7️⃣0️⃣
https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM
💔❤️🔥DR SADEEQ❤️🔥💔
BOOK TWO
BY
NARNAH KANWAR SOJA
My 15Novel love, comedy drama
"Love is a flame that burns bright, even in the darkest night." ✨
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲
MORNING UPDATE
ENJOY YOUR DAY
BUSSINES GROUP
👇👇👇👇👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/JjkU7xG4zcWIAvtWRgeFtT
COMMENTS SECTION
👇👇👇👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/ErBzFgfrIhE9QWSOhld1g1
NOVEL ELITE
CHANNEL FOR MORE NOVEL'S
👇👇👇👇👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaGtQnP96H4UODNQaq35
Dr Sadeeq ya shiga office kai tsaye, idonsa cike da ɓacin rai da maganganun dewa a zuciyarsa wanda ba lallai ya iya fitowa ya faɗa gaba ɗaya saboda rashin son magana ,Ya ɗaga wayar ya kira Atika a gaggauce. tana ɗauka ta shigo office nasa fuskar ta yaye jaaa sosai tana mata ƙaiƙaye ta wanke ta wanke Amman a banza har ya tara tunanin ko lotion nata ko powder ta ne yayi expired sai ga kifar Dr SADEEQ a wanan lokacin haka taso a ya mutse, yana ganin ta ya miƙi cikin ta da jijjiyar waya
“Ki saurara, Atika… ki tsaya lafiya. Kada ki taɓa Indo ko da dai kadan,” ya yi ƙarfi da murya mai tsanani. “Wallahi, idan kika sake taɓa Indo, duk abin da ya faru, to kisani kika nema kuma ba zan bari wani ya shiga tsakani ba kin ji?”
Atika ta girgiza kai, zuciyarta na bugawa da sauri, tana jin tsananin tsoro. da ganin matukar fusata akan fuskar sa
Dr Sadeeq ya ja dogon numfashi, ya ƙara da cewa:
“Ke kuma, ke tattara kayanki ke bar gida nan. Ban son ki ko kaɗan a wannan gida yanzu. Ki gane? Ba zan sake faɗa miki sau biyu ba i already hate u ke tafe ki samu wani namjin why only me .”
Atika ta yi shiru, ta sani cewa wannan gargaɗi ne daga mutum mai iko da tsanani, wanda ba zai yi wasa da wani abu ba. Ta ɗan ɗauke kai, sannan ta rage murya ta ce “To… na ji but wallahi Dr i love u duk wulakanci da zakamin zan gayyama cewa inason ka kuma ka rubuta ka ajiye nicce nan matar ka baka da wata mata a duniya bayan ne domin Mommy”
"Shout up idiot, ina magana kina magana who the hell are u get out from my office I hate u ", ta fita ta tura ƙofar da ƙarfin tsiya kamar zata ɓallansa gida biyu ya zauna yana tunani, ya dage kansa dake sara mai zuciyarsa cike da kulawa ga Indo da kuma tsanani akan Atika. Yana sane da cewa, daga yanzu, ba zai bari kowa ya cutar da Indo ba—ko da Atika ce.
@@@@@@@@@@@@
A haka Atika ta zauna a part nasu daga karshe taye singn ta dawo gida Domin fuskar ta na mata tsananin zafin ga zuciyar ta tana mata raddi da sharri daban daban akan Dr SADEEQ me zataye domin ta burge da ko kuma ta rabashi da Indo zuciyarta na raya mata abubuwan daban daban tabbas Dr yana son Indo but why menene yagani a jikin Indo me Indo take dashi ba ilimi ba ba waye Ba haka zalika na dirin jiki ba , a haka ta shigo gidan kai tsaye ta nufi gadon ta ta kwanta tana tunanin daban daban har bachi mai nauyi ya kwashe ta ..........
Indo ce zaune tana yanke wa Kaka kumba tana ta murmushi ita kaɗai kaka ta zungure ta da sanda " nikam Indo gayyamin ya akaye kika haɗu da Sadeeq kar ke ɓoye min komai kinjii jikkata domin zan taimaka muku ƙwarai da gaske kibani labarin ke nan Indo ta gyara zama ta zayyano wa Kaka komai abinda tasani ,Amman ta kasa gayyamata cewa Dr fa yana ɗaukar ta izuwa wani gida kuma yace yana sonta ..
Tagama Kaka taye murmushi na manya "Allah sarki gaskiya ya rigi amana Sadeeq daban yake da mutanen gidan nan yana da taushin hali da jarumta ban taɓa ganin sa da wata macce da yake kula da ita kamar ke ba daga ranar da na fara ganin sa a gabanki bisa kallon da yake miki hakan ya tattabbar da soyayya ce mai ƙarfi tsakanin ku kuma kina sonsa ko ". ta faɗa tana ɗaga girar sama Indo ta ganta " a'a Kaka ba wata soyayya kar ma kiye tunanin wanan ai Dr yafi ƙarfi na nisa ba kusa ba kina ganin sa ga ilimi ga kuɗi ga kyau ai sai manyan mata " ta faɗa tana ganin idon Kaka.
" munafuka gashi ina ganin kina sonsa kawai bazai iya faɗa a gidan nan bane don yasan bazaa yarda ya aure ke ba shi yasa kuke ta ɓoya , Indo ta tashi Kaka Kinga nace miki tausayin ne kawai ne kin takura min na tafe ma na kwanta sai dare zan dawo "
Kaka tace" Ja:ira zaku zo nan neman shawara ta ne "Indo ta kwanta a gadon ta, zuciyarta na ɗumama da tunanin Dr Sadeeq. Ta ɗauki wayarta a hankali, ta rubuta:
"I miss you Dr Balarabe..."
Sai ta ajjiye wayar a gefe, ta rufe ido tana murmushi cikin nitsuwa.
A gefe kuma, Dr Sadeeq na office, ya ɗauki wayar ya duba. Da ganin sakon, idonsa ya yi ja, zuciyarsa ta yi tsalle kamar ƙaho. Ya karanta sau goma, bai gaji ba — kalmar Indo ta kama shi da nitsuwa, ta sa zuciyarsa ta shagala.
Har yana cikin haka, sai Dr Kamal ya shigo cikin office, murmushi a fuska, yana tsokana:
“Eh Sadeeq, me ya same ka? Ka manta da aiki ne ko dai wannan yarinya ce ta dauke ka cikin soyayya haka kawai?”
Ya yi dariya yana girgiza
Dr Sadeeq ya ɗaga kai ya kalle shi, idonsa cike da kulawa amma kuma tsanani a fuska:
“Kamal… ka barsa yanzu. Wannan ba wasa bane, abinda ke faruwa da Indo, na san yadda zan kula da ita.”
Dr Kamal ya yi tsokaci, amma ya san tsanani da irin ikon Sadeeq, sai ya ɗan rage murmushi:
“To ai na sani, ni kawai ina tsokana ne, amma ka san kai kadai ce kake son kulawa da ita, ko ba haka ba?”
Sadeeq ya ɗaga hannunsa yana cewa:
“Eh… kada ka sake tsokani ni da ita, Kamal. Wannan ya fi kowane abu mahimmanci yanzu.”
Sai Dr Kamal ya yi dariya, ya juya ya fita, ya bar Sadeeq shi kaɗai da wayar , Indo da kuma zuciyarsa da ke nitsuwa cikin farin ciki da damuwa a lokaci guda.
Sadeeq ya kalli sakon, ya sake ɗan murmushi. “Wallahi… wannan yarinya… tana da wata hanya ta shiga zuciyata da ba zan iya misaltawa ba.”
Ya zauna a kujera, yana tunani a hankali, cikin natsuwa da kulawa ga Indo.
Ta jingina da pillow, zuciyarta na wani irin bugun da ba soyayya kaɗai ba.
A hospital kuwa…
Dr Sadeeq yana kallon sakon nata a screen ɗin wayarsa.
Yayi wani murmushi da ba kowa yake yinsa ba — but bai rubuta mata komai ba.
Kawai ya maida wayar ya ɗan runtse ido kamar mai nitsuwa.
Sai gadan-gadan aka buɗe ƙofar office:
“Emergency! Dr Sadeeq, please come quickly!”
Nurse Maryam ta faɗa cikin hanzari.
Dr Kamal ya shigo shima yana maza:
“Sadeeq let’s go! Patient collapsin’ in Room 12 no pulse!”
Sai kawai Sadeeq ya miƙe da sauri ya ɗauki stethoscope, ya bar wayarsa a kan desk, bai ma sake dubawa ba.“Let’s move! Prepare adrenaline!”
“Theatre in 1 minute!”
Sun fice da gudu.
Ƙofar ta baje da ƙarfi ta rufe bayan su.
Wayarsa kuwa ta rage a table, shiru, tana haskakawa kamar tana jiran shi ta mutu.
Seconds later…
Ta miƙe ta shiga bandaki tana murmushi da takaici.
A THEATRE
Dr Sadeeq yana ta aikin ceto rai “Charge to 200! Clear!”Patient ya motsa kaɗan.
Kamal ya ce “Good, pulse is back!”Sadeeq ya huci:“Stabilize him. Let’s keep monitoring.”
Dare ya yi…
Indo ta zauna a tsakar dakin Kaka, tana ɗan tattare kai da pillow kamar wacce ke jiran wani abu ya faru.
A zuciyarta kuwa:
“Ai yau dole mu haɗu… ko dai ya kira ni… ko dai ya dawo part ɗin nan…”
Sai kawai ta duba wayarta:
2 missed calls — nata ne, ba nashi ba.
Shiru.
Ba ko 1 message daga gare shi.
Wani abu ya yi mata zafi a zuciya kamar ana murɗa mata zuciya da spoon Ta tsaki:
“Hmmm… ai gara kawai. Tunda Dr yayi ignoring, nima a bar maganar yau. Kamar ni nake binshi fa."
Kaka ta dubeta da mamaki “Indo, yau bazaki jira ku gaisa bane da Sadeeq?”
Indo ta yi murmushi na shagwaɓa sannan ta kwanta jikin cinyar Kaka:
“Kaaaakaaa… wallahi kaina na ciwo ne.
Gaskiya bachi nake jiGobe akwai makaranta kuma Bansan jira-jira yau ba.”
Kaka ta yi wani murmushi na manya:
“Tooo shikenan. Ki je ki kwanta. Amma ni dai na sani, ba ciwon kai bane ke, rashin ganin Sadeeq ɗin nan ne.”
Indo ta yi saurin kallonta, ta murguɗa baki:
“Kakaaa, wallahi ki bari. Na ce ciwon kai ne. Ba wani "Kaka ta yi dariya ta ce “To shike nan, ai ni ban ce komai ba.”
A DAKIN INDO…
Ta shiga dakin a hankali, ta rufe ƙofa tana mai janye numfashi.Tana jin zuciyarta kamar tana magana:
“He didn’t pick…
He didn’t call back…
He didn’t even text…
Ko ina? Ko lafiya? Ko busy?
To ai tunda hakan ne… sai dai da safe.”
Ta cire dogon riga ɗinta a kasalance, ta ɗauki kayan barci Half vest blue wando leggings mai laushi
Ta kalla kanta a mirror:
“Hmm Indo… kina wani taya kanki damuwa akan wanda ma bai ji kiran ki ba.”
Ta kwanta, ta jawo bargo, ta juya gefe tana tattare pillow “Ba zan kirashi ba. Da safe kawai…”
Wayarta na gefe, tana haske kaɗan, tana nuna Delivered — no reply a hankali bacci mai sanyi ya fara jawo ta… tana jiran safe… tana jiran abin da bai zo yau ba.
UMMMMMMMMMMMMMMMMMMMM
TO
BE
CONTINUED
............
08101235739
DR SADEEQ BOOK 2
.jpg)