8️⃣1️⃣
💔❤️🔥DR SADEEQ ❤️💔
BY
NARNAH ƘANWAR SOJA
BOOK 2
My 15novel comedy love and drama
https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM
THIS BOOK IS DEDICATED TO MY LOVELY BROTHER ABUBAKAR SADEEQ AND MY LOVELY SISTER AISHATU INDO.......
MORNING UPDATE
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲
BUSSINES GROUP
👇👇👇👇👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/JjkU7xG4zcWIAvtWRgeFtT
BARKA AUNTY INDO MARUBUCIYAR SAWUN KEKE TA SAMU ƘARUWA HAIHUWA ALLAH YA RAYA MANA BABY GIRL AMEEN
TITLE
Love is a flame that burns bright, even in the darkest night
AFTER SOME DAY'S
Indo ta zauna kan gadonta, ta ji zuciyarta kamar an daure ta da ƙyalle. Ta ɗaga wayar a hankali, ta rubuta sako cikin rawar hannu:
“Please I need to go…
I like the school.
Thank you.”
Ta tura ta rufe idanuwanta, tana jin kamar tayi babban abu can Dr Sadeeq kuwa… Da zarar ya ji sautin piiing! sai ya kamo wayarsa da sauri.
Yana buɗewa, ya sauke idonsa kan sakonta.
“Please I need to go…”
Ya sake karanta “I like the school…”
Sai zuciyarsa ta matsu, ta yi wani irin nauyi mai tsanani.
Ya maimaita sakon.
Sau ɗaya… sau biyu har sau goma a jere.
Kamar mai neman wani sirri a kalmomin, ko zai ga kalmar“Don tafi daga gare ka ne.”ko “ka barni.” “Bana son ganin ka.”
Amma babu
Ya jingina da kujerar office ɗinsa, wayar a hannu, idonsa na raguwa cikin kunci da natsuwa da hannu ya shafi kansa a hankali.
“She wants to go…”
Ya ambata da murya mai rauni ya kuma sake kallon sakon na ƙarshe:
“thank you.”
Abinda yafi doke zuciyarsa shine wannan “thank you” ɗinkamar Indo na masa sallama ne har abada.
Sai ya runtse idanu yana jin wani abu ya tokare zuciyarsa, ya ɗaga wayar ya koma messages
Ya duba chat ya sake karanta sakon sau na goma sha ɗaya…
ba tare da ya rubuta komai ba.
Ya kasa rubuta komai
Domin a zuciyarsa kalma biyu ke masa yawo:
“Indo is leaving me…”
Ya jingina da tebur ɗin, ya lumshe ido, murya ta shaƙe cikin zuciyarsa:
“Please Indo… kar ki barni haka" ya kashe wayarsa.
Ya jingina kai, yana barin shiru ya cika dakin.
Darenta ya lalace.
Ranar Indo kuma ta fara sabon tunani.
A ɓANGAREN ILHAM kuwa…
Da ta koma gida, zuciyarta cike da damuwar Indo, ta same Daddynta a falo yana kallon news.
Ta zauna a gefensa, ta ɗan janyo numfashi sannan tace:
“Daddy… akwai magana.” ya kalle ta da murmushin kulawa “What is it my princess?”
Ilham ta fara ba shi labarin Indo — yadda take rayuwa a gidan Kaka, yadda take da ƙwarin hali amma tana da rauni, yadda ta rame saboda damuwa, yadda take muradin boarding domin samun sauyi da natsuwar zuciya.
Ta ƙara da cewa:
“Daddy, please… Indo is my only friend.
Ni kuma bana so a raba mu.
Ka taimaka a karɓa mana form ɗin nata mu tafi tare.”
Daddy ya yi shiru, yana sauraren ta sosai.
Ya jinjina kai a hankali, ya ce:
“Hmm… I understand now.
Kin faɗa min komai, kuma gaskiya yarinyar tana bukatar sauyin muhalli.
Don haka… babu damuwa.”
Idon Ilham ya faɗaɗa cikin murna Daddy ya sake cewa:
“Da safe idan na haɗu da Dr Sadeeq zan yi masa magana.
I’ll handle everything
Ilham ta miƙe da sauri ta rungume shi:
“Thank you Daddy! Wallahi you’re the best!”
ta yi tsalle tana dariya kamar ƴar ƙarama.
A zuciyarta kuwa:
“Indo will be so happy…
Mu biyu – one school, one hostel, one life.”
Kwanciya tayi da murmushin nasara —
ta san gobe Indo ba zata yi kuka ba… zata yi murna.
Suna fitowa daga masallaci da asuba, iska mai sanyi na tafe a hankali, Daddy ya kalla Dr. SADEEQ da murmushi mai tarin nutsuwa.
“Dr. Sadeeq, akwai wata magana da nake son mu yi kafin ka shiga gida"
Dr. SADEEQ ya tsaya, ya ɗan ɗaga gira, saboda Daddy ba ya yawan yin irin wannan maganar sai abin ya da muhimmanci.
Dr. SADEEQ:
“To Alhaji, me ya faru?”Daddy ya ja numfashi
“Indo… ta yi magana. Tana matuƙar son karatu. Kuma ta ce tace maka… ka taimaka mata. Har ta ba Ilham labari gaba ɗaya.”
A nan Dr. SADEEQ ya zaro ido kaɗan cikin mamaki
“Indo ta gaya muku duk haka?”
Daddy ya jinjina kai.
“Eh, ba komai bane ai. Ni dai na ce a karɓo mata form. Ita da Ilham za su tafi tare. Kai ma ka shirya, zan so mu yi maganar sosai game da lamarinta.”
Dr. SADEEQ ya yi shiru na tsawon sakanni biyu, yana kallon gabansa kamar yana nazari. A zuciyarsa ya ce “Ashe Indo ta damu har haka? Ashe tana ɗauka ni ba zan taimaka mata bane?”
Sai ya ɗago kai da murmushin da ba kowa yake gani ba
“Alhaji , wallahi tunda Indo ce… babu wani abu da ba zan yi ba. Zan taimaka mata har inda ƙarfina ya iya kaiwa. Kuma na yi mamaki kawai saboda bata taɓa gayamin haka da kanta ba.”
Daddy ya fashe da dariya mai sanyi
“To ai yaran zamani. Wasu sai sun ji kwarin gwiwa kafin su fadi abin da ke zuciyarsu. Ka tsaya ka ji magana, ba sai an yi hayaniya ba. Ni dai ina goyon bayanka, ina goyon bayan karatunta… ku shirya kawai.”
Dr SADEEQ ya saki wani murmushi mai cike da jin daɗi.
Dr SADEEQ:
“Insha Allah Alhaji . Zan shirya komai yau.”
Suka ci gaba da tafiya gidan, kowannensu cikin tunani—Daddy cikin farin cikin hangen gaba, Dr SADEEQ kuma cikin mamaki, da wani sabon yanayi da bai taba ji ba tun da ya fara sanin Indo.
@@@@@@@@@@@@@@@@
Zuciyar Dr. SADEEQ dai ta ɗauki nauyi sosai. Bayan su Daddy sun yi tafiya gida, ya nemi Kamal a gefe, ya zauna da shi cikin natsuwa:
“Kamal… wallahi ba komai. Alhamdulillah, zata samu sauki yanzu. Ni kuma zan tabbatar na sauke amanar da Allah ya bani. Zan kula da ita yadda ya kamata, har sai ta kai ga abin da ya dace da ita.”
Kamal ya ɗan jinjina kai, ya fahimci irin damuwar Dr. SADEEQ da irin soyayyar da yake ɗauka ga Indo.
“Allah ya taimaka maka, Dr. Sadeeq. Ka san kai ne kadai ke da ikon sauke amanar da Allah ya ba ka. Amma kada ka yi gaggawa, ka ba ta lokaci, kada ka matsa mata… in ba haka ba zata tsananta.”
Dr. SADEEQ ya ɗaga hannunsa ya dan shafa fuska, ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi
“Na sani Kamal… zan yi hankali. Amma zuciyata tana cikin farin ciki, saboda a yanzu na fahimci cewa ba zan bar ta cikin wahala ba. Allah ya sa ni mai adalci gare ta.”
Kamal ya jinjina kai, ya danna kafadarsa cikin goyon baya:
“Yau ka fara aiki mai girma. Ka tuna, hakuri da kulawa za su zama makami mafi ƙarfi.”
Dr. SADEEQ ya zauna a waje kadan, yana tunani, zuciyarsa cike da sabon buri. Wannan lokaci ne da ya fahimci cewa, soyayya da amanar da Allah ya bashi za su haɗu don kare Indo daga duk wani abu da zai cutar da ita.
.jpg)