6️⃣3️⃣
DR SADEEQ GROUP UPDATE
👇👇👇👇👇👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM
💔❤️🔥DR SADEEQ❤️🔥💔
BOOK TWO
BY
NARNAH KANWAR SOJA
My 15Novel love, comedy drama
"Love is a flame that burns bright, even in the darkest night." ✨
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲
THANK YOU FOR UR CARE UMMU KULSUM U ARE ALWAYS IN MY MINE
NIGHT UPDATE
ENJOY YOUR NIGHT
COMMENTS SECTION
👇👇👇👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/ErBzFgfrIhE9QWSOhld1g1
BUSSINES GROUP
👇👇👇👇👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/JjkU7xG4zcWIAvtWRgeFtT
NOVEL ELITE CHANNEL FOR MORE NOVEL'S
👇👇👇👇👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaGtQnP96H4UODNQaq35
Mommy tunda ta ji kalmar “Kaka tazo”,
jikin ta ya fara rawa kamar wacce aka ɗora a fan ɗin harmattan “Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un… yau ma Kaka? a nan? kuma ni ban sani ba?”
Ta dafe kirji, ta fara takawa hankali babu natsuwa— domin tuni ta san , Idan Kaka taxo, gida ba zama, Gida ba dariya gida faɗa ce da masifa.
Da gaggawa Mommy ta wuce part ɗin Hajiya Binta. Ko sallama bata tsaya yi ba ta fara knocking jiƙam-jiƙam har sai da ta tura ƙofar ta shiga parlour ɗin.
A can Hajiya Binta na zaune saman doguwar kujera tana latsa wayarta kamar ba tasan duniya ba ta daga kai a hankali ta hango Mommy ,ta miƙe fuska babu alamar mamaki “Lafiya? Zaki shigo min part haka? ko kishin ya motsa ne?”
Mommy ta yi wuf zuwa gabanta tana haki kamar wacce ta yi gudu
“Binta ki daina wanan… ba lokacin gardama muke ciki ba wallahi.
Na ga Sadeeq yace ”
Hajiya Binta ta katse ta cikin zazzafar raini:
“To sai me?Sadeeq ai yaron ke ne ina ruwa na da abinda zai ce
Ko kina zaton zai yi boye-boye da abinda ya kwaso gidan nan ne ?”
Mommy ta girgiza kai da sauri ta matso sosai.
“Ba wancan nake nufi ba, Binta…
Ashe baki gane matsalar gidan nan ta dawo ba?”Hajiya Binta ta ɗaga gira biyu cikin tambaya Mommy ta furta a hankali cikin rawar murya “HAJIYA KAKA… tana gidan nan yanzu.”
Shiru ya cika falon.
Hajiya Binta ta tsaya kamar statue.
Wayarta ta faɗi saman carpet ba tare da ta sani ba ta buɗe baki a hankali:
“Kaka? Nan? A yau?
Ke kin tabbata?”Mommy ta gyada kai:
“Na gani da idona… tana nan a part nata"
Wallahi jimawa kaɗan za ta tsaya mana faɗa daga ƙofar part ɗinmu har zuwa naku.
Idan bata ga tarkace ba sai ta ga tarin rashin tarbiyya.”
Hajiya Binta ta miƙe tsaye daga kujera cikin razana kamar wacce aka kira asibiti.
“Innalillahi! azumi fa da saura me ya dawo da ita ”
Ta dubi Mommy da idon damuwa:
“To me za mu yi yanzu?
Kaka idan ta shiga fa daki ɗaya, ta ga wani ba daidai ba— Allah ya kiyaye!”Mommy ta dafe goshinta:
“Sai mu shirya"
Hajiya Binta ta yi caraf “Bata da tausayi ko kaɗan Allah ya taimaka kawai"
Mommy ta yi saurin rintse ido.
“Bari mu haɗu mu tsara… kafin Kaka ta iso takan mu”
############₦₦₦₦₦₦₦₦₦₦₦₦₦₦
Tunda Indo ta shiga ɗaki, ta tsaya bakin ƙofa ta fashe da kuka , kukan ya fito daga ƙasan ranta — kuka mai nauyin ɓacin rai da zafin ciwo, wanda ko iska ba za ta iya ɓoyansa ba.
kukan ya ja mata bacci, baccin wahala, baccin mara ƙarfi, sai kiran sallar Magariba ya tashe ta kamar ana hira cikin ranta ta buɗe idonta a hankali…
Duniya ta juya mata ciwo ya turnuƙe kanta kamar ana bugun gangar yaki Nan take ta tuna “Kaka tazo… Allah na, banje ba tunda da rana ”
Ta tashi da ƙyar— kamar wacce aka ɗaure da sarka ta shiga toilet ta kama ruwan zafi, ta zuba a cup mai feshin turare, ta wanke fuskarta a hankali domin ciwon ya yi mata zafi.
Sai ta yi wankan jiki da sauran ruwan zafi, tana jin sanyi ya ɗan ratsa ta kaɗan ta fito, ta ɗaura alwala, ta tsaya ta yi sallah.
Amma da ta kai ruku’u, kanta ya yi mugun sarawa, numfashinta ya ɗauke, jikinta ya fara kakkarwa kamar mai sanyi da zazzabi.
A lokacin da ta jingina da gado tana neman kuzari, zuciyarta ta tsinke da kalaman da suka fito da kanta:
“Idan ban je nayi wanki ba… Hajiya Binta fa?
Asabar da Lahadi ita ke tura ni wanki…
Kuma ba tare da sanin Dr ba.”
Ta ɗauki hanci ta sauke numfashi mai nauyi—
Zuciyarta ta ji tsoro, ga ciwo, ga gajiya, ga rashin jin daɗi da ta yi sujjada a raka’a ta biyu, ƙarfin jikinta ya ƙare ta sake kwanciya a gefen sallayar, tana jin jiki ya daina zama nata.
Ciwon kanta ya ƙaru sosai kakkarwarta ta tsananta hannunta ya fara rawar sanyi, idonta na kafe wa ta rumtse idonta a hankali…
Ta tuna da Mama… yadda take shafa mata kai idan tana fama da zazzabi.
Tunanin Mama ya yi mata ciwo fiye da komai.
Sai wasu sirarran hawaye suka fara zubo mata — masu ɗumi, masu zafi, masu ɗauke da nauyin shekaru.
Ta yi ƙoƙarin juyawa, amma jikinta yaki.
Idonta ya rufe a hankali kamar bacci mai zafi yana jan ta ƙasa.
Bacci ya kwashe ta…
Bacci mai cike da zazzabi da kuka da yunwa—
Baccin da idan Dr Sadeeq ya gan ta,
zai san ba komai bane. Indo tana cikin zazzabi mai hatsari.
&&&&&&&&&&&&&&&&&&&-&&&&&&&&&&&&
Dr Sadeeq ya fito daga wanka karo na ba adadi tun bayan Magariba zuciyarsa cike take da wani irin damuwa mai nauyi—duk lokacin da ya tuna yadda Indo ta yi tafiya kamar mai jin ciwo.
Ya ɗauki wayarsa ya danna lambar ta.
Ringing Ringing babu ɗauka ya sake kira Ringing, still babu amsa ,ya ɗan tsaya ya ɗaga gira, ya sake kiran karo na uku—
Kafin wayar ta wuntsule da sauti:
“Switched Off.”
Ya tsaya cak hannunsa ya sauka a hankali daga ainihin wayar, zuciyarsa na ruguza da tambayoyi, ta kwanta?
ta yi bacci? ko dai bata da lafiya?
ko ciwon cikin ta ne ya dawo ? but yanzu ai farkon watan ne , Ita kuma sai end of the month ko wani abu ya faru mata tun safe?
cikin hanzari ya fita zuwa corridor domin duba ta da kansa.
Sai dai kafin ya karasa part ɗin nata, ya ji muryoyin su Mommy da Hajiya Binta a parlour suna magana, yanda suka je suka gaida Kaka da banzan halin da ta musu ,suna mayar da zancen cikin alhini da neman mafita
Ya janye hankalinsa daga motsinsu, ya koma part dinsa yana shiga bedroom, ya ajiye wayar, ya dafe goshinsa duk jikinsa ya yi sanyi da tunani Indo bata ɗauka.
Wayarta kuma ta kashe.
Ta yi sallah, ko ta kwanta?
Ko dai bata da lafiya?
Ya zauna kan gado, ya jingina da katifa cikin damuwa wani gajeren numfashi ya saki.
Da niyyar ya sake kallo wajen nata anjima, sai ya kwanta baccin gajiya da damuwa suka ɗaukesa tun kafin ya rufe ido gaba ɗaya.
Ya kwanta ba tare da ya san Indo na kwance tana fama da zazzabi mai zafi ba, bata da ƙarfi har ta kasa kiran taimako.............
.jpg)