AUREN WATA UKU*
04
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
Tafiya yake cikin mota sautin Marin da mahaifinsa ya shata masa bai daina k’uwa a dodon kunnuwansa ba. Shi ba wai zafin Marin bane ya tsaya masa a rai, Marin nasa da yai gaban employees d’in Kampanin kuma masu aiki under department d’in da yake running shine abinda yafi komai k’ona masa rai. Ya sani shi dai a idanun mahaifinsa baya yin komai daidai sabida haka wann ba sabon abu bane wajensa. Ba a wajen aiki ba a gida ba.. Amma meyasa zai wulak’antasa gaban ma’aikatansa irin haka..? Ya cije labb’an bakinsa kad’an zuciyarsa na kuma k’una. Mahaifinsa ya tsanesa baya k’aunarsa, kai duka iyayen sa guda biyu basa sonsa basa k’aunarsa. Shi zai iya cewa tun tasowarsa baida wani good memories da both mahaifansa wato mahaifinsa da kuma mahaifiyarsa. Mahaifiyarsa tin tasowarsa cikin tilasta masa da tsaurara masa take wajen ganin yayi abinda zai burge mahaifinsa ya kumayi alfahari dashi. Saidai duk abinda yayi baya burge mahaifin nasa. Kullum cikin nuna masa baiyi daidai yake ba. Kullum cikin kusheshi yake da jifansa da kalamai masu muni. Tsakaninsa da iyayensa akwai wani Katanga da yai ma soyayya shamak’i dashi. Baisan soyayyan iyaye ba. Ya taso ne cikin tilastawa da k’ok’arin burge mutanen da bai tab’a birgewa ba a cewarsa. Yai gajeren tsaki yana mai kokarin kauda tinanin.
A farfajiyan gidan yai parking motarsa jikin wani tapkeken roundabout da furanni suka k’awata tsakiyarsa ga ruwa na kwaranya daga tsakiya. Cikin sassarfa ya nufi cikin gidan har lokacin zuciyarsa bai daina masa zafi ba.
Zaune ya taddata a parlornsa ta mik’e santala santalan fararen k’afafunta da suka sha ado da k’unshi . Sai faman karkad’a k’afafun nata take tana tururi ita kad’ai alamun dai isowarsa take jira.
Baiji mamakin ganinta a parlorn tinda yasan kullum cikin controlling rayuwarsa take.
Baice komai ba sabida ransa da yake a mugun b’ace.
Har yasa Kai zai shige ya sinkayo muryarta “Ai na zaci daga can bazaka dawo nan ba tinda ka zama sallamamme .”
Cak ya tsaya yana saita numfashinsa a hankali “Couldn’t you wait for me first to at least do something wrong kafin ki fara aibatani.” Ya k’arashe daidai sanda mahaifiyarsa ta k’araso gabansa ta tsaya suna fuskantar juna.
Ganin ciwo a fuskarsa ya sanya yanayinta canzawa. Alamun rauni ya bayyana saman fuskarta “Haidar.. Me ya sameka.. Ina ka samo rauni..?” Ta tambaya cikin nuna kulawa.
Murmushi mai ciwo ne saman fuskarsa. Lokaci guda ya girgiza Kai yace “Don’t act like you care Mom. Kin San hakan zai faru. Am I right.?”
Ta d’an tsare fuska “Wani irin magana ne nasan haka zai faru.. Had’arin mota Kai ko me.. Tinda dai nasan baka shiga sabgan mutane balle nace fad’a Kai da wani..”
“Babu ko d’aya Mommy..” Yai fasali yana mai shafa raunin da mahaifinsa yaji masa a labb’ansa “Meyasa ciwo a jikina zai d’aga miki hankali da girma na idan bai d’aga miki hankali a lokacin k’uruciya na ba.?”
Ya kafeta da idanu. Jin tayi Shiru batace komai ba yasa shi murmusawa kad’an da gefen bakinsa “Of course you don’t have the answer. Well, zaki iya kiran wann a matsayin tukuici na mahaifina. All thanks to you, your Majesty, Mommy.!”
Ta furzar da huci kad’an “Mai ya had’aka da mahaifinka..?”
“A usual stuff.. Banyi daidai ba, Dikda bana tunanin Akan wann ne kawai..” Ya d’an daidaita tsayuwarsa kafin yaci gaba “Nafi zaton kece kika bashi shawarin yai mun wulak’ancin da ya mun.. A naki tunanin ta haka ne kawai zaisa ki fahimci mai kike son fahimta gameda D’anda kika dasa rashin yarda da daidaito a tsakaninku tun yana k’aramin yaro. Na sani ku biyun baku zama on the same page with each other unless wann abun will hurt me deeply. Ko ba haka bane Mommy.?” Ya k’arashe yana dubanta.
Furzar da huci tai had’ida girgiza Kai “It’s for your own good Aliyu.. Dik Fad’i tashin da nake inayi ne domin ka zama mutumin K’warai sann rayuwarka ta inganta.. Bazai yuwu bayan tsayin dakan da nake Akan D’ah na na zuba ido rana daya komai ya rushe ba. Aliyu ka daina kwana a gida.. Ka tsiri wasu d’abi’u da ba naka ba.. Some strange behaviors wanda a baya bakayi. A baya baka tab’a maida mun magana kan duk abunda zan umarceka.. But now.. You’ve changed.. Completely Haidar.. Ina kake kai kudaden da kake fitarwa daga kampanin mahaifinka.. So kake ka hadani fada dashi..? A nashi tunanin nice nake daure maka gindi kake abinda ka so.. A nashi tunanin nasan duk halinda kake ciki.. What he was wrong about shine yanzu Aliyun da ya sani ya banbanta da Aliyu na wanda baya boye mun komai.. D’ah na mai biyayya a gareni koda na kasance mai tsauri akanshi.. Haidar din da baya mun musu koda munada banbancin ra’ayi..” Ta danyi fasali muryarta na rawa tana kuma matsowa kusansa “Aliyu nasan ba shaye shaye kake ba tunda bakayi ba a lokacin da tak’ura da tsanani zasusa kayi. Sann bana tunanin mata ne suka d’auki hankalinka tinda shima bakayi a baya ba lokacin da ya kamata ace kayi idan kai me yi d’in ne… Toh menene ya dauki hankalinka a duniyar nan.. Haidar please..”
D’aga mata hannu yai alamun dakatarwa “Kin rasa wann daman akan D’anki Mommy tuntuni..
Ya dan juyo yana dubanta kafin yaci gaba cikin rarrabewar kalmomi “What I do with my life is none of your Business… You said it right. Ni ba wann k’aramin yaron da kike kullewa a d’aki ki hana masa lokutansa na k’uruciya ki tilasta masa cinye takardu koda baya so..” Ya d’anyi fasali kafin yaci gaba “Kin mance ne na tuna Miki Mommy.? That unhappy little boy ya girma Mommy. Kuma zai yanda yake so da rayuwarsa ba yanda ke kike so ba.. After all, duk abinda kike yi kinayi ne sabida benefits d’inki.. Ba abu guda da kikeyi domin ci gaba na.. Kinayi ne kawai domin amfanin kanki.. Burinki shine ya mallaka min company sabida watak’ila akwai abinda kike tsoro ko kuma yake Miki barazana da rasa dukiyarsa wanda ni ban sani ba.. Shiyasa kike amfani Dani domin na zame miki makamin ki.. D’anki ba komai bane a wajenki face weapon. Yes, I am nothing to you face makaminki. Haka ne Mommy..?” Jinjina kansa yai jin bata amsa ba “Wace irin uwa ce take haka ma d’anta Mommy.? Ya k’arashe idanunsa cikin nata.
Dikda zuciyarta dake harbawa bata bari tsoro ya bayyana saman fuskarta ba. Saima girgiza Kai da take “Don’t you dare question my motherhood.. You’ve no idea what it takes to be a parent..!” Ta k’arashe tana sakin huci.
Jinjina mata kai yai “Eh bansan mene zama iyaye ba kuma bana so nai experiencing daidai da dak’ik’a guda. Kinsan dalili sabida ban taso naga misali mai kyau wajen mutanen da ya kamata na gani daga garesu ba.. “ Ya d’an kuma matsowa had’ida sassauta murya “Kin gama sanin duk abinda ke faruwa cikin rayuwar D’anki.. Do you know why..?” Ya tsare mahaifiyar tasa da idanu kafin yaci gaba “Because I’m not that scary little cat da kikai traumatizing d’inshi da son zuciya irin naki. Bazaki sake amfani dani domin cimma burinki ba.!” Daga haka sa kai yai ya shige cikin huci.
Tabi bayansa da kalamansa na kuma dakan dodon kumnuwanta har zuwa tsakar kanta. Salati kawai take.. Meke faruwa da ita..? Meke faruwa da D’anta. Ko zamanin yarinta zamanin da take kulle Haidar cikin d’aki mai duhu bai mayar mata da maganganun irin haka. Hasalima duk abinda zata masa shiru yakeyi. Ya koma kaman mai tsoron mutane, dik yanda mutane suke baya zama baya kuma cewa um balle um um. Akwai lokacin da har sukai zaton ko ya kurmance ne har saida aka had’a masa da therapy kafin maganarsa ya dawo. Ita tsoro abun ya soma bata. Yafi kama da aikin asiri.
Yana tura k’ofan d’akinsa ya hangi Anisa ‘yar k’anwar mahaifiyarsa dake aure garin Kano tsaye closet d’insa rungume da rigarsa ta lumshe idanu. Jin an turo k’ofa ya sanyata bud’e idanunta suka kuwa had’a idanu.
“What are you doing in here..? And can you explain why you are holding that..?” Yai mata nuni da rigarsa dake cikin hannunta da idanunsa.
Ta saki murmushin yak’e “Na shigo na gyara maka d’akin ne.. Mommy tace kwana biyu baka kwana a gida.. Nima d’in jiya da dare na shigo garin..”
Baiyi mamaki ba dan Mommy ta turo Anisa d’akinsa. Yasan kad’an ne da aikin Mommy ta turo Anisa tai mata binciken k’wak’waf cikin d’akinsa dukdai dan ta gane what’s been going on cikin rayuwarsa.
“Get out.. I need to change..” Ya fad’i yana mai shigewa cikin d’akin lokaci guda yana k’ok’arin undressing Kansa. Suitcase ya ciro Anisa tana gani ya shiga ciro kayansa yana sakawa ciki.
Mamaki ya cika Anisa da ganin yanayinsa. Tasan bai iya fushi ba dukda kuwa ba kasafai kake gane normal days d’insa ba. Definitely dai wani abu na faruwa dashi. Ta girgiza kai kad’an. Sauri sauri ta fito ta nufi wajen da Mommy Ke tsaye tana tsaka da salallami. Anisa d’iyar k’anwar Mommy ce mai suna Asshe dake zaune a garin Kano. Daren jiya tazo gidan dama takan d’an zo tai masu kwanaki lokaci zuwa lokaci.
“Mommy wai lafiya.. Wai meke faruwa ne a gidan nan..?”
Har lokacin Mommy bata amsata ba ta kasa furta koda kalma. A haka Haidar ya k’araso ya shigesu ya barsu nan tsaye suna binsa da kallon mamaki.
“Aunty Kwaise..” Ta kira Mommy da sunanta kafin taci gaba “Wai meke faruwa ne.. Ina zaije shi da suitcase..?”
“Ban sani ba mana Anisa. amma hala Ke zaki iya sani..” Mommy tace a hasale.
Anisa da mamaki bai saketa ba tace “Mommy ta ya zan sani nida jiya jiya nazo gidan..”
Mommy ta shiga janyo hannunta cikin sauri tana fad’in “Binshi zakiyi ki gane mana yanda zaije… Maza maza kafin ya b’ace kinsan yanda car keys suke ai. D’au d’aya ki bi mana bayansa. Kar barshi ya b’ace ma ganinki Anisa..”
Anisa kaw tamkar wacce take jira gudu gudu tai yanda Mommy tace.
Tana tafe saman kwalta cikin k’ok’arin bin hanyar da taga Haidar yabi ganin bai b’ace mata ba kaman daga sama taji an daki bayan motarta da k’arfin gaske wanda hakan yai sanadiyar da motar Haidar ta b’ace mata.
A dole ta danna birki kanta ya daki jikin staring wheel. Kafin ta sami zarafin fitowa daga cikin motar mutumin da ya daki nata motar ya b’ace bashi a wajen. Mamaki ya cika Anisa ganin babu kowa bayanta da alama wanda ya mata wann aika aikan yayi gaba. Ta furzar da huci a hankali tana kuma duba bayan motar.
Bin bayan Haidar da batai ba kenan dole ta koma gida.
**
KANO
Yau d’in yaran Mama sunzo yini daga gidan mazajensu dan tini Mama ta kirasu a waya d’aya bayan d’aya ta sanar dasu abinda ya faru na amshe lefen Ummulkhairy da akai. Dan haka washe gari kaf suka hallara. Sukai bak’e bak’e tsakar gidan suna watsa habaice habaice. Idan an Fad’i abinda ya basu dariya kaji Sun saki shewa harda gud’a.
Umma kaw ta kasa ko fita tsakar gida sabida habaice habaicensu. Ko abincin rana Sun kasa fita suci kasancewar girkin Maman ne. Ta kuma hana Ummul da Khulsum fita ko k’ofa.
Khulsum ta dubi agogo k’arfe d’aya saura na rana. Ta dubi Umma dake zaune ta rapka uban tagumi tana sauraron habaice habaicen Mama dasu Salima.
“Umma lokacin sallan azahar yayi zan fita nai alwala..” Ta Fad’i tana k’ok’arin mik’ewa.
Saurin janyota Umma tai tana aika mata mugun kallo “A haka ne zaki fita su cinyeki da habaice habaice.. Nemi waje ki zauna akwai sauran lokaci.” Ta k’arashe tana zaunar da Khulsum da k’arfin gaske.
Khulsum ta dubi mahaifiyarta da tsanin mamaki “Haba Umma dan Allah shikenan har ibada ma kar muyi sabida muna tsoron maganan mutane.. Umma shikenan yau a d’aki zamu yini sabida maganganun mutane.. Umma dan Allah ina kika tab’a Jin mutane Sun fasa magana.. Kuma waye magana ya taba kashewa.? Umma komai mukai wllhi sai anyi magana gara ma ki bari mu fita muyi ibada mu rok’i Allah mafita da zaman tagumin da muke uwar d’aki.. Umma zaman mu a d’aki fah bazai sa su fasa maganganunsu ba..”
Kuka Umma ta kece dashi tana fad’in “Dik ba kece kika jawo ba.. Kin tsaya kina dambe bakin kwalta.. Yo ba da dole Zubairu da yaga haka yak’i dawowa ba.. Nayi imani ba don ya hanngi Ummul na rabon fad’a ba da ya taho ya nemi afuwa ya kuma sa an maido da lefen nan dan Zubairu yaron kirki ne.. Amma jarabar fad’anki ya jawo Zubair ya kufce ma ‘yaruwarki.. Dole ma kice kar mu damu da maganganun mutane sabida ba lefenki aka amshe ba.. Wayyo ni Suwaiba wani laifi nai nake fuskantar irin wann iftil’ai..!” Ta kuma d’aura hannayenta aka tana kuka.
Su Mama dake mak’ale bakin k’ofa komai a kunnuwansu. Badia ta janye labule ta lek’o tana fad’in “Gaskiya Khulsum bakida mutunci wann ai zubar mana da mutuncin gida ne dambe da k’artai a bakin layi..!”
Mama tai karaf tace “Ah toh hassada take maku ku da kuka samu Allah ya rufa maku asiri kuke d’akin mazajenku bari tai abinda zai Shafa maku bak’in fenti wajen dangin mazajenku.. Yo sukaji ‘yaruwarku guda an kuma amshe lefe da sadakinta d’aya kuma tana dambe da k’artai a bakin layi ai cewa zasuyi duk zuri’arku haka kuke ke Salima me kishiya ta samu abun goranta Miki..”
Haba nan fah Salima ta kuma harzuk’a ta fad’a d’akin tana kokawan janyo Khulsum tana fad’in wllhi bata isa ta kashe mata aure ba.
Umma na kuka take rok’on Mama da yaranta da sukai ma Khulsum taron dangi suyi hak’uri su fice. Itakam Ummulkhairy kuka ma ya hanata katab’us yayinda Mama ke kuma ingizasu. Kan kace me ayarin yan cikin gidan Sun cika a k’ofan sashen su Ummulkhairy suna bama idanu abinci. Tuni masu jin haushin Khulsum suka goyi bayan Mama da yaranta cewa Khulsum zata b’ata masu sunan ahali bayan fentin da Ummulkhairy ke Neman shafa masu suma ak’i Neman auren yaransu.
Ana wann kacaniyar mahaifinsu ya dawo daga Kasuwa. Ganin iyalansa haka yasa shi Jin kaman wani abu ya sokesa a k’ahon zuciya. A hankali ya dafe k’orjinsa yana k’ok’arin silalewa.
SameenaAleeyou…📚
