Masarautar Alhamra Page 1 by Asmeetah Writer

 

Masarautar Alhamra Page  1 by Asmeetah Writer

*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* 


_🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_

✍🏽 By ASMEETAH WRITER

~Hasken Jajirtattu~

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

*(J.W.A)*

_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.



   ```JARUMAI WRITERS TEAM``` 



⚠️ SANARWA MAI MUHIMMANCI ⚠️


Wannan littafi dukiyata ce a matsayina na marubuciya.

⚖️ Ba a yarda wani ko wata ya:

kwafa

gyara

sauya

ko amfani da wani sashe na wannan labari

ba tare da izini na kai tsaye ba.

Duk wanda ya saɓa, alhaki yana kansa..


📢 SANARWA GA MASOYAN KARATU 📢

Daga yau, za a fara turo sabon littafina:

🔥 MASARAUTAR ALHAMRA 🔥


📌 COMMENT SECTION an tanada shi ne domin:

sharhi

ra’ayi

tattaunawa akan littafin kawai

❌ Ba a yarda:

turo link

talla

ko turo wani littafi a comment section



▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇

🔗 WhatsApp Channel:

https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43


💬 Comment Section Group:

https://chat.whatsapp.com/ERHR7h6oEY76fTvAQFZauw


📚 ArewaPen:

https://arewapen.com/u/asmeetahwriter


📖 Wattpad:

https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter


🎥 YouTube (Audio & Reading):

https://www.youtube.com/@AsmeetahNovel


📲 Contact:

09065443871


📅 FARA TURA BOOK:

🔥 01 — 01 — 2026 🔥


📘 BOOK ONE 

           ```MATAKIN FARKO``` 


CHAPTER  1️⃣ 


 *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ*



A tsakiyar wannan ƙaton almara, an gina babban fadar sarki. Ginin da kansa wata shaida ce ta mulki, komai an yi shi ne don nuna girman iko...

Cikin wannan Fada, a babban ɗakin mulki, an ajiye kujerar sarauta wanda sai da aka narkar da dubban Ton na Zinare kafin aka gina ta, tana haskaka dukkan ɗakin da haske mai yalwa.

A kan wannan Kujerar izzah, Sarki NOURDEEN yake zaune.

Yana sanye da rigar sarakuna mai nauyi, wanda aka zana masa Gwal mai yawa a jiki. Amma abin da zai sanya ko wane mutum ya daskare a mazauninsa shine kansa da jikinsa ba siffar mutane yake ɗauke da ita ba.

Tsayayyen mutum ne, amma kansa da fuskarsa irin na Basaraken Zaki ne!..


Gashin zakin ya rufe wuyansa da ƙirjinsa, yana kwance har zuwa kan rigarsa. Ya sanya hular sarauta mai ƙayatarwa a kansa, wanda ya ƙara bayyana girman Ikon Sa na halitta. 

Wannan siffar zaki ba halitta ba ce, tsafin Iko ne mai zurfi da ya yi domin ya tabbatar wa duniya cewa, Shi ba mutum bane, shi ne MULKI!.


Wannan tsafi an yi shi ne don ya dasa tsoro da fargaba a cikin zukatan dukkan mutanen Alhamra City da ma duniya gaba ɗaya. Ba wanda ya taɓa sanin Ainahin kamannin Sarki...


Ba mai izzar da ya isa ya haɗa ido huɗu da Zaki Nourdeen.

Idan ka yi kuskuren haɗa ido, ba za ka sake yin bacci cikin daɗin rai ba. Saboda kwayar idanunsa ba ta mutane ba ne, haske-haske take fitarwa wanda ke iya kama ruhin mutum mai laifi cikin sauƙi.


Sarki Nourdeen yana zaune cikin wannan izzah mai kisa, kuma a gefensa akwai Zabga-Zabga Fadawa masu ƙarfin tsoratarwa.

Rundunar Masarautar an raba ta zuwa Tsare-Tsare masu Muhimmanci..


Rundunan Yaƙi..

 Waɗannan su ne Jikin Sarki na Waje, ƙarfaffu waɗanda ke shirye a ko wane lokaci Sarki ya yanke shawarar fita yaƙi da duniya...


Bodyguards. Waɗannan su ne ƙashin-Bayan Sarki, aikinsu shine tsare cikin masarauta da kuma kiyaye sirrin Fada...


Security. Su ne jinin da ke gudana a masarautar. Kowannensu da aikinsa. Wasu a cikin Share-Sharen ƙaton Masarauta suke, wasu suna kula da Flowowi, wasu kuma suna kula da kayan alatu na Fada.


Bayi Mata, waɗanda suke kula da Girke-Girke da Wanke-Wanke da sauran Ayyuka masu dama.


A masarauta mai girma irin Alhamra, aiki baya ƙarewa, kuma kowa yana da matsayin sa wanda ba a canzawa...

       

                       ✨✨✨


A yau ne Sarki Nourdeen yake zaune cikin izzah. Yana tare da manyan masu kuɗi (Billionaires) na Alhamra. Duk da kuɗin su, suna zaune ne akan ƙananun kujeru na girmamawa, kansu a durƙushe ƙasa kamar yadda ya dace da darajar Sarki Zaki.

Taron ya shafi kasuwancin Gine-ginen zamani ne da kuma yadda za a ƙara yawan Kuɗin masarautar...


Wani daga cikin masu kuɗin, Alhaji Hadi wanda ya fi shahara da kwaɗayi da rashin tausayi, ya dafa hannu a jikin ƙaramar Kujerar sa ya ce,


"Ya mai martaba, sarki mai Izzah! Mun shigo da wata Arkalla domin tsarin ci gaba ya tafi dai-dai, dole ne mu ƙara haraji a kan talakawa da suke zama a titin ƙasa. Wannan zai tilasta musu su sayar mana da filayen su, sannan mu gina ƙarin Gine-ginen Alatu a wurin. Za mu cutar da su kaɗan, amma hakan zai inganta mulkin ka."


Sarki Nourdeen ya jinjina kansa kaɗan, wanda ya yi kama da rakaɗa na Zaki (Lion’s nod). Fuskarsa ta ƙara murtuƙewa har ta bada asalin tsoro ga kowa..


Sarki Nourdeen, duk da girman kai da izzar da ke dasa tsoro a zuciyar kowa, bai goyi bayan ZALUNCI ba.

Ya ɗaga hannun Zakin sa mai nauyi, ya ajiye a kan kujerar zinarensa.

 Muryarsa mai ƙarfi da zurfi ta ratsa dukkan ɗakin...


"Ku dawo da wannan Arƙalla. Alhamra ba ta buƙatar ƙarin kuɗi da aka samu ta hanyar ZALUNCI. ZALUNCI ga talakawa shine RAUNI ga Mulki na. Ba zan goyi bayan hakan ba. Ku tashi, ku sake kawo shawara mai tsafta."...


Alhaji Hadi da sauran masu kuɗin suka tashi cikin sanyin jiki, suka durƙusa ƙasa suna ba da haƙuri...


A cikin babban masarautar Alhamra da ke cike da ƙarfe da zinare,  wata yarinya siririya kyakkyawa da ba za ta wuce shekara goma sha shida 16 ba. Ita ce Gimbiya FIRDOS, wacce aka fi sani da Chingching..


Chingching ta fito ne daga tsararren filin wasan ƙwallo da ke cikin Area part ɗinta wanda ba nisa sosai tsakani da babban fadar sarki.... 

Tana sanye da gajeren wando na ƙwallon ƙafa tana wasa da ƙwallo a hannunta, alamun ta gama wasan ne. Duk da sanyin masarautar, jikinta duk gumi ne wanda ke nuna ƙarfin hali da rashin natsuwa da take da shi..


Security masu tsaron part ɗinta ne suka biyo ta da gudu suna son dakatar da ita, domin in har akayi garajen barin gimbiya ta fito sararin masarauta to akwai tashin hankali...


Chingching ganin anason dakatar da ita kafin ta isa fadar sarki yasa ta ƙara wa manta gudu, tana gudu tana buga ball ɗinta, sumar gashinta na tsalle yana faɗa wa kan gadon bayanta..

Kasancewar ta ƴar shafal da ita yasa bata jin nauyin jikinta da gudun da take kuma ta saba motsa jiki..


Bodyguards na area masarauta ganinta yasa  suka rufa bayanta da gudu har sai da ta shiga Area fadar Sarki, tana ci gaba da buga ƙwallon a bakin ƙofa. Ba ta damu da Doka ba...



A lokacin da Chingching ta nufi cikin babban ɗakin mulki, ta yi kucuɓus da masu Kuɗin da suke shirin fita. Su suna guduwa ne daga cikin fadar saboda harzukan Sarki Zaki da suka gani...


Cikin sauri da rashin sani mutanen suka ture ta a wajen ƙofa. Tangal-Tangal tayi da niyyar faɗuwa ƙasa. A firgice, wasu mata ma'aikata suka yi saurin riƙo ta. Sun san cewa idan har Gimbiya ta taɓa ƙasa, to tabbas Sarki Zaki zai ɗauki hukunci mai tsanani..


Mutanen jikinsu na rawa saboda tsoro, suna ba da haƙuri ga ma'aikatan da Gimbiya.

Sarki Nourdeen ya miƙe tsaye a kan kujerarsa a fusace, fushin Zaki ya bayyana fili! Ganin ƙaramar Gimbiyarsa, wacce ya fi so fiye da komai, an ture ta.

A zabure, masu kuɗin suka durƙusa ƙasa gabansa, suna ba Sarki haƙuri cikin firgici.

Cikin shagwaɓa mai tsanani ta nufi Sarki, tana faɗin.


"Daaaad..."


Ta kwantar da kanta a kan faɗaɗɗen ƙirjin Zakin sa, wanda ke da tsafin gashi mai laushi. Cikin sanyin murya da shagwaɓa ta ce


"Ka rabu da su, by mistake ne..."



Muryar Sarki, wacce ta kasance cikin tsawa da kaifi ga masu Kuɗin, ta zama mai laushi da natsuwa a yayin da yake magana..


"Ku durƙusa a gaban  Gimbiyata, ku ba ta haƙuri," Zaki Nourdeen ya ce. "Amma kada hannunku ya gogi fatar jikinta. Domin ita ɗin Gwal ce mai mahimmanci a rayuwata..."


A ruɗe masu kuɗin suka durƙusa wa Chingching suka ba ta haƙuri.

Cikin shagwaɓa ta musamman, ta ce


"Uhm! Uhmm!! Uhm! Na yafe muku..."


Cikin farin ciki da mamaki suka fara yin godiya. Daga nan Sarki ya sallame su.


Bayan masu kuɗin sun tafi, Sarki ya fara huci saboda fushin da ya danne. Ya umarci a ƙira masa waɗanda suke kula da Chingching, wato  ma'aikatan part ɗinta.


Ya kalli Chingching, yana gyara mata gashin gaban goshinta da hannun Zakin sa. Haka yake goge mata zufar goshinta zuwa wuyanta tare da faɗin.


"Ina kika shiga kika yi zufa haka?"


Chingching tana shagwaɓar da ta saba, ta ce


"Uhm! Uhmm!! Dadd, ƙwallon ƙafa nayi..."


Sarki ya sake tambaya  "Ke da su wa?"


Ta sunkuyar da kanta kaɗan.


"Uhm uhmm Dadd, ni kaɗai. Ba ka hanani shiga cikin bayi ba."


Muryar Sarki ta sake yin ƙarfi ya ce,


"Tabbas na hanaki! Domin duk sanda na ganki da su, sai na hukunta su. Abin da ke da daraja baya wulakantuwa."



Dai-dai lokacin, waɗanda suke kula da Chingching suka shigo da sallama, kansu a ƙasa suka durƙusa cikin girmamawa.

Sarki ya dube su cikin fushi ya ce


"Meyasa kuka bar Mamana ta fito daga yankinta? Kun karya min dokata! Domin a tsarina, gimbiyoyina ba za su taɓa fitowa cikin Masarauta ba tare da wani dalili ba..."



Altine, wacce ke asalin kula da ita, tana rawar jiki ta ce


"Ranka ya daɗe, a gafarce ni. Ita ta dage akan dole sai ta fito. To bamu da hurumin hanata, domin hakan zai iya jawo mana matsala idan bamu mata abinda take so ba..."



Sarki ya daka musu wani irin gigitaccen tsawa har sai da suka zabura da niyyar guduwa amma suka dakata!


"Dole a bi umarnina, amma kuma dole ku mata abin da take so! Shin meye abinda babu a part ɗinta? Bana buƙatar fuskar Gimbiyata ya zamo madubi ga ko wani dabba."


Altine wacce take rawar jiki har yanzu ta ce


"Akwai komai a bangarenta,  komai akwai. Tafi son na outside ne. Amma Allah ya taimaki ran Sarki, bazamu ƙara wani kuskure ba..."



Ita kuma Chingching tana ta wasa da gashin Zakin Sarki wanda ya zamo kamar gemu. Sai murɗawa take tana dariya.

Duk tsawar da Sarki yake yi, a kunnen Chingching murya ne mai sanyi da laushi. Ya sanyaya muryarsa a kunnenta, yayin da muryarsa ta zama kibiya a kunnen kuyangensa.

Bayan ya gama huci, ya riƙo hannun Chingching ya ce


 "Ku kaita part ɗinta, ku yi mata wanka."


Chingching ta kalli siffar Zakin mahaifinta, ta tambaya


"Dadd, meyasa kake canza kamanni zuwa Zaki?"


Sarki ya kalleta da Idanuwansa masu haske ya ce


"Mamana, a duk lokacin da na kasance da ku kaɗai  Gimbiyoyina, ni cikakken mutum ne. Amma a gaban idon mutane na, ni Zaki ne kamar haka."



Chingching tayi murmushi tana kallon mahaifinta, Altine ta riƙo hannunta  sannan suka tafi. A saman doki aka ɗaura ta aka nufi da ita can part ɗinta wanda ta kasance ita kaɗai sai masu kula da ita..


A hankali ake tafe da ita daga saman dokin. 

Nan aka shige da ita cikin wani tsararren part..

 Yanki ne wanda ke nunawa kowa cewa Ita ce Gwal mai mahimmanci!

Part ɗinta wani irin gini ne mai ƙayatarwa wanda ya yi kama da dreaming part kamar an tsamo shi daga littafin Almara na Gine-gine.

A can gefe, akwai kayan wasa masu tsada.. Ƙayataccen filin ƙwallon ƙafa da handball wanda ta fito daga ciki...

Sai dai, dole sai an hau saman Upstairs wanda yake da tsayin da ba kowa zai iya juran hawa koda yaushe ba inba wanda ya saba yau da kullum ba, koda wanda ya saba ma sai ƙafafunsa sunyi ciwo kafin a shiga Babban Falonta...

Shiyasa ma'aikatan ta kullum a cikin shan maganin ciwon jiki suke.

       

Abun mamaki ita ƙaramar gimbiyar yanda kasan ta samu wurin wasa haka ta mayar da matakalan, tana jumping tana wasa kamar wacce take exercise, nan danan ta haura kamar biri...


Daƙyar suka ƙaraso suka isketa a falo.

Falon cike yake da kayayyakin alatu ga ƙaton plasman a manne a jikin bango, Fridges masu tsada, da Flowowi. Komai yana da tsari da daraja...

A saman can ne bedroom ɗinta yake wanda saika sake hawa wani benin..

     Gado ne katafaren gado wanda aka yi masa zane da fararen kayan alatu, wanda ya dace da Gimbiya....Cikin wannan ɗakin kwana ne wani keɓaɓɓen ɗakin kayayyakin sakawa da ke cike da tsararrun kaya na Sarauta yake...


Sai dai cikin bedroom ɗinta ba kowa ke zuwa ba sai Uwar ɗakinta wato Altine. 


Chingching ta shiga bedroom ɗinta cikin kasala bayan gajiyar ƙwallo.


Ta tsaya tana riƙe da kunkumi idonta akan Altine wacce ta shigo...


"Uma Altine! Kin ga gumin nan? Na gaji sosai fa! Yau ƙwallon nan ta gajiyar da ni, kuma Dadd ya ce kar na sake fita, amma ni ina son outside ɗin nan!"


Altine tana rarrashinta ta ce,  "ki yi haƙuri ki cire saina miki wankan ko..."


Ɗan tsaki ta ja cikin damuwa da gajiyar da tayi cikin hanzari, ta cire kayan jikinta wanda gumi ya jika, sannan ta ɗaura towel mai laushi ta shige bathroom..


 Altine ne ta ɗauki kayan da ta cire a ƙasi don kai su washing machine da ake wanke kayanta...


Ita kuwa Chingching tana shiga Bathroom ta shige cikin Bathtub mai girma ta zauna..


Bathroom ɗin ba ƙaramin ɗaki ba ne, tsaruwarsa sai ta sa ka zuba abinci a ƙasin wurin ka ci saboda tsaftar wurin da tsarinsa. Wani irin ƙamshi mai daɗi da tsada ne yake fita. Tiles ɗin ƙasan ma ɗumi ne da shi a yayin da kake takawa...


Bayan mintuna kaɗan

Altine mai kula da ita ta shigo ciki domin taya ta wanka, domin har yanzu Chingching bata iya wanka da kanta ba saboda gata da ta saba samu..


Wani irin kallo Chingching ta yi mata cikin shagwaɓa ta ce, 


"Uma Altine, kin san fa na gaji, kuma kike ƙara gajiyar da ni, don kawai kin ga ina da kyau shine zaki bar ni haka..."


Altine murmushi tayi sannan ta ce,  "Ƴar uma yau kuma me nayi?..." 


Chingching tana turo baki ta ce,  "tin ɗazu inata jira, ina ta jira a cikin ruwan zafi..."


           "To ki yi haƙuri Ching Ching..."


Murmushi Chingching tayi domin tana jin daɗin sunan nan especially idan aka furta cikin launi,  sunan ya samo asali ne daga tin tana ƙarama ƴar 2years ta ji ana ƙiran mahaifinta da King, itama tace sunanta Ching ma'ana King.. Anan ta samo Chingching....



Da ɗan ƙaramin part a ƙirjinta, Altine ta fara mata wanka sai ƴan ƙananun nonuwa a bayyane...

 Ita kuma tana Pressing ƙaton wayarta ta zamani wanda ke da tsadar gaske da aka kawo mata daga ƙasar Turai...

Ba komai ne a cikin wayan ba domin babu sim sai gema–gemai da finafinai..


Tana danna waya, tana complain, 


 "Wash! Wannan ruwan ya yi zafi! Uma Altine, karki murzani sosai mana, kin san fatata ba irin taku ba ce, ni fa Gwal ce kamar yadda Dadd ya ce!"


Altine tana murmushi tana mata, ta san cewa Chingching surutunta baya ƙarewa. Bayan an gama mata wanka da turarukan da ƙamshinsu zai iya sumar da mutum,

aka goge mata jikinta da white towel mai laushi tare da fefesa mata turaruka masu ƙamshi mai ƙarfin gaske.

Aka sanya mata tsararrun kayanta na Alhurma mai tsadar gaske wanda ya nuna asalinta na Gimbiyar Sarauta. Tana zaune a gaban mirror da fitilu masu haske da suke haskawa, ana tsara mata Make-up  da kuma salon gashi mai kayatarwa.


 Tana kallon kwalliyar da Altine ke mata, tana gyara mata daki-daki..


"A'ahhh Uma Altine, ni wannan kwalliyar bai mun kyau ba, a goge a sake yin wani..."


Anyi hakan ya kai sau huɗu, a tsara kwalliya a sake gogewa kullum a cikin haka ake..


Daga ƙarshe ne Altine ta ce,   "idan aka sake goge wa ai fuskar zata ɓaci..."


Tana turo baki ta ce,  "Allah? To a bar shi amma nasan ban yi kyau ba..."


"Kin yi kyau mana gimbiyata..."

   

"Uhm! Uma Altine kenan, idan a mijinki ne zaki tsaya ki tsara masa kwalliya a kan ki, nine bakya tsaya wa ki mun mai kyau..."


Uma Altine ba abin da take sai murmushi domin ta san halin, abun complain baya mata kaɗan..


Bayan an kammala kwalliya. Ba ƙaramin  kyau tayi ba ta bugawa a jarida,  Altine ta kalle ta da murmushi na gaske sannan ta ce,


"Gimbiya Chingching ta fito tayi kyau tsaf! Yanzu kuma mai ake buƙata? Abinci gashi can an shirya miki kala-kala, sai wanda kika zaɓa. Ko kuma kwanciya za ki yi ki sha baccin ki? Ko dai kallo za ki yi? Duk fim ɗin da kike so akwai. Muna sauraron Gimbiya..."


Chingching tayi murmushi mai ɗauke da dabara, tana gyara sakun makeken gilashinta na Gwal. Ta ce da mafi girman shagwaɓar ta...


Mu sauƙa falo tukun...

      Hakan kuwa akayi, a falon suka tarar da sauran ma'aikata mata ko wacce da uniform ɗinta na aiki..


Chingching tana tsaye duk ta ƙare su da kallo sannan ta ce,


"Abin da nake so yanzu shine inason ganin Gimbiya Auntyna ta musamman!"


Altine da sauran ma'aikatan duk suka zaro ido a ruɗe. Wani irin haɗiyar yawu suka yi, a tsorace suka ce.


"Dan Allah Gimbiya, kiyi mana afuwa, ki zaɓi abin da kike so bayan wannan!"


Altine ta ci gaba da faɗi da murya mai rawa


"Kin dai san wannan dokar takun a rubuce take. Cewar a shekara sau uku ne za ku na haɗuwa da juna a Babban Fadar Mai Martaba. Yanzu idan yaji labarin mun karya doka, dole za'a hukunta mu..."


Chingching ta ɗan turo baki irin sakalan yaran nan ta ce,


"Ai naga, naga, bazai sani ba. Kawai ku kaini a ɓoye..."


Altine, wacce dattijuwa ce a tsakaninsu, ta yi saurin durƙusawa ƙasa, tana roƙon Chingching da ta bar wannan batun. Hawaye ya fara zuba a idanunta.

Chingching ganin yanda Altine take zubar da hawaye ne yasa ta jin tausayinta. Ta ce.


"Uma Altine, ki daina kuka. To, to, to, ni na haƙura maaa..."


An ɗan rarrashi Chingching, ta ci abinci duk da kaɗan take ci, amma ko wani kalar abinci sai tayi test ɗinsa..ita ko a Film daga kalar abinci sai tace a mata irinsa, da haka ne kwanakin baya taga wani kalar abinci a Chinese film tace nan duniya sai taci irinsa, ko da aka mata taci ta rinƙa amai kamar hanjin cikinta zai fita har sai da likita ya duba ta... A ranar kuwa waɗanda suka mata girkin basu sake kwana a cikin masarautar ba bayan hukuncin da aka yi musu...


Sai da ta kammala ciye–ciyenta sannan ta kalli Altine ta ce.


"Uma Altine, inaso zanyi Sallah, sannan nayi bacci..."


Altine tana murmushi ta ce,  "mu je na rakaki bedroom ɗinki to..." 


Chingching ta ɗan turo baki ta ce,  "ina jin bacci sosai, don haka bazan iya haurawa sama ba..." 


Altine ta san kan kwanan zancen, indai ta fara da haka to goyo take so...


Sunkuya wa Altine tayi sannan Chingching ta ɗale baya tare da kwantar da kanta..


Altine ta nufi saman bedroom da ita, tana zuwa ta sauƙe ta sannan ta ce, 

     "Kin ce sai kin fara yin Sallah ko?..."


Jinjina kai Chingching tayi tana lumshe ido..


Altine ta shimfiɗa mata sallaya, ta zaro mata hijab daga cikin jerin hijabanta na sallah dake kusa, saɓanin sauran kayanta dake can other side na bedroom...


Altine ta san dokar nan. Idan har Gimbiya za ta yi sallah sannan ta yi bacci, to  fita take ta barta ita kaɗai a ɗaki.


Chingching ta tsaida sallah, sannan tayi addu'o'in ta cikin tsarki. Ta kwanta a kan sallaya har bacci ya ɗauke ta a wurin, daman a hannu take...


Bayan wasu mintuna, Altine ta shigo ta same ta a kwance a ƙasan sallaya. Kirjinta ne ya buga. Da gudu ta shigo ta ɗauke ta tare da ɗora ta kan katafaren gadonta wanda idan ka kwanta akai za ka sa ran lotse wa ne tsabar laushi...


An kashe mata hasken ɗaki aka bar mata green lamp light mai natsuwa....



                  ✨✨✨✨


Cikin dare misalin ƙarfe 1:00am, Chingching ta fara mafarkin da ta saba yi kullum a dalilin bege da take yi wa 'yar uwarta.


"Aunty! Aunty!! Aunty!!! Ki zo Aunty! Wayyo Aunty..."


Cikin ƙanƙanin lokaci, sai ta ji an rufe mata baki da wani irin sanyayyen hannu mai laushin gaske kamar sarauniyar audiga.

A hankali, Chingching ta ɗan buɗe lumshashshun idanuwanta wanda bacci yake faman yaƙi da su. Ta sauƙar da kallonta akan kyakkyawan idanun wacce ta rufe mata baki...


Idanuwanta yanda kasan an tsaga su, gasu manya-manya, gasu farare tass. Eyelashes zara-zara, ga wasu cikakkun gashin girarta a kwance wanda suka kusan haɗewa biyu. Hasken fatarta fari ne tass irin farin Larabawa.

Amma sai dai, ba'a ganin fuskarta complete domin a rufe yake da kyalle mai sheƙi. Sai iya dara-daran idanuwanta da gashin girarta ake gani. Ta kewaye gashinta da fuskar gaba ɗaya cikin sirri mai zurfi.

Haka take kallon cikin idanuwan Chingching da nata.

Chingching a hankali ta furta: "Aunty..."

Daga nan ta lumshe idanuwanta gaba ɗaya, bacci ya ƙara ɗaukan ta cikin natsuwa...


Wasu zafafan hawaye ne suka gangaro a fuskar wacce Chingching ta ƙira da Aunty. Haka take kallon fuskarta tana bacci, a yayin da take shafa mata sumar gashinta tana hawaye tana mata addu'o'i kamar yanda ta saba zuwa cikin dare ta ga 'yar ƙanwarta. Domin tasan a wannan lokacin take mafarkin bege da kewa.

Tana zaune, tana taya Chingching zama har tsawon awanni. Idonta yana kan ƙanwarta da aka hana ta gani. Sai dab da asuba kafin a ankara, ta tashi, ta bi ɓoyayyen hanyarta ta tafi cikin sirri mai zurfi zuwa Part ɗinta.....



 ```TOH MA SHA ALLAH ABOKAI, MASOYA, ƳAN UWA.``` 

 ```ALLAH YASA WANNAN FARKON PAGE ƊIN SABON BOOK ƊIN MU YA NISHAƊANTAR....```


 ```YANDA ZAN GANE CEWA KUN JI DAƊIN BOOK ƊIN TO NAGA COMMENTS, LIKES, SHARES...```


 ```WAƊANDA BASU YI FOLLOWING ƊINA A CHANNEL BA YANZU DAMANE TA HANYAR KARATU A SAUƘAƘE, KODA AN WUCE KI BAZAKI RASA YANDA KIKA TSAYA BA, DOMIN CHANNEL DUNIYA NE...```


 ```WAƊANDA SUKE SON YIN COMMENTS SU FAƊI ABUNDA KE RANSU AKAN LITTAFIN TO KUYI JOINING GROUP.. KADA KU BARI AYI BA KU...```

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post