fuskarshi ya ce, "Kuma kun sani, tuba na ba zai kar6u ba a wurin Allah, ban tuba ba saida asirina ya tonu? Bayan na sani na take sani?"
Roƙonsa suka dinga yi suna masa magiya kamar zasu haɗiyi zuciya, Sheikh imam Malik ya sanya baki ya ce ya taimaka ya amsa buƙatar ƴa'yansa shine abu na ƙarshe da zai yi musu a duniya, da ya san halin da ya jefa su da bai musa akan buƙatarsu ba, har yanzu suna son shi, kuma musuluncin da zai kar6a kan shi zai yi mawa, shi ba zai ce kar ya musulunta ba, babu wanda ke shiga tsakanin bawa da mahaliccinsa, in Allah ya so shi da rahama sai ya ga ya samu sassauci.."
Kalamai masu tausasa zuciya Imam Malik ya furta masa, amma baba Obie ya kafe akan bakansa.
Sojoji suna ƙoƙarin su shigar da shi, kwatsam! Muryar Hajiya Saratu ta karaɗe kunnuwan kowa.
"Baba! Baba...!" A ruɗe ya shiga wurga idanunsa yana ƙoƙarin ya hango ta, kamar mahaukaciya, babu kallabi ko takalma a ƙafafunta, twins suna a biye da ita, hannayen kowan nan su ruƙe da mayafinta da takalmanta, ganin halin da take a ciki ne yasa mutane suka dinga darewa suna bata hanya don ta wuce, kowa ya razana da ganin Minister of Health cikin wannan halin.
Hankulan Yayyenta ya tashi, basu san tayaya ta buɗe ƙofar ɗakin da suka kulle ta ba, wallahi da gudu ta nufi baba Obie tana ƙarasowa ta rungume ubanta tana kuka, shima kukan ya 6alle masa, hankulan kowa dake a gurin ya dawo kan su, gwanin ban tausayi, baiwar Allah mace mai rauni, a lokacin ta fidda rai da shi, cikin shesshekar kuka ta ce, "Baba ka yi haƙuri, kulle ni suka yi a cikin ɗaki shiyasa ban zo ba, meyasa zasu hanani ganinka bayan wannan ne gani na ƙarshe tsakanina da ubana. Baba ka yi haƙuri ni dai na yafe maka duniya da lahira, Ubangiji Allah Ya yafe maka, kuma zan dawwama ina yi maka addu'a akan Allah ya yafe maka zunubbanka..."
Kalaman Saratu sun karya zuciyarshi, rungumar da ta yi mashi tasa ya ji sanyi a cikin zuciyarshi.
"Saratu, mahaifin ku ya ƙi kar6ar musulunci..."
Sheikh Imam ne ya faɗa yana daga bayanta.
Baiwar Allah ita sam ta manta baban nasu ba musulmi bane, hada guzurin cazbaha ta kawo mashi wadda zai dinga yin tasbihi da ita a cikin jail.
Maganar Sheikh Imam Malik ce ta tunasar da ita, nan fa ta fara roƙon shi tare da damƙa mashi casbahar a cikin tafin hannunsa ta dunƙule masa yatsunsa don kar ya yada ta.
"Baba na roƙe ka ka musulunta saboda tsoron Allah baba, ba don saboda mu ba, don Allah ka taimaka ma rayuwana..." Tana kuka hada majina, har lokacin bata raba jikin ta daga na shi ba.
Tunkan ta ji amincewar shi ta shiga karanto mashi kalmatusshahada, cikin karyayyar murya ya dinga amsa mata har ƙarshe.
Gaba ɗaya suka haɗa baki gurin furta, "Alhamdulillah, Allahu Akhbar..."
kwata kwata ba su yi zaton zai iya furta Kalmatusshahada ba.
Suna kuka suka ce, "Mun yafe maka baba, duniya da lahira, Ubangiji Allah ya yafe maka."
At lease ya samu sassaucin radadin da yake ji a cikin zuciyar shi ganin ya faranta masu.
Sheikh Imam Malik ya tausaya masu bai san sa'ar da hawaye suka fara zarya kan kuncin shi ba.
"Baba na canza maka suna, daga yanzu Imam zamu dinga kiran ka ba Obinna ba..."
Cikin kuka ta faɗa, murmushi ya yi, idanunsa akan fuskarta a lokacin ta ɗago da kanta.
Ya sumbaci goshin ta, ya miƙa ma Hateem hannu ya matso kusa da shi yana share ƙwallarsa, shima ya sumbaci goshin shi tare da hugging nasa, Sharafudeen ya matsa ya rungume shi, tare da sumbatar goshinshi, da sauri Deen da Lateef suka rungume shi, suma ya sumbaci goshin su, Abdul Razak ya matsa ya sumbace shi, Sir Mubarak ma ya je ya rungume shi sosai.
Owais dake kallon komai shima ya zo ya yi hugging nasa tare da sumbatar goshinsa, ƴan jarida da ke kallon komai sun ma kasa mayar da hankalinsu kan aikinsu, sai aikin share hawaye suke yi, basu ta6a ganin soyayya tsakanin Uba da Ƴa'ya irin wannan ba, kowa al'ajabi ya ke yi, duk irin cutarwar da ya yi masu amma basu daina son shi ba, wannan bakomai bane face Ikon Allah.
Cikin raunanniyar murya ya furta, "Allah Ya yi maku Albarka..." Ya mayar da dubansa kan Imam Malik ya ce, "A matsayina na mahaifinsu, na baka amanar su, na mallaka maka ƴa'ƴana, ka maye musu gurbina, ga autana duka na baku amanarta, ita kaɗai ce mace a cikin ku tana da rauni, don Allah Imam ka amshi tayi na ba don mugun halina ba... "
Cikin sanyin murya sheikh Imam yace,
"Na kar6a hannu bibbiyu Imam, zan ruƙe maka amanar su, In sha Allah bazan bari su yi maraicin Uba ba..." Murmushin ƙarshe Baba Obie ya sakar musu, daga haka sojoji suka shigar da shi cikin motar.
Wani irin kuka hajiya Saratu ta fashe da shi, ta zube kan gwiwowinta tana ambaton, "Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un..!"
Cikin sauri yayyenta suka rurruƙeta tare da miƙar da ita tsaye, Hateem ya rungumeta a ƙirjin shi, suka haɗu suna lallashin ta cike da ƙarfin hali.
Suna a wannan halin, suka jiyo kukan Praveen kamar ƙaramin yaro, yana ta sambatu yana ambaton sunan Hajjaty da ƴa'ƴanshi, kusan a tare suka kai duban su kan shi, yayin da Prison Officers suka nufi ɗayar motar kurkukun, sai tirjewa yake yi, idanunsa jawur ya ke duban twins ɗinsa da Saratu da ta ɗago da kanta daga ƙirjin Hateem tana duban shi.
Haushin shi da tsanar shi ne ya cika zuciyar su, babu alamun sun ji tausayin shi.
Zaid ne kaɗai ya ɗan tausaya mashi har ya je gaban shi ya ɗan rungume shi, Sir Mubarak ya nufe shi yana zura hannu cikin trouser pocket ɗinsa ya zaro wasiƙar da Hajjaty ta bayar a bashi, ya zura mashi a cikin aljihun gaban rigar shi sannan ya ce, "Hajjaty ce ta bayar a baka, bata samu damar zuwa ba, tana a kwance gadon asibiti tana jinyar zuciyarta, idan ka samu halin karantawa ko a cikin jail ne ka daure ka karanta..."
Wata irin karayar zuciya mai haɗe da nadama ce ta riske shi, bai ƙara samun damar furta kalma ba, Prison Officers suka tura ƙeyarsa cikin Motar.
Iyalan Ɗan Iya ne kaɗai ba a samu wanda ya halarta ba, sun fi kowa fusata, dama can ba son uban nasu suke yi ba.
A kan idon kowan nan su motocin suka fuce daga arean kotuna
Kafin mutane su watse, Alƙali Salahudeen sai da ya nemi ganawa da ahalin Obinna, musamman ya zauna da su a office ɗinsa bayan ya bayyana musu irin halin da ya shiga na jin abun da Obie ya aikata, ya kuma jajanta musu sannan ya jinjinawa Owais da ƴan team ɗinsa bisa ƙoƙarin su na kamanta adalci da gaskiya.
Kafin barin su kotun, chef na gidan Owais wanda ke kula da ɗakin Natasha ya kira Owais a waya cikin tashin hankali ya faɗa masa cewa ya je kai mata abinci, ya iske ta kwance ƙasa rai hannun Allah, tana yin bleeding ta hanci da baki, yanzu haka sun garzaya da ita Obie Hospital.
Hankalin Owais ba ƙaramin tashi ya yi ba, a hanzarce ya faɗa ma su Ummi abun da ke faruwa da Natasha, ya ce ma Sajeed da Sajeeda su shiga motarshi, a gaggauce suka shige cikin motocin su, a lokacin Sarah ta ji komai itama ta shiga motar Omar saboda ta ƙudiri aniyar sai ta ɗanɗana mata raɗaɗin da ta ji na abun da ta yi ma ƴarta Unaizah.
Lokacin da suka ƙaraso Asibitin bayan da suka fito daga motocin su cikin sauri suka nufi ciki.
Kaitsaye suka wuce ICU, suna ƙarasawa bakin ƙofar ɗakin, sai ga Docs din dake dubata sun fito fuskokinsu babu annuri.
Gaba ɗaya suka ruɗe fargaba ta cika su.
Owais ya tambayi Doc din meke damunta? Ya jikin nata?"
Cikin karyayyar murya doc ɗin ya ce "Unfortunately, the patient's condition has taken a turn for the worse, Her blood cancer, specifically Leukemia has progressed rapidly, and we're seeing signs of severe bone marrow failure...." Salati Ummi ta zabga tare da ɗaura hannayenta saman kanta, Hajiya Sarah da ta zo da niyyar ta ɗauki fansar abun da ta yiwa ƴarta koda jin bayanin likita sai ta ji jikinta ya yi sanyi.
A ruɗe Chief Owais ya dubi ummi yana tambayarta dama tana da blood cancer? Cike da damuwa ta ce batasan komai game da ciwonta ba, in ma ta daɗe a jikinta bata ta6a faɗa mata ba, bata ma tunanin Natasha tasan tana da leukemia.
Doc ya katse maganar Ummi da cewa,
"We're doing everything possible to manage her symptoms and stabilize her condition, but I must be honest with you the prognosis is grim she's at high risk of sepsis, organ failure, and even cardiac arrest."
We're monitoring her closely and adjusting her treatment plan accordingly, but I want to prepare you for the worst, It's possible that we may lose her at any moment...."
Gaba ɗaya damuwa ta ƙara mamaye zuciyar su, Owais kamar yasan ba zata rayu ba ya yi dubarar zuwa da ƴa'ƴanta, kwata kwata ba su san gurin wa aka kawo su ba.
Shi ya ruƙo hannayensu a cikin nashi, ya shigar da su ɗakin, sauran ma duk suka shigo, Ummi ta zauna kan chair din gaban gadon, ta ruƙo hannun Natasha dake a kwance cikin mawuyacin hali, fuskarta asanye da oxygen mask da wasu na'urorin dake taimaka mata, Hajiya Sarah tana a tsaye daga bayan Ummi ta ƙura idanunta akan Fuskar Natasha tana tuna abubuwan da aka faɗa mata ta yiwa ƴarta, amma da ta tuna cewa Mahaifin Unaizah ne ya ja mata, hakan yasa ta ji zata iya yafe mata, musamman da ta ga halin da ta ke a ciki.
Da hannu Owais ya nuna mata Hajiya Sarah ya ce, "Matar Jan Wuya ce, Mahaifiyar Unaiza."
Zare blue eyes dinta ta yi, cikin ruɗu da razanar jin maganar shi take kallon Sarah.
Hawaye ne suka ciko idanunta, jikinta na kerma ta soma ƙoƙarin cire Oxygen mask ɗin fuskanta, da sauri Ummi ta dan ɗage mata shi kaɗan ta yadda zata iya yin magana.
Cikin shesshekar murya da gajarcewar numfashi Natasha taita kokarin furta ta yafe mata, ta yi nadama, ta yi danasanin abun da ta yi ma Unaizah, Musa ne sanadi, kuma hada ƙarin bata san wanene shi ba, da tun farko tasan manufar shi akan ta, da ba abun da zai hana ta kar6e ta, bata ta6a cutar da Unaizah ba, tana son ta, tana jin ta kamar ƴar da ta haifa, duk da tasan bata ba ta tarbiya ba, amma ta yi haƙuri tasan ta biyewa son zuciya, bata raini Unaizah yadda ya kamata ba..."
dakyar ta ke iya magana saboda raɗaɗin da jikinta ke yi mata.
"Who's she"? Gabriel ne ya tambaya.
A hankali Owais ya dube su, suna tsaitsaye bakin gadon hannunsu ruƙe cikin na juna.
"Mahaifiyar ku ce Sajeed, kamar yadda mahaifinku ya raba Sarah da ƴarta batare da saninta ba, itama haka ya rabata da ku bayan da ta haife ku, batasan kuna a raye ba..."
kallon juna suka yi cikin ruɗu da al'ajabi.
Sajeeda da ta gama ruɗewa ta ce, " Idan wannan ce mahaifiyar mu toh wacece ɗayar wadda ta raine mu?" Girgiza kai ta yi. "She'll never be our mom, I don't like her, she has no morals."
yayin da ta ke yin maganar Natasha tana kallonsu idanunta cike tab da ƙwallar baƙin ciki da takaici.
Sajeed ya ce, "Kunsa na ruɗe, tayaya wannan zata zama mommynmu? Bayan mommynmu tana nan, wadda ta haife mu ta kuma raine mu!"
Cikin rawar murya ta ce, "I know I don't deserve for you to call me Mother, Redneck betrayed me, separated you from me, I never knew I had you, but I want you to know it's not my fault Please forgive me, Forgive me..." Ta faɗa tana kuka.
"..Ku duba halin da nake a ciki, I'm not going to live, I want you to call me Mommy, just once, and hug me, I love you like my soul, I really wanna feel the warmth of your bodies against mine.."
ta ƙarashe maganar tana kuka ta dubi ummi, "Ku sanya baki, ku taimaka min, ina son su kamar raina, ina so na ji ɗumin jikin su.."
Cikin karyayyar murya Ummi ta dube su. "I'm sorry, As she said, it's not her fault, your father cheated on her and lied to her she didn't know you were alive, all she knew was that you died at birth, No one will love you as much as your mom, she carried you for nine months in her womb and labored, The one you're talking about is not your mother, she's his mistress"
Maganar Ummi ta yi tasiri a cikin zukatan su.
Owais ya ce, "Ku duba halin da ta ke a ciki, mu tausaya mata, bana so ku yi danasani daga baya.."
Cikin sanyin jiki suka matsa kusa da ita, Ummi ta miƙe tare da taimaka mata ta miƙe zaune, Sajeeda ta rungumo ta sosai cikin shesshekar kuka ta furta. "Forgive me, Mommy, but I love you, I don't want you to die, ina sonki, bana son ki mutu, Ina so mu rayu da ke, kada ki tafi ki bar mu..."
tsantsar ƙaunar su da son su ne ya mamaye zuciyarta, suma haka su ka ji son ta.
Bayan da Sajeeda ta raba jikinta daga na Natasha, ta matsa ma Sajeed shima ya rungumota tighly kamar zasu koma mutun ɗaya, "Tun da na ganki raina ya bani muna da alaƙa saboda na ji tsantsar ƙaunar ki a zuciyata, ban so muka haɗu a ƙurarren lokaci ba, amma za mu yi maki addu'a, Allah ya baki lafiya mommy, muna son ki fiye da yadda muke son kan mu, zamu baki kulawa mommy, zamu kasance a tare dake har sai kin ji sauƙi.."
Kukan farin ciki ne ya kubce mata, ta ƙara ƙanƙame shi, ta miƙa hannunta dake kerma ta tallabo Sajeeda ta haɗa su ta rungume a ƙirjinta, sautin koke koken su ya cika ɗakin.
Kowa da ke a gurin ya tausaya musu.
Sun daɗe a manne da juna babu mai lallashin wani sai daga bisani Ummi ta lallashe su ta samu ta shawo kan su.
A hankali Natasha ta mayar da dubanta ga hajiya Sarah dake ta share hawayen ta.
In a broken voice ta ce, "I didn't do you justice, I had the opportunity to meet my children, and you never saw your daughter until she died, I wish I could go down on my knees and ask you to forgive me, but I can't, my body is weak..." Tana magana twins ɗinta suna share mata hawayenta.
"Amma a madadin Unaizah da kika rasa, ga twins ɗina, na bar maki su har abada, ban cancanta na zama mahaifiyar su ba, na san ma bazan rayu ba, ki ruƙe su a gurin ki, na bar maki su.."
Cikin shesshekar kuka Sarah ta ce, "Na yafe maki Natasha, ba laifinki bane, laifin Musa ne, kuma shima yanzu haka yana a prison, Bazan kar6i ƴa'yanki ba bayan kina a raye, ki ruƙe abunki, babu wanda zai iya maye gurbin ki a gurin su..."
Girgiza kai Natasha ta yi tana ƙoƙarin buɗe baki da niyyar ta furta kalma, kwatsam suka ga ta fara jijjiga, numfashinta ya dinga kokawar ɗaukewa, ta dinga zubda gumi.
Cike da fargaba suke kallon ta cikin tashin hankali, Sajeed ne kaɗai ya yi tunanin biya mata shahada, gaba ɗaya suka shiga maimaita mata don sun fahimci ba rayuwa za ta yi ba.
Cikin kuka twins ɗinta suke faɗin kada ki mutu mommy, muna sonki, muna son mu rayu da ke, kar ki mutu ki bar mu a lokacin da muke cikin buƙatar ki!"
Sajeed da ya cire rai da ita bai daina furta mata shahada ba yana faɗin Mommy ki biya don Allah idan kika musulunta Allah zai yafe maki zunubanki, kuma muma zamu sa mu yi maki addu'ar samun rahama..." Da ƙyar da siɗin goshi suka samu Natasha ta biya shahada da numfashinta na ƙarshe.
Alƙalamina bazai iya misalta muku raɗaɗin da twins ɗin Natasha suka ji ba na rashin mahaifiyar su, bayin Allah sun zama abun ban tausayi a ranar da suka fara ganin mahaifiyar su a ranar ta mutu, Musa ya cuce su, wata shari'ar sai a lahira.
Ummi ta yi kukan rashin Natasha, Chief Owais ya yi danasani da tun farko bai yi saurin haɗa ta da ƴa'yanta ba, hatta hajiya Sarah saida ta zubda mata ƙwalla saboda tausayin ƴa'yanta da ta bari. A ƙarshe Hajiya Sarah ce ta kar6i twins ɗinta da hannu bibbiyu.
😭😭😭
________________________________
Haƙiƙa dangin baba Obie sun fuskanci jarabawa mafi tsanani a rayuwar su.
Mutane saida suka hana Ahlin Obie sukuni, har ta kai ga basu iya buɗe wayoyinsu ko su fita waje batare da ƴan jarida da mutane sun farmake su ba, gaba ɗaya fita ta gagare su, suka killace kansu a cikin Estate ɗin su, saboda surutun mutane da masu barazanar lahanta su.
Sun fuskanci barazana da tozarci daga gurin abokan hamayyar su na jam'iyoyin da ke adawa da su.
Duk wanda ya ra6e su sai laifin baba Obie ya shafe shi, hakan yasa abokan su ƴan siyasa suka dinga zame jiki daga gare su, kowa tsoro ya ke kada su shafa mashi baƙin tabo, babu irin 6atancin da ba a yi masu ba, cin mutunci da ƙazafi iri iri ba wanda ba a yi masu.
Surukansu suka fara ƙoƙarin yanke alaƙar su da su, waɗanda suka fi ɗaukar zafi, mahaifin Her Excellency Muhibbat da yake jan wuya ne babban mutum ne, bai son duk wani abu da zai ta6a mutuncinsa, tun a ranar da Muhibbat ta kira sa tana kuka ta bayyana masa komai da ke faruwa ya ce ta dawo gida babu ita ba Abdul Razak, ya yanke alaƙar su, da yake halinta ɗaya da na Ubanta bata musa mashi ba, duk da tana son mijin nata amma ta biyewa mahaifinta, batare da sanin kowa ba ta gudu daga Obie estate ta tafi gidan Ubanta da ke a nan Abuja.
Her excellency Jameela ma a ranar da suka ji komai, ta koma gidan ubanta mai martaba sarkin Adamawa saboda tsoron kada abun ya shafe ta duk da itama bada son ranta ba, su dukansu ma babu wadda ta yi hakan don son ranta, saboda suna son mazajensu da ƴa'yansu, amma ba yadda suka iya, baba Obie ya karya zukatan su, ya ha'ince su ya kuma ci amanar su, ya yaudari yardar da suka yi ma shi, da suna alfahari da kasantuwar su surukan shi yanzu ya 6ata komai, abun da ya fi ƙona masu rai, jariran su da ya dinga sadaukarwar, shi yasa ransu ya 6aci suka zuciya.
A yanzu ƴa'ƴan Obie sun gane waɗanda suke tare da su saboda Allah, da waɗanda suke tare da su saboda arziƙinsu da kuma ɗaukakarsu.
_Ba zaka ta6a gane me sonka tsakani da Allah ba har sai musiba ta afka maka a sannu zasu dinga guduwa suna barinka_
Senate Lateef bai samu matsala da Hajiya Madina ba, mahaifinta malamin addini ne koda ya ji komai da ya faru daga jiharsa ya zo har Abuja ya ziyarce su don ya yi masu jajen abun da ya faru da su, ya kuma haɗa da yi masu nasiha akan su yi haƙuri kada su sare Allah yana a tare da su a sannu komai zai zama labari..
Hakan ba ƙaramin faranta ransu ya yi ba. Baiwar Allah Turai bata bari ta karya zuciyar mijin nata ba, sai ma lallashin shi da ta dinga yi tana kwantar masa da hankali saboda ganin halin damuwar da ya shiga.
Sharafudeen bai samu matsala da Gimbiyarsa ba saboda ita ɗin jininsa ce, abun da ya shafi family ɗinsa ya shafe ta.
A bangaren Prime minister Hateem tabbas iyalinsa sun girgiza da jin abun da baba Obie ya aikata amma basu bari sun baiyana damuwar su ta yadda zai karya zuciyar Hateem ba, Gimbiya Mujeedat ta yi jarumta gurin danne damuwarta da kwantar masa da hankali, wallahi kowa ya yi tunanin Sheikha Mujeedat ce ta farko da zata fara neman yanke alaƙa da su saboda martabar royal family ɗinta amma sai ta basu mamaki, ta ja mijinta a jiki, ta nuna ta ƙara jin ƙaunarsa da tausayinsa, kuma ta ce in ma yana tunanin zata juya masa baya to ya daina, bata aure shi don su rabu ba face don su rayu na har iya rayuwar su, don haka laifin babansa bai shafe shi ba, kuma ba zata bari mijinta da ahlinsa su tozarta a idon duniya ba, zata bada gudummuwarta don ganin mutuncinsu bai zube ba.
Gimbiya Mujeedat ta ƙarfafa masu ta kuma basu mamaki sosai, sai dai Hateem bai samu nutsuwar zuciya ba, saboda yasan yadda royal family suke, sun ƙi jinin abun kunyar da zai zubar masu da mutuncin su a idon duniya.
Yana ta jin fargaban kada iyayenta su neme shi, Unexpected sai ga kiran mahaifin Mujeedat, Emir Khalid ya shigo wayar Hateem da kan shi ya kira shi ya ce ya ji abun da ke faruwa a family ɗin su, ya zo ya same shi a fadar shi yana son ganin shi.
Tun da suka yi wayar nan kwanciyar hankali ya ƙarewa Prime minister saboda zullumin me zai biyo bayan kiran nasa, don wlh ji yake zai iya barin komai har muƙaminsa amma ba zai iya rabuwa da Mujeedat ba, koda za a kashe shi ne, saboda tsantsar son da yake mata.
Abu biyu ya haɗe mashi, ga gwamnatin ƙasar Canada suna jiran dawowar shi, don har ya zarce kwanakin da ya ɗiba, sun ji shiru ko sun kira baya picking kuma ba ya basu response na saƙonninsu.
A lokacin duniya ta ji komai da ke faruwa da ahalinsa, amma gwamnatin kasar Canada da ƴan ƙasar sun fi so su ji daga bakin shugaban ƙasar nasu.
Da ya ga bashi da wata mafita, ƴan uwansa suka bashi shawarar ya yi magana da Deputy ɗinsa in ma mulkin zai ajiye sun goyi bayan shi don sun san a halin yanzu ba lallai gwamnatin Canada ta bar shi ya ci gaba da yin mulki ba saboda abun kunyar da mahaifinsu ya aikata.
Live video ya yi a presidencial page ɗinsa tare da press, ya bayyana masu halin da ya ke a ciki ya ce su yi haƙuri da abun da zai faɗa, yasan ba lallai hukuncin da zai yanke ya yi masu daɗi ba, amma a yanzu ya yi raunin da ba zai iya ci gaba da shuwagabancinsa ba, kuma ba zai iya dawowa Canada ba, saboda ba zai iya tafiya ya bar ƴan uwansa a cikin mawuyacin hali ba, don haka su yi masa afuwa, su nemi wani adalin shugaban da zai maye gurbin sa... "
Wannan Live video ɗin da prime minister ya yi da manema labarai cikin ƙanƙanin lokaci ƙasar Canada ta dauka, labarin murabus ɗin sa ya tayar da tarzoma a duk faɗin kasar Canada, kuma mutane da dama sun yi baƙin ciki da matakin da ya ɗauka kuma sun nuna ƙin amincewar su, haka zalika mutanen da ke kula da shi a tsawon wa’adin mulkinsa sun ƙuduri aniyar shawo kan shi don ya koma Canada ya ci gaba da aikinsa saboda su basu gaji da shi ba, bayan haka bai yi laifin da doka zata amince da yin murabus ɗinsa ba, laifin mahaifinsa bai shafe shi ba, har yanzu suna son shugaban ƙasar su.
Bayan da yayi wannan Live video ɗinne, ƴan uwansa suka ƙarfafa masa gwiwa akan ya amsa kiran surukinsa, bai yi ƙasa a gwiwa ba, ya bar ƙasar tare da iyalinsa, tafiyar sirri suka yi saboda jama'a dake neman su farmake su ruwa a jallo.
Abun da ya ƙara sagar masu da gwiwa rashin tuntu6ar su da Familyn mahaifiyarsu ba su yi ba, a zaton su sune mutane na farko da ya cancanta su ja su a jiki su lallashe su akan mummunar ƙaddarar da suke fuskanta amma sai suka ji shiru daga 6angaren su, hakan ba ƙaramin karya masu zuciya ya yi ba, duk sai su ka ji ba daɗi, suna ganin kamar suna gudun su ne saboda kada martabar family ɗinsu ya rushe, gashi kuma su ne kaɗai dangin da suke da shi a duniya.
Saida damuwa ta kusa illata su, gaba ɗaya suka yi murabus daga kan muƙaman su saboda depression da suke fama.
A lokacin da gwiwarsu ta sage, suka raunata, basu da madogara da ya wuce Allah da Sheikh Imam dake zaryar zuwa yana ƙarfafa masu gwiwa, sai da suka fidda rai da komai, a wannan Lokacin ne kuma Allah ya juye al'amarin yadda basu ta6a zata ba.
Dangin da suke ta jira su ji daga gare su suka yi masu zuwan bazata, gaba ɗayansu, tun daga kan kakanninsu na 6angaren Uwa, tsohon sarkin ƴarbawa, har izuwa kawunnan su, da yayan mahaifiyarsu mai martaba sarkin ƴarbawan jihar Lagos mai ci a yanzu gaba ɗayan su, suka zo Abuja a cikin family private jet ɗin su tare da royal guards ɗin da ke basu kariya.
Tun a airport ƴan jarida suka dinga dandazo gurin neman ƙarin bayani daga gare su, sai dai ko kusa da su basu isa su ƙarasa ba, saboda royal guards ɗin da ke a kewaye da su.
Kuma duk a rana ɗaya Edward's family na bangaren mahaifiyarsu Hateem suma suka zo Nigeria, kowa yasan irin power ɗin da ke gare su, sune ake ma laƙabi da jinin siyasa, they are famous politicians tun kaka da kakanni.
Sun ji komai da ya faru daga bakin Momma da ta kira yayanta ta sanar da shi, family ɗinta sun girgiza da jin tana a raye, sun kuma fusata da jin zaluncin da mijinta ya yi mata, basu ta6a zaton haka daga gare shi ba, hakan yasa suka yi takakkiya tun daga Canada suka zo Nigeria a family jet ɗin su.
Silar zuwan su abubuwa da dama sun faru, haƙiƙa Ahlin Obie sun yi farin ciki da zuwan dangin iyayensu mata, sun zo a lokacin da suke a mawuyacin hali, a kuma lokacin da suka yanke ƙauna da komai na duniya, waɗannan powerful families ɗin guda biyu suka haɗa kansu, suka tsaya masu tsayin daka, suka zama ƙashin bayansu, ɗari bisa ɗari suke goyan bayan su. A Obie Estate suka zauna tare da su, saboda sun yi alƙawarin ba zasu ta6a bari ƴa'yan Obinna su tozarta ba, kuma za su yi adawa da duk wani wanda ke kokarin 6ata masu suna da masu sukar su, akan abun da mahaifinsu ya aikata, sannan suka ce basu yarda da maganar murabus ɗinsu ba, dole su koma kan muƙaman su tun da ba mutane ne suka cire su ba, kuma ba mahukunta bane suka yanke masu hukuncin sauka daga kan mulkinsu ba, bayan haka ba su yi laifin da za a tsige su daga power ba. Wannan maganar da suka yi, sun yi ta ne a gaban manema labarai kafin ka ce me tuni maganar ta yaɗu ta ko'ina zancen ake yi a faɗin duniya.
Abokan hamayyar su da suka matsa masu lamba, ta hanyar ƙulla masu makirci don su 6ata masu suna su kuma sa a tsige su daga kan muƙamansu, yanzu faɗan ya koma tsakanin Powerful families ɗinnan biyu da abokan hamayyar su,
Har ƙara suka kai ahalin Obie kotu akan a yi adalci akan cin amanar ƙasa da mahaifinsu ya yi da kuma zaluncin da ya yi, ƙarshe haƙar su bata cimma ruwa ba, cikin rashin sa'a, kotu ta yi watsi da ƙarar, inda ta ce bata gamsu da hujjojin da suka gabatar ba, ƴa'yan Obinna basu da alhakin laifin da baban su ya aikata!"
Da suka fusata da hukuncin kotun, ƙungiyar maƙiyansu suka shirya ɗaukar mataki da kansu, suka fara ɗaukar hayar gidajen talabijin da ƴan jarida da kuma mutane karnukan ƴan siyasa don yaɗa mummunar manufar su ga ahlin Obie,
Amma duk a banza, haƙar su bata cimma ruwa ba, babu abun da suka rage su da shi, sai ma farin jinin da suka ƙara masu, mutane sun ƙi basu goyan baya..
Basu daddara ba koda suka ga ba su yi nasara ba, sai suka ɗauki hayar protestors suka bazu kan titunan Abuja suna ta nuna adawar su akan basu yarda abar ƴa'yan Obinna su ci gaba da mulki ba, dole a yi masu adalci a sauke su daga kan muƙamansu, a kuma hukunta su akan abun da babansu ya aikata saboda suma suna sane da sa hannunsu, in ban da raunin wayou tayaya za'a ce tsawon shekarun da suke a tare da shi basu ta6a sanin abun da yake aikatawa ba! su basu yarda ba, a bincike su dukiyar su bata halal bace, suna da sanya hannu!
Maganganu iri iri marasa daɗi na 6atanci suke faɗa a kansu, ƙoƙari suke su ɗaura masu laifin baba Obie.
Ma su adawa da su ba irin cin hancin da basu ba alƙalai ba, da masu zanga zanga amma gaba ɗaya basu yi nasara ba, Allah ya nuna masu iyakar su, ƴa'yan baba Obie kainuwa ne dashen Allah, sai ya zamana kamar suna ƙara masu farin jini da tausayawar al'umma, dama an ce hassada game rabo taki ce.
Al'umma suka dinga yin zanga zanga akan tituna da ta yanar gizo hannayensu ruƙe da alluna mai ɗauke da taken zanga zangar da suke yi.
Suka cika kunnuwan al'umma suna faɗin,
_Justice for Obinna's sons! Justice for Hajiya Saratu, Minister of Health! Justice for President Sharafudeen! Justice for Senate President Lateef! Justice for Hateem Obinna! Justice for Sir Mubarak, Chief of Army Staff! Justice for Lagos State Governor Abdul Razak! Justice for the Governor of Kaduna, Deen Obinna! They are not criminals, their father's crimes do not affect them, They are innocent, We will not allow them to be removed from power, We support them and will oppose anyone who challenges their positions!_
Wannan zanga zangar ta yi silar dawo masu da farin cikin rayuwar su, ganin yadda mutane suke nuna ƙauna da goyan bayansu
A can Canada suma sun fara zanga zanga a online suna nuna ƙin amincewar su da murabus ɗin Hateeem,
_"We don't have a leader other than Hateem! We love Hateem! We want him to come back and continue to protect our country! Grant him justice! We do not want to remove the president of our country! Let justice be served to him, his father's guilt will not affect him, He is a good person and a just leader, We accept him and we support him_
We will not stop! We will do our best to bring back our president
Farin ciki kamar zai kashe su, koken da mutane suke yi akan su gwamnati ta amsa buƙatar su, tare da cewa su dama basu tsige su daga muƙamansu ba, sune suka nuna basu so amma yanzu tunda mutane sun nuna ƙin amincewar su don haka zasu dawo kan muƙamansu sannan sun basu hutu har zuwa lokacin da suka ji zasu iya ci gaba da ruƙe muƙaman nasu, yanzu mataimakan su ne ke ci gaba da gudanar masu da mulkin nasu.
Yayin da su kuma suke a estate ɗinsu, a ƙarƙashin kulawar families ɗinsu
Abokan hamayya sun ji kunya, don dole suka ajiye makaman yaƙin su saboda ba yadda zasu yi da dangin Obinna sun yi masu fintinkau, Allah ya kare abunSa, ba yadda suka so su wulaƙanta ba.
Ɗaukakar su ta nunku, arziƙin su ya bunƙasa, ko'ina zancen su ake yi, abokanan hulɗar su da suka juya masu baya tuni sun fara yin nadama, daga baya suka dinga zuwa neman yafiyar su tare da jajanta masu abun da ya faru da su.
Haka zalika surukansu da suka yanke alaƙa da su, kunyar duniya ta ishe su, tuni sun gane kuskuren su na yanke alaƙar su da su, ganin ba yadda suka zata ba, hakan yasa suka zo har estate ɗinsu don su jajanta musu da kuma neman sasanci tsakanin su da matayansu.
yanzu fa duk wanda ya ra6i ahalin Obie sai ya yi farin jini a gurin al'umma
Ƴan uwa da abokan arziki sai zuwa suke yi suna jajanta masu.
Duk wannan abun da ya faru bayan zuwan danginsu, Hateem baya a Nigeria, tun lokacin da aka kammala shari'ar Elders yana a Dubai tare da iyalinsa domin amsa kiran da His highness ya yi mashi, tun bayan tafiyar su babu wanda yasan me ya faru? Me ya sa surukin nasa ya nemi ganinsa? Kwata kwata basu ji daga gare shi ba, kuma sun damu da su san a wani hali ɗan uwan nasu ya ke a ciki, saboda bai neme su a waya ba, ko sun kira wayarsa bata shiga, haka matarsa da ƴa'yansa duk basa samun su a waya, ko meya faru ta bangaren prime minister
Isod agents basu ƙyale kowa ba, sun bada himma, duk wani mai sa hannu a kurkukun ƙaddara saida suka kama shi, da waɗanda ke a Nigeria da waɗanda ma ba a Nigeria suke da zama ba, sai da suka bi diddigin su, suka dinga yi masu ɗauki ɗai ɗai suna damƙa su ga hukumar ƙasashen su.
Da bincike ya yi bincike saida suka gano mutane sama da ɗari biyar waɗanda suka ta6a sadaukar da jininsu don biyan buƙatar kan su, gaba ɗaya suka gurfanar da waɗanda suka ta6a yin sadaukarwar a kotun ƙasashen su, bayan haka suka mayar wa dangin su da ƴa'yan su, sai gashi gaba ɗaya sun yi nasarar gano dangin fursinonin hannun su, wasu turawa ne, wasu larabawa, wasu ƴan yankin Asia ne, wasu kuma ƴan Africa ne.
haka suka dinga bankaɗo sirrin masu sadaukarwa ta hanyar amfani da littafin rijistar fursinoni🔥
Idan muka koma bangaren ƴa'yan baba Obie suma Owais ya mayar masu da ƴa'yan family din su da suka rage.
Daga cikin jikokinsa na kurkukun ƙaddara, da suke a raye, akwai Parveen ɗiyar Hajiya Saratu wadda Praveen ya sadaukar da ita, Azeeza da Jemimah ƴa'yan Sir Mubarak da Hajiya Turai ne, asalin sunan Jemaimah Naja'at ne sunan mariganya matar Sir Mubarak, bayan su sai ɗan gidan Prime Minister, Last born ɗin shi Omair, wanda aka fi sani da Danish wanda a yanzu baya a raye.
A bangaren Deen da matarsa Hajiya Jameela suma sun samu triplets cikin ƴa'ƴan su da suka rage wanda Obie ya sadaukar.
Hanna, Hibba, Hawwa, babu wanda yasan ƴan uku ne saida Owais ya gano a cikin littafin rijistar.
A bangaren Abdul Razak da Her excellency Muhibba, suma Allah ya azurta su da samun twins cikin waɗanda Obie ya sadaukar, su ne Rubina da Mubeen, wani iko na Allah Hajiya Muhibbat kamar ta yi kaki Rubeena kamanninsu ya 6aci.
Senate Lateef shima ya samu ƴayansa biyu daga cikin prisoners Yasmin da Sarah.
A bangaren Mr. President shima Allah Ya azurta shi da samun last born ɗinsa, bakowa bane face Javed wanda asalin sunan sa shine Hateem, kamanninsa sak da na ƙanwar Owais Hindu, launin fata ne ya bambanta su.
Abun da ya fi ɗaurewa Unaisah kai, jin cewa Deeja da Haris ƴa'yan kawun daddynta ne Abdallah Buzu da Hajiya Adama hakan na nufin ƙannan Uzair ne, in ba zaku manta ba, Haris ya ɗare Deeja da shekaru kusan biyu, ko a prison Haris ne tsaran Danish, kowa ya yi mamaki ashe ƙaunar da ke a tsakanin Deeja da Haris ta ƴan uwantakar jini ce.
Ita ma Hajjaty, Owais ya mayar mata da yaronta Naufal, gaba ɗaya lokacin da ya mayar masu da ƴa'yan a ranar da ya shirya musu walima a gidansa suka haɗu gaba ɗayan su, ya buɗe littafin rijistar a gaban kowan nan su ya zayyana musu sunayen ƴa'yansu da Obie ya sadaukar da kuma waɗanda suka rage a raye, ya kira sunan su ya nuna masu iyayen su, murnar da suka yi a wannan lokacin bata misaltuwa, daɗi kamar zai kashe su, daga su har iyayen nasu tsantsar farin ciki ne ya mamaye zukatansu, wata irin ƙauna mara maisaltuwa ta shiga tsakaninsu a ƙanƙanin lokaci.
kwata kwata basu nuna ƙin amincewar su ga iyayen su ba saboda Owais ya riga da ya bayyana musu wanda ya sadaukar da su kuma sun halarci kotu sun gan su sun kuma ji hukuncin da aka yanke musu.
A ranar da U.S Armies suka yi masu bankwana zasu koma America, sun yi kukan rabuwa da su, gaba ɗaya prisoners tare da senior agents suka raka su Airport, U.s Armies sun ji zafin rabuwa da su saboda shaƙuwar da suka yi da juna, ba zasu ta6a mantawa da su ba a rayuwar su, ta silar aikin da suka yi sun samu awards daga ƙasashe daban daban, tun kafin ma su koma America har president ɗinsu ya yi masu alƙawarin za a ƙara masu matsayi idan suka dawo, Prisoners sun ji kewar rabuwa da su, suma baza su ta6a manta taimakon da suka yi masu ba, sune na farko da suka fara tsamo su daga dajin Evil Forest, ƙaddara ce ta haɗa kuma ta raba. Har bayan tafiyar U.s armies basu daina jimamin rabuwa da su ba.
game Bukatar Kurkukun ƙaddara Ya tuntu6i number din nan 08103884440