Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe Page 92 Complete

Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe Page 92 Complete

Takun Ƙarshe

 THE DAY BEFORE WEDDING DAY🔥 

Tana a kwance cikin bathtube wanda ke a cike da ruwan ɗumi  daidai kirjinta ruwan ya tsaya ta kishingide kanta, idanunta suna a lumshe tayi zurfi a cikin tunanin ta.

"burina zai cika na ganin nayi aure sai dai farin cikina ragagge ne..."

Bata ƙare zancen zucin nata ba, tajiyo sautin ƙwanƙwasa kofa daga waje, Kwan! Kwan!!

"Unaisah! My baby Girl! Kina ina! Daddynki Ya dawo, Yana son ganin ki" Benazir ce ke kwaɗa mata kira..

waro idanu tayi cike da farin ciki ta yi saurin ɗauraye jikinta da ruwa, ta fito daga kwamin ta warci towel dake rataye jikin hanger ta yi daurin gaba da shi.


Sai rawar jiki ta ke yi jin daddynta ya dawo daga tafiyar da yayi zuwa joss, shigowa bedroom dinta ta yi adaidai lokacin Benazir ta shigo dakin.


Unfortunately, garin rawar jiki, sul6i ya kwashi kafar Unaisah gaba daya ta tafi zata kifa, a gigice Benazir ta nufeta kafin ta karasa tuni ta kife ƙasa nan take daurin towel din da tayi ya warware ya dawo kan qugunta sumar kanta ta baje kasa.


"Subhanallah, daughter, tashi baki ji ciwo ba! " kasa amsa mata tayi saboda zafin dataji sakamakon dakar tiles da kirjinta yayi.


Cikin sauri Benazir ta nufe ta, tana kokarin kai hannu don ta miƙar da ita, kwatsam ba zato ba tsammani ta yi arba da  waist tattoo dinta ya zanu raɗau.


"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un..."


  Ta faɗa da tashin hankali tsantsa akan fuskarta.


sallallamin da tayine yasa Unaisah ta tattara sauran karfin daya rage mata a jikinta tayi saurin miƙewa tare da jan towel din ta daure kirjinta.


Ta yi zaton faɗuwar da ta yi ne yasa Benazir ta ɗaga hankalinta hakan yasa tayi saurin furta"mommy, banji ciwo ba, lafiyana lou," 


daura hannu biyu Benazir tayi asaman kanta tana fadin"nashiga Uku! Unaisah Uban wa ya zana maki tattoo a waist din ki! Yaushe akai! A ina"?


 gabanta ne ya faɗi aruɗe ta zabura ta mike Tsaye jikinta ya kama kerma kamar mazari duk tabi tasha jinin jikinta..


"Bakiji ina magana bane? Uban wa ya zana maki tattoo? Da yaushe akayi maki shi ." 


ta faɗa rai a6ace ta fusgota ta juyar da ita tare da tum6uke towel din ta ƙura idanunta akan tattoo din, zanan giant snake ne nannaɗe da sunan Garkuwa da wani irin salo akayi tattoo din launin black and red ya yi bala'en yin kyau a fatarta.



Unaisah duk tabi ta rude tsabar kaɗuwa cikin sauri ta mayar da towel din da benazir ta cire mata ta mayar kan kirjinta ta daure shi.



"banza shashasha!, kina a cikin hayyacin ki kuwa? Ba zaki amsa min tambayana ba? Sunan uban waye garkuwan? 



Ta fada kamar zata rufeta da bugu, ta tsorata sosai, bata ta6a ganin mommynta cikin fushi irin na yau ba.


Cikin rawar murya ta furta"nick..nick.. Nickname dinsa ne"_


"Shi ubanwa"! Ta katse ta da tsawa.


"Dad.. danish..." zare idanu Benazir tayi"na shiga Uku Unaisah, baki da hankaline? tayaya zaki yi zanan tattoo da sunan wani kato a waist din ki, Kin manta gobe za'a daura maki aure? Wani irin abun kunyane kikeso kija mana Unaisah? Idan mijinki yaga wannan me kike tunanin zai biyo baya..."


ta faɗa idanunta cike tab da kwalla, ji ta ke kamar ta kikkifa mata mari kota huce takaicin da ta ke ji.


Cikin shakakkar murya ta furta"ki yi hakuri mommy, nayi kuskure.. "


"Sorry for your self Unaisah, wlh ba zaki kwana da tattoo din nan a jikin ki ba ! Wai meke damunki ne? Bayan kinsan haramunne yin tattoo a jiki? Ina hankalinki ne? Girgiza kai tayi batare data iya furta kalma ba..


"dole ki goge shi a yau din nan kafin gobe, ki rasa sunan wa zakisa sai sunan matacce mutumin da babu shi araye, Ina laifin ma sunan wanda zaki aura"! Ta faɗa cikin bacin rai...


Zafafan hawaye ne suka wanke fuskarta masu dumi


In a weak voice ta furta"bazai gogu ba, in har ba fatar jikina za'a gurje ba.." 


"Kina nufin permanent tattoo ne"?


 Girgiza kai tayi"temporary tottoo ne, amma zai dauki lokaci kafin ya goge"


"Hmmm, nasan maganinki, Idan na faɗa ma dadynki, kin yi bayani kuma Allah ba zaki kwana da shi ba, lalle zansa in dame shi, wallahi kin ban kunya, har kika iya zuwa wani ƙato ya zana maki tattoo a waist ɗinki don hauka"


 tana fada ta juya zata fuce, da gudu tabi bayanta tayi saurin shan gabanta tana kuka tace'dan Allah ki rufa min asiri kada daddy yaji, wlh ransa zai baci, zai yi fushi dani, bana so na rabu daku kuna fushi dani, zan iya samun matsala agidan aurena.." 


ta fada tana jan magina, hawaye wasu nabin wasu akan fuskarta.


"nayi danasani mommy banyi zaton zai zamarmin matsala ba sai da kika ankarar dani, ki yarda dani wallahi ba namiji ya zana min shi ba, babu wanda yaga tsiraici na, tsautsayi ne yasa naje akayi min a tattoo studio kuma artist din da tayi min macace, wallahi bata ga jikina ba, iya fatar gurin da tayi zanan tagani kadai ban kware jikina ba, kuma wallahi a private room dinsu ne babu wanda ya gani"!


 cikin shesshekar kuka ta faɗa.


"Mommy ki taimaka min mu nemi mafita kafin gobe..." 


 kalaman Unaisah sun karya mata zuciya, wani irin tausayinta ne ya kamata.


"Unaisah meyasa kika yi tattoo da sunan garkuwa"? Ta kuma tambayarta!


"Zan fada maki amma kada ki fadamawa kowa, ki rufa min asiri, nasan zakiji haushina watakilma kiyi min kallon mara hankali amma wlh ba haka bane, soyayyarshi jarabtace daga Allah, in ba haka ba tayaya zuciyata zata dinga azabtar dani da son matacce? Ba irin addu'ar da banyi ba akan Allah ya yaye min son shi, ya mantar dani tunaninsa amma har yanzu babu abun daya sauya mommy..." 


kasa ƙarasa maganar tayi saboda kukan daya kwace mata.


Da sauri Benazir ta rungumota a jikinta, taja ta suka zauna kan couch, ta ƙanƙamate cike da tausayin ta, take jin kukanta a cikin kunnanta.


"Meyasa baki fadamin ba tuntuni? tayaya zaki zauna da damuwa aranki baki sanar dani ba? Kina da tamkatane Unaisah"?


 Cikin shesshekar kuka tace"saboda inajin tsoron abun da zai biyo baya, kuma banaso daddy yaji, saboda tunkafin rabuwa na da Danish ya nuna baya sona da shi, yaya owais ne zabinshi, shiyasa nake kokarin inga na cika mashi burin shi amma abun yaci tura.. "


"La'haula wala'quwata Illah billah"


 ta fada tana shafa sumar kanta, batasan ya zatayi da ita ba! ta razana da jin abun da ke damunta, al'amarine mai girman gaske son wanda baya araye.


"akwai wanda ya san da maganar nan"?


"Batool kaɗai na taba fadamawa"


"Kashh,! baki kyautamun ba Unaisah, Idan matsala ta same ki irin wannan ni ya kama ta, ki fara sanarmawa, ni na haifeki, ni nasan ciwon kanki, duk duniya babu wanda zai fahimceki kamar yadda ni zan fahimce ki, zanfi kowa rufa maki asiri"!


"Nagane kuskurena mommy, zan dinga fada maki..." 


hankalin Benazir ya tashi sosai jin yadda jikinta yaɗau zafi, ko a tarihi bata taba jin soyayya makamanciyar wannan ba, tayaya wanda ke araye zai dinga dakon soyayyar mamaci?


 Lamarin akwai ɗaure kai duk da ba abin mamaki bane tunawa da halin data ta6a shiga lokacin da taji abun da ya faru da taj kusan hauka ta yi ita.


"Kina kallon hotunansa ne ko akwai wani abu dake tuna maki da shi"?


"Babu, saboda azabtuwar da nakeyi yasa na goge komai nashi daga kan wayata, Amma na kasa goge momeries dinshi dake a cikin brain dina, mommy, in zai yiwu, ki kaini asibiti su goge min memory dinshi ta yadda zan manta da komai nashi, Idan ba haka ba bazan iya zaman aure da waninsa ba, zanjama kaina zunubi ne.."


 Ta razana da jin abun da tace,  aruɗe take kallon fuskarta da ta 6aci da hawayen ta, cheeks dinta sunyi jawur..


Benazir ta rasa ya zatayi da ita? Da me zata iya taimaka mata?lamarin yafi karfin tunaninta, bata taba ganin hoton Danish ba amma daga labarin da Unaisah ta taba bata na irin rayuwar da sukayi a tare yasa taji inama ace har yanzu yana araye, saboda taji dadin kyautatawar da yayima Unaisah... "



Numfasawa tayi a hankali ta ce


 "Unaisah, na tausaya maki, i feel your pain, wlh da inada halin da zan iya cire m


Mayar da kiran yayi Video call  


ga mamakinta sai taga duhu a screen din..


"Tabarakallahu Ahsanul khalikin, dagaske kece kika koma haka? kyawunki ya razana ni Unaisah"


"Why i can't see you honey, duhu screen din"!


"Dagangan na toshe camera din, baki tuna wani abu ba?..." ya tambaya.



tuntsirewa tayi da dariya tunawa da wannan ranar da bazata taba mantawa ba..


"Oh kaima ka kira ne don ka gaisa da mutanan duniya, shekararka nawa? Ina mai wayar?..


 Ta fada da zolaya..

Sautin dariyar shi tajiyo ta cikin wayar.


Murmushi tayi tana jin wani irin nishadi da kwanciyar hankali na ratsa ta..


"Unaisah, Ina fata babu namijin da ke kalle min ke? In ba haka ba Kishi zai iya kashe ni"  


dariya tayi har fararen hakoranta suka bayyana kamar gonar auduka tar da su.


Wata irin nannauyar ajiyar zuciya ta soma jin yana saukewa mai haɗe da fitar numfashin sa..


aruɗe ta furta"hubby? Kana lafiya kuwa? Naji voice dinka ya sauya.


"Ke kika jefani a halin da nake ciki Unaisah, kallonki da nakeyi a yanzu ba karamin fusgana kike ba.." 


gabanta ne ya faɗi ta manta rigar bacci ce a jikinta time din daya kira picking kawai tayi ba tare data rufe jikinta ba, a rude ta soma dudduba jikinta duk fa yana kallonta da alama ta manta.



Mikewa tayi daga kan kujerar ta je ta dauko throw pillow da duvet, ta dauki wayar ta koma kan couch ta kwanta tare da rufe rabin jikinta da bargon, ta rungume pillown a kirjin ta.


Saida ta daidaita nutsuwarta tukunna ta saita fuskarta akan screen din wayar..


"Hello! Husband to be kana ji na"? Shiru taji bai tanka mata ba..


Tayi zaton matsalar network ne, batasan duk wani motsinta akan idanunsa.


Har ta fidda rai da sake jin muryar shi taji yace"Ina ma ace nine kika rungume kamar yadda kika rungume pillow din hannunki.." 


runtse idanunta tayi tana jin wani irin yanayi mara misaltuwa, sometimes idan yana furta mata kalaman soyayya har tunani takeyi ina matarsa Nazli sarauniyar kyau? Ko itama yanayi mata irin haka? Ko da yake ita da take agida ai already tafi ta jin ire iren daɗaɗan kalamansa.


"Am sorry idan baki ji dadin maganata ba, bazan iya jurewa bane Unaisah, ni kadai nasan halin da nake shiga idan ina sauraron muryarki, kona kalli fuskarki shiyasa na haramtawa kaina ganinki har sai bayan an shafa fatihar auranmu, a lokacin dana tabbatawar kaina kin zama mallakina halak malak..." 


nema ya ke ya kasheta da daɗaɗan kalamansa gashi yanzu baya kunyar gaya mata irin wadan nan kalaman, gaba daya ya haifar mata da jin kasala a jikin ta..


Cusa kanta tayi cikin pillow duk wani abu da ya ke ji itama tana jin shi sosai..


Cikin harshen turanci ya daura da cewa 


"A wannan lokacinne zan bayyana maki irin kaunar da nake maki kamar raina, zan gatantaki Unaisah, zan baki dukkan kulawata da soyayyata, zan mantar dake duk wani bakin ciki da kika taba dandana a cikin zuciyarki, zaki zama sarauniya a masarautar gidana, zan zama hadiminki me yi maki hidima, zan kuma zama sojanki mai baki kariya, in kuma zama likitan da zai dinga ceto rayuwarki a kowani hali na ciwo, na maki alkawari a dare ɗaya zan canza maki rayuwa.." 


 bitting lower lip din ta tashiga yi tsigar jikinta na ɗan tashi

Cikin rawar murya ta furta"yaya Owais, bacci nake ji, sai Allah yakaimu, ka kulamin da kanka.."


tana karashe maganar bata jira amsarshi ba tayi rejecting call din.


Fashewa tayi da matsanancin kuka mai tsuma zuciya, gaba daya ya tuna mata yanayin da su ke shiga ita da Danish idan suna a tare, daƙyar bacci 6arawo ya yi awon gaba da ita.



💥💫


aki son shi daga cikin zuciyarki da nayi, sai dai bazan iya ba, sannan bazaiyiwu muje asibiti don acire maki tunaninsa ba, kinsan bame yiyuwa bane amma tun da har kin fahimce son shi jarabtarkice to kiyi hakuri Unaisah kiyi hakuri, ki cinye jarabawarnan da hakuri da addu'a."



Nasiha mai ratsa zuciya Benazir tayi mata sosai har saida taji tayi shiru ta daina shesshekar kuka, tukunna ta samu kwanciyar hankali..


"Zan tayaki da addu'a Allah  ya yaye maki abunda ke damunki Unaisah.."


"Ameen mommy, nagode da kulawarki a gare ni.." bata kare maganarba, Muryar Taj ta katse su"Ummu Unaisah naji shiru bata fito ba? Ko bacci takeyi ne"?

Daga murya tayi"a'a na iske ta ta shiga wanke ne, Yanzu zamu fito.." 


"Tashi ki shirya, pls kada ki bari ya gane akwai abunda ke damunki kafin nasan yadda zamuyi da tattoo din nan" 


in a cool voice ta amsa da toh, dakyar ta miƙe ta nufi wardrobe dinta, ta dauko kaya ta sanya.




Lokacin da suka sauko down a saman Sofa suka iske taj yana kallo a plasma tv Ya daura kafarsa daya kan daya.


Takun tafiyarsu ne yaja hankalin shi ga kallon su, murmushi yayi tare da mika mata hannu.


Da sauri ta nufeshi ta kwantar da kanta saman kafadarshi"sannu da dawowa daddy, nayi missing dinka, ya gajiyar tafiya ya ka baro uncle Muhsin din? Ina fata ya samu lafiya"? 


"Alhamdulillah My Angel,  nayi missing naki nima, Muhsin yana gaishe da ku, jikinshi da sauƙi fatan na same ku lafiya, Ya shirye shiryen biki" cike da jin kunyarshi tace"Alhamdulillah."


Kallonta yayi da kyau"masha Allah daughter, umminta me kike batane naga ta sauya min tayi kyau kamar lu'u lu'u ..."


Dariya Benazir tayi"Sirrin mune na mata, kaima lokacin da zaka aure ni ba haka ka rude ba duk ka susuce da ganin yadda nayi kyau..." 


bata ƙare maganar ba ya galla mata harara afakaice kasa kasa da murya yace"meye haka pls"?


Yar dariya tayi"me kuma ya rage Tajo, ai daga gobe ta wuce Unaisah zatasan komai.." 


ta fada tana ɗage masa gira.


throw pillow ya janyo Ya wurga mata tayi saurin cabe shi a hannun ta


"babu wani boye boye Tajo, daga gobe ne" 


"Ummu unaisah ki daina! Aa wai meke damunki ne"!


 Bushewa tayi da dariya, Unaisah data langwa6e kanta saman kafadar shi tayi shiru tana sauraron su.


"Wai ya maganar sadakinta ne? Ko yayi tunanin kyauta zamu bashi ita ne? Naji shiru tun satin da aka sanya bikin naketa jira inji ance ga sadakin Unaisah amma shiru kakeji wai malam yaci shirwa" 


"Mun yafe masu sadaki, salatin annabi za'ayi don auren yayi albarka ko Unaisahna" ya faɗa tare da leken fuskarta.


 murmushi tayi tare da jinjina mashi kai.


"Hmm Yanzu mutun yayi magana ace ya yi sa6o, ko ya kafurta amma taj meya kawo wannan maganar? In albarkar aure akeso nima in na saka mata ya wadatar ko"


 Ƙyalƙyacewa su ka yi da dariya gaba ɗayan su cike da nishadi su ke yin firar su..



*AGIDAN DR SHUREIM🔥*



A hankali Motar shi ta kunna kai cikin harabar gidansa, a tsanake ya ke yin driving yana bin karatun alqur'anin da ya kunna..


Bayan yayi Parking din motar ya kasheta, A hankali ya fito as usual sanye da arab dress dinsa..


Fitowa Ummi tayi daga cikin gidan, ta nufe shi da sauri tana karasowa sukayi hugging din juna kamar sun shekara basu hadu ba..


Dagowa tayi ta sumbaci kuncin shi"Welcome back habibina, ya kake ya aiki? Ina fata kana lafiya? Ta faɗa tare da kar6e jakar hannunsa..


Fuskarsa dauke da murmushi yace"mar'atussaliha, Alhamdulillah Ina lafiya, fatan na same ki lafiya.."

"Lafiyalou"

Ruƙo hannunsa tayi a cikin nata"mu shiga daga ciki.." 


A bedroom dinsa suka tsaya ta taimaka mashi ya rage kayan jikin shi.


"His excellency, wanka ko abinci wanne kafi bukata in taimaka maka da shi .." ta tambaya tana kallonsa yayin da ya ke a zaune gefen gadon sa.


"Ke" ya bata amsa a takaice

Kayataccen murmushi tasakar ma shi" ta matsa kusa da shi bai aune ba yaji ta fara kissing nashi sai da tabari ya fara hawa kan network tayi saurin raba jikinta daga na shi.


"Nasan akwai gajiya a tare dakai da kuma yunwa, bari na kawo maka abinci..." wani marayan kallo ya bita da shi yana hadiyar yawu.


Kashe mashi ido daya tayi ta juya yabi bayanta da kallo mai cike da shauki, har saida ta bace ma kallonshi tukunna ya jingine kansa jikin pillow, yana mai kara godewa Allah daya mallaka masa ummi amatsayin matarsa, dadinta yakeji fiye da komai na duniyar nan, idan yana atare da ita mantawa ya ke yi da komai.


Har ta shigo bai dawo daga duniyar tunanin da yake yi ba, a saman table ta daura tray din hannunta mai dauke da lunch dinsa.


"Mijin so, am back, ka tashi in ciyar dakai girkina" murmushi yayi tare da mikewa ta janyo table din agabansa.


Yana niyar bude baki yayi magana tayi saurin daukar glass na juice ta kafa mashi abaki ya dan kur6a yana jinjina kanshi alamar yayi dadi.


Abaki ta dinga bashi abincin yana ci.


"Ina Batool ne? Batasan na dawo bane? Ko ta tafi gidan Bikin ne"? Girgiza kai tayi"a'a bataje ko'ina ba, may be tana a bedroom din ta"


"Taci abinci?


"Nayi nayi da ita tace min bata jin yunwa, dana matsa mata sai tace min da anjima idan ta shiga gurin Unaisah zasuci a atare"


Shiru ya danyi jimm kafin yace"kira min ita"


"Okay Sir" aje spoon din tayi ta juya tana tafiya da rangwaɗa dagangan take yi don ta rikita shi.


Murmushi yayi tare da dan girgiza kan shi..


A cikin kunnanta ta tsinkayi shesshekar kukan Batool, wani irin faduwar gaba taji, da karfi ta shiga bubbuga kofar dakin ta"babe! Babe! Me kike ma kuka ne? Zo ki bude mun kofa!


Shiru taji ta daina kukan kuma babu alamun zata bude kofar.


"Babe! Kina jina kika shareni? Ba zaki bude min kofa ba"? ta fada da damuwa akan fuskarta.


Dakyar ta samu batool ta buɗe mata kofar dakin, bin ta da kallo tayi, idanunta sunyi jawur sun kumbura, Cheeks dinta sunyi jajir alamar tasha kuka, sumar kanta duk ta hargitse

Hankalin ummi idan yai dubu to ya tashi.


Dafa kafadunta tayi"meke damunki? Baki da lafiya ne? Waya ta6a min ke? Meyasa ki kuka.."?


 Duk tabi ta rude..

Cikin sanyin murya batool tace"babu komai, bana jin dadi jikina ne" girgiza kai ummi tayi"ban yarda ba batool, dole akwai abunda ke damunki, Mu shiga ciki ki fada min.." ta fada tare da jan hannunta suka shiga ciki ta zaunar da ita gefen gadon itama ta zauna.


"Kada ki boyemin Batool dina, ki fadamin abun da ke damunki zan taimaka maki mu nemi mafita"!



Kasa sanar da ita tayi saboda tana fargaban yadda zata dauki abun idan taji.


Amma ya zatayi bata da mafita..

lallashin ta ummi ta soma  yi tana lalla6ata don ta faɗa mata.


Har saida taji zata iya sanar da ita.


"Ummina, bana son kayan da aka raba mana na yan matan amarya, ni bazan sanyasu ba, nafison kalar rigar da Unaisah zata sanya a ranar bikin ta.. "


 kasa karasa maganar tayi ganin yadda Ummi ta saki baki sototo alamar mamaki ya kamata..


"Nasan zaki fahimce ni shiyasa na fada maki, wallahi in har ban samu kalar rigar Unaisah ba, ba zanje gidan bikin ba ranar auran ta.." 


ruɗune tsantsa akan fuskar Ummi"batool kinsan me kike fada kuwa? Dagaske kike ko wasa kike min" fuskarta babu annuri tace"wallahi dagaske nake maki, dan Allah ki siyamin kalar rigarta komai da komai"


"Batool zan iya yi maki komai a dunyar nan indai baifi karfina ba, amma in banda abunki tayaya zaki ce irin bridal gown din Unaisah ki ke so? Batool tafi karfin mu, bamu da kudin da zamu iya siya maki ita, har yau ni banma ga rigar ido da ido ba, a hoto Benazir ta nuna min ita, ba'a kaiga kawota gidan ba! Sai zuwa gobe"

  



kwata kwata Batool bata fahimtar bayanin ta"ummina ba za ku iya siya min irin ta ba? Shikenan ni bazan iya mallakar komai da Unaisah ta samu ba?


 Idanunta cike tab da kwalla ta karashe maganar, arude ummi ke dubanta cike da fargaban kada abunda take kokwanto ya tabbata akan ta.


"Ki fahimce ni Batool, bamu da halin da zamu iya siya maki ita!tafi karfin arzikin mu, kuma babu yadda za'ai ki sanya kalar rigar Unaisah aranar auranta, zakija mana surutu tun da ba auranki akeyi ba"


"amma ki canza wata rigar mai saukin kuɗi in sha Allah zamu siya maki, amma dan Allah kidaina fadin ba zaki iya mallakar komai da Unaisah ta samu ba, kema zaki iya samun fiye da shi amma kinga wannan bridal gown din da kike magana akai ba iyayen ta bane suka siya mata ba, Mijin da zata aurane ya siya mata..." bata kare maganar ba, taga ta zabura ta mike tsaye jikinta ya hau yin kerma cikin muryar fushi mai tattare da bacin rai tace"zanje na fadawa Abbana, nasan zai siya min irin ta.." fucewa tayi daga dakin.



 

A rude Ummi tamike tabi bayanta gabanta naci gaba da faduwa ta rasa gane meke damun Batool ne? kamar ƙamar yarinya, Meyasa takeson irin rigar Unaisah? Maganganunta kamar suna nufin tana hassada da ita, wallah bata fata abun da take hasashe ya zamana gaskiya.


Ko sallama ba tayi ba ta shigo dakin, abun da ba dabi'arta ba, motsinta yasa shureim dagowa ya dubeta, kwata kwata bai lura da moods din fuskarta ba.


Zama tayi gefenshi ko gaishe da shi batayi ba cikin shesshekar kuka tace"Abbana dan Allah, dan sonka da annabi, ka siya min irin rigar Unaisah ta aure! Wallahi ita nakeso Abba"  bai san sa'adda ya furzar da ruwan lemun daya kur6a abakinsa ba, da sauri Ya aje cup din kan table ya dubeta da idon basira.


"Batool me ke damunki? Ba kiyi min sallama ba, ko gaishe ni bakiyi ba, ba sannu da dawowa  kuma ki rasa da wani zance zaki tarbeni sai da wannan"? Ya fada fuskarsa a yamutse.


Bata kaiga furta kalma ba, Ummu ta shigo dakin, anan ta fayyace masa komai..


"Haba Batool, wallah idan akan farin cikinki ne sai inda karfinmu ya kare, ba abunda ba zamu iyayi maki ba, amma ki gane rigar Unaisah tafi karfin mu, kuma in banda abunki ai babu me sanya irin rigar amarya ita nata dabanne, kuma ba an baku kyautar anko na kawayen amarya ba?  kiyi hakuri ki sanya su mana.."



bai kare maganarba, ta fashe masu da kuka kamar ranta zai fita, gaba daya ta daga masu hankali, suka rasa shawo kanta, dr shureim daya rude yayi zaton iskane suka shigeta nan take ya fara yi mata rukiya



Cikin shesshekar murya ta furta"abba da hankalina! Ni ce batool, babu wani aljani a jikina, Ku dainayi min ruƙiya kawai kuyi min abunda nakeso, ban taba tambayarku wani abu kun kasa yi min ba, meyasa ba zaku iya siya min kalar rigarta ba! Tayaya zan yarda kuna sona?


 Maganganunta sun daga hankulansu.


Tsawa  dr shureim Ya daka mata ganin taki ta saurare su


"Ya isa haka Batool, na fahimci rashin wayau ke damunki, karki kuskura ki kara wata magana anan idan ba so kike ranki ya 6aci ba! Haba sai kace yarinyar goye?  Kodan kinga muna lallashin ki shiyasa kike mana abunda kika ga dama? In banda rigima me zakiyi da rigar amarya? Ke za'ay ma aure ne? 


Ummi ce ta balbaleta da fada ta inda take shiga bata nan take fita ba, Dr shureim sai kokarin dakatar da ita yakeyi saboda baisan 6acin ran batool dinsa.


Miƙewa tayi fuskarta sharkaf da hawaye cikin fushi ta fuce daga dakin, suka biyota da sauri suna ambaton sunanta kafin su karaso tuni ta shige daki ta kulle kanta.


Bubbuga kofar suka dinga yi suna lallashinta akan ta buɗe ma su ƙofa, tana ji tayi banza ta kyalesu, gaba daya tsoro sukeji kada ta lahanta kanta. 


Da suka gaji da buga kofar, a kan stairs suka zauna ransu duk ajagule.


"Ina ma ace zan iya siya mata rigarnan wlh dana siya mata, saboda banason bacin ran batool, Idan tana kuka har cikin raina nake jin ɗaci, saboda tana tuna min lokacin da tana jinjira"


hawayen da suka cika idanun shi suka soma kokarin saukowa kan kuncinsa da sauri ummi ta sharesu da yatsunta.


"Pls, kada ka sanya damuwa aranka, ni kaina nayi fatan hakan amma ba zamu iyaba, dole sai mun danne son da muke mata mun koya mata hakuri da babu idan ba haka ba zamuci wahalarta agaba.."


Gyaɗa kansa yayi"ni lamarin ma tsoro ya bani wlh, lokaci daya ta sauya dabi'unta irin na yara amma meyasa takeson dolin doliya sai irin rigar Unaisah"? 


Ya tambaya yana duban ummi.


"Kasan wani abu, nifa ba tun yau ba, na lura da wani abu, Batool tana kwaikwayon komai na rayuwar Unaisah, na rasa gane gasa ta ke yi da itane? Kishi ne ko hassada.." 


bata kare maganarba ya katseta"bana tunanin haka, pls mu kyautata mata tazo" 


Ummi tace"dole fa sai munsan meke damunta tukunna zamu kamo bakin zaren, Batool fa saboda bedroom din Unaisah yana a upstairs yasa itama ta nace mana akan mu maida mata bedroom dinta up, sannan ta matsa mana akan mu maidata jami'a don tayi graduation tare da su Unaisah, ka lura da kyau yanzu haka zanan kunshin hannunsu iri ɗaya ne babu banbanci"


Ta fada tana duban shi, abun duniya ya ishe shi.


"Aisha, bansan ya zanyi ba! Wai menene dalilin dayasa take son komai irin na Unaisah ne? Ummi tace"nima abun da nakeso na sani kenan, dole akwai abunda take mawa.." 


gaba daya sun rasa mafita.


Gashi ta kulla kanta adaki tun safe su ke ta kokarin shawo kanta amma abun yaci tura, ba ci ba sha, har marece ya yi Batool bata fito ba, ko magana batayi gaba daya ta daga hankulansu.


Suna a zaune cikin falo kan sofas sun zagba tagumi, kwatsam sallamar Unaisah ta katse su cikin sauri suka dubi kofar falon, Shigowa tayi sanye da hijab ta ruke lunch box a hannunta.


Tuni kamshinta ya cika hancinan su.


"Unaisah.." 


"Na'am Aunty Ummi, Uncle shureim ya ku ke? Ina fata kun wuni lafiya.." 


murmushin yaƙe suka sakar mata"lafiyalou Unaisah, Ya shirye shiryen biki"


"Alhamdulillah, munji shiru baku leko ba, Nima gurin yar uwata nazo duk yau banji duriyarta ba"


walwalar fuskar su ce ta dauke duff, damuwar da suke boyewa ta bayyana akan fuskokinsu.


"Ina Batool din? Ko tana daki"?

Har suna hada baki gurin furta"tana aɗa..  Au bata nan ta tafi unguwa.." kallon juna su ka yi.


Da ruɗu Unaisah take dubansu jin yadda suka bada amsa daban daban.


"Aunty Ummi, meke faruwa ne? Ina Batool? Ko wani abu ya faru da itane"?


Ƙwafa Ummi tayi"Unaisah, Batool tana a daki, amma bata jin dadi, bacci takeyi, ki bari zuwa anjima zamu leko gidan tare da ita.." 


girgiza kai tayi"i'm sorry Aunty Ummi bazan iya tafiya banganta ba, Inaji araina wani abu na faru badaidai ba, gaba dayanku da damuwa akan fuskokin ku, bayan haka tunda bikina ya matso Batool kullum tana a tare dani, amma yau ko kadan bata leko ni ba, tayaya hankalina zai kwanta? Dan Allah kubarni naga yar uwata.." 


ta fada tana kokarin wucewa ciki da sauri suka sha gabanta kamar mara sa gaskiya duk sunbi sun rude, kwata kwata basu san tasan meke faruwa saboda sunsan son da take ma yar uwata zata iyayi mata komai donta faranta mata rai su kuma basu san hakan ya faru zataja masu abun kunya ne.


"Dan Allah Uncle shureim ku fada min meke faruwa? Kada ku boyemin abunda ke damun ku.. "


 idanunta cike tab da kwalla tayi maganar.


Kallon juna su kayi, Ummi ta dinga girgiza mashi kai donta lura kamar so ya ke ya fada mata.


"Unaisah, dan Allah kiyi hakuri ki koma gida, wallahi bamu son kiji abunda ke faruwa, ba zakiji dadi ba,"


Gyada kai tayi"tunda ba zaku fadamin ba, zanje na fadawa mommyna da daddyna, nasan su zaku iya fada musu..." 


juyawa tayi cikin sauri suka tarota.


"Unaisah, abun kunyane, Mun rasa gane kan Batool, ta canza mana, rigima takeyi mana kamar karamar yarinya, saboda kawai tace mu siya mata irin gown din auranki munce mata bamu da halin da zamu siya mata shine ta kama fushi damu, taita kuka, tun safe ta kulle kanta adaki, baci ba sha, munyi munyi da ita akan ta bude mana kofar dakin ta ƙiya.." dr shureim ne yayi maganar. 


Ummi tace"dan Allah karki damu kanki Unaisah, in banda abun Batool ai abun amarya na dabanne babu mai yin irin shigarta.."


Gabanta ne ya fadi, damuwa ta mamaye zuciyarta, dama sai da tayi fargaban hakan cos tun shekaran jiya da aka raba ma su Invitation bags ta lura Batool bata gode ba.


"Dan Allah Unaisah kada ki fadama kowa, daga mu sai ke, yadda mukayi maganar anan mu binneta anan pls, wlh abun kunyane maganar nan ta fita, kema mun fada maki ne saboda ba mu da mafita"


Cikin karyayyar murya tace"Batool bata kyautamin ba, kawai saboda tana son rigar aure na shine ta haramtawa kanta zuwa gurina, Ta kulle kanta adaki? ta tambaya cike da takaici.


"Bana fata Allah ya nuna min ranar da Batool zata nemi wani abu agurina in gaza yi mata shi, tafi karfin komai wallahi, zan iya hakura da komai in bar mata" 


waro idanu waje sukayi cike da mamakin maganarta, juyawa tayi da sauri ta nufi up, suka bi bayanta da sauri.


Knocking kofar tayi"Ukhty Batool Buɗe mun ƙofa, Nayi missing naki, Inason ganin ki" 


A cikin kunnanta ta tsinkayi muryar Unaisah daga waje, tana a zaune kan couch ta yi kuka har ta gaji, jikinta sai kerma ya ke yi saboda zazza6in daya kamata.


 taji dadin jin muryar Unaisah saboda tayi kewar ganinta, sai dai batajin zata iya hada ido da ita..


"Nasan kina jina Batool, Dan Allah ki bude min kofa kinji"?


 Magiya ta dinga yi mata, dakyar ta samu Batool ta buɗe mata kofa..


Kallo daya da Unaisah tayi mata sai da taji tausayinta ya kamata, daga gani ko wanka batayi ba, rigar jikinta ta yamitse kamar wadda aka kwato daga bakin kura.


bataji dadin halin da batool ta jefa kanta ba saboda kawai tana son irin rigarta?


Ruko hannunta tayi suka koma ciki, a saman gado suka zauna suna fuskantar Juna.


Ummi da shureim suna daga waje suna sauraron su.


"Meyasa bakizo gidanmu ba? Kin barni da tunanin wani hali kike a ciki ." ta faɗa tana dan jifarta da harara.


Duk ta kame kanta, kamar wadda tayiwa sarki karya fadawa suka turketa.


"Um.. Bana jin daɗine, amma kina araina.."


"Meke damunkine Batool?Dubarki dan Allah, daga gani ko wanka bakiyi ba.." ta fada tana bude Lunch box din data kawo mata.


"Ba abunda ke damuna.."


"Okay Aunty Ummi ta fada min baki ci abinci ba, ga lunch na kawo maki, abincin da mommy tayi ma daddyne na debo maki"


murmushi ta danyi fuskarta ba walwala.


"Naji dadi ya dawo lafiya, da anjima zan shiga na gaida shi, bari na wanko bakina"


"Kina nufin ko brush baki ba" daga mata kai tay, ta sauko ta shige toilet, ajiyar zuciya Unaisah ta sauke a ranta tana mai mamakin ta.


Jim kaɗan ta fito ta dawo kan gadon ta zauna, Unaisah ta soma bata abaki tana ci..


Duk akan idon su Aisha, jikinsu yayi sanyi sosai..


Saida taci ta koshi tana ta santin abincin, daga bisani Unaisah ta karasa cinye sauran data rage..


Ta daura lunch box din gefe ɗaya.


Ruko hannunta Unaisah tayi a cikin nata, idanunsu a cikin na juna..


"Bayan rigar aurena sai me kikeso nawa"? Gabantane Ya fadi wata irin kunya ce ta kamata adabarbarce ta furta"um..waw..waya fada maki? Ni bance ina son rigar auren ki ba, cewa kawai nayi kalarta nakeso ba taki ba. " 


murmushi Unaisah tayi"meye na daga hankali aciki? Tambayarki nayi kawai ki bani amsa, banaso gobe ki ga wani abu nawa a ƙurarren lokaci kice kinaso kwara ki fadamin tun yanzu in sani.." 


"Unaisah karki.." ummi data dauko maganar bata karasaba, Dr shureim Ya toshe mata baki"pls, kibarsu suyi magana atsakanin su"! Cike da takaici tayi shiru


"Kada kiji komai Batool, tun da har kika nuna kina son gown dina, ni kuma na bar maki ita har abada, nama haramtawa kaina sanyata, koda zan rasa suturar da zan sanya ne aranar aurena.."


"Wallahi bazai yiwuwa ba, Batool bazata sanya rigarki ba, sai dai ita kada taje bikin, kima daina wannan maganar bame yiwuwa bane.." cikin fushi ummi ta fada ranta ya baci 


"Shashasha Unaisah har tafiki hankali da wayou bayan ke yakamata kifita saboda kin girme ta da shekaru biyu amma saboda kawai ki kunyata mu a idon duniya shiyasa kika nace akan rigarta kikeso to wlh ba zaki sanyata ba..." 


balbaleta da fada tayi ta inda ta shiga bata nan take fita ba.



Dr shureim yace"ummu batool, ki bar su suyi magana atsakanin su please.."


"Aunty Ummi, Uncle Shureim pls, ina neman alfarma agurinku, kada ku hanani kyautatama yar uwata, idan har ban bata rigar nan ba wani abu da ba'a fata ya faru zanyi danasani ne,.."


bata ƙare maganar ba ummi ta katse ta"Unaisah, koda zata hadiyi zuciya ta mutune ba zata saka rigarki ba.." 


bata kare maganarba dr shureim yaja hannunta suka fuce daga dakin.


Batool ta fashe da kuka tana fadin"unaisah banaso, bazan kar6a ba, ki tafi kawai ki bani guri, na tsani kaina, na bata ma iyayena rai, kowa haushina yake ji, bansan meke damuna ba, bansan meyasa nake jin haushin inga kin fini da wani abu ba.."


 tallabo fuskarta Unaisah tayi ta soma lallashinta dakyar ta samu ta shawo kanta.


"Yanzu fada mun bayan rigar me kikeso? Karki wani damu da su ummu, ni nasan ta yadda zan shawo kansu... "


 ajiyar zuciya ta sauke, idanunta sun kankance saboda kukan da ta sha.


"Inasan komai da zaki sanya ranar auranki, Jewelry dinki, da takalmanki, da irin make up din da za'ayi maki"


gaban Unaisah ne ya faɗi arude ta ɗan zare idanunta tana kallon Batool, cike da fargaban kada ta furta tana son mijinta a ƙarshen zancen ta.


Cikin sauri ta katse ta"ki kwantar da hankalin ki, za'ayi maki komai irin nawa.." farin cikine ya cika zuciyar Batool.


"Nagode sis, yanzu na kara yarda ina da yar uwa maison farin cikina, wadda zata iya sadaukar da komai saboda ni.."


 murmushin yaƙe Unaisah tayi zuciyarta cike fal da zullumin kada nan gaba tace tana son mijinta, ba zata iya bar mata shi ba saboda shi kadaine madadin danish a duniyar nan, kuma bazata iya bari Batool ta zama kishiyar ta ba, saboda tana jin tsoron kishin batool tun ayanzu tana gasa da ita inaga idan su  ka auri miji ɗaya"?


Sau uku Batool tana kiran sunanta bata amsa ba, ta lula duniyar tunani.


"Unaisah! " ta fada tare da bugun kafadarta, aɗan firgice ta

Ƙyafƙyafta idanunta tare da duban Batool.


"Me kike tunani ne"? washe baki tayi"bakomai sis dina, Ina fata babu sauran abunda kikeso ko"?


"Idan kin bani kayan auran naki, ke wanne zaki sanya"


"Karki damu, zan za6i cikin kayan da nake da su in sanya"


"Amma baki tunanin yaya Owais zaiyi magana idan yaga baki sanya kayan daya siya maki ba ni na sanya? Kuma mutane ma zasu tuhume ni.."


"Karki damu Batool, ai babu wanda yasan kalar rigar, mu ma awaya muka ganta baza asan tawa bace.." murmushi Batool tayi"amma bana so ki sanya wasu kayan da suka fi nawa kyau, nafison komai namu iri daya.."


 daure fuska Unaisah tayi ganin ta fara wuce gona da iri.


"Batool, tun da na baki rigar, ni naji bazan sanya wata bridal gown dinba, idan bakiso in fi ki kyau Ki bani ankon ki in sanya kinga sai in saje da yan matan amarya, ke kuma ki zama amarya! Ina fata hakan ya yi maki" ta tambaya babu fara'a akan fuskarta


Shiru tayi da alamun rashin jin dadi akan fuskarta, sai tayi abu yazo yana damunta.


"Kiyi hakuri idan na bata maki rai"


Girgiza kai Unaisah tayi"baki bata min rai ba" yanzu ki tashi mu tafi gida, kinsan yau daren biki ne, yan matan amarya zasu haɗu saboda su yi final rehearsal na rawar dinner da za'ayi bayan biki"


"Toh, zan yi wanka, Ki jira ni" amsawa tayi da toh, ta zauna shiru tana jiran ta..


Saukowa Batool tayi daga kan gadon ta nufi gaban dressing mirror nata, ta wutsiyar ido Unaisah ta hangota yayin da ta ke kokarin boye robobin kayan matan data satar mata a cikin drawer chest.


Ta ɗauki roba daya wanda na wanka ne, tayi sauri ta shige toilet da shi.


Murmushi tayi tare da dan girgiza kanta.


Lamarin Batool na nema ya ɗaura mata hawan jini, yanzu ta daina tunanin hassada take da ita ko gasa, cos in har gasa ta ke yi da ita meyasa batason tafita da wani abu? Ita kawai burinta komai nasu ya zo ɗaya kada ɗaya yafi Ɗaya ❗❓



~_____🌹______💗______💋_______💫_____🌹_______~





Da marecen Ranar bridemaids su ka haɗu gidan biki, abayan gidan suka yi Final dance rehearsal.


kowa dai ya ci burin zuwan ranar auren Unaisah, ni kaina jiran ta nakeyi, dani da readers dina, kai hatta alkalamina a ƙagare ya ke daya rubuta.


har sai wuraren ƙarfe goma tukunna kowaccen su ta nufi gidan su da ke a cikin Estate din.


kasa runtsawa tayi saboda zullumi da fargaban ranar daurin auran nata, gani take data runtse idanunta, safiya zatayi, ita kuma bataso hakan ya faru, da tana da halin da zata ƙara kwanakin da tayi sai dai ita kanta ta ƙagu data ga ranar nan da ta dade tana jiran ta tunkan ta mallaki hankalin ta, tarasa meyasa take jin kamar batayiwa Danish Adalci ba idan ta auri wanin sa? Amma in ta tuna baya araye kuma dan uwansa zata aure sai taji sanyi aranta.


Yayin da take wannan tunanin tana a kwance kan gadonta tayi rubda ciki, babu haske a dakin saina laptop screen dinta data kunna tana kallon wani shortdrama mai taken Let me taste your husband, ta daura chin dinta saman pillow.


su biyu su ke yin kallo daga bisani Batool ta 6ingire da bacci, tana a gefenta ta rufe masu rabin jikinsu da duvet.


Abun da yafi damunta, yadda zata fahimtar da iyayenta game da rigar auranta da zata ba Batool, duk da tasan ba lallai su nuna bacin ransu ba tunda Batool ce amma dole suji ba dadi.


Mutun ɗaya da take ganin ya kamata ta sanarmawa shine Chief, tasan bazaiji dadi ba ya sayi abun da kudin shi don ta sanya ya ji dadi, fisabilillahi kuma sai yaga taje gidansa babu rigar? Me zata faɗa masa idan ya tambayeta, sai dai batajinma zata iya fada mashi saboda tasan a karshe zaice zai siya mata wata ne, ita kuma bataso ƙwara ta nemi wata mafitar.



Bacci ne ya fara cin karfinta ta fara gyangyadi tana ganin biji biji a idanun ta, a hankali ta fara yin hammar bacci tana lumshe idanunta.



Phone ringing dinta ne Ya katse mata kallon, agajiye ta rufe laptop din ta tureta gefe, ta janyo wayar tayi picking ta kara a kunne..



"Na kira ne don na tuna maki, daga yau ne, ina fata kin fara bankwana da kowa, cos daga yau kin gama kwana a ko'ina sai a gidana" duk da baccin dake nema yaci karfinta sai da taji dadin muryarsa.



"farin ciki kake yi don zaka rabani da iyayena"?


"Yeah, ina farin ciki zan daukaka darajarki, in aureki, mu raya sunnar manzon Allah SAW, mu kuma hayayyafa kamar yarda iyayenmu suka yi, ko bakison kiyi koyi da su ne"?..


Batasan sa'adda murmushi ya su6uce mata ba, tattausar lafazinsa, Yana kashe mata jiki



"Inaso, burina ne tun ina ƙarama... " kasa kasa take magana gudun kada batool taji ta farka tasan halinta yanzu ta matsa number akan tana son itama ta yi aure rana ɗaya da ita.


"Fadamin me za ki shirya a agobe? Me kika tanadarmin? Me kuma zaki fara yi idan kika ganni  amatsayin angonki? Hamma tayi cikin muryar mai kama data rada ta furta"ka jira goben tayi zaka ga shirin da nayi maka, zan tanadar maka kaina da soyayyata, idan na fara ganin ka amatsayin angona zanyi sujjada don nuna godiyata ga Allah daya mallaka min kyakkyawan bawan nan nasa..." 


shiru taji baiyi magana ba.


"Yaya Owais? Kana jina ko kayi bacci?.. Har saida tafara gajiya, ga bacci daya kanainayeta har ta fidda rai da zai yi magana taji yace"bana tunanin zan iya cin abinci gobe, har sai naganki agidana, a tare zamu ci dinner saboda inaso ki bani abaki"



"Nima bazanci komai ba, zan jira har time da za'a kawo ni gidanka"


Tsawon mintuna babu wanda ya kara furta kalma sunyi shiru sun nutsu suna sauraron sautin numfashin junan su..


Kowannansu da abun dayake saƙawa aran shi.



A haka bacci yaci karfinta bata Ƙara sanin inda kanta ya ke ba.



~_____🌹_______🔥_____💋_____💘_______💞______🌹_______~



💥💫RANA BATA ƘARYA SAI DAI UWAR DIYA TAJI KUNYA! FRIDAY AFTERNOON, THE  WEDDING DAY (RANAR DAURIN AURE) 🔥



A washe garin ranar ɗaurin aure, tun da asubahin farko, baki suke ta yin sammako suna zuwa gidan biki


Kafin rana ta haska, tuni Gidan Biki Ya cika makil da Al'ummar annabi, babu masaka tsinke, Yan Uwa da Abokan Arziƙi sun cika gida, Abun sai son barka..



Tun da asubahi Hajiya Layla da Hajiya Sarah tare da Ummi da Mami su ka fara ɗaura girke girken abincin bikin.



Auren Unaisah Ya zo da abun ɗaure kai, Har ranar biki babu wanda yasan menene sadakin ta, ko lefenta ba'a kawo gidan su ba, kuma ba'a san ina za'a kai ta ba, amma kowa yasan da katafaren sabon Duplex house din Owais da ke a cikin Estate.



Gaba ɗaya Unaisah ta rasa nutsuwarta da kwanciyar hankalin ta, jiya sun kwana adaki daya da Batool, Yau da safe ta farka babu Batool, ta kira layinta batayi picking ba, sai text message da ta ga ta turo mata.



_sis kiyi haƙuri da abun daya faru jiya, bazan iya sanya Bridal Gown din ki ba, saboda bada ni ta dace ba, kece amarya ke ya dace ki sanya, pls na rokeki don darajar manzon Allah SAW kada ki ki sanya rigarki, In har kina son farin cikina, kuma kada ki damu da rashin zuwana, bana jin dadin jikina ne, sai zuwa anjima zan shigo, ki kula min da kanki rabin raina_ 



Abun da takaranta a cikin sakon kenan, sai dai takasa yarda cewa Batool ta hakura da sanya gown dinta, tana kokwanton anya ita ce da kanta ta tura mata sakon? Kodai sanyata akayi dole ta rubuta mata? Saboda tasan mawuyacin abune Batool ta canza ra'ayi, kuma jiya taga halin da ta shiga akan son rigar, bata tunanin ta cikin sauƙi  zata iya hakura, saidai idan wani abunne ke faruwa.



Taso taje gidan nasu, sai dai ba halin ta fita, saboda shirye shiryen da ake yi mata na shiga ɗakin Mijin ta.



A yanzu haka tana a tsaye cikin bedroom ɗin ta agaban Dressing Mirror,  tana fuskantar madubin ta nutsu tana jin motsin hannuwan designer din da ke ta aikin gyaggyara mata Bridal Gown din da ke a jikin ta, designer din ce ta zo da ita daga Wedding store din su da ke a cikin garin, a wurin su Owais ya yi Order din ta, daga waje su ke shigo da kayan su, babbar macace bayerabiya.



tuni makeup artist ta kammala yi mata kwalliya, idanun ta suna a rufe gam, ta nutsu tana shaƙar fragrance ɗin jikin ta, Yayin da ta yi zurfi a cikin tunanin ta..


_Kada ki yi kuka Unaisah, kada ki bari wani yasan abunda ke damunki! Nasan da wuya, amma Ki daure ki jure, ki rufa mana asiri, dan Allah Unaisah, kada ki bamu kunya a idon duniya, ki bari ayi auran nan Lafiya, Allah yana sane dake, yasan halin da kike a ciki, idan kika miƙa lamuranki gare shi zai kawo maki mafita ta inda ba mu zata_


Maganganun mommynta take tunanowa a cikin zuciyarta,  a lokacin data sameta da safe adaki tana kuka kan darduma.



A cikin Kunnan ta ta tsinkayi Muryar Designer din da ke ta ya ba kyawun ta.




"Wow, Oh My God! Unaisah, you look absolutely stunning, just like a real queen, This bridal gown fits your curves perfectly, and I can't wait to see your husband's reaction when he sees you in this amazing gown I'm sure he'll be blown away"



"Unaisah, now you can open your eyes, please I want you to see how this bridal gown transforms you."



Gently ta soma buɗe idanunta kaitsaye ta fara hango kanta ta cikin madubin gabanta.


Speechless, da sauri ta karasa buɗe idanunta ta zare su, bakin ta abuɗe take kallon ikon Allah..


Wata hadaddiyar mermaid silhouette bridal gown ce, strapless dandatsetsiya




"Unaisah, this bridal gown is custom-made and a limited edition, designed by the renowned fashion designer, Your husband bought it especially for you, and it was expensive"


Waro idanu waje tayi ta kara bude bakin ta da mamakin jin abun da designer din tace.





Kyafƙyafta idanunta tayi kamar a mafarki take kallon kanta ta cikin madubi da tsantsar mamaki akan fuskarta.


A hankali Designer din ta soma kokarin daura mata wani diamond-ecrusted veil asaman hadadden hair style din ta.

 

Ga wani hadadden Bridal flower hair pin da akayi mata ado da shi asaman gashinta.



Ƙafafunta suna asanye da wasu hadaddun High Heels, irin takalmin da in ka sanyasu kake jin tsoron taka ƙasa saboda fargabar kar su 6aci, dakyar aka sanya mata takalman saboda bata saba sanya takalmi mai tsini irin wannan ba..


Akan idanunta ta ɗauko hadaddiyar diamond necklace mai fasalin 5-carat diamond center stone, an kewayeta da adon smaller precious stones, daga cikin jewelry box din data buɗe agaban mirror


ta fara sanya mata a wuyan ta.

 


Gaba ɗaya ta ruɗe da ganin tsadaddun kayayyakin da take sanya mata a jikinta sai kace wata sarauniya"?


Gaba daya ji take kayan sunyi mata nauyi, adon yayi mata yawa, bata kai matsayin da zata sanya su ba, gaba daya kanta ya daure tamau da al'ajabi, So take ta tambayi designer din farashin su sai dai takasa saboda tana jin tsoron taji abun dayafi karfin kunnanta, tarasa gane diamonds din gaske ne ko na ƙarauƙarau ne? Taga dai sai kyalli stones din sukeyi, Badan badan kar ace matar dg batasan  diamond ba ko ace tayi ƙauyanci da ba abun da zai hana ta tambaye ta.



"Something Is missing!"  designer dinne Ta furta.



Aruɗe Unaisah ke kallon ta ta cikin madubin gabanta, ta ɗan yamutsa fuska, adabarbarce tace "ma'am ban gane me ki ke nufi ba? 


 

Murmushi tayi"its something special daya kamata ace na gani a yatsanki, wanda shi kadaine zai kara tabbatar mana da cewa Ke din amarya ce.."



 confusingly, ta ɗago da yatsunta da suka zanu da lalle ta ƙura masu ido, nan take ta gane me ta ke nufi wato zobe da babu"


"Meyasa  Angon naki bai sanya maki ba har ranar auranku, Bansan ko mantawa yayi ba amma ko dai bakuyi dating din juna ba before, auran haɗi ne babu shiri?" (gulma ajali) 


Wani irin haushin ta ne Ya kamata, dama tagaji da tsayuwa..


"Karki damu, bai rage maki kyawun yatsunki ba, kawai muhimmancinsa nake dubawa" 


 Shiru tayi cike da takaici batare data furta kalma ba.


"bari na kira angon naki muji" tana kokarin zaro waya daga aljihun rigarta Unaisah tay saurin ruko wuyan hannun ta..


"Pls, babu bukatar ki kirasa! yanzu haka suna a masallaci gurin daurin aure, bana so mu takura masa, Indai zobene ba mantawa yayi ba, ya riga daya fadamin zai saka min bayan daurin auren mu.... " ajiyar zuciya ta sauke..




A gidan Dr Shureim



Yana atsaye gaban Mirror Yana karasa shirya kan shi, tsadaddar shadda ce a jikin shi Launin Blue sky, A hankali Ya ke  sanya agogo awuyan hannunsa sai sauri yakeyi ganin Lokacin sallar juma'a na dab da cika..


Mika hannu yayi da niyar ya dauki arab turban dinsa daya daura gaban mirror, Unexpected yaga ta zura hannu ta bayansa ta riga ɗauka, juyowa ya yi tare da duban ta, sleeping gown ce sanye a jikin ta, ta tufke gashin kanta da ribbom.


"Sanyin idaniyata"


ta karashe maganar tare da manna masa sumbata kan kuncinsa, ta shafo sajen shi ya lumshe idanun shi tare da furta"Masha Allah" 


Janye hannun ta yayi tare da kawar da shi ya lura nema take ta zautar da maluntakarsa.



"please, Ustatha, kada ki karya min alwalata, baki ga time ba, nafa kusa makara.." ya fada yana nuna mata agogon bango.


"I'm Sorry, mijin so, nima yanzu zan shirya in tafi gidan bikin, Benazir tana ta kira na, kasan mune manyan kawayen uwar amarya, Yar mu zatayi aure yau dole mu kure kur adakanmu"


 Murmushi dr shureim yayi"Zan yi missing ummu Batool, inaso na zama mutun na farko da zai fara ganin shigar da zakiyi yau, but please ki rufemin ko'ina na jikin ki, bana so wani ya gane min sirri na.."


Yar dariya tayi"karka damu abban batool, zanyi yadda ka ke so" murmushi suka sakar wa juna.


"Ina Batool sarkin rigima? Ko acan ta kwana ne"?


"Eh, tana atare da yar uwarta"


Numfasawa yayi"pls nasan abun daya faru jiya ya 6ata maki rai, mu yi hakuri da ita, tun da bata taba mana haka ba.."


"Kada ka damu komai ya wuce, amma zanji kunya yau in har Unaisah taba batool bridal gown  dinta, mutane zasuyi tsegumi, su kansu iyayen ta bazasu ji dadi ba, inaga mijinta da ya siya mata rigar? Ta fada da damuwa akan fuskarta..


Shima damuwarce karara akan fuskarsa"bamu da mafita, kuma bana son ganin Batool cikin damuwa, jiya naji zafin ganin yadda take kuka akan mun furta ba zamu iya siya mata kalar rigar Unaisah ba, amma da Unaisah tazo kinga ta sasanta komai, muyi hakuri da komai zai biyo baya, tun da ta riga da tace zata ba, karmu shiga tsakaninta da yar uwarta pls.."


 ta6e baki Ummi tayi"tom, Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa" ya amsa da ameen.


"Muje na rakaka bakin mota"


"But ki tsaya abayana" dariya tayi dan ta gane mi yake nufi.


Ahaka suka tafi yana agaba tana abayan shi..


Bayan taga Tashin Motar dr shureim da sauri ta nufo upstairs tun tana tafiya akan matakalar ta soma jiyo sautin bugun kofar da Batool takeyi daga cikin dakin ta


Bam! Bam!! Bam!!!



Daga bisani tajiyo muryarta cikin kuka


"Ummina ki budemun Kofar pls, ki taimaka ki buɗe min, na gane kuskure na, kuma na tuba bazan ƙara ba, dan Allah don sonki da manzon Allah SAW ki buɗe min ƙofar ɗakina! Inaso naje gurin Unaisah! Inaso na hadu da yan uwana gurin biki, wallahi na haƙura da bridal gown din zan sanya ankon amarya, bazan ƙaracewa inason wani abu kalar nata ba"


 tsantsar tausayinta ne Ya mamaye zuciyar ummin nata, sai dai bata jin zata Iya buɗe mota ƙofa, Batool nema take taja masu abun kunya.


Idanunta ne suka cicciko tab da kwalla, ta jingina kanta jikin kofar tana jiyo kukan Batool dake karya mata zuciya..


"Laifinki ne Batool, ke kika ja na rufe ki, bada son raina ba, meyasa baki jin maganata? Meyasa kikeso kija mana abun kunya ne"?


"Bazan kara ba Ummina, na daina ki yafe min, ni ma bansan meke damuna ba!, bansan meyasa nakeson komai irin na Unaisah ba, banaso naga tafi ni da wani abu, nafison komai namu iri ɗaya" 



Da rudu Ummi ta saki baki sototo tana sauraron ta..


"Batool why why? Ba fa ciki daya kuka fito ba, sister dinki ce but ki sani don kuna yan'uwa ba hakan yana nufin kaddararku iri ɗaya ba, kowa da yadda Allah ya tsara mashi rayuwarshi, ni na narasa gane Kishi kike da ita? Ko hassada kike mata? Ko kuwa kawai gasa ne"? ta fada idanunta na fitar da ƙwalla..


"Ko kinyi tunanin bansan komai bane? Kinyi henna irin nata, kinyi gyaran gashi irin nata, komai na gyaran jiki da akai mata kema saida akai maki sai kace ku biyu za'a aurar? Angaya maki komai akeso mutun yayi irin na amarya? Ta karashe maganar tare da bugun kofar cikin 6acin rai



"Why Batool? Kin ɗaga min hankali, na tsani hassada arayuwana, mugun ciwo ce dake kashe rayuwar mutun Ya gur6ata masa tunani, bana so ki zama daya daga cikin wadanda zasu nakasa rayuwarsu da hassada..."


"Ki fahimce ni ummina, Wallahi ba hassada nake ma Unaisah ba, kuma bana kishi da ita, sannan ba gasa nake da ita ba,  nima bansan meke damuna ba, Ina jin haushin abun da nakeyi, na tsani kaina.." cikin shesshekar kuka ta ƙarashe maganar..


"Batool na fahimce ki, Ki daina kuka bana sonji" amsawa tayi da toh..


Zurfin tunani ta shiga, tabbas ta yarda da maganar Batool amma meyasa take mata haka?


 Zuciyarta ce ta bata amsa da cewa"ko dai son Owais ta ke yi shiyasa ta ke yin komai irin na Unaisah donta burge shi kamar yadda Unaisah zata burge shi .."


 gabanta ne Ya fadi daram.


Arude ta furta"batool Kina jina!

"Inaji ummina"


"Ki ji tsoron Allah ki faɗamin gaskiya! Ko dai Dg kike so"?


"Ni ba sonshi nake ba.."_ bata kare maganarba Ta katse ta"naji bakison shi, amma baki tunanin shi? Ko jin faduwar gaba idan kika gan shi"? 


Shiru tayi  kamar bataji me tace ba.


Knocking kofar tayi"baki bani amsa ba, nasan kina jina, pls ki faɗamin zan nema maki mafita ne" 


"Duk abun da kika tambaya inayi, sai nayi tunaninshi nake jin dadi araina, ko 6atamun rai akayi da zarar na tuna shi nake mantawa da komai, kuma bana jin dadi idan Unaisah ta fadamin ya siya mata abu, ni bai siya min ba, ko inji suna waya, wlh haushi nakeji kamar in haɗiyi zuciyata, amma inason unaisah, kawai ni banason kulawar da suke ba Juna ita da Chief, .." 


kasa ƙarasa maganar tayi jin Sallallamin da Ummi ke yi..


"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un, abun da nake gudun ya faru ya faru! Batool son shi ki ke yi! Shiyasa kike kishi da Yar uwarki, ki faɗa min tun yaushe kike son shi"?


"Ummi ba son shi nike ba, Ni bazan iya son mijin Unaisah ba, kuma na daɗe inajin shi araina, tun kafin nasan yana son  Unaisah ..." 


wani irin sarawar ciwon kai Ummi taji, ji take inama zata Iya cika ma batool burinta, saboda batason ta nemi wani abu ta rasa amma wannan karan tazo da abun daya fi karfin su.


"Batool, Kiyi hakuri, nasan da ciwo, amma ki daure, ki cire shi aranki, nasan kin sani, Unaisah itace Second wife din shi, ba lallai In yana da ra'ayin ƙara aure ba, kuma ni bana so ma kaddarar aure ta hadaki da Unaisah, saboda zaku yi ta samun sabani ne, in sha Allah zan tayaki da addu'a Allah ya za6a maki mafi alkhairi cikin samarin dake zuwa neman auren ki. .." 


bata karashe maganar ba, Batool Ta rushe da kuka kamar ranta zai fita..


Itama kukanne ke nema Ya kwace mata..


"Zan tafi Batool, ummu Unaisah tana jira na, kada su ji ni shiru, nasan zaki kuntata amma bazan iya bude ki ba, zamanki agida sai yafi mana kwanciyar hankali please, Kiyi hakuri ki daina kuka banaso, kici breakfast din dana ajiye maki akan table"


 tana karashe maganar ta juya da dan gudunta ta sauko down tana kuka ta nufi ɗaki don ta shirya.


A bangaren Batool,  tana ta bubbuga kofar, hawaye sun wanke fuskarta, ƙunci da bakin ciki suka mamaye zuciyarta, gaba daya ta haukace ta koma bubbuga kanta jikin kofar, nan take hancin ta ya soma bleeding, fatar goshinta tayi jawur tana barazanar fashewa saboda buguwar da ta yi, lokaci daya wani azababben ciwon 6arin kai Ya ziyarce ta, wani irin jiri ne ya kwasheta bata sa'adda ta yanke jiki ta kife kan floor ba, ga wani irin chest pain daya fara addabarta, gaba daya ta fita hayyacin ta, cikin karyayyar murya ta soma sambatu 



_mutuwa zanyi in ban same shi ba, na fita son shi, ita bashi take so ba, ni nake son shi.. " 💔




Alhamdulillah, Aure Ya ɗauru, bayan kammala Sallar Juma'a Dubban Jama'a Sun shaida ɗaurin auren Director General Owais Sharafudeen Obinna tare da Amaryarsa Unaisah Zaheer Tajudeen, Wanda aka gudanar A Masallacin Sheikh Imam malik,  duniya ce ta shaida daurin Auran Unaisah, ba'a taba daurin auren daya yaɗu irin nata ba, in a short time Labarin auranta ya karaɗe duniya,Yan jarida suka dinga magana akan shi,  Social media ko'ina zancen auran ta ake yi, abu biyune Yasa Aurensu Yayi shura, Na farko kowa yasan Dg da Unaisah tun lokacin da asirin kurkukun kaddara ya tonu su ka yi farin jini na fitar shari'a.


 Abu na biyu dayasa Auran Unaisah Ya shahara a fadin duniya, bakomai bane fa ce Expensive Downry dinta, yana ɗaya daga cikin sadaki mafi tsada a duniya, sadakin da kowa ya ke ta jira yaji menene, Taj Bai bayyana ba ko ita Unaisan da mommynta basu sani ba, ya boye ne saboda baison surutun mutane, baima so sadakin ya kai haka tsada ba, ba yadda zaiyi ne saboda mahaifiyar ango ce ta biya sadakin shalelenta, sai agurin ɗaurin auren, shiekh Imam Malik Ya zayyana sadakin Unaisah tiryan tiryan kowa yaji kuma ya shaida.



Sadakin Unaisah dai an biya shine da 50-carat Heart-Shaped Diamond Pendant mai darajar gaske.

 


su nan wannan sadakin burin kowace ƴa mace, dole mutane suyi tsegumi, Labarin sadakin Unaisah Ya zama ruwan dare ko'ina zancen shi akeyi, Mutane har sun fara tunanin yaya gidanta zai kasance! Don sun fahimci angonta ashirye yake da ya ƙarar da tattalin arzikinsa akanta, ganin yadda yake almubazzaranci da dukiya akan amaryarsa, kamar baison zafin neman ta ba, ya siyeta da darajarta tun da aka fara shagalin bai kashe abun da yayi kasa da dala dubu ba, al'umar duniya sun ruɗe.


Gidajen Talabijin da radio sai taɗin auren su a ke yi..



Kwata kwata Unaisah batasan Auranta ya kammalu ba, sai dai faduwar gaba da take taji, a lokacin designer din ta gama shiryata, Unexpected wayarta da ke ajiye kan drawer ta soma ruri.



 da sauri madam ta mika mata wayar, ta kar6a tare da duban me kiran nata.


"Murmushi tayi, cike da zullumin mai zai faɗa mata tayi picking call ɗin ta kara a kunnanta..


Sanyayyar muryarsa ce ta ratsa kunnanta"Alhamdulillah Unaisah my Angel, kin zama mallaki na, halak malak, ke tawa ce, burina ya cika na ganin ranar dana daɗe ina jiran ta..." 


nutsuwa tayi tana sauraron shi aranta ta ayyana wai dagaske auranta ya ɗauru? Yanzu ita matar yaya Owais ce? Kishiyar Nazli? Ya Allah


Idanunta ne suka cuccuko da kwalla cikin rawar murya ta furta"yaya Owais, ina tayamu murna, Alhamdulillah.... " 


cikin shesshekar kuka ta yi maganar, tana so ta zukunna tayi sujuddusshukur sai dai gown din jikinta ta matse ta..


Kamar daga sama ta tsinkayi miryoyinsu a cikin kunnuwanta..


Wata irin buɗa suke rangwaɗawa cikin zazzaƙar muryarsu, daga can cikin gidan ayyyiririiiiiiii..




"You're no longer Unaisah Zaheer Tajuddeen! You're now Mrs Owais, Come and take your crown, our bride queen! His princess, Yeeehhhhhhh"



A lokacin kiran nasa har ya katse, godiya tayi mata designer din, sukayi sallama da juna ta tafi.


 A tsanake ta soma tafiya zata fuce daga ɗakin cikin sauri.



Tana fitowa taci karo da bridemates suna tunkaro inda ta ke, gaba daya sun razana da ganin adon jikin ta, tayi masu kyau, fuskokin su ɗauke da fara'a sai murna su ke yi, gaba ɗayan su sun sanya anko din su,  sun daura Red Aso ke headband akan su,  sunyi kyau sosai.


suna tafiya suna ta ka rawa yayin da su ke bin waƙar.  


_Ta zamo amarya

Badan tayi daukaka ba

Ta zamo amarya

Ba domin tafi kyau ba

Ta zamo amarya

Ba domin itace ba

Sai dan mijinta nasan ta

Ashe kaunace_


Baby yau ko gobe (baby)

Ya zamo angon ki (eh)

Amarya ta zama taka (baby)

Kar kayi mata wayo (eh)

Baby yau ko gobe (baby)

Ya zamo angon ki (eh)

Amarya ta zama taka (baby)

Kar kayi mata wayo..


Kunyace ta kama ta ta juya zata koma inda ta fito, da sauri su ka yi mata ƙawanya suka cigaba da 

Waƙe ta suna kewaye ta sai tiƙar rawa su ke yi.


Farin ciki ne ya cika ta, har ta kasa rufe bakin ta, ta dinga sakin dariya tana bin su da kallo ɗaya bayan ɗaya.



Walwalar fuskarta ce ta ɗauke, lokacin da ta lura babu Aminiyarta a cikin su..


"Ina Batool? Batazo ba? Ko tana a cikin gida"?


ta tambaya tana duban su, Parveen tace"ba tazo ba, tun ɗazu muke nemanta bamu ganta ba.. "


"May be bata gama shiryawa bane" acewar Sajeeda.



"Kun tambayi mommynta"? ta faɗa fuskarta a yamutse.


"A'a bamu tambayeta ba" suka haɗa baki gurin furtawa..


Nan take ranta ya bata akwai wani abu daya faru wanda ya hana Batool zuwa, zaiyi wuya in ba maganar jiya bace..



Cikin sauri ta soma tafiya suka bi bayanta kaitsaye suka nufi main Falo na gidan, tun kan su shiga suka soma jiyo haniyar al'umma da ta cika gidan, ga sautin kiɗan Ƙwarya daya karaɗe kunnuwan su.



Suna shiga ciki gaba ɗaya idanu su ka dawo kan Amarya Unaisah, kowa ya zare idanu haɗi da buɗe baki suna bin ta da kallo kamar zasu haɗiyeta saboda kyawun da ta yi.



Jemimah da ke ruke da hannunta ta dinga rada mata ta dinga fadin Tubarkallah kar su cinye mata kurwarta, batasan sa'adda ta saki dariya ba.



Aikuwa kowa yayi ta santin ta suna yaba kyanta, duk ta kasa saƙewa dakyar take iya kallon su cike da jin kunya, Ankon da iyaye mata suka sanya tsadaddar atampa ce chiganvy, kowacce ta kashe ɗaurin kallabin ta abun sai wanda ya gani, gida ya cika makil wasu suna ta taka rawa, yayin da wasu suke cin abinci, wasu fira su ke yi cikin nishaɗi.



Hajiya adama ce ta nufosu tana karasowa ta rungume Unaisah tare da shafa bayanta tana fadin"Masha Allah Unaisah, My baby Angel, Ubangiji Allah ya baku zaman lafiya, Allah Ya baku zuri'a ɗayyiba..." a hankali take amsawa da ameen ameen mommy.

.

"Kai Masha Allah, tubarakallahu Ahsanul khalikin, Ayyiriyiriiiii!  Amarsu Ta Ango! amarya Bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida!, Dan Allah ku bani guri, In rungumi jiƙata, adinga hadawa da tubarkallah.." muryar Hajiya layla suka jiyo tana magana cikin raha, kowa dake agurin ya kama dariya, murmushi Unaisah tasaki tana kallon grandma ɗin ta dake tunkaro su hannun ta ruƙe da juice da take sha, tana karasowa ta rungumeta tana shi mata albarka tare da fatan Alkhairi tana amsawa da ameen ameen hadi da yi mata godiya.


Unexpected suka tsinkayi Muryar Sister Zahra tana yi mata kirari


"farin wata sha kallo, tauraruwar dake haskaka sararin samaniya, dawisu sarkin ado, the Dg's wife, nan gani nan bari, dukiyar dg ce... "


 gaba ɗaya suka sanya dariya, suna kallon ta yayin da take shigowa ta ƙofar falo, ankon yan matan amarya ne a jikin ta, kana kallon ta zaka gane akwai ciki a jikin ta, tayi ƙiba hutu ya zauna mata, Unaisah taji dadin kirarin da tayi mata, tana ƙarasowa ta rungume Unaisah kamar zata mayar da ita cikin ta.


"Unaisah ina yi maki fatan Alkhairi, Allah yasa mutuwa kadai zata raba... " amsawa tayi da ameen nagode Aunty Zahrana, Allah ya sauke ki lafiya.

"Ameen nagode Unaisahna"


"Ina Aunty Aneelerh"? 


Zahra tace"suna acan dakin Uwar Amarya..."


"Nagode Aunty Zahra, bari naje na same su... " ta faɗa tare da juyawa ta nufi dakin mommyn ta.


A bangaren Benazir, bayan da Taj ya kira wayarta ya faɗa mata aure ya ɗauru.. 


 bai ƙare maganar ba, tayi rejecting call din ta zauna gefen gado, batasan sa'adda ta fashe da kuka ba saboda bata shirya rabuwa da Unaisah ba, tana jin kewarta tunkafin zuwan wannan ranar, Aisha da Aneelerh sun taru akanta, suna ta lallashinta tare da bata ba ki.



"Haba mana, Unaisah ba wata uwa duniya zataje ba, a cikin estate din nan gidan ta ya ke, ko ihu kikayi zata jiyo ki ne, sunna fa zata raya, ke ba abun farin cikin ki bane? Yar ki tayi aure, ta auri nagartaccen namiji ɗan babban gida, da kowa ke burin ya haɗa zuri'a da su...  "


 Aisha ce ta fada cikin sanyin murya.


Tana shesshekar kuka tace"hmm ba za ku gane ba, ni banyi wata rayuwa mai tsayi da Unaisah ba, duka fa baifi shekaru ƙalilan ba da mukayi atare, yanzu kuma tayi aure, zata koma gidan mijinta da zama, ita kadaice fa gareni, ina sonta a kusa dani, gani nake kamar in ta tafi ba lallai ta samu kulawar da muke bata agida ba, har yanzu yarince fa, ku duba kuka ga irin kishiyar da zata zauna da ita, ina jin duk ba daɗi, bansan ya zanyi ba..."


Aneelerh tace"please ki daina wannan maganar, kin san yadda dg ke sonta, in sha Allah Unaisah zata samu kulawarsa, karki wani damu da kishiyarta, bata fi Unaisah da komai ba, kuma kowa da matsayinsa a wurin dg, ni nasan zaiyi adalci a tsakanin su in sha Allah"


Cigaba da share kwalla tayi tana sauraron su


"Hakuri zakiyi Benazir, kowa fa haka akayi masa auran nan, kin sani kema, ni banaso Unaisah tazo ta sameki kina kukan nan wallahi zaki daga mata hankali ne..." jinjina kai ta danyi ta soma share hawayen ta da hanky.


"Yawwa ko kefa, bari na gyara maki daurin ɗan kwalin..." ta fada tana gyara mata head ɗin ta daya karkace.


 gaba dayansu sunyi kyau cikin ankonsu..


Aisha tace"farin ciki yakamata muyi Benazir, tun da aka fara bikin nan dg ke 6arin dollars akan Unaisah, kamar baisan zafin neman su ba, sai fa kana son abu kake siyansa da daraja, maganar kishiya mu aje ta gefe, Unaisah fa babu mai iya ja da ita wallahi, ita da take da mu? Babu wani lagwon namiji da ban sani ba, Allah idan dg ya shiga tafin hannun Unaisah mai ƙwatarsa sai ya shirya...." 


gaba ɗaya suka sanya dariya..


Anilah tace"godiya yakamata muyi wa Allah, Wallahi Unaisah tayi dacen miji, ga kyawawan halaye, komai Allah ya basa! kinji kuwa yadda al'umar duniya ke taɗin bikin Unaisah"? 


Murmushi Benazir tayi"mungode ma Allah, ɗiyar mu tayi goshi, Ina alfahari da dg, na yarda da son da ya ke yi mata, fatana Allah ya basu zaman lafiya da ita da mijinta da kishiyar ta... "


Gaba ɗaya suka amsa mata da ameen.


"Ummm Itama dai Unaisah zataje taji abun da mu ka ji A first night din mu.."


waro ido su ka yi jin abun da Benazir tace, aikuwa suka tuntsire da dariya, Aisha tace"Allah ya shirya ki Benazir, me hali bazai ta6a canzawa ba, har yanzu kina nan da rashin kunyarki, yanzu nan fa kika gama kukan munafurcin za'a rabaki da ƴarƙi..." dariya Benazir tayi"to ya zanyi Aisha! Abun nan fa ya riga daya faru, dole Unaisah ta tafi gidan mijin ta shikenan ba zanyi raha ba.." 


Aneelerh tace"baiwar Allah, tun kafin ta mallaki hankalinta take da burin yin aure, tunkan tasan ma'anar auren, ba dan komai ba sai don saboda ganin irin rayuwar farin cikin da mu ke yi Nida Uzair a lokacin, ni dai fatana Allah yasa Unaisah ta more rayuwar auranta kamar yadda take saran zataji dadi idan tayi aure, Allah yasa kar tayi danasani, saboda inason ta cika burin ta"


 idanunta cike tab da kwalla tayi maganar tunawa da marigayi Uzair.


gaba daya jikin su yayi sanyi..


In a broken Voice Benazir da Anila suka hada baki gurin furta"ubangiji Allah yajiƙan Uzair, Allah yakai rahama kabarinsa"


 "cikin sanyin murya ta amsa masu da Ameen"


Shiru su ka yi na ɗan wani lokaci babu wanda ya ƙara furta kalma.


"Yakamata mu fita kar aji uwar amarya shiru bata leƙo waje ba, kuma mun bar su mami da aikin tar6ar baki"


 Aneelerh tace ta faɗa tana mikewa Ummi tace"in da Allah ya rufa mana asiri sai bayan biki da sati ɗaya za'ayi dinner, kafin ranar zamu ƙara shiri"


"Ni dai ba haka naso ba wallahi, banji dadi da Owais ya tsara dinner har sai bayan sati daya da yin auren ba, dama dai agida zata zauna kafin ranar dinner din da naji dadi, kuma wai ba gidanta za'a fara kaita ba, gidan iyayensa za'a wuce da ita, jiya Taj ya ke faɗa min, na rasa gane meyasa suka za6i su yi hakan? Bansan ko haka suke yin auren su ba, Ni dai a asanina amarya gidanta ake fara kaita bayan biki"


Ummi tace"wannan duk ba abun tashin hankali bane, munsan mutanan nan, sunyi mana halaccin da ba zamu iya biyan su ba, komai suka yanke akan Unaisah muyi masu kyakkyawan zato"


Ajiyar zuciya ta sauke"hakane kuma, nima na faɗa ne kawai  ba dan ina nufin wani ba" 


Aneelerh tace"ni nafi tunanin Owais ne a bayan komai, may be akwai wani surprise da zaiyi ma Unaisah shiyasa bayason kowa nata ya rakata gidanta, saboda ita ya ke son ta fara zuwa, shiyasa ya tsara a fara kaita gidan su daga can sai ya ɗauke ta yakaita gidan sa...  " ta kare maganar idanunta a cikin na Benazir dake kallonta..


Ummi tace"ni kuma abun da nake tunani game da dinner din da za'ayi after one week da yin auren, watakil yana son kafin ranar ta samu ciki.... " 

waro idanu waje su ka yi jin abunda Ummi tace ita kanta da tayi maganar sai taji abun bankwarakwai, gaba daya suka bushe da dariya cikin nishaɗi..



Knocking din ƙofa ne ya katse firar ta su.


"Wanene"?


"Mommy ni ce..." ajiyar zuciya ta sauke"shigo ciki" buɗe ƙofar tayi ta shiga, waro idanu waje su kayi tare da bude baki suna kallon ta, wata irin kunya taji ta kamata, tayi saurin sunnar da kanta ƙasa.


"Wow, babe Unaisah irin wannan kyau haka? Kamar wadda zataje gasar miss world? aisha ce ta faɗa tare da rungumar ta, tana dan shafa bayanta"masha Allah Unaisah finally kin zama matar dg, Allah ya sanya Albarka a auranku..."


 amsa mata tayi da ameen Benazir ta nufo ta, da murmushi kan fuskarta, tana ganin mamanta ta yi saurin karasawa gareta ta rungumeta tightly a kirjinta, batare da sun iya furta kalma ba, kowa yana jin rashin dadin rabuwar da zasuyi da juna.


"Unaisah.." Anila ce ta kirata a hankali ta raba jikinta daga na mommynta taje ta rungume Anila.


Bayan data dago Ummi ta ruƙo hannunta ta zaunar da ita daga gefen gadon mommynta, suka zauna gefe da gefen ta, Benazir tana daga tsaye tana kallonta da rinannun idanun ta.


Ummi ce ta fara yi mata nasiha game da zamantakewar Aure, mai matuƙar ratsa zuciya, ta bata shawarwarin da zasu amfane ta, ba Unaisah ba hatta Benazir da Aneelerh sunji dadin nasihar da Ummi tayi mata sosai, bayan da tagama Aneelerh ta ɗaura da yi mata huɗuba, gaba ɗaya suka sa taji ƙarfin gwiwa atare da ita.


Bayan da Aneelerh ta gama, Benazir tace"Unisah, ni ba abun da zance, saboda duk wani abu da zan faɗa, mommies dinki sun faɗa, illa iyaka ince ki ɗauki shawarar su, in sha Allah ba zaki ta6a yin danasani ba ..." idanun ta ne su ka cuko da kwalla.


"Please kada ki zubar da hawayenki Unaisah, Zaki 6ata kwalliyar..." 


Ummi ce ta fada jinjina kanta ta dan yi tana kokarin shanye hawayen ta.


In a broken voice tace"gaba daya Kun kashe min bakina, na rasa tayaya zan iyayi maku godiya, kun gatantani, kun nuna min ƙauna, kun yi min abun da bazan iya biyanku da shi ba, kullum cikin bani shawarwari kukeyi, kun gyarani, kun ilmantar dani, Allah ne kadai zai iya biyanku, Ina alfahari da ku.." 


tun da ta fara yin magana suke kallonta da murmushi kan fuskar su.


Wayar Ummi ce tayi ruri ta mike ta nufi kofar dakin tayi picking, Unaisah tabi bayanta, sai da tabari ta kammala wayar sannan tace"Aunty Ummi, Yar uwata bata zo bikina ba, meyasa ko bata da lafiya ne"? juyowa tayi ta dubi Unaisah


"ba zata samu zuwa ba, cikin ta ke ciwo, amma karki damu tasha magani, lokacin dana baro gidan bacci ta ke yi, ko ba yau ba Batool zatazo gidan ki tun da nan kusa ne" 


girgiza kai Unaisah tayi kamar zata saka kuka tace"Aunty Ummi, kiyi haƙuri amma raina na bani wani abu ne ya faru! Ko sakon da ta turo min raina na bani ba ita ta rubuta shi ba, Ba dan ban yarda da maganar ki ba, dan Allah ki fada min meke damunta? Meyasa ta canza ra'ayinta na kar6ar rigata"?


"Me kuma ya hanata zuwa bikina? Bayan itace babbar ƙawar Amarya, nafi bukatar ganinta akan kowa"


 yanayin yadda tayi maganar da damuwa ne yasa ummi taji jikinta ya yi sanyi laƙwas.


In a cool voice tace"haka ne Unaisah, kin faɗi gaskiya, amma ba abun da kike tunani bane, bazan iya fada maki ba, amma zuwan Batool gidan bikinnan ba alkhairi bane! Kwara zamanta a gida, zaifi mana kwanciyar hankali, ni narasa gane meke damunta kamar mai iskokai..."


 ta fada cikin kunci da 6acin rai. 


"Batool ta bani kunya Unaisah, ta karya min zuciyana..." 


gaban Unaisah ne ya faɗi ganin hawayen dake sauka kan kuncin Ummi.


Cikin rudu tace"Aunty Ummi! Meyasa kikace haka? Saboda abun daya faru jiya? Ko wani abun tayi maki"? 


numfashi taja tare da dan jinjina kanta tace"ba wannan ba Unaisah, ai ƙwara abun da tayi jiya, yau takarasa haukacewa, kawai abun da nakeso dake, pls ki manta da batun zuwan Batool, ba zan ta6a bari tazo ba, kuma kema ban yarda kije inda take ba, ki bata lokaci har sai ta canza tunanin ta..." 


kalaman Ummi sun ɗaga hankalinta, kamar tayi kuka take ji, magiya tadinga yi mata akan ta taimaka ta yafe ma Batool laifin da tayi mata, tabarta tazo in ba haka ba bazataji dadi ba.


Amma ummi ta rufe ido tace wallahi Batool ba za tazo ba, tama cire rai da ganin ta har sai an kammala bikin ta, kuma karta kuskura taje inda take ko tace zata faɗa ma wani in ba haka ba zata sa6a mata, Unaisah ba yadda ta iya dole tabi umarnin Aunty Ummi.


Babu wanda yasan meye faru a tsakanin su, gashi kowa ya damu da rashin ganin Batool, musamman bridemaids, duk wanda ya tambayi ummi ko Unaisah game da Batool sai dai su ce bata da lafiya.




~_____________________________________🌹🔥~




Around ƙarfe biyar na yammacin ranar, motocin su Taj suka karaso cikin gidan domin daukar Amarya, bayan ya kira Benazir ya fada mata su fito da Unaisah suna jiran su.



A main Falo, Benazir tare da aminnanta suka shugo da Unaisah... 


A saman Carpet ta zauna, Hajiya layla da Hajiya adama ne suka fara yi mata nasiha bayan sun gama daga bisani suka sanya mata albarka tare da yi mata fatan Alkhairi dakyar take amsawa kamar zata sanya kuka, Mamie da Ummi ma su ka yi mata huɗu ba kan zamantakewar aure a karshe suka sanya mata albarka tare da fatan Alkhairi..

Daga bisani Hajiya sarah tayi mata nasiha itama.


Kowa dake agidan saida ya yi mata addu'o'i da nasiha tare da fatan Alkhairi, kamar zata fashe da kuka saboda sun karya mata zuciya ji take kamar in ta tafi ba zata sake ganin su ba.


Sallamar Ƴan Uwanta Maza ne ta katse hanzarin su, atare suka kai duban su gare su..


Su biyar ne suka shigo, sun ɗauki wankan Shadda getzna blue sky, hannayen su sanye da tsadaddun agoguna, ga wasu hadaddun takalma a kafafunsu, hair cut din su yafi komai jan hankali, Sajeed da Haris ne agaba, Naufal da javeed suna abiye da bayan su tare da Mubeen a gefen su.


Bridesmaids na ganin su suka fara murna tare da nufar su kamar za su yi hugging din su, suna ta sakin wani ƙayataccen murmushin gefen fuska.




"Daddy Taj ne Ya turo mu don mu fito masa da Unaisah muna jira" Sajeed ne ya faɗa




"Tashi mu tafi Unaisah..." Hajiya adama ce ta faɗa, sai da suka taimaka mata gurin mikewa saboda raunin da ta yi, rungumeta Benazir tayi sosai, ta dinga zuba mata addu'o'i tare da sanya mata albarka, tace ta kwantar da hankalinta, a duk lokacin da take bukatar ganinta ta kirata awaya, cikin shesshekar murya ta amsa mata da toh, kowa dake agurin sun basu tausayi sosai, tsakanin uwa da ya sai Allah..


Yan Uwanta maza suka shiga gaba, Bridemaids suka take mata baya, yayin da sauran yan rakiya suke abiye da bayan su.


Daga cikin waɗanda zasu rakata, bayan braidsmaids, sai hajiya adama da hajiya layla, da kuma Aneelerh, da Ummi da sauran su.


Har suka fuce daga falon Benazir bata daina bin bayansu da kallo ba, kamar tabi su take ji, badan hajiya layla ta kwa6eta ba ai da ba abun da zai hana taje raka diyarta, a karshe zama tayi dirshan kan kujera ta zabga tagumi idanunta cike tab da ƙwalla, Mami da Ummi ne suka kewayeta suna lallashin ta.


A Parking space suka hango iyaye maza, gaba dayansu ankon shadda getzner su ka yi suna atsaitsaye suna jiran fitowar su, tun daga kan Taj dake a ruƙe da hannun Baby junaid, ya shige cikin manya, shima ankon ne ajikin shi, Ya manna bakin glass sai shan kamshi ya ke yi kamar shine angon, Dr shureim yana atare da su, Uncle Abdallah, ga mijin dr yusra wato yaya Salsabeel namu ya sauya ya zama babban mutun, amaryar fa yar gata ce, gaba ɗayan su ne su ka zo tafiya da Unaisah gidan Iyayen mijinta.



Fuskokin kowan nan su ɗauke da fara'a, ta cikin mayafinta take hangen su, kaitsaye ta nufi daddynta, tana karasowa yayi hugging din ta yana shafa bayan ta, ji ta yi kamar ta fashe da kuka.


A kunne yayi mata raɗa"Unaisah, nima inajin abun da ki ke ji, please kada ki sanya damuwa aranki, ki kwantar da hankalin ki, kinsan wa kika aura, ni nayi imanin ba zaki taba danasanin auran za6ina da ki ka yi ba, yau ranar farin ciki ce a gare ki dani kaina, burin da kika daɗe da shi Allah ya cika maki shi Unaisah kin tuna? Ko in tuna maki"? 


Ya faɗa yana leken fuskarta, dariya ta saki har fararen hakoranta su ka bayyanta.


Ɗagowa tayi da kanta daga kan kirjin daddynta, Uncle Abdallah Ya ruƙo hannunta tare da yin hugging dinta, yayi mata addu'o'i tare da fatan Alkhairi, kafin ta matsa gurin Uncle shureim  shima ya sanya mata albarka tare da fatan Alkhairi, ta dinga amsawa da ameen hadi dayi masu godiya, Salsabeel ma ya yi mata addu'o tare da fatan Alkhairi.


Zuƙunnawa tayi gaban baby junaid daya haɗe rai kamar bai ta6a yin dariya ba.


Shafa kumatunsa tayi"my little bro, fadamin waya 6ata maka rai"? Yana cika yana batsewa yace"hmm fushi ni ke da ke, bani ki ka ce zaki aura ba! Shine kikayi auran ki" gaba daya suka sanya dariya, tunawa ta yi da Uncle Uzair da daddynta a lokacin baya, sunyi burin su haɗa ya'yan su Aure, Allah bai nufa ba.


Saitin kunnanshi takai bakin ta cikin raɗa tace"na gane laifi na my little bro, ka yi haƙuri, amma nayi maka alƙawarin in sha Allah zan haifa maka kyakkyawar baby kaga kaima sai kayi auran.."


 6a66akewa yayi da dariyar farin ciki.


"Ki haifa min kyakkyawa mai irin idanunki, da komai naki" dariya tayi cike da nishaɗi.


"Pls kada ka fada ma kowa, daga ni sai kai, alkawari" ta fada tare da miƙa masa yatsanta, Ya sargafo shi da yatsan shi, suka sakarwa juna murmushi.


Kowa ya nutsu yana kallonsu sun burgesu sosai.


Peck ta manna masa a forehead dinsa.


Kafin ta miƙe tsaye, Suna haramar shiga cikin motocin.


Unexpected suka tsinkayi muryar Batool a cikin kunnuwan su.


"Sister ku jira ni... " gaban Ummi ne ya faɗi rass! aranta ta ayyana kamar muryar Batool? Anya itace? Tayaya akai ta buɗe ƙofa bayan na kulle ta, Ya salam in kuwa itace An yanka ta tashi..


kusan atare suka dubi inda take..



cikin sauri ta ke yin tafiya dakyar take taka kafarta saboda tsinin high heels din kafarta, tayi bala'en yin kyau a cikin ankon ta, ta saka Red Aso ke headband akanta, Sumar kanta da tasha gyara ta lullu6e bayanta, sai ka rantse da Allah itama amaryar ce saboda yadda ta yi kyau.


 hankalin Ummi fa ya tashi a sukwane ta daura hannu daya akanta.


 sam taƙi yarda ta haɗa idanunta da Ummi saboda gudun karta hanata sukuni, tunkan ta karaso Unaisah ta nufe ta suka rungume juna, sauran ƙawayen suka nufe su gaba ɗaya su ka kewaye Batool suna ta santin kyan da ankon yayi mata.


Jiki asanyaye Ummi ta dubi dr. shureim harara ya watsa mata tare da yin ƙwafa, nan ta ke ranta ya bata shine ya buɗe ma Batool ƙofa, haɗe rai tayi tana dan murguɗa masa bakin ta a fakaice.



Ruƙo hannun ta Unaisah tayi suka nufo su, with respect ta gaishe da iyayen nasu, suka amsa mata da fara'ar su.



daga bisani, daddyn Unaisah ya buɗe mata backseat ta shiga ta zauna, Aneelerh da hajiya layla suka sanyata tsakiyarsu.


Taj Ya shige mazaunin driver, 


tuni ummi ta ruƙo hanun Batool suka shige motar dr Shureim, hajiya adama a motar abdallah ta zauna tare da baby junaid.


bayan kowan nan su Ya shiga a jere motocin su ka soma tafiya slowly saman titin estate din wanda zai sadasu da gidan su Ango.



Acikin motar Taj Aneeleerh da Hajiya layla sai ƙara yi ma Unaisah Nasiha su ke yi duk don ta sake ta daina jin fargaba. 



A hankali dr shureim keyin driving yana satar kallon Ummi da ke zaune a gefen sa ta cikin madubi, kwata kwata bata lura ba, ta dage sai aikawa Batool harara ta ke yi ta mirror, duk tabi tasha jinin jikin ta da ganin irin kallon da mommyn nata keyi mata, tuni idanun ta sun cuko da ƙwalla.



"Why Aisha? meya haɗa ki da Batool dayaja har kika kulleta adaki? Laifin me ta yi maki please? Ko dan saboda abun daya faru jiya ?



Har saida ta ɗan ji gabanta ya faɗi, cike da ƙarfin hali tace"bata faɗa maka abun kunyar da ta gaya min ba ne... "? 


 

Walwalar fuskarsa ce ta ɗauke, cike da damuwa yace"koma me tayi maki bai kai laifin da zaki kulle ta aɗaki ba, ita ka ɗai agida, idan wani abu ya faru fa? Baki ga yadda na taras da ita ba, kwance kan floor, hancin ta yanata bleeding, kwata kwata bata a hayyacin ta, badan Allah yasa naje gurin dakin nata ba har na jiyo shesshekarta da ban san me zai biyo baya ba"



Hankalin ta ba ƙaramin tashi yayi ba jin abun da ya ce, duk tabi ta rude ta juyar dakai ta dubi Batool data sadda kanta kasa.


"Am sorry babe, banyi don na bata maki rai ba, kodan na ƙuntata maki, sai dan ina gudun abun da zai biyo baya, kinsan ina sonki, bana son duk wani abun da zai bata maki rai, nasan in har kikazo gidan biki za'a iya samun matsala shiyasa naso ki zauna gidan, zaifi mana kwanciyar hankali, bansan haka abun ya faru ba... " 


Cikin sanyin murya tace"bakomai Ummina, ya wuce, ni yakamata in baki hakuri, ban kyauta ba, nayi rashin hankali amma bana so ki damu akaina, In sha Allah bazan kara maimaita kuskuren da nayi ba,.."


 ajiyar Zuciya Ummi ta sauke, taji dadin maganar Batool.



"Bakiji yadda naji dadi ba, haba yanzu nasan batool dina ce.."_


 murmushin karfin hali Batool ta yi wanda bai kai zuci ba, 



~____________________________________🌹~



Idan muka koma bangaren Gidan su Ango, gaba ɗaya Dangin su sun hallara a main falo suna jiran ƙarasowar Amarya da dangin ta, wasu daga cikin matan family din suna a tsaye gaban entry Hall suna jiran zuwan su don su tarbe su.



Lokacin da Motocin suka ƙaraso slowly su ka yi parking a gefen Entry hall a jere, cikin sauri Securities din dake sintiri agurin su ka yi hanzarin matsowa tare da bude cardoors din su.


Gaba dayansu suka fito, Unaisah tana a tsakiyar Aunty Aneelerh da Hajiya layla, ta rufe fuskarta da veil.



Yan Matan Family din dake jiran karasowarsu suna ganinsu suka nufesu suna rangwaɗa buɗa Ayyiriyiriiii, gaba ɗayan su sun ɗauki wankan swiss cord Lace riga da skirt, sun saka asoke akan su dana kafada, sun wanku abunka ga dirarrun mata.


Suka kewaye su suna rangwaɗa buɗa.


A haka suka nufi ciki da Unaisah gabanta nata faɗuwa rass rass ta rasa me ke mata daɗi..


Suna shiga cikin katafare falon wani daddaɗan ƙamshin turare ya cika hancinan su, ga sautin kiɗan waƙar larabawa da ke tashi..



Ta cikin net din gyalen take  satar kallon al'umar dake a cikin falon..


Gaba ɗaya Iyayen ango da kawunnansa  da iyalan su sun hallara a babban falon, kowan nan su yana a zaune kan Sofas karkuso kuga yadda manyan matan suka ca6a adon zinari a wuyansu da hannayen su, wasu diamond necklaces suka sanya, sunyi shiga ta alfarma, sunyi matuƙar yin kyau, Yayin da Uban Ango da Uncles dinsa suke a sanye da dandatsetsiyar shadda  blue sky, wuyan hannayen su asanye ya ke da expensive watches.


cike da aji da ƙasaita su ke sakin murmushin dattako suna kallon dangin Amarya da ke shigowa falo tare da amaryar su..


Hajiya saratu tana a zaune kan sofa tsakankanin Uwar Ango da sheikha mujeedat, tayi ƙiba dumurmur da ita kai kace bata taba shiga damuwa ba arayuwarta, a yanzun ma da ta ke a zaune plate ne ruke a hannunta mai ɗauke da chicken wings soyayyu hankalinta kwance ta ke cin abun ta, hali na nan 


Can na hango Hajjaty da mommy Turai zaune kan Sofa suna ta fira, yanzu fa sun zama dangi, babu mai goranta musu,  shigowar dangin amarya ne Ya katse hanzarin su, kusan atare suka miƙe gaba dayan su don nuna girmamawa, hakan ba ƙaramin faranta ran dangin amarya ya yi ba, cikin fara'a da mutunta juna suka soma gaggaisawa, mazan suka soma yin musabaha, matan kuma sunayin gaisuwar larabawa a tsakaninsu, sunyi masu kyakkyawar tarba, daga bisani kowan nan su Ya samu guri Ya zauna, Dangin amarya suna fuskantar dangin Ango, Unaisah da bridesmates da yan uwan ta maza suna zaune kan lallausan rug..


 

Unexpected idanunta suka hango mata Prime minister ta cikin gyalenta, yana a zaune kan sofa, daga gefen shi mai girma Sharafuddeen suna fira, wani irin faɗuwar gaba taji, wallahi sai taga kamar Danish ne, saboda sumar kan da Hateem ya tara ta kara fiddo da kamanninsa da Danish,  nan take tafara tariyo kyakkyawar fuskarsa, ta dinga jin zuciyarta na bugawa da matsanancin ƙarfi, hawaye su ka ciccika idanun ta, ƙuncin ya mamaye zuciyarta har wani zazza6i take ji a jikin ta, a hankali ta dauke idanun ta daga kan Daddy minister ta mayar da su kan Sheikha Mujeedat, mahaifiyar Man dinta, bazata ta6a manta al,ajabin da tayi ba aranar da taji cewa Danish dan Hateem ne, dama ta daɗe tana ji aranta danish dan wani hamshakin mai kuɗi ne ko basarake ashe hasashenta ba karya bane, wallah taso Danish Ya rayu da iyayen sa, duk da tasan koda yana araye bama lallai ya kulata ba, saboda yafi karfinta nesa ba kusa ba, ba ma ajinta bane indai ta matsayin family za'abi, aranta ji take inama man dinta yana araye koda bazai kulata ba, zataso tagansa cikin rayuwar farin ciki.



Batasan sa'adda hawaye suka fara zarya kan kuncin ta ba..

Kunnuwanta ne suka soma jiyo mata tattaunawar su.



"Madallah, Munji dadin karramawar da ku ka yi mana, wannan ya kara tabbatar mana da cewa yarmu ta shigo gidan mutane masu daraja, da ƙima kuma gidan mutunci da karamci_________ "


 Hajiya adama ce tayi maganar cikin nutsuwa.


Gaba ɗayan su murmushine akan fuskokinsu ga dukkan alamu sunji dadin maganarta.


Ta ɗaura da cewa"babu shakku ko fargaba a tare damu, saboda munsan hannun da ƴar mu ta faɗo, toh ga ƴarkunan Mun kawo maku amana, Allah ya tayaku ruƙon ta.." ta faɗa tare da nuna Unaisah da hannun ta..



Gyaran murya malika sarauta tayi, hankali ya dawo kanta, gently ta soma magana cikin ƙasaita


"Mun kar6i amanarku da hannu bibbiyu, Gaba ɗayan mu muna farin ciki da zuwan ku, kuma muna farin ciki da zuwan Unaisah cikin Family din mu, wannan abun alfahari ne agare mu, samun suruka irin Unaisah, wadda ta fito daga gida na mutunci da tarbiya zai yi wuya a duniyar nan, in sha Allah, alkawarine mukayi maku, Unaisah bazata ta6a maraicin barin gidan iyayenta ba, kuma bazata ta6a danasanin Auran ɗan mu ba... " Kalamanta sun faranta ran su, aneelarh har taji ƙwarin gwiwa atare da ita tasan in ta bama benazir labari ba qaramin dadi zataji ba..




Hajiya saratu tace"Ai in sha Allah yadda Unaisah ta shigo family din nan, mutu karaba mu da ita, zamu tsaya tsayin daka don ganin ta zauna lafiya agidan mijinta, ko yaji bazai dawo da ita gidan iyayen ta ba..." ta ƙarashe maganar tana cizgar fiffiken kaza..


Gaba ɗaya suka sanya dariya cikin raha..


Burin Unaisah gimbiya Mujeedat tayi magana, so take taji muryarta kota samu salama a cikin zuciyarta, saboda gaba daya muryarta irin ta Danish ce dan banbancin kadan ne shi yana namiji ita kuma mace..



Aikuwa Cikin sa'a ta tsinkayi muryar Mujeedat a cikin kunnanta, cikin harshen turanci ta ke yin maganar ta.. 


"yadda Unaisah ta nunama jinin mu ƙauna, ta amince zata rayu da shi tabar gidan iyayenta da danginta saboda shi, ta dawo namu don ta raya sunnar ma'aiki, in sha Allah ba zamu bari tayi danasani ba, ba zamu ba ku kunya ba, Unaisah ƴace agurin mu, kuma lu'u lu'u ce mai daraja mai wuyar samuwa, da kowa ke burin ya mallaka amatsayin surukar sa, amma mu Allah ya azurtamu da samunta, iyayenta sun mana halaccin da ba zamu iya biyan su ba, sun dauki yarsu sun bamu badan isarmu ba, badan matsayinmu ba, badan sun gaji da ita ba, kuma badan basu sonta ba sai don suna son yarsu ta raya sunnar ma'aiki, tayi aure itama ta hayayyafa kamar yadda suma su ka yi, in sha Allah zamu ruƙe Unaisah da hannu bibbiyu, zamu bata kulawarmu, soyayyarmu, goyon bayan mu, kamar yadda muke yiwa ya'yan mu, saboda itama Amana ce agare mu.. "


yadda ta ke yin magana cikin nutsuwa da kasaita tana watsa yatsun hannayenta dake asanye da zobban diamond ba karamin burgesu tayi ba, ta tafi da imanin su.


Baiwar Allah Unaisah kamar sakarya tuni ta shagala tana ta kallon tausasan la66an sheikha mujeedat, danish kawai take tunawa, ji take inama ace itace surukarta wayyo Allah..


Babu wanda yasan kallon ƙurullan da takeyi mata saboda mayafin daya lullu6e fuskarta, falon yayi tsit kowa ya nutsu yana sauraron daddaɗar muryar Sheikha mujeedat, basu taba zaton zata iya magana har haka ba, saboda izzarta..


Sarauta taji daɗin jawabin Sheikha mujeedat, ta taimaka mata data ari bakin ta..


Matar akwai wayewa da tsantsar ilmi akan ta..



Basu bar gidan ba, anan suka tsaya saboda walimar da suka faɗa masu za'ayi anan, da lokacin yin walimar ya yi, gagarumin shagali suka haɗa masu, babu wanda bai nishaɗantu ba, sun ji dadin karramawar da su ka yi ma su.



Bayan kammala walimar, around ƙarfe shida, suka yi masu sallama zasu koma.


 Unaisah kamar tayi hauka saboda zullumi da fargaban karsu tafi su barta, Har bakin motocin su suka rakosu, daddynta ya rungumota yana lallashinta, shi kanshi daurewa kawai yakeyi har kwalla sai da yaji ta cika idanun sa, ta rungume Aunty Aneelerh da aunty Ummi sunata lallashinta, duk saida tabi bridemaids ta rungume su, cikin shesshekar murya take yi musu godiya.


 Kwata kwata babu wanda ya lura babu Batool a cikin su har suka kammala yin bankwana da Unaisah da zumar zasu sake haɗuwa gurin dinner din ta bayan kowan nan su Ya shige cikin mota, akan idanun Unaisah motocin su ka tafi.


Kamar tayi hauka, kwata kwata ta manta da mutanan dake a bayanta ta fashe da kuka, batai aune ba, taji an rungumeta, har saida taji gabanta ya faɗi jin kamar sheikha Mujeedat ce.


Shafa bayanta tayi"karki yi kuka, zaki 6ata makeup dinki, tun kan angon naki ya gani, kiyi hakuri kinji surukata, nasan ba daɗi ka rabu da kowa naka ka shigo cikin dangin da baka taba rayuwa da su ba, amma ki kwantar da hankalin ki, mu ma da haka muka fara, nayi maki alkawarin zan share maki hawayen ki..." 




ai tun da hancinta suka shakar mata turaren sheikha ta kuma tabbatarwa kanta itace ta rungumeta tuni ta nemi kukan da ta ke yi ta rasa, ita dai tana son maman danish din ta, duk da tana jin fargaban karta ta juya mata baya tun da mijin yar ta ta Aura, sai lokacin ma ta tuna da kishiyarta Nazli  bata ganta agidan ba.


Komawa su ka yi da ita cikin gidan, Sarauta ta ruƙe hannunta suka nufi dakinta, a kan gado tace ta zauna, jikinta asanyaye ta zauna tana ta jin faduwar gaba, har abinci tasa maids suka ka kawo mata, tace mata bata jin yunwa taci abinci agida.



Allah Allah take su mika ta gidan ta, saboda takasa sakewa anan gaba daya a matse ta ke, ta ƙosa ta cire bridal gown din jikinta, ta matse ta sosai.


Around ƙarfe shida na mare ce bayan anyi magrib, su ka fito da Unaisah daga cikin gidan, suka nufi jigunanniyar Motar sarauta da ita, gidan baya ta shiga ta zauna sanyin A.c ya daki fatarta, ta ruɗe da ganin haɗuwar motar, irin wadda sarakuna ke hawa, Sheikha mujeedat da hajiya malika ne a mazaunin gaba, tayi mamaki sosai, tayi zaton Owais ne zai zo ya tafi da ita, amma sai taga akasin hakan, tsabar gatanci su biyu zasu kaita gidan ta.


Gimbiya mujeedat ce ke sarrafa motar..


"Unaisah, Akwai gift boxes da muka ajiye maki a ɗakin ki, Idan kin shiga zaki gani... " Sarauta ce ta faɗa, cikin sanyin murya ta  amsa da toh tare dayi mata godiya, tace batason godiya, babu wannan atsakanin su, sun zama ɗaya, murmushi tayi.



"Ko akwai abun da kike buƙata"?


gimbiya Mujeedat ce ta tambayeta, a hankali ta sanya hannu ta yaye mayafin ta ta saci kallonta ta madubin motar dake fuskantar ta, kaitsaye idanun su suka shiga cikin na juna, wani irin faɗuwar gaba taji ganin ta kashe mata ido ɗaya tare dage mata gira, cike da jin kunyarta ta sunnar da kanta ƙasa adabarbarce ta furta"bana buƙatar komai, nagode da kulawar ku"


 murmushin gefen fuska sheikha mujeedat tayi tare da kallon Sarauta itama da murmushi akan fuskarta.


"Kina ta farin ciki kamar ba ƴarki akayima Kishiya ba" Saurata ce ta faɗa da zolaya.



bushewa tayi da dariya"ba zaki gane ba, wallahi Sonta na ke yi, yarinyar tana da Qualities da nakeson inga mace da shi, gaskiya munyi dacen suruka, Owais Ya more mata.." ta faɗa tana satar kallon Unaisah da ta sadda kanta ƙasa, duk tasha jinin jikin ta, tun da sheikha ta kashe mata ido.




GIDAN AMARYA UNAISAH, wani kaya sai amale, Alƙalamina ya girgiza, an kashe min bakina, saboda bazan Iya misalta Haɗuwar Katafaren Gidan ba,  


har motar tayi parking a parking space Unaisah bata ɗago da idanun ta ba,  saida taji alamun buɗewar Cardoors din sannan ta lura.


Bata motsa ba, har saida suka rigata fitowa daga cikin motar, Sheikha mujeedat ta miƙa mata hannunta"mun ƙaraso gidan naki, my baby in-law, zaki iya tafiya kan ƙafafunki, ko kinaso in goyaki in shigar da ke  ciki.."?



 murmushi tayi cikin sauri ta zura hannunta a cikin na sheikha, ta rukota ta fito waje, suka tsaya daga gaban ta, addu'o'i su ka soma yi mata tana amsawa da ameen daga bisani suka sanya mata albarka, tayi zaton zasu rakata cikin gidan ne amma sai taji akasin hakan.


"Ki shiga daga ciki, ki jira mijin ki yana akan hanya..." Sarauta ce ta faɗa.


Jiki asanyaye ta amsa da toh hadi dayi masu godiya, walking slowly ta nufi ƙofar shiga falo...


A hankali ta ke satar kallon ginin kamar a mafarki saboda tagaza yarda gidan ta ne, ta razana da ganin haɗuwarsa, wai anan zatayi rayuwa, hasken electricity ta ko'ina tamkar da rana...


Rantane ya bata basu tafi ba, slowly ta juya tare da kallon su, ile ko suna atsaye gaban motar su suna kallon ta.


Tarasa gane meyesa ba'abari kowa nata ya rakota ba, sai ita kadai? Kamar mara dangi? Ita a yadda ta sani kawayen amarya suna kwana a gidan amarya, amma ita ko rakiya babu wanda yayi mata, sai dai Uwar ango da matar Kawunsa suka rakota, duk da haka taji dadin gatantata da sukayi..


Tana isa bakin kofar, ta ɗaura hannunta jikin glass din da niyar ta tura nan take kofar ta soma zamiyewa, Unexpected tana dira ƙafarta, ta tsinkayi muryar sa a cikin kunnanta.


_My baby bride, I've been counting the minutes until you walked through that door, I'm so glad you're home, I've got a whole night of love planned for us_


arazane ta zare idanunta ganin bata ga kowa ba, ranta ne ya bata muryar na'ura ce sai dai tayi sak irin ta Owais.


Numfasawa tayi tare da sauke nannauyar ajiyar Zuciya, tana ƙarasa shiga ciki, ƙofar tayi locking kanta, Kamar 6arauniya cikin sanɗa take tafiya sautin takunta na fita ƙwas!!ƙwass!


Batasan Ina zata Nufa ba, ganin hanyoyi daban daban Cikin falon, na ƙasa dana stairs harda glass Lift..



again ta kuma tsinkayar muryar na'ura a cikin kunnanta tana yi mata kwatance inda zata ga bedroom ɗinta, a hankali ta nufi hannunta na dama, ta hau stairs ta 6ulo second floor, harta fara gajiya saboda matsewar da takalmanta su ka yi, rigar ma ta fitine ta, dakyar ta gano wata hadaddiyar ƙofa, nan take ranta ya bata shine bedroom ɗinta, ganin tana da security yasa ta ɗaura finger ɗinta, nan take ƙofar ta buɗe a hankali,  wani spiral stairs tayi aran gama da shi, cikin 6acin rai ta bubbuga kafafunta, aranta ta ayyana babu abun da zai hana ta tu6e bridal gown din nan ko yazo ko bai zo ba, sai ta cire ta..


Hawa tayi kan staircase din tana cikin tafiya kamar wadda kwai ya fashe mawa akai..


A matuƙar ruɗe ta ɗan dakata dayin tafiyar tana kallon abun daya daure mata kai, wato ainihi stairs din da take akan shi kaitsaye zai kaita cikin Bedroom ɗin ta daga inda ta ke atsaye kan staircase din tana hangen katafaren Master Bedroom ɗin.


Farawa da bismillah, a hankali take bin bedroom din da kallo tun daga kan katafaren Four poster bed din cikin sa irin na sarauniya, an ƙawata shi da 24 karat gold leaf, and precious gems, gaba dayansa wasu dogayen curtains ne kewaye da shi shara shara with a velvet canopy,  gefe da gefen gadon wasu dankara dankaran bedside drawers ne ɗauke da crystal lamps, buɗe baki tayi kamar shashasha tabi ceilling din dakin da kallo wasu kawatattun Feather pendant lamp ne da ke haskaka tsakar dakin, tun daga gaban gadon har izuwa interior din dakin an shimfide shi da tattausan Ivory shag rug, very fury, daga saman shi Glass candles ne a cikin kwalba sai ci suke da wuta gwanin ban sha'awa, ga wasu floor Lamps na tsaye a tsakar ɗakin, daga can cikin kusurwar data kalli bangaren dama na bedroom ɗin seating area ne wata White corner couch ce zungureriya  yar ubansu mai numfashi, an ƙawata saman ta da throw pillows, gabanta glass tables ne mai dauke da crystal vase, ga wasu bean bag chairs dake a gurin ɗumduma ɗunduma  jefi jefi take ganin gift boxes akan rug masu kyan gaske nan take ta fahimci kyaututtukan da Surukarta tace zata gani a ɗakin ta ne, ko menene a cikin su?



wani ni'imtaccen sanyin A.c mai haɗe da kamshin turaren ɗaki ne Ya ratsa kofofin hancin ta har saida ta lumshe idanun ta, tun da uwarta ta haife ta bata ta6a ganin tsantsararren bedroom irin wannan ba! Har ta fara kokwanton anya mallakin ta ne?



Saboda yafi karfinta, batajin zata iya kwana a cikin sa"


Ni kaina da nake rubutawa na jinjinawa haduwarsa, A hakan ma bakomai zan iya fayyace maku ba, saboda ina jin tsoron ruwan alkamina ya kare gurin zayyana maku komai.


A hankali ta ƙarasa saukowa cikin bedroom ɗin wanda gaba ɗaya furnitures ɗin cikinsa launin Bold pink and navy ne, aranta sai santin bedroom din ta ke yi, tana kara jinjinawa haduwarsa, har wani jinjina kanta takeyi irin ta ruɗen nan.


Bata nufi ko'ina ba sai gaban gadon daya tsone mata ido, saman shi tabi da kallo lumbutsetsiyar mattress ce shimfide da bedsheet, rabinta a lullu6e ya ke da lallausan duvet, gaba ɗaya kewayen mattress din an jera throw pillows a sama, daga tsakiyar mattress din furanni ne launin pink and Red masu ƙamshin gaske.. 



Juyawa tayi baya tana karewa ko'ina kallo kamar wuyanta zai balle



"Hmmmmm " ta furta sautin tana ruƙe qugun ta, gaba daya ta kasa furta kalma..




Wuce wa tayi ta nufi interior din dakin, daga cikinsa kana Iya hangen komai dake a cikin toilet  ta cikin Glass wall, haka zalika data nufi ciki tayi arba da kofar dressing room wadda shima bangon glashinne tana hangen walk-in closet dinta, shaƙe da suturun sanyawa kamar a company, ga wani faskeken dressing mirror ɗan uban su...



Babu ce kadai ke babu adakin Amarya Unaisah, amma fa an zuba mata tsadaddun furnitures na gani na faɗa.


Daga ganin fasalin ɗakin zaka fahimci don masoya akayi shi..


A ƙalla ta shafe rabin awa tana bin ɗakin da kallon ƙurulla batare da gajiyawa ba, daga bisani ta fara tunanin Ina mijin nata ya ke? Taji shiru babu motsin sa, gashi taƙosa tagan shi saboda idanunta sunyi maraicin ganin shi, ta yi kewar shi, tun bayan da aka sanya bikin su bata ƙara ganin sa ba, kamar yadda yayi alƙawarin sai bayan auran su zai bayyana saboda ba zai iya jure kallon ta ba, still tana jin fargaban haɗuwa dashi a matsayin mijin ta.


Tana tsaka da yin tufka da warwara, cikin ta ya fara kukan yunwa, ga wani irin baccin gajiya dake kokarin fisgarta har wani jiri jiri take gani a cikin idanun ta da ke lumshewa, a hankali ta dubi agogon bango, ƙiris ya rage afara kiran sallar isha'i, baiwar Allah tana ta sa ran ganin shi shiru baizo ba, tunawa tayi da wayarta da sauri ta shasshafa jikinta, yamutsa fuska tayi tunawa da babu wayar atare da ita, ta mantata a gida, taji takaici kamar tayi kuka..



Matsawa ta yi daga gaban tamfatsetsen dressing mirror din ɗakin, ta zauna kan kujerar gabansa, tana ta jiran ƙarasowar yaya Owais, don su ci dinner a tare kamar yadda suka ɗaukarwa juna alkawarin zasuyi a karo na farko da suka kasance ma'aurata 🌹


Batasan sa'adda ta fara yin gyangyadi ba, ga wata jarababbiyar hamma data cuka bakin ta, ta ɗan kishindiɗa bayanta jikin kujerar..



A lokacin data fidda rai da zuwan angon nata, bacci ya yi awon gaba da ita, ta saki baki da hanci tana ta yin minsharin gajiya.




~_________________________________🌹~

   



*DG OWAIS🔥*



Around ƙarfe tara na dare daidai wata Hamshakiyar Mota ta biyo titin da zai sada ka da gidan Amarya.



Idanunsa suna a lumshe yayin da ya ke a hakimce cikin backseat na hamshakiyar motar shi, ya ɗauki wankan dandatsetsiyar shadda Getzner wagambari Launin sky blue short sleeve shirt, da dogon wando, ya daura babbar riga ta alfarma daga sama, anyi mata aikin hannu har ƙyalli ta ke yi.



ga wata haɗaɗɗiyar Hula daya daura a kansa, hakan bai boye lallausar sumar kan shi ba, ta lullu6e ilahirin ƙeyarsa har izuwa saman wuyansa.


 Wuyan hannunsa na dama na asanye da tsadaddiyar agogo ƙirar Rolex Daytona.


 gaba ɗaya Ƙamshin turarensa ya buɗe Motar, girma da kwanciyar hankali sun zauna masa, ta yadda ko fatarsa ka kalla zaka shaida hakan, sajen fuskarsa ya fi komai jan hankali, Yadda ya lumshe idanunsa sai ka yi zaton bacci ya ke yi alhalin kuwa idanunsa biyu tsabar qasaita ce ta angon Gimbiyar Izza.


Babban Amininsa big guy Omar yana a zaune saman seat din gefensa, ya tattara hankalinsa akan iphone dinsa da ya ke daddanawa, kusan shigar su kala daya banbancin su shi bai sanya babbar riga ba.


Wayarsa ce tayi ringing, picking yayi tare da kara wayar a kunnansa..


"Wifey, me ki ke yi har yanzu baki yi bacci ba"?


On the other hand tace"yaya Owais nake nema, Ina kiransa baya shiga, pls idan kuna a tare ka ba shi wayar" kallon Owais ya yi tare da cewa"Hindu ce, tana son magana dakai" batare daya buɗe idanunsa ba ya mika masa hannu ya kar6i wayar ya kara a kunne..


Shiru yayi yana sauraron ta"big bro, ka yi hakuri ban shigo gida ba yau, bana jin dadine, inataso in tayaka Murna, Allah ya sanya alkhairi, Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba..."


 Ƙasa ƙasa da murya ya amsa da ameen My Lil' sis, nagode da addu'arki, karki damu, nasan halin da kike a ciki bai kamata kina fita ba, idan kinji sauƙi ranar Dinner sai ki shigo"


"Okay yayana nakaina, nagode da kulawarka agareni, Ka gaishe min Amaryarmu"



"Zataji, nima ki kula min da kanki," amsawa tayi da toh kafin su kayi sallama ya mika ma Omar Wayar.



"Kamar kana da damuwa? nifa na lura da kai tun gurin ɗaurin aure babu annuri akan fuskarka"



Bai iya furta kalma ba, yayi shiru yanayin fuskarsa ba walwala.



"Owais, kar dai kace min har yanzu kana... " bai ƙare maganar ba ya yi saurin katse shi da cewa"pls ba sai ka faɗa ba, kamanta kawai, bana son ji"




jinjina kai Omar yayi batare daya ƙara furta kalma ba.




Officer din da ke driving dinsu kwata kwata bayajin abunda suke tattaunawa, Yana a driver's seat,  a hankali Motar su ta ƙara so layin Gidan tana kokarin kunna kai ta main entrance, kamar ance ya dubi window glass din Motar, Unexpected idanunsa sukayi mashi Tozali da mutun ra6e jikin bangon gidansa kamar aljana.



Da ruɗu akan fuskarsa ya furta"tsayar da motar anan.." nan take drivern ya tsaya..


Big guy yace"meya faru naji kace a tsaida motar bayan bamu kaiga shiga ciki ba"? 


Ya faɗa yana kallon fuskar Owais da hankalinsa ke akan abunda idanunsa ke nuna masa..


Bai iya bashi amsa ba, cikin sauri ya buɗe murfin motar ya fito ya nufi bangon dayake hango mutun a ra6e.


kasantuwar akwai hasken electricity tamkar da rana shiyasa ya iya ganin ta dakyau.


Fitowa Omar ya yi daga Motar ya bi bayan shi..


Daya kusa karasa kusa da ita sai ya ɗan rage saurin shi ya ƙura idanun shi akanta.



babu kallabi akanta, kamar mahaukaciya, sumar kanta duk ta rufe fuskarta, mayafinta da gyalen suna a ƙasa ta jefar da su.


Babu alamun taji motsin mutum kamar wadda ta suma atsaye.


Daga gabanta ya tsaya sa'ilin daya gane wacece yayi mamakin ganin ta da dadaren nan tsaye jikin bangon gidansa kamar aljana, cikin ruɗu ya furta"Batool....! Kece! Me kike yi anan"? Shiru bata motsa ba..


Ɗaga murya yayi"Batool... "!


 Kaitsaye kiran ya shiga kunnanta bata tsammaci shine ba, a firgice ta zabura zata arta wa na kare yayi saurin furta"ni ne Batool, yaya Owais, meke damunki ne.."?


 dakawa tayi a tsananin tsorace ta zare brown eyes dinsa akan fuskarsa, wani shock taji sa'ilin data saka idanunta a cikin nashi, ƙamshim turaren shi ya cika hancin ta.


Omar daya karaso daga gefen shi ya tsaya yana dubanta cike da mamakin ganin ta.


cikin rawar murya ta furta"yaya Owais.. Yaya Omar.. "


"Batool me kike yi da daren nan a jikin bangon gidana? Keda wa ku ka zo ne"? Shiru ta yi batare data furta uffan ba.


Big guy yace"ba ƴan matan amarya sun tafi gidajensu daga gidansu ango bayan walima ba? Ko tare da ke aka rakota nan ne"? 


Kunya ce ta kama ta daƙyar ta iya furta"inason ganin Unaisah saboda banyi bankwana da ita ba, shiyasa nazo" kallon juna su ka yi da alamun rashin yarda da maganarta.


"Batool dare ya yi, nasan iyayenki sunata nemanki, Unaisah ta yi bacci yanzu, Muje na sauke ki gida" dg ne ya faɗa cikin sigar lallashi.


"Mu tafi kinji"? Jinjina kai ta yi ba dan taso ba, da sauri Omar ya ɗauko mata veil dinta da dankwalin ta, ta kar6a ta ruƙe a hannunta, su ka yi gaba tabi bayan su, buɗe mata mota Omar yayi ta shiga ta zauna, Dg ya zagaya Other side din ta ya zauna.


Omar ya shiga mazaunin gaba ya zauna.


Kafin Drivern su ya tashi Motar Omar yace"ka fara sauke ni agidana" amsawa yayi da toh..


Tun da Motar ta soma tafiya babu wanda ya ƙara furta kalma, Batool ta yi shiru ta nutsu tana shaƙar kamshin turarensa.


Idanunta sun ciko da ƙwalla, sai satar kallon shi take yi da rinannun idanun ta da suka kaɗa jawur, bakomai take ji ba face raɗaɗin rasa shi da tayi, kallon shi da takeyi ba karamin fama mata raunin son shi yakeyi ba, wata irin wutar son shi ce ke rura a cikin zuciyarta.


Kwata kwata baisan halin da take a ciki ba, cos ya mayar da idanunsa a lumshe yana ta tunanin baby bride dinsa yasan tana can tana jiran ƙarasowar shi.


Bayan sun sauke Omair agaban gidansa, yayi mashi sallama tare da fatan alkhairi kamar karsu rabu da juna bayan tafiyarsa, drivern ya karya kwana ya nufi gidan dr. shurem.


Daga bakin ƙofar shiga yayi parking, jin shiru Batool bata da niyar fita yasa shi firta"mun ƙaraso gidan naku, ki sauka ki shiga" 


ko uffan batace ba, lamarin ya daure masa kai, a hankali ya dube ta, kaitsaye idanunsu suka shiga cikin na juna, wani faɗuwar gaba yaji ganin yadda fuskarta ta 6aci da make up dinta sakamakon kukan data sha, jan baki har takan kumatunta, idanunta sunyi luhu luhu jawur da su.


Aruɗe ya furta"me yake damunki ne? Kinyi kuka ne? Baki da lafiya.. " cikin shesshekar murya tace"kukan rabuwa da Unaisah ne" girgiza kai yayi"ban yarda ba Batool, ba gaskiya kika faɗamin ba! Saboda wannan yafi karfin kukan rabuwa da unaisah, sai kace mutuwa tayi? Bafa kasar ta bari ba, tana a cikin estate din nan aduk lokacin da kikaso ganinta zaki iya zuwa gidanta ko ita tazo gidan ku, babu wanda yayi maki iyaka da ita... " 



yanayin yadda ya ke yin magana cikin tauttausan lafazinsa ba karamin rikitata ya ke yi ba,  jikinta sai tsuma ya ke yi ji take kamar ta rungume shi ko ta samu sassaucin abun da take ji game da shi.


"Fadamin me yake damunki? Kada ki 6oye min Batool, Ni mai share maki hawaye ne, zan iya komai saboda farin cikin ki... " 


bai ƙare maganarba, ta rushe da kukan daya razana sa, ta gaza jure raɗaɗin, gaba daya ya rasa shawo kanta, Cikin shesshekar murya mai hade da haki ta shiga zayyana masa abun da ke damun ta.


"Ya.. ya .. Owais, kak.. Ka auri Unaisah ni baka Aureni ba, bayan na fita sonka, Why don't you love me? ko ban cancanta kaso ni ba?  Meyasa ni ba zaka soni ba! Ka san yadda nakeson ka kuwa, zan iya rasa komai in jure amma bazan iya jure rashin ka ba, ni kadai nasan halin da nake a ciki, babu mai fahimtana, mutuwa zanyi yaya Owais...  "


Hankalinsa Idan yayi dubu toh ya tashi, kalamanta sun razana shi, sam ya kasa katse ta kuma      ya kasa furta kalma saboda ruɗanin daya shiga! Kyawawan idanunsa daya zare suna akan fuskarta data yi sha6a sha6a da hawayenta, soft brown lips dinta sun jiku da hawayen ta tana magana tana shesshekar kuka cikin kunci, Jikinta har kerma yakeyi kamar wacce sanyi ya kama.


"Kai kaɗaine namijin dana so na rayu da shi, bazan iya yin rayuwa da waninka ba, kayi hakuri idan na 6ata maka rai, na kasa jurewa ne, ina da kunya ina da hakuri, amma wannan karon na rasa su gaba daya akanka, tun da nasan na rasaka na har abada... "


 daƙyar ta ƙarshe maganar saboda kukan daya sarketa, ga wani zafi da kirjinta ya yi mata.


Dakyar ya iya tattara nutsuwar shi guri guda ya fahimci inda ta dosa.


 cikin sanyin murya yace"meyasa tuntuni baki faɗamin kina sona ba? Meyasa kika 6oye min Batool? kuma baki tashi faɗamin ba sai bayan dana auri Unaisah? What do you want me to do now? Ya kike so nayi yanzu? wani irin zurfin ciki ne kikayi um"? Kasa magana tayi sai kuka takeyi.



"Fadamin tun yaushe kika fara sona"? 


Cikin shesshekar murya tace


"tun ranar dana fara ganinka amma nima bansan ina sonka ba, bansan me nake ji agame dakai ba sai daga baya na gane a lokacin kuma na makaro saboda na gane Unaisah kakeso tun da daɗewa.. "


 bata ƙare maganar ba ya katse ta da cewa"What made you fall in love with me"? 


batare data ɗago da idanunta ta dube shi ba tace"saboda ina sonka saboda kuma kyawawan halayanka da dabi'unka, amma wlh bayan wannan banso ka don wani abu ba"



 lumshe idanun shi yayi a hankali tare da sake buɗe su kan fuskarta"Allah bai haramtamin auranki ba, don haka ki faɗamin kina son in aureki ki zama ta uku a gidana"?


 a ruɗe ta girgiza kanta"ko da zan mutu bazan iya auren mijin Unaisah ba, ina kishi da ita akan ka, idan na aure ka zamu samu sa6ani da ita, ni kuma banason duk wani abu da zai haɗani da yar uwarta, wallahi na ƙwammace ciwon sonka yayi ajalina"!



Jinjina kansa yayi ya dan numfasa kafin yace"Do you want me to divorce her and marry you?"


 afirgice ta dube shi, cikin sauri ta kawar da idanun ta daga nashi saboda kwarjinin da yayi mata.


"Nasan zolayana ka ke yi, ba zaka ta6a sakin Unaisah saboda ni ba, ita kake so, itace za6inka, kada ka tausayamin don na fada maka halin da nake a ciki game da sonka... "


 katse ta yayi"dagaske nake Batool, zan iya sakin ta in aureki in har kin amince min"! Ya faɗa babu wasa akan fuskarsa


 Gabantane Ya faɗi a ruɗe tace"har abada bazan ta6a bari ka saki Unaisah ba, kwara ni na ƙare rayuwata batare da nayi aure ba akan dai ni in rabaka da ita don ka aureni, kuma tafi dacewa da kai, tafi ni cancanta da kai... " 


murmushin gefen fuska ya yi still idanunsa na akan fuskarta, yafi kowa sanin kunyarta da kamun kanta, Yasan yadda Batool take jin shakkar shi shiyasa yayi mata uziri saboda ya fahimci takasa jure wa ne..


Ɗaga murya yayi tare da furta"ka maidani gidana" Drivern Ya amsa mashi da Okay Sir..


Aruɗe tace"zan sauka, Yanzu zan sauka"


Ta fada tana kokarin ture murfin motar don ta fita sai dai ta kasa buɗe ta, a lokacin har drivern ya tashi motar.


"Ki kwantar da hankalinki, Zan kaiki gurin Unaisah ne, Ko baki son ganin ta"?


Girgiza kai tayi"inason ganin ta, amma ai ka fadamin tayi bacci, na hakura zuwa ranar dinner mun haɗu, Gida nakeso na koma banjin dadi inajin bacci..."


 a tsorace tayi maganar kwata kwata babu nutsuwa a tare da ita, tayi zaton zai mayar da ita gidanne don ya faɗa ma Unaisah abin da ta gaya masa duk da tasan mutunne shi mai sirri bazai iya yin hakan ba.


"Yaya Owais dan Allah ku aje ni anan, bansan zuwa gidanka, ni banaso Unaisah tasan me na fada maka zata ji ba dadi, nasan nayi kuskure amma bazan ƙara ba.. " cikin kuka ta faɗa.


Bai saurare ta ba, ya yi shiru tare da kawar da idanunsa daga kan nata.


Baiwar Allah duk tabi tasha jinin jikin ta.



Bayan motar ta ƙaraso Cikin gidan, A parking space drivern ya tsayar da ita, cardoors din suka buɗe, a tare suka fito Yana a 6angaren hagu tana a dama.



Cike da mamaki ta ke bin katafaren ginin da kallo.


"Mu shiga ciki" ya fada tare da yin gaba, cikin sanyi jiki tabi bayan shi..



Tunda suka shigo Main falon Ta soma zazzare idanunta tana ƙarewa ko'ina kallo, ta razana da ganin haɗuwar Furnitures din falon daga gani an zuba dukiya ta fitar shari'a.



Ganin ta toge a falo yasa shi juyowa tare da kallonta, da sauri ta sunkuyar da kanta ƙasa tana wasa da yatsunta


"Ki shiga tana a ɗaki"


 ya faɗa tare da nuna mata ƙofar bedroom da yatsansa, amsawa tayi da toh tana jin wani irin faduwar gaba kamar anayi mata lugudan ta6are a kirjin ta, tarasa meyasa take jin kamar wani abu badaidai ba..



Da sallama abakinta ta shigo bedroom din, har saida gabanta ya fadi rass saboda razanar da ta yi na ganin ƙawatuwar kayan ɗakin, kamar na sarauniya, tayi zaton zataga Unaisah aciki sai dai bata ganta a ko'ina ba, bata kawo komai aranta ba, ta soma ƙwala mata kira


"Ukhtyna! Unaisah! Kina ina ne? Batool ce, ki yi hakuri nazo da daddare inaso nagan ki ne yanzu zan tafi" 


shiru ba'a amsa mata ba, ranta ne ya bata kota shiga toilet ne hakan yasa tayi tunanin komawa falon don ta faɗawa Yaya Owais.



Juyawa tayi da sauri tana ƙoƙarin fucewa daga dakin Ya kunna kai ciki, Kirjinta ya bangaji na shi, da sauri taja baya adabarbarce ta furta"am sorry bansan zaka shigo ba, na duba banga Unaisah ba, ko tana a cikin toilet ne"! Ta faɗa tana zare idanun ta.



"Unaisah bata anan, tana a  gidan ta"!


"Yaya owais... Ban.. Bangane me kake nufi ba, nan ba gidan ta ba ne? " bai kula ta ba, Ya nufi Ciki, Kayan jikinsa Ya soma ragewa, Batool ta razana da ganin yana tu6e kayansa saida ya rage daga shi sai short.


Jikinta na 6ari ta nufi kofar dakin, ta soma kokarin budeta ta kasa, duk tabi ta ruɗe..


"Yaya Owais, ƙofar ta kulle, ka buɗe min in tafi gida tun da Unaisah bata anan, daddy zai min faɗa" 


Takun tafiyar sa ta jiyo daga bayanta,  tayi zaton bude mata kofar zaiyi..


Kwatsam ta tsinkayi voice dinsa a cikin kunnanta


"Batool, there's something I've been wanting to tell you for a long time"


(Batool akwai abun da na dade inaso na faɗa naki")


Zare idanu tayi batare data juyo ta dube shi ba.


"Na daɗe ina sha'awar son kasancewa da ke ban ta6a bayyana maki ba saboda bana son na zubda mutuncina a idanun ki..." 


bugun zuciyarta ne ya tsananta, jin furucin chief,  rudu da al'ajabi ya hana ta furta kalma..


"tun da kina sona, Ki bani hadin kai, babu wanda zaisan munyi, daga ni sai ke, zai zama sirri a tsakanin mu"  



A firgice ta juyo tare da duban shi, tsabar rudu yasa ta fara ganin kamar ba Chief bane.



Sexy abs dinsa ba ƙaramin rikitata yayi ba.



Murya na rawa tace"yaya Owais, kasan me kake faɗa kuwa? Kai da kanka" girgiza kai tayi"ni nasan bayin kanka bane, baka acikin hayyacinka, saboda Ba halin ka bane, Sharrin shaiɗanne"!


 


Kashe mata ido yayi tare da ɗage mata gira, ya dan lashe pink lip dinsa.


"ina a cikin hayyacina Batool, ba ku ma shaiɗan bane ke tunzurani ba, ni ne da kai na..."


 zare idanu tayi tana girgiza kanta'yaya Owais meke damunka ne? kamar wanda yasha kayan maye! kana da aure, kuma yau ka ƙara aure, idan kana bukatar ka kawar da abun dake damunka, ka tafi gurin matayenka, sune muhararramanka da Allah ya halatta maka ka sadu da su, amma bazaiyiwu in baka hadin kai ba! Kasan babu kyau, ba zan bari mu sa6ama Allah ba, kai mutumin kirkine mai tsoron Allah da son taimakon, ba zan ta6a bari shaidan Yasa ka aikata abun da zaka sa6ama mahaliccinka ba..."


tun da tafara magana Ya kafe kyawawan idanunsa akan tausasan lips dinta kamar tana ƙara tunzura shi, kwata kwata baya fahimtarta.


Sauke idanunsa yayi kan dukiyar fulaninta da su ka cika kirjinta sun matse gaban rigar kamar zasu fasa ta, Allah yayi ta da sura kamar umminta..



Yawu Ya haɗiya Yana shaƙar ƙamshin Humran ta..



Ganin yadda yake bin surar jikinta da kallo yasa ta ƙara tsorata da shi ta rasa gane meke damun yaya Owais"?


Ta kasa yarda dagaske ne maganar daya furta, Ranta ne Ya bata kodan sun ke6e da junane? Dama kuma babu kyau mace da namiji su ke6e, can kuma ta tuna meyasa ya kawota gidan nan bayan babu Unaisah a ciki hakan na nufin dama can da wata manufa yayi hakan, girgiza kai tayi, zuciyarta ta raya mata Watakil yasha ƙwayane ko kuma zai iya yiwuwa gyaran jikin da tayi irin na Unaisah ne yasa shi kamuwa da sha'awarta, amma meyasa ma zaiji hakan? Bayan matayensa sunfi ta da komai a tunaninta kenan..



"Batool, ba zaki iya biyamun buƙatana ba? Sau ɗaya kawai, ki taimaka min, Zan iya rasa raina, bakiji yadda nake jin kwaɗayin In kasance da ke ba..." 


ya faɗa yana marairaice mata fuskarshi yadda kasan ba Chief namu ba, Ikon Allah Ikon Gaske..



Yawu mai zafi ta hadiya


"Yaya Owais, kayi hakuri, ni maiyi maka komai kakeso ce don in faranta maka rai, nasan har abada ba zamu iya biyanka ba, amma wallahi bazan ta6a bari mu sa6ama  Allah ba, ina jin tsoron shi, kuma banaso mutuncinka ya zube, ka dubi girman Allah, dan Son da kake ma ma'aiki manzo SAW ka tausayamin, nazo duniya bata hanyar aure ba, idan na amince maka muka aikata alfasha rayuwata zata gur6ace ne, pls kada ka matsa min, ka barni in tafi gida..." 


tana karashe maganar jikinta na kerma cikin sauri ta juya da niyar ta buɗe  ƙofar.


Batai Aune ba, Kwatsam Taji Ya tallabe waist dinta da tafukansa, Ya cuccu6eta ya daga ta sama tare da juyawa da ita Ya nufi katafaren gadon dakin, tuni mayafinta ya fadi kan floor.


Fashewa tayi da kuka tana fadin


"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! yaya Owais ka da Ka cutar da ni, na roƙe ka, ka barni in tafi gida, ka da ka yi amfani da son da nake maka gurin lalata rayuwana.."



bai dakata ba har saida Ya Jefar da ita kan gadon, Ta faɗa ta rubda ciki, silar hakan yasa yalwatacciyar sumar kanta ta baje har saman mattress, jikinta na 6ari tayi saurin miƙewa zaune, Ta dube shi Yayin da ya ke kokarin zamiye short dinsa.



Fashewa tayi da kuka tana fadin 


"Ni bazan iya cin amanar Yar uwata ba, bazan sabawa mahaliccina ba, kada ka goga min kazantar zina a jikina, Idan kanason In kwanta dakai har kwara ka aureni, zanyi maka abunda kakeso tunda ina son ka, amma wallahi ban ta6a sonka da zina ba"


 Runtse idanunta tayi tare da daddafe kanta da tafukanta, ƙwaƙwalwarta ta fara tariyo mata abun daya faru tsakanin iyayenta kafin suka same ta, tsigar jikinta ce ta soma tashi, shatun jijiyoyinta suka fito ruɗu ruɗu saman fatarta, Lokaci ɗaya ta buɗe idanunta da suka kaɗa jajir, Agigice Ta zabura zata dira daga kan gadon yayi saurin haurawa kan gadon ya damƙo kafafunta tare da janyo da ita, ya rungumeta akan faffadan kirjin shi, kuka ta ke yi kamar ranta zai fita.


Cikin shesshekar kuka take fadin"dan Allah yaya Owais kada ka cutar dani, bazan iya jurewa ba, Mutuwa zanyi, ina son na tafi gida, Idan ka aikata min hakan Iyayena zasu yi bakin cikin da zaisa su rasa ran su, nima zan mutu da bakin cikin abun da kayi min... "


 a hankali ya soma shafa sumar kanta yana tattare ta guri guda yana jin wani irin yanayi na shauƙin ta.


Yana Jin yadda Zuciyarta ke bugawa da karfi, Numfashinta na fita a hargitse.


Unexpected taji Ya furta"ki daina kuka, bazan iya cutar da ke ba, zan mayar da ke gida, amma sai kin shiga toilet kin wanke fuskarki sannan zansa akawo maki abinci ki ci.."


 wata nannauyar ajiyar zuciya data sauke har saida yajita a kirjin shi.



Dakyar ta haɗiye kukan, taji nutsuwa da kwanciyar hankali sun zo mata.



raba jikinta tayi daga nashi idanunsu suka shiga cikin na juna, tausayin ta ne ya kama shi ganin yadda kumatunta suka yi ja, labbanta da fatar idanunta sun kumbura, sun yi jawur, hakanan ya tsorata baiwar Allah bata ji ba, bata gani ba.



"Hankalina ba akwance yake ba idan ina a tare dakai, ka maidani gida kawai"


"Kiyi abunda nace idan kina son komawa gida" 



da sauri ta amsa da toh, ta sauko daga kan gadon ta nufi toilet ta shige tare da jan ƙofar ta datse don karya farmaketa a ciki.



Ƙayataccen murmushi yayi.



Almost mins yana jiranta before Yaji motsin bude toilet door.


fitowa tayi daga ciki ta toge a bakin kofar, saukowa yayi daga kan gadon, da hannu Ya nuna mata kofar closet Room"ki shiga, Ki sauya kaya, na jikinki sun yamutse, banaso suga abunda zai sa su zargi wani abu"


 cike da rashin yarda ta furta"basaina shiga ba, idan munje gidan zanyi musu bayani"


Ɗaure mata fuska yayi"zakiyi abun da nace maki ko kuwa"?


 Cikin sauri ta nufi closet room ta shige.


Jim Kaɗan ta fito Jikinta sanye da abaya fara, tayi rolling mayafi akanta, Yana a zaune bakin gadon yabi ta da kallo from head to toe, ta yi mashi kyau a cikin abayar, ta fito a balarabiyarta.


Miƙewa yayi tare da nufar kofar dining room "ki biyoni" cike da jin shakkar shi tabi bayansa.


Saman dining chairs suka zauna suna fuskantar Juna, ga kayan dinner shaƙe da table din gabansu, ya lura har yanzu a tsorace take da shi, duba da yadda Jikin ta ke kerma..


"Zaki iya ci da hannunki! Ko in baki abaki"! 


Da jin Hakan Yasa cikin sauri ta ɗauki glass of juice me sanyi ta kwafa abaki tana sha tana satar kallon shi yayin daya sadda kan shi ƙasa sai taga kamar murmushi ya ke yi amma bata gaskata hakan ba.



Bai yi zaton yarinyar ta samu tarbiya har haka ba, da wuya ya jaraba mace da tayin kanshi taƙi amincewa sai akan Batool, tsoron Allahnta, da kamun kanta, da kuma yardar da tayi masa sunfi komai Jan hankalin shi a gare ta.



Satar kallonta yayi, tana tsaka da cin meatloaf mai dan karan daɗi, Yatsun hannunta nata kerma kaf kaf kamar wacce sanyi ya kama,  Allah Allah take ta gama ta tafi gida.



Kaɗan taci ta dakata, tare da duban shi "yaya Owais, na koshi, dama dazu naci abinci gidan biki, zan tafi basai ka kaini a mota ba, Unaisah tana can tana jiran ka, kaga dare ya yi sosai"


Yanayin yadda ta ke yin magana cikin sanyin murya ba ƙaramin jan hankalinsa ta ke yi ba.


Bata ƙare maganar ba, Ya katse ta da cewa"ban yarda kin koshi ba, You're still hungry, Either eat more, or we'll stay here forever"


arude ta soma cuccusawa abaki, taci samosa, taci spring rolls, ta hada da straw berry shortcake, Tana gamawa ta kai hannu ta dauki milk shake ta sha sosai duk yana kallonta, bakin ta yayi dama dama da cake.


Tana haki ta furta"yaya Owais na ci da yawa yanzu, zan tafi"


 bata jira amsar shi ba ta mike tana zazzare idanun ta.


"Muje nakai ki a mota ta, idan kikayi min gaddama zamu kwana anan ne" a firgice ta amsa da toh.


"Ki jira ni a falo, zan shiga ciki in sanya suturana" amsawa tayi da toh.


Akan idonta ya fuce daga falon ya nufi Cikin bedroom.


Cike da zullumi take ta jiran shi, babban tashin hankalinta, ummin ta da daddynta tasan zasu nemeta, gashi ta manta ma inda ta jefa wayarta.




Tasan idan ta koma gida zasu iya yi mata faɗan daren da tayi a waje, kuma zasu tuhumeta akan Kayan da ta canza a jikin ta, Ya ilahi ta furta tana dafe goshinta daya jike da gumi.



Fitowa yayi jikin shi sanye da jallabiya ash, ya ruƙe car key dinsa a hannu.



"Na manta kayan dana cire a closet room" 



ta faɗa batare da ta bari sun haɗa idanunsu ba.



"Zaki iya zuwa ki dauka"


 cikin sauri taje ta ɗauko kayan ta ƙuɗundunesu a hannunta.



Bata iske shi a falon ba, hakan yasa ta fito harabar part din,  a parking space ta hango shi a tsaye Ya jingina bayan shi jikin motar shi, ba wadda sukazo gidan da ita ba.



Kafin ta ƙaraso Ya buɗe mazaunin driver Ya shiga, tana ƙoƙarin buɗe back seat muryarsa ta katse ta"Am I your driver"? Cike da izza ya furta.


 Da sauri ta dawo mazaunin gaba Ta bude ta shiga ta zauna tana ta faman sauke a jiyar zuciya, ta ɗanyi mamakin ganin shi ne zai yi driving da kan shi bayan bata saba ganinsa yana driving ba.



Bayan ya tashi motar,  ya yi  reverse ya fusgeta da matsakaicin gudu motar ta fuce daga gida.




~____💘_____💋______🌹______💕_______💗________🔥~




*🔥UNAISAH💗*




tana tsaka da sharar baccin ta, Kwatsam hasken ɗakin Ya ɗauke ɗuff, sai na Candles da ke ci, ƙarar qira'ar alqur'anin daya karaɗe ɗakin ne Ya farkar da ita a firgice ta farka tana zare sleepy eyes ɗin ta, wata irin faɗuwar gaba taji sa'ad da ta lura babu hasken fitilun ɗakin sai na candle lights! 



Zuciyarta ta shiga harbawa da sauri da sauri kamar ana mata lugudan ta6are a ƙirjin ta.


Bata ta6a tsintar kanta a cikin tsoro irin na wannan lokacin ba tun bayan rabuwarta da kurkukun ƙaddara!


Abu biyu ne yazo aranta, watakil Yaya Owais ne Ya kashe hasken ɗakin sa'ilin da take bacci don ya bata mamaki, ko kuma Electricity din gidan ne Ya samu matsala, gaba daya ta manta menene yayi silar farkawarta daga bacci.


A tsorace ta furta"Yaya Owais? Kai ne ka shigo? Kana ina? Nasan kaine ka kashe min hasken ɗaki, dan Allah kayi min magana, gaba daya na tsorata.." 



Ta faɗa tare da miƙewa daga kan kujerar, jikinta nata kerma kamar mazari.


La66anta na kerma ta kuma cewa"hubby, pls kada ka wahalar dani, bazan iya jurewa ba, idan kaine ka yi min magana ko hankalina ya kwanta, tun ɗazu nake jiran zuwanka... " 


bata ƙarashe maganar ba, Unexpected ta tsinkayi sautin takun tafiya a cikin kunnanta daga bayanta, tuni tasha jinin jikin ta, jin yaƙi amsa mata yasa tayi tunanin ba ya ya Owais ba ne, wani ne ya shigo gidan, nan fa ta ƙara shiga tashin hankali, tsoro ya hana ta juya ta fuskance shi, sai faman zazzare idanunta ta ke yi, dakyar ta iya ƙyalla idanun ta ta cikin mirror ɗin gaban ta ta soma hango shi da taimakon Candle lights...



Walking magestically ya ke nufo cikin bedroom ɗin kamar baison taka ƙasa, daga ƙasa ta soma ƙare ma shi kallon ƙurullah da tsantsar ruɗani da fargaba saboda bata tantance wanene ba, tsayin sa ya zarce na Chief Owais.


Sanye ya ke cikin shiga ta larabawa, wata hadaddiyar dishdasha long tunic, launin ivory white ta bayyana tsantsar zazzafar surar sa mai matuƙar jan hankali, daga fadadan kafadunsa wata madaidaiciyar  bisht cloak ce (alkyabba ) launin Golden-brown, daga gefenta da bakin ta gaba daya adon duwatsu masu daraja ne lullu6e da rigar, sai kyalli su ke yi suna sheƙi, wuyan hannunsa na dama yana asanye da Expensive  rolex Watch  irin wadda sai dan wane da wane su ke sanyata, both mid fingers dinsa suna a sanye da  gemstone-encrusted rings, yayin da kafafunsa ke asanye da hand made Leather arabian shoes, mayar da idanunta tayi akan fuskarsa cike da fargaba take kokarin gano wanene sai dai kash rabin fuskar tasa yayi covering dinta da Gold leaf Mask, gaba ɗaya kansa a naɗe ya ke da turban, irin naɗin larabawa, daga kasan rawanin doguwar sumar kansa ce ta zubo, wutsiyoyin kitsonsa biyu suka hauro ta saman kafaɗarsa har izuwa kan broad chest dinsa, daga bayan sa wata sumarce har mid back dinsa mai kyan gaske tana ta sheƙi brown shar da ita.. 


Duk ƙamshim da bedroom din ta ke yi saida Ƙamshin turarensa ya disashe shi, wani irin sweet fragrance mai rikita shauƙin bawa, daga yanayin tafiyarsa ta fahimci yana da izza da qasaita daga gani mutum ne mai tsantsar ilmi da aji kuma wayayye mai cikar kamala da nutsuwa.


Unaisah ta gama ruɗewa, Tsoro da fargaba suka cika Zuciyarta da ke tayi mata dakan sakwara, aranta tana ta tunanin wanene wannan Hamshaƙin saurayin?  shin tayaya akai ya shigo gidan Auranta? Kwata kwata bata yarda Mutun ne ba, tafi alakanta shi da jinsin jinn saboda zubin sa!



 Anya kuwa Yaya Owais ya sanya malamai suyi safkar alkur'ani a gidan kafin ta tare?



Tana kokwanto saboda gayanan tunkan aje ko'ina ta fara ganin ifritun Aljani..




Yawu ta haɗiya mai zafi makoshin ta ya bada sauti ƙutt, cikin rawar jiki ta fara tunanin mafita! Gashi tamanta waya agida balle ta kira wani ta fada masa Aljani Ya kawo mata farmaki, ita kadai baiwar Allah, tunanin guduwa tayi duk da tasan ba lallai takalman kafarta su bata hadin kai ba saboda tsinin su.


Ganin Ya kusa karasowa cikin ɗakinne Yasa Ta fara neman gurin da zata 6uya cikin rawar jiki ta soma ja da baya cikin sanɗa don karya ji takun ta.



zukunnawa tayi ƙasa da rarrafe ta dinga yin tafiya ta nufi karkashin gado ta shige ciki ta 6uya gabanta nata faɗuwa, aranta tana mai cigaba da ambaton La'Ila ha'illa anta subhanaka Inni kuntu minazzalimin"



~________________________________🌹~




A hankali ya ƙarasa shigowa tsakiyar dakin, cikin takun ƙasaita ya nufi gaban gadon, Unaisah dake a karkashinsa tana leƙen ƙafafunsa da ke tunkaro gadon, tashin hankali tuni gumi ya wanke fuskarta, runtse idanunta ta yi gam ta dinga karanto Ayatul kursiyo a cikin zuciyarta da sauran addu'o'in neman kariya daga sharrin jin.



A hankali ya zauna daga gefen gadon ya ɗaura ƙafarsa ɗaya kan ɗaya..



Zuciyarta ce ta tunzurata akan ta duba ƙafarsa taga idan irin na mutanene ko kofaton jaki irin na aljanu kamar yadda Aunty Danejo ta ta6a bata labarin cewa Idan aljanu suka yi suffar mutane zaka iya gane su ta kafarsu saboda ba irin na mutane bane, Kofaton Jaki gare su.



Cikin sanɗa ta zuƙunno da kanta ta ƙurawa fatar ƙafarsa ido, Har saida gabanta ya faɗi ganin kafar tasa fara sol kamar ta jariri yadda kasan bai ta6a taka ƙasa ba, hasken fatar sa irin pure shining white ɗin da ba acika samun shi ba ne naturally.



Ruɗewa tayi, duk da tana kokwanton kamar mutunne tun da bata hango kofaton jaki ba, zuciyarta ce ta raya mata idanunta ne suke nuna mata ba daidai ba, watakil owais ne girgiza kai tayi in har Owais ne bazai ta6a zama fari ba.


Ganin Ya motsa kamar ya miƙe yasa ta katse zancen zucin nata,  kanta harya fara ciwo, ga yunwa da bacci tana ji, ga zullumi da fargaba sun cika zuciyarta..


Shigewa toilet ya yi, tana lekensa taga glashin bangon toilet din ya disashe, aranta ta ayyana ya koma mazauninsa kenan, tunda ance toilet gurin zaman aljanu ne, cikin sauri da rawar jiki ta fito da niyar ta fece, kwatsam ta hango tamfatsetsiyar waya ajiye saman bedside drawer, fasa fita tayi


Yatsun hannunta na kerma ta dauki wayar ta danna number din daddynta ta kira ta kara a kunne cike da fargaba..



Unexpected wayar Taj dake aje kan bedside drawer ta fara ringing, at same time suka farka.


   

"Wanene Ke kira" ta tambaya tana duban Taj daya dauko wayar yana kallon screen dinta yace"ban sani ba amma bari na ɗaga maybe wani emergency call ne"


Amsawa tayi da ''to'' Picking yayi ya kara a kunne


ko sallama batayi ba ta fashe da kuka kamar ranta zai fita.


Har Benazir saida taji yo kukanta, hankali atashe suka dubi Juna..


Har suna haɗa baki gurin furta"Unaisah! Meke damunki? Meyasa ki kuka um miya faru wayar waye kuma wannan"?


Dakyar ta shanye kukan, Cikin shesshekar murya tace"yaya Owais baizo ba, Inata jiran shi ni kadai agidan tsoro nake ji, kuma yanzu wani ifritun aljani ƙaton maridi ya shigo dakina, baka ganshi ba daddy, dogo fari fat kamar fatalwa ya saka kayan larabawa, tun dazu nake boye a karkashin gado har saida Ya shiga toilet sannan na samu na fito har na dauki waya, wallahi daddy Mutuwa zanyi in baka zo ka ɗauke ni ba, kashe ni zai yi, dan Allah daddy ka zo tare da Baba Imam ya kora mana aljanun gidan da ayar Allah,  in har ba so ku ke ku rasa ni ba.... " 



daƙyar ta ƙare maganar..


Hankalin Benazir idan yai dubu to Ya tashi, Taj ne kadai bai ɗaga hankalinsa ba, kallon juna su ka yi.


Kafin wani ya furta kalma kiran ya katse.


"Bazan iya jira ba, zanje kawai na tafo da ita, tayaya zai barmin ƴa a irin wannan lokacin tana ta jiran shi, wunin yau ko abinci bata ci ba saboda sunce zasu ci agidan su, gashi harta fara gane ganen aljanu"


Cikin 6acin rai ta ƙarashe maganar tana ƙokarin saukowa daga kan gadon Taj yayi saurin  ruƙo hannunta, cikin fushi kamar zatayi kuka tace"kana fa jin abun da tace! So ka ke mu rasa ta ne? Tun kan aje ko'ina har ya fara nuna rashin kulawa akanta! Ba fa dan na gaji da ita na bashi ita ba"


Murmushin gefen fuska Taj yayi"Ummu Unaisah, Ki kwantar da hankalinki, ruɗewa tayi ne amma ba aljani bane tagani, Mijin ta ne"


 Aruɗe Benazir tace"ita fa da kanta tace aljani ne! Unaisah batasan fuskar Owais bane da zata rasa gane shi!? ina Owais yaga hasken fata? idan kai baka dauki maganarta serious ba nina ɗauka.." 


tana ƙarashe maganar ta fusge hannunta daga nashi ta nufi closet ta dauko veil ta yafa.


"Karki Fita Benazir, ban baki izni ba, ki dawo zanyi maki bayani.." 



"Ai fa sai ka yi Tajo, kaima kasan ba sauraron ka zan yi ba... "  



~____________________________________🥺💘~



_A 6angaren Unaisah, batasan ya akai kiran ya katse ba, ta dinga trying baya zuwa, kamar ta yi hauka, batai aune ba, kwatsam ba zato ba tsammani taji motsinsa abayanta, Kamar numfashinta zai ɗauke tsabar razana, bugun Zuciyarta ya tsananta, gumi Ya cigaba da tsastsafo mata ta saman goshinta da hancin ta, wani irin tsoro ne ya ziyar ce ta, duk tabi tasha jinin jikin ta..._


Kafin tayi wani ƙwaƙƙwaran motsi sanyayyar Muryarsa ta ratsa kunnanta"My Phone.... " 



Ya Ilahi Wani irin ruɗanine Ya cika zuciyarta jin muryar ifritun Aljanin tayi mata shige da ta wani wanda ta daɗe da rasa shi arayuwar ta, muryarsa da ko a mafarki taji ta saita shaideta, ko da tana a cikin maye ne..


Kwata kwata batasan wayar wacece ta ɗauka ba, sai da taji maganarsa, tana zazzare idanu ta ɗan saci kallon wayar da ta ruke a hannun ta, ƙara zare idanunta tayi tamkar ƙwayar idon zata faɗo ƙasa a kiɗime take kallon hoton ta da ke akan Wallpaper ɗin wayar ganin abin ta ke kamar a mafarki kamar idanunta sun samu matsala....! 



Mutun ɗaya ta ta6a turama hoton ta whatsapp dinsa, kuma a time din data tura masa hoton view once ne ba a iya ɗaukarsa ko ayi sharing even screenshot amma tayaya ya samu hoton? Nan ta ke ta ƙara tabbatarwa kanta ba mutun bane, sakin wayar tayi ta faɗi kan floor



Ƙarfin halin juyawa tayi slowly ta fuskance shi cike da fargaba ta ɗan saci kallon fuskarshi, bata iya ganin ta dakyau sai dai Kyawawan sleepy eyes din sa waɗanda ke a lumshe 


Ko a mafarki taga me irin tsayuwarsa sai ta gane shi, Amma tagaza yarda da abun da zuciyarta ke raya mata, a ganin ta bame yiwuwa ba ne, cike da fargaba ta ɗan matsa dab da shi  ta ɗan tsaya jikin ta na kerma ta ke ƙare mashi kallon ƙurulla...


A ranta tana ta ambaton La'ila ha'illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin..


Cikin rawar Murya tace"Bab.. Bawan Allah kaji tsoron Allah kada ka cutar dani! Ka faɗamin Wanene Kai? Mutun ko aljan? Kasan ni ne? A ina ka sami hoto na? Me kuma ya kawo ka gidan aure na har cikin ɗaki na"?



shiru babu alamun zai furta kalma, ko motsi bai yi ba bai kuma ɗaga idanunsa ya dube ta ba..


Almost minutes..


Batasan ya akai take jin wani abu a zuciyarta wanda bazata iya misalta shi ba, kuma duk duniya mutun ɗaya ne idan tana atare da shi a kusa da ita take jin wannan abun...


Kafin ta ƙara furta kalma, taga Ya motsa ta ɗan zare ido tana duban shi, gently ya sanya hannu ɗaya akan fuskarsa ya soma ƙoƙarin cire mask ɗin sa..


Lokacin daya zame Mask din gaba ɗaya Ya sake shi Ya faɗi ƙasa wata irin zabura Unaisah tayi kamar zata watsa aguje saboda ruɗewar da ta yi, Ilahirin jikinta Ya kama kerma kamar mazari, gaba daya ta rikice tabi ta ruɗe ta razana da ganin fuskar mutumin data rasa tsawon shekaru akan fuskar Ifritun Aljanin nan, tsigar jikinta duk ta tashi, wani irin faduwar gaba take ji a kirjinta kamar ana buga ganguna.


 Kyakkyawar fuskarsa da bazata taba manta kamanninta ba saboda haddar da tayi mata.


 cikin ɗimuwa ta soma murza idanunta da yatsunta sosai don taji aranta gizau ya ke mata bashi bane, saida ta gama murje idanun ta buɗe su still babu abun daya sauya yana nan yadda ya ke.


Kamar mahaukaciya Ta bushe da dariya lokacin ɗaya kuma takama kuka tana fadin"ba zaka ta6a bari in zauna lafiya ba, ka mutu ban huta ba, fatalwarka bazata bari in zauna gidan aurena lafiya ba, ka hana zuciyata sukuni a gidan iyayena nan ma ka biyoni don ka tarwatsa aurena! Meyasa zakayi min haka? ya ka ke so nayi da raina? ko so ka ke nima na mutu nabiyoka mu rayu a kabari ɗayane um"? tuni idanunta sun kaɗa jajir.



"Idan so kake mu rayu a tare, ka kashe ni sai mu koma kabarin ka a tare, nima zanso hakan saboda bana jin dadin rayuwana batare da kai ba.." 



ta ƙarashe maganar tana matsawa kusa da shi, kamar ancire mata tsoronsa da fargabansa daga zuciyarta, tun da ta sama ranta cewa fatalwarsa ce.


A hankali ta kwantar da kanta saman broad chest dinsa, ta zagayo da hannayenta ta saman bayansa, batasan ya akai ta tsinci kanta da jin wani bakon al'amari atare da ita, bugun zuciyarta a cikin nashi, nutsuwa da kwanciyar hankalin da taji a jikin ta sa'ilin data haɗa jikinta da nashine yasa ta kara ruɗewa, ta dinga jin kamar shine ba fatalwarsa bace tunda in fatalwace bazata iya riqeta ba duk da haka ta kasa gaskata cewa Danish ne.


Cikin kuka tace "Ka ɗauke ni, mu tafi ƙabarinka, mu rayu a tare, bazan ta6a gudun fatalwarka ba my Man, nasan nice na hanaka kwanciyar kabarinka" ta riga ta sallama masa kanta yayi duk abin da zai yi.


Duk wani motsinta yana jinshi a jikin sa, bugun zuciyarta, shesshekar kukanta, fitar numfashinta, dumin jikin ta da ƙamshin ta.



Tayaya zai iya fahimtar da ita cewa ba fatalwarsa bace! bai mutu ba yana araye? Tayaya zai iya kare kansa daga gare ta, yana jin fiye da abun da take ji aranta, banbancin ɗayane shi yasan tana araye kuma ya nisanta kanshi da ita saboda manufar sa..



Yana jin yadda take ƙara narƙe mashi a jiki kamar zasu koma mutun ɗaya...



Numfasawa yayi a hankali cikin nutsatstsiyar muryarsa ya furta.



*_"UNAISAH, I'M NOT A GHOST! I'M NOT A DEMON AS YOU THINK, I'M NOT DEAD, I'M ALIVE, I'M YOUR DANISH! YOUR SHIELD, I KNOW IT WILL BE HARD FOR YOU TO BELIEVE ME"!*_



(UNAISAH NI BA FATALWA BA NE! BA KUMA ALJANI BANE KAMAR YADDA KIKA ZATA, NI BAN MUTU BA, INA ARAYE, NI NE DANISH DINKI! GARKUWAR KI, NASAN ZAI YI WUYA KI YARDA DANI..... " )



bai kai ƙarshen maganar tashi ba ganin yadda ta fisge jikin ta daga nashi, ta sanya runannun idanunta a cikin kyawawan  idanun shi farare tass kamar an ɗiga zaiba, Reddish iris dinsa Ya ciza launinsa kyau iya kyau,  cikin ruɗu da razana ta ke girgiza kanta, yayin da hawaye ke cigaba da yin sintiri kan kuncin ta..


La66anta na kerma tace"Ba zai ta6a yiwuwa ba, sai dai idan mafarki na ke yi, amma wanda ya mutu baya dawowa, ka riga da ka mutu, fatalwarka ce"



tana ƙarashe maganar, tabi ta gefen shi da gudun ceton rai ta nufi door room din tana ƙarasawa gaban ƙofar Unfortunately tayi locking kanta..


Bugun ƙofar ta din ga yi tana ture ta da dukkan ƙarfinta kamar zata 6alle ta, cikin shessheƙar murya take ambaton



"Mommy! Daddy!! Hubby !! Aunty Danejo!! Batool ... " don su kawo mata ɗauƙi Dan ba karamar firgita tayi ba.


Duk yana atsaye yana kallon ta, phone dinsa data jefar kan floor ya dauko, Walking slowly ya nufi ƙofar, kwata kwata bata ji motsin tafowarsa sa ba, har ya ƙaraso daga bayanta ya tsaya tare da yi mata rumfa da faffaɗan ƙirjinsa hannayenta da take bugun ƙofar da su Ya ruƙo  a cikin nashi Ya manna su jikin ƙofar, gaba ɗaya ya kashe mata sauran kuzarin daya rage a jikin ta ya haifar mata da jin matsananciyar kasala, tuni ta nemi shesshekar kukan da takeyi ta rasa wata nutsuwa ta soma ratsa ta..



 sosai yayi tighting dinta ta yadda zai samu damar fahimtar da ita, da ya ke yasan halin kayansa da wuyar sha'ani ga kafiya.



"Ki bani dama In yi maki bayanin da zaki fahimta! Ko da ba zaki yarda da ni ba... " kasa buɗe baki tayi don tayi magana..


Hakan Ya bashi karfin gwiwar cigaba dayin maganarsa..


"Ba ki shaida mutuwa na ba Unaisah! Baki ga gawata ba ido da ido! tayaya ba zaki yarda cewa ni ne ban mutu ba"?



Daƙyar ta iya furta"saboda Danish ba zai iya rayuwa batare dani ba, in har yana araye bazai iya rayuwa nesa dani ba, ko inda babu ni, amma Yau kusan shekaru da mutuwarsa, tayaya zan yarda cewa yana araye"?




Kwata kwata bata iya ganinsa cos Ya manne jikinta da glass din ƙofar, amma shi yana iya hangen fuskarta, wallah shi kadai yasan me ya ke ji, almost years rabonsa da muradin ransa..



Bata ƙare maganar ba Ya katse ta"ki faɗa min me zanyi maki wanda zaisa ki yarda da magana ta? 


"Babu, abunda zaka faɗamin In yarda, Kawai kabarni in tafi, ko ka 6ace ka koma ƙabarin ka, in ba haka ba daddyna yana akan hanyar zuwa gidan nan, tare da sheikh imam malik zai zo, Zaiyi maka ruƙiya ya ƙonaka da ayar Allah..."    


maganarta taso bashi dariya, tausasan la66anta Yabi da kallo sun jiƙu da hawayen ta...


"Okay, bari na kira daddyn naki, may be Idan shi yayi maki bayani ki yarda.." faduwar gaba taji



A hankali Ya zame hannunsa daga kan nata, Ya zaro wayar daya saka a aljihu Ya daddannata


Unexpected taji Muryar Taj yana yin sallama ta cikin wayarsa..


"Nayi kokarin na fahimtar da Unaisah cewa nine ban mutu ba taƙi yarda dani..." 


"Idan tana a kusa ka bata wayar"


Kara mata wayar ya yi a kunnanta..


Arude tace "wallahi Ba daddy na bane, ɗan uwanka aljani ka kira don ka ruɗani"


sautin dariyar Taj ce ta cika kunnanta, arude ta ke dan zazzare idanun ta akan glass din ƙofar..


"Unaisah, ki kwantar da hankalinki, ki nutsu ki saurareni! Daddyn ki ne, muna waya ɗazu ta katse, ban samu damar da zan fayyace maki komai ba, bawan Allahn dake a tare dake Ba aljani bane, ba kuma fatalwarsa ba ce, Danish ɗinki ne ya dawo araye kuma a matsayin mijin ki... "



 maganarsa ta kara rikirkita tunanin ta, kokarin fahimtarsa ta ke yi sai dai tarasa nutsuwar yin hakan..


Mayar da wayar yayi kan kunnansa"bansan ya zanyi da ita ba, taƙi ta saurareni"



Taj yace"ta ruɗene amma ka yi kokarin fahimtar da ita ta yadda zata yarda..."


"Okay shukran... " sallama su kayi, ya mayar da dubansa kan Unaisah data haɗa uban gumi kan fuskarta..


Kafin ya furta kalma ta katse masa hanzarin sa



_"Idan har dagaske kaine tayaya akai ka rayu bayan ka faɗa cikin rijiya? A ina ka ke yin rayuwa tsawon shekaru batare da sanin mu ba? Kayi loosing memory ɗinka ne? ko kuwa doguwar suma ka yi ne"?_ 


"Zanyi maki bayani, mu koma mu zauna" make kafadarta tayi"ba zan matsa daga inda na ke ba! Har saika bani amsar tambayana"! Yadda tayi maganar ya tabbatar masa da cewa ta fara yarda shi ɗin ne.


Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post