6️⃣4️⃣
DR SADEEQ GROUP UPDATE
👇👇👇👇👇👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM
💔❤️🔥DR SADEEQ❤️🔥💔
BOOK TWO
BY
NARNAH KANWAR SOJA
My 15Novel love, comedy drama
"Love is a flame that burns bright, even in the darkest night." ✨
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲
THANK YOU FOR UR CARE UMMU KULSUM U ARE ALWAYS IN MY MINE
MORNING UPDATE
ENJOY YOUR DAY
COMMENTS SECTION
👇👇👇👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/ErBzFgfrIhE9QWSOhld1g1
BUSSINES GROUP
👇👇👇👇👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/JjkU7xG4zcWIAvtWRgeFtT
NOVEL ELITE CHANNEL FOR MORE NOVEL'S
👇👇👇👇👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaGtQnP96H4UODNQaq35
WASHEGARI — 8:00am
Indo bata fito ba.
Har gidan ya gama motsawa, murya ɗaya ba a jiyo ba daga part ɗinta Hajiya Binta ta fito daga kitchen tana tattare mayafinta, ta ɗauki goran ruwa ta ta sha gaban Layla da Nazifa tana cewa, “Ke Layla, ke Nazifa, ku fito da wankin kaya wannan yarinyar mai juya-juya tun jiya bata fito ba.Wai ko uwarta ce zata mata aikinta , ta harari kofar dakin Indo.
“Kai! Har yau bata taso ba, shiigiyar yarinyar tun jiya tasan tana aiki Asabar da Lahadi ai .
Sai ta juyo ga Nazifa.
“Kayan Atika duk a haɗa mata da na Na’iba, ga na Layla suma a kawo—kinji Nazifa?”
Nazifa ce ta tsaya cak.
Ta tabe baki tana murmushi mara ƙarfi, ta ce a hankali “No Hajiya i’m okay.
Bani da kayan dirty.” Ba don ba ta da kaya ba—
a'a, tausayi Indo ya hanata shiga cikin wannan zalunci na wanke mountain of clothes na gida gaba ɗaya.
Nazifa yarinya ce shiru–shiru, marar hayaniya, marar son cutar da kowa, tafi gani latsa wayar ta , akan shiga harkar kowa a gidan
Mommy ta juyo da saurin tsaki.
“Nazifa ta sunkuyar da kai, ba tare da ta ce komai ba ta juya ta kama hanyar laundry—
amma zuciyarta cike da wani irin tsoro da mamaki Ina Indo? me yasa bata fito ba har yanzu? ko dai tana bacci...
A hankali, Nazifa ta buɗe ƙofar dakin Indo.
tana shirin cewa “Indo ki tashi ke fara wanki”
sai ta tsaya turus Indo kwance…
bargo a gefe, hijab ɗin sallah a gefe, idonta ja kamar mai kuka.
Jikinta duk ya ƙanƙame kamar wacce aka jefa a ruwaNazifa ta ƙaraso da sauri“Indo! Indo!”
Ta taɓa goshinta… zafi!
Sai kuma ta ja hijab ɗin Indo ta ɗan dago rigarta ɗan kadan— jiki ɓoro-ɓoro, jajaye kamar marks ɗin duka.
Nazifa ta dafa kirjinta “Astaghfirullah… wai me ya same ki? Indo wa ya miki haka??”
Tana girgiza ta, Indo ta buɗe ido rabi:
“Mmm… kai… ina ciwo, Dr …”
ta lumshe ido gaba ɗaya ta sake faɗawa bacci mai nauyi.
Nazifa cikin tashin hankali ta buɗe first aid box nata—ta dai-dai tunda tana karatun Nursing Sauri-sauri ta haɗa injection mai sauƙaƙa zafi Paracetamol IM, ta yi mata ta lullube Indo, tana share gumi da handkerchief.
sannan ta danna tawul mai ɗumi ta shafa kanta da wuyanta.
&&&&&&&&&&&&&&&&&&&&&
A gefe kuma Dr Sadeeq
ya fito daga wanka yana goge kansa da tawul, yana ƙoƙarin sake kirar Indo. Still switch off.
wayar tana kiran sa.
ya duba Office Call ya ɗaga da ɗan tsawa:
“Emergency for what on SUNDAY??
Stop kidding me!”
Sai suka tura schedule Emergency consultants meeting — 9:00am
Sent: 11:58pm yesterday.
Sadeeq ya riƙe kansa:
“Damn… I slept off.” Ya janyo ash-colored jamfa ya sanya zuciyarsa tunani guda ɗaya “Indo bata da lafiya ne?”
Amma lokaci bai jira shi ba, dole ya fita ya bar gidan da tashin hankali a ransa.
Back to Nazifa
Nazifa ta zauna a gefen Indo tana tsare ta da ido, ta ga hawayen Indo sun fara yin ƙyalli a gefen kumatunta har cikin baccin zazzabi.
Nazifa ta rike hannunta ta ce a hankali:
“Indo… don Allah ki farka"
Babu amsa.
Sai numfarfashin Indo ya ƙara yin nauyi Nazifa ta rikice
“Idan Mommy ko Atika suka shigo nan… Indo zata mutu a wahala.”
Sai ta miƙe da sauri, ta bar dakin tana neman Hajiya Kaka, domin ita kaɗai ce zata iya ɗaukar Indo ta kare ta daga su Mommy da Atika.
Indo na kwance a gado, numfashinta sama-sama, jikinta duk zafi kamar ana ƙona ta a ciki.
Hawaye suna ƙoƙarin zubowa amma ƙarfinta ya ƙare.Nazifa na fita, zuciyarta cike da damuwa, sai wayarta ta yi ring ta duba — Hubby calling.
Nazifa ta tsaya, ta daure ta yi murmushi saboda tuntuni take jiran kiran nasa tun jiya.
Ta ƙarasa dakinta da sauri, ta rufe ƙofa ta kwanta a gado tana magana da shi cikin shagwaɓa.
Daga hankali ta manta da abinda ya faru da Indo
A Bangaren Mommy
Mommy ta dade tana jiran Indo ta fito don aikin gidan — bata fito ba kamar yadda ta saba, zuciyarta ta fara huci ta nufi dakin Indo da sauri, ta tura ƙofar sai taga…
Indo kwance tana sauke numfashi
Mommy ta tsaya kaɗan tana kallonta kamar ta ga abu mai ban haushi, ba damuwa ko tausayi a fuskarta ta ɗaga pillow ɗin Indo ta kwada mata ƙwAAF! a kirji Indo ta firgice ta buɗe ido da ƙyar, tana hargitse jikin zazzabi , Mommy ta ɗaga gira cikin tsawa “Don ubanki wa zai miki wankin week ɗin nan!?”
Indo ta ɗaga hannu da ƙyar tana neman magana “Mo… Mommy… banda lafiya please…”Mommy ta katse ta da wani irin mugun tsaki:
“Lafiya? Lafiya ta ubanki!?
Ina ruwa na ke mutu! Idan kinason ruwan a rana sai kin tashi ki wanke kayan nan!”
Ta zare pillow ɗin daga gadon, ta jefa shi gefe, tana kallon Indo kamar wata baiwar da ba ta da wata kima Indo ta sake buɗe baki cikin rawa da jiri “Mommy… Don Allah… jiki na… zafi yake…” Mommy ta ɗaga hannu tana bubbuga belt “Idan baki tashi ba… wallahi sai na karya ki yau tun da kika zo wannan gidan kin zama kwadayi da rainin hankali!”
Indo ta yi ƙoƙarin tashi amma kafafuwanta sun kasa, ta koma ta zauna tana hawaye masu zafi “Mommy… zan tashi… kar ki dake na amma jiki nayi zazzabi… na kasa gani—”
Mommy ta ɗaga belt ɗin zata buge ta…
Sai kawai kofa ta bude da ƙarfi — KAKA!!!
“Me zangani??” Kaka Rabi ta hargitsa muryarta tana shigowa dakin. “Wani irin zalunci ne ake nunawa yarinya? Ashe har da duka take, Zainabu? Baiwar Allah ta yi laifi kika dake ta?”
Mommy na ganin Kaka ta ɗaga kanta ta cikin masifa, cikin sauri ta juya ta fice daga ɗakin tana riƙe kirji kamar wacce aka kama da laifi.
Kaka ta ƙarasa kan gadan Indo ta daga bargon ta shafa goshinta—ta firgita. Zafi jau jau kamar an saka mata wuta nan take ta fara kwala kira da ƙarfi
“Ku zo nan! Ku zo gaba ɗaya, kafin in karya muku gidan nan!”
A parlour kuwa, kowa ya hallara cikin ruɗu. Kaka ta tsaya tsakiyar falon kamar alƙali a kotu, ta fara zagi cikin zafin rai:
“Marasa kunya! Marasa tarbiyya! Ba wai Indo ce kawai ba—daga ku har uwayenku! Duka yarinya mara lafiya? Ashe ita ce muguntar da kuke ɓoyewa?”
Nazifa ta tsaya a gefe idanu cike da hawaye tace:
“Wallahi Kaka Indo ba lafiya na tafi ne nagayamiki na ɗauko wayarta ta Amman… da na dawo sai naga Mommy na dukanta.”
Kaka ta runtse idanu tana girgiza kai:
“Zainabu! Don rashin imani kina dukan yarinya? To wallahi yau sai kin bata haƙuri. Idan kuma kika ƙi — kwanan ki a wannan gidan ya ƙare.”
Gidan ya yi shiru, zuciya kowa na bugawa… Indo kuwa tana can a bayan su tana rawar zazzabi kamar za ta suma........
.jpg)