Yaɗin Mage Page 1 by Ummu Affan

 

Yaɗin Mage Page 1

*U M M U  A F F A N 2026*

YAƊIN MAGE...

BOOK 1

©FATIMA SUNUSI RABIU

   *Ummu Affan*

HAƘƘIN MALLAKA: Ummu Affan


GODIYA: Ta tabbata ga sarki Allah gagara misali, dubun tsira da aminci su ƙara tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (S A W)


JINJINA.

Har kullum gare ku take iyayena, abin alfaharina Allah ya ƙara muku lafiya.



SHAFI NA ƊAYA



ƊANDUME JIHAR KATSINA.


Unguwa Gangare.


Gidan Abulle.

Ta muskuta daga zaunen da take, kana ta dube ta ba yabo babu fallasa ta ce.

"Hmmm! Wai Abulle me ki ke son ki ce ne? Nufinki ba ni da hankali ko ban san abin da nake ba?"


Tana faɗa kuma ta miƙe tsaye, tare da gyara fallan zanin da ta ɗaura a kanta, wanda ake rufawa matsayin mayafi a shekarun baya. Abulle wacce take kallon Suwaiba baki buɗe ta ce,

"Ba dai tafiya zaki yi ba?"

Ba kuma ta jira amsarta ba ta ɗaura da cewa.

"Ban ga fa laifinki ba Suwaiba, kuma ba na jin har duniya ta naɗe zan iya ganin laifinki a wannan fagen, ai ni wallahi zan iya ma fin abin da ka ke yi akan kishi, kishiya ko bala'i, kishiya ko masifa, wallahi kishiya abar gudu ce kuma ko ma me zan iya aikatawa domin ganin ta bar mini gidana." Yadda tayi maganar har kumfa ke fita daga bakin na miyau tsabar yadda take son nuna maganar har cikin zuciyarta ta fito.


Suwaiba ta ɗaga labulen ta fito Abulle tayi saurin yayar ɗan kwalinta da ke yashe a ƙasa kusa da inda ta tashi, ta bi bayan Suwaibar da har ta fito tsakar gidan, sai dai kafin ta maganantu har ta rigata furta.

"Tabbas kuwa, yaƙi ma yanzu na fara akan almurar, Abulle na tsani Hafsatu na tsani 'yar da ta haifa, idan ban ga bayanta ba ban amsa sunana ba."


"Nikam ina goyan bayanki Suwaiba, domin idan ba ki ga bayanta ba, ita ƙoƙarin da za tayi na taga bayanki ne, yaƙi kam kar ki fasa. Domin tsakanin kishiyoyi yanzu ba amana, duka kallon hadarin kaji ake wa juna"

Abulle ta amshe cike da ƙoƙarin ingiza mai kantu ruwa.


Suwaiba ta fara tafiya tana ci gaba da surutu, Abulle kuwa har ta rakota hanyar ƙofar gida,  har zata fita ta kuma juyowa.

"Wannan ki ka ce na sakawa Salisu a abin sha ko?"


"Eh haka malam ya ce,  nima dai mutumin nawa tunda na saka masa na lura har tsorona yake ji yanzu."


"Yauwa 'yar gari, haka nake so, ina godiya aminiya."


Tana faɗa suka yi sallama ta gyara lulluɓinta tayi gaba, tafiya take tana saƙar zuciya.


'Shegiyar mata daga kawota wata tara na haifi 'yar ta Bintu yanzu ga ciki a jikinta 'yar duk ta tsamure saboda babu ishashshan nono sam bai ishe ta ba.'


Ita ce ma ta zuga Salisu akan a daina ba ta nono sai abinci, yarinya ko shekara ɗaya ba tayi ba, ciwo na yau daban na gobe daban, burinta yunwa ta kashe Bintu ko kowa zai huta. Ta kuma jan wani sabon tsakin tunowa da yadda Salisu ke son Bintu,  muddin ya dawo kasuwa yana rungume da Bintu,  abincinsa ma tare suke ci ko da yana ɗakinta ne. Haka ta dunga karanta wasiƙar jaki har ta ƙarasa gida.


Gini ne na ƙasa da tasha bulasta, ƙofar gida shaguna ne har biyar kuma dukkansu ana sana'a a cikinsu, ɗaya mai sayar da mai da manja, sai mai shagon provishion,, ɗaya kuma katifa ake sayarwa da kujeru, ɗaya kuma bayerabiya ce tana sayar da kayan jarirai sai ɗayan kuma shagon mai shayi ne. Tun daga ƙofar gidan zaka lura gida ne babba kuma na haya, zaure ne mai faɗi sai duguwar hanyar da zata kai ka ciki, ɗakuna ne guda shidda jere ko wanne falle ɗaya, sai ɗaya gefen kuma ɗakuna guda uku sai bayi biyu ɗaya na wanka ɗaya na bayan gida, da ƙatuwar rijiyarsu a tsakar gida. Suminti ne shimfiɗe a tsakar gidan sai siririyar kwata ita ma da ta ƙawata gidan tun daga shugowarka har ƙarshe wajen bayi, kuma gefen rijiya wurin duk ya ɓaci babu suminti a wurin sai chaɓali.


Mata takwas ne ke rayuwa a cikin gidan. Ɗakin Baaba ne farko babbar mace ce don ta gama aurar da 'ya'yanta tas sai jikarta ɗaya Saliha da take ruƙo, shi ya sa matan gidan duka ke kiranta Baaba yadda 'ya'yanta ke kiranta kuma uwa suka ɗauketa, tana da fawa sosai hakan yasa Baaba take iko da matan gidan, wanda ya girmamata yabi abin da take so shi ne nata, wacce kuwa taƙi bi, to tana cikin matsala domin tuggu da duk wani maƙyirci daga wurin Baaba yake fitowa. Ɗaki na gaba shi ne ɗakin Malama, ita kuma malamar islamiyya ce, asalin sunanta Halima amma kowa da Malama yake kiranta mace ce mai haƙuri da sanin addininta tana da faɗar gaskiya komi ɗacinta shi ya sa sam ba sa shiri da Baaba mugun ga maciji ne tsakaninsu. 


Ta uku ita ce Asabe, amarya ce ɗanta ɗaya, Asabe tana girmama Baaba tana ɗaya daga cikin 'yan ɗakinta. Ɗaki na huɗu kuma shi ne ɗakin Hafsatu wato amarya ga Suwaiba. Hafsatu tana da sauƙin hali amma fa tana da faɗa idan ka taɓata, ba ta son raini haka ba ta ɗaukar ƙananun magana irinsu ake kira da sha yanzu magani yanzu, da zarar ka mata abu bai mata ba, nan take ta ke ɗaukar hukunci ayi bala'i ayi masifa idan ma dambe ta kama tana saka wando a dambata, wannan dalilin ne ya saka ba sa shiri da Baaba, musamman ma da tun kafin a aurota Suwaiwa 'yar ɗakinta ce duk gidan babu wacce tafi ƙauna irin Suwaiba, hatta Salisu tana ƙaunarsa a cewarta tamkar ɗan cikinta haka take kallonsa, dalilin da yasa shima yake ƙaunar Baaba musamman da kasancewarsa ba ɗan gari ba neman kuɗi yazo, kawai sai ya liƙe Baaba da mijinta tamkar iyayensa da suka haifesa, yana musu biyayya hakan yasa ka ita ma Suwaiba ke yiwa Baaba biyaya kamar zata goyata, 'ya'yan Suwaiba kuwa jikoki ne a wurin Baaba ƙaunarsu take sosai. To wannan dalili yasa ba sa ƙaunar Hafsatu duk da ba sa nunawa a fuska gara ma Baaba wani lokacin tana nuna mata ƙiyayya ɓaro-ɓaro amma Suwaiba kam ba zaka taɓa ga ne alƙibilarta ba, mace ce mai fuska biyu ba ka taɓa gane gabanta ko bayanta.


Suwaiba yaranta uku sai ta huɗun da take ruƙo kuma ita ce babbar ciki 'ya ce ga Salisu 'yar uwargidansa da suka rabu, Maryama kenan babbar sai Asiya babbar 'yar Suwaiba sannan Khamis sai ta ukun Mariya, ita kuma Hafsatu 'yar ta Bintu, sai cikin da take da shi yanzu, tana cikin wankan jego Bintu, Suwaiba ta haifi Mariya. Ɗaki na ƙarshe a ɓangaren ɗaki ne na Suwaiba.


Ƙofofin bayi ne ke kallon hanyar waje, ɗaya ɓarayin kuma ɗakin Inna ne ita ma tsohuwa ce matar mai gidan kenan tana da sanyin hali, idan baka sani ba kazo gidan ɗauka zaka yi Baaba ce matar me gidan, ɗayan ɗakin kuma amarya ce a ciki wacce ba ta shekara ba ko haihuwa ma ba tayi ba, sai ɗakin gaba da wata bazawara ce ke ciki, ba ta wuni gidan ma gidan aiki take zuwa sai dare take dawo wa bacci.


To kun dai ji yadda wannan gida ya kasance da kuma mutanen da ke cikinsa.


Suwaiba.


Har zata wuce ciki sai kuma ta fara leƙawa ɗakin Baaba.


"Baaba sannu da gida."


Jin shuru ta ɗaga labulen tare da kunna kai, sai ta hango ba kowa hakan yasa ta fito tare da shigewa ciki.


Malama da ke jikin bangon ɗakinta tana duƙa tuwo ko kallo ba ta isheta ba ta shige gaba, malama kam ta girgiza kai ba tare da ta ce komi ba. Ta ja tsaki lokacin da taji Redion Hafsatu a kunne tana shan waƙar Barmani choge ta ciki da goyo ikon Allah, Redio ce irin wacce ake saka kaset tunda ta sayo ta wani zuwa da tayi garinsu ta taho da kaset ɗin Barmani kullum cikin sakawa take, abin yana mata ɗaci musamman wani kaset na waƙar Fatima Bintu shima tana yawan saka shi, tasan saboda 'yarta Bintu take sawa duk da waƙar ta yabo ce, sai taji tafi tsanarta fiye da ta Barmani saboda yadda ta tsani Bintu.


Ta ɗaga labulen fuskarta ba yabo ba fallasa.

"Hafsatu kina ciki?"


"Ina nan Innarsu Asiya kin dawo?"


"Eh." Ta faɗa tare da sakin labalun, a kullin ta kalli doguwar kujerar Hafsatu sabuwa sai taji kamar ta shiga ta ƙone 'yar banza tsabar baƙin ciki.


Don ita gadonta mai rumfa ne kawai a ɗakinta, sai wata yaƙunanniyar katifa a ƙasa da take kwana ita da yaran, shi kuma Salisu a gadon ranar da yake ɗakin. Hafsatu kuwa gadonta mai rumfa ga kuma ƙarami da bonu, bugu da ƙari ga doguwar kujera sai keken ɗinki saboda Hafsatu tela ce kuma ta iya ɗinki sosai shi ya sa take samu tun zuwanta garin. Tana shiga ɗaki ta iske Maryama kwance ta buga mata uban dundu.


"Kwanciyar me ki ke yi da rana tsaka, shegiyar yarinya ba zaki tashi ga ƙulle-ƙulle na nan ki ɗauki talla ba?"


A furgice yarinyar ta tashi wacce ba zata wuce shekaru goma da haihuwa ba, 'yar matashiya ce tana kuka a hankali amma ta kasa magana, Suwaiba ta ɗauko farantin tallar ta dungura mata a kai tana cigaba da cewa.


"Ko zaman ubanki zaki mini har da su kwanciya tsabar kina so ki fara raina ni, maza ki tafi talla kuma ki dawo gidan nan ba kiyi ciniki ba sai na yanka ki."


Fita tayi tana kuka tare da riƙe farantin tallar da kyau. Suwaiba ta cire zanin kanta ta ninke tare da ɗaurawa saman gana mazgo ɗinta, ta gyarawa  Asiya da Khamis kwanciyarsu a hankali don ta ga sun fara motsi sakamakon hargowar da tayi da kuma alama duk lokaci guda suka kwanta da Maryama.


Ta kwanto Mariya a goye, jin ta fara motsi, zaunawa tayi ƙasan tamfalɗin da ta shimfiɗe duka tsakar ɗakin da shi ta fara shayar da ita. Ta girgiza kai tunowa da ita kayan miyan nan ne sana'arta, su kuka, kuɓewa busassa,, barkono, gishiri, farin maggi da sauran dangoginsu da ake miyar yauƙi. Idan da ta duba keken ɗinkin Hafsatu sai taji ranta ya ƙara ɓaci, taji zuciyarta kamar zata faso ƙirjinta tsabar zafi da ƙuna.


Hafsatu.

Tana jin waƙarta tana bi tana gyaɗa kai cike da jinta cikin nishaɗi, yau ita ce da girki, ganin tayi ɗinki ta gaji sai ta ɗan kwanta saboda lokacin sha biyu na rana ne, da niyyar zuwa ɗaya sai ta girka. Bintu ma ta rarrafo, ta rungumeta a jikinta nan take kuwa bacci ya yi awan gaba da su.


Kukan yaran da taji a kanta ne ya farko da ita a gigice. 


"Hafsatu me ki ke nufi da yaran nan? Biyu har ta kusa amma baki ɗaura tukunya ba ga yara sun gaji sun fara kuka?"


Ta buɗe ido a hankali tare da tashi tana miƙa bayan ta gyarawa Bintu kwanciyarta.

"Subuhanallah! Wai har biyu tayi? Na fa ɗan kwanta ne zuwa biyu jikina duk ba daɗi."


Wata uwar harara ta jefa mata, sai ta wayince.

"Oh sannu, kin san lamari na masu juna biyu, amma dai kin san gida idan da yara sai ana kaffa-kaffa, ko don ita Bintu koko take sha ne?"


"Ah ah haba dai Suwaiba ai kema kin san bazan yi haka saboda wai Bintu koko take sha ba, har abincin ma tana ci."


Tana faɗa ta miƙe, Suwaiba taja tsaki ƙasa-ƙasa tare da kama hannun yaranta suka fice daga ɗakin.


Kokon Bintu Hafsatu ta Eyba ta kaiwa Khamis da taji yana da kuka, taje ta kunna itace ta ɗaura sanwar shinkafa da faduka, kasancewar iccen mai kyau ne kuma busasshe, ba ta ɗau lokaci mai yawa ba ta kammala, kamar kullum robobi ne kowa da na shi. Maryama Asiya Khamis har da 'yar goye Mariya, ita ma ta saka a nata kwanon sai na Bintu duk duk suke sa'o'i da Mariyar. Sai kwanon Baaba wanda aka ware takanas ko wanne girki zasu yi da nata tamkar uwa ce ga Salisu kuma abin da ta ce shi yake yi. Sai kuma faranti da ake kaso biyar ko wanne ɗaki a kai idan Hajara bazawara ba ta nan kuma kaso huɗu, sun riga da sun samarwa juna duk wani girki to sai an ba 'yan gida ko ba yawa dai haka za a kasa. Bayan ta kai wa kowa ta kai wa Baaba nata wacce ta amsa ba yabo ba fallasa, tare da cewa,


"Ya jikin na Bintu kuwa?"


"To da sauƙi za a ce Baaba."


"Amma kina mata daurin nan da na amso kuwa? Hafsatu son jikinki ya yi yawa ko don kin ga 'yar fari ce baki kula da ita? Zan saka Salisu ya kira Gwoggonki gaskiya muyi maganar nan da ita."


Gaban Hafsatu ya buga, amma baa ta ce komi ba ta juya, sai dai a ranta tana furta.


'Ba ta da aikin komi sai haɗa mata da miji faɗa, aniyarki ce zata biki wallahi.'


Maryama ce ta shugo ta dawo daga talla idanuwan nan nata jawul, Hafsatu ta ce,

"Ke daman baki gidan nan?"


Gyaɗa kai kawai tayi ba ta ce komi ba, Hafsatu ma ta taɓe baki ta koma ta ɗauki abincin Bintu ta shiga da shi ɗaki ta rufe mata, ta iske ta farko ma, ɗaukarta tayi ganin tayi mata fitsari sai ta sa ruwa a wurin ta goge da tsumma ta fito ta ɗauraye mata jiki ta shanya wandon, tazo ta ɗauki nata abincin, daidai fitowar Maryama zataci nata abincin, ta kalli abincin, wanda ta sakawa Mariya shi aka ma Maryama. Bayan saboda su ba sa ci sosai suna shan nono ita da Bintu duk da an yaye Bintun to kai ɗaya take saka musu kaɗan-kaɗan na manyan yana yin ukun nasu musamman ma na Maryama da ke shekara goma Asiya bakwai Khamis biyar sai Mariya da Bintu da ke ɗaya da kusan rabi yanzu. Hafsatu ta girgiza kai domin ta taɓa magana akan hakan amma ranar sai da aka shiga tsakaninsu da Suwaiba faɗa sosai suka yi wai ta saka mata ido bayan tare tazo gidan ta isketa da Maryaman. Tabbas yarinyar da yunwa jikinta, shiyasa Asiya da ta girma da shekaru uku har ta fita gaɓa-gaɓai na girman jiki. Har zata wuce ɗaki sai ranta ya ƙi mata daɗi ta dawo da baya tare da ɗaga labulen ƙofar Suwaiba....


_Rayuwar gidaje guda huɗu, inda za a nuna muku tsantsar zaman takewa irin ta aure na malam bahaushe. Ƙalubalen da ke cikin zaman gidan aure shin laifin mazan ne ko kuma na matan? Wannan labari na Yaɗin Mage zai warware muku zare da abawa akan zaman takewar aure, surrukan da ke cike tare da tarin ƙalubalen da ke cikinsa. Gidaje guda huɗu a labari guda, kuma ku wanne gida da kalar tasu zaman, ku dai ku biyo alƙalamin Ummu Affan in sha Allahu ba zakuyi da na sanin bin labarin ba.._


08104335144



*🩺 GHT HERBAL SOLUTIONS 🩺*  

*Maganin da ke dawo da lafiya, da izinin Allah!*


Muna sayar da ingantattun magunguna na zamani da aka gwada kuma suka shaida aiki.  


*Duk wannan cutar ana warke wa sosai mutum ya dawo nml*


*Ga wasu daga cikin cututtuka da muke da magani a kai:*

✅ Ulcer  

✅ Hawan jini  

✅ Ciwon zuciya  

✅ Ciwon Suga (Diabetes)  

✅ Ciwon daji  

✅ Ciwon koda & hanta  

✅ Zazzabi mai tsanani  

✅ Ciwon gabobi & ciwon jiki  

✅ Ciwon ido & kunne  

✅ Asma, tarin fuka & mura  

✅ HIV  

✅ Matsalar rashin haihuwa  

✅Gyaran fata

✅Na kurajen fuska

✅Na rage kiban

✅Na Saka kiba

✅Na infection 

🟢 Da sauran su...


*Me ya bambanta GHT?*  

🌿 Magungunan mu halal ne kuma an tsaftace su.  

🔬 Sun wuce binciken lafiya da gwaji.  

🌟 Suna da matukar tasiri – an samu sauki ga dama-dama.  

🧕🏽 Muna kula da sirrin marasa lafiya.  

🚚 Muna da isar da magani kai tsaye (Delivery available).


Domin ƙarin bayani 08104335144

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post