Dr. Sadiq Page 67 Complete by Nana Kanwar Soja

Dr. Sadiq Page 67 Complete

 6️⃣7️⃣

https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM   

💔❤️‍🔥DR SADEEQ❤️‍🔥💔

   BOOK TWO 

    BY

    NARNAH KANWAR SOJA 

My 15Novel love, comedy drama

"Love is a flame that burns bright, even in the darkest night." ✨

  💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

*(J.W.A)*

🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚


(🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲 

   MORNING UPDATE 

ENJOY YOUR DAY


    BUSSINES GROUP    

    👇👇👇👇👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/JjkU7xG4zcWIAvtWRgeFtT    


    COMMENTS SECTION 

   👇👇👇👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/ErBzFgfrIhE9QWSOhld1g1

   

 NOVEL ELITE  CHANNEL FOR MORE NOVEL'S 

    👇👇👇👇👇👇

 https://whatsapp.com/channel/0029VaGtQnP96H4UODNQaq35  


    

MOMMY TA KIRASA…


Bai jima da fitowa daga gida Kaka ba sai wayarsa ta fara ringing yana gani MOMMY ce zuciyarsa ta buga ya ɗaga a hankali:

 “Mommy, ina kwana…”bata tsaya ma sauraron gaisuwarsa ba ta fara magana a kausashe:

 “SADEEQ, ina baka umarni. Yarinyar nan Indo daga yau ban yarda kana kaita school kai ba driver ba ne. School bus zata dinga daukarta. wannan umarni ne, ba shawara ba.”

Kafin ya yi magana, ta katse wayar ya tsaya ya rasa me zai ce. Hannunsa ya ɗan yi sanyi. Wannan kalaman Mommy sun rada masa wani irin zafi. Tuni zuciyarsa ta fara tambaya:


 “Mommy saboda me? me ya faru? ko wani abu ta gani?”




A hargitse ya kira makarantar, ya sanar da su cewa daga gobe school bus ce zata dinga ɗaukar Indo. Ya biya kuɗin a bank app nan take. Ya kashe wayar yana jin kamar an kwashe masa wani abu daga zuciya.


Yana jingina da kujera idanu a rufe, zuciyarsa tana bugawa a hankali:


“Indo ta canza min lokaci ɗaya. Ba magana, ba kallona… yanzu ma Mommy ta saka hannu? Me Indo ta ji? Me take tunani? ko wani ya gaya mata magana, me yasa ban taɓa lira da cewa ana azabtar da ita da aiki ba ?”


Ransa ya ɗaure ya danna kansa da yatsa:

“Me yasa Indo ta juya min lokaci guda? me yasa bata taɓa gayyamin matsalar ba?”




Cikin zuciyarsa akwai tashin hankali, damuwa, da tsoron rasa ta, duk da ba su fara soyayyar da ake furtawa ba yana nan zaune shiru, sai kuma ya furta a hankali:

 “Indo… ki faɗa min kawai. Me ke damunki?”


    


    


Bayan kwana biyu tana fama da rauni da ciwo, yau ta tashi da wani sabon ƙarfi ta gyara ɗakin Kaka tsaf kamar wacce aka sa ido ta wanke ƙasa, ta shimfiɗa gado, ta share window — komai fes.


Sai ta koma ɗakinta ta shirya a hankali.

Ta saka uniform ɗinta mai tsabta, ta ɗaura ribbon ɗin kanta, ta feshe jikinta da turaren da ta fi so.

Duk da hakan idan aka kalli fuskarta za’a ga ta rame kaɗan — saboda damuwa da ciwon da ta sha.


Tana fitowa parlour zuciyarta na bugawa.

“Zai fito ya gan ni?”

“Ko zai ce min good morning kamar kullum?”

Ta tsaya kusa da kofa tana jiran motsin Dr Sadeeq a yau ma sai ta yi sa’a ya fito da kansa ya tura ta makaranta Amma shiru

Clock ɗin hannun ta,  ta fara bugawa kamar ana tsokane mata rai 8:00am ya kusa yi.


Ta sake kallon hallway — shiru.

Babu alamar footsteps dinsa, babu kayan aiki, babu muryarsa.Sai kawai ta ji hornnnn! hornnn! Ta firfito a guje zuwa gate School bus ce tsaye a gaban gate.


A nan zuciyarta ta buga ƙarfi:

 “Toh shi kenan… ba zai fita ya ga ni ba. Ba zai kaini ba.”Ta sauke numfashi mai nauyi.

Hawaye suka tsaya cak a idonta — ba zasu zubo ba, amma sun kunno kai.


Ta furta a ranta:

 “Wato yanzu saboda ya tsanani har bazai kaine makarantar ba kenan… sai dai school bus?” Ta runtse ido:

“Wato hakan ya tabbatar min yana son Atika. Ita bata so gani na tare dashi — shi ma yanzu ya biye mata.”


Ta kamo jakar makaranta da hannunta mai shaking.Kallon bus ɗin ta sake:

 “Kenan ban da amfani a zuciyarka, Dr Sadeeq… tunda abin da Atika tace yana faruwa.”Ta share idonta da sauri kada wani ya gani Sai kuma ta furta cikin zafi da ciwo a zuciya “To wallahi nima daga yau na fidda rai da kai.”

Ta fice daga kofa a hankali, ba hayaniya, ba kuka — amma ƙirjinta ya gama karyewa da  ta kusa shiga

Sai kawai taji wata kamshin turare ta biyo bayanta Atika.l

Ta fito daga mota kirar Jeep ta gidan su tana jingina da kofar. Ta saka dark glasses, ta cije leɓenta da murmushin mugunta Ta ce da wata murya mai cike da raini:

“Hmm… yau ma ai kin koma ‘bus students’ kenan Na ga Doctor ya gaji dake.”

Indo bata ji daɗin maganar ba, amma ta yi shiru Atika ta matso da murmushi mai zafi:

 “Kin ga dai, ni ban ce ba da kaina ba 

Ba wani ‘relationship’ a tsakanin ki da shi.

Ai tunda Mommy ta ce ba zai kara kaike  school ba… ƙarshe shi ma ya amince.”


Ta daga gira:

 “Dama duk bawan da ban so ya kusanci abinda nake so sai na cire shi.”

Indo ta ja numfashi mai zafi.

Ta rasa me zata ce.


Sai kawai ta shiga bus, ta zauna a gaban window ta rufe kofa ba tare da kallon Atika ba.



Indo tana sauka daga school bus bata ko waiwayo ba tana isa harabar makaranta, yaran sun fara rarrabuwa, amma ita a tsaye take kamar wacce bata da wurin zuwa.

Kamar kullum, ta san cewa yanzu tana jira  Ilham ta fito a tashi su tafi gida tare.

Amma yau Ilham ce ta fara cewa da tausayawa “Indo tunda gidanmu na  kusa, me zai hana mu tafi a  mota gidanmu?”


Indo ta yi murmushi, wanda a zahiri murmushi ne—amma a zuciya ciwo ne.

 “A’a Ilham… bakomai wallahi Bus zai dawo na jira shi kawai.”

Bata son shiga cikin wata mota da ba ji da gani ba—don tasan Dr bai gaya mata hakan ba 


Ilham ta gaishe ta ta wuce.


Bus ɗin makaranta ya ƙara horn kamar yana gaishewa, ya tattaka gaba ya wuce ya barta a ƙofar gidan su 

Indo ta tsaya tana kallon baya har ya ɓace.

Sai ta juya… ta kama wata hanya dabam.

Hanyar da ko sunan Dr Sadeeq baya zuwa ba. 

Wani ƙaramin plaza ne, akwai shago na madara, na kayayyaki, na kayan shafa, na saloon, da ƙaramin chemist a gefe.


Indo ta tsaya a bakin chemist ɗin tana jan numfashi kamar wacce ta yi gudu da tunani.


Tana shiga, Staff ɗin suka kalleta saboda uniform ɗin makaranta da yanayin fuskarta.

Ta ɗauko dubu ɗaya daga jakarta ta jingina a counter  “Dan Allah a bani maganin sa zawo.”

Pharmacist ɗaya ya zaro ido:

 “Maganin menene? Kashi ne yake wahala?”

Indo ta lumshe ido Cikin sanyin murya ta ce  “Eh Yau… sati biyu kenan bana iya kashi.

ko da nayi, sai na kwana da zafi.

Dan Allah a bani maganin da zai budeni.”

Suka dubeta da mamaki irin na "yarinya haka amma tana da wannan matsalar?"


Wani ya tambaya  “me kike ci? ko kina shan ruwa sosai?”

Indo ta gyada kai a hankali “Ina shan ruwa.

Amman ba komai… ku dai bani magani.”

Basu matsa mata ba.

Suka bata irin magungunan da ake haɗiyewa da na sha dake sauƙaƙa kashi.

Bata yi jinkiri ba ta saka a jakarta.

ta miƙa musu kuɗi suka ce a tausashe:

“Allah ya baki lafiya.”

Indo ta yi murmushi mai rauni—dariya ce amma ba farin ciki bane.


Tana fita daga chemist ɗin ta tsaya daga waje don ta daidaita uniform ɗinta.

Ta ji iska mai sanyi ta buga mata fuska, da ƙamshin rana ta safe.

A zuciyarta sai ta furta a hankali:

 “Ko ina gida zai fi makaranta yau.

Ko da ban da kowa… zan zauna kawai.”


Ta kama hanyar zuwa gidan su, tana tafiya da jakar makarantar da ta zama kamar jakar ƙunci.A zuciyarta, Dr Sadeeq zai tambaya:

“Ina ta shiga?”amma ta ɗaure:

 “Even idan ya tambaya… dama ba damuwata bace.”Ta wuce cikin shiru, tana jin nauyin zuciya fiye da nauyin jiki..........


    


    


    


    


    🤲 ADDU’A SHIGA SABUWAR SHEKARA 🤲


Ya Allah,

Muna shiga wannan sabuwar shekara ne da sunanka Al-Rahman, Al-Rahim.

Ka sanya ta zama shekarar alkhairi, salama da albarka a rayuwarmu.


Ya Allah,

Ka gafarta mana dukkan kura-kuranmu na shekarar da ta wuce,

Ka karɓi kyawawan ayyukanmu,

Ka gyara abin da muka ɓata da rahamarka.


Ya Allah,

Ka ba mu:


lafiya mai ɗorewa 🤍


natsuwar zuciya 🕊️


halal mai yalwa 💫


ilimi mai amfani 📖


imani mai ƙarfi 🌙



Ka kare mu daga:


bakin ciki,


tsoro,


cutar zuciya da ta jiki,


makircin mutane da shaidan.



Ya Allah,

Ka cika zukatanmu da haƙuri, yafiya da soyayya,

Ka sanya mu zama haske ga kanmu da wasu.


Idan akwai buri a zukatanmu,

Ka cika shi idan alkhairi ne,

Idan ba alkhairi ba ne,

Ka kawar mana da shi ka ba mu abin da ya fi alkhairi.


Ya Allah,

Ka sanya wannan shekara ta zama farko na farin ciki, nasara da kusanci da Kai.

Ka sa mu gama ta da Imani kuma ka karɓe mu da Rahama.


🤲 Amin Ya Rabbal ‘Alamin 🤲

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post