A yayin tattaunawarsa a cikin Shirin Ganin Talk Show, Auta Waziri ya Bayyana irin dangantakar dake tsakaninsa da Mommy Gombe inda Mutane da yawa na ɗaukar hakan a Matsayin Soyayya.
"Mommy Gombe Abokiyar aiki na ne ba soyayya mu ke yi ba, kawai zaman Mutun ci ce ne, wani lokaci mutane idan suka ga yadda alaƙar ku, irin kuna yawan video da mutum kawai mutanen gari sai su ɗauka shikenan ka zama saurayi da budurwa da mutum kuma alaƙa ce kawai ta masana'anta."
Duk a cikin shirin Ganin Talk Show, Auta Waziri ya yi bayanin yadda ya sami sunan Auta Waziri.
"Yadda na sami suna Auta waziri, da Farko dai ana kira na da Autan Naziru Kasancewar da waƙar sarauta nakeyi sosai na fi yin su da waƙoƙin Aure."
Ya ƙara da cewa "Yadda sunan kuma ya fara samo asali akwai wani Maigidana Zubairu Wazirin Dabai shi ya fara Autan Waziri kawai da naji daga nan ma kawai ai in ma koma Autan Wazirin kawai"
Dangane da wasu yan matsaloli da suka faru a baya inda wasu ke tunanin Auta Waziri waƙar Naziru yake hawa ba nashi ba.
"Lokacin Sarkin waƙa bai jima da Ya fara tashe, lokacin mutane basa iya banbance Muryar mu duk da dai ga banbancin nan a fili." Ina ji shi
"Hakan bai dace ba ganin irin wannan ba daidai bane ace suna yana wayan clashing da har za'a iya zuwa ayi amfani da shi wasu ma su ce kace kaza ko kaza ya faru shiyasa na maida sunan ya koma Auta Waziri."
"Ko a lokacin bana hawa waƙar Naziru saidai nayi waƙar aji kamar na shi, amma ko a lokacin nakan banbanta salon kiɗa, nakan ɗauki kiɗa mai sauti saboda shi lokacin yana amfani da gargajiya ne wanda sune asalin sarauta, lokacin anajin yanayin ne kawai yazo ɗaya amma za'a ce Auta Waziri kayi mana waƙa." Auta Waziri
"Matsalolin da ake yawan samu shine, wasu zasu zo su baka aiki kai baka san yadda suka tattauna da masu aiki ba zasu zo su ce Auta, ina so kayi min waƙa lokacin ma ban fito da logon Auta Waziri ba."
Ya bayyana cewa so da yawa mutane suna bashi waƙa amma zasu ce kada ya fadi sunan Da saboda wannan dalili "Da nake sakawa a farkon waƙata, so zasu ce Auta Waziri kayi mana waƙa amma dan Allah Bama sai ka sa suna ba, Ni a lokacin ban damu da nayi waƙa na sa suna na ba, sai mutum ya je yace Naziru ne kuma ba Naziru bane, so waɗannan abubuwan sun kawo issues za'a ce Auta anji kayi waƙa ance Naziru ne ko an kira Ni zan ce Ni bance Naziru ba ban fadi suna ba da sauran su."
