DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥
BAYAN WANI LOKACI 🔥
Kasantuwar gwamnati ta kar6e ƙadarorin Elders yasa suka fara tunanin barin Obie Estate kafin wa'adin da aka basu ya cika, sai da suka fara yin shawarar game da inda zasu mayar da iyalin su, da har sun fara shawarar zasu mayar da su ƙasar Canada su zauna a family House ɗin su, a ganin su zai fi masu kwanciyar hankali.
Momma ta ce shawarar su bata yi ba, tayaya zasu mayar da iyalan su Canada su kuma suna a Nigeria, duk da suna da halin da zasu iya zuwa duk ƙarshen mako su dubo su, amma ya za su yi da matasan ƴa'yansu da ke buƙatar kulawar su? Suma kuma suna son su a kusa da su, ta ce amma su bata lokaci zata yi shawara da family ɗinta dana mahaifiyar su Sir Mubarak tun da sun ce su faɗa musu kome ake ciki za su taimaka musu.
Batare da sanin su ba, Momma ta yi shawara da families ɗin, ta bayan fage suka fara nema masu gidajen da zasu zauna, cikin Ikon Allah, suka gano wani sabon katafaren housing Estate da ba a jima da kammala shi ba, a nan cikin garin Abuja ya ke, da suka yi bincike sai suka gano mamallakin Estate ɗin bakowa bane face Deputy President Ahmad Musa.
Momma ce ta nemi alfarmar haɗuwa da shi, a ranar da ta je guest house ɗinsa tare da Imam Malik suka ziyarce shi, da yake yanzu Imam Malik shine na hannun damanta, da shi ake komai.
ya yi masu kyakkyawar tarba cikin mutunta juna, bayan sun tattauna game da sabon Estate ɗinsa, da yake yasan komai da ya faru kuma yasan su wa zata siya mawa, hakan yasa ya ce zai yi musu ragi saboda Allah saboda kuma zumuncin dake a tsakaninsa da Sharafuddeen, hasalima ba siyar da shi zai yi ba, ya yi sa ne saboda ya zuba ƴan haya a cikin sa amma dai zai bar musu shi.
A ƙalla Estate ɗin yana ɗauke da gida je sama da arba'in a cikin shi, tare da private facilities, bai kai Obie Estate ba, amma yana da girma ya haɗu saboda amenities ɗin dake cikin sa, komai da mutun zai buƙata akwai a cikin estate ɗin, darajar sa ba ta kananun kudi ba ce amman duk da haka ya ce zai yi masu sauƙi.
Da yake harka ce ta arziƙi, basu nemi ragin yadda ya faɗa musu ba, nan take momma ta kira Elder Brother ɗinta ta faɗa mashi, ta kuma kira sarkin ƴarbawa ta sanar da shi, ba tare da 6ata lokaci ba dangin biyu suka haɗa masu kudin saidai wanda bangaren dangin momma suka bada sun fi yawa. Bayan da suka gama ciniki, suka biya shi kuɗin, ya damƙa musu takardun shaida da yarjejeniyar mallaka musu Estate ɗinsa a gaban lauyoyin su.
Lokacin da ta kai musu takardun Estate din, sun yi murnar da ni kaina bazan iya misalta muku ita ba, ko sisin su babu a ciki.
dangin su sun faranta masu rai, sun gatanta su, sun nuna masu soyayya mara iyaka.
Abu ɗaya da ya rage musu kafin su koma shine kayan furniture ɗin gidajen, batare da 6ata lokaci ba Prime minister ya ce su bar komai a hannunshi, ba ya buƙatar su haɗa kuɗin su zai ji da wannan.
Daga shahararren Companyn furnitures na kasar Canada ya yi musu Order na komai da za su buƙata a cikin gidajen dama estate ɗin gaba ɗaya, kaya masu kyau da tsada, Cikin sati guda, ma'aikatan companyn suka gama yi masu jere, abun sai wanda ya gani.
Bayan da su sheikh Imam Malik da ƴan kungiyar su ta malaman ahlussuna suka yi masu safkar alqur'ani a cikin Estate ɗin, a rana ɗaya suka koma tare da iyalansu, Har walima saida suka yi.
Chief Owais bai bar Taj ya koma Jos ba kamar yadda Taj ya so ya tafi da ƴarsa tun da basu da mazauni a Abuja, Unexpected Chief ya gwangwaje shi da kyautar gida a cikin sabon Estate ɗinsu, wayyo Allahna saboda farin ciki har ƙwalla saida ya zubar, Unaisah ma ta yi murna saboda bata so ta tafi ta bar ƴan uwanta fursinoni.
Haka zalika Imam Malik da Dr Shureim sun samu kyautar gidaje a cikin estate ɗin daga momma, ita ta basu saboda bata son su rabu da su, ta ji daɗin kyautatawar Imam Malik ga ahalinta, shiyasa ta janyo su kusa don a ci gaba da rayuwa a tare, sun yi murna sosai, zaman apartment ya ƙarewa Imam Malik dama hayar sa yake biya yanzu sauƙi ya samu ya yi gidan kan shi, Shureim ma ya mallaki gidansa yanzu burin sa ɗaya da ya rage shi ne auran Aisha.
Chief Owais da kan shi ya nemi alfarma a gurin momma ya ce yana son gidaje biyu a estate din su a sayar masa, ta tambayesa me zai yi da su? Ya ce mata zai siyawa Salsabeel da Matar Alhaji Musa, saboda ya ji a bakin Alhaji Ubaid cewa Hajiya Sarah tana shirin komawa America kuma baya son ta tafi da ƴa'ƴanta saboda zumuncin dake a tsakaninsu da cousins ɗin sa.
Momma ta ce ya kwantar da hankalinsa, itama tana goyan bayan shi, ba zata bari jinin tsohuwa Tamira ya tagayyara ba, Salsabeel nata ne, tana jin shi kamar ɗanta, don haka tana son Salsabeel ya dawo gidanta da zama, zata ware masa part ɗinsa, in kuma ya tashi yin aure zata bashi kyautar gida, bayan haka Hajiya Sarah ta ci albarkacin marayun da take ruƙo, suma ta mallaka musu katafaren gida a cikin Estate ɗin, Owais ya yi murna sosai, duk da haka bai gamsu ba saida ya ƙara neman alfarma agurinta akan ta siyar mashi wasu gidajen akwai waɗanda zai bamawa, ta fahimci Owais so yake ya dawo da duka iyalan Elders a estate ɗin su, koda ta tambaye sa meyasa yake son ya dawo da iyalan elders estate ɗinsu, ya ce mata saboda zumuncin su ya ƙulle, yana son prisoners, ya shaƙu da yaran baya son ya raba kansu da ƴan uwansa, yana nufin cousins ɗin sa su Parveen,
Bayan haka a ganinsa ta haka ne zasu samu ƙwarin gwiwar gudanar da rayuwar su cikin farin ciki da annashuwa ba tare da fuskantar wani ƙalubale ba saboda sun san juna, babu wani bare a cikin su.
Ta yi farin ciki da jin kyakkyawar niyyar shi, ta ce mashi kar ya damu, ba zasu siyar masa da gidajen ba, zasu basu kyauta saboda Allah, a ƙarshe Uncle Abdallah da Abie sun samu kyautar gidaje a sabon estate ɗin Ahlin Obinna.
Yayin da Hajjaty da ɗanta Naufal, suke a ƙarƙashin kulawar Sir Mubarak, part ɗinsu yana a cikin gidan sa.
Alhaji Ubaid da Hajiya Layla suna shirin komawa Joss tun da ƙura ta lafa, Hajiya Sarah ta hana su tafiya, ta dinga roƙon su akan su taimaka su zauna a kusa da ita, tun da sun riga da sun zama ɗaya, ko don su taimaka mata gurin kula da ruƙon marayun da aka bar mata, har ta ce in sun amince sai su koma gidan da Owais ya bata kyautar shi a estate ɗin su tun da wannan gidan da suke a ciki na Alhaji Musa gwammanti ta kar6e shi, da zarar wa'adin da aka basu ya cika zasu kar6e ginin ne..
Sun ji daɗin yadda ta nuna bata son su tafi, dama ba son tafiya suke yi ba, kawai don ba yadda zasu yi ne tunda ba gida gare su a Abuja ba. A ƙarshe gaba ɗayan su suka koma gidan Hajiya Sarah na Imam Estate, yana da girma da faɗi, side by side duplex ne, bangare ɗaya na Hajiya Sarah da ƴa'yanta, ɗayan bangaren na su Hajiya Layla ne, babu abun da suka nema suka rasa a gidan, sun ji daɗi sosai tsakanin su da ahalin Obie sai godiya da addu'a.
Alhaji Ubaid gaba ɗaya ya siyar da kadarorinsa na Jos, da kuɗaɗen yake amfani gurin tafiyar da iyalinsa da na Alhaji Musa, yanzu shi ke ɗawainiya da su, don ma Hajiya Sarah tana da arziƙinta, dama can mace ce mai zafin nema babbar ƴar kasuwa ce, daga baya ne ma da gwamnati ta ƙwace kadarorin Alhaji Musa itama ta rasa aikin da take yi a companyn sa.
Amma Alhamdulillah yanzu gaba ɗaya waɗanda suka rasa ayyukan su cikin family ɗin Elders sakamakon abun da ya faru Sharafudeen ya ɗauke su aiki a babban companynsa, babu mai zaman banza, Kowa ya na ƙoƙarin neman na kansa.
Gaba ɗaya dai Ahlin Elders sun zama tsintsiya ɗaya maɗaurinta ɗaya, wata irin shaƙuwa da zumunci mai ƙarfi ne atsakanin su.
Shin ya labarin Zeenatu? tun bayan da tayi doguwar suma sai da ta shafe makonni bata dawo hayyacinta ba, tana a ƙarƙashin kulawar docs, bayan shari'ar Elders da sati ɗaya, Zeenatu ta farfaɗo cikin hayyacinta, mommynta da ƴan uwanta sun yi murna sosai, har kukan farin ciki suka yi duk da a lokacin bata magana sai dai idanunta da ke tsiyayar da hawaye, sun fahimci har yanzu da damuwar abun a ranta, bayan doc ya sallame ta suka dawo gida da ita, tsantsar kulawa suke bata, kwata kwata bata tambayi ina daddynta ba, saboda tsanar da ta yi mashi ko sunan shi bata son ji, kuma wani iko na Allah Zeenatu ta daina son Yaya Shureim da aure, babu soyayya a ranta, da suna ta zullumin tayaya zasu faɗa mata game da soyayyar Shureim da Aisha amma da suka lura babu son shi a ranta, yanzu kallon ɗan uwa kuma Yaya take yi masa sai suka godewa Allah da ya kawo masu mafita, bakomai ne ya faranta ran Zeenatu ba, face ganin tagwayen da mommynta ke ruƙo, har tambayarta ta yi su wanene? Nan Hajiya Sarah ta labarta mata komai game da su, ta tausaya ma rayuwarsu, ta kuma ji daɗi da ya kasance mommynta ne zata ci gaba da ruƙon su, da kallo ɗaya ta ji ta kamu da ƙaunar su, suma haka suka ji, yanzu ta samu tsararrakinta a gidan duk da sun girme ta da shekara ɗaya.
Batare da 6ata lokaci ba, Alhaji Ubaid ya mayar da su school, daga jami'a suka fara shi ya yi masu ƙoƙari gurin sama masu takardun secondary da kuma admission na shiga jami'a da taimakon Owais.
A baya kafin zuwan su twins kurkukun ƙaddara sun yi karatu harma sun kammala secondary, shiyasa karatun su ya zo musu da sauƙi, gaba ɗayan su yanzu suna a jami'a, sajeed Yana karantar Cybersecurity, yayin da Zeenatu da Sajeeda suke karantar Human Rights, su suka za6a da kansu saboda suna da burin su bada gudummuwa gurin kare hakkin ɗan adam.
bayan haka kuma suna zuwa islamiya wadda ke a cikin estate ɗin neman ilimin addini sun bada himma sosai.
Hajiya Sarah ta yi namijin ƙoƙari gurin tafiyar da rayuwar su, babu abun da suka nema suka rasa da arziƙinta ta ke kula da su, ba zaka ta6a gane ba ita ta haifi twins ba sai in an faɗa maka, haka zalika Alhaji Ubaid da Hajiya Layla suna bada gudummuwa gurin tallafa mata akan kula da yaran, Shureim da Benazir da Omar ma ba abar su a baya ba, suna ƙoƙari gurin koya masu abun da basu iya ba, sun zama yayye nagari a gare su.
A zahirin gaskiya rayuwar Prisoners a gurin iyayen su sai son barka, wata irin soyayya suke nuna masu, tsantsar gatanci, kulawa da tarairaya kamar jinjirai, sai abun da suke so iyayen su suke yi masu, gaba ɗaya sun sanya su a school ɗin cikin estate ɗin su bayan private teachers ɗin da ke zuwa yi masu lessons na boko dana islamiya a cikin home classroom din su.
Yara fa sun zama ƴa'yan mommy da daddy, hutu ya zauna masu, babu tashin hankali babu damuwa, sai zallar farin ciki da jin daɗin rayuwa, in ka gansu ba zaka ta6a yarda sun yi rayuwar ƙunci a gidan kurkukun ƙaddara ba, su kan su mantawa suke yi da sun ta6a shan wahala a rayuwar su, Yanzu sun waye, ilimin boko da na addini ya shiga kan su, halayan su da ɗabi'un su sun sauya, lamarin Ubangiji kenan, gwanin hikima, mai yin yadda ya so, mai jujjuya al'amurra, godiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin Sarki 👑🌹
Bayan da ƙura ta lafa, kwanciyar hankali da farin ciki suka wanzu a zukatansu, bayan shekara ɗaya da rabi Dr Shureim ya auri Aisha, yayin da Taj ya mayar da Benazir ɗakinta, Owais ya auri Nazli, A canada aka yi shagalin bikin su na gani na faɗa, ya so ya haɗa da Unaisah ya aure su a rana ɗaya amma ta nuna bata shirya ba, tafi so ta kammala karatunta, bai musa mata ba, shima ya goyi bayan ta yi karatu, da taimakonsa ya yi mata hanya ta zana jarabawar ssce batare da ta shiga ss one ba, dama a baya kafin ƙaddara ta kaita kurkukun ƙaddara ta kammala junior secondary, shiyasa karatun nata ya zo mata da sauƙi, tana a jami'ar da su Sajeed suke, anan take karantar Computer Science, Owais ya yi masu alƙawarin in har suka kammala karatunsu zasu ɗauke su aiki a hukumar su ta Isod saboda suna buƙatar irin su.
Tun farko abun da ya sa Unaisah ta ƙi yarda ya aure su a rana ɗaya ita da Nazli saboda tana jin shakkar ta zama kishiyar Nazli wayayyar ƴar gayu, tafi son ta ƙara wayewa ta yi zurfi a ilimi sannan ta koyi abubuwan da bata iya ba don kada Nazli ta raina ta, a yanzu ta dage damtse gurin koyon girki a wurin mommynta, kuma ta bada himma sosai gurin karatunta, bata wasa da yake Allah ya yi ta da brain she's gifted, tana da baiwar haddace karatu da saurin koyo shiyasa bata jin wahalar komai.
Bayan da ya auri Nazli sai da ya yi hutun wata biyu a gidansa na Canada tare da amaryarsa Nazli, gaba ɗaya suka sauke girman kai da izzar su suka nuna ma juna soyayya, tun a first night ɗinsu suka raya daren su, daga bisani suka tafi honeymoon.
Owais bai tashi dawowa Nigeria ba, sai lokacin bikin Omar da Salsabeel, kuma shi ya haɗa Omar da matar da zai aura, bakowa bace face ƙanwarsa Hindu, yayin da Momma ta haɗa Auran Salsabeel da Yusra ƴar gidan his excellency Abdul razak, kuma cikin sa'a jinin su ya haɗu, duk da a lokacin da momma ta zo mashi da maganar Yusra, ya ji shakkar haɗa shi da ita saboda yasan tafi ƙarfin shi, gata dai ɗiyar gwamna, wayayya, kyakkyawar budurwa, jinin shuwa, a da kafin yanzu tana da girman kai da izza, amma tun bayan faruwar lamarin nan ta sauya hali, ta zama mutuniyar kirki, koda momma ta faɗa mata game da Salsabeel ta kuma nuna mata hoton shi a waya, nan take ta ce ta amince in har yana sonta, zata aure shi, amma tana son bayan sun yi aure ya koma makaranta ya nemi ilimi, itama zata taimaka mashi, Salsabeel ya yi farin ciki mara misaltuwa a lokacin da momma ta faɗa mashi yadda suka yi da Yusra, har sujjada ya yi don nuna godiyar sa ga Allah, Auran gata Momma ta yi ma Salsabeel, ko sisin shi bai kashe ba, tun daga lefensa har sadaki ita ta bayar, har kuka saida ya yi mata saboda farin ciki, A ranar bikin su anyi gagarumin shagali a Imam Estate, amare sun tare a gidajen mazajen su, abun sai son barka.
Idan muka koma bangaren Faryat, reshe ne ya juye da mujiya, yanzu ita ke son Jazz shi kuma yana ja mata aji, ta sauya hali ta nutsu ta koma tagari, ta daina duk wani abu mara kyau da take yi, amma Jazz ya ƙi sauraron ta, wahalar da ita yake yi, kusan kullum sai ta yi kuka saboda azabtuwar da ta ke yi da son shi, idan ta kira wayarsa baya picking, ko saƙo ta tura mashi baya mata reply, a ƙarshe ma ya yi blocking duk wata hanya da zata haɗa su, har gidansu ta zo gaban mommynsa ta zuƙunna kan gwiwowinta tana kuka sha6e sha6e ta dinga roƙonta akan ta sasanta tsakaninta da Jazz in har bata aure sa ba mutuwa zata yi, shi kaɗai take so, ta yi danasanin komai da ta yi masa, ta tuba.
Turai ta tausaya mata musamman da ta ga ta gyara rayuwarta, ko shigar banza ta dai na yi, kullum cikin hijabi da jan cazbaha take, ta ce mata ta yi haƙuri zata yi magana da shi, amma ta ɗan ɗaga ƙafa saboda a yanzu jazz fushi ya ke yi da ita, ta bari sai lokacin da ya huce in sha Allah zata ci gaba da lallashin shi, da ƙyar ta shawo kan Faryat har ta samu ta koma gida, sai da ta kai ga kullum da zazza6i take kwana duk don saboda Jazz, Hajiya Saratu tasan komai da ke faruwa tsakanin Jazz da Faryat, amma bata sanya baki ba, saboda tana jin kunyar Jazz da Mahaifiyarsa, tsakaninta da Faryat addu'a ne da ta ke yi mata da kuma lallashinta.
Shi kan shi Jazz ɗin ba don ya daina sonta ba yake share ta, sai don yana son ta ji irin raɗaɗin da shima ya ji a lokacin da ta ke yi masa wulaƙanci saboda ta ga ya mutu akan ƙaunar ta, amma har lokacin bai daina sonta ba, yana da burin auranta.... 💔
A bangaren Zayn ya yi nadama tun bayan afkuwar lamarin, ya shiryu ya sauya halayensa daga munana zuwa kyawawa, ya zama mutumin kirki, ya daina biyewa matan banza daga shi har Zaid yanzu basu wasa da ibadar su ko a masallaci sune a sahun gaba, sa6anin da ko masallacin basu zuwa sai an tasa ƙeyar su suke zuwa yin sallah.
Soyayyar Zahra kullum ƙara nunkuwa take yi a cikin zuciyarsa, sai dai ya kasa tunkararta da maganar saboda kunyar wulaƙancin da ya yi mata a baya, duk da itama yasan hada mahaifinta a cikin elders, ƙaddarar su iri ɗaya, amma yana jin shakkun ya je gareta, gudun kada ta juya masa baya ko ta kore shi, da damuwa ta ishe shi ya kasa dannewa ya faɗa ma Zaid halin da yake a ciki, Zaid ya shawarce shi da ya shirya su je gidan su Zahran ya nemi yafiyarta yasan zata yafe mashi saboda yasan Zahra tana son shi.
A ranar da su ka je gidan su Zahra, bayan sun yi parking suka kasa fitowa su shiga ciki saboda zullumi, har sai da Abie ya fito daga gidan zai tafi Office ya hango baƙuwar mota a harabar gidan, suna ganin shi suka fito tare da nufar shi cikin girmamawa suka gaishe shi ya amsa masu da fara'a ya ce baigane su wanene ba kamar ƴan'uwan Owais, har suna haɗa baki gurin cewa eh ƴan uwansa ne su, ƴa'yan Hajiya Saratu sun zo ne suna son ganin Zahra, murmushi Abie ya yi ya ce su shiga daga ciki, godiya suka yi mashi tare da wucewa cikin gidan.
Sallamar su ce ta katse karatun ƙur'anin da Mahboob ya ke yi, sai da ya kai ƙarshen ayar da ya janyo, tukunna ya dube su yayin da yake akan kujera ruƙe da kur'ani, da murmushi ya amsa masu sallamar, sun ji daɗin sakin fuskar da ya yi musu.
Mahboob kenan bawan Allah tun bayan mutuwar Ana ya canza, yanzu gudun abun duniya ya ke yi, baya son kuɗi tun da ya ga yadda suke kai mutun ga halaka ya ji sun fita a ran shi.
A yanzu daka bashi kyautar kuɗi tsurar su ƙwara ka siya masa wani abu ka bashi saboda baya kar6ar kuɗi, har kawo wannan lokacin bai daina yiwa Ana addu'a ba, tana a ran shi, a duk lokacin da ya tuna zaluncin da mahaifinsu ya yi mata sai ya ji ɗaci a ran shi.
Bayan sun shiga cikin falon ya nuna masu sofas suka zauna, ya miƙa masu hannu suka yi musabaha, daga bisani Zaid Ya tambayesa ina mutanan gidan? ya ce su Umminsu basa nan sun tafi anguwa, amma Zahra tana a ɗaki tana bacci.
Sun ji daɗin jin tana nan, Zaid ya ce ya kira masu ita in ba damuwa, miƙewa ya yi ya nufi ɗakin Zahra ya yi sallama daga ciki ta amsa mashi, farkawar ta kenan daga bacci, bayan da ya faɗa mata baƙin da ke neman ta, ta yi mamakin jin zuwan Zayn, mutumin da ta sani da girman kai, tana kokwanton in shine! Me ma ya kawo shi gidansu nemanta bayan baya son ta? A ranta ta faɗa, har tambayar Mahboob ta yi ta ce ya kuwa tabbatar shi ɗinne ya zo? Yana murmushi ya ce mata da gaske shine ya zo tare da twin brother ɗinsa Zaid.
Cikin sauri ta sauko daga kan gadon ta shiga toilet, kafin fitowarta Mahboob ya wuce bedroom ɗinsa don ya basu guri su zanta.
Bayan ta fito daga toilet shaf shaf ta shirya kanta cikin abaya, ta fito ta nufi falon, tunkan ta ƙarasa ta hango su, har saida gabanta ya ɗan faɗi ganin abun da bata zata ba..
Zama ta yi kan sofa ɗin dake fuskantar su, ta yi masu barka da zuwa, bayan sun gaisa kowannansu ya yi shiru, sam Zayn ya kasa haɗa idanunshi da nata saboda nauyinta da yake ji amma ganinta da ya yi ya sanyaya zuciyar sa sosai, yana jin in har ya mallaketa zata sama masa farin cikin da ya rasa a rayuwarsa.
Jin sunyi shiru sun kasa magana yasa Zaid yanke shawarar fara gabatar mata da abun da ya kawo su..
Cikin nutsuwa ya fayyace mata komai ya ce yasan ɗan uwansa bai kyauta mata ba, ya yi mata wulaƙanci a baya, amma a yanzu ya yi nadama tun bayan fallasuwar sirrin grandpa ɗinsu da daddyn su sun sauya halinsu, koda can Zayn yana sonta, shi shaida ne saboda baida hira da ta wuce tata, amma a lokacin girman kai ne yasa bai nuna mata so ba.
Tun da ya fara yin maganar Zahra ta zare idanunta cike da mamaki take sauraron Zaid..
Bai ƙare maganar ba, Zayn ya kar6e da cewa, "Wallahi na shiryu Zahra, na gyara halayena, Ki tausaya ma rayuwana, nasan kin daina sona a yanzu amma ki yi haƙuri ki yafe min abun da na yi maki a baya, na yi danasani kuma wallahi ina son ki, in har kika bani dama zan nuna maki irin ƙaunar da na ke maki.
Tsantsar farin ciki ne ya lullu6e zuciyarta tsabar murna kamar ta zuba ruwa ƙasa ta sha amma kwata kwata bata bari ya gane ba, baiwar Allah tun bayan abun kunyar da ubansu ya aikata bata ƙara samun farin ciki irin na yau ba.
Da suka ga ta yi shiru babu fara'a akan fuskarta sai suka yi tunanin bata ji daɗin zuwan su bane, Zaid ya ce ta yi haƙuri idan kalamansu sun 6ata mata rai, za su tafi amma ta zauna tayi tunani idan ta yanke shawara ta sanar da su..
Ya ƙarashe maganar cikin sanyin murya tare da ruƙo hannun Zayn da ya tsareta da idanunshi, shi kaɗai yasan me yake ji a game da ita, baya jin zai iya haƙura su koma gida batare da Zahra ta faɗa masa ra'ayinta akan shi ba.
Zame hannunsa ya yi daga na Zaid ya miƙe daga kan kujerar ya je gaban sofa din da take a zaune ya yi kneeling a gaban ta, wani yanayi ta ji mara misaltuwa, ta kasa haɗa idanunta da nashi, cikin karyayyar murya ya ce, "Bazan iya tafiya batare da kin yafe min ba, nasan har yanzu kina fushi da ni, amma ki yi haƙuri Zahra! ki taimaki rayuwana, ki rufa min asiri, a halin yanzu zan iya haƙura da komai amma banda ke! Wallahi ban zo don na 6ata maki lokaci ba, Auren ki nake so na yi.. "
idanunsa cike tab da ƙwalla ya ƙarashe maganar, ji tayi kamar ta fashe da kuka saboda tausayin shi, cikin sauri ta ce ya tashi ya zauna, ya girgiza mata kai tare da cewa in har tana son ya miƙe toh ta faɗa masa me ta yanke akan shi.
Shiru ta yi tana tunani, a ranta ta ayyana Allah ne ya kar6i addu'arta, ta daɗe tana roƙon Allah ya karkato da hankalin Zayn akanta in alkhairi ne shi a rayuwarta, saboda tana son shi tana son ya zama mijin ta, sai gashi ya zo mata a lokacin da take buƙatar wanda zai rufa mata asiri, saboda samarin da take da su duk sun juya mata baya saboda abun kunyar da ubansu ya aikata amma yanzu ta yi farin ciki da zuwan Zayn saboda tasan ƙaddararsu ɗaya ce idan suka yi aure zasu rufawa kansu asiri, babu wanda zai goranta ma wani..
Numfasawa ta yi da ɗan murmushi akan fuskarta ta ce, "Ni ban fara son ka don in daina ba, har yanzu ina son ka, zan iya cewa na fi kowa farin ciki da ka gyara halayen ka, kuma na yi murnar ganin ka, sannan shawarar da na yanke na amince zan aure ka Zayn.. "
Bata ƙarashe maganar ba, ta ga ya yi sujjada yana kukan farin ciki, batasan sa'adda ta ji hawaye sun wanke fuskarta ba saboda daɗin da ta ji..
Hatta Zaid dake kallon su saida ya ji ƙwalla ta cika idanunshi, ya tausaya musu ya kuma ji daɗin nasarar da ɗan uwansa ya yi akan Zahra..
Tun a wannan lokacin shaƙuwa ta shiga tsakanin su, daga bisani da kanta ta kawo masu abinci da abun sha ta ce suyi haƙuri mamakin ganinsu ne ya mantar da ita bata kawo masu komai ba.
Duk da ba abincin ya kawo su ba, amma saida suka ci saboda ta matsa lamba akan su ci girkinta, aikuwa Zaid ya yi ta santi yana faɗin Zayn ya yi dacen mata saboda ta iya girki zai dinga zuwa gidan su cin abinci, Zayn ya ce karma ya soma, don shi kawai zata dinga yin girki shima in yanaso to ya nemi mata ya aura, Zahra duk tana jin su, murmushin farin ciki ya ƙi barin fuskarta, Zaid ya ce gashi farin sunansu duk iri ɗaya, dama can Allah ya ƙaddara Zahra ta Zayn ce shima zai nemo mai irin farin sunan sa ya aura.
Cikin nishaɗi da annushuwa suka yi firar su, da zasu tafi har bakin mota ta raka su suka yi sallama kamar kar su rabu da juna, su kansu sun ji daɗin karramawar da Zahra ta yi ma su.
bayan tafiyar su ta watsa da gudu ta nufi ɗaki tana taka rawar murna.
Benazir ce ta haɗa soyayyar Aneelerh da Zaki Mubarak Obinna, cikin sa'a jininsu ya haɗu, soyayya mai ƙarfi ta shiga a tsakanin su, da farko Benazir ta yi zaton zai ƙi amincewa da Aneelerh a lokacin ma baya a Nigeria yana a Canada, a waya ta kira shi ta yi mashi tayin aminiyarta, harta faɗa mashi abun da ya faru da mijinta, ya ce ya gode da tayin da ta yi mashi amma baya jin zai iya son wata ƴa mace a halin yanzu, ta ce ya jira ta tura mashi hotonta tana da tabbacin in ya ganta zai so ta, saboda Aneelerh tamkar madadinta ce, bayan da suka kammala wayar, ta tura mashi hoton Aneelerh da baby Junaid a wayarsa, ko minti biyar ba a yi ba, sai ga kiran shi tana yin picking ya ce ta tura mashi contact ɗinta, amma baya son ta faɗa mata ita ce ta haɗa su, yana son ya nemi soyayyarta da amincewarta, ba tare da ta yi tunanin haɗa su aka yi ba, zata iya amincewa don ta yi mata kara ba don tana son shi ba.
Benazir ta ji daɗin maganarsa, nan take ta tura mashi contact din Aneelerh via chats din su..
Lokaci na farko da Aneelerh ta ga kira da baƙuwar number kuma daga ƙasar Canada sai da gabanta ya faɗi saboda ruɗewar da ta yi, kamar bazata ɗaga kiran ba, amma ta yi shahada ta ɗaga, tun daga kan muryarsa ta fahimci mutunne mai nutsuwa da kamala, bayan sun gaisa ta tambayesa wanene shi? Kuma a ina ya samu contact ɗin ta? Da zolaya ya ce a mafarki aka nuna masa ita tare da contact ɗinta, da ta ji hakan sai ta yi dariya ta ce ita dai ya faɗa mata wanene shi? Tana ji aranta ya santa shiyasa ya kirata.
Ya ce haka ne ya santa, amma ta yi haƙuri ya kar6i contact dinta batare da saninta ba, kuma ya kira batare da izininta ba, amma kar ta ga laifin sa, sonta ne ya ja hakan tun da ya ga hotonta ya ruɗe..
Tambayarsa ta kuma yi wanene ya basa contact ɗinta? Kuma a ina ya ga hotonta?"
Still bai sanar da ita ba, sai dai ya ce ta duba whatsApp ya tura mata saƙo..
Bayan sun gama wayar, ta shiga whatsapp ta duba saƙon da ya tura mata..
Hotonsa ne tare da bayaninsa.
Farat ɗaya ta gane ɗan uwan Chief Owais ne saboda kamanninsu, da kuma sunan shi da ta gani Zaki Mubarak Obinna..
Zurfin tunani ta shiga tana ƙoƙarin gano wanene ya bashi contact ɗin ta! Don ta ji aranta wani ne yake son haɗa su..
Da ƙyar ta tuna da labarin da Benazir ta basu na abun da ya faru da ita bayan ta bar gidanta da kuma hannun mutumin da ta faɗa! Nan ta fahimci haɗin Benazir ne...
A ranta ta ayyana in kuwa hasashen ta ya zamana gaskiya zata yi farin ciki sosai, a lokacin ta yi mamakin yadda har ya kira ta a waya, gani take ya fi ƙarfin ta, gashi babban mutum mai arziƙi ga kyawun sura, ita kuwa har aure ta ta6a yi ga ɗa tana da shi, har kokwanto ta yi anya Benazir ta faɗa masa komai game da ita? Tayaya yana saurayi zai nemi soyayya da bazawara mai ɗa!
Bayan da ya sake kiran ta, ta ce mashi ta gano komai, Benazir ce ta bashi contact ɗinta, kuma shine mutumin da ya taimaki Benazir bayan da ta bar gidan mijin ta..
Baiyi mamakin jin ta gano ba, nan take ya fayyace mata abun da ke tafe da shi, ya ƙara da cewa yana sonta ba don Benazir ta haɗa shi da ita ba, a karo na farko da ya kalli hotonta ya ji ya kamu da ƙaunarta, kuma da aure ya ke sonta..
Zare idanu ta yi, cike da mamaki ta ce dagaske ya ke ko wasa? Kuma Benazir ta faɗa masa ta ta6a aure tana da ɗa?"
sautin muryarsa da annuri ya ce ta faɗa masa komai, har hotonta dana ɗanta ta tura mashi ya gani, kuma yana son yaronta, zai kula da rayuwar su gaba ɗaya, kar ta ji komai.
Bazan iya bayyana maku farin cikin da Aneelerh ta yi ba, a daren ranar da suka fara soyayya, kusan kwana su ka yi suna waya..
A washe garin ranar, tun da sassafe ta je gidan Benazir don ta yi mata godiya, Taj da ya ji labarin a gurin Benazir ya nuna farin cikinsa duk da ya so ya auri Aneelerh saboda akwai sonta a zuciyarshi kuma yana son ya ruƙe Junaid a gurinsa amma sai ya haƙura saboda ya ji labarin kyawawan halayan Zaki sai ya ji ya kwanta masa arai, ita ma Aneelerh ta so Taj a baya, amma saboda bazata iya auran mijin aminiyarta ba shiyasa ta haƙura da shi, dama can Allah bai ƙaddara za su auri juna ba. Duk a shekarar bayan dawowar Zaki daga Canada, ya turo magabantansa gidan su Aneeleerh, abun Allah! daga zuwa sanya biki suka ji daɗi nan take suka zarce da ɗaura aure bayan sallar azahar, duk da Abie ya faɗa masu yana buƙatar lokaci da zai yi ma Aneelerh kayan ɗaki, Sir Mubarak ya ce basu buƙatar komai daga gare su, Zaki yana da gida da komai na buƙata a estate ɗin su, ba su son a kawo ta da komai. Alhamdulillah, bayan shagalin bikin Aneelerh a ƙarshe ta tare a gidan mijin ta..
A gurin bikin Aneelerh, Allah ya haɗa wasu masoyan, Zaid da Sajeeda! Da kallo ɗaya Allah ya jarabce shi da sonta, kuma cikin sa'a ta amince da soyayyar shi.
Yayin da Mahboob namu ya faɗa tarkon son Zeenatu dama ya santa tun lokacin baya da Benazir ta ta6a zuwa da ita gidan su, amma bai so ta a lokacin ba saboda yana tare da Ana, bayan haka ko babu Ana ba zai so ta ba a lokacin saboda yana jin tashen maƙon shi baison auren mace mai kyau wadda zai yi wahalar kashe mata kuɗin zuwa saloon balle ita da ta ke baturiya😂
To a ranar walimar bikin Aneelerh suka haɗu, yaita kallonta yana bibiyarta batare da sanin ta ba, duk wani motsin ta akan idanunshi, kwata kwata bata lura ba, har saida Sajeeda ta ankarar da ita tukunna ta lura da bawan Allan dake ta bibiyarta, tarko ta ɗana masa ta fuce daga event hall ɗin walimar ta la6e baya gurin furanni, yana fitowa ta sha gabanshi, ta haɗe rai ta ce ya faɗa mata meyasa ya ke ta kallonta yana bibiyar ta duk ya hanata sukuni.!
Baisan sa'adda jarumta ta zo ma shi ba, ya gyara tsayuwar shi cikin nutsuwa ya faɗa mata abun da ke a ransa.
Abun ka ga rainon turai, da ta ji ya kwanta mata arai nan take ta kar6i tayin soyayyar shi, tun kafin a tashi daga walimar suka ke6e a garden su biyu suka sha soyayyar su, har bayan da suka koma gidajen su basu rabu da juna ba, chatting suka ci gaba da yi, tun daga wannan ranar ne shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakanin su, sai da ta kai ga Mahboob ne ke zuwa gidansu ya ɗauke ta ya kaita school idan an tada su ya je ya ɗauko ta, Hajiya Sarah tasan da komai, kuma ta ji daɗin kulawar da yake ba Zeenatu, saboda shi yasa yanzu bata zama da damuwa a ranta..
*BAYAN WASU SHEKARU🔥