Masarautar Alhamra Page 5 Complete by Asmeetah Writer

 

Masarautar Alhamra Page 5 Complete

*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* 


_🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_


✍🏽 By ASMEETAH WRITER

~Hasken Jajirtattu~



💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️


   ```JARUMAI WRITERS TEAM``` 


⚠️ SANARWA ⚠️


Wannan littafi dukiyata ce a matsayina na marubuciya.

⚖️ Ba a yarda wani ko wata ya:

kwafa

gyara

sauya

ko amfani da wani sashe na wannan labari

ba tare da izini na kai tsaye ba.

Duk wanda ya saɓa, alhaki yana kansa..


▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇

🔗 WhatsApp Channel:

https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43


📚 ArewaPen:

https://arewapen.com/u/asmeetahwriter


📖 Wattpad:

https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter


📲 Contact:

09065443871


📅 FARA TURA BOOK:

🔥 01 — 01 — 2026 🔥


📘 BOOK ONE 

           ```MATAKIN FARKO``` 


CHAPTER  5️⃣


 *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ*



A lokacin da saƙo ya isa ga Gimbiya Ayat cewa Sarki Zaki yana ƙiran dukkan gimbiyoyin masarautar Alhamra, gabanta ne ya faɗi tasss. Jin cewa dalilin ƙiran shi ne zargin shigar wani jami'in tsaro mai suna Inuwa cikin ɗakin Gimbiya Maayah, ya sa ta ji kamar ƙasa ta tsage ta shige.

Ta koma cikin bedroom ɗinta, ta kulle kofa tana zarya. Zuciyarta na bugawa...


Tare da maganar zuci..


"Idan na bayyana a matsayin Gimbiya Ayat, zan zauna lafiya a kan kujerata, amma 'Inuwa' zai zama ɗan gudun hijira wanda za a saka ran jami'ai dubu don kamo shi. Idan kuma na bayyana a matsayin Inuwa, zan fuskanci fushin Mahaifina a gaban kowa!"...


Bayan dogon tunani, Ayat ta gane cewa idan har aka rasa Inuwa a filin taron ma'aikata, to bincike zai yi tsanani har ya kai ga kowane lungu na fada. Dole ne Inuwa ya bayyana don sanyaya fushin Sarki, sannan kuma Gimbiya Ayat dole ta bayyana don kar a zarge ta da rashin halartar taron gimbiyoyi.

Anan ne Ayat ta ƙulla wata dabara...


Ta yanke shawarar cewa za ta fara bayyana a matsayin Gimbiya Ayat a farkon taron. Sannan yayin da taron ke tsaka da ɗumi za ta nemi izinin fita don ta koma ta rikiɗe zuwa Inuwa, sannan ta shigo filin fadar a matsayin wanda ya kawo kansa....



Domin ta amsa ƙiran sarki a matsayin gimbiyar da ba ta san komai ba, ta fito cikin shigarta ta alfarma da mayafinta na sirri. Ta isa babban fada inda sauran gimbiyoyin suke zaune, tana isa ta nuna alamun rashin jin daɗi, ta zauna a kan kujerarta tana dafe kai, ta sanar da sarki da sauran gimbiyoyin cewa tana fama da tsananin ciwon kai, kuma watakila ba za ta iya jure tsawon taron ba....


 Ta yi wannan dabarar ne domin ta samu damar sulalewa...


Daga Kursiyyin Sarki ya jinjina kai sannan ya ce da ita.


"Ki jira lokaci yayi, domin na ga ana ƙoƙarin rushe dokata..."


Ayat wani irin bugun zuciya take ji, lokaci guda gumi ya fara yanko mata..


 Sarki ya bayar da umarnin a ƙira duk ma'aikatan tsaro gaba ɗaya don a tantance su a filin fada, kuma ya buƙaci ganin wannan yaron mai suna Inuwa...

Ganin hankalin kowa ya koma kan ma'aikatan da ke shigowa, Gimbiya Ayat ta ƙara tsorata domin ta fara jin daɗin fita.... Ta ƙara nemi izinin babban Sarki cikin muryar tausayi....


"Ranka ya daɗe, jiri na ɗibana, ina buƙatar na koma ciki na ɗan huta kafin taron ya yi nisa."..


Tana yi tana dafe goshinta ga wasu zafafan hawaye dake gangaro mata duk da tana rufe da rabin fuskarta da mayafi...


Sarki Zaki, cikin nuna tausayi ga 'yarsa ya ba ta izini....

 Ayat ta bar fadar da gaggawa, nan danan motarta ya kaita part ɗinta... tana isa sassan sirri na ɗakinta ta bankaɗe kayan gimbiyancin, ta matse kirjinta da zanen audugar nan, ta ɗauko rawanin ta ɗaura. Ta manna gashin baki da gemun ta na yaudara...


Da gudu ta bi hanyar sirrinta ta fita wajen masarauta... Wani doki ta gani shi kaɗai ganin kar lokaci ya ƙure ne yasa ta hau dokin ta nufi babban fadar sarki ..


Daidai lokacin da jami'an tsaro suka fara layi a filin fada, kuma aka fara neman sunan Inuwa, sai ga ta ta fito ta bangaren ma'aikata. Zuciyarta na bugawa cikin tashin hankali...


Ta isa gaban Sarki, ta durƙusa a tsakiyar filin fada, a lokacin da duk idanuwan ma'aikata, da na sauran gimbiyoyin ke kanta.

Ibrahim yana gefe yana kallon yadda Inuwa ya fito da kansa, ya lura da cewa yaron nan ko Inda-inda bai yi ba wajen amsa laifinsa, wanda hakan ya ba shi mamaki...


Sarki Zaki ya daka tsawa yana kallon Inuwa...


"Kai ne kake ikirarin sunanka Inuwa? Kai ne ka shiga ɗakin gimbiya Maayah ba tare da izini ba? Shin ka san hukuncin wanda ya keta alfarman masarautar Alhamra?"


"Gafara nake nema, ya shugaban jarumai. Ni ne Inuwa wanda ya shiga ɗakin Gimbiya Maayah ba don keta alfarma ba, sai don isar da saƙon gaggawa da na ga ya dace ta sani."


Duk fadar ta yi tsit. Ibrahim ya ƙurawa Inuwa ido, yana mamakin karfin zuciyar wannan yaron. Maayah kuma ta kasa ɗauke idonta daga kansa, tana jin wani irin kishi da fargaba a lokaci guda.


Sarki Zaki ya ƙafe Inuwa da idanuwa masu firgitarwa kamar mai nazarin wani abu...


Ayat da ta fahimci tana kan ƙwayar idon Sarki sai kuma wani irin zufa ya fara yanko mata, jiki na rawa tana haɗiyar yawu kamar wacce aka yanke wa hukuncin kisa...

Domin ta san cewa Sarki yana da mugun wayo kuma waɗannan idanuwansa na halitta da wuri yake kama mutum mai laifi ko yake ƙoƙarin ɓoye wani abu...

   Magana ta fara a cikin ranta..


"Innalillahi wa inna'ilaihi raju'unn,  innahu min sulaimanu wa innahu bismillahi rahmanu raheemm, a wannan lokacin nasan kashina ya bushe, domin sarki ya kamani, na shiga uku, na shiga uku, wayyo ni...."


Sarki kuwa hannunsa yana kan talsumin takobinsa. Daidai lokacin da zai ba da umarnin a damƙe shi, sai muryar Gimbiya Maayah ta sake ratsa fadar...


Ta ɗan gyara zama, tana kallon mahaifinta cikin natsuwa.


"Abbah, ina neman afuwar ka ga wannan yaron. Ni na ba da umarnin a aiko min da wannan littafin domin ina da wani Assignment na makaranta da nake son kammalawa cikin gaggawa. Ganin cewa lokaci ya ƙure, sai na nemi jami'an tsaro su kawo min shi har ɗakina."...


Wani irin dogon nishi duk mutanen fadar suka sauƙe. Ibrahim ya jinjina kai yana mai farin cikin jin hakan...



Sarki ya kalli Maayah, sannan ya kalli Inuwa wanda ke durƙushe yana gumi..


"In har haka ne Maayah, me ya sa bai bayyana kansa ga babban jami'in tsaro ba? Me ya sa ya shiga ta hanyar  ɓoye har sai da aka neme shi aka rasa a jerin sunayen ma'aikata?"


Maayah ta yi murmushin ƙasaita...


"Abbah, watakila tsoron kwarjininka ne ya sa shi kasa magana. Amma na tabbatar shi ne ya isar min da saƙon da na buƙata."


Sarki Zaki ya numfasa, sannan ya kalli Inuwa...

 

"Ta ya ka kasance a cikin jami'ai na alhalin baka da ƙirar jarumai?...

          Kai ɗan ƙaramin sauro ɗago ka kalli cikin idanuwana..."


Anan fa Inuwa ya ƙara gane cewa Allah ɗaya yake, domin hakan da zai yi shine hanyar buɗewar tonon asirinsa... Haka yake ta nuƙu–nuƙu ya kasa ɗago wa...


"Kaiii magana nake maka, a cikin jarumai na babu lusari mai ƙaramin ƙira kamar ka... Ta ya ka samu shiga cikin jarumai, kuma babu sunanka a cikin jerin jaruman masarautar nan, ban kuma sanka baaa...."


Maayah sai murza hannunta take cikin damuwa, ta rasa ta yanda zata kare shi...


Sai muryar babbar gimbiyar masarauta suka ji kamar daga sama...


"To indai hakane, ya cancanci kisa domin ya karya doka, ya sanya tufafin jarumai ba tare da izinin mai martaba ba, wannan babban laifi ne..."


Gimbiya Zayana ta furta tana ƙare wa Inuwa kallo da waɗannan cat eyes ɗinta, ga wasu zafafan Golden hair color yanda suka bazu a gadon bayanta.... Kana ganinta kasan iyalan turawa ne....


Inuwa ya ji wani irin murɗawar zuciya na tsantsar tsanar wannan babbar Yayar tasu, domin can jininsu bai haɗu ba kuma kusan shawarar ta Sarki yake ɗauka fiye da ta kowa....


Gimbiya Yumna a tsorace ta ce,     "A'a wannan ai bai cancanci kisa ba, wannan ƙaramin abu ne za'a hukunta shi da kisa?..."


Wani irin kallo Gimbiya Zayana ta wurga mata, har sai da ta shiga taitayinta sannan ta ce,


"Kada ki ce zaki yi jayayya da hukuncin sarki, domin shawarata itace akan dai-dai..."


Yumna ta sunkuyar da kai domin ita ɗaukan kanta take kamar ba gimbiya ba... Daga bisani cikin sanyin murya ta kuma cewa, 

       

"Na ke ga, duk wanda zai sanya kayan tsaro don ya kare martabar masarauta to ba maƙiyi bane, kuma inda ace akwai abin da yake ɓoye wa da an gano tintinin..."


Maayah ta ƙara da cewa,  "Gaskiya ne Abul, a dubi lamarin, a ƙyale shi ya cigaba da aikin da ya fara..."


Sarki ya jinjina kai cikin kakkaurar murya ya furta.


"Na ji daga gare ki Zayana, sannan na ji daga bakin ƙannenki Maayah da Yumnah, kasancewar Ayat ta koma part ɗinta....yanzu Inason jin daga bakin auta ta Firdos..."


Chingching tana zaune ba abinda take sai game a waya, sai dariya take tayi tana wasan harbi... Duk abin da ya faru tin daga farko har zuwa yanzu bata san me ake tattaunawa akai ba....


Gimbiya Zayana a fusace ta ce  "Wannan mahaukaciyar shawarar mai zata bayar?..."


Wani irin kallo Sarki ya wurga mata, nan Zayana ta kawar da kai...


Maayah itama ta ce,  "Abul, dan Allah ka ɗauki shawarar mu, Chingching ba abinda ta nutsu ta ji a wannan tattaunawar..."


Sarki bai biye musu ba, ya kalli Chingching sannan ya furta cikin sanyi murya 

          "Mamana..."


Ai Chingching hankali ya tafi ko ƙiran bata ji ba.... Sai da sarki ya yi magana da ɗaya daga cikin ma'aikatan akan su karɓi wayar...


Hakan akayi a ruɗe ta ɗago tana tura baki cikin shagwaɓa,   "Ku bani wayataaa..."


Sarki a nutse yake mata magana.  

"Mamana ki dubi wancan ta durƙushe..."


Ta kalli Inuwa wanda mahaifinta ya nuna mata sannan sarki ya cigaba da faɗin...


"Mayaudarin jami'i ne, ya sanya kayan jarumai ba tare da tantance shi ba, shin wani hukunci za'a masa?..."


Chingching tana turo baki ta ce,  "Yoo too ya ɗago ya kalle ni mana..."


A hankali Inuwa ya ɗago suka haɗa ido da Chingching domin lokacin da ya fita Chingching bata ri ga ta iso ba, saboda hakane yasa basu haɗu ba...


Inuwa ganin ƙanwarsa yasa ya ji wani irin sanyi a ransa..


Chingching a ɗan ruɗe ta ce,  "Laaaa!!! Aunty?..."


Ta sauƙa daga kujerarta ta nufi Inuwa da sauri, tana zuwa ta durƙusa a gabansa...

     Shi kuwa Inuwa yanda kasan an caka masa mashi a saitin zuciya haka ya ji...ji yayi kamar ya haɗiye ransa ya mutu.

Wani irin yawu ya haɗiya..


Duk mutanen wurin sai da suka sha mamakin jin Chingching ta furta Aunty Kuma wacce take ƙira da Aunty, Ayat ce... Sauran kuma Aunty wance...


Chingching ta ƙare ta da kallo sai kuma ta sake turo baki ta ce, 

       "Ohhhh! Ashe namiji ne,  na ɗauka Aunty ce ai, na ga idanun iri ɗaya..."


Kowa sauƙe numfashi yayi domin kowa yasan sokoncin Chingching...

    Ta koma ta je ta zauna sannan ta ce,  "Wannan abokina ya mun kyau, kuma  kayan jarumai sun masa kyau, kuma nima inada kyauu...."



Sarki kawar da kai yayi domin bazai tsaya sauraron shirmen Chingching ba... Ya dubi Inuwa sannan ya ce.

 

"Tashi ka tsaya! Saboda kariyarsu Gimbiya, na yafe maka yau. Amma daga yau, sunanka zai bayyana a jerin masu tsaro. Za ka koma ƙarƙashin kulawar Ibrahim kai tsaye... Shi ne zai kula da kowane motsinka, da kuma yi maka training yanda ya kamata...."



Gabanta ya sake faɗuwa. Zama ƙarƙashin kulawar Ibrahim yana nufin cewa asirinta ya kusan tonuwa. Ibrahim mutum ne mai lura, kuma tana sane da cewa har yanzu yana mamakin ta...


A ɓangaren Maayah kuwa, tana kallon Inuwa tana jin wani irin daɗi a ranta. Ta riga ta yi nasarar sa shi kusa da ita, domin tana da ikon ƙiran Ibrahim kowane lokaci don ya kawo mata shi...



Bayan an tashi daga taron, Inuwa ya fito daga fadar da sauri yana son sulalewa ya koma part ɗinsa don ya sake komawa Gimbiya Ayat. Amma yana tafe, sai ya ji ƙatoton hannun Ibrahim a kafaɗarsa.

Ibrahim ya rage murya yadda su biyu kawai za su ji..


"Kayi sa'a yau, Ɗan Ƙwaƙur. To Ɗan Ƙwaƙur yanzu ka zama nawa. Tunda hannunka nada laushi kamar na mace, ba zan saka ka aikin wahala ba. Aikinka shi ne,  za ka riƙa yi min tausa, kana shafa min baya, sannan kana sosa min gashi idan na gaji da aiki. Ina son jin daɗin wannan laushin hannun naka."..


Ayat ta ji gabanta ya faɗi, amma dole ta amince don kar asirinta ya tonu. Ibrahim ya sa ta a gaba suka tafi sashen jami'an tsaro na yankinsa don tantance ta.


Daidai lokacin da Ibrahim ya ɗan kauce don duba wasu takardu, Inuwa ta yi amfani da damar ta sulale da gudu ta hanyar sirri...


 Tana isa part ɗinta, ta ciccire kayan maza, ta yar da gashin baki da gemun. Ta sauƙe numfashi, sannan ta sanya asalin shigar gimbiyarta mai cike da ado da ƙawa...


Ta ɗaura mayafinta na sirri wanda yake rufe fuskarta baki ɗaya. Wannan mayafin shi ne babban kariyarta, domin hatta Sarki Zaki bai san asalin kamannin fuskarta ba tun tana yarinya. Ta fito cikin izzah, ranta a ɓace, ba wai zargin shigar ɗakin Maayah ba ne ya fi damunta ba, a'a, labarin cewa Maayah na zuwa makaranta (Private School) a cikin Alhamra City yayin da sauran aka hana su fita ne ya ƙona mata rai...


Tana fitowa daga part ɗinta, ma'aikata suka yi ƙoƙarin tare ta saboda dokar hana fita da Sarki ya bayar bayan kiran gaggawa. Ayat ta daka musu tsawa mai firgitarwa..


"To! Bamu gama meeting da Sarki ba! Bana son iskanci dallah!"


Ma'aikatan suka ja baya a tsorace, suka ba ta hanya. Ta shiga motarta ta alfarma, security ya ja ta har zuwa Centre of the Kingdom...


Ayat ta shiga fadar cikin takun ƙasaita. Ta tadda sauran gimbiyoyin a zaune tare da Sarki..


Gimbiya Zayana tana zaune cikin takama da izzah. Ita mutum ce mai zafi da mulki, kuma ko kaɗan ba ta ƙaunar Ayat, musamman yadda take rufe fuskarta...


Gimbiya Yumna ita kuma tana zaune cikin sauƙin kai da fara’a..


Gimbiya Maayah kuwa tana nan kanta a sunkuye, tunanin Inuwa kawai take yi a ranta...


Gimbiya Chingching tana zaune kusa da kujerar Sarki.

Tana shiga, Chingching ta miƙe da gudu ta zo ta rungume ta..


"Aunty na! Nayi kewarki sosai! Akace kin koma part ɗinki kanki na ciwo, naji ba dadi... sai kuma gaki kin dawo!"..


Ayat ta rungume ƙanwarta tana jin sanyi a ranta. Yumna ma ta ƙaraso suka rungumi juna cikin mutunci. Amma Zayana tana ganin Ayat ta ja tsaki, ta kauda kai cikin ƙyama....



👍 Like

🔁 Share

💬 Comment

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post