Dr. Sadiq Page 76 Complete

 

Dr. Sadiq Page 76

7️⃣6️⃣

   

💔❤️‍🔥DR SADEEQ ❤️‍🔥💔


BY


    NARNAH ƘANWAR SOJA 


    BOOK 2

My 15novel comedy love and drama 


    

    https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM


  

THIS BOOK IS DEDICATED TO MY LOVELY BROTHER ABUBAKAR SADEEQ AND MY LOVELY SISTER AISHATU INDO.......



    MORNING UPDATE 


    

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

*(J.W.A)*



    

🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚


(🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲 



    BUSSINES GROUP    


    👇👇👇👇👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/JjkU7xG4zcWIAvtWRgeFtT    


    


        

TITLE 

    Love is a flame that burns bright, even in the darkest night


    BARKA DA SHIGOWA SABUWAR SHEKARA 

    


     Da sassafe lokacin da ake kiraye-kirayen Asuba, Dr. Sadeeq ya fita a hankali daga ɗakin, ya tabbatar kofar ta rufe ba tare da hayaniya ba. Zuciyarsa cike da farin ciki, nutsuwa da wani sabon nau'in soyayya da bai taɓa ji ba a rayuwarsa.


Ya tsaya ɗan lokaci a bakin ƙofa yana kallonta tana bacci — baccin da shi ya kawo mata, mai nauyin allurar hutu da ya yi mata saboda ta huta. A ransa ya ce:


“Ke ce kyautar da ban taɓa zato ba Indo… Allah ya tsare min ke.”



Washegari…


Indo na farkawa, idanunta har yanzu nauyi suke yi. Tana ƙoƙarin tashi sai ga hasken wayarta yana walƙiya — one new voice note.


Ta ɗaga wayar a hankali, zuciyarta tana dukan dumm… dumm… kamar ana buga ganga. Ta kunna sakon.


Murya mai sanyi, mai raɗaɗi, murya da ta saba sanyaya zuciyarta, ta ji shi yana faɗa:


“I’m sorry Indo… but wallahi I love you. Ki bar komai a tsakaninmu sirrinmu… our first night.

Kiyi hakuri idan na yi over. Amma ke kika mayar da ni cikakken namiji jiya. Allah ya saka miki da alkhairi.

Please ki kula da kanki My Queen.”


Sakon ya ƙare da wata ajiyar zuciya mai nauyi da ya yi — mai kama da na mutum da yake riƙe da wani abu a ransa.


Indo ta tsaya jingine da gado, hannu a kirjinta, hawaye masu sanyi suka gangaro. Ba na bakin ciki ba — hawaye ne na soyayya da jin daraja.


Ta ce a hankali:


“Ya Salam Dr. Sadeeq…”


Indo na kwance har yanzu tana jin nauyin jikinta, banda jin daɗi. Idonta ya kumbura saboda baccin ya yi nauyi, zuciyarta kuma kamar an jefa ta a cikin ruwa — tana ji tana ɓuya tana jin kunya da tsoro iri biyu.


Sai kawai ta hurgar da wayarta gefe, kamar ma ba ta son ta ga sunansa.

“Bazan sake magana dashi ba… wallahi bazan yi ba.” Ta maimaita a ranta.


Tana kwance haka har ƙarfe takwas.

Kaka ta zo da mamaki, domin Indo ba ta saba yin baccin safe ba, musamman a weekend.


Ta tura ƙofar ta shiga, tana kallon yadda Indo ke bacci kamar wata mai shayarwa da ta gaji.


Kaka ta ce da ƙarfi:


“Ke tashi ki zo kimin kitso! Kince yau zakimin, ko sai na buga miki sanda? Yaran zamani da baccin banza!” Indo ta buɗe idonta a hankali, idon jajaye kamar mai zazzabi.Ta ce da murya mai rauni:


“Kaka… yau banda lafiya ciki na ke ciwo sosai.”

Kaka ta tsaya cak, ta zaro ido:


“Ayyo! Ayyo Indo? To shikkenan, Allah ƙara lafiya Dr. Sadeeq yazo na gayyemai yazo ya baki magani.”


Indo ta tsaya shiru kamar an caka mata wuka.

Da sauri ta miƙe zaune tana girgiza kai:


“A’a Kaka! Don Allah kar ki gayyamai komai…

Ina jin zan warke da kaina. Kar ki dame shi.”


Kaka ta ja dogon tsaki:


“Aikin banza. To dai ki sha magani ko kishi ruwa. Ni na tafi.”Ta fita tana gunguni.


Amma Indo kuwa — da magana ɗaya Kaka ta faɗa — zuciyarta ta rikice banda ciwon ciki dai, kunya da tsoro ne ke murɗa ta.


Ta ɗora hannu a kirji tana jin bugun zuciyarta kamar ana dokawa da guduma.


“Fusata nake dashi. Bai da wayo wallahi. Ni ma ai mace ce… ya yi tunanin ina iya kallon idonsa yau?”


Ta sake maimaitawa a ranta:


“Alkawari na dauka… daga yau ba zan sake magana dashi ba.”sai wayarta ta sake yi vibration a gefen gado ta runtse ido Sunansa ne. Dr. Sadeeq. Calling…

Indo ta ga kiran Dr. Sadeeq yana shigowa… ta ɗaga idonta ta kalle shi da tsana, zuciyarta ta hau tsalle.


“Wallahi bazan amsa ba.”

Ta kashe wayar nan take.


Wayar ta sake ringing…

Ta ƙara kashewa.

A karo na uku ya sake kira… nan fa ta dakan wayar gaba ɗaya ta switch off.


Ta tashi a hankali, tana rik’e ƙasan cikinta saboda zafin nan na budurci da bai saba da abin da ya faru ba.

Ko da tana jin tsoro, Indo ta ɗan yi wayo: ta hada ruwan zafi a bucket, ta naɗe kanta da towel, ta shiga bathroom ɗin su.


Ruwan zafi ya taba jikinta ta tsinci kanta da ƙara:


“Ayyooo…!”

Zafin ya motsa mata tunaninta, hawaye suka cika mata ido.

Amma ta daure saboda ta san hakan zai sauke mata radadin.


Ta yi wanka a hankali kamar wacce ke ladabtar da kanta.

Bayan haka ta sa simple riga, mai laushi, ba wata ado.

Ta koma ta kwanta, ta ɗaura hannu sama tana jin baccin ya dawo, amma zuciyarta cike take da fushi – baccin bai isheta ba a bangaren Dr. Sadeeq kuwa da  farko ya zuba ido a wayarsa  kiran na zuwa busy yayi murmushi mai sauti, ya tafa hannunsa:


“Fushi take… ai dole ta yi. Amma tawa ce.”

Ya kwantar da kansa a gado ya numfasa da nishadi kamar mijin da aka gama yi wa faɗa amma ya ji daɗin komai.


Ya wuce gym, ya yi wanka da kumfa farare, cikin bathtub mai ɗumi.

Ya lumshe ido yana tuno daren jiya,

yana murmushi,yana ganin Indo ta rikice,

yana jin yadda ta yi kuka, yadda ta yi ƙoƙarin gudu…


Shi kaɗai yasan irin farin cikin da ya shiga jiya.

A yau ya zama namiji cikakke — kuma Indo ce ta ba shi hakan.


Ya fito daga wanka yana shafa kansa wadda ruwan kumfa ke zuba a gwiwowinsa.

Cikin nutsuwa da annuri, ya saka farin T-shirt, ya shafa turare, ya nufi part ɗin Mommy.


Yana shiga ya rusuna da girmamawa:


“ gd morning Mommy…”


Ta amsa da murmushi mai kama da na mace mai iko “Sadeeq, Daddy zai dawo on Wednesday.” ya gyada kai kuna dan annuri a fuskarsa Mommy ta tsuke fuska nan take da murya mai ƙarfi ta ce:


“Inason ka tabbatar da maganarka da Atika. Wannan ba shawara bace, umarni ne.

Karka manta… ka koreta daga gidan nan saboda hayaniyarta karka yi tunanin ka yi nasara ko ka tsere.

Atika matar ka ce HAR ABADA.” Yana son bude baki, idan akalla ya ce “Mommy—” ta daga hannu cikin masifa “Dakata. NOT even a word. You can go.” ya tsaya yana jin gabanshi ya fadi yayi salati a ransa ya fita daga d'akin kamar wanda ya yi rashin nasara a yaki

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post