*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑*
_🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_
✍🏽 By ASMEETAH WRITER
~Hasken Jajirtattu~
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
```JARUMAI WRITERS TEAM```
⚠️ SANARWA⚠️
Wannan littafi dukiyata ce a matsayina na marubuciya.
⚖️ Ba a yarda wani ko wata ya:
kwafa
gyara
sauya
ko amfani da wani sashe na wannan labari
ba tare da izini na kai tsaye ba.
Duk wanda ya saɓa, alhaki yana kansa..
▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇
🔗 WhatsApp Channel:
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
📚 ArewaPen:
https://arewapen.com/u/asmeetahwriter
📖 Wattpad:
https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter
📲 Contact:
09065443871
📅 FARA TURA BOOK:
🔥 01 — 01 — 2026 🔥
📘 BOOK ONE
```MATAKIN FARKO```
CHAPTER 6️⃣
*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ*
Ayat tana tsaye a tsakiyar fadar, ta gama kallon sauran gimbiyoyin daga sama har ƙasa, musamman Maayah wacce aka fifita ta da fita makaranta. Ta ƙarasa gaban Sarki Zaki, ta tsaya tana kallon kujerarsa ta mulki.
Ranta ya gama ɓaci, tana jin cewa mahaifinsu ya yi fifiko a tsakanin ƴaƴansa..
Ta buɗe baki cikin muryar ƙasaita ta furta.
"Gafara nake nema ya Shugaban Masarauta. Na dawo ne domin na ji daga gare ka... Wace irin doka ce ta ba wa Gimbiya ɗaya damar fita zuwa makaranta a tsakiyar birni, yayin da sauran gimbiyoyin ke zaman mazauni a cikin ganuwar fada? Shin wane aibi ne gare mu da ba za mu iya fita kamar Maayah ba?"
Duk fadar ta yi tsit. Zayana ta ɗago ido tana kallon Ayat, tana jiran ganin yadda Sarki zai amsa wannan ƙalubalen. Maayah itama ɗagowa tayi tana kallon ta ganin yanda take ƙalubalantar makarantar ta..
Sarki Zaki ya kalli Ayat wacce ke tsaye tana huci, idanunsa sun canza launi. Ya fahimci cewa wannan karon, bawai maganar saɓa doka ba ce kawai, fushin da ke cikin zuciyar Ayat ya haura matakin da zai iya controls ɗinsa da umarni...
Cikin sanyin murya mai cike da kwarjini, ya ce
"Ki sassauta murya da zafin rai a cikin wannan fadar. Wannan yanayin za ki nuna shi ne a gaban bayinki, ba a gaban Sarki ba."
Gimbiya Zayana wacce take jiran dama ta tanka wa Ayat, ta harare ta cikin izzar turawa, muryarta na fitar da nuna fin ƙarfi ta ce,
"Wannan saɓa doka ne ya shugaban masarauta! Hukuncin da ke rubuce a littafi shi ne duk wanda ya ɗaga murya ko ya nuna fusata, in dai ba sarki ba ne, to za a kulle shi a ɗakin duhu muddin gimbiya ce. In kuma a cikin bayi ne, to ɗaurin rai da rai ne... don haka hukunci ya tabbata a kan Ayat!"....
Ayat ta juyo cikin zafin rai, ba tare da tsoro ba, ta daka wa Zayana wani irin tsawa da ya sa fadar ta amsa kuwwa...
"Hukunci bai tabbata a kaina ba ZAYANA! Ki dakata mini haka! Ina magana ne da mahaifina, ba da ke ba. Don haka ba na son shishshigi!"
Zayana ta gigice, ta miƙe tsaye jikinta na rawa saboda tsawar da Ayat ta yi mata. Ta dubi Sarki cikin neman goyon baya ta ce
"Ya Sarki! A matsayina na babbar gimbiya, wacce na fisu a shekaru da komai, ya kamata Ayat ta riƙa yi min tsawa haka? In da a gaban ma'aikatana ne, ba ka ganin za ta kunyata ni ne? A ɗauki hukun........."
Sarki Zaki bai bari ta ƙarasa ba, ya ɗaga mata hannu cikin alamun ta yi shiru. Ta koma ta zauna tana huci.
Idon Sarki ya koma kan Ayat. Cikin tsatstsauran murya ya ce
"Ɗaga murya da fusata ne zai sa na ji tsoronki na amsa miki tambayarki? Kada ki kuskura ki tabka babban kuskuren da za ki yi nadama, Ayat. Tambayar taki kuma ba zan amsa miki ba in dai da wannan yanayin naki ne."
Ayat ta jinjina kai, hawaye ya cika mata ido amma ta danne. Ta nuna Chingching sannan ta cigaba..
"Gaskiya ne, na fahimta... kana nuna fifiko ne a tsakaninmu. Ga ƙaramar ƙanwata, yarinya ce ƙarama amma me ya sa ba za ta je makaranta ba? Oh, kana gadara da cewa ana zuwa koya mana boko da Arabic har gida ko? To me ya sa Maayah take fita? Sannan kana maganar cewa zan tafka kuskuren da zan yi nadama? Uhm, dama can na fahimci ba ka ƙaunata... baka sona ko kaɗan!"
Muryar Ayat ta fara rawa yayin da ta jefa babban zargi...
"Anya kuwa kai ka haife ni? Ina tantama, domin tun ina ƙaramar yarinya nake fuskantar ƙalubale. Tabbas na ɗaga murya a fadarka, na kuma cancanci hukunci. In ma kisa ne, a yi min, domin na fi son hakan! Na gaji da duniyar nan da take cike da alatu wanda babu farin ciki a cikinta. A koda yaushe ina fatan na kasance a cikin bayinka domin sun fini wargi da walwala a cikin masarautar nan!"..
Zayana ta sake fusata ta ƙira sunanta. "AYAT!"
Ayat ta ɗaga mata hannu cikin zafin rai.
"Ba da ke nake ba!"
Idanunta sun yi jawur tsabar kuka.
Duk fadar ta yi tsit. Chingching ta fashe da kuka saboda yadda ta ga Yayarta ta fita hayyacinta..
Maayah kuwa gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi, tana jin laifin kanta ne ya sa Yayarta cikin wannan halin...
Sarki Zaki ya ƙura wa kwayar idon Ayat ido, ransa ya ɓaci matuƙa, amma akwai wani ɓoyayyen abu da ya gani a cikin idanun nata wanda ya sa ya yi shiru yana nazari.
Sarki Zaki ya miƙe tsaye, fuskarsa a murtuke tamkar hadari. Bai ce uffan ba, kuma bai ɗauki hukunci akan Ayat ba, ya juya cikin takun fushi ya bar fadar ya nufi sashensa na musamman. An bar gimbiyoyin nan biyar a tsaye, kowacce da abin da yake damunta..
Gimbiya Maayah ta matso kusa da Ayat cikin sanyin jiki, tana son ba ta haƙuri..
"Aunty Ayat, dan Allah..."
Ayat ba ta bari ta ƙarasa ba, ta ɗaga mata hannu cikin dakatarwa. "Ba na son jin komai daga gare ki, Maayah. Ki tafi kawai."
Maayah ta haɗiye yawu, ranta ya ɓaci, ta juya ta fice daga fadar inda motocinta suka ja ta zuwa part ɗinta.
Yumna ta ƙaraso kusa da Ayat, ta kamo hannunta tana shafawa cikin sigar rarrashi,
"Dan Allah kiyi haƙuri Aunty Ayat, gaba ɗaya ranku ya ɓaci daga ke har Sarki..."
Ayat ta jinjina kai, muryarta ta ɗan yi sanyi ta furta
"Naji, Yumna. Ke ma ki tafi part ɗinki."
Bayan Yumna ta tafi, sai aka bar Zayana da Chingching wacce ke tsaye tana kuka a gefe.
Zayana ta taka har gaban Ayat, tana harararta da idanunta na kyanwa...
"Gimbiya sakaliya marar kunya! Kin fusata Sarki wanda hakan zai janyo miki tashin hankali. Dole kiyi respect ɗina tunda ni ce babbarku. Idan kuma rashin kunya ce kamar mahaifiyarki, to kuwa zakiyi asara duniya da lahira!"
Ayat ta juyo a slow, ranta ya ƙara ɓaci.. murmushi kawai ta sake tare da faɗin..
"Mahaifiyata kowa zai yi mata kyakkyawar shaida akan ita mutumiyar kirki ce. Ta rasa rayuwarta ne a ɗakin mijinta, tana haihuwar ƙanwata Firdos... Ke kuma fa? Mahaifiyarki tana can Australia zaman zawarci!"
Zayana ta fusata ta ce,
"To naji! Amma uwar tawa ai a gidan mulki take a can Australia ba zaman ƙasƙanci ba. Kin zo zaki zubar wa masarauta mutunci, wallahi sai an ɗau hukunci akanki!"
Ayat ta yi murmushin raini sannan ta ce,
"Zubar da mutunci wa masarauta yayi kamar yadda kika ajiye mata ƴar waje a cikinta? Ƴa fa kike da ita wacce ba ta sunnah ba! Kuma tana nan a cikin masarautar nan. Ke ba'a ɗauki hukunci akanki ba sai ni?"
Wani irin jiri ya kwashi Zayana, ta fusata ta ɗaga hannu za ta mari Ayat. Cikin zafin nama irin na jaruman tsaro ta cafke hannun ta murɗe shi kaɗan...
Wata dattijuwa, tsohuwar ma'aikaciyar fada da ta raine su, ta shigo.
"A'a, ya haka? Gimbiyoyi da faɗa kuma?"
Zayana ta daka mata tsawa.
"Ke kuma ina ruwanki tsohuwar banza!"
Ayat ta mayar mata, "Kinga irin rashin kunyar ba? Tsohuwar da tun kafin a auro uwar ki take masarautar nan, amma kike zaginta!"....
Zayana tana nuna Ayat da yatsa ta ce,
"Har yanzu baki san komai game da ni ba, da kuma ƴar da nake da ita, amma lokaci zai yi da za ki ji koma meye kuma kafin nan sai kinyi nadama domin mahaifiyata ba za ta taɓa ƙyale ki akan wannan batun ba...."
Daga nan ta daka uwar tsaki, ta fice tana huci ta shiga motarta..
Chingching ta ƙaraso tana kuka ta rungume Ayat. Ayat ta lallaɓa ƙanwarta, ta sanya ta a mota aka kai ta part ɗinta, ita ma ta shiga tata motar don komawa ɗaki, ranta cike da tunanin yadda rayuwarta ta kasance a haka...
✨
Misalin ƙarfe 8 na dare, Gimbiya Ayat tana zaune a cikin bedroom ɗinta, ranta a jagule da tunanin rigimar da suka yi da Zayana da kuma bacin ran da ta ga mahaifinta ya shiga...
Domin har cikin ranta bata son wannan zafin ran natan, tana so ta rage amma ta kasa...
Tana cikin wannan halin, sai taji ƙiran gaggawa daga babban elevator ɗin part ɗinta...
Ma'aikatan part ɗin gabaɗaya sun ruɗe, kowa na girgiza ganin Sarki Zaki da kansa ya tako har sashen Gimbiya Ayat...
Wannan lamari ne da ba a saba gani ba, domin sarki ƙiran gimbiyoyinsa yake yi zuwa fada, ba shi yake zuwa gare su ba. Ma'aikatan mata duk suka zube a ƙasa suna gaishe shi cikin girmamawa...
Sarki ya haura stairs ya nufi ɗakin Ayat. Tana jin muryar cewa Sarki ya iso, ta miƙe tsaye cikin mamaki da fargaba. Yana shigowa ɗakin da siffarsa ta Zaki mai ban tsoro, Ayat ta ɗago kai cike da firgici..
Amma yana haɗa ido da ita, sai wani abin al'ajabi ya faru.
A gaban idon ta, siffar Zakin nan ta ɓace, Sarki ya koma asalin mutumtaka. Farin dattijo kyakkyawa mai cike da kwarjini da muradi ya bayyana. Wani irin sanyayyen murmushi ya sakar mata, wanda ya nuna cewa duk fushin da aka gani a fada, ya riga ya yafe mata. Ayat ma ta kasa boye farin cikinta, murmushi ya suɓuce mata a ɓoye cikin mayafinta.
Ya tsaya na ɗan lokaci yana kallonta. Daga bisani cikin sanyin murya ya furta.
“Ayat…”
Sarki ya zauna a bakin gadonta na alfarma, ta durƙusa ta gaishe shi cikin ladabi. Bayan ta gaishe shi, Sarki ya nuna mata kusa da shi..
“Ki zauna.” ya faɗa yana kallonta..
Ta zauna, zuciyarta na bugawa kamar zata fito.
A wannan lokacin, duk wani ɓacin rai da rigimar da aka yi a fada tsakaninta da shi ya gushe. Sun zauna tamkar wasu aminan juna, inda Sarki ya zo ne domin ya sanyaya zuciyar ɗiyarsa wadda yake gani a matsayin wata bangare ta rayuwarsa.
Sarki ya numfasa, ya kalli Ayat sannan ya fara magana cikin sanyi..
“Na zo ne ba domin in hukunta ki ba.”
“Na zo ne domin in cire miki wani nauyi daga zuciyarki.”
Ayat ta ɗago kai a hankali. Idanunta suka haɗu da nasa...
Ya cigaba da faɗin
“Na san kina tunanin an fifita Maayah a kanki ko?.”
“Na san kina jin kamar an tsare rayuwarki ne, ita kuma an buɗe mata kofa.”
Ayat ta haɗiye yawu.
Hawayen da ta riƙe tun da rana suka fara taruwa...
“Abul…” ta faɗa da muryar da ke rawa,
“Me yasa ita take fita makaranta, mu kuma a’a?”
Sarki ya yi shiru na ɗan lokaci, kamar yana zaɓar kalmomi.
Sai ya ce a hankali
“Tun kafin in auri mahaifiyarta…
Muka yi yarjejeniya da ita.”
Ayat ta buɗe ido tana kallonsa a yayin da ya cigaba.
“Yarjejeniyar cewa Maayah ba za a hana ta ilimi ba. Ta dage, ta ce rayuwar ‘yarta ba za ta tsaya a bango ba.”
Ya ɗaga idonsa zuwa Ayat..
“Ba fifiko bane, Ayat.
Alƙawari ne da aka riga aka ɗauka.”
Ayat ta sauke numfashi mai nauyi.
Zuciyarta ta ɗan yi sanyi… amma ba gaba ɗaya ba.
“To ni fa?” ta tambaya a hankali.
“Ni ba ‘yarka ba ce?”
Sarki ya miƙa hannu, ya ɗora shi a kan nata..
“Ke ‘yata ce.
Kuma akwai abubuwan da na ke kare ki daga gare su.”
Ya tsaya yana nazari tare da furta...
“Ba hukunci bane.
Kariya ce.”
Daga nan ya miƙe tsaye.
“Ki yarda da ni, Ayat.
Ba duk abin da aka rufe miki, an rufe shi ne don cutar da ke ba.”
Sarki ya kamo hannun ta tare da miƙar da ita, ya matse shi a hankali yana kallon cikin idanunta waɗanda har yanzu akwai sauran jajirwar kuka..
"Ayat, ki duba fuskata. Ba zan taɓa iya jure ganin waɗannan idanun naki cikin hawaye ba. Fushin da na nuna a fada ɗazu, ba fushin tsana ba ne, fushi ne na uba da yake son kare mutuncin ƴarsa a gaban jama'a. Ki yafe wa mahaifinki idan na sa ki jin cewa ba kya da daraja a wurina."
Ayat cikin muryar kuka ta ce,
"Abul, na zata ka manta da ni ne. Na zata Maayah kawai kake so shi ya sa kake ba ta damar da kake haramta mana."
Ya juya ya nufi ƙofa, sannan ya tsaya.
“Kada ki bari shakku ya cinye zuciyarki.”
Daga nan ya fice, ƙofar ta rufe a hankali.
Ayat ta zauna ita kaɗai a ɗakin.
Zuciyarta ba ta sami cikakkiyar amsa ba…
amma ta daina jin wani ciwon yanzu, ganin mahaifinta ya tako har zuwa yanda take....
✨✨✨
Washegari, garin Alhamra ya waye da wani irin sanyi mai ratsa jiki. Ayat ta tashi ne ba don ta koshi da barci ba, sai dai don nauyin aikin da ke kanta a matsayinta na Inuwa. Idanunta sun ɗan yi lupu-lupu saboda rashin barci da tunani wanda ya hana ta runtsawa...
Ta shirya tsaf, ta sanya ɗaurin kirjinta, ta sanya kayan maza, sannan ta ɗaura rawanin ta duk ya rufe goshin. Ta sulale ta fita daga part ɗinta ta nufi sashen jami'an tsaro....
Tana isa sashen su Ibrahim, ta tarar da shi a zaune a wani fili na sirri da yake hutawa. Yana ganin ta, sai ya saki wani murmushi wanda ya nuna cewa ya daɗe yana jiran ta. Babu sauran zargi a tare da shi, sai dai wani irin sha'awa na son jin laushin hannun yaron da yake ganin tamkar mace...
"Ka zo kenan, Ɗan Ƙwaƙur?" Ibrahim ya faɗa yana miƙewa.
"Na zata ka gudu ne saboda rigimar da aka yi a fada jiya. Zo nan, yau jikina duk a mace yake, ina buƙatar wannan tausan naka."
Ibrahim ya cire babbar rigarsa, ya rage daga shi sai farar singlet wadda ta nuna ƙwanjin hannunsa da faɗin ƙirjinsa. Ya kwanta rubda-ciki a kan wata shimfiɗa ta alfarma, sannan ya yi nuni ga Inuwa..
"Fara daga kafaɗata, ina jin zafi sosai a wurin."
Ayat ta matso jiki na ɓari. Ta sanya hannayenta masu laushi a kan kafaɗun Ibrahim. Da zaran ta fara murzawa, Ibrahim ya sauƙe wani nannauyan numfashi..
"Masha Allah... Hannunka akwai albarka, Inuwa.... Wannan laushin hannun naka ko mace ba lallai ta kasance da shi ba. Sosa min gashin kaina ma yanzu."
Yayin da Inuwa yake sosa masa gashi tare da shafa masa baya a hankali, sai tunanin labarin da Sarki ya ba ta jiya ya dawo mata. Tana tunanin yadda rayuwarsu take a matsayin gimbiyoyi amma a yau gata tana tausa wa ma'aikacin mahaifinta. Wani ƙwallon kuka ya taso mata, ta kasa haɗiyewa...
Ibrahim ya ji jikin Inuwa yana ɗan rawa, kuma ya ji kamar wani abu na ɗiga a bayansa. Ya juyo da sauri ya ga Inuwa ya sunkuyar da kansa ƙasa, kuka yake yi ƙasa-ƙasa..
"Lafiya? Me ya faru Inuwa?"
Ibrahim ya tashi zaune cikin damuwa, ya kamo hannun Inuwa.
"Ko tsokanar da ma'aikata ke maka ce ta sa ka kuka? Ko kuma Gimbiya Maayah ce ta sanya ka wani aikin da ya fi ƙarfinka?"
Ayat ta kasa magana, sai kawai ta ƙara sunkuyar da kanta, tana jin dumin hannun Ibrahim a nata. A wannan lokacin, Ibrahim ya ji wani irin tausayin yaron ya kama shi, ya manta ma da cewa shi Master ne, ya fara lallashin Inuwa kamar ƙaninsa...
A lokacin da Ibrahim ya ga Inuwa yana kuka, zuciyarsa ta karye. Bai san lokacin da ya miƙa hannu ya janyo yaron zuwa kirjinsa ba, ya rungume shi sosai yana shafa bayansa don rarrashi..
Ayat ta ji wani irin shock ya ziyarci ilahirin jikinta. Tsoro da fargaba suka ziyarce ta. A ranta tana jin zafi da ɓacin ran yadda namiji ƙato, wanda ba muharraminta ba, ya rungume ta. Tana jin kamar ta keta hurumin asalin gimbiyancinta da mutuncinta, amma tana tsoron ko kaɗan ta nuna hakan don kar asirinta ya tonu a hannun Master Ibrahim...
Shi kuwa Ibrahim, rungumar da ya yi wa Inuwa ta jefa shi cikin wani yanayi na daban. Ya ji jikin yaron ya yi masa laushi da sanyi kamar na mace, wani irin kasala da feelings suka fara bin jijiyoyinsa. Ya fara sauƙe nannauyan numfashi, zuciyarsa tana bugawa da ƙarfi.
Ya rasa gane me yake faruwa da shi.
"Me yake faruwa da ni? Dan uwana namiji ne fa amma nake jin wannan yanayin? Tir da shaiɗan! Allah ya raba mu da wannan masifar," ya faɗa a ransa, yana kokarin kore tunanin cewa jikin da yake rungume da shi ba na namiji ba ne.
Jin yadda Master ya fara sauƙe ajiyar zuciya mai ƙarfi ne ya sa Ayat firgita...
Ta yi sauri ta janye jikinta ta ja da baya tana kallonsa da tsoro a idanunta. Ba tare da ta ce uffan ba, ta juya ta bar wurin da gudu tana kakkaɓe jikinta...
Inuwa ya nufi bakin gate ɗin fada cikin gaggawa, tana son barin harabar fadar baki ɗaya don ta je bakin kogi ta huta. Ta isa wurin littafin shige-da-fice ta fara signing....
Daidai lokacin, sai ga wata mota ta alfarma ta nufo gate din. Gimbiya Maayah ce a ciki, tana sanye da tsararren uniform na makarantarta mai kyan gaske. A ka'ida, Maayah tana da mugun girman kai, ba ta taɓa leƙo kai ta kalli jami'an tsaron da ke gaishe ta ba..
Amma yau, ganin Inuwa tsaye a bakin gate yana rubutu, ya sa ta zabura....Ta rage gilashin motar kaɗan, ta leƙo tana kallon sa ta cikin glas. Zuciyarta ta harba, wani irin masifar so ya sake mamaye ta...
Inuwa ya san cewa motar Maayah ce, kuma ya fahimci tana kallonsa amma ya ƙi ɗagowa. Wani irin raɗaɗi ya ji a zuciyarsa na ganin yadda Maayah ke fita cikin lumana da mota zuwa makaranta, yayin da ita kuma take cikin shigar maza tana badda kama tana fuskantar kaskanci... Duk da tasan dalilin mahaifinsu na barin Maayah ta fita, hakan bai hana ta jin kishi ba...
Maayah kuwa, har motarsu ta fice daga gate ɗin, tana nan maƙale a glas ɗin motar tana waiwayo baya tana kallon Inuwa. Ta kasa ɗauke idonta daga kansa, tana jin cewa yaron nan ya riga ya tafi da duk kan hankalinta....
Ayat tana kan dokinta, tana tafiya cikin daji kaɗan da zai kaita zuwa bakin kogi. Zuciyarta har yanzu tana bugawa saboda rungumar da Ibrahim ya yi mata da kuma kallon da Maayah ta jefa mata. Tana cikin wannan tunanin, sai idonta ya sauƙa akan wata Kuliya kyakkyawa, mai laushin gashi, kwance a ƙasa tana nishi...
Ganin yadda kuliyar take nuna ciwo a kafar hagu, Ayat ta kasa sharewa. Duk da shigar maza take yi, zuciyarta ta mace mai tausayi ta motsa. Ta yi sauri ta sauƙa daga kan dokin ta ƙarasa kusa da ita.
Ta ɗauki kuliyar ta ɗora a kan cinyarta, tana rarrashinta da murya kasa-kasa...
"Kiyi haƙuri kyakkyawa, yanzu zaki ji sauƙi..."
Ta ciro wani mai na musamman (Pain relief ointment) wanda take yawo da shi ko da yaushe a matsayinta na jami'in tsaro. Ta shashshafa wa kuliyar maganin a wurin ciwon, sannan ta ciro wani tsumma mai tsafta ta ɗaure mata ƙafar. Maganin yanada tasiri sosai, domin jininsa na ratsa jiki...
Tana ajiye kuliyar, sai ga ta ta fara takawa. Ko da yake tana ɗan dingishi, amma zafin ya mutu baki ɗaya. Ayat ta bi ta da kallo tana murmushi har ta ɓace a cikin ciyayi...
Ganin kuliyar ta tafi cikin ƙoshin lafiya ya ba ta wani irin nutsuwa. Ta sake hawa dokinta ta ƙarasa can bakin kogi, inda iska mai daɗi take busawa...
Tana isa wurin, ta sauƙa ta fuskanci kogin wanda ruwansa yake sheki kamar lu'u-lu'u. Wannan shi ne kaɗai wurin da take jin tana da yanci, wurin da tsuntsuwarta take jiran ta, kuma wurin da take iya tuna abokinta na yarinta...
Ayat ta kalli kewayen kogin, ta ga kowa shiru, babu kowa sai sautin tsuntsaye da busar iska. Tunanin ɓacin ran da take ciki da ƙuncin da ta samu wurin Ibrahim ya sa ta jin tana buƙatar wanka don ta wanke damuwar zuciyarta...
Ta ajiye dokinta a gefe, ta nufi bakin ruwan tana jin kamar duniyar tana hannunta...
Ba ta sani ba, a bayan bishiyar da tsuntsuwarta take, akwai wata halitta mai kwarjini a tsaye, cikin shigarsa ta fararen kaya masu daukar ido, dogon farin gashinsa yana kaɗawa a cikin iska...
Ransa a ɓace yake, yana tunanin meyasa wannan yaron ya ƙara ƙetare iyakar yankin da ya zaɓa don hutawa a duniyar mutane. Hannunsa ya fara miƙa wa don ƙiran takobinsa na sihiri don ya halaka shi, amma abin da ya gani ya sa shi daskarewa a wurin...
A gaban idonsa, yaga Inuwa ya cire rawanin kansa ya jefar a gefe. Sannan ya kwance ribon ɗin gashinsa, sai ga wani uban gashi, baƙi mai santsi ya zubo har gadon bayanta zuwa kunkumi...
King Diamond ya zaro ido cikin mamaki. A tunaninsa namiji ne, amma sai yaga abin ya sauya. Ya kalli yadda take fincike gashin baki da sajen da gashin girar da ta ƙara don badda kama. Sannan ta fara ɓalle rigar mazan dake jikinta ɗaya bayan ɗaya...
Idon King Diamond yana kanta, ya kasa ko kyafta idon. Ganin surar tsararriyar mace, mai fata mai sheƙi da kwarjini ya bayyana a gabansa, ya sa ya ji wani irin Shock wanda bai taɓa ji ba a duk tsawon mulkinsa na duniyar aljanu...
Ayat kuwa, tana jin daɗi ba tare da sanin cewa idon sarki aljani yana kanta ba. Ta rage saura iya short nicket da bra, gashinta a kwance a bayanta. Ta fara takawa a hankali tana shiga cikin sanyin ruwan kogin.
Tana zura kafarta, wani daɗi ya ratsa ta, ta lumshe idanunta tana murmushi.. Ta nitse a cikin ruwan tana wasa, tana iyo cikin nishaɗi kamar wata tsuntsuwar ruwa...
King Diamond yana nan a tsaye tamkar gunki, ya kasa motsawa. Kyan Ayat da irin yadda take wasa a cikin ruwan ya taɓa wani sashi na zuciyarsa da ya daɗe a bushe....
Yana tsaye a ɓoye, yana kallon ta yayin da take wasa a ruwa. Kwatsam, sai tunanin tattaunawar da suka yi a baya ya dawo masa. Ya tuna yadda ya ji wani abu game da wannan yaron amma bai ba shi muhimmanci ba..
Ya dunƙule hannunsa, ya lumshe idanuwansa, nan take siffarsa ta mutum ta ɓace, ya koma siffar aljan wadda mutum ba zai iya ganinsa ba. Ya sulale zuwa tsakiyar ruwan, ya tsaya daidai saitin inda take wasanta.
Ayat tana nishaɗi, tana nitsewa tana fitowa tana dariya ita kaɗai, ba ta san ana kallonta ba. Sautin dariyarta ya fara ratsa kwakwalwar King Diamond. Wannan dariyar ta faɗo masa da irin dariyar Ayat tana yarinya iri ɗaya ce, ba ta sauya ba...
Ya ƙura mata idanu, yana kallon kwayar idonta domin tabbatar da wacece ita. Abin da ya gani ya sanya shi tsinci kansa cikin wani sanyayyen murmushi...
"Ayat ɗina ce..."
Ya faɗa a ransa. Wannan dariyar ba za ta taba ɓace masa ba. A lokaci guda, ya ji wani irin shauƙi na son ya rungume ta..
Yanke hukunci ya yi akan ya bayyana kansa gare ta a yanzu. Ya lumshe ido, nan take ya dawo siffarsa ta mutum sanye da fararen kaya da dogon farin gashinsa yana sheƙi a saman ruwan. Ya tsaya daidai gabanta, idanunsa na kallon kyakkyawar fuskarta.
Ayat ta sa hannu ta shafe fuskarta domin ta goge ruwan da ya taru a idonta. Tana buɗewa, sai ta yi ido huɗu da wannan halitta mai ban tsoro da kwarjini a lokaci guda. Ganin dogon farin gashinsa da shekin da yake yi ya sanya ta firgita matuƙa.....kuma bata san da mutum a wurin ba kwatsam ta ganshi a ruwa tare da ita...
Ba ta san lokacin da ta saki wani irin mahaukacin ihu ba. Saboda tsananin gigita da tsoro, numfashinta ya tsaya, nan take ta sume ta faɗi cikin ruwan. Ta fara nutsewa zuwa kasan kogin, gashinta yana yawo a saman ruwan...
Ya tsaya cak a saman ruwan yana kallon inda take nitsewa, ya ji wani irin mamaki ya ziyarce shi..
Ya fara duban jikinsa yana jujjuya hannayensa da kallon fararen kayan jikinsa, a ransa yana tambayar kansa,
"Me kyakkyawar yarinyar nan ta gani a jikina da har ta kai ga yanke jiki ta suma? Shin kwarjini na ne yayi mata yawa ko kuwa muni ne dani?..."
👍 Like
🔁 Share
💬 Comment
.jpg)