*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑*
_🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_
✍🏽 By ASMEETAH WRITER
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
```JARUMAI WRITERS TEAM```
⚠️ SANARWA⚠️
Wannan littafi dukiyata ce a matsayina na marubuciya.
⚖️ Ba a yarda wani ko wata ya:
kwafa
gyara
sauya
ko amfani da wani sashe na wannan labari
ba tare da izini na kai tsaye ba.
Duk wanda ya saɓa, alhaki yana kansa..
▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇
🔗 WhatsApp Channel:
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
📚 ArewaPen:
https://arewapen.com/u/asmeetahwriter
📖 Wattpad:
https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter
📲 Contact:
09065443871
📅 FARA TURA BOOK:
🔥 01 — 01 — 2026 🔥
📘 BOOK ONE
```MATAKIN FARKO```
CHAPTER 3️⃣
*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ*
Bayyanowar ta cikin babbar masarauta...
Tana haɗuwa da tawagar ɗaiɗaya amma babu wanda yayi tunanin Gimbiya ce. Tana ƙoƙarin wurin daidaita tafiyarta kamar namiji, domin tana ganin yanda sauran suke yi.
Sai ga wani tsararren mota cikin Masarauta ya tsaya a gefenta. Kirjinta ya yi wani irin bugawa sosai, ta ɗauka an ganota ne. Sai ta ga ɗaya daga cikin Security ne mai jan mota, ya ce da ita.
"Ya! Mutumin hau na rage maka hanya zuwa can Center ɗin Masarautar mana..."
Ayat ta shiga cikin gaggawa, amma jikinta yana ɗan nuna gajiyawa irin bata saba ba saboda matsin ƙirji.
Security ya kuma cewa.
"Kana daga cikin tawagar da zasu fita ne?"
Ayat tana fargaban magana saboda kar ya ganota ta murya duk da tayi training. Tayi shiru.
Security ya ce, cikin ɗan tsawa.
"Kai ɗan rainin wayo, ina magana kana mun shiru, in ban jefar da kai ba!"
Ayat anan ta tsorata, ta daidaita muryar ta mai sanyi.
"Amm... Dani za'a fita..."
Security ya ce
"Yadai naji muryarka haka, kodai mura kake?"
Haka suka kasance har suka isa Center of the Kingdom. Ayat tana ta wara idanuwa tana ganin tsararrun abubuwan da suke cikin Masarautar nan. Tana tunanin daman haka Masarautar nan take da girman gaske?
Dai-dai lokacin da suka isa, yanda wasu tawagar suke shirin fita daga Masarautar.
Ayat ta sauƙa tana zazzaro ido cike da bege. Ta shiga cikin tawagar da suke ƙoƙarin fita outside ɗin Masarauta.
Suna fita daga cikin Masarautar, ta yi wani irin ajiyar zuciya mai tsayi wanda ya fito daga tsakiyar zuciyarta.
Iskar waje ne ya buge ta a fuska!
Iskar da ta daɗe tana mafarkin ji, shekaru ashirin da biyar tana zaton yanda duniyar waje take. Hawaye ne ya gangaro daga idonta...
"Duniya... ga ni."...
Ta furta cikin ƙarƙashin maƙoshinta..
AYAT tana ta fargaba yanda kayan suka matse ta da kuma tsoron ko wata dabara zata warware. Bayan ta tsallake gwaji na farko na mai motar tsaro, ta sulale ta bar cikin tawagar tsaron, ta tafi yawonta a ɓoye.
A ɓoye ta ɗauki dokin ɗaya daga ciki, ta zagaya bayan Alhamra wurin da babu wanda ke zuwa. Anan ta tarar da wani kogi mai kyau da wurin gudanar ruwa mai zurfi. Wurin yana da rata sosai da cikin garin. Ba kowa sai kukan tsuntsaye da natsuwar ruwa.
Zama tayi tana shan iskar wurin domin wurin ba ƙaramin burgeta yayi ba. Har yanzu tana sanye da shigar mazanta. Ta zauna a bakin kogin, ƙafafunta cikin ruwa mai sanyi.
Can sai ta ji wani abu ya faɗo ta bayanta!
A zabure ta miƙe cikin tsoro mai tsanani tana ƙara! Cikin muryar mace tamkar ba namiji ba, firgici ya sa ainihin muryarta ta dawo!.
Tana juya bayanta sai kawai ta ga wata farar tsuntsuwa kyakkyawa a kwance a ƙasa, an harbo ta daga sama.
A tsorace ta kama ƙirji tare da jin zafin matsin ƙirji da ƙugun cikin tsoro da tausayi. Ta nufe ta da gudu ta ɗauke ta. Can sai ga wasu matasa ‘yan farauta sun zo ɗaukan tsuntsuwar daman su suka harbe ta da mashi.
Ganin AYAT a shigar tsaro suturar maza ta fadar Alhamra yasa suka tsorata suka ce.
"Wayyo! Ɗaya ne daga cikin Security Fadar Alhamra! Mu gudu!"
Nan suka juya suka gudu cikin gaggawa.
AYAT ta sauƙe idanunta a kan tsuntsun. Ta zauna a bakin ruwa. Ta ciro Allura da Zare a jikin rawanin da ta ɗaura. Ta fara ɗinke wa tsuntsuwar wurin da aka cake ta da mashi cikin salonta. Tayi treatment ɗinsa sannan ta ba shi ruwa.
Tana ajiye tsuntsuwar, sai ta ga ta miƙe, amma bata iya yin sama sosai ba.
Itama ta miƙe tana binta da gudu. Ta ga tsuntsuwar ta sauƙa a saman wani tsararren bishiya yanda ƙoyayenta suke cikin raga-raga irin abin da suke koyaye akai har wasu sun kinkishe.
Ta sha mamaki sosai. Ita kaɗai ta fara murmushi tana jin daɗin ceton da tayi.
Tsuntsuwar tana kwance akan ƙoyayenta a ɗan sama da bishiyar kaɗan.
AYAT tana tsaye tana kallonta tare da shafa mata baya. Ta ce, cikin muryar maza mai tausayi..
"Ashe ke ɗin Uwa ce. Nagode Allah da yasa nake nan a wannan lokacin... Shin anan kike rayuwa? Kusa da kogin nan mai kyau? To kar ki damu, zan riƙa zuwa miki ziyara... kuma zan cigaba da kare rayuwarki...
Sunana AYAT, amma a shigar mazan nan sunana 'INUWA'. Wato Inuwarki, mai tare miki rana. Idan na ƙara dawowa zan ba ki takaitaccen tarihina mai cike da kaddara... Ki kula da kanki da yaran ki."
Daga nan ta rufe ta da wasu ganyaye yanda duk wanda yazo bazai san akwai halitta a wurin ba. Nan ta juya zata tafi.
Ganin yamma tayi, nan ta zaro ido a tsorace ta furta.
"Na shiga uku! Daidai wannan lokacin ake rufe Masarauta... kuma nasan ma'aikatana zasu nemeni daidai cin abincina. Wayyo banaso a samu matsala a rana ta Farko!"
Daga nan ta hau saman dokin ta fara gudu dashi, ta ratsa cikin city ta nufi Masarautar...
Ana shirin rufe babban gate sai ga ta, ta nufo da gudu tana tsayar da su da muryar maza mai ƙarfi.
Ɗaya daga cikin masu tsaron Get ne ya ce, cikin tsawa.
"Kai ɗan ƙwaƙur! Daga ina kake?"
Cikin muryar maza a ɗan tsorace, ta ce
"Man dokin ne ya ƙare..."
Duk suka kalli juna jin rainin hankali irin nasa.
"Wannan fa dokar sarki ka karya, don haka zamu je dakai can sai kayi masa wannan bayani..." a cewarsu.
Zaro ido tayi! Ta ji zuciyarta tayi mugun bugawa. Nan ta sauƙo a kan doki ta fara ba su haƙuri da muryar ta mai sanyi.
Ganin bazasu haƙura ba, yasa ta riƙo hannun wani daga ciki cikin fargaba. Duk ta ruɗe tana ba shi haƙuri.
Wanda ta riƙe wa hannu ne ya ji wani irin sanyi ya ratsa shi da ta taɓa hannunsa. Ya ji hannun laushi ya kuma ratsa jikinsa. Ya ɗan ruɗe jin hannun namiji mai sa shauƙi.
Security ya tambaye shi cewa, "Meye sunanka domin ban taɓa ganinka a cikin wannan masarautar ba."
A ruɗe ta ce.
"Musa... Kabiru... Iliyasu... Shafi'u..."
Security ya ce "Kai bana son hauka fa! Anya kai ba ɗan Daudu bane?"
Ta daidaita muryar ta, ta furta sunan da ta sanar wa tsuntsuwa....
"Inuwa.... Inuwa sunana..."
Ɗaya daga ciki ya ce.
"Wannan daga gani ba abinda ya iya domin ɗan daudun cikin mu ne, ga murya a ranrangwaɗe..."
Ɗaya daga ciki ya ɗaga ƙafa ya canƙe ta a wurin mazauninta yana faɗin
"Wuce ka bamu wuri dallah!"
Nan ta fara Tangal-Tangal zata faɗi. Da ƙyar ta daure ta wuce da ɗan gudu–gudu...
Su na masa dariya, har sun sa masa suna 'Ɗan Ƙwaƙur'.
AYAT wato Inuwa kai tsaye ta nufi part ɗinta a babban yankin masarautar. Hanya ɗaya kawai take so ta sulale ta koma part ɗinta tun kafin a ankara da bata nan. Tasan akwai matsala domin dole yanzu za'a buƙaci ta fito akan ta ci abinci.
A hanyarta, wani babba daga cikin Security ya dakatar da ita da cewa.
"Kai! Sauƙo nan..."
Ayat ta sauƙa cikin rikicin zuciya da gajiya. Security cikin nuna isa irin na Shugaba mai role, ya ce
"Uhmm! Wannan Littafin za ka kai wa Gimbiya MAAYAH! Ta buƙaci a kai mata ne."
Cikin ajiyar zuciya na tsoron an tsallake wani haɗarin da kuma sabon tsoro lokaci guda, Inuwa ya karɓa. Ya hau dokin, yana nazarin ina ne part ɗin MAAYAH? Domin tun da take bata taɓa zuwa ba. Sai dai idan lokacin haɗuwa yayi a haɗu a babban fadar sarki.
Haɗiyar yawu tayi domin iya part ɗin ƙanwarta Firdos ta sani kawai.
Tana cikin tafiya, ta tarar da wata mata baiwa ita ma Ma'aikaciya ce. Ta tambaye ta da muryar maza mai sanyi
"Amm, shin ko kin san ina ne part ɗin Maayah?"
Matar ta zabura tana zaro ido ta ce, "Maaaa me?"
A ɗan ruɗe yace "Ohh Gimbiya Maayah..."
Matar ta ce "Ohh yanzu naji batu, amma kai baƙo ne ko? To haramun ne ka ƙira sunan Gimbiyar Sarki kai tsaye ba tare da girmamawa ba." Daga nan ta kwatanta masa..
Inuwa ya ƙara gaba ya sha mamaki ganin tsaruwar part ɗin Maayah. Tsaruwar da ya nuna tsananin alatu da kuma tasirin mahaifiyarta 'Yar Hindu. Da farko masu tsaron part ɗin ne suka tare shi. Ya musu bayanin saƙo ya kawo mata.
Ɗaya ne ya miƙo hannu akan zai kai mata..
Inuwa ya ce "No! Sirri ne! Ni aka buƙaci na kai mata da hannuna."
Jin ya ambaci sirri da umarnin sarki yasa suka barshi ya shiga. Har sai da ya tsallake gate biyar kafin ya isa Center na part ɗin. Nan ya fara ganin mata masu dawainiya da ita sunata zirga-zirga.
Ya shiga babban falon. Wani irin sanyi ne ya ratsa shi. Ga ƙamshi kala-kala na turaren hindu ko wanne fita yake.
Ganin ba kowa a falon, kowa yana ta zirga-zirgan aiki, hakan ya ba shi daman haurawa can saman ɗakin yanda yake da tabbacin anan take. Sai da ya haura stairs bakwai kafin ya iske bedroom ɗinta. Wani irin sanyayyen waƙar hindu ne yake tashi a slow...
Inuwa ya shiga bedroom a nutse yana baza idanu. A hankali ya shige ya rufe glass door a hankali. Ya tarar ba kowa anan ma. Can ya fara jin motsin ruwa alamun a bathroom take tana wanka.
A bakin gado ya zauna, yana ƙoƙarin buɗe littafin ya ga abin da yake ciki..
Littafi ne na english novel, na tsantsan soyayya. Duk da Maayah ba soyayya take da kowa ba, amma tana son labaran soyayya sosai...
Inuwa ya ɗan juya idanunsa yana jinjina kai. Domin a rayuwarsa babu wani tsarin soyayya ko wasa da soyayya... A cikin ransa ya ce
"Shan kokko ɗaukan rai. Kowa dai da damuwarsa. Ita kuma labaran soyayya ne damuwarta. Allah sarki! Da dukkan alamun aure take so, kuma gashi ba halin yin aure! Domin babbar Yaya ma wacce tayi 30 something tana nan bata yi aure ba, balle mu 'yan 20 something..."
Haka ta rufe littafin ta ajiye a kan gadon. Tana kallon hotunan Maayah a manne a jikin bangon ɗakin.. Ya kafe idonsa akan hoton mahaifiyar Maayah wacce ta kasance ƴar hindu. Can hawaye ya fara zubo masa domin ya tuna da mahaifiyarsa wacce ta juma da barin duniya ita da ƙanwarsa Firdos
A hankali ya share hawayensa..
Daidai lokacin, sai ga Maayah ta fito daga bathroom! Tana ɗaure da ɗan guntun towel a kirjinta, gashinta ya sauƙo har gadon baya. Tana taku kamar wata ɗawisuwa cikin kasaita. Kana ganin kasan 'Yar Sarauta ce mai kyan Hindu..
Ganin mutum a tsaye a tsakiyar ɗaki yasa ta tsorata. A ruɗe tayi baya. Cikin rashin sa'a, ƙafarta ya zame, tayi baya zata faɗi!
Inuwa yayi saurin riƙe hannunta ya jawo ta gaba. MAAYAH ta faɗo a jikinsa! Dake shima babu ƙarfi saboda asalin mace ce duk ɗaya suke, hakan yasa duk sukayi baya suka faɗa kan gado!
Maayah tana saman Inuwa!
A hankali ta ɗago tana kallonsa da gashin bakinsa da rawaninsa.
Maayah ganin yanda lips ɗinsa suke Soft-lip gasu jajawur. Ga Idanuwa manya-manya farare tass. Ga Soft-body fari tass.
Maayah a tunanin namiji ne yasa ta fara jin shauƙi, da wani irin feeling mai zafi da ya ziyarce ta. Haka suke kallon juna.
A hankali Maayah take sunkuyar da kanta tana shirin ɗora pink lips ɗinta akan lips ɗin Inuwa da niyyar Kiss!
A ruɗe ya janye ta gefe ya miƙe da sauri! Yana kallonta ya juya da gudu ya fita daga ɗakin.
Da sauri-sauri yake tafe yana so ya bar part ɗin gaba ɗaya da tunanin abin da Maayah take shirin aiwatar wa.
Itama Maayah cike da mamaki take zaune. Tana tunanin meyasa ya gudu mata, duk da ba wani namijin da ya taɓa shigo mata room sai yau karo na farko kuma taji matuƙar sha'awarsa. Haka take duba kanta tana mamakin meye aibunta da har zai gudu tunda Allah ya bashi daman shigowa.
A hankali ta furta cikin sanyayiyar murya.
"Wannan bashi da lafiya! Kamar yadda Maayah take tsararriya, kyakkyawa mai kyan sura shine zaiyi rejecting ɗina? To ma meya kawo shi, ya zo ya tada mun da hankali..."
Idonta ne ya sauƙa akan littafin da ya kawo mata.
"Ohhhh! Book aka aiko shi ya kawo? Amma ban taɓa ganin security mai kyan wannan ba! Kyansa ya wuce misali! Taya zan sa a nemo mun shi? Na kamu da son sa lokaci guda! Ina jin wani abu a kan sa sosai..."
Haka ta gama maganganunta. Sannan ta miƙe ta fara bin waƙar da yake tashi a ɗakin tana rawa (Indo-Arabic Dance). A hankali take motsa jikinta irin rawar hindu tare da ƙaramin Towel a kirjinta!
Ayat wato Inuwa tana cikin gagarumar gadarar tserewa. Ta bar part ɗin Maayah cikin sauri tana da yaƙinin cewa Maayah zata sa a nemo ta. Bayan ta shiga babban gaiden ta hanyar ƙofar da tabi, kai tsaye ta nufi ɓoyayyen hanyarta wanda ke kaiwa zuwa part ɗinta ta cikin ƙasa.
Tana jin gajiya sosai. Gajiya ta farko a rayuwarta. Matsin ƙirji, gudun dawowa, da tsananin fargaba na tonon asiri guda biyu, a ƙofar fada da kuma a ɗakin Maayah.
Tana shiga ɗakinta, ta kulle ƙofar sirrin tana sauƙe ajiyar zuciya mai tsayi. Tuni taji motsin Bayin ta a waje, suna shirin zuwa da abincin dare kamar yadda dokar sarki ta tanada.
Ba ta da ko minti ɗaya!
Cikin gaggawa ta fara cire shigar Maza.
Ta cire Rawanin tare da gashin baki da gemu da ta manna..
Ta zaro takalman maza masu nauyi.
Ta jawo Belt da Riga da wando masu tsayi.
Mafi muhimmanci, ta cire ɗamarar da ya matse ƙirjinta da ƙugu. Da zarar ta cire shi, sai ta ji isasshen numfashi ya shige ta! Ta ji kamar an ɗaga mata wani dutse a jikinta.
Ta tura kayan maza a cikin ɗakin ajiya na sirri da ta tanada. Sannan ta miƙe ta shiga Bathroom domin yin wanka na gaggawa don ta wanke ƙura da gumi na duniyar waje....
Bayan ta fito, ta koma cikin kayan Gimbiyanci na masarauta tare da mayafinta mai rufe fuska. Tana cikin doguwar kujerarta ta alfarma a dai-dai lokacin da ma'aikatan ta suka danna ƙwanjin neman izini a ƙofa.
Ta yi murmushi a cikin ranta....
"Na ci nasara a rana ta farko!...."
```LIKES ƊINKU SHINE ALBASHIN MARUBUCI
```
👍 Like
🔁 Share
💬 Comment
