Rainonta Zanyi Page 8 - Novels Elite

Rainonta Zanyi Page 8 - Novels Elite

Abokiyar Hira Novels

RAINONTA ZANYI🔞*

ROMANTIC LOVE STORY



FREE PAGE 8

*FREE PAGE ZAI ƘARE A PAGE 10 GA MASU BUƘATA REGULAR PAYMENT ₦500 VIP GROUP ₦1000 SPC PAYMENT ₦1500 VIA 6037312299 MOHAMMED AISHA KEYSTONE BANK*


“Danne ɓacin Ransa yayi tare da kutsawa izuwa Falon Abie , wanda shigowar sa yasa Hajiya Nadiya gyara zaman ta tare da kokarin daidaita natsuwarta kamar babu Abin dake damun ta ”. Abie Barka da Dare , Mummy Barka da Dare , ya furta yana mai neman wuri yana Zama ”. Ganin sa da kuma jin Muryar sa yasa Aleena murtiƙe fuskar ta tamau tamkar wacce taga mugun Abu , Muryar Abie ne ya katse ta inda yake cewa “ Afeef baka kwanta ba Ashe ?”. Lumshe idanun sa yayi yana buɗe su tare da cewa “ Eh Abie ai....Uncle Afeef barka da Dare ”. Muryar Aleena ya katse sa , inda ya murtiƙe fuska tare da share ta Tamkar baiji mene tace ba ko bada shi take yi ba ”. Ganin haka yasa Mummy Nadiya kallon sa tana cewa “ Afeef ,aleena na magana ”. Kallon Mummy yayi kana ya kalli Aleena yana cewa “ Naji Mummy....Ganin haka yasa Aleena miƙewa tana hugging Abie tare da cewa “ Abie Sai da Safe , Mummy zan kwanta! Ta furta tana mai janye jikin ta daga na Abi tare da kallon ɓangaren da Mummy Nadiya take zaune ”. Ohk muje kiyi barci ko? , Ta furta tare da kokarin miƙewa , don take ta saka Aleena barci don bata barci sai Mummy na gyefen ta....Ganin haka da son ɓata mawa Aleena Afeef ya katse Mummy da cewa “ Mummy ki zauna magana zamuyi yanzu ”. Tun da Aleena taji haka bata saurari mene Mummy zata ce dashi ba haka Abie ta fice da Sauri , don A yanzu Afeef ya fara bata Tsoro lamarin sa ”. Don tuni ta fara tunanin ba zai rasa Aljanu ba akan sa ”. 


.....Kallon Afeef Mummy tayi tare da jiran jin maganar da zai fito daga bakin sa ”. Ɗan Shiru yayi kana ya numfasa yana cewa “ Mum Banyi tsammanin ganin haka ba , Wannan wacce irin tarbiyya ce kuka ba Aleenah? Sam ba yanda naso ba Mummy yarinya babu ƙwaɓo bata san komai ba sai Rashin kunya? Ina buƙatar Aleena ta dawo hannu na zan kula da ita...” Kai Afeef bana Son jin Wannan maganar, Abie ya katse sa cikin hanzari wanda hakan yasa Afeef yin shiru , Hajiya Nadiya ce ta furta “ Kana da matar da Zata riƙe ta ne? Sannan Soyayyar Aleena ba zan taɓa iya Tabbata da Jiki na ba , Sam ba zan Iya baka Aleena ba Afeef , nasan ka Sarai na kuma san Halin tsaurin ka , Aleena na yi mata Rainon jin daɗi dawowanka kana Neman birkita mun yarinya da tunanin ta baki Ɗaya ”. Ina ta rabuwa da kai da yi maka kawaicin baƙunta ”. Tsayawa Afeef yayi baki buɗe yana mamakin kalaman Mummy , A hankali ya fara tuno da Ranar farko da ba zai taɓa matasa da ita ba a rayuwarsa ta shigowar Aleena cikin rayuwar sa dana iyayen sa wanda a farko suka nuna bigire ma Al'amarin amma kuma a yanzu suke nuna ikon su fiye dashi akan Aleena”.


“A safiyar Alhamis wanda shine musabbabi kuma maƙasudin komai na Rayuwar Su ”. 

Gida ne mai cike da Annuri kowa har ma'aikata a wannan Rana farin ciki suke sakamakon Bikin da ake na Zagayowar shekarar Afeef , Tun daga farkon Dirning table har karshen sa da Wannan safiya shaƙe yake da cima iri da ban daban ”. Mummy Nadiya kuwa farin ciki sai kaiwa da komowa take yi wuya yasha gwala gwalai na kece Raini ”. Sai aikin kiran ƴan uwa da Abokan arziƙi take tare da Sanar masu da lokacin fara party . A hankali Yake saukowa kansa cikin Head Phone yana sauraren Waƙar Alan ”. Mummy bara naje na dawo ”. Muryar sa ya katse Mummy wacce cikin sauri ta katse Wayar nata tare da cewa “ Afeef nan da Ɗan lokaci fa Zamu fara amsar baƙi ina kuma zaka je da Wannan..... Sorry Mum , ba zan dauki lokaci ba zan dawo ”. Kamin Ta yi wata magana ne Maleek ya shigo da Abokanan Su Hafiz da Lukman wannan yasa Afeef cewa “ Mummy sai mun dawo ’. Bin su da ido Tayi har suka fice kana daga bisani ta juya tana Nufar wurin masu Aikin kitchen ”. 

Mamaki ne ya kamani ganin a wannan lokacin dukan su basu haura 17 ba sai ƙasa da haka amma Moton gidan Afeef ya ɗauka suna ficewa da Abokan sa ”. Happy birthday Bro! Suka furta tare da kallon Afeef wanda yayi murmushi yana cewa “ Na gode ”. Yanzu ina muka yi for the celebration ? Lukman y furta yana murmushi tare da kallon fuskokin su duka ”. Murmushi Afeef shima yayi kana yace “ Kawai yau ina so mu shiga Wata Ƙauye ne mai kamar jeji wanda babu mutane sai tsiraru ka fahimta dai , Wurin da babu Hayaniya sosai hope You get me well? ”. Shiru duka suka yi kana Malik cike da shaƙiyanci yace “ Oh Yes ,sai dai cikin mu babu wanda yasan irin wannan ƙauye , imfact bamu san hanyar ƙauye ba ma ,don babu wanda ya taɓa zuwa a cikin mu ”. Hafiz ne ya karɓe zancen da cewa “ Kawai muyi ta tafiya mu miƙe kamar zamu bar gari mu hau babban Titi mufa masu basira ne”. Dariya suka saka a tare kana suce ƙwarai ka kawo shawara ”. Haka ko suka yi gudu kawai suke shararawa tun suna gari har suka fara fita wajen garin , daga haka suka fara Wuce hanya babu gidaje kusan Awa hudu suna tafiya kana su isa Wata ƙaramar ƙauye da suka gani daga Gyefe dakatawa suka yi da tafiyar yayin da Afeef ya fito yana bin hanyar da kallo ”. 


A hankali ya fara kutsa kan sa yayin da Hafiz dan gayu ya tsaya baya yana cewa “ Gaskiya nidai ina da ga nan , Kuyi gaba ina jiran ku , ba Zanje na shaƙi kwalara ba .... Kece wa da Dariya Lukman yayi yana cewa “ Mu da muke tunanin Celebration a....ya isa don Allah idan ba zaku ba Ni na wuce , ku baku san kusan life experience? A'a Haba ku taho muje kai ka tsaya kayi mana Gadin mota”. Afeef ya furta yana ƙare shigewa cikin hanyar wanda Gyefe da Gyefe gonaki ne ”. Biyo bayan shi Lukman yayi haka Abdul Maleek ....Wow Maleek wurin nan yayi kyau sosai , Dama haka ake shukar Masara kenan? Eh mana baka ganin hoton a littafai? Lukman ya amshe maganar ”. Cike da Rashin tsoro suke nusa cikin gonar kamin su fara shiga ƙauyen ”. Muryar Afeef ne ya katse su yana cewa “ Ina zuwa , Dole na ciro masarar nan guda Ɗaya ”. Owk Suka furta suna juyawa tare da jiran sa amma idanun su duka na akan Gidajen kauyen da suke iya hangowa can nesa ”.  


.....Shi kam Afeef ciro masarar yayi yana kokarin ciro ta biyu ne yaji muryar mace cike da Rauni a bayan sa Wanda sai da yaji tsoro , Bawan ALLAH ka taimake Ni. Da sauri ya juyo yana kallon ta kana ya sauke idanun sa akan Kunshin abin dake hannun ta ”. Muryar Afeef na Rawa ya furta “ Who are u? Ke ...k wacece? ”. Motsa bakin ta tayi da yake karkarwa idanun ta na zubda Hawaye , Kurum sai ta miƙo masa Jaririya wacce take tsumma da Alama ko wanke ta ba'a yi ba ”. Tirƙashi🤔💃🏻 mu tara a page 9 kar ku manta free page yana daf da karewa ga masu buƙata regular group ₦500 vip group ₦1000 SPC payment ₦1500 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post