8️⃣0️⃣
💔❤️🔥DR SADEEQ ❤️🔥💔
BY
NARNAH ƘANWAR SOJA
BOOK 2
My 15 novel comedy love and drama
https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM
THIS BOOK IS DEDICATED TO MY LOVELY BROTHER ABUBAKAR SADEEQ AND MY LOVELY SISTER AISHATU INDO.......
MORNING UPDATE
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲
BUSSINES GROUP
👇👇👇👇👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/JjkU7xG4zcWIAvtWRgeFtT
BARKA AUNTY INDO MARUBUCIYAR SAWUN KEKE TA SAMU ƘARUWA HAIHUWA ALLAH YA RAYA MANA BABY GIRL AMEEN
TITLE
Love is a flame that burns bright, even in the darkest night
AFTER SOME DAY'S
Ilham ta shigo class ɗin tana ta tsalle da shewa, tana kiran“Albishirii Indo! Indo!!”
Indo, wadda take jingine a kujerarta tana rubutu, ta daga kai a hankali ta ce“Albishiirrr? To goro.”Ilham ta damƙe hannunta cikin rawar murna ta ce:
“Indo! Zan koma BOARDING SCHOOL! THE REGENT SECONDARY SCHOOL — BOARDING FOR GIRLS ONLY! Daddy ne ya kawo shawara. Yanzu haka za a fara min registration. Na samu transfer! Kinga yanzu ina SS1 ke nan!”
Indo ta tsaya cak. Kallon idanunta ya canza, zuciyarta ta matse kamar za ta fashe tace da murya mai rauni:
“Ilham shine kike murna? zaki barni? Don Allah kar kitafi… Kar ki barni ne kadai kece kawata, ke ce mai bani shawara… ke ce yar uwata. Ilham please… don Allah kar ki tafi ki barni.”
Kallon Ilham ya canza nan take. Murnar da take yi ta tsaya, ta rungume Indo sosai tana shafa bayanta.
“No Indo… ban shirya rabuwa dake ba wallahi. Amma saurari bayani na.”Ta zaro wani form daga jakkarta, ta ce:
“Gashi nan Form nawa. Amma yana da biya biyu. Daya na registration ne Ki kaiwa Brother Sadeeq… ki ce ke kike so ku koma school ɗaya da ni boarding.”
Indo ta sake girgiza kai tana kuka kadan:
“Ni? Ni na koma boarding?”
Ilham ta share mata hawaye ta ce:
“Eh Indo. Rayuwar boarding za ta gyara mana komai. Zamu tashi tare, mu kwanta tare, mu yi karatu tare, mu yi rayuwar mu tare. Ba zan tafi in bar ki cikin damuwa, cikin tunani… ba zan taba yi miki hakan ba.”
Ta kamo hannun Indo sosai kamar kada ta zame.
“Karki ce zamu rabu. Zamu tafi mu biyu. Ni da ke. Zan gaya wa Daddy na, zai kawo maki ɗayan form naki Ina so ki tafi da wanan nawa guda ɗaya”
Indo ta kalli Ilham, zuciyarta na rawa cikin tsantsar dadi da tsoron rabuwa“Ilham… kina nufin… ba za ki barni ba?”
Ilham ta yi dariya ta ce:
“In bar keke Indo? Haba kawata! Ni ba zan iya ba. Ina haduwa da wani mutum kamar ke a makaranta sau biyu?”suka yi dariya kadan, suna harar juna da soyayya ta kawance.
Ilham ta kara cewa
“Yanzu ki shirya kawai… mu tafi REGENT tare. Ke da ni. Boarding life za ta gyara mana komai, ki gani.”
Indo ta lumshe ido, zuciyarta cike da natsuwa ta ce:“Na amince Ilham… Indai tare zamu tafi.”
Ilham ta kwashe da dariya ta rungume ta:
“Yesss! Yi murmushi mana Indo… kawai mu tafi mu canza rayuwar mu!”
Indo ta runtse ido tana murza yatsunta a hankali, kamar wadda take boye tsoro a zuciya. Sai ta ce da Ilham cikin siririyar murya:
“Amma Ilham… ina tsoro. Ina tsoron Dr Sadeeq ya ce bai yarda ba. Shi yanzu ma fa jin ni yake tsana… ni ma banason ganin shi. Amma wallahi nafison na bar wannan gidan yanzu… na bar duk tunanin da yake damuna.”
Ilham ta kama hannunta sosai, ta matsa kusa da ita ta ce da kyau:
“Indo, listen to me… wannan ba matsala bace. Na san how to handle him.”Indo ta zaro ido:
“Yaya? Ni fa tsoron shi nake ji yanzu Ilham…”
Ilham ta yi murmushin dabara na ƙawaye masu wayo “To ki saurara ki ji yadda za ki samu Dr Sadeeq ya amince cikin sauki.”
Ta girgiza yatsa kamar malama, ta fara lissafi
Ilham ta ce“Dr daya ganeki kina roƙo, zai ɗauka kina shiririta ko kina gudunsa. Ki canza strategy.”. Ki rubuta masa short message mai taushi — ba dogo ba.Ilham ta ɗaga gira:
“Ki rubuta masa kamar haka:
“Ina so in koma boarding don karatu saboda na gaji da wannan tunanin da nake yi kullum. Karatu ya fara min wuya. Please, ka taimaka min don Allah.”
“Kada ki yi kuka. Kada ki zarge shi. Kada ki kawo komai. Ki barshi ya ji laifi kansa — wallahi zai amince!” Kada ki tura masa yanzu. Ki jira ya dawo gida “Dr idan yana gajiya… yana sauƙin yarda ki jira dare ko bayan sallar isha’i, lokacin da zuciyarsa ke sanyi.”Ilham ta yi dariya:
“Indo, lokacin da kika guje masa sai zuciyar namiji ya fara faduwa — yana tunanin yaya za ki guje shi? Nan ne yake saurin yarda da duk abinda kike so.”. Ki bari ni in fara masa magana sosai da Daddy na — mu hada masa pressure mai kyau.
“Daddy na yana da suna sosai kuma Kinga munmaƙobta ne duk matsallaci daya suke sallah Idan ya kira shi ya ce ‘yarinyar nan tana da kyau da karatu, ta dace da Regent’ wallahi Dr ba zai yi musu ba.”
Indo ta ji sanyi sosai, ta dafe kirjinta tana kallon ƙawarta.
“Ilham… kina nufin idan na bi wannan plan ɗin… zai yarda?”
Ilham ta dungura hancinta:
“I promise you Indo. He will. Kuma wallahi wannan boarding zai ma taimakeki ki rage damuwa, ki huta da wahalar su Mommy kullum. Ki koma inda zuciyarki zata huta.”
Indo ta nisa sosai, idanunta suka cika da kwanciyar hankali:
“Nagode Ilham… da gaske. Ni dai ina son in tafi.”Ilham ta rungume ta:
“To shikenan kawata. Da dare ki tura masa message ɗin. Let’s start your new life.”
Indo ta jingina da katangar gadonta, wayar hannunta tana rawa, zuciyarta bugawa kamar ana kirga mintuna. Dare yayi shiru, hasken lamp ɗinta kaɗai ke haskawa. Ta sha numfashi sau uku kafin ta rubuta:
“Dr, don Allah ina so in tafi boarding school. Ina son na mayar da hankalina kan karatu saboda tunanin da yake damuna kullum. Karatu yana min wahala yanzu.
Don Allah ka bani izini. Na gode.”
Da tsoro ta danna SEND.
Tana turawa sai jikinta yayi sanyi, ta rufe fuska da bargo a can part ɗin Dr Sadeeq…
Dr Sadeeq
Yana zaune a ƙarƙashin hasken farin lamp, cikin doguwar rigarsa mai laushi, yana shan coffee mai zafi a cikin kofi ɗin sak el-classic.
Laptop ɗinsa a buɗe — yana rubuta report din Daddy na company.
Sai kawai ya ji tiiiiikk! — sautin message
Ya ɗan kallewa kamar ba shi da niyyar buɗe shi yana ganin sunan “INDO 🌙💙”
Goguwar zuciyarsa ta tsaya na daƙiƙa ɗaya.
Hannu ya ɗan yi sanyi ya latsa message ɗin ya karanta
“BORDING SCHOOL…”
Sai jikinsa ya yi wani irin tsalle, zuciyarsa ta matse kamar an murɗa ta.
Ya ajiye kofin coffee din da sauri har ya buga kujerar.
“Boarding??”
Ya ambata cikin murya mai ƙasala da tashin hankali.
Ya sake karanta message ɗin, idonsa ya ɗan ɓoye zafin da ke tashi a zuciyarsa:
“…na gaji… tunani… karatu yana min wahala…”
Sai ya ji wani abu ya tsinke masa a kirji.
Yayi murmushi mai rauni, ba na farin ciki ba — na nauyi a ransa yana cewa:
“Indo… kina guduna ko? Ke bakya so mu zama kusa ne?”
Ya jingina da kujera, ya rintse idanuwansa yana furta, “Wayyo Indo… bazaki tafemin ba. Ki barni ni kaɗai yanzu?”
Hannu ya kai kan screen, yatsunsa na rawa, ya rubuta a hankali:
“Boarding ko, Indo?
Wayyo, kina nufin baki son zama kusa dani?
Baki son mu zama family ne?
Baki son ki… ki rike zuciyata kusa da taki?”sai kuma ya share — ya goge komai yayi nisa mai nauyi A ƙarshe ya rubuta:
“Indo, kina so ki tafi?
Ko kina so ki yi nisa da ni ne kawai?” ya tura mata
Da zarar ya tura ya jingina da kujerar, zuciyarsa cike da tashin hankali, jin kamar wani abu ya fara zame masa daga hannunsa.
Ya dafa goshinsa:
“Allah ya tsare min ke Indo… amma kar ki barni haka.”
A gefe guda Indo ta ga message ɗin…
Idonta ya ƙara faɗa…
Zuciyarta ta yi wani irin tsayawa…
Sai ta fara tunanin:
“Yanzu ya gane ina gudunsa?”
Cinikin dare ya fara armashi…
..........................................................................
.jpg)