Rainonta Zanyi Page 9 Complete

Abokiyar Hira Novels Audio free

RAINONTA ZANYI🔞

ROMANTIC LOVE STORY

9.

*FREE PAGE ZAI ƘARE A PAGE 10 GA MASU BUƘATAR SHIGA GROUP NA WANNAN LITTAFI REGULAR PAYMENT ₦500 VIP GROUP ₦1000 SPC PAYMENT ₦1500 VIA 6037312299 MOHAMMED AISHA KEYSTONE BANK KO KATIN MTN TA WANNAN NUMBER 08081202932.*


Ka taimake Ni ka taimaki wannan yarinyar dan Girman ALLAH kayi nesa da Ita da Wannan ahali da kuma wannan Rayuwa .....“Afeef Afeef..!! Muryar Mummy ya katse shi wanda hakan yayi sanadiyar dawowan sa daga Duniyar tuna Bayan da ya lula ”. Na'am Mummy ”. Afeef kayi haƙuri da duk abin da ka gani game da Aleena , nice wacce nayi kuskuren bata irin wannan Rainon wanda soyayyar ta ba zai barni na.....Ba komai Mummy , zan kwanta yanzu Sai da Safe...yayi maganar yana katse ta tare da Nufar ƙayataccen Gadon sa yana faɗawa tare Jan blanket mai laushin gaske ”. Ganin haka yasa mum Nadiyya ja baya tana Kai hannun ta ga switch tare da kashe masa Hasken Ɗakin kana ta juyo tana ficewa tare da Nufar Bedroom ɗin Aleena don ta sata barci ,zuciyar Hajiya Nadiya bugawa yake da karfi da karfi tabbas tsoro ne fal ranta bisa ga kiran da Ya ɓullo daga Ɓangaren Hajiya Kaka da zuri'ar baki Ɗaya ”. Tsayawa tayi a jikin ƙofan Bedroom ɗin Aleena tana Tunani mai zurfi tabbas Abu Ɗaya take tunani wanda kuma ba zata iya jura ba shine Cin mutuncin Wannan zuri'a ga Aleena , tabbas takuma san za'a yi shi , kar suyi yunƙurin sanar da Yarinya Abin da bata taɓa sanin sa ba , Tana kallona matsayin Mahaifiyar ta biological mother , sannan Daddy mahaifinta kar suyi yunƙurin tarwatsa mun Ƙwaƙwalwar yarinya ƙarama ba zan iya jura ba , Aleena bata da laifi ,Afeeef shine mai laifi don haka komai ya sauka a kan sa ne ba Aleenah ta ba ”. 


Mummy Mummy !! Muryar Aleena ya katse ta wacce take daga ciki , da Sauri Hajiya Nadiya ta murɗa Handle Door ɗin tana shiga tare da ƙaƙaro murmushin dole bisa saman fuskar ta ”. Baby na Ashe ba kiyi barci ba?” . Why are you standing there? Aleena tayi maganar tana kallon Mummy dake ƙarisowa tare da zama kusa da ita ”. Sorry dear, na ɗauka kinyi barci ne kuma bana Son nayi motsi ki tashi ”. Rufe manyan idanun ta tayi kana ta buɗe su tare da kai hannun ta tana riƙo hannun Hajiya Nadiya a sannan tace“ No, ban taɓa barci ba tare da naji jikina jikin ba Mummy , i love You mum”. Murmushi Hajiya Nadiya tayi kana tace “ I love You so much baby na , ya akayi kika ji tsayuwa ta ?”. Murmushi Aleena tayi wanda sai da hushiryar ta suka bayyana kana tace “ Ƙamshin ki na daban ne Mummy na ”. Saurin rungume ta Mummy tayi tare da shafa bayan ta a hankali ƙwallahh na ciko mata ido , cikin sauri ta mayar da Hawayen ta , Mummy Bara nayi barci da Wuri cox gobe zamu je Gidan Grandma itace mahaifiyar Daddy ko?”. Gyaɗa mata kai Hajiya Nadiya tayi ba tare da tace komai ba ”. Shiru Aleena tayi tana kallon Fuskar Hajiya Nadiyya kana tace “ Mummy menene? Kaman bakya farin ciki ?”. Murmushin dole Hajiya Nadiya tayi kana tace “ Ina farin ciki , yi Addu'a ayi barci kuma mai Daɗi ”. Ok mum kiss😘 me ...uhmmm mum tayi kissing Saman Goshin ta tare da furta “ Good night dear ”. 

**

Babban Falon Hajiya Kaka duka familyn ne cike ƴaƴa da jikoki, tun kamin Hajiya tayi magana tuni kowa yasan labarin komai da kuma abin da ya tara kowa wato dalilin kiran nan na Hajiya Kaka ”.  Ƙosassun hajiyoyi kake gani ko wacce tasha gayu na garari, haɗuwan nuna kuɗi da ƙudi , ko Wada kalon nata izzar da mulkin tare da ji da Izzar kuɗi ”.  Cike da Sarganta irin ta ƴaƴan boko Nasreen ta dubi Honorable dake zaune kamin ta kalli Prof Sulaiman tana cewa “ Oh wai har yanzu Aƙwai sauran wanda ake jira basu iso ba? Time has already done....but sun bar mu muna jira”.  Kallon ta duka sukayi kamin Ruƙayya ta furta “ Ai wanda basa nan da yawa , Sanin kan ki ne Akwai Uncle's din mu da cousins wanda basa kasar nan meeting din ma sai dai a basu labari , yanzu familyn Daddy Abdu ne kaɗai muke jira Kuma suma nasan suna Hanya ”. Kallon kallo aka hau yi tsakanin Nasreen da Ruƙayya wanda a karshe ko wacce ta watsa ma yar uwar ta harara da kallon banza ”.  


Hajiya Suwaiba ne ta furta “ Hajiya ko a sake kiran su ne ? , A ji sun.... Kamin ta kare magana ne Suka ji sallamar Su Mummy wacce ta shigo Sanye cikin shiga ta alfarma ƙaryar me Raini duk cikin su .... Alhmdllh Kalmar da su Prof suka furta kenan tare da Ba Daddy hannu suna musabbabi da gaishe da juna kana Daddy ya gaisar da Hajiya wacce take amsawa jiki sanyaye , don ganin Aleena yasa ta tabbatar da Maganar Hajiya Suwaiba a yanzu . ALLAH sarki itakam Aleena Da bata san komai ba , Sai washe baki take a dole taga Ƴan Uwa. Shi kam Afeef cike da bakin rashin mutunci da miskilanci ya nemi guri ya zauna yana cika da batsewa.... Who are you? Nasreen ta katse Aleena dake kokarin zama cikin su cike da Wulakantarwa ”. Sorry Dear baki sanni ba ko? Sunana Aleenah Ni ƙanwar Uncle Afeef ce , Ga Mummy na nan ..... Enough waya faɗa Miki ke kina ɗaya daga cikin zuri'ar nan ? Baki da hankali yau zaki fita daga cikin mu ....” dammnnn”. Ƙirjin Aleena ya buga cike da rashin fahimta , take kallon Nasreen Wanda ruƙayya ta furta “ Nasreen Meke damunki ne? Prof ne cike da Rashin son ganin laifin yar sa ya furta “ Of course She's right, Ai bamu san ta cikin wannan a halin ba . Don haka Afeef dole a yau ya fitar mana da Wannan yarinya ya maida ta danginta don mu Bama riƙe bare ”. Tuni wuri aka fara Hayaniya don ko Muryar Hajiya kaka ba'a ji , duka familyn maganar su daya basa buƙatar ganin Aleenah a zuri'ar su ”. Kuka Mummy keyi tamkar ranta zai fita , babu abin da take faɗi sai kalmar hasbunnallahu wani'imal wakil ”. Shi kam Gogan ko a jikin sa ko ɗarrr duk wannan Hayaniya da ruwan da ya ɓallo amma be saka ko jin wani abu a zuciyar sa ba ”. Kamewa yayi tare da harɗe ƙafan sa ɗaya kan ɗaya ”. 


....Ƙallon Mummy Aleena tayi cikin hawaye Muryar ta na rawa haka jikin ta ,don bata taɓa ganin ƙiyayya ba a rayuwar ta sai soyayya da sauri ta rungume Hajiya Nadiya tana furta “ Mummy mu tafi Gida Tsoro nake ji , Mummy da gaske bakyace Mummy na ba? Uncle Afeeef tsinta na yayi kamar yanda ake tsintar Mage a hanya dama ana tsintar mutum Ni ma tsinta na aka yi ?”. No my baby I love you! Hajiya Nadiya ta furta tana rungume Aleena cikin matsanancin kuka da tashin hankali ”. Alh Abdu ne cikin ɓacin rai ya furta “ Aleeena ƴa tace! Koda dukan ku zaku ƙi ta ,Ni ina kaunar ta tun da Ni ne na Raine ta ”.....Baka isa ba , a yau sai kayi umarni da Afeeef ya tattara ta ya mayar da ita inda ya tsintota ”. Ɗagowa Aleena tayi tana bin Afeeef da kallon dama kaine ka tsince ni? ....Muryar Hajiya kaka ne ke wannan magana cike da Ba Daddy Umarni ,wanda sai a sannan Afeeef ya tanka da cewa “ take it easy Hajiya , Me yayi zafi , Daddy zai iya rabuwa da Aleenah and mummy ma da kowa haka , amma Afeeef har Abada ba zai rabu da Aleena ba , Alƙawari ne na dauka , Zan Rayu da Aleenah na rabu da kowa ”. Takawa yayi yana matsawa izuwa inda Mummy take kamin yace “ Taho Ki dawo Rainon Uncle Afeef, zaki zauna dani  Afeef?”.  Yayi maganar yana kallon Aleena wacce kamin tayi magana Muryar Alhaji Ahmed ya katse su yana furta “ Sai dai ka zaɓa ko mu iyayen ka duka da mahaifiyar ka ko wannan yarinyar mara Asali?”. Ɗago da lumsassun idanun sa yayi wanda suka rine izuwa ja kana ya saki murmushi yana furta “ Waya ce maka bata da Asali , Asalin ta shine Afeef Uncle Ahmad, Don haka na zaɓi Rainona , Na Dauki Aleenah RAINONTA ZANYI........to masu karatu mu tara a page 10 Wanda yake last free ma su buƙatar biyan kudin littafin mu Regular payment ₦500 vip group ₦1000 SPC payment ₦1500 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932....”#Mamanteddy”.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post