*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑*
_🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_
✍🏽 By ASMEETAH WRITER
~Hasken Jajirtattu~
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.
```JARUMAI WRITERS TEAM```
⚠️ SANARWA MAI MUHIMMANCI ⚠️
Wannan littafi dukiyata ce a matsayina na marubuciya.
⚖️ Ba a yarda wani ko wata ya:
kwafa
gyara
sauya
ko amfani da wani sashe na wannan labari
ba tare da izini na kai tsaye ba.
Duk wanda ya saɓa, alhaki yana kansa..
▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇
🔗 WhatsApp Channel:
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
💬 Comment Section Group:
https://chat.whatsapp.com/ERHR7h6oEY76fTvAQFZauw
📚 ArewaPen:
https://arewapen.com/u/asmeetahwriter
📖 Wattpad:
https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter
🎥 YouTube (Audio & Reading):
https://www.youtube.com/@AsmeetahNovel
📲 Contact:
09065443871
📅 FARA TURA BOOK:
🔥 01 — 01 — 2026 🔥
📘 BOOK ONE
```MATAKIN FARKO```
CHAPTER 2️⃣
*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ*
Bangaren Gimbiya Ayat wuri ne da aka gina shi da zurfin ilimin fasahar zamani. Baya ga kwarjinin sa, part ɗin yana da girma da faɗin da mutum zai iya ɓace wa a cikinsa idan bai saba da hargitsatstsen tsarin sa ba.
Domin isa zuwa inda Ayat take, dole ne ka hau wasu tsalallekun benaye masu nisan gaske. Saboda girman wannan nisan, akwai na’urar nan ta zamani mai tafiya da kanta wato escalator wadda take ɗaukar ma’aikata da dakarun tsaro zuwa can sama.
Bayan dogon benin da kowa ya sani, akwai wata Hanyar Sirri ta musamman wadda Gimbiya Ayat kaɗai ta san da ita. Wannan hanya tana amfani ne da wani babban na'ura mai daukar mutum elevator wanda aka ɓoye shi a wani guri da idon dan Adam ba zai iya gani ba.
Idan zai yi sama, wannan elevator ɗin yana tsayawa ne a wani ɗaki na musamman. Kana buɗe ƙofar ɗakin nan, zaka tsinci kanka a tsakiyar babban ɗakin kwanciyar Gimbiya Ayat.
Idan kuma ƙasa mutum zai yo, dole ne ya shiga ta wannan ɓoyayyen ɗakin dake cikin bedroom ɗinta, inda elevator ɗin zai lula da shi har zuwa ƙarƙashin ƙasa.
A can ƙarƙashin ƙasa, akwai wani katafaren gidan ƙasa mai ɗauke da doguwar hanya. Wannan hanya tana miƙewa ne har zuwa wajen yankin Gimbiya Ayat, inda zata fitar da mutum ta bayan filin masarauta, daidai inda Garden Area yake.
Ta ƙarƙashin ƙasar, akwai wasu matakala da mutum zai hau, sannan ya tura murfin ramin ya fito. Wannan wurin yana ɓoye ne a cikin ciyayi da furannin lambun masarauta, ta yadda babu wanda zai taɓa zargin cewa akwai rami a wurin. Da zarar mutum ya fito, zai tsinci kansa a cikin lambu, daga nan kuma sai ya samu hanyar da zata kai shi babban filin masarauta.
Wannan ginin an ƙera shi ne da dukkan alamu domin tserewa daga barazana kamar gobara, harin maƙiya, ko ɓarayin ƴan fashi.
Wannan hanyar shine hanyar sirrin Gimbiya Ayat, tanan take fita daga part ɗinta ba tare da kowa ya sani ba, saita nufi hanyar part ɗin ƙaramar ƙanwarta Chingching...
Sannan ta wannan hanyar take komawa part ɗinta dake can sama cikin lafiya...
Wannan wurin yana nuna Matsayinta na Gimbiya da kuma Izzar da take ɗauke da ita. Iskar da take shiga Part ɗin Ayat mai tsabta ce kuma sanyi mai ɗorewa....
Muryar babban fada da hayaniyar ma'aikata ba sa taɓa kaiwa part ɗin Ayat. A nan ne shuru da natsuwa suke mulki.
AYAT tana ɗaya daga cikin gimbiya ta musamman a cikin su biyar...
Yanzu, misalin ƙarfe 5:00 na Asuba, bayan ta dawo daga aikin sirri na ziyartar ƙanwarta, tana zaune a cikin babban falon ta. Falon yana cike da kayayyakin larabawa na zamani..
Tana zaune a kan doguwar kujerar larabawa wacce aka yi mata zane da zinare. Tana sanye da Kayayyakin Sarauta masu daraja, amma abin da ya zama Alamar ta shi ne....
Fuskarta a rufe take koda yaushe!
Wannan ba dabi'a ba ce, dokar sirri ce.
Wani kyakkyawan mayafi ne wanda aka ɗinka da zaren azurfa ke rufe daga idanunta zuwa ƙasa... Wannan ya sa Idanuwanta suka zama abin tsoro da kuma abin sha'awa.. Waɗannan ne dara-daran idanuwan da Chingching ta gani a daren jiya...
Sarki Nourdeen, mai izzar Zaki, ya daina ganin fuskar Gimbiya Ayat tun tana ƴar shekara biyar. Wannan ya faru ne sakamakon wani al'amari mai girman gaske da ya faru a shekarun baya, wanda ya shafi sirrin mulki da kuma ƙaddara.
A masarautar, an cika ɓoye wannan al'amari, wanda hakan ya sa Ayat ta zama alamar sirri a idon kowa...
Tana zaune, jikin ta ya gaji saboda karya dokar da take yi kusan kowane dare don ƙaunar ƙanwarta. A hannunta ko tana riƙe da ƙaramin akwati da aka yi masa zane na tarihi, wanda a cikinsa take adana hotuna na Firdos da kuma hoton wanda ta rasa tin tana ƙarama...
Ayat ta ɗauki mulki a matsayin nauyin ƙaddara, ba walwala ba. Tana ganin tsaurin kan mahaifinta zai iya rushe masarautar Alhamra idan har bai sami magaji ba....
Ta tashi, ta nufo wani babban mirror mai haske, ta kalli idanuwanta a ciki.
Cike da tausayin kanta ..
"Kina karya doka, Gimbiya Ayat! Kin saɓa wa umarnin mahaifinki wanda ya fi ƙaunar rayuwarki fiye da kowa. Amma idan har wannan dokar tana cutar da ruhin ƙanwarki, to dole ne ki zaɓi tsakanin Doka da ƙaddara," Ta faɗa a cikin muryar larabci mai ƙarfi, mai shiga zuciya.
Ayat zama tayi bayan ta gama kallon kanta a jikin mirror duk da fuskar a rufe yake, a kan tsararren Sofa na falonta ta zauna.
Duk da kayan alatu na sarauta da ke kewaye da ita daga kayayyakin fruits masu tsada a kan ƙaramin table ɗin gilashi zuwa Zane-zanen Azirfa a jikin falon amma damuwar duniya duk ya bi ya ishe ta.
Tana zaune, jikinta a lulluɓe da mayafinta na rufe fuska, amma a cikin idanunta akwai wani zargi da tunanin neman mafita da ke ci gaba da cin zuciyarta.
Tana tunanin mafitar da za ta samu domin gujewa wannan tsatstsauran dokar da aka kafa musu tun tsawon shekaru, tun suna yara. Zama wuri ɗaya a cikin part ɗin ya bi ya ishe ta, amma babban abin da yake tasar mata da hankali shi ne dokar ganin 'yan uwa mata sau uku kawai a shekara.
Cikin zuciyarta, ta fara magana da kanta, muryarta mai ƙarfi da zurfi yana bayyana rikicin zuci,
"Wannan al'amarin yana damu na. Shin ya zanyi? Meye mafita? Shin a haka zamu ƙare rayuwarmu? Babu soyayya, babu ƙawaye! Babu zuwa makaranta sai dai a koya mana a cikin ɗakunan mu. Wayyo kaico na! Wayyo 'Yar ƙanwata Firdos wacce bata san koda mahaifiyarta ba ma sai ni. Tana zaman kadaici. A shekara sau uku zan rinƙa ganinta? Bazai taɓa yiwuwa ba! Impossible!"
Sai ga wasu zafafan hawaye suna zubo mata daga gefen kyallen mayafinta wanda ya rufe fuskarta. Hawayen na nuna tausayi ga ƙanwarta, amma kuma suna tuna mata wani abu mai mahimmanci a rayuwarta wanda shine dalilin da yasa take ɓoye fuskarta har ma ga mahaifinta....
Wannan Dalili ya ta'allaka ne a kan wani babban abokinta wanda ya rayu a cikin wannan Masarauta..
Yaron asalin shugaban wannan masarautar Alhamra wanda yanzu baya raye a duniya, Yayan mahaifinta wanda sai bayan ransa kafin sarkin Nourdeen ya hau...
Sarkin da ya shuɗe yana da yara maza biyu wato twins, ɗaya daga ciki ne babban abokin Ayat, amma kuma a lokacin iyayen nasun suna zaman gaba a tsakaninsu akan mulki.. duk da sun kasance ƴan uwa..
Daga lokacin da shaƙuwa ta soma a tsakanin Ayat da wancan yaron sai mahaifinta ya nemi rabasu lokacin bai zama sarki ba..amma yana neman mulki..
Shima wancan sarkin yayi ƙoƙarin raba ɗansa da Ayat, wannan al'amarin ya faru ne tun suna yara..
Tun daga wannan lokacin ne Ayat take kulle fuskarta da alkawarin,
'Babu wanda zai ƙara ganin fuskata sai shi yaron da aka raba ni da shi...'
Tsawon shekaru har yanzu shiru, babu labarinsa. Bata sani ba shin yana raye ne ko ya mutu. Amma Alkawari ta ɗaukar wa kanta cewa. Shi ne first ɗin ganin fuskarta. Idan kuma ta rasa shi har abada, to kuwa sai idan ta zama Gawa ce za'a ga fuskarta!..
Abin da yake mata yawo a kwakwalwarta a koda yaushe shine. Yadda zata bi don shan iskar duniya.
Hanyar da zata na bi don fita daga cikin Masarauta ba tare da asirinta ya tonu ba, sannan ta dawo lafiya. Tunda take a rayuwarta bata taɓa fita daga cikin Masarauta ba. Bata san ya tsarin garin Alhamra yake ba...
Kamar yadda muka sanar a baya.
Ayat ta kasance tana da ɓoyayyen hanyarta da ba kowa ya sani ba. Hatta Security da Bodyguards na masu gadinta basu san cewa Ayat tana fita daga yankinta ba a kowace rana musamman bayan ziyarar ƙanwarta..
Gimbiya AYAT tana zaune a kan Kujerar Alfarma ta falonta. Tana kallon sararin sama ta katangar gilashin taga mai tsabta wacce ta kewaye Part ɗinta. Zuciyarta cike da damuwa da kuma wani irin kewa mai zafi da ba ta iya bayyana wa kowa ba. Rayuwarta ba komai bace face zuwa ɗaki, daga ɗaki, zuwa ɗaki.
Shekaru Ashirin da Biyar! Amma bata taɓa taka ƙasa a waje ba. Wannan ƙuntatawa shine babban kunci da ke kanta...
Tana cikin wannan tunanin
sai ta ji takun sawu a bakin ƙofar sannu a hankali..
Mai aikin tsaron ta wanda aka keɓe shi musamman domin hidimarta da kuma kula da rayuwarta, ya durƙusa yana danna ƙwanjin notice alamar neman izini kamar yadda dokokin sarki suka buƙata.
Muryarsa cike da ladabi yake faɗin
"Gimbiya... idan nayi kuskure ki gafarta. An kawo sabbin fina-finai daga sashen masarauta. Na tattara miki waɗanda zasu burge ki..."
Ayat ta juyo a hankali, fuskarta cikin izzah da kama kai irin na masarautar su. Ta ɗaga hannu kaɗan alamar ya shigo...
Ya shiga da kwalin fina-finai a hannunsa. Ya durƙusa sosai kafin ya miƙa mata.
"Na tabbatar da ba su da hani kuma ba su da abubuwan da zasu tada al'amura, Gimbiya na ba ki izini ki kalla cikin kwanciyar hankali."...
A takaice ta kalleshi sannan ta furta.
"Izini?..."
A ruɗe ya ɗan rusuna ya ce,
"Ina neman afuwa Gimbiya, a gafarce Ni.."
Ta karɓa cikin nutsuwa.
Lokacin da ya fita, ta yi dariya kaɗan, dariya ta farko wacce ba ta samu damar yi a bainar jama'a ba.
Ta buɗe kwalin tana jera fina-finan a saman tebur. Sai wani babban poster ya ja hankalinta..
MACE A SHIGAR MAZA
Hoton ya nuna wata mace sanye da gashin baki, ɗan gemu, rawani, da rigar maza..
Ta zaro ido kamar an kunna wata fitila a cikin zuciyarta.
"Wannan kuma...?" ta furta a hankali, idanunta suna kan poster..
Ta zauna gaba ɗaya, ta juya kanta gefe, tana murmushi da mamaki...
"Mace ce kuma haka ta ɓace a cikin maza?"
Cikin hanzari ta buƙaci ganin Film ɗin..
Ta kalla cikin nutsuwa, tana lura da kowane daki-daki.
Yadda take sa gemu kamar na maza.
Yadda ta ɗaure ƙirji ta yadda babu alamun mace.
Yadda ta yi tafiya ba tare da wani motsi na mace ba.
Yadda kowa ya amince Namiji ce.
Gimbiya Ayat ta shaƙi iska mai sanyi. Sai ta jingina da kujera ta rufe ido kaɗan.
A karon farko cikin rayuwarta, ta ji irin wannan tunanin mai ƙarfi ya shiga zuciyarta.
"Ni ma zan iya! Ni ma zan iya fita! Ni ma zan iya yin rayuwa kamar mutane!"
A hankali ta buɗe ido. Ta san wani abu guda ɗaya.
Ba za ta taɓa sanar da kowa ba! Ko bawanta mafi amincewa. Ko uwar gidanta. Ko waye domin idan ta furta, ta san cewa za su saka ido su rufe duk wani motsinta...
Cikin nutsuwa ta miƙe ta fara hawa saman bedroom ɗinta da sauri-sauri ganin ma'aikatanta suna ta zarya...
Tana shiga ta nufi ɓangaren mirror sites, ta zauna a dogon kujerar gaban madubi ta fara duba fuskarta da tsantsar damuwa..
Manya-manyan idanuwanta masu kyan gani da sha'awa..
Lips ɗinta masu laushi da cika..
Girarta mai kyau wacce ke nuna 'Yar Halitta..
Ƙirjinta mai kauri da halitta.
Sai kuma ta furta a hankali cikin tsantsar damuwa..
"Taya zan ɓoye waɗannan?"
Ta miƙe tsaye gaba ɗaya. Surarta ce ta mace cikakkiya, da ƙwalliya ta halitta.
Yanayin tafiyarta mace ce ta masarauta.
Breast ɗinta manya ne sosai, ba za su ɓuya da sauƙi ba.
Ƙugunta siriri ne irin na Gimbiya da ba ta yin aiki.
Ta ɗan murza haɓarta irin na fim ɗin da ta gani, tana tunanin.. "Ina zan samo wannan?"
Sai ra'ayoyi na dabaru suka fara zarya cikin kanta.
Tyt mai matse ƙirji (Binding) don gyara Siffar Kirji.
Rigar maza mai faɗi wacce za ta ɓoye kugu da siffar jiki.
Rawani ko turban da zai rufe gashin kanta.
Concealer domin gashin baki.
Daidaita tafiya ta canza daga mace zuwa namiji mai nauyi..
Sallama da murya mai sanyi kamar na maza.
Ta kuma san cewa. Kwamandan tsaron fada na kallo ne sosai... idan ta kuskura ta yi kuskure za a gane.
Amma zuciyarta ta yi ƙarfi sosai akan wannan sirrin.
"Ina bukatar na shaƙi iska. Koda da minti ɗaya ne... Zan fita!"
Tun daga lokacin da ta gama kallon fim ɗin rikiɗewar mace-ta-zama-namiji, zuciyar Gimbiya AYAT bata sake samun nutsuwa ba. Wannan fim ɗin ba nishaɗi bane a gare ta, mafita ce!
Ko da ta kwanta tunanin fita ne a ranta.
Haka inta tashi.
Har ma abincin safe ta manta da shi.
Part ɗinta guda ce, babba, mai tsari na musamman, da mata uku na yi mata hidima kullum cikin kulawa. Sai dai wata doka ƙarara ta Sarki ta sanya ta cikin kunci..
"Ko da rana, ko da dare, Gimbiyata ba za ta taka ƙafarta ta wuce wannan Part ɗin ba."
Wannan ya sa dukkan ƙofa biyu na part ɗin ke da tsaron da ba ya barin ko kwari su wuce. Hakanan tsaronta ne ya zama kulle–kulle da tsare–tsare a gare ta...
Tayi tunani mai zurfi. Ta san cewa idan ba za ta fita ba, to dole kayan su shigo gare ta!
Gimbiya ta fara da sauƙin abu, magana da bayinta amma cikin hikima domin kada su gane ainihin manufar ta.
Rana ta Farko...
Ta ƙira mai ɗinkin ta, wacce ke ɗinka mata kaya na mata tun tana ƙarama...
Tayi mata bayani kan cewa,
"Ina son ganin suturar maza ta fadar nan, wacce ake yi wa jaruman tsaro..."
Mai ɗinkin ta ɗago tana kallonta a hankali, tana mamaki amma ba ta ce komai ba. Tana tunanin.
"Yarinya ce? Me zata yi da kayan jarumai tana mace?" A cikin ranta.
Sai kawai ta amsa da cewa
"Idan Gimbiya ta buƙata, zan kawo miki misali guda domin ki gani."..
Gimbiya tayi murmushi na ɓoye jin daɗin zuciyarta.
"Da wannan zan iya sanin yadda uniform ɗin su yake a zahiri, da kuma inda zan ɓoye Ƙirjina.." itama ta furta a ranta.
A ranar kuwa aka kawo mata kayan jaruman fadar masarautar Alhamra..
Ganin tana so ta cire konkonto a zuciyar mai ɗinki sai ta ce da ita,
"Ina so zanyi kyautarsu ne, zan aika wa wani zai fara aiki a wannan masarautar domin an gama masa interview..."
Jinjina kai mai ɗinkin tayi tana murmushi sai yanzu ta gamsu..
AYAT ta cigaba da tsara ma'aikatanta gaba ɗaya, tana neman kayan dabaru ɗaya bayan ɗaya.
Ta ƙira mai gyaran kai ta ce,
"Ina so a koya mun yadda ake haɗa rawani domin na ga yanda Jaruman Fada ke yi..."
Mai Gyaran kai ya yi mamaki amma bai yi tambaya ba saboda Gimbiyar ba a tambayarta abinda take son yi...
Hakan kuwa ma'aikacin ya koya mata a jikin wani gunki a cikin part ɗinta..
Bayan ya gama naɗawa a kan gunkin sai ta buƙaci ya bar shi a kan gunkin kawai..
Bayan ya tafi sai ta zaro ɗaurin rawanin a kan gunkin yanda bazai warware ba domin ba ƙaramin naɗi akayi ba....just zata rinƙa ɗorawa ne akanta ba tare da ya warware ba....
Daga baya ta sa aka kawo mata mai kula da takalman jarumai..
Ta ce da shi.
"A kawo min takalmin jarumai guda ɗaya... domin na lura suna da inganci, ma'aikacina nashi ya daɗe da lalacewa amma bai samu an bashi wani ba har yanzu..."
Mai kula da takalma ya ce, "Gimbiya ai duk wani jami'in fada da ya lalata takalminsa to siya wani yake da kuɗin aljihunsa idan aka bashi na farko kyauta..."
Gimbiya ta ce, "har nawa ne kuɗin?.."
Ya ce, "ai gimbiya kuɗin da yawa, zai kai 150k..."
Tayi murmushi sannan ta ce, "amma sarki ya san da hakan?.."
Ya sunkuyar da kai a ɗan tsorace ya ce, "Gimbiya wannan ne sana'ar mu a cikin fadar nan, ko wani jami'in da yake kula da abubuwa to kafin ya bada sai ya karɓi kuɗi...."
Gimbiya ta ce, "amma ku kuka siyo abubuwan da kuke sayarwa ko Masarauta ce ta bada ?.."
"Masarauta ne Gimbiya kuma sarki bai sani ba..."
"Cin hanci kenam? Masarauta ta bada abu akan duk wanda nashi ya lalace a bashi ya cigaba da amfani da wani amma ku kuke sayar musu, baku da jari amma kunada riba, to ku sani duk abin da kuke yi zan aikawa sarki..."
A take mutumin ya durƙusa yana roƙon gimbiya...
Gimbiya ta ce, "shin albashin da ake baku duk wata baya isar ku ne?.."
Cikin kuka ya ce, "wallahi wadatacce kuɗi ake bamu sosai, amma zamu daina karɓan kuɗin kowa, a gafarce mu..."
Gimbiya Ayat ta jinjina kai sannan ta ce, "kada na sake ji to, kuma ka je ka kawo mun takalma sawu biyu..."
A ruɗe ya miƙe yana faɗin. "Insha allahu za'a kawo a yanzu..."
Ayat tayi tunanin takalmin ma'aikacinta ma ya lalace shiyasa yanzu ta buƙaci sawu biyu, na ta da kuma nashi..."
Ba da jumawa ba, ya kawo mata "Sample" na takalmin maza...
Ta karɓa tana bashi umarnin akan ya samo mata belt na ɗamara..
Nan ya je ya samo mata.
Bai san cewa, tana tara dukkan kayayyaki ne a sirri don ta kammala shirin rikidewarta ba!
Yanzu sauran gyara murya..
Wannan shine mafi wahala kuma mafi haɗari a cikin shirinta.
Gimbiya ta kalli fim ɗin da ta gani sau 3 tana nazarin yadda mace take rage murya ta zama ta namiji. Sai ta fara gwaji a gaban madubi a cikin shurun daren part ɗinta...
"Assalamu alaikum..." ta furta too Weakly. Ta girgiza kai...
"Alaikumus salam..." muryarta ta yi tsayi High-pitched. Ta sake girgiza kai.
Sai ta ɗan saki numfashi mai zurfi, ta ɗan yi ƙasa kaɗan da muryarta, tana dannewa...
"Alaikumus salam..." Wannan lokacin murya ta yi laushin mace, amma kuma yayi kamar na namiji mai natsuwa da Izzah..
Ta yi murmushi ta kaɗa kai. Da wannan zan iya ratsa ko'ina... ba wanda zai gane.
Haka ta yi ta atisaye kusan rabin dare har sai da muryar ta ta kama tsarin da take so...
✨✨✨
Washegari kuma tana koyon tafiyar namiji...
Haka take ta fafatawa a cikin bedroom ɗinta..
Da farko, tafiyarta, tafiyar mace ce sosai ƙugunta na rawa, ƙafa tana sauƙa da salo irin na Sarauta.
Ta tsaya, ta rage, ta daidaita, ta danna ƙafarta ƙasa da ƙarfi.
Ta saita ƙafar daidai yanda baya ɗan tashi, tana banƙare ƙirji, jiki a sake....
Ta fara tafiya kamar takun raƙumi..
Nan ta sauƙe ajiyar zuciya domin ba ƙaramin gajiya tayi ba..
Sai kuma ta ɗauko kayan jaruman fada ta saka a jikinta tana gwada tafiyar da kayan har zuwa ƙasin falonta...
Ƴan bayinta suna kallo suna mamakin ganinta a haka, suka ce
"Gimbiya me kike yi haka?"
Bata ce komai ba face,
"Ina gwajin salon tafiya ne kawai."
Sun bar ta, suna tunanin wata yar wasan kwaikwayo ce ta taso mata..
Amma ita a zuciyarta tana maganar ciki, "dole na yi kamar maza... ina buƙatar in ratsa ƙofa babu zargi..."
Ta ƙara komawa can saman bedroom da kalar tafiyar maza...A wannan ranar kwana tayi tana atisayen tafiyar maza..
Ta gama shirin atisayenta. Yanzu abinda ya rage mata shine yanda zata sa a kawo mata kayan Concealer na yanda zata saka gashin baki da gemu..
Nan ta ƙira wani ma'aikacinta wanda ya kawo mata finafinai ta sanar masa, cewa.
"Ina so ka kawo mun design na gashin baki da gemu da kuma saje domin ina son gwajin sabon salon fim da na kalla..."
Ma'aikacin ya yarda da hakan domin Gimbiya ba ta taɓa tambayar abu mai kama da haka ba. Sun ɗauka sabuwar sha'awa ce kawai...
Amma ita a zuciyarta ta gama tattara komai, kayan maza, rawani, belt, takalma, riga, murya, tafiya, gashin baki, gemu... duk sun cika shirin ta.
Cikin dare Gimbiya Ayat ta tsaya a gaban madubi. Hannunta na ɗan rawa, zuciyarta na bugawa fiye da yadda ta taɓa ji a rayuwarta. Ta shimfiɗa kayan jaruman maza a gabanta..
"Zan iya... dole na iya," ta furta a hankali, tana ƙarfafa zuciyarta.
Ta fara da faɗaɗden belt na matsin ƙirji mai matuƙar Ƙarfi. Ta ɗaure ƙirjinta da belt mai faɗi, domin ta rage nauyin nonuwanta da kuma gyara surar ta zuwa madaidaicin namiji.
Sai da ta yi ƙasa da numfashi, tana jin matsa da zafi mai yawa. Zafin ya yi yawa har hawaye suka taru a idonta..
"Da haka maza ke ji?" Ta yi murmushin wahala da azaba...
Bayan ta ɗaure, ta saka wandonsu na maza wanda ya yi mata nauyi, ya yi mata tsawo, sai ta ɗaura Belt ɗin ɗamara kamar yadda ta gani a fim..
Sannan sai gashin baki da ɗan gemu da ta ƙirƙiro. Ta mamanna su da ruwan gam, ta ƙara musu tinti da ƙananan launin ruwan ƙasa da take amfani da shi a eyebrows ɗinta. A hankali ta manna zuciyarta na bugawa..
"Na fara zama wani daban," ta furta...
Ta miƙe yadda maza ke miƙewa da ƙarfi. Ba tare da ta ɗaga ƙafa sosai ba, sannan ta daidaita jujjuya kugun dake ta matse su sosai. Salon ta ya canza zuwa na ɗan daudu..
Ta ɗaga ƙafa kaɗan. Ta yi tafiya a ƙetare cikin ɗakin. Sai ta sake dawowa.
"Ya kaji? Kamar namiji?" Ta yi tambayar da ba wanda zai amsa.
Ta yi tari don buɗe makogwaro. Ta sauƙe numfashi ƙasa..
"Ee... kai... Kawo dukkan tawagar nan zuwa ƙofar Masarauta," Ta yi ƙoƙarin yin muryar maza...
Wani dariya ya kuɓuce mata...dariyar mace.
"No! Muryar mace ce!"
Ta ƙoƙarta. Ta sake gwadawa. Sai ta yi ƙasa da murya..
"...ka... kawo tawagar nan..."
Cikin daren nan take ta maimaitawa, har sai da muryarta ta fara tsuke wa kamar namiji maai shekaru 18–20..
Ta janyo rawanin da ta ɓoye. Ta ɗora shi a kai. Ya rufe mata gashin kanta wanda ya daɗa nuna Izzah.
Ta tsaya. Madubi ya nuna wani Sabon Mutum..
A gaban madubi wani saurayi tsaye mai shekaru 20 ne, siriri, mai ɗan gashi a ƙasa da baki da kwantaccen saje..
Zuciyarta ne ya yi wani irin tsalle cikin bugawa, dũkan da har ta ji a kunne..
"Na zama wani... amma ba zan iya janye wannan ba," ta faɗa cikin murya mai zurfi..
Da sassafe, bayan bayinta sun tabbatar da tana cikin ƙoshin lafiya, duk ta sanar da su cewa.
"Yau bana buƙatar ganin kowa. Duk wacce ta shigo yanda nake hutawa sai ta fiskanci ukuba."
Duk sun jinjina kai tare da bin umarninta..
A wannan lokacin ne da ta san an yi mata ƙofa ta Aminci, ta kulle ɗakinta yanda za'ayi tunanin tana ciki. Ta bi hanyarta ta sirri ba tare da kowa ya ganta ba ta fice... A cikin lambun da take fita ta fice..
Haka take tafiya a hanyar masarautar da ta miƙe zuwa can yankin babban fertility ɗin Masarautar...
(Center of the Kingdom)..
```DAN ALLAH KUYI MUN ADALCI🙏 KAMAR YANDA NA BAKU LOKACI NA DON NA FARANTA MUKU, KU MA KUYI ƘOƘARIN SANYA NI CIKIN FARIN CIKI 🙏🙏🙏```
```LIKES ƊINKU SHINE ALBASHIN MARUBUCI```
👍 Like
🔁 Share
💬 Comment
