Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe Page 91 Complete

Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe Page 91 Complete

Takun Ƙarshe

 Suna tsaka da fira, sallamar Batool ta katse su, a tare suka dago suna kallon ta yayin da take shigowa hannunta ruke da Graduation gown din Unaisah, sajeed da Haris suna abiye da bayan ta, kowannan su Ya ruke kayan Unaisah data jefar, a rude Benazir da Ummi suka mike suna duban su.


"Babe! Ina kuka baro Unaisah din? Wannan ba graduation gown din ta bace"? Ummi ce Ta faɗa tana nuna rigar hannun Batool.


 

Sajeed ne ya labarta mata abun daya faru, hankalinsu Ya tashi..

Batool Tace"ummina bata dawo gida bane"?


"Bata dawo ba Batool, bamu ganta ba, amma abun da daure kai? Kamar dai mai tabin hankali, babu abunda akai mata kuma? 


Ta fada da ruɗu akan fuskarta.


Damuwa ce ƙarara akan fuskar Benazir"Ku fada min gaskiyar abun daya faru! Ko dai ta samu sa6ani da wanine a cikin ku"?



"Wallahi Aunty Benazir babu abun da akayi mata.."


"To ina ta tafi ne"? Ta kuma tambaya.



Ummi tace"tun da ranta a6ace ya ke zai iya yiwuwa ta shigo tagan mu saita lallaba ta wuce ciki, muje mu duba dakin nata.."



Cikin sauri suka nufi bedroom din ta.


"Babyna Kina a ciki"? benazir ne ta fada tana bubbuga ƙofar dakin.


Daga ciki suka jiyo voice din"mommy, am sorry na dawo ban fada maku ba, bana jin dadi ne amma da sauki yanzu.  "


"Haba Unaisah, wani irin rashin lafiyane zai sa ki watsar da kayan graduation dinki"? Shiru tayi saboda bata da amsar da zata ba..


"Zoki buɗe min ƙofa tunkafin ranki ya 6ace" saukowa tayi daga kan gadon ta buɗe ƙofar, gaba ɗaya suka bi ta da kallo..


Daga yanayin ta suka fahimci bata da lafiya.


"Me ke damunki"? 


"Mommy, zazza6i ne amma na sha magani" shafa wuyanta Benazir tayi jin da zafi yasa ta yarda da maganarta"Allah ya baki lafiya" ameen ta masa, danejo ma tayi mata sannu da jiki..


Ummi tace"Allah ya baki lafiya, ki koma ki kwanta, ki samu kiyi bacci"


Amsawa tayi da toh.


Ummi ta dubi Batool "Babe, ki zauna tare da ita, ki kula mana da ita" amsawa tayi da toh.



sauran su ka yi mata fatan samun lafiya.


Sajeed da Haris suka mikama Batool kayan Unaisah, bayan ta kar6a suka nufi ciki ita da Unaisah




Bayan ta ajiye mata kayan a cikin closet din ta, ta juyo ta dubi Unaisah dake a kwance kan gado.



"Sis, badai har yanzu baki daina wannan tunanin ba"? Ta faɗa da damuwa ta zauna kusa da ita tana kallon fuskarta da tayi jawur saboda kukan da tasha.


"Batool na rasa ya zanyi, kwanakin nan kamar ana sabunta min kaunar shi..." ta fada tana jan majina..


"ke kadai kika san da wannan maganar, pls amana kada ki fada ma kowa amma bana jin zan iya zaman aure, saboda tunaninsa da nakeyi zai iya jaza min matsala..." idanun Batool tuni sun cicciko da kwalla, tausayin yar uwartata ne ya kamata.


"Ba irin addu'ar da banyi ba akan Allah ya cire min son shi amma babu abun daya sauya, Ina azabtuwa Batool" ta fada tare da cusa kanta cikin pillow.


Girgiza kai Batool tayi hawaye har sun fara sauka kan kuncin ta"bani da maganin abunda ke damunki, al'amari ne mai girma Unaisah, nima yafi karfina, zaman aure bazaiyi yiwu da tunanin son kasancewa da wani wanda babu shi araye, amma menene mafita"?


"Babu mafita Batool"


"Baki tunanin idan muka faɗawa su mommy zasu nema mana mafita" a firgice ta dago tare da zare idanunta cikin na Batool


"ukhty kinsan me kike fada kuwa? Wannan ba mafita bace, tayaya ma zan iya fada masu? Abun da kunya kuma ba zasu dauki maganata serious ba, zasu ce bani da hankali ne"


 Jinjina kai Batool tayi"kin faɗi gaskiya Ukhty, to ko in fadama daddyna" wani kallo mai kama da harara Unaisah tayi mata, Batool ta kwashe da dariya..


"In haka ne nima inje in faɗawa daddyna mana ..' dariya su ka yi..


"Kinsan wani abu, pls mu cigaba da addu'a, babu abunda ya gagari ubangijinmu, in sha Allah zai yaye maki damuwarki, ni yanzu burina ki maida hankali akan shirye shiryen dake tunkaro mu, daga yau hutu ya kare mana, babu zama har sai mun mika ki dakin mijinki..."


 yamutsa fuska tayi"dama ni ai ba hutu gare ni ba, gaba dayana a takure nake, tun da aka sanya bikin nan bani da hutu, wlh har nagaji da zuwa beauty spa din nan, kamar wata yar sarki zatayi aure, gaba daya an sauya min jikina da gyara"


dariya Batool tayi"sis tsakaninki da Allah baki ji dadin yadda kika koma ba? Fatarki tayi smooth babu ƙwarzane ko tabo kamar ka taba jini ya digo, ga gashinki ya ciza launin shi yayi laushi sai kamshin ya ke yi, ƙin ƙara kyau sosai,  masha Allah kamar hurul aini..." ta6e baki Unaisah tayi aranta taji dadin yabon kyanta da Batool ta yi.


"Kema kin sauya sis, gyaran jikin nan ya kar6eki wlh, kamar kece amaryar ma" murmushi batool tayi"Albarkacinki nake ci Unaisah, shiyasa nima nake samu ana zuwa dani spa din, naso ace tare zamuyi aure arana daya, amma Allah bai nufa ba, daddy yace saina kammala karatu ko zai barni in kula masu zuwa neman aurena" 




"Nima nayi fatan haka batool, amma karki damu, kema in sha Allah zakiyi aure nan bada jimawa ba"



"Na cika ki da surutu mrs owais, ki kwanta ki huta, Yau henne night ne, har nakosa time yayi wlh..." 



Ta faɗa tare da lullu6e mata jikin ta da bargo 


"Nan da wasu yan kwanaki a gadon mijin ki zaki dinga kwanciya" harara Unaisah tayi mata tana murmushi..


Tana jiyo motsin fitar Batool daga dakin sama sama kafin bacci mai daɗi ya yi awon gaba da ita..



Wuraren Ƙarfe  4 da rabi, Yan matan Amarya suka fara taruwa cikin gidan,  idan kuka ji na ambaci yan matan amarya kunsan wa nake nufi, Abokananta na amana wato ex-prisoners.



Ringing din wayarta ne ya farkar da ita, slowly ta buɗe idanunta da suka kada jawur, tayi shiru tana kallon ceilling.


Har kiran ya katse batayi picking ba, wani kiran ne ya kara shigowa da sauri ta ɗauko wayar daga kan drawer ta yi picking tare da karawa a kunnanta.



"Na kira ki ne, don na tuna maki saura kwanaki kaɗan ki zama matata"



 murmushi tayi"I can't wait to own you my man"


Sautin kayataccen murmushinsa tajiyo mai haɗe da fitar numfashin sa.



"I saw your graduation pictures on social media, and people were commenting on them, I felt indescribable jealousy why did you share your photos? why babe? Ba nace banda pics ba.." 


 yamutsa fuska tayi kamar tana a gaban shi"Am sorry, kasan ba yadda za'ai in hana photographers ɗaukar hoto na banma san sunyi ba, kuma wallahi bani nayi sharing din su ba, friends dina ne, amma zan kiyaye nan gaba"



"Okay,  karki damu, na fahimce ki"


Yana kokarin katse kiran tayi saurin furta"am na manta ban fada maka ba, Yau Henna night ne, wani kalar lalle kake so inyi"?



"Unaisah, check your WhatsApp I'll send you a message, take care"


"Okay ka kulamin da kanka" daga haka su kayi sallama.



Saukowa tayi daga kan gadon ta nufi toilet ta shige don tayi wanka.



Bayan mintuna, ta fito Jikinta sanye da bathrobe fara,

Closet ta nufa don ta shirya kanta, jim kadan ta fito jikinta sanye da kimono Robe.


Wayarta ta dauko ta shiga whatsapp chat dinsu don taga idan ya tura mata sakon



Murmushine ya bayyana akan kyakkyawar fuskarta sa'ilin da idanunta suka sauka akan screen din wayar tana karanta message din shi.



_I prefer maroon henna, zaifi dacewa da soft skin din hannun ki, When the henna is done, send me pictures so I can see"



Batasan ya akai ta ke jin dadi a duk lokacin data ga sakon shi ta whatsapp.  


Reply ta yi masa "Okay Sir"


~______________________________~




Unexpected ta tsinkayi muryoyin su daga waje



"Our bride-to-be! Sis! Mrs Owais! Unaisah! Where are you? It's time for the henna! Masu lallen sun zo, we're waiting for you"



Kafin ta yi wani yunkuri suka turo kofar ɗakin nata, Ko sallama babu, zare eyes dinta tayi da mamakin ganinsu ta shiga furta sunayen su"Hibba! Hawwa! Rubina! Hannah! Saukar Yaushe? Shine baku kira kun fadamin za ku zo ba"? Ta faɗa tare da nufar su ta soma yin hugging din su.


"Muna sane muka ki sanar dake saboda mu baki mamaki" hanna ce ta fada tana dariya.


Hawwa tace"tun bayan sallar La'asar, muka iso, a gidan daddyn mu mu ka sauka.."



"Amma dai kun shammace ni wlh, naji dadin ganin ku mutan kaduna da lagos, da har na fidda rai da zuwanku"! 



Haɗa baki su ka yi gurin furta 


"mun yi missing na ki, muna tayaki murnar kammala karatu, ay mana afwa bamu halarta ba, mun zo a makare, fatan mun same ki lafiya"?



"Nima nayi missing naku, wlh karkuji komai zuwan da ku ka yi ya fanshe laifin ku.. "



 ta fada tana kallon su, kowaccensu hutu ya zauna mata, sun ƙara girma sun zama cikakkun yan mata, suturun jikinsu masu tsada.



"Ya gajiyar tafiya? Ya kuma kuka baro mutanan gidan" har suna hada baki gurin furta"suna nan lafiyalou, sunce mu gaishe masu da amaryar su"


"Wow Sis kinga yadda kika canza? Kinyi haske kin kara kyau, fatar ki sai ƙyalli take..."



 rubina ce ta fada tana taba skin dinta" buge hannunta Unaisah tayi tana dariya.



Hibba Tace"wallahi nima abun da zance kenan, kin zama babbar mace, tubarkalla anya Unaisah baki shan maganin ƙara hips da breast"  zare mata idanu Unaisah tayi, gaba daya suka tuntsire da dariya..


Kamar daga sama suka tsinkayi muryar Batool daga bayan su..


"Ƴan sa ido, Tubarkalla,  komai na sis dina natural ne daga Allah,  dama zuwa kukayi don ku sanya mata ido ko"  ta fada da zolaya yayin da take karasa shigowa cikin dakin.


Dariya suka sanya gaba dayansu..



"Ba zuwa nayi don muyi fira ba, nazo ne don in fada maku ku fito mu sauka down lokacin ƙunshi yayi"



ta ƙarashe maganar tare da ruko hannun Unaisah a cikin nata su ka yi gaba sauran suka bi bayan su.


Tunkan su ƙarasa saukowa down, suka hango sauran bridemaids din da ke shigowa.


Parveen ce agaba ta dauki wankan abaya, idanunta sanye da shade baki, Yadda kasan hajiya saratu na tafiya, Cikin dattako take taku ɗaiɗai tana hura hanci, ta ruke hand bag a hannunta na hagu, ɗayan hannun ta ruƙe Cupcake din da take ci.


Sai shan ƙamshi ta ke yi kamar iska nayi mata wari, tana ji da kanta ɗiyar minister.


"Wa nake gani kamar foodie? Dagaske ke ce"? Hawwa ce ta faɗa.


Muryar ta da taji ne yasa ta kai dubanta garesu tana ganin su ta washe baki tare da ɗaga masu hannu ta nufe su, bakomai ne ya basu dariya ba face ganin gefe da gefen bakinta da yayi dama dama da cake din da take ci.


Tana karasawa gurinsu suka soma rungumarta.


"Ni babu wanda zai rungume ni? Ko baku ganni bane"?



 A tare suka dago tare da duban ƙofar shigowa falo, waro idanu waje su ka yi ganin Jemimah a tsaye ta ruƙe qugunta, sanye take da lace ta coge daurin kallabi, Yarinya fa ta girma a yanzu takai kusan shekara goma sha biyar.


 Su biyu ne su ka zo, tana a tare da yayarta Azeeza da ke tsaye  a bayanta, itama ta ƙara girma duk da har yanzu babu tsawo sai dai tana da dirin jiki, ayanzu ta wuce shekara ashirin da ɗauriya.



"Jemimah? Wa ya gayyace ki? Ba mun ce bamu san ganin Yara ba? Ko akwai tsaranki anan ne.."?


 da zolaya Parveen tayi maganar tare da nuna mata hanyar fita"Get Out"!



  harara Jemimah ta watsa mata"ki bari idan bikin ki yazo sai ki hanani zuwa, kuma ai Sis Unaisah ne ta gayyace ni, ba ke ba"



"Gaskiya jemimah ki nemi tsararrakin ki, tayaya zaki zo cikin mu, akwai tsaranki ne"?


Ƙyalƙyacewa su ka yi da dariya..

Zura hannu tayi cikin purse dinta suka kura ido suna jira suga dame ta zo masu.


Pistol ta zaro, ta saita su da ita.


Gaba daya suka razana tare da duƙewa ƙasa suna rokonta karta harbesu, kwashewa tayi da dariya.


Bushewa da dariya Azeeza tayi tare da girgiza kai tace



"bafa bindigar gaske bace, ta wasan yaran ce.." 



ajiyar zuciya suka sauke tare da mikewa tsaye gaba daya sunyi zaton bindigar gaske ce, saboda sunsan zata iya dauko ta daddyn ta..


"Duk wanda ya kara gigin kora ni, sai na fasa kan shi da bindigar nan" ta fada tana nuna kawunan su da bindigar, daga ka ganta kaga sangartacciya dabi'un ta irin na yara, tuntsirewa su ka yi da dariya..


Batool tace"Like father Like daughter, Jemimah wannan bindigar ta wacece kika dauko ko ta daddy mubarak ce"?


 Azeeza tace"shiya siya mata hada kakin sojoji, saboda ta faɗa mashi idan ta gama karatu soja zata zama irin shi, don ta dinga zuwa yaƙi"


 ƙyalƙyalewa su ka yi da dariya cikin nishaɗi.


Kafin suka fara huggin dinsu irin gaisuwar da suka saba yiwa junansu duk idan suka hadu..


"Assalamu alaikum, me ake tattaunawa ne ba a jira na karaso ba... " gaba daya suka jiyo tare da kallon su, kusan a tare suka shigo, Deeja ce tayi maganar, shigowarta kenan jikinta sanye da atampa, ta kashe daurin dankwalin ture kaga tsira, ga wani hadadden shade da tasaka ma idanun ta.



A kafaɗa ta yafa veil din ta hannunta ruke da wayarta..

Cike da farin ciki suka hada baki gurin furta"DEEJA!" 



"Na'am ƴan amanana! Am sorry amaryar mu, banzo da wuri ba, yau natashi ba lafiya amma da sauƙi yanzu Alhamdulillah".



 ta faɗa tana nufar su, daya bayan daya ta yi hugging din su tare da manna masu peck a foreheads in su, duk su ka yi mata ya jiki? ta amsa da sauƙi.


Badajimawa ba, Sajeeda da Zeenatu suka shigo tare da Sarah da yasmin da sauran kawayensu wadanda gaba dayansu Ex-prisoners ne gaba dayansu sun daukin wanka na mutunci, sun kai su Ashirin bayan sun gama gaggaisawa da junan su nan fa wata sabuwar firar ta 6arke a tsakanin su, haniyar firar da su ke yi ta cika Gidan gaba ɗa ya, bakajin komai sai sautin surutun su da dariyar su.



Ƙarfe biyar daidai masu ƙunshi su ka ƙaraso gidan.



A main Falo suka baje kolin su, sai da suka fara ƙawata seating area din falon da kayan decoration din su, daga daidai inda zasuyi zaman ƙunshin suka shimfiɗa  Red Rug (jan kilishi) daga kewayen shi floor sofa set ne daga saman kilishin wasu ɗunɗuma ɗunɗuman floor cushions ne a jere, kamar shimfiɗar sarki, daga tsakiyar rug din farantai ne ɗauke da kayayyakin ƙunshi.



Kafin su fara Aunty Danejo ta kawo masu soft drinks da snacks a cikin tray, sunji dadi har su ka yi mata godiya.



Music ɗin da su ka kunna a speakers ya karaɗe ko'ina na gidan, hakan ba karamin armashi ya karawa daren na su ba. 


Daga tsakiya Amarya ta zauna kan cushion.


Bridemaids suka zazzauna gefe da gafen ta, Batool tana a hannun damanta kamar yadda suka saba kasancewa, yayin da Hennah artists din su ka zauna akan floor Sofas, batare da bata lokaci ba suka fara harhada kayayyakin lallen kafin daga bisani suka fara yiwa yan matan amarya ƙunshi.


Gaba ɗaya Jira suke wadda zatayiwa Amarya ƙunshi ta ƙaraso saboda ta ce ƙunshin ta kaɗai ta ke so.


Bridemaids cikin nishadi da annashuwa suke, ana masu kunshi suna bin wakar da aka kunna ma su...


Wadanda ba'a farawa kunshin ba, suka miƙe tare da jan layi suka fara taka rawar tambola..


Jemimah da Parveen sun zaƙe sai tikar rawa su ke yi har haɗa qugunsu su ke yi.



"Da girman kujerar ki Yar ministern Lafiya, Takawarki lafiya toron giwa, Hajiya Parveen, rai ba buri saina abinci, an gaishe ki ƙaramar su babbarsu Naja'at bi ni ka lalace" 


har sun fara washe baki jin kirarin da Unaisah keyi masu amma da sukaji sharrin da tayi masu sai suka haɗe rai suna zumbura baki.


Gaba ɗaya suka sanya dariya hada ma su yi masu ƙunshin sai da su ka dara..



*HAJJATY🌹*



Gaba daya ta shiga damuwa ganin Lokaci na nema Ya kure mata, sai sauri ta ke yi ta kammala Girkin da ta ke yi, tasan in har ba zuwa tayi ba, Unaisah ba zata bari wani yayi mata kunshi ba, duba da yadda ta kwalla fa rai akan son tayi mata kunshi tun da ta ta6a ganin zanen kunshinta a hannunta ta rude da kyawun shi.


wannan ne karo na farko da zata farayi mata kunshi bataso taji ba dadi, shiyasa take ta sauri ta gama girkin ko ta samu ta shirya ta tafi.


Tana atsaye gaban Gass Cooker  ta bude soup pot tana jujjuya miya da spoon din hannun ta.


Kwatsam taji an fusge spoon din hannun ta, aikuwa a razane ta saki murfin tukunyar, tayi saurin juyawa don ganin wanene



Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke lokacin da idanunta suka shiga cikin na shi..


Cikin rawar murya ta furta"um..yay.. Yaya mubarak, am sorry, bansan ko kayi min sallama ban ji ba"


Murmushi yayi yana jin dadin rudewar da takeyi idan ta gan shi, ba karamin kyau takeyi mashi ba idan tana magana a tsorace.


"No karki damu banyi sallama ba, ni yakamata na baki hakuri na tsorata ki" murmushi ta ɗanyi sam hankalin ta ba akwance ya ke ba


Mika mata spoon din yayi tasa hannu ta kar6a.


Wani kallon so da ƙauna suke jefawa junan su, duk tabi tasha jinin jikin ta, zallumine ya cike ta, tana jin tsoron Turai ta gansu a tare cikin kitchen, tasan zataji kishi.


"Kin bar babynki da yunwa, Baki bashi abinci ba" ya faɗa yana shafa cikin shi..



Cikin rawar murya tace"am.. Sorry yayana, na kusa kammala girkin, ka koma dining ka jira ni yanzun nan zan kawo maka.. " ta fadi hakanne don ta samu ta lalla6a shi ya fita..


Allah mai jujjuya al'amurra, bata taba zaton zata so wani ɗa namiji bayan Praveen ba, ada ji take babu wanda zai iya maye mata gurbin dan uwanta Praveen amma a yanzu da babu shi, Sir Mubarak Ya sace zuciyarta da soyayyar shi, kulawar shi, komai ma..


"Kora ta ki ke yi ko"? Girgiza mashi kai tayi a'a wallahi..


Murmushi yayi "nasan me kike jima tsoro, to meye na damuwa a ciki? Ta riga da tasan ina sonki, da amincewarta ko kin manta cewa itace ta fara bani shawarar  in nemi soyayyarki saboda tana son ku rayu a karkashin inuwa ɗaya.. "  


Kamar zata sanya kuka tace"na sani ni ba wannan bane damuwana, kasan dai babu kyau mace da namiji su ke6e ko"? 


Har ya buɗe baki zai yi magana Unexpected muryar Naufal ta katse su.



"Daddy! dama kana a kitchen?




Da sauri Sir Mubarak ya ja da baya tare da shan mur yace



"Tambai, kai zan tambaya yaushe ka dawo gidan"?



Ƙumshe dariya Hajjaty ta yi tare da juyawa ta cigaba da duba girkin ta.


 yamutsa fuska yayi aransa ya furta"hmm a sannu zan gano menene a tsakanin ka da mommyna, kai ta daure min fuska kana shan mur"


"Tun ɗazu na dawo.." 


ya fada tare da nufar mommynsa data basu baya.


"Mommy, Unaisah ta kira ni awaya tace tana ta kiran ki bakya picking, ke suke jira kije ki mata ƙun shi"


Cike da jin kunyar shi ta furta"na manta wayar a daki, pls, Idan sun sake kira ka fada masu aikine ya rukeni, amma dana gama zan taho.." 


amsawa yayi da toh, ya juya zai fita ya ɗan juyo ya saci kallon Sir mubarak karaf idanunsu suka shiga cikin na juna.


Ɗage mashi gira yayi"ɗan sa ido  kwanan nan zan sake aske maka sumar kanka"



ƙasa ƙasa da murya yayi maganar don kada taji su.



Cike da jin kunyar shi Naufal yayi saurin fucewa daga kitchen din cike da fargaban kada ya aske mashi sumar kanshi daya tara kamar mace.



Girgiza kai sir mubarak yayi..

Yana son Yaron sosai kamar yadda ya ke son Jazz ba ka ta6a gane ba ƴa'ƴansa ba ne.



fuskarsa da murmushi ya dubu Hajjaty.


"Ki aje girkin ki tafi zanyiwa yar uwarki magana tazo ta karasa, kin sa masu rai, Jira bashi da dadi"

 

Girgiza kai tayi"no, pls, kada kayi mata magana, zanyi kokari in gama"


"tun da baki so in kira ta, to ni ki bari  in karasa maki girkin" 


zare idanu tayi da mamakin maganarsa tace "ya mubarak, da kanka.." girgiza kai tayi"ban yarda ba, bazan bari kayi girki ba, bayan kana da masu girka maka" 


Sallamar Turai ce ta katse firar su, Aruɗe hajjaty taja baki tayi shiru, 


gaba daya idanun su akan ta.


Fuskarta ɗauke da murmushi tace"love birds, zan iya sanin me kuke zantawa ne"? 


Murmushi su ka yi

Sir mubarak yace"kin hana in ajiye masu aiki a gidana, gayanan yar uwarki aiki yayi mata yawa, ga gidan biki sunata jiranta zatayiwa amarya ƙun shi..." 


6ata fuska Turai tayi"banji dadi ba, meyasa baki faɗa min ba? Kin bar bayin Allah sunata jiranki"


"Banaso na takura maki ne, kuma nama kusa karasawa.."


bata ƙare maganar ba, Turai ta katse ta"bana son jin wani abu, pls, kije ki shirya ki tafi in ba so kike raina ya 6aci ba" har cikin ranta taji dadi"nagode sosai"

Ta fada tare da kama hanya ta fuce.


Kallon Sir mubarak tayi"pls, yakamata kana dan jurewa, ka san inda zaka dinga tunkarar hajjaty, yaron nan har yanzu wani kallo ya ke maka..." dariya su kayi.


"In sha Allah zan gyara uwargidana, ina fata ban 6ata baki rai ba.." 


Harararsa tayi"kishi nake ji, idan naganka da hajjaty..." ta fada da zolaya.


"Amma kasan wani abu, silar zuwanta cikin rayuwar mu abubuwa da dama sun sauya, Hajjaty tana da kirki bata gajiya da kyautatawa ya'yana, kamar ita ta haife su tana son su, bata gajiya dayi masu kunshi da kitso da kwalliya, saida nace ta bari bana so tana wahala amma ta nuna rashin jin dadin ta.." 


tun da tafara yin magana murmushi ne akan fuskar sir mubarak, yana jin dadin yadda Turai ke yabon ta.


"Babe, bana jin zan iya kishi da hajjaty, duk da nasan dole inji ba daɗi amma Kuma idan na tuna, Nina baka shawarar ka aureta dadi nake ji, saboda ba karamin taimako zamu yi ma rayuwarta ba, ina jin tausayin rayuwarta, bata da kowa in ba Allah da mu ba"



idanunta ne suka cicciko da ƙwalla.



"Am so proud of you, bani da tamkarki turai, kin cika mata tagari, kyawawan halayanki sunfi komai jan hankalina, baki da son kai, da wata ce ba zata taba bari kawarta da take a cikin wani hali na rashi, ta auri mijinta ba, ke ta dabance..."


 ya fada tare da rungumota, murmushin jin dadi ta saki"kaima ka cika miji nagari,  Uban marayu, ina alfahari da kai"


 yaji dadin kalamanta.


Peck ya manna mata a forehead dinta.


"Nagode sosai Ummu Naja'at, Allah yayi maki albarka, Allah ya saka maki da aljanna silar kyautatawar da kike mani"


"Ameen daddyn Azeezaty.." dariya suka sakarwa juna.



~________________________________🌹~


Lokacin da Hajjaty ta karaso murna ta cika su, batare da bata lokaci ba, ta kama hannayen Unaisah ta fara tsantsara mata ƙunshi, both side na hands dinta da tafin hannunta dana kafarta, da yatsunta duka ta kawata su da maroon henna, sai da kowa ya raina kunshin shi saboda haduwar kunshin Unaisah, abunka ga fatar amarya taji gyara, duk da suma bridemaids din nasu yayi kyau.


Ko da Batool taga kunshin Unaisah nan fa ta haɗe rai tace itama Hajjaty take so tayi mata kunshi kuma irin na Unaisah ta ke so komai da komai..


Hajjaty tace bazai yiwu ba, anfi son kunshin amarya ya banbanta dana bridemaids.



Kowa bai goyi bayan ayi mata irin kunshin Amarya ba, hakan yasa ranta ya 6aci, har tayi zuciya ta mike zata bar gurin

Unaisa tayi saurin dakatar da ita,  cikin sanyin murya ta lallashe ta tace ta dawo ta zauna ayi mata irin kunshinta, dakyar ta shawo kanta ta koma ta zauna har suna tsonakarta da cewa copycat din amarya, komai amarya tayi sai tayi itama, bata ko kula su ba.


Abun daya ɗaurewa Unaisah kai,   meyasa Batool ta ke son yin komai irin nata? Yanzu ta gane dalilin dayasa tun farko taki yarda ayi mata kunshi ashe jira takeyi ayi mata irin nata, ta rasa gane meyasa batool take kishi da ita? Meyasa take kwaikwayonta? tun bata fahimta har saida tafara ankara, daidai da spa idan sukaje komai akayi  mata na gyaran jiki, batool sai tace ayi mata irin nata, komai da ake ma amarya itama sai anyi mata, ko kallonsu kayi ba zaka ga banbanci ba, kamar dukan sune amaren, kuma idan ta nuna tanaso ayi mata irin nata wani ya nuna rashin goyan bayanshi, ranta baci ya ke yi, har sai ta samu ta lallasheta, bawai bakin ciki take yi da hakan ba, ta yarda da Batool sai dai tarasa gane meyasa take yi mata haka? 

Lokacin da lallen nasu ya bushe Hennah artists dinne suka wanke masu shi, su ka shafe masu zanan kunshin da mayuka masu kara fito da kyawun kunshi.


Bayan da suka kammala zaman kunshin, henna artists suka tafi bayan da aka hada masu sha tara na arziki, Hajjaty ce kadai bata kaiga tafiya ba.

ta kira Unaisah gefe daya ta fada mata tana son suyi magana.


Unaisah tace su shiga daga ciki.


A bedroom din ta suka shiga.

Ta daura Handbag dinta akan gadon Unaisah suka fuskanci juna..



"Unaisah ba sai da nace maki kyauta zanyi maki kunshin ba? ya akai naga alert na dubu dari uku kudin menene har haka"? arude Unaisah tace"bani na tura maki kudi ba, amma muga alert din" miƙa mata waya hajjaty tayi tasa hannu ta kar6a tare da duba reciept din.


Murmushine ya bayyana akan fuskarta"Aunty hajjaty, wannan alert din daga Chief ne, ni na fada masa ke zakiyi min kunshi amma bansan cewa shi zai biya ba"


Murmushi Hajjaty tayi"sunyi yawa Unaisah, sai kace ni nayiwa duka yan matan amarya kun shi?


"Please karki damu, rabonki ne,  yaji dadi kinyiwa amaryarsa lalle shiyasa shima ya baki tukuicinsa.." 



annurin farin ciki ne ya bayyana akan fuskarta, Taji dadin yadda Unaisah take bata girma.



"Saboda za6ana da kikayi a matsayin wadda zata yi maki lalle, nima ga nawa gudummuwar .." 



ta ƙarashe maganar tare da buɗe handbag dinta, Unaisah ta kura ido a kagare da son ganin menene ta kawo mata.


Set ta curo na kayan gyaran jikin amarya..


Dayawan su, Sudanese dilka, kabbasa spray, Hair bakhhoor diffuser, sandal sukkariya, dilka soap, turaren tsugunno da sauran su, saida ta gama jerasu agaban Unaisah tukunna ta soma yi mata bayanin yadda zatayi amfani da su, ta nutsu tana sauraron ta hadi da dan jinjina kan ta..




daga bisani ta ɗaura da yi mata nasiha


"sai fa an cire kunya da girman kai ake nunawa miji soyayya, ki zama karuwar mijinki, kullum ki kasance cikin gyara da tsafta, bana son tuna rayuwata ta baya amma zan fada maki sirrina saboda inaso kisan surrukan mallakar miji ba boka ba malam, wanda in har kika bisu nayi imanin mijinki ba zai ta6a gajiya da ke ba, zai kasance kullum cikin marmarin ki"



daɗine ya lullu6e Unaisah ta kasa kunne tana sauraron sirrikan da Hajjaty ke faɗa mata, ta bayyana mata komai batare da jin kunyarta ba, sai dai ita idan taji abun daya fi karfinta ta ɗan sunnar da kanta ƙasa ko ta rufe fuskarta da tafinta ko ta sanya pillow.


Amma fa taji dadin shawarwarin da hajjaty ta bata game da zamantakewar aure..



Unexpected ta dinga hango inuwar mutun jikin window din dakinta, ta wutsiyar idanun ta kamar akwai wanda ke yi masu la6e.


"Bansan da wasu kalmomi zanyi maki godiya ba aunty Hajjatyna, Allah ne kadai zai iya biyanki, ke ta dabance, Kina da kirki, kinason yar nan taki sosai.


Taji dadin maganar Unaisah"karki damu Unaisah, ni dai fatana ki zauna lafiya a gidan mijinki..  "


Ta fada tare da mikewa, itama Unaisah ta mike.

Wayar Unaisah ce tayi ringing da sauri ta juya ta dauko tayi picking tare da karawa a kunnanta.


"Mommy, har mun gama zaman kunshin, Naji shiru baku dawo nan ba"


On the other hand Muryar Benazir ta amsa da cewa"muna a part din Danejo,  aikine ya ruƙe mu, ba lallai mu shigo nan ba, zamu kwana anan"


"Am sorry mommy, mun barku da aiki"


"Karki damu, Ya zaman kunshin naku? Ina fata anyi maki mai kyau"?


"Eh mommy, Aunty hajjaty ce tayi min, yanzu haka muna a tare, baki ga alherin da tayi min ba, ta kuma bani shawarwarin da zasu amfaneni"



"Kai Amma naji daɗi wallahi, idan tana a kusa ki bata wayar inyi mata godiya"


"Toh" ta fada tare da mikawa hajjaty wayar da fara'arta ta kar6a, Benazir ta dingi yi mata godiya.


A hankali Unaisah take dan satar kallon Window glass ta wutsiyar idanun ta, Tarasa gane wanene ke yi masu la6e, kuma yaki tafiya yana nan yana sauraronsu baisan tana ganin inuwar shi ba.


Bayan da hajjaty ta yi sallama da Benazir, ta miƙa mata wayar ta kar6a ta kara a kunne.


"Unaisah, Ki kula min da kanki"


"Toh mommy, kema haka"


Daga haka sukayi Sallama, bayan ta ajiye wayar, suka fito tare da hajjaty don tayi mata rakiya.


Gaba ɗaya ƙawayen amarya agidan za su kwana saboda sunyi dare sosai, duk da babu nisa gidajen su amma akwai tazara kaɗan.



Har bakin gate ta rakota, bayan sunyi sallama ta dawo gida.


Har lokacin bridemaids basu je sun kwanta ba, sun cika falon da haniyarsu.


Gyaran muryar da tayi masune yaja hankalin su ga kallonta.


"Kuje ku kwanta, Gobe akwai aiki agaban mu" 


ba musu suka amsa mata da toh.


Bayan ta nunnuna masu Bedrooms din da zasu kwana a ciki, duk mutun uku daki daya.


A tare da Azeeza da Jemimah suka nufi Bedroom din ta.


Bayan sun shiga, ta ɗauko masu rigunan baccinta taba su suka musanya dana jikin su, kafin su ka kwanta kan gado.


Kamar ance ta kalli kayan da Hajjaty ta kawo mata nan take gabanta ya fadi ganin babu wasu daga Cikin su, dayake komai kala biyu ta kawo mata, an ɗebi kala ɗaiɗaya anbar mata sauran.


To fa! Ta fada da rudu akan fuskarta aranta ta ayyana wanene ya shigo dakinta ya sace mata kaya? Da sauri ta dubi window tunawa da inuwar mutumin data gani dazu yana yi masu labe, zato zunubi amma tana ji a ranta dakyar in ba Batool bace ta sace su tun da itace ke gasa da ita, In ba ita ba waya damu da kayan amarya.


Girgiza kai ta danyi tare da kallon su jemimah har sunyi nisa a baccin su.


Wayarta ta ɗauko, Ta kira layin batool almost 3 times tana ringing batayi picking ba.


harta fidda rai sai ga kiran Batool ya shigo wayar

Da sauri ta yi picking"sis Ina kika shiga ne? Ba adakina zaki kwana ba"? 


On the other Hand Batool tace"ai ni gani nan harna kwanta.."


"A wani daki ne Kuma ku nawa ne"?


"Mu ukune ni da Sajeeda da Zeenatu"


"Meyasa ba zaki dawo nan ba? Nafi son inji ki a kusa dani" ta fada kamar zata saka mata kuka.


"Kiyi hakuri Ukhtyna, na riga na kwanta, Kuma muna a down stairs, kinga dare yayi bazan iya fitowa ni kadai in dawo nan ba.."


 kanta ne ya daure, Batool bata taba yi mata gaddama akan tayata kwana ba in ta bukata sai yau, nan take ta tabbatar da zargin da takeyi mata, wato tana jin tsoron tazo asirinta ya tonu ta gane itace ta daukar mata kayanta.."


 cikin sanyin murya tace"karki damu sis, ki kulamin da kanki, sai Allah yakaimu"


"Kema haka.." bayan sunyi sallama, ta koma kan kujerar gaban study desk dinta ta zauna, table Lamp ta kunna nan take haske mai kyalkyali ya gauraye gurin.



Lumshe idanunta tayi tana shakar kamshin dake fita daga jikin ta.



Duk yadda taso ta hana zuciyarta kawo mata tunanin shi saida ta gagara..


Kalamansa ne suka soma dawo mata a cikin tunaninta..


_Unaisah my desire for you burns fiercely, taking your virginity has become my utmost dream, For what feels like an eternity, I've been tormented by my longing for you, I've concealed it for your sake, but my craving for you only intensifies_


_I'm patient, Unaisah, not wanting to rush or harm you, I yearn to make love to you with your trust, your consent, I don't mean to pressure you, I simply can't wait to be with you_


_When I return, grant me my heart's desire, Unaisah And let's create a memory that will last a lifetime..."_


 siraran hawaye ne suka soma gangarowa ta cikin idanunta dake a rufe kaitsaye suke dira saman kuncin ta..



Cikin rawar murya ta furta"meyasa tun lokacin da kana araye bangane yadda kake azabtuwa da son kasancewa dani ba? bani da hankali Danish, ni sakarya ce"!



"Abun da kake ji nima inajin shi Danish, inama ana iya dawo da wanda ya mutu? Da ba abunda zai hana in dawo dakai don in cika mana burin mu.." da sauri ta toshe bakinta, gudun kada shesshekar kukanta ya farkar da masu yin bacci a ɗakin..



"Allah ya jaddada rahamarsa a gare ka my Man"


_ta saba yi mashi addu'a duk da bata da tabbacin koya musulunta before ya mutu_


"ina fata nima Allah ya dauki raina saboda na kosa ayi tashin alkiyama kona sa ke ganinka"  



Tana kuka ta fada. (Unaisah da wauta)



 kamar mai tabin hankali ta dinga sambatu ita kadai, taki tashi taje ta kwanta, duk daren Allah Haka take fama.


Unexpected kira ya shigo wayar ta, duba sunan me kira tayi ganin Angon nata ne yasa tayi picking call din tare da kara wayar a kunne..


Sexy Voice dinsa ce ta ratsa kunnanta"me kike yi har yanzu baki yi bacci ba"? 


Lumshe idanunta tayi slowly tana ji kamar Danish ne ke yi mata magana..


"Tunaninka nakeyi..." 


"Nima na kasa runtsawa saboda tunaninki, saura kwanaki kadan suka rage, i can't wait to see you on my bed" 


kunya ce ta kamata har takasa furta kalma, ta rasa ya akai take jin muryarshi sak irin ta Danish ko dan ta sama ranta shi ? 


Allah yayi dare gari ya waye, Da sassafe Amarya da ƙawayen  suka farka daga bacci kowaccen su ta shiga toilet tayo wanka, suka shirya kan su cikin abaya, Already an tanadar masu abinci mai rai da lafiya na breakfast din su a dining area..


Bayan da suka zauna yin beakfast, kowa Ya ci ya koshi, In ka cire Unaisah data kasa ci dayawa, kalaman chief owais ne keta dawo mata a cikin tunaninta, duk ta rasa sukununta, da tunanin shi ta farka daga bacci, batason ganin komai in ba shi ba, gashi ya haramtawa kanshi zuwa zance har sai bayan an shafa fatihar auransu.


Around Ƙarfe shabiyu na rana, Benazir ta kira Unaisah awaya ta ce tana son ganinta tare da ƙawayenta, su hadu a part din Danejo...


Bayan ta sanar da su, gaba ɗaya suka dunguma izuwa Sashen Aunty Danejo, suna shiga main falo suka fara hango haɗaɗɗun Invitation bags a saman rug, daga jikin kowace jaka an rubuta will you be my Bridemaid? tare da sunan mamallakin jakar.


Nan take suka gane nasu ne za'a basu, farin Ciki Ya cika su kamar su zuba ruwa kasa su sha.


Anan suka taras da Benazir da Ummi tare da Danejo, with respect suka gaishe da su, Unaisah ta zagaya ta bangaren mommynta tayi hugging din ta bayan sun gaisa tayi hugging din Danejo dake ta sakar mata murmushi.


Batool tuni ta yi gurin mommynta, su kayi hugging din juna.


Bayan sun gama gaggaisawa da ƴan matan amarya..


Benazir tace"gaba daya munayi maku barka da zuwa, jiya bamu samu zama ba, shirye shiryen biki ya hana mu leko gurin ku, shiyasa bamu samu zuwa munyi maku barka da zuwa ba, amma kuna aranmu, munji dadin zuwan ku..." Ummi ta ɗaura da cewa"muna fata kunyi bacci lafiya kun tashi lafiya, Ya kuma gajiyar zaman ƙun shi"


 atare suka hada baki gurin furta"Alhamdulillah, Mun tashi lafiya, muma munyi farin ciki da kuka gayyace mu, kuma in sha Allah da mu za'a kare bikin nan"


 murmushi suka saki gaba dayansu sunji dadin maganar su.


Danejo tace"wadannan invitation bags din da kuka gani, musamman saboda ku ango ya bada akayi maku daga Company, ba wai iya jakar bace, hada kyaututtuka na musamman a cikin su, Kun shirya gani?.."


 Ihun Farin Ciki suka sanya tare da shewa Yeehhhhhh..


Ummi tace"yawwa my ladies, ku jera layi, duk wadda muka kira sunanta sai tazo ta kar6i nata"


 cikin sauri suka shiga layi suka yi shiru cike da zakuwa suke jira abasu don su ga menene a ciki..



Ummi da Danejo ne ke daukar bags din idan suka duba sukaga sunan dake a jiki sai su kira su ba mai ita..


"Sadeeja, Zeenatu, kuzo ku kar6i naku" Benazir ce ta kira sunansu atare.


Bayan da sukazo ta damka masu bags din a hannayensu kafin ta manna masu peck a forehead dinsu"yan matana, Allah ya nuna min naku da raina da lafiyata..."


 ta fada tana shafa kafadarsu cike da jin dadi suka amsa da ameen Aunty tare dayi mata godiya.


"Deejatun harisu! Azeeza matsoraciya, naja'at Sojanya foodie Rai ba aburi,  kuzo ku kar6i naku.."


 Unaisah ce ta kira sunayensu tana jin dadin tsokanar su, gaba daya mutanan dake falon suka tuntsire da dariya jin sunayen data kirasu, Benazir sai kallonta takeyi kamar zata hadiyar yar tata, wani irin alfahari ta ke yi da ita.


Bayan ta mimmika masu bags din su, ta ɗaga murya ta furta"UKHTY will You be My babbar kawar amarya?  Ta fada tare da daga jakar dake a hannunta sama mai dauke da sunan Batool.


Farin cikine Ya lullu6e Batool da sauri ta nufeta suka rungume juna.


 kallon juna Ummi da Benazir su kayi wani dadine ya lullu6esu ganin yadda ya'yan nasu suka hada kansu, suma sun zama aminnan juna kamar dai su ɗin.


Bayan Sun gama rarraba masu jakunkunan, tun anan wasu suka fara budewa suna duba kayan dake a ciki..



A hankali Batool ta zaro outfit din da ke a ciki, fitted gown ce dinkakkiya, ta code lace maroon da ashoke, asaman sofa ta daura kayan, ta fiddo  

invitation card mai ɗauke da event programmes, hada phone case with wedding logo harafin sunan amarya dana Ango ne a jiki O&U ga wani karamin kit, bayan data buɗe cikin shi,  tissues ta gani tare da breath mints and pain relievers.



Murtuke fuska tayi wani irin 6acin raine Ya turnuke zuciyarta, babu wanda ya lura da yanayinta sai Unaisah dake ta satar kallonta, aranta ta ayyana meke damun Batool? Kishi take dani? Ko bakin ciki takeyi! Ya  Allah kasa zargina karya zamana gaskiya.



Batool in wani abu kikeso ni me iya bar maki ce ta fada a ranta.


Ƙawayen amarya sun rude da ganin zunzurutun kyaututtukan da aka basu, ango ya gama masu komai, sun fahimci Yana ji da su, sai santin kayayyakin sukeyi suna yabawa banda babbar kawar amarya.


"Yeehh hohoho Wayyo Allahna Nima ga nawa kayan"


 Jemimah ce ta furta da karfi, gaba daya hankali ya dawo kanta, tana akan kujera ta zazzage kayan dake a cikin jakarta sai washe baki takeyi farin ciki Ya cika ta..



Ƙyalƙyacewa su ka yi da dariya suna kallon ta.



"Amma ni abin daya ɗaure mun kai? Tayaya akai wadanda suka dinka mana kayan sukasan size din mu, ku dube ni ku gani? Nayi kyau"? Parveen ce tayi tambayar yayin da take nufo su daga wani daki ta fito, jikinta sanye da  kayan data gwada.


Sakin baki su ka yi suna kallon ta, Kayan sunyi mata kyau sunbi shape din jikin ta.


Benazir tace"masha Allah, autar minister, you look gorgeous, nafi tunanin angone ya bada awonku may be yana da shi, Ko kar6a ya yi agurin parents din ku" 


har suna haɗa baki gurin yi masu godiya.


Ummi tace"bamu yakamata ku godemawa ba, Unaisah da angonta.." sunnar da kai Kasa Unaisah tayi, gaba daya suka nufeta sunayi mata godiya"thank you sis, pls ki fadama hubbynki muna godiya, Allah ya kaimu lokacin da rai da Lafiya, Allah ya cika maku burinku" kasa kasa da murya take amsawa da ameen.


Tana lura da Batool data haɗe rai, sai ci ka takeyi tana batsewa, kowa yana yi mata godiya ban da ita, ta rasa gane laifin me tayi mata ❓


"banga na yan uwanmu maza ba, Ko su banda su ne"? 


Deeja ce ta tambaya taji shiru ba abata na yayanta ba..


Benazir tace"hada su, amma nasu ba gurin mu aka kawo ba, ai su ta bangaren ango suke ko"?


ta fada tare da ɗage mata gira..


Dariya Deeja tayi"nagode auntyn mu.."



Cikin kwanakin da suka rage, bothside dangin ango da dangin amarya sun dage damtse suna ta shirye shiryen Bikin ya'yan na su, haka zalika Amarya da ango suma shiri su ke yi na musamman domin tarbar ranar auran su.



*ANEELERH🌹🔥*



Fitowa tayi daga Bedroom din ta dake a downstairs ta nufi main falo, sanye take da bubu gown ta material, tayi rolling mayafi akanta, Masha Allah ta zama babbar mace, fatarta tayi haske irin na wadanda hutu ya samu mazauni a jikin su, daga gani tana samun kulawa agidan mijin ta.


A cikin kunnanta ta tsinkayi muryar mijin nata "idan ina yi maka Assignment ka dinga maida hankali akan bayanin da nake yi maka, kana ji na ko"?  


Ɗagowa tayi a hankali ta ɗaura idanunta akan shi, Su biyu ne zaune kan rug, ya tasa baby junaid agaba yana yi masa Assignment da textbook dinsa, daga gefen sa Laptop dinsa ce da ya ke aiki da ita..


Baby Junaid an girma yanzu sai dai har yanzu bai daina shagwa6a ba saboda step father dinsa ya sangartashi da gatanci, idan kagansu a tare ba zaka ta6a cewa bashi ne ya haife shi ba, hatta kayan jikin su kala ɗaya ne.


"Assalamu alaikum.. " sallamartace ta katse su, a tare suke dube ta, Murmushi ta sakar masu Junaid ya ambaci sunanta Mommy

"Na'am daddys Boy..." ta fada tare da kallon Zaki dake bin ta da kallon kauna.


"Sannu da kokori honey, Halan shine ya hana ka yin aiki, kullum baya gajiya da kawo maka assignment, har cewa nayi ya dinga bani inayi masa amma yafi son wahalar min da kai"  ta karashe maganar tana zama daga gefen shi.


murmushin gefen fuska yayi mata"ai ni nace ya dinga kawo min inayi masa, saboda banaso ya takura min ke" 


Taji dadin maganarsa


"kana ji da mommyn babynka, yanzu dai ya maganar zuwa gidan biki, please ka barni inje, gaba daya satin nan ban leka ma su ba, nasan me kake mawa, wlh zan kula maka da kaina.." ta faɗa tana marairaice masa fuska.


"Ki fahimce ni wifey, bawai banso ki motsa jikin ki bane No, fita ayanzu bazaiyiwu gare ki ba, tayaya zakije gidan biki kina fama da laulayin ciki"?  zumbura masa baki tayi.


Hankalin baby junaid ba akansu yake ba, ya mayar da idanunsa akan plasma tv yana kallon cartoon.


"Ai na daina laulayin, Jikin da sauƙi yanzu... " bata kare magabar ba, taji tashin zuciya, nan take ta soma yunƙurin amai kafin tayi wani yunƙuri aman ya kubce mata kaitsaye ta kwarara shi asaman lap dinsa, zare idanu tayi tana faman jan numfashi, babu alamun yaji kyankyami ko haushin ta sai ma murmushin daya sakar mata"kinji sauƙi ko? Kuma kin daina laulayi"? Ya faɗa da zolaya, cike da jin kunyarshi ta sunnar da kanta ƙasa.


"A haka zakije gidan biki, kina yi masu amai, su kansu zasuji ba dadi" idanunta ne suka ciko da kwalla"na hakura da zuwa, amma pls ranar biki, kabarni inje"


Jinjina kai ya yi"In sha Allah zan barki kije, yanzu tashi muje toilet ki wanke min wandona da kika 6ata da amai" 


atare suka mike, tare da barin falon, kwata kwata Junaid bai lura sun fita ba,  


"Junaid... " muryar khadija mai aikin su ce ta katse shi, dagowa yayi tare da dubanta yayin da take nufo shi "Aunty Khady, yunwa nake ji, har yanzu baki gama mana girkin bane"? Ya fada yana yamutsa mata fuska.


 Murmushi tayi sai naga tayi min kamanceceniya da tsohuwar mai aikin Anila.


"kwantar da hankalin ka, na kammala shirya mana Dinner, Ina aunty Aneelerh da daddyn naka ne"? adan rude ya juya yana duban gurin da suke ganin babu su yasa shi cewa"nan suke zaune fa, ƙila sun shiga ɗaki"


"Okay, kaje ka faɗa masu dinner is ready amma ka fara knocking room door din kafin ka shiga kamar yadda na koya maka"


 Amsawa yayi da toh ya mike da sauri ya nufi bedroom din mommynsa..


Shin wacece Khadija mai aikin Anila? ko zaku iya tunawa da Yan uwan mariganya Aisha wadda kuka fi sani da (ANA) 🥺? 


_Janet da Esther, wadanda bayan da suka musulunta Ana ta sauya masu suna, Janet khadija, Esther (Zainab) tun lokacin da al'amarin Mutuwar Ana Ya fasu sunji tashin hankali da bakin cikin abin daya faru da yar uwarsu a lokacin da labarin ya risƙe su, wanda silar hakan yasa gaba dayansu suka kamu da depression har jinya sukayi gadon asibiti, sunji mutuwar Aisha, saboda suna son ta fiye da komai, tamkar uwa take a gare su, da ya ke Anila tasan basu da kowa a arewa kuma marayu ne tasan idan suka koma ƙauyensu na kudu a matsayin musulmai danginsu ba zasu kar6e su ba, wannan dalilinne yasa ta kai kukan ta gurin abie a lokacin da sukazo cikin mawuyacin hali, ta rokesa akan ya taimaka ya bar su su cigaba da zama tare da su, abie yace ko bata fada ba shima bazai bari su koma ba,  zai ruke su a hannun shi, kuma zai dauki nauyin komai na rayuwarsu, tun daga lokacin zainab da Khadija suka kasance karkashin kulawar Abie da iyalin sa, a yanzu haka Zainab tana zaune agidan abie yayin da khadija ta ke aiki agidan Anila, Yanzu haka sun kusa yin aure har an sanya bikin auran su_


Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post