6️⃣1️⃣
https://chat.whatsapp.com/JjkU7xG4zcWIAvtWRgeFtT
💔❤️🔥DR SADEEQ❤️🔥💔
BOOK TWO
BY
NARNAH KANWAR SOJA
My 15Novel love, comedy drama
"Love is a flame that burns bright, even in the darkest night." ✨
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲
THANK YOU FOR UR CARE UMMU KULSUM U ARE ALWAYS IN MY MINE
MORNING UPDATE
ENJOY YOUR DAY
A hankali Indo ta fito saboda yunwa ta kama ta, jikinta kuma yana ta zafi kamar ana hura mata wuta daga ciki. Yayin da ta sauko daga step, ta tsaya cak.
A gabanta, wata tsohuwa farar mace ce zaune. Tana da manyan glasses a idonta, tana sanye da atamfa mai tsada da dinkin buba, ta narke a kujerar ta, ƙafa ɗaya kan ɗaya, tana tauna goro kamar wata sarauniya.
Tsohuwa ce kyakkyawa, tsaf-tsaf, tana rike da sanda — amma ba ta kama da mai rauni ba.
Tsaf kamar Dr. Balarabe!
Indo ta lumshe ido tana dubanta. Tabbas akwai kama… har ranta ya buga.
A hankali ta matsa gaba ta ce:
"Kaka… barka da rana."
Tsohuwar ta ja goro ta cire glass ɗinta kadan, ta zuba mata ido sama da ƙasa.
"To barka, yarinya. Ke kuma wacce ce? Allah dai ya sa ba dangin su Binta ba… nace!"
Indo ta yi ƙoƙarin yin dariya — dariyar nan da ake ji akwai tsoro a ciki.
"A’a Kaka, ba dangin kowa ba ne."
Kaka ta harare ta:
"Ke yarinya, banson rainin hankali. Bakiyi kama da danginmu ba, bakiyi kama da masu aikin gidan ba… Amma ki ce min wacce ce ke kafin na buga miki sanda nan!"
Indo ta yi dariya tana ja da baya kamar wacce aka ga kwai a takalmi:
"Kingaaa tsohuwa… ai bazaki iya bugun nan ba. Ina da kafa, kafin ki motsa ni tun daga nan na toshe ƙofa miki! Ni ba dangin kowa ba ne, Dr Sadeeq ne ya kawo ni daga Yola… ƙauyen Modirre. Ke kuma wacce ce?"
Kaka ta gyara zama, ta murɗa fuska, ta kalli Indo sama da ƙasa tamkar mai tantance jakunkunan kasuwa.
"Ai kuwa yarinya, dole wannan kyawu haka sai mai asali. 'Yan gidan nan ba su gaya miki suna da KAKA ba ko? Tu ni ce nan — sillar kafuwar gidan nan!
Yaro na ne wannan gidan. Mai gidan shi, Mu’azzam. Sadeeq jikina ne na farko . Kuma zai dawo ya sameni mara kunya tunda ya manta dani ya daina zuwa a duk wata "
Indo ta fashe da dariyar da ta gigita kanta — dariyar da taji ta fita daga zuciya kafin ta sarara.
"Kaka rigimar ke kin yi kama da sabuwar budurwa wallahi. Hatta sanda kina riketa kamar za ki yi dambe da ni!"
Kaka ta ɗaga sanda ta nuna ta , "Ke! Wallahi idan nayi aiki da ke sai kin gane tsohuwa bata tsufa a zuciya! Ina jin rigimar mutane tun kafin a haife ki!"
Indo ta ɗauke kai tana dariya amma da sauri ta kama ciki tana tintsirewa da zafi.
Kaka ta tsuke fuska "Yarinya meye haka? Kina dariya kina karkarwa? kinga kamar mai yunwa?"
Indo ta lumshe ido, tana ƙoƙarin tsayuwa daidai "Eh… yunwa ce kawai Kaka."
Kaka tayi tsalle daga kujerarta fiye da yadda ake tsammani daga mace mai shekaru:
"To ai me kika jira? A gidan nan ace yunwa a Zo ki shiga kitchen ki samu abinci ke nan! In ba haka ba sai ki fadi mana a nan gaban kofa, su zo su ce ni na tsorata ki nima kuma yunwa nakiji!"
Indo ta bita da mamaki — zuciyarta cike da sabuwar sha'awar ta da tsoron wannan tsohuwa mai zafi amma mai zuciya mai kyau....
Indo ta tsaya ta haɗe gira biyu, tana kallon Kaka wacce ta yi ƙwafa ta kuma tauna goro da ƙarfi kamar tana da wasa a rai.
“Kaka ai abinci anan kan dining table ake ajewa, bare na duba mana.
Ki yi zaman ki kar ki karya ƙafa kina sallati—”
Kaka ta ɗaga hannu da sauri kamar zata kai mata duka:
Kaka:
“Mara kunyar yarinya ce miki akai!
Ni nayi tsufa da bazan iya tafiya ba?
Ni nace abinci a nan sama ku kawo min!
Ku zuba nan tsakiyar ɗakin, in gani ko zan iya cin abincin naku!”
Ta harare Indo da idanu masu ƙarfi da ƙyashi, kamar ta ce: Ki sake min magana, ki ga me zan yi!
Indo ta kame dariya, amma bakin nata ya kasa zama lafiya
“Kaka, wallahi ki tsaya ki ji… idan na kawo miki abinci nan, Dr Sadeeq zai yi fushi—” Kaka ta tashi tsaye cak, sanda a hannu, ta turo baki gaba
“To ke! Ina ruwanki da fushin Sadeeq?
Ni ce uwarsa! Ni ce Kakarsa!
Ni ce na haifi wanda ya haifi wanda ya haife shi!Shi ni nake yi wa fushi, ba shi ba!”
Indo ta waiga gefe tana ɓoye dariya, sannan ta ce a hankali:
“To Kaka, ai kawai nace…"
Kaka ta katse ta da muryar tsiya:
“Ke ki yi shiru! Ki je ki kawo min abinci nan,
Idan ma baki zo da shi ba — To wallahi za ki san me ake kira da sannin tsohuwa!”
A zuciyar Indo kamar ta yi ihu da dariya ta fashe.Sai ta ɗaga hannu tayi sallama:
“Toh Kaka! Gobe ma zan kawo miki a saman gado idan kina so.”
Kaka ta yi murmushi irin na tsohuwar da ta san ta ci galaba
“Hakuri kenan.
Ai dole ku ji maganata — ni fa tsohuwa ce amma ba matsiyaciya ba!”
Indo ta ƙarasa dining table tana rarrafe saboda tsoron kar su Hajiya ko Atika su shigo su tarar da ita a wannan "ɗanyen aiki" da Kaka ta bata. Ta buɗe cooler ɗin pink, ƙamshin fried rice da stew ya cika gidan kamar restaurant.
Ta fara zubawa da kyau, ta ɗora ferfeson ƙafar saniya a gefe kamar wata chef. Ta ji kunya sosai — don a gidan nan fa ba wanda yake cin abinci a ƙasa.
Indo ta lumshe ido:
“Indai Hajiya Binta ta ganni… wallahi sai ta kashe ni.”
Ta ɗauko small carpet, ta shimfiɗa tsaf a tsakiyar ɗakin sai ta ɗaga kai ta kalli Kaka.
Kaka na jingine da sanda, tana kallon Indo kamar ta ga wata yarinya mai hankali ta farko a duniya.
Ta turo baki, ta yi tsaki
“Yauwa jikkata!
Kin fi yaran gidan nan hankali
Ai su zasu dawo su gan ni kamar a radu a gidan su.”
Indo ta kame dariya, amma tayi masa “phhhh” ta fashe.“Kaka wai kamar a radu?”
Kaka ta dafe ƙirji:
“Eh mana! Ni fa ba bare ba ce!
Ni ce sillar gidan nan! ubansu ya fito daga cikina.
Su suna ta girmamawa, ni kuma indai abinci ne — a gabana ake ajewa!”
Indo ta yi tsalle ta matsa gefe tana matse dariya
“Kaka wlh idan Hajiya ta shigo ta ganki a ƙasa kina cin abinci wallahi… zan gudu.”
Kaka ta wanke ta da harara:
“Karki gudu!
Ki zauna ki bani ruwa ki kuma zauna ki kalle ni — ko zan hadiye!”
Indo ta dafe ciki tana dariya har idonta suka ƙwalla.
Da sauri ta ajiye ruwa ta koma gefe tana kallo yayin da Kaka ta fara cin rice kamar wata baby da aka ragewa haƙuri bayan kwana biyu.
Sai Kaka ta ɗan ɗaga plate ɗin tace:
“Indo…
ki kirani Madam idan muna cin abinci.
Ku yaran yanzu baki san ladabi.”
Indo ta faɗi ƙasa tana dariya sosai har ta kusa zamewa.
Dr SADEEQ ya ƙaraso parlour cikin takun maza, jallabiya milk, gashin kansa ya yi tsari kamar wanda ya tashi daga dogon bacci. Fuskar sa akwai alamun azumi—kadan gajiya, kadan natsuwa.
Ya leƙa dakin, yana shirin zuwa dakin Indo kamar yadda ya saba, amma sai ya tsaya TURUS kamar mutum da aka dannawa pause.
Abin da ya gani ya buga masa brain ɗin gaba ɗaya.
Indo zaune a ƙasa, ta matse jikinta kamar wacce aka kamo tana cin abinci ta ɓoye.
Kaka kuwa — Queen of drama — tana nan zaune akan carpet, kafafuwanta a miƙe, tana kwasar rice kamar ‘yar shekara 16, tana jujjuya spoon kamar wacce ke cin abinci a gidanta.Kaka ta ɗago ta kalle shi kamar bata san uban gidan bane.
“Wai kai ne SADEEQ? Zo nan mana! Ka tsaya a bakin ƙofa kamar wanda ya ga kyanwa ta haifi kare !”
Indo kuwa ta saki plate ta durƙushe da sauri. Idonta ya cika da tsoro, jikinta na rawa. Ta fara tura kanta ƙasa kamar za ta ɓuya.
Dr SADEEQ ya dafe kai, idonsa ya sauka kan Indo—fuskarta kumbure, ta jiƙa kamar wacce aka watsa ruwa, ga wani expression da yake masa signaling cewa something is wrong.
Sai ya ƙaraso a hankali.
Dr SADEEQ, cikin muryar mamaki da tsanaki:
“Indo… me ke faruwa?
Why didn’t you pick my calls tun safe?”
Indo ta kafa kai ƙasa, ta haɗiye yawu, jikinta ya fara rawa.
Amma Kaka ce ta tare:
“Kai magana ban gama ba!
Na same ta a sama ta yi min welcome sosai.
Ke kuwa Indo ki saki jikinki ki ci abincin ki — duk wanda zai yi magana akan na zauna a ƙasa sai na daki shi da wannan sanda!”
Ta danna sandarta ƙasa TAK!
Dr SADEEQ ya yi shiru, ya ɗago ido ya kalli Indo sosai.
Ya matsa ya zauna a gabanta, ya kama hannunta da ta ɓoye ciki.
Yana ta duba fuskarta, yana ganin kumburin da ta ɓoye da powder.
Dr SADEEQ (cikin tausayi da shakku):
“Indo… waye ya miki wannan?
Me ya ɓata miki jiki? why are you shaking?”
Indo ta kurɓi numfashi, idanunta cike da hawaye, amma ta kafe tana kokarin dariya kamar ba komai.
“Ni… ni… ai ba komai sanyi ne kawai
“Indo… tell me the truth.”
Idonta ya gana da nasa...
