Dr. Sadiq Page 79 Complete

 

Dr. Sadiq Page 79

7️⃣9️⃣

💔❤️‍🔥DR SADEEQ ❤️‍🔥💔


BY


    NARNAH ƘANWAR SOJA 


    BOOK 2

My 15novel comedy love and drama 


    

    https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM


  

THIS BOOK IS DEDICATED TO MY LOVELY BROTHER ABUBAKAR SADEEQ AND MY LOVELY SISTER AISHATU INDO.......



    MORNING UPDATE 


    

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

*(J.W.A)*



    

🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚


(🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲 



    BUSSINES GROUP    


    👇👇👇👇👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/JjkU7xG4zcWIAvtWRgeFtT    


    


        

TITLE 

    Love is a flame that burns bright, even in the darkest night


    BARKA DA SHIGOWA SABUWAR SHEKARA 


    

  

Indo ta fara samun sauƙi sosai. Duk da cewa har yanzu bata gama mantawa da abin da ya faru ba, jikinta ya soma dawowa da ƙarfi. A gidan Kaka kuwa, ana ta motsi, ana ta shiri saboda jibi za a fara azumi.


Gida kamar kasuwa, ana shigo da kaya iri-iri; shinkafa, taliya, sukari, garin koko, miya, kayan miya, kayan tsire, kayan gyaran jiki da ma waɗanda Indo bata taɓa gani ba. Kaka da kanta tana ta duba kaya, tana karɓa, tana umarni kamar shugaban babban gida.


Indo na kwance a gadonta tana kallon ƙofar dakin da ake ta zirga–zirga. Sai ta lumshe ido a hankali tace a ranta:


“A lokacin da nake tare da ƴan uwa na a Modirre, ina zan san ana shirin azumi haka. Na saba da kaka-nazari, yunwa, da ɗan abincin da ake samu da ƙyar. Ashe akwai rayuwar da ake shirin azumi da dariya, da kaya kala-kala, da turare, da tsabta irin wannan…”


Ta ji wani abu ya tsinke mata zuciya. Ba kishi ba ne, ba kuma bakin ciki ba—wani irin sabon yanayi ne na gane bambancin rayuwar ta baya da yanzu.


Sai ta ɗan murmusa kaɗan, murmushin da ya fi kama da hawaye a zuciya ta ce:


“Da Mama tana raye da ni, da yau muna cikin yardar Allah, muna ta shirye-shiryen azumi tare… Allah ka jiƙan ta.”

Ta share ƙaramin hawaye, ta kalli sama.

A waje kuwa ana ta dariya; Layla da Na’iba suna ta cece-kuce da murnar zuwan Daddy, Mommy na ta umarni, Kaka na ta tsawata “Ku kawo wannan nan! Ku cire wannan can!”

Gidan cike yake da farin ciki—banda Indo da ta ji ranta ya yi wani irin nauyi mai sanyi… mai kama da kewa da godiya a lokaci guda.


 


    


    

Washegari da sassafe Indo ta tashi cikin natsuwa. Jikinta ya warke sosai, sai dai zuciyarta tana da rauni mai zurfi. Ta shirya cikin uniform dinta—farar riga da skirt mai launin blue—kamar yadda ta saba. Amma duk da shiryawar, idan aka kalle ta sosai za a ga ta rame kaɗan. Damuwa ce ta danne ta tun jiya har yau.


Ta kalli madubi ta ɗan gyara hular uniform ɗinta sannan ta ɗan yi numfashi mai zurfi.


“Kawai yau ban son ganin sa… ko a hanya,” ta fada a hankali a zuciyarta.

Ta ɗauki bag ɗinta ta fito parlour, ta gaida Kaka cikin ladabi “Allah ya tsare ki Indo, ki kula da kanki.”


“Amin, Kaka.” Ta dan murmusa kadan amma murmushin ba ya kai zuciya.


Ta fita bakin titi tana jiran bus. Ranar tana da sanyi, iska tana kadawa sannu–a–hankali tana motsa gefen uniform ɗinta.


Tana tsaye ta sunkuyar da kai, saboda ba ta son ko ta hangi Dr Sadeeq daga nesa.


Sai kawai ta ji ƙamshi mai tsada ya wuce iska—ƙamshin da ta sanshi har cikin zuciyarta.

Ta dago a hankali ga shi nan.


Dr Sadeeq ya fito daga part ɗin Mommy cikin fararen kaya masu tsabta, sun kama jikinsa sosai, kansa yakiye, fuskar nan tasa mai cike da natsuwa da annuri. Kallon farko kawai ya ishe ta ta ce a zuciya:


“Mugu…”


Shi kuwa yana ganinta yaji komai na jikinsa ya yi laushi. Murmushi ya faɗaɗa masa sosai—irin murmushin da ya fito daga zuciya.


Ya ɗaga hannu a hankali “Indo…”

Ta juya kai kamar bata ji ba ya kara kiran sunanta dan kadan da murya mai dadi:


“Indo…”

Sai kawai taga bus ta tsaya. Da gaggawa ta shiga ba tare da ta waiwaye ba, tana jin zuciyarta na bugu alamun tsana da tsoron sake haduwa da shi.


Bus ta tafi. Shi ya tsaya tsakiya yana kallon bayanta har bus ta ɓace.


Sai ya ja dogon ajiyar zuciya ya ce a hankali, kamar yana magana da kansa:


“Yanzu haka… ta tsaneni. Batason ganin fuska ta ko gaisuwa… babu.”

Ya daga kafada ya jingina da jikin gate ɗin gida, ido a rufe na sakan biyu.


“Fine… fina zama nesa yanzu… amma Indo, wallahi zan gyara abin da na bata. Zan jira lokacin da zata dawo min da kanta.”


Ya janye kai, ya juya cikin gida da zuciya mai raɗaɗi da ƙauna a lokaci guda.

@@@@@@@@@@@@


    A break time, dalibai suka fara fita suna dariya suna watso ruwa. Indo kuwa tana tafiya a hankali har ta same Ilham a kujerar ƙarƙashin shade.


Ilham ta kalleta da sauri ta ce,


“Wayyo Indo! Me ya same ki? Kin rame sosai wallahi.”Indo ta dan saki murmushi marar kuzari.

“Bana ce miki… cikina ke bani ciwo ba.”


Ilham ta kankance ido tana kallon ta sosai.

“Hmm… cikinki? Indo wannan ba sabo bane. Is normal, ai wasu lokutan haka ake.”


Indo ta ɗaga kai a hankali—ba ta son ta kara yin magana game da jikinta.


“Zo nan ki zauna,” Ilham ta ce tana jan hannunta. “Kawata, shafa min kai ki fada min naji… akwai labari ko?” Ta rike hannun Indo cikin surutu.


Indo ta lumshe ido, ta ce da rauni,

“Ilham… kawai ki bani snacks ɗin nan mu ci, kada ki tambayeni komai yanzu.”


Ilham ta yi dariya ta ce,

“To shikenan madam, bari kawata ta huta. Ga chocolate, ga drink, ga meat pie. Wallahi dole ki ci, na sani bakya cin abinci idan kina deep thinking.”


Indo ta ce,

“Na gode kawata ta…”


Suka fara cin snacks ɗin duka su biyun. Ilham tana yi mata zolaya, Indo tana dariya kadan–kadan, duk da ba ta sake gaba ɗaya ba. Sauran ’yan ajin suna kallon su suna cewa “Indo yau bata da energy wallahi.”


Sai Ilham ta ce,

“Kawata ce wannan. Ku bari ta huta. Break is for relaxation ba damuwa ba.”


Suka zauna a cikin inuwa suna hira sosai. Ilham tana kokarin tsaranta ta dawo mood ɗinta, tana basarwa tace:


“Kinji baka kawata? Nan da nan zaki farfado… yanzu dai after school zamu tafi tare ko?”


Indo ta gyada kai tana lumshe idanu — tana jin dan natsuwa saboda Ilham ta bata nutsuwa sosai.



    ALLAH KA HAƊA MU DA ƘAWAYE NAGARI


BY NARNAH KANWAR SOJA 💯

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post