Masarautar Alhamra Page 4 Complete

 

Masarautar Alhamra Page 4

*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* 


_🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_


✍🏽 By ASMEETAH WRITER

~Hasken Jajirtattu~



💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️



   ```JARUMAI WRITERS TEAM``` 


        ⚠️ SANARWA⚠️


Wannan littafi dukiyata ce a matsayina na marubuciya.

⚖️ Ba a yarda wani ko wata ya:

kwafa

gyara

sauya

ko amfani da wani sashe na wannan labari

ba tare da izini na kai tsaye ba.

Duk wanda ya saɓa, alhaki yana kansa..


▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇

🔗 WhatsApp Channel:

https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43


📚 ArewaPen:

https://arewapen.com/u/asmeetahwriter


📖 Wattpad:

https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter



📲 Contact:

09065443871


📅 FARA TURA BOOK:

🔥 01 — 01 — 2026 🔥


📘 BOOK ONE 

           ```MATAKIN FARKO``` 


CHAPTER  4️⃣ 


 *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ*




Bayan ta kammala cin abinci cikin natsuwa a gaban bayinta domin su ne ke kula da hidimar ta suka tattara komai suka fita, suka bar ta ita kaɗai. Ta jingina a gadonta, zuciyarta na yawo cikin tunanin duk abin da ya faru a wannan rana..


“Lallai wahalar da na sha a jikina ta fi zaman kunci a wuri ɗaya. Na ga yadda duniya take, na ceci wata halitta, Uwa!...”


Ta ji gamsuwa da dukkan wahalolin da ta fuskanta, domin sun buɗe mata ido, domin rayuwar waje tana da haɗari amma tana da daɗi. A ranta ta sabunta alkawarin cewa dole ta koma bakin kogi, domin ta sake ganin tsohuwar tsuntsuwa da ’ya’yanta...


A dai-dai wannan lokaci, yayin da Gimbiya Ayat ke cikin natsuwa a ɓangarenta, Ibrahim jagoran tsaro da ta riƙe hannunsa a ƙofar fada yana cikin rikicin tunani a bakin aikinsa.

Ibrahim jarumi ne na tsaro da ya shafe sama da shekara goma yana aiki. Ya san fuskoki da jikin mazaje na masarautar. Amma abin da ya faru jiya ya bambanta da duk abin da ya taɓa sani.

Maimakon ƙarfin hannun namiji, sai ya ji sanyin taɓawa ya ratsa shi.

Ya zauna yana kallon hannunsa, inda Ayat wacce ta ƙira kanta Inuwa ta taɓa shi. Har yanzu yana jin taushin fatar, santsi kamar na jariri... Ya cika da fargaba da ruɗewa..


Muryarta a sanyaye, mai laushi, cike da salo...


“Wane irin namiji ne wannan?” Ibrahim ya tambayi kansa. “Hannunsa ya yi taushi fiye da kima, kuma ya kasa faɗin sunansa. Ya ce Inuwa… Wannan dole wani abu ne daban a masarautar.”


Ya girgiza kansa, zuciyarsa ta ƙi yarda da cewa Inuwa cikakken namiji ne. Sha’awa ta gauraya da shakka a ransa.

“Dole ne na nemo wannan Inuwa,” ya yanke shawara..


 “Sai na san wanene, kuma me ya sa hannunsa ke da irin wannan taushin da bai dace da namiji ba.”



       ```Bayan Kwana Biyu``` 


Gimbiya Maayah ba ta samu nutsuwa ba tun bayan tserewar Inuwa daga ɗakinta. Ta yi watsi da littafin soyayya da aka kawo mata, domin abin da take karantawa ya koma gaskiya.

Ta zauna a kan gadonta na alfarma, tana shafar hannunta a inda Inuwa ya riƙe ta. Wutar sha’awa ta ratsa ta fiye da duk labaran da ta taɓa karantawa. 

    A lokacin wata babbar ma'aikaciyarta ta nemi izinin shigo wa, Maayah ta lamunce mata domin ita tasa a ƙira ta..


“Mama Liyatu, akwai wani da ya kawo min littafi jiya. Sabon ma’aikaci ne a sashen tsaro. Ina so a nemo min shi,”   Ta faɗa cikin muryar gimbiya mai nuna cewa umarni ne, ba zaɓi ba.


Mama Liyatu ta durƙusa cikin ladabi...

“Ranki ya daɗe, menene sunansa?”


Maayah ta yamutsa fuska. Sannan ya ce,


“Ban san sunansa ba, amma yana da kyau matuƙa, ido manya-manya, ga lips masu taushi. Sannan yana da rawani kamar na jaruman tsaronmu, amma ya fi su tsafta da kamshi."


Mama Liyatu ta shiga cikin ruɗani. Ya ya za ta nemi namiji mai kyau a cikin ɗaruruwan jami'an tsaro?


Maayah ta sake jaddadawa:  "Ki je sashen aikin tsaro na fadar cikin gida. Ki ce ana neman wanda ya kawo saƙo a ɗakina jiya. Dole ne a samo shi. Amma ki yi aiki a ɓoye, kar wani ya san cewa Gimbiya Maayah ce ke neman sa."


Mama Liyatu ta fita tana mamaki da kuma cike da tsoro. Ta san cewa wannan aiki ne mai haɗari, amma dole ta bi umarnin Gimbiya....


                       ✨✨✨


A cikin part ɗin Gimbiya Ayat tana shirin fitar ta na biyu. Zuciyarta ta yi ƙarfi yanzu, domin tsoron da take ji ya rage, kewar tsuntsuwarta ta ƙaru.

Tana zaune tana gyara kayanta na maza.. Matse-matsinta ya rage zafi yanzu domin jikin ta ya fara saba wa da sabon salo.

Tana nazarin tsarin fitar ta,  manufarta ɗaya tak a yau shine zuwa bakin kogi don ta ga tsohuwar tsuntsuwa da ‘Ya’yanta...


La'asar ta yi bayan tayi sallar ta, ta gama shiryawa tsaf don fitar ta na biyu. Ta nufi babban gate ɗin fada tana jan dokinta. Tana isa, sai ta tarar da wasu rukunin jami’an tsaro su biyar, waɗanda tuni suka sa mata ido suna murmushin mugunta.


"A’a! Ga Ɗan Ƙwaƙur nan zai fita yawon shakatawa!"

ɗaya daga ciki ya faɗa yana dariya.


"Wane irin namiji ne wannan? Ko tafiyar sa ma sai ka ce ta mata," in ji ɗayan, yayin da suka riƙe ƙugu suna kallon yadda Inuwa ke taku cikin sanyi..


Ayat ta ɗaure fuska, ta canja murya zuwa ta nimiji.


“Za ku ba ni hanya, ko kuwa hira za mu tsaya yi?”


Duk suka kwashe da dariya. Sun riga sun yarda cewa Inuwa ɗan daudu ne, namiji mai ƙirar mata, shi ya sa ma ba su damu da sanya shi a lissafin jarumai ba...


Kafin ta ƙarasa fita, babban jami’in da ke gadin littafin shige-da-fice ya dakatar da ita.

"Tsaya nan! Ka san dokar fada, duk wanda zai fita dole ya yi signing a littafin nan, sannan idan ka dawo ma ka sa. Idan ba haka ba, za a ɗauka ka gudu ne."


Gaban Ayat ya faɗi. Ta san cewa sa hannun mace da na namiji akwai bambanci, kuma rubutun ta na gimbiya ne mai kyau da tsari. Amma ba yadda za ta yi. Ta karɓi biro hannu na rawa, ta rubuta "INUWA" cikin babban rubutu na maza don ɓadda kama.

Bayan ta gama, ta haye saman dokinta. Ta daka masa zunguri, dokin ya tashi da gudu ya bar harabar fadar yayin da masu gadin ke yi mata tafi suna mata dariyar tsokana.


A gefe guda, Ibrahim yana kallon komai daga nesa. Bai shiga cikin masu yi mata dariyar ba, domin tunanin sa ya wuce nan. A ransa ya ƙara tabbatarwa,


 _“Lallai Inuwa ɗan daudu ne. Taushin hannun, tafiyar sa… amma me ya sa zuciyata ke son sake jin waccan taɓawar?”_ 



A cikin ɗakinta, Gimbiya Maayah ta kasa zama. Ta sallami bayinta, ta rage ita kaɗai. Tana riƙe da littafin English novel ɗin da Inuwa ya kawo mata, tana shafar bangonsa kamar tana shafar hannunsa....


“Meyasa ya gudu? Meyasa ya ƙi karɓar kuncina?” ta furta a sanyaye. “Shin ban yi masa kyau ba ne, ko tsoron matsayina yake ji?”


Sha’awa ta mamaye ta gaba ɗaya


 Ta tambayi kanta cikin sanyin murya.

Hankalinta ya gama tashi domin ta fara jin cewa Inuwa ne kaɗai namijin da zai iya goge mata kishirwar soyayyar da take karantawa a littattafai.   Ta riga ta yanke shawara a ranta,

dole ne a nemo mata Inuwa ko da hakan zai tayar da rikici a masarautar....


              ✨✨✨


Ta isa bakin kogin da sanyin yamma. Iskar wurin tana kaɗawa da wani irin sanyi mai ratsa jiki, amma hakan bai hana ta nufar gindin bishiyar da ta ɓoye tsuntsuwarta ba..


"Inuwar ki ce ta dawo..." 


Ta faɗa cikin sanyin murya yayin da take ƙarasawa.

Tsuntsuwar ta miƙe, fuka-fukanta sun fara nuna ƙarfi, wurin da ta ɗinke ya bushe sosai. Wani irin farin ciki ya mamaye zuciyar Ayat, a matsayinta na Gimbiya, ba ta taɓa jin daɗin da ya kai na ceton wannan rayuwar ba. Tana cikin gyara mata ganyen da ta rufe ta da shi, kwatsam!


Wani tsararren kibiya ya wuce ta gefen fuskarta da mugun gudu, ya caki jikin bishiyar, saura kaɗan ya sami tsuntsuwar. Ayat ta ji numfashinta ya tsaya na daƙiƙa guda. A tsorace ta juya baya, hannunta ya kai kan takobinta...


A tsaye, a kan wani dutse dake gefen kogin, ta ga wani tsararren mutum wanda ba ta taɓa ganin kyakkyawa kamarsa ba. Gashin kansa fari ne sol kuma dogo, yana yawo cikin iska. Idanunsa suna da wani irin kwarjini da sanyi wanda da wuya ka samu mutum mai irin yanayin sa...


    King Diamond ya bayyana ne a matsayin mutum a cikin wannan fili nasa na sirri..

Ayat ba ta san shi ba, kuma shi ma bai nuna ya san ta ba, duk da cewa su abokan wasa ne tun suna ƙanana kafin canjin halitta ya raba su...


"Waye kai da kake neman hallaka tsuntsuwar da na sha wahalar ceto?"


Ayat ta daka masa tsawa, muryarta ta fito kauraye kamar namiji.

King Diamond bai ce uffan ba, sai wani irin kallo da yake jifanta da shi. A ransa ya san wannan wurin nasa ne, kuma tsuntsuwar tasa ce, amma ganin wannan saurayin yana ta fafutuka a kai ya ba shi mamaki..


Ayat ba ta jira ba, ta zaro takobinta da sauri.


 "Idan harin tsuntsuwar nan kake, to sai dai ka fara ta kaina!"


King Diamond ya ɗaga hannunsa, nan take wani kyakkyawan takobin azurfa ya bayyana a hannunsa daga iska, tsafi ne ya ƙira takobin ta bayansa don ɓoye ainihin ikonsa..


Ƙarar haɗuwar takubbansu ta karaɗe bakin kogin..


 Inuwa ya kai masa farmaki da karfi da kwarewa irin ta jaruman Alhamra. Ta daka tsalle ta kai masa sara ta sama, amma cikin kwarewa Diamond ya kauce, takobinsa ya tare nata cikin sauƙi.

Faɗan ya yi zafi. Ayat tana amfani da dabarun guje-guje da lankwasa jiki don kaucewa takobinsa mai nauyi... 

Duk lokacin da Diamond ya kai mata hari, takobinsa baya taɓa fatarta, domin a zuciyarsa ya fara fahimtar cewa wannan saurayin dake gabansa yana da wani sirri na daban, amma bai bar hakan ya bayyana ba.

Ta kai masa wani naushin takobi ta gefe, Diamond ya goce yasa hannu ya daki ƙirjinta, baya tayi ta faɗi ƙasi tana sakin numfashi, shi kuwa ya tsaya yana kallonta kamar yana tantance wani abu...


Ganin yanda yayi galaba akanta ne yasa ta miƙe a fusace tana kuka ta sake kai mata takobinta cikin zafin rai...


Har cikin ranta inda zata same shi, zata sassarashi ne...

Amma shi, ya ɗauki faɗan a matsayin gwaji ne kawai, domin inda yana da niyyar kashe ta, cikin sauƙi zai gama da ita..


Takobinta yana gogan nashi yana fitar da tartsatsin wuta.

Sun shagala da faɗan, kowannensu yana mamakin kwarewar ɗan uwansa. Ayat tana faɗa ne da dukkan ranta don kare tsuntsuwar da take ganin ita ce kadai abokiyar sirrinta, yayin da King Diamond yake fada yana nazarin wannan baƙuwar dake da kwarjinin gaske a idanunta.


Yayin da takubban suke ta tartsatsin wuta, King Diamond ya fahimci cewa wannan dake gabansa ba zai daina kai hari ba har sai numfashinsa ya ɗauke...


 Ganin jajircewar Inuwa, Diamond ya yi amfani da wani irin zafin nama wanda idon ɗan adam ba zai iya gani ba.

Kafin Ayat ta sake kai wani harin, Diamond ya damƙe damtsen hannunta wanda take riƙe da takobin. Wani irin ƙarfi ta ji kamar an murƙushe ƙarfe. Cikin ƙanƙanin lokaci, ya juyo da ita tare da wurgar da ita da ƙarfi zuwa cikin kyakkyawan ruwan kogin dake gefensu...


Ruwan dake da matuƙar sanyi kamar ƙanƙara ya haɗiye ta. Ayat ta lume cikin zurfin kogin, inda sanyin ya ratsa ƙasusuwanta. Amma saboda ƙwarewarta na iya ruwa, ba ta firgita ba. Ta buga ƙafafunta, ta yi sama tana sauƙar da numfashi da sauri.

Ta goge fuskarta tana waige-waige da jajayen idanunta don ta ga inda wannan maƙiyin nata ya shige. Amma abin mamaki, gurin ya waye shiru...

       King Diamond ya ɓace tamkar bai taɓa kasancewa a wurin ba, sai sautin iska dake kaɗa ganyen bishiyoyi..


"Ji banza! Ya ji tsoro ya gudu..."    Ta furta cikin fushi. A wannan karon, muryarta ta asalin mace ta fito sarai, domin fushin ya sa ta manta da shigar mazan da take yi..


Ta fito daga cikin ruwan tana ɓari saboda sanyin wurin, kayan jikinta duk sun jiƙe sun yi jagab. Ta nufi gindin bishiyar da gudu, inda tsuntsuwar take zaune cikin fargaba. Ayat ta sa hannu tana shafa tsuntsuwar cikin rarrashi..


"Kiyi haƙuri kinji? Kar ki ji komai, ina tare da ke. Ki kula da yaranki, zan rinƙa zuwa miki a koda yaushe,"

    ta faɗa cikin murya mai cike da ƙauna.

Ganin yadda duhu ya fara bayyana a sararin samaniya, ta fahimci cewa lokaci yana son ƙure mata. Idan mangariba ta yi ba ta shiga fada ba, asirinta zai iya tonuwa. Cikin hanzari ta sake rufe tsuntsuwar da ganye don kariya, ta ja ragamar dokinta tare da lilo a kansa.


 Ta nufi hanyar zuwa masarautar Alhamra dake da nisa sosai. Iska tana busa jikinta dake jiƙe, amma zuciyarta tana cike da tunanin wane ne wancan mutumin mai gashin azurfa? Kuma me ya sa ya ɓace cikin lokaci guda?....


              *Bayan Isha'i* 


A cikin fada kuwa, Ibrahim  bai yi barci ba. Yana zagaye a cikin sashen tsaro sai ya ji wasu ma'aikata suna tsegumi.


"Kaji fa, wai jiya an ga wani sabon Security ya shiga har Bedroom ɗin Gimbiya Maayah! Kuma har yanzu ba a san ko wanene ba."


Gaban Ibrahim ya faɗi. Ya tuna da Inuwa. Ya tuna yadda yaron ya rikice wajen faɗin sunansa..


"Lallai wannan Inuwa ko Ɗan Ƙwaƙur ba jami'i bane kawai... Akwai wani babban al'amari a tare da shi. Ta yaya ma'aikacin tsaro zai shiga har bedroom ɗin Gimbiya idan ba yana da wata kariya ta musamman ba?"


A ɗayan ɓangaren, Mama Liyatu ta dawo da rahoton cewa..


"Ranki ya daɗe, na bincika ko'ina a sashen ma'aikata. Babu wani jami'i mai irin siffar da kika faɗa a cikin jerin ma'aikatan fada. Masu tsaron ƙofa ne kawai suka ce sun ga wani mai kama da ɗan daudu...."


Maayah ta miƙe tsaye cikin mamaki da kuma ƙarin sha'awa..


"Wato ma'aikacin bogi ne? Kuma ya shigo har ɗakina ya fita ba tare da an kama shi ba?"


Murmushi ya suɓuce mata. Wannan ya ƙara sa ta ji cewa Inuwa wani babban mutum ne mai ban mamaki wanda ya fi ƙarfin ma'aikacin fada...


A washegari har labari ya karaɗe ko ina. Har ya je kunnen sarki zaki..


Ko wace gimbiya an sanar mata cewa ana son ganinsu a babban fadar sarki..


Gimbiyoyi biyar duk an sanar da su cewa sarki yana son ganinsu na gaggawa..



👍 Like

🔁 Share

💬 Comment

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post