👑⚔️ IZZAR BASARAKE ⚔️👑
The Majesty of an Emperor 💎
(Veins Of Arrogance…..) 🩸👑🔥
Da sunan Allah Mai rahma Mai jin ƙai Alhamdulillah after a long while da nayi nesa da rubutu Allah ya sake bani ikon dawowa, zan fara wannan sabon littafin nawa Honestly i really don’t take that for granted at all
🔐
Duk abin da zaka karanta a cikin wannan littafin pure fiction ne, from A to Z There is nothing real in it sai dai darussan dake a ciki da abubuwan da zasu sa ka duba rayuwa from a different angle
⚠️ Gargadi
Ban lamunta a taɓa komai daya shafi wannan littafin ba, ba tare da izinina ba If you do that without my permission zan ɗauki matakin da ya dace
*✒️ From the Pen of Boss Bature 💋✍️*
writer of "Abban Sojoji” da “Kurkukun Kaddara”
Now kuma, we’re entering a fresh chapter na sabon littafina😊 wanda nake roƙon Allah Ya bani haƙuri da juriya da lafiyan da zan kammala shi lafiya kamar yadda na fara
Littafin ya ƙunshi fadakarwa, ilmantarwa da nishadantarwa
da sauran abubuwan al’ajabi, shocking twists da surprises da sai wanda ya karanta zai ji su a zuciya 🥰
Idan na rubuta wani abu da ya yi kama da rayuwar wani ko labarin wani, hakan purely coincidence ne not intentional at all
sannan Ni ma mutum ce like you 😊 not a computer I can make mistakes I’m not always right Ina yin daidai, ina yin ba daidai ba So please ku yi min uzuri inda na sa6a, idan any part na taɓa zuciyar wani ba daidai ba
Idan kuma na yi kuskure a matsayinku na ’yan uwana Musulmai zaku iya ankarar da ni politely, with respect and love
Allah ka bani ikon rubuta abinda zai amfani al’ummar Annabi (SAW), wanda zai zama alkhairi a gare ni da ahlina har bayan raina Allah kada Ka bari na aikata sabo a cikin rubutuna Ka kare ni, Ka tsare ni daga fadawa halaka, Ka tsarkake alkalamina da zuciyata.
Special Shout-out & Appreciation
First of all, mamana da ’yan uwana Aunty Zee, Munah Pa, khady bature da sauran su thank you for always having my back, masu ƙarfafa min gwiwa ba tare da gajiyawa ba, a koda yaushe.
Thank you for the constant encouragement, endless support da addu’o’inku da ba su taɓa yankewa ba Wallahi ku ne real MVPs dina 💘🫶
To my beloved Aunty Kubrah💘 one of the special people who encouraged me may Allah reward you abundantly 💖
Na yi missing comments na fans dina Fatan in sha Allah zamu sake haɗuwa lafiya a wannan sabuwar tafiya ta sabon littafin nan
Ina roƙon Allah in sha Allah zaku ji daɗin labarin ku more shi, ku ji daɗin kowane page, kowane twist
That’s my sincere hope and prayer 🥺🤍📖✨
🔥 TAKUN FARKO 🔥
…and this is where the story truly begins 🕊️…
A ƙasan katafariyar daular masarautar nesa da gine-ginen alfarma na sarauta haka Kuma ya nisanta daga hayaniyar al’umma, akwai wani keɓaɓɓen gini, Wuri ne da rai ke shiga amma baya fita yadda ya shigo Ana yi masa laƙabi da makabartar rayayyu wuri ne da ko maƙiyi ba za ka yi masa fatan ya kasance a cikin sa ba.
Ba ko ina bane wurin nan face kurkukun Daula wanda asalin suna shi bakin kurkuku, Kafin a shiga cikin sa, sai an ketare babbar ƙofar ƙarfe mai kauri, wadda A tsakiyarta an sassaka tambarin Zaki, alamar ƙarfi da iko na daular.
Kafin a buɗe ƙofar, sai an bi tsauraran matakan tsaro binciken shaidar ido (retina scan) da tantance tafin hannu (palm biometric scan) sannan sai kuma an samu izini daga jami’ai biyu Shugaban Kurkuku da Jagoran Dakarun Tsaro
Babu wata dabara ko ƙarfi da zai tilasta ƙofar ta buɗe ba tare da cikakken izini ba daga jami'an Nan ba
(Bakin Kurkuku) rabin gininsa yana ƙarƙashin ƙasa, rabinsa kuma yana saman ƙasa Bangon waje an gina shi da duwatsu masu duhu, irin na fortress
Katangar tsaro ta farko tana da matakai uku dutse mai kauri, ƙarfaffen ƙarfe a tsakiyarsa, da na’urorin tsaro na zamani masu gano motsi, da yunƙurin lalata gini.
A saman bangon akwai hasumiyoyin tsaro na ƙarfe, kamar na tsohon zamani, amma a cikinsu akwai na’urorin sa ido na zamani masu juyawa a hankali, suna bin kowane motsi a cikin yankin (CCTV).
Akwai dogayen hanyoyi (corridors), ƙasansu anyi shinfida na dutse mai santsi wanda aka tsara domin hana saurin gudu Duk yunƙurin tserewa yana haddasa kulle hanyoyin fita kai-tsaye, fitowar dakarun tsaro da kama fursuna nan take.
Kuma A kowane corridor akwai gawurtattun dakarun tsaro na musamman, waɗanda ake wa laƙabi da Mala’ikun Mutuwa saboda tsaurin halinsu da rashin tausayi, Sanye suke da bakaken kaki, abin rufe fuska, da tambarin zaki a ƙirjinsu.
Wasu suna ɗauke da makaman gargajiya, wasu kuma da makaman zamani Ana sauya dakarun tsaro lokaci-lokaci domin kauce wa sakaci ko sabani.
A saman corridors akwai hanyoyin sintiri na ɓoye, inda jami’an tsaro ke sa ido kan fursunoni daga sama ba tare da an lura ba sannan a kowane sashe akwai ƙararrawa na’urorin gano motsi Ko ƙaramin motsi da bai dace ba akayi yana iya jawo ƙararrawar sirri tayi qara ga jami’an tsaro
A cikin bangaren fursunoni, kowane ɗaki (cell) yana da ƙaramin gadon ƙarfe, bango mai azabar sanyi da ƙofar ƙarfe, da ƙaramar taga
Ana kulle ƙofofin kowane ɗaki da makullan lantarki na tsaro, waɗanda ba za a iya buɗe su ba sai da izinin manyan jami’ai ta tsarin tantancewa
Babu wadataccen haske a cikin kowane ɗakin kurkukun, kullum a rage suke, ba dan komai ba sai dan hana fursuna jin daɗi ko sabawa da walwala
A wasu sassan akwai ɗakuna masu haɗari sosai, bangon su an ƙarfafa shi ƙwarai da matakan tsaro masu tsauri, ko taga babu sai murya kaɗai ke fita.
A cikin rabin ginin kurkukun dake a ƙasan ƙasa da akwai Deep Cells wurin da aka tanadar domin waɗanda aka yankewa hukuncin ɗaurin rai da rai
Babu tagogi babu haske sai idan jami’an tsaro sun amince Bangon ɗakunan nan ba sa yaɗa koda sauti ne kuma an kulle duk wata hanyar sadarwa tsakanin su, waɗannan sune ainihin wadanda suke a cikin maƙabartar rayayyu gasu dai da rai amma basu da yancin komai dan duk wanda aka kai nan toh ya mutu a idon jama'ar duniya shida fita sai a lahira.
Kowane fursuna yana sanye da na’urar bin diddigi a hannu ko ƙafa, wadda ke sanar da jami’an tsaro duk wani yunƙurin tserewa ko tada hankali, kuma hakan yana haddasa hukunci nan take.
Ana gallazawa fursunoni da yunwa, sanyi ko zafi, hukuncin tsayuwa na tsawon awanni, da aikin dole Matsin tunani da wulakanci sun fi bulala zafi Kowane kuskure yana jawo hukunci nan take, babu sassauci
Ayyukan da ake tilasta musu sun haɗa da haƙar ma’adanai, noma a gonakin sarauta sassaka da gyaran ƙarfe fasa duwatsu, da ɗaukar kaya a ƙarƙashin ƙasa.
Abinci kaɗan ake ba su ruwa kuma sai an auna shi Wani lokacin ma in za'a basu abinci watsa musu shi akeyi a kasa ko a jikin su kamar dabbobi haka zasu bi suna ci Ba su da ikon magana sai da izini
A wannan kurkuku, rai ba shi da daraja Bakin Kurkuku ba kurkuku kaɗai ba ne makabartar rai ce Yawancin fursunonin da ake kaiwa ciki wlh azaba ce ke kashe su Kullum ne sai an fitar da gawarwaki
Amma akwai rai guda ɗaya da ya yi tsawaicin kwana yana numfashi a cikin wannan wuri na azaba
A cikin ɗaya daga cikin ɗakunan deep cells, akwai wani magidanci da ya shafe shekaru yana rayuwa tsakanin wahala
Yana zaune a kan tsohuwar katifar gadon ƙarfe jikinsa jingine da bango, yana sanye da tsoffin uniform na fursinoni mai ɗauke da lamba, kansa a langwa6e yake da bangon kamar ba rai a tattare da shi hargitsastsiyar sumar kansa da take doguwa buzu buzu kamar ta mahaukata duk ta rufe fuskarsa har ba'a iya ganin idanuwansa, ba dan raunannan Numfashin da yake fitarwa a hankali ba da sai a ɗauka gawa ce, ahalin yanzu Idanunsa sun dusashe sakamakon duhu da tsananin wahala, kwamtsa ta cikasu ta yadda ko buɗe su bai iyayi
Fatar jikinsa cike take da tsofaffi da sababbin tabo na bulala, na duka, Hannayensa sun cika da karce-karce sakamakon shekaru na fasa duwatsu, noma, da haƙar ma’adinai Wasu daga cikin yatsunsa ma har sun fara nakasa
Idanunsa sun sha ganin bala’i Sun jure daruruwan darare ba tare da bacci ba
Hawaye har sun daina fita idan zai yi kuka Abin da ya rage masa shi ne kukan zuciya wanda ya fi raɗaɗi fiye da na ido Duk da haka azabar zuciyarsa ta fi duk raunukan jikinsa zafi
musamman idan ya tuna mummunar kaddarar da ta same shi da ahlinsa mafi soyuwa a gare shi
Shi kansa yana mamakin yadda ya ke raye har zuwa wannan lokaci ba tare da bakin ciki da ƙunci sun kashe shi ba Ya yi imani cewa lokacin mutuwarsa ne bai yi ba.
Duk da tsananin halin da yake ciki hankalinsa bai gushe ba Zuciyarsa ba ta manta da ambaton Ubangiji ba Bai karaya ba bai kuma yanke ƙauna da rahamar Allah ba A kowane hali na lafiya ko rashin lafiya bai bar ibadarsa ba, ko da kuwa a zuciyarsa kaɗai ne zai yi ta
Yawancin waɗanda aka kawo tare da shi duk sun mutu Wasu sun kashe kansu saboda tsananin azaba Amma shi ko sau ɗaya bai taɓa tunanin kashe kansa ba Duk da ya sare da rayuwar duniya komai ya fita aran shi, ba shi da wata fata a duniya face mutuwa saboda ita kaɗai ce sauƙi agare shi
Farkon kawo sa Prison din Ana azabtar da shi fiye da sauran fursunoni, sai lokacin da rashin lafiya ta tsananta agare shi kaɗai ake raga masa
Abin da ya ɗaure zukatan sauran fursunoni gare shi shi ne kyawawan halayensa abaya kafin yanzu Tun da daɗewa yana raba abincinsa ga waɗanda ba su samu ba, yana taimaka wa kowa gwargwadon iko, duk da mawuyacin hali na azaba Har ma Wasu fursunoni suna cewa ayyukansa na mutanen aljanna ne Wasu kuma suna shakkun ko ya akayi ya aikata laifin da ya kai shi kurkukun saboda mutum mai irin kyakkyawar zuciyarsa da wuya a same shi da laifi Amma sanin zuciyar bawa sai Allah.
Hatta Yan uwansa fursinoni tausayin shi su ke ji..
A kowane mako sau biyu kawai ake ba da sassauci ga fursunonin deep cells, irin ranar kafuwar hamshaƙiyar daular, da ranar haihuwar (sarkin sarakunan da ke mulki yanzu), wanda al'umma sukewa laƙabi da fir’auna saboda zaluncinsa Duk wani sarki kan yi yafiya ga fursunoni a farkon hawansa, amma wannan *BASARAKEN* bai ɗauki rayukan bayi da fursunoni da muhimmanci ba, face kamar dabbobi.
"Ƴa'ƴana! Ahlina" sune kaɗai kalaman da suke fita abakinsa a duk lokacin da wani ya nemi da ya yi magana ...
Shin wanene wannan bawan Allahn?
Wane laifi ya aikata har ya faɗa wannan makabartar rayayyun?
Me ya sa labari ya fara da shi?
*Daga alƙalamin Boss Bature💋*
