6️⃣0️⃣
https://chat.whatsapp.com/JjkU7xG4zcWIAvtWRgeFtT
💔❤️🔥DR SADEEQ❤️🔥💔
BOOK TWO
BY
NARNAH KANWAR SOJA
My 15Novel love, comedy drama
"Love is a flame that burns bright, even in the darkest night." ✨
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲
THANK YOU FOR UR CARE UMMU KULSUM U ARE ALWAYS IN MY MINE
NIGHT UPDATE
Indo na kwance lumshe cikin baccin da ya yi mata nauyi, tunanin daren jiya da Dr Balarabe yana zagaye a cikin zuciyarta kamar waka mai daɗi.
Sanyi ne kaɗai yake ratsa dakin… amma ba irin wanda fankar ta ke hadawa ba wannan sanyi daban ne mai kaifi. Mai ban tsoro.
FUUUSHHHHHHH!!!
Ruwa mai sanyi kamar daga fridge ya zuba a kanta, ya wanke ta gaba ɗaya, ya ɗiga a kan matashin gadon har ya jike ƙasa. Indo ta tashi da firgici, ta dafe kirjinta tana haki kamar wacce aka tsallake da ita daga wani wuri.
“Subhanallah!! Me…?!”
Ta faɗa tana firgice tana share idonta amma hakan bai yi mata mamaki irin na ganin wace ta aikata hakan ba.
Atika.
Tsaye a ƙofar dakin, hannunta riƙe da gallon ruwan sanyi, cikin rigar sports ta fari da wando black—ta sha kwalliya kamar ta je shooting—fuskar ta cike da ƙiyayya da tsabar haushin Indo.
“Kaji tsinanniya,” ta furta da dariya mai kaifi.
“Kin yi bacci kamar ƙaramar akuya… Kina tunanin Dr zai dawo ya tashe ki ko?”
Indo ta kasa ko motsawa na ɗan lokaci, sanyi na ratsa ta, jikinta yana kakkarwa. Amma idanunta sun fara sauya ƙalar kuka da kuma ɓaci.
Atika ta matsa kusa da ita—ƙafarta ta taka ruwan da ya zube a ƙasa ta yi tsaki.
“Kin san yau Asabar ba kowa gidan nan. Mommy ta fita. Dr ya fita. Ni kuma…”
Ta runtse ido, ta ɗan ɗaga kai.
“…ni nake da damar koya miki waye ni, waye uwa, waye matar Dr da gaske.”
Indo ta haɗiye yawu, tana jin sanyi ya cakude da tsananin firgice,“Atika… me na yi miki?”
Atika ta zaro mata ido.
“Kin yi competing dani ne! Ke? Yarinyar da aka ɗauko daga ƙauye, ke kike tunanin Dr zai so, uban ina kuka je dashi jiya daga makaranta ?! Wallahi yau zan koya miki tarbiya!”
Ta janye pillow ɗin Indo, ta jefar.
Indo tayi ƙoƙarin miƙewa ta zauna, jikin ta harbawa yake, ruwan sanyi yana gangarowa daga gashinta zuwa ƙugunta. idan akwai abinda Indo ta tsana a rayuwar ta shine ruwa musamman ruwan wanka shi yasa na bata son wanka, kuma har yanzu bata wanka kullum kullum,amman dai da sauki kasancewar ta shigo hannun mai son tsabta..
Amma kafin ta yi magana, Atika ta rike hannunta ta murɗa! Indo ta saki ƙara, amma ba mai ji.
“Ba zaki ƙara kusantar Dr ba, kin ji ko?!” Atika ta huci kamar wacce ta sha hayaki.
Indo ta kalle ta tana koƙarin kwace hannun ta:
“Na gaya miki daga farko… kada ki zaga Mama ta! Wannan ne ya kawo rigimar ki dani… Yanzu kuma…”tayi ƙwafa Idanunta sun cika da ɗaci “…zan rama komai.”
Atika bata ba ta ko dama ta miƙe ba, ta daka tsalle kai tsaye ta zauna kan Indo, ta matse ta da ƙarfi kamar wacce ake riƙe mata zuciya ta fashe.
Indo ta yi ƙoƙarin zillewa, amma jikinta ya ɗan yi sanyi tun daga ruwan da aka kwarawa ta, ta zama marar ƙarfi.
“Ke ba kya ji?!” Atika ta huci tana ɗaga hannu sama ta sauke wa Indo.
“Wallahi yau sai na koya miki baƙin ciki!!”
TAAF!!
Wani mari ya sauka kan Indo har idonta ya ɗauke na ƴan seconds.
Ta riƙe kuncinta, hawaye ya cika mata fuska. ta kama hannun Atika tana ƙoƙarin kwacewa amma Atika tafi ta ƙarfi sosai.
ta juya hannunta ta murɗa, sai Indo ta yi ƙara don zafin ya ratsa mata gaba ɗaya.
Atika ta ci gaba da dukanta
ga gashi ta masu yawa da tsawo sun watse rigar baccin ta ta jike, ƙafafuwanta na rawa saboda tsoro da zafi, tayi wani mugun tsaki, ta damƙi hannun Indo ta murɗa shi gefe.
“…ke kike shiga min hanya? Ke?! Ƙaramar yar kaucen nan?!”
Indo ta tara ƙarfin zuciya ta ture Atika da gwiwa… amma har yanzu Atika na kan ta, tana damƙe ta kamar tana riƙe da wani abu da ta tsana.
Ruwan hawaye ya fara zuba daga idon Indo, ba don ta ji haushi ba, don ba ta saba wulakanci irin nan ba.
A hankali, da muryar kuka, Indo tace:
“Ki bar ni… ki barni wallahi… Ki bar ni Atika…”
Amma Atika ta ƙara matsa kanta, ta damƙi gashin Indo ta ja da ƙarfi:
“Ki daina kirana Atika! Ki kira ni matar Dr!!”
Indo ta kurma ƙaramar ƙara saboda zafin gashin da aka ja mata.
Ta ƙara ture hannun Atika amma Atika ta ture ta ƙasa Ɗakin ya cika da huci
da numfashin mutum biyuda zafin da Indo ba ta taɓa jin irinsaba
" Idan kunne yaji to gangan jiki ya tsira, dabara ya rage ga mai shiga rijiya yarinya" ta fita ta barta zube.. Indo ta zauna a gefen gado kamar wacce aka tattake mata zuciya da ƙafa.
Hawayen da ta share basu ƙarewa ba—
amma yanzu ba kuka bane… zafin zuci ne ke tsiyaya ta cikin idon ta.
Jikinta yana rawa kamar wacce ake tsoma cikin ruwan sanyi, ta ji dukkan gabobinta sun yi mata nauyi.
Ciwo a kai, ciwo a wuya, ciwo a baya, ga dukan da Atika ta yi mata na fisge mata ƙarfi gaba ɗaya ta ja numfashi mai nauyi
ta bar bathroom ,ta samu bargo ta rufe jikinta gaba ɗaya har ƙafarta, zazzabi na sauka mata kamar wuta a ƙarkashin fatar jiki A hankali ta miƙe ,ta sanya doguwar rigar pink;
amma rigar ma ta tsaya mata tamkar an zana ciwon da ke jikinta.
Ta tsaya gaban madubi fuskarta ta kumbura,
kuncinta jajur, ga zanen yatsun Atika a gefe—
kai ka ce hoton zalunci, dafe ƙirjin ta
ta runtse idonta da ƙarfi,
a ƙasan maƙoshinta ta furta a hankali, amma da ƙwarin zuciya:
“Indo ba ta mutu ba.
Indo ba zata taɓa zama wacce ake wulaƙanta ba.
Indo A’ishatu ce dan anyi duniya da lahira don Manzo…”
“…To ke Atika, sai kin san kin taɓa A'ishatu Indo wallahi sai kin koya wa zuciyarki nadama.”
Ta share guntun hawaye.
Ta gyara dakin kamar wacce taje yaƙi ta dawo, tana ƙoƙarin kwashe duk lalata, tana maida lamura tsaf.
Ta tattara ta gyara shimfiɗa, ta share gashin da ya zube a ƙasa.
Amma zuciya?
Zuciyar ta na rawa kamar ana hura wuta a ƙarƙashinta Ta zauna ta jingina da bango
ta lullube jikinta da bargon,
ta lumshe ido, zuciyarta na fadin:
“Sai na mike.
Sai na dawo karfafa.
Sai ki gane Atika… cewa Indo ba yar aikin kauye ce kawai ba.
Indo ce zabin Dr Balarabe.”Idonta ta rufe a hankali jiki na rawa zazzabi na hawa
amma zuciyarta cike da ƙudiri.........
BE READY
