AUREN WATA UKU.!*
*12*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
Tinda suka koma gida ya gaza samun sukuni. Tunaninta ya addabesa. So yake ya tambayi mahaifiyarsa gameda ita. Sosai yaji yana son sanin labarinta.
A parlor ya tadda Hajja tana had’a wasu kayan d’inkinta. Ya zauna daga gefe.
Ta d’ago ta dubesa “Har kaci abincin kenan..?”
D’an furzar da fuci yai kad’an yana mai shafe fuskarsa da tafukan hannayensa “Naci Hajja ya isheni..”
Ya d’anyi gyaran murya kad’an yana duban kayyayakin dake gabanta “Wai Hajja har yanzu bazaki hak’ura da d’inkin nan ba. Yanzu fah Allah ya rufa mana asiri I can take care of you , you don’t need to do all these things.”
Murmusawa tai “Ban raina k’ok’arinka ba Hisham. Amma kasan idan ba idona ne ya tafi ba ko k’arfina ya k’are bazan iya daina sana’ata ba. Sana’ar da na raineka da ita har ka zama abinda kake a yau cikin k’udirar Ubangiji. I love being independent kai kafi kowa sanin hakan.”
Ko shakka babu ta tuna masa zamansu a Maiduguri, hardships da suka fuskanta da ma duk wani k’alubale na rayuwa. Ya d’an jinjina kai ba tareda yace komai ba.
Ta kuma d’agowa tana dubansa. Sai ta aje abinda take ta bada hankalinsa akansa sosai. Ta ambacesa da sunansa na yanka. Ya d’ago yana dubanta. Taci gaba “Ni a halin yanzu nafi buk’atan ka gina naka ahalin. Ka haura talatin already. Kayi karatu ka samu aiki mai kyau. Rayuwarka ta inganta Mai kuma yayi saura bayan iyali. Bazan tak’ura maka ba ko na tilasta maka amma ni a nawa tunanin ya kamata ka fara making efforts. Kaga yanda kake tafiya ka barni ni kad’ai d’in nan sai ka barni da abokan wasa.”
Ya d’an murmusa dan ya d’ago mai take nufi.
“Toh Hajja ki sama min Matar mana kawai a nan tinda ni dai har yanzu ban samu ba.”
Tab’e baki tai tana mai ci gaba da abinda take “Idan na zab’a maka zaka amince da zab’ina ne.. Kasan ku yaran zamani ba’a maku katsalandan a wann sha’ani. Yanzu sai ku ba wa mutum kunya.”
Ya kuma murmusawa “Haba Hajjata. Nasan bazaki tab’a zab’a min abinda zai cutar dani ba. So na baki wuk’a da nama.”
“Ta d’an kuma tab’e baki “Na Jika dai.. Amma tina kace haka shikenan.. Ka jira kaga.. Next zuwa da zakai zaka tadda iyalinka na jiranka ne..”
Ya d’an zaro ido waje “Hajja ina kika tab’a jin anyi aure Ango bai halarta ba..?”
“Za’a fara akanka tinda Wakili kawai zan tura ya karb’ar maka. I already have someone in mind dama.”
Ya d’an fito daga cikin kujeran cikin zak’uwan san jin yaji ko wacece “Da gaske Hajja.. Who’s she.. A ina take..?”
Ta d’an dubesa “Idan lokacin yayi ka ganta.”
Ya kuma murmusawa kad’an. Shiru kaman babu mai cewa komai sai Hisham yai gyaran murya kad’an “Nikam Hajja nace… Ita yarinyar nan Ummul-khair…”
Hajja ta zuba masa idanu jin yanda yake maganar cikeda kulawa ga wani k’alk’ala na musamman da ya ambaci sunan Ummul dashi “Umhum ina sauraronka.” Ta fad’i still tana dubansa.
“Wai dama kun jima da sanin juna ne.. Or do you have any relationship with her family.?”
Hajja ta d’an murmusa “ Banda abinka Hisham yanzu ak’alla shekaru hudu fah muke nema a garin nan. Kaga ai ya kamata na saba da mutane kuma idan baka mance ba na sanar dakai ina koyar da sana’ar d’inki ma ‘yanmata. Toh Ummul tana cikin d’alibai na.”
Hisham ya jinjina kansa a hankali “And she’s from around this neighborhood..?”
Hajja ta kuma murmusawa kad’an dan ta lura da curiosity na d’an nata gameda Ummul. Ita idan har abinda take hasashe ya tabbata zatafi kowa farin ciki. Dan Ummul yarinyar kirkici wacce jarabawa da k’alubalen rayuwa sukai marfi ma rayuwar nata.
Gyara zamanta ta d’anyi ta kaikato sosai tana duban Hisham “Naga alama dai tambayoyi ne kazo dasu wann karon.. Amma ka bari har Allah ya wayi gari lafiya kaga yanda ranar yau d’in ta kasance mai tsawo. Idan ka samu ka huta zuwa gobe da safe idan Allah ya nufemu da kaiwa sai na amsa maka duka tambayoyinka.. Maza tashi kaje ka kwanta haka ka huce gajiya kuma. Kaga nima kwanciya zanyi haka nan.” Ta k’arashe tana k’ok’arin tattare kayan.
Hisham ya amshe yana linke mata su . Dan yanda ya kwana biyu baya tareda ita d’in nan dik abinda zaisa ya samu albarkanta baya wasa da wann abun komin k’ank’ancinsa.
**
Sassafe Mommy ta fito da zummar komawa Abuja dan dama day trip tayi niyyan yi amma sabida accident da suka d’an samu dole ta bari sai Washe gari bayan an duba lafiyan motar an tabbatar zata iya tafiya.
Ta dubi Asshe “Na bar miki wuk’a da nama amma ki tabbata wacce duk za’a samu tanada futures da qualities da zamu iya jan ra’ayin Haidar dasu in just a short time. Lafiyayya wacce batada wani cutan da zai iya shafan d’ana.”
Asshe ta d’an numfasa “Bakida matsala Aunty Kwaise ai kaman yanda kikace ne a duniyar nan babu abinda kud’i bazai sai maka su ba. Ni yanzu damuwata matar da muka bige wacce har yanzu Ke asibiti gashi babu wani means of identification tareda ita balle a samu wani nata.”
Mommy tace “Aff kinga ni na mance ma da batun wann matar. Yanzu tareda waye aka barta a asibiti.?”
Asshe tace “Mai aikina Marka ita ta kwana da ita suna can tare yanzu haka..”
Mommy ta jinina Kai dan dama wani private hospital suka kaita “Duk abinda ake ciki dai kin sanar dani. Ni yanzu tafiya ya kamani, dan kinsan na fad’a miki Engr baisan na taho ba shima baya nan ya tafi Lagos tafiyar da ta shafi Kasuwancinsa.. So bani so ya dawo gidan ya tarar bana nan. Anisa ce kawai gidan kinsan kuma yanda take saitin da sauk’i.
Asshe ta kuma jinjina kai “Zakiji komai in sha Allah Aunty Kwaise. Allah ya tsare hanya.”
Suna tsaka da sallaman Hilal ya k’araso wajen. Mommy ta dubesa “Bazan amsa goodbye d’inka ba tinda har zaka zo hutu k’asar nan kuma jirginka ya sauk’a a Abuja ka kasa zuwa ka dubani.. Inji kaima kabi sahun d’an uwanka Haidar ne.?”
Hilal matashin saurayi d’a ga k’anwar Mommy Wato Asshe ya d’an murmusa yana shafa kansa. Baifi sati da zuwa Nigeria ba karatu yake a k’asar Cyprus. Ya samu zangon hutu.
“Haba mana Mommy ta kinsan bazan miki haka ba. Tareda Abba da matarsa muka dawo Kano daga Abuja shiyasa. Nasan duk Anisa ce ta had’ani dake. Amma kafin hutuna ya k’are zaki ganni in sha Allah. I still have 2 weeks here.”
Mommy ta murmusa “Toh shikenan sai na ganka.. Ina nan Ina zuba ido.”
Hilal ya murmusa yana tabbatar mata zaizo. Ya nufi wajen driver yana tambayarsa hope motar bata samu matsala ba.
Mommy ta dubi Asshe ta d’anyi k’asa da murya “Oh kiji min Hilal wai Abbansa da matarsa. Kinji yaro na taya mahaifiyarsa kishi.”
Asshe ta tab’e baki “Yo yarinya ce k’arama Anisa ma ta fita Kinga kuwa yaushe zai wani bata matsayi.”
Mommy tai yar bazawarar dariya “Allah ya rufa asiri dai bai had’eku gida d’aya ba dan nasan da sai an kwashi ‘yan kallo tsakanin yarinyar da Anisa wataran.”
Asshe ta kuma tab’e baki “Ai Anisa gaba take da Uban nasu tinda yayi wann jarababben Aure. Sun had’e kai da sauran ‘yanuwanta ‘yanmata yaran uwar gidana suna gaba da ubansu ya auro sa’arsu. Shiyasa ma bata cika son zaman Kano yanzu ba tafi son zama can Abuja wajenki to avoid seeing her father here.”
Mommy tai shiru tana tuna case d’in dake nata gidan. Ta d’an numfasa “Gwara su idan sunyi gaba da Ubansu sunada dalili.” Tai maganar tana k’ok’arin shigewa mota suna kuma sallama da ‘yaruwarta.
Kasancewar fitan sassafe tayi yasa ta samu isowa da wuri. Tuni tasa ma’aikata an soma dafe dafen abincin da za’a tarbi Daddy dasu.
Suna zaune shida ita a parlor bayan ya ida cin abinci magazine rik’e cikin hannunsa yana dubawa.
Mommy dai sai digesting maganganun da boka ya sanar da ita take. Ta rasa ta yanda za’ayi ta soma sanar da mijinta batun. Toh ma mai zata soma sanar dashi. Cewa d’ansu yayi Aure ba da saninsu ba.? Kodai mugun asirin da aka jefesa dashi.? Ko kuma auren da Malaminta yace a masa wanda shine makarin sihirin. Ta ina zata faro. Tana tsaka da tunanin kaman wanda aka jefo sa suka sinkayo sallamansa.
Yau Mommy ta rasa duban tausayi take masa ne ko duban sakacinta akansa.
Kallo d’aya mahaifinsa ya masa ya watsar.
Ya k’ariso hannunsa rik’eda shud’in Folder mai d’aukeda logo na Kampanin mahaifinsa jiki Wato (MB).
Gaisar da iyayen nasa ya soma yi daga nan yanda yake tsaye bayan kujera dan yasan he’s always not welcome. A gidan da ya kamata ya kira da home.
Mommy ce ta amsa gaisuwarsa yau d’in da sakin fuska. Ga wani mugun sanyi da tayi. Mahaifinsa kaw bai samu zarafin amsa masa ba.
Mommy ta d’anyi murmushin da yafi kama da yak’e tana duban mijin nata da kacaukam hankalinsa Ke bisa Magazine d’in dake hannunsa. Wani article ne ya d’auki hankalinsa yanda aka rubuta ‘FG to approve the billion dollars bridge project to Maitama Builders.’ Project din da Haidar keta fad’I tashi akai ganin an zab’esa matsayin Project Manager.
Mommy ta d’anyi gyaran murya “Engr Haidar na gaidaka.”
Har lokacin idanunsa naga magazine d’in “Na ganshi ai.. Sai ya fad’i abinda ya kawo shi. Yai maganar ko kallon yanda Haidar yake baiba.
Haidar ya had’iyi bak’in cikin da ya tokare masa mak’oshi.
Mommy dai gaba d’aya jikinta a sanyaye yake yanzu tinda Malaminta ya sanar da ita abinda Ke faruwa. Ya zama dole ta bada himma wajen had’in kan ahalinta bazata bari azzalumai suyi nasara akansu ba. Ta dubi Haidar wanda ya kafe mahaifina da ido kaida gani kasan ba kallon komai yake masa ba face tsana. Ta k’ak’aro murmushi “Haidar you heard your Dad.. Ka shigo ka gabatar masa abinda ya kawo ka nasan ya shafi aiki tinda ga company’s folder hannunka.
Bai dubi Mommy ba tinda dukansu haushi suke basa ya k’arasa yanda mahaifinsa yake. Ya aje folder d’in gefensa kad’an “This is the new proposal my team and I have been working on.. It contains all the details, the construction deliverables.. The scope and budget of the project..” Ya d’anyi fasali jin bai amsa sa ba kafin yaci gaba “You..can go through it and see, before we present it to the board of directors..”
Har lokacin bai amsa sa ba. Kaman ba dashi yake ba haka Daddy yayi. Haidar ya kuma had’iyan k’uncinsa. Duk abinda mahaifinsa zai masa akan wann project d’in ya zama dole ya shanye. Alk’awari yayi sai yasa mahaifinsa ya cinye duka kalamansa. He never backs down. He must fulfill all his promises. Zai wanke kansa zai kuma sa mahaifinsa ya cinye kalamansa sann daga k’arshe he will personally take the company down to the ground. To the last kobo. Ya ranste sai ya tarwatsa mahaifinsa da kansa.
Sai matse file d’in yake cikin hannuna jijiyoyin jikinsa na kuma tashi kaikace ketata zai.
Muryar Mommy ya sinkayo tana tausan mijin nata da yaji bayanan d’an nasa ya kuma sauraresa.
Kaman bazaice komai ba sai yai masa nuni da hanyar da zai sadaka da study d’insa daga nan cikin parlorn.
“You can leave it over there. Maybe, I’ll go through it when I’m less busy…” Daddy yace yana mai rufe magazine d’in had’i da zame farin glasses na k’ara k’arfin gani “I just hope it is not one of your foolishness.”
Haidar ya rintse idanunsa yana jin abun har cikin k’ahon zuciyarsa. Bai kuma juyowa ya dubi mahaifan nasa ba yasa kai ya shige cikin sauri kafin zuciya ta d’ibeshi.
Yana shigewa Mommy ta mik’e tabi bayansa da sauri dan wani tunani ne ya fad’o mata wanda k’ila damarta kenan akansa.
A waje yanda ya aje motarsa ta cimmasa.
Ta bud’e murya ta kirawo sunansa.
Kaman bazai tsaya baya, sai kuma ya dakata ba tareda ya juyo ba yana mai furzar da huci a hankali.
Mommy tai saurin k’arisowa yanda Haidar ya kaikaito yana dubanta.
“What now.? Kin mance ne baki bani naki insults d’in ba shine kika biyoni waje..?” Ya fad’i idanunsa akan mahaifiyarsa.
Mommy tai k’ok’arin dannewa dan yanzu ta tabbata he’s not in his right state of mind.
“Kaga Haidar I’m not your enemy here.. In fact taimakonka nake so nayi.. Naga yanda kake matuk’ar so kai handling project d’in nan… Kuma nima na tabbata kai kafi cancanta kayi d’in… I can be your ally until your achievement.”
Murmushi Haidar yai hannayensa dafe da kunkumi yake duban Mommy. Sai kuma ya girgiza kai yace “Seriously Mommy.. You wanna be my Ally..? Since when Mommy..? Yaushe kika fara damuwa dani da abinda ya shafe ni..?”
Mommy ta zuba masa idanu.
Haidar yaci gaba “Kinsan meye damuwarki Mommy.. Shine ya amince na jagoranci aikin sabida personal interest d’inki. Kinsan na jima da sanin ni a wajenki ba komai bane face weapon. Makaminki.. Kuma kar ki mance na fad’a miki bazaki sake amfani dani ba wajen cimma wasu mnufofinki. Wancan Aliyun ya Riga ya mutu Mommy.. He’s long been dead.!”
Yana ida fad’in haka yasa kai ya shige motarsa sai sakin huci yake.
Zai bud’e marfin motar kenan Mommy tai saurin dafa hannunta saman nasa. Hawaye suka soma gangaro mata. Cikin tsananin rawar murya take furta “Haidar… What did they give you.. What have they done to you to turn you against us like this..?”
Cikeda k’osawa ya zame hannun Mommy daga saman nasa “Ba hawayen da zaki zubar da zaisa na yarda dake Mommy. You destroyed that bond tin da jimawa. So kar ki saka ma kanki ciwo Mommy.. I do not give a damn about this family. I’m doing this project for my own personal interest of course. Kuma bazaki tab’a sani ba until my mission is accomplished.” Yana ida fad’in haka yasa kai zai shige motarsa.
Mommy ta bud’e murya tace “Idan ni ce Matar Aliyu Maitama har sai kazo nan ka amince da buk’ata ta kafin ya saka hannu da sunanka saman project d’in nan.!” Tana ida fad’in haka tasa kai ta juya cikin gida ba tareda ta kuma sauraronsa ba.
Juyowa yai yana duban Mommy yana so ya fahimci mai take nufi cikin kalamanta. Yasan mahaifiyarsa tinda ta fad’i haka tanada wani babban dalili a k’asa tana kuma so ya tank’wara shi ne yayi wani abinda take so. Zaiyi duk yanda zaiyi ya tabbata bai fad’a tarkon da take k’ok’arin d’ana masa ba.
**
Kano.
Waya ta ida yi da Marka yanda ta sanar da ita Matar ta farka amma bata cewa komai. Kuma bata fad’i yanda danginta suke ba balle a nemsu. Ga dukkan alamu idan ba mai tab’in kai bane k’ila had’arin ya tab’a mata kai.
Hilal ne ya tuk’ota zuwa asibitin. Ta dubi Marka ta dubi matar wacce Ke ta zabga kuka saman gadon asibiti.
Marka taci gaba da fad’in “Ayya Hajiya ‘yan jikokina suna gida basu ganni ba tun jiya. Wllhi duk na gaji gida nake son zuwa ga wann asibitin babu mutane sosai balle likitoci kinsan yanda asibitin kud’in nan suke zuwan likita nada k’aida da lokaci. Tak’i magana tinda ta tashi kuka take. Inaga Hajiya kawai idan likita yazo ruwan da aka d’aura mata ya kare kisa a sallameta ai kunyi naku Allah ya gani.”
Hilal ya girgiza kai yana duban Matar cikeda tausayi “No Ammi. Ba haka za’ayi ba. Inaga kamata yayi akaita wajen k’wararru su sake dubata. Watak’ila ta sami wani internal injury. Kamata yayi akaita a dubata a bata all the treatment that’s needed. Idan ya kama mu mik’a case d’inta ma hukuma su zasu bincika yanda danginta suke. But we can’t abandon her not knowing ina danginta suke. Watak’ila sunata nemanta tin faruwar had’arin.”
Asshe ta katsesa “Kai Hilal nayi na musulunci tinda har asibiti mun kawota. Har wacce zata kwana da ita na bari. So bazanyi treating ciwon haukanta ba. Tafiya take tsakiyar kwalta dama can k’ila da guntun haukarta.” Ta dubi Marka tace “Marka jeki abinki zan fad’awa nurses d’in da suke bakin duty da zaran likita yazo suna iya sallamarta.”
Marka tai godiya da fatan samun sauk’i ta fice.
Hilal ya girgiza kai zai kuma magana ta nuna masa waje “Fita mota ka sameni ina zuwa zanyi magana da mutanen asibitin.”
Ba Don yaso ba ya girgiza kai ya fice.
Asshe zata take masa baya kenan ta sinkayo muryar Matar tana fad’in “Lafiyata garau. Kuma duk ina sauraronku. So nake ku d’aukeni ku kaini can babban asibitin koyarwa yanda mijina yake ko zan samu na ganshi. Tani ta hana ni ganin shi tace nida Ummul mu muka taru muka saka masa ciwo.. Ta ina zan soma neman kud’ad’en da Tani tace na nemo na jinyar Malam. Tani takai mak’ura wajen makirci da zalunci.” Ta soma kokawan sauk’owa daga gado dikda drip dake d’aure hannunta. Fad’i take “Na tabbata tana can ta d’aura laifin komai akan Ummul da bak’in k’addarar da yai ma rayuwarta dabaibayi.”
Asshe tai saurin k’arisowa ta dakatar da ita.
Umma ta d’ago ta dubeta sai ta fashe da kuka “Wllhi lafiyata k’alau ina cikin hayyacina. Sun kasa gane banida wani buri da ya wuce naga Ummul a d’akin mijinta. Toh meyasa Tani zata d’aura alhakin ciwon Malam akaina da Ummul.?” Taci gaba da rera kuka irin na wanda damuwa ya masa dabaibayi.
Asshe ta janyo farar kujera a gefe ta zauna tana duban Matar “Sunana Hajiya Asshe, mun bigeki da mota akan hanyarmu.”
“Yaya Tani ce tace lallai lallai sai na nemo kud’ad’en da za’ayi ma mijinmu jinya idan har ina so na sake ganinsa. Ta nad’i sautin muryata cikin waya itada Badi’a sunce ko Kotu akaje ya iashesu Hujja.”
Asshe ta zuba mata idanu jin yanda taketa maganganu marassa ma’ana. Labarun da yafi kama da wanda ke cikin depression. A hankali ta d’an jinjina kai ta dubi Matar “Akwai yanda yake miki ciwo ne. Kina so na kira Likita.?”
Umma ta girgiza mata kai alamun a’a”Baiwar Allah ni fah lafiyata lau. Yaya Tani ce ta yanka ragon hauka ta d’aura mun dan kawai Ummul ta kasance ‘yata.” Sai ta d’anyi fasali ta kuma duban Asshe “Amma wacece ke.?”
Asshe ta k’ura mata idanu tana karantarta sai tace “Toh ma sha Allah. Tinda kince babu yanda yake miki ciwo.” Tai fasali dan sosai take so taji labarin Matar musamman da taji abubuwan dake fita bakinta shan cikin Matar bazai mata wahala ba “Ki kirani maganin matsalolinki.!” Ta matso had’ida d’aura hannunta saman na Umma “Ki yarda dani zaki iya sanar dani duk damuwarki. Ni ba muguwa bace nasan zaki fahimci haka tinda bayan bigeki da mukayi bamu k’yaleki ba saida muka tabbata mun d’aukoki mun kawoki asibiti. Kuma ban barki ke kad’ai ba har saida na ajiye wacce zata kula dake. A nan muka shigo da yarona kikaji yana cewa kar mu kyaleki har sai mun tabbata kin isa ga ahalinki lafiya. Wann kawai ya isheki ki yarda mu mutanen k’warai ne ba masu cutarwa ba. Kuma a yanda yanzu duniya ta koma babu yarda tinda har ni nayi shahada na yarda dake ya kamata nima ki d’auki duk yarda ki bani. Watak’ila Allah ne ya dubeki ya had’aki da maganin matsalolonki.”
Da mamaki Umma Ke dubanta “Maganin matsalolina ni Suwaiba..?” Tai maganar tana nuni da kanta. “Baiwar Allah anya kaw kinsan matsalolina..? Ai inaji kaf fad’in garin Kano da kewaye babu matar da ta kaini matsaloli tinda har na kasance mahaifiya ga Ummulkhairi.!”
Asshe ta kuma gyara zama cikin son jin taji komai “Wacece Ummulkhairy.?”
Umma ta kamo bakin zaninta tana share hawayen dake kuma zubo mata “Ummulkhairi, ‘Yata da na mata lak’abi da Uwar alkhairi..! ‘Yata da naci mata buruna da dama.” Ta kuma duban Asshe sai ta girgiza kai wasu hawayen na kuma gangaro mata “Amma babu buri guda d’aya da ya cika. Kinsan dalili..?”
Asshe da ko kifta idanu batayi saurin girgiza kai tai alamun a’a.
Umma taci gaba “Sabida mutane sun canfa mun ita.. Duk namijin da yazo neman aurenta guduwa yake. Kodai wani abu ya gifta a fasa Auren. Amma fah dukda wann guje mata da mazan keyi basu fah fasa neman aurenta ba. Kinsan meyasa..?” Tai tambayar murmushi mai ciwo saman fuskarta kafin taci gaba “Sabida Ummul d’ita tubarkallah ce san kowa k’in wanda bai samu ba.” Sai kuma ta fashe da kuka “Amma meyasa ta kasa Auruwa..? Meyasa duk masifa da nake fuskanta a nawa gidan Auren ta dalilinta ne.? Meyasa maza ke guje mata. Meyasa k’addararta yazo a haka.” Ta k’arashe cikin gunjin kuka.
Asshe ta kamo hannayen Umma cikin nata tana k’ok’arin kwantar mata da hankali “Ki daina kuka. Shi Aure lokaci ne. Baya duba matsayi ko kyaun halitta. Wata da komai ta rasa miji wata ba komai Allah ya bata. Shi Aure kaman hab’o ne da zaran lokaci yayi sai kiga anyi..”
Cikin zuciyar Asshe fal mamaki. Ganin abun take kaman almara. Abinka da mai b’atacciyar zuciya sai ta kuma gaskgata aikin bokansu. Gashi tin ba’aje ko ina kaman sun had’u da makarin sihirin dake jikin Haidar a sauk’ak’e. Sai ta kuma yarda gaskiya Malaminsu ya fad’i ta mance cewa wann duk zai iya zama jarabawa daga Ubangiji mai komai ya baka abinda kake nema d’in a kan gab’ar da kake nema. Wani shikenan sai ya kuma dulmiya cikin b’ata. (Allah kai mana tsari da shirka. Ameen)
Ta saki murmushi tana duban Umma “Ummulkhairinki zatayi Aure. Aure na bajinta. Aure irin na kece raini. Auren nuna ma duniya.!”
Umma ta dubeta da mamaki. Sai ta girgiza kai tace “Anya kuwa Ummul d’ina nada rabon Aure a wann duniyar.?”
Asshe ta murmusa “Idan har kika aminta dani Ummul d’inki zatayi Aure..” Tai maganar cikin jaddada kalamanta.
Hilal ne yai knocking ya lek’o jin shirun yayi yawa. Nan ya hangi mahaifiyarsa da patient d’in kaman sun jima da sanin juna. Mamaki ya cika Hilal. Ya d’an girgiza kai yana mamakin saurin yarda da juna da mata keda shi saikace ba Ammi bace ta gama cewa su tafi su kyale matar. Bai gama mamaki ba saida yaga Amminsa sun fito tareda Matar dan dama da ya shiga tace masa bari likitan yazo ya masu sallama tinda taga isowar motarsa. Shidai Hilal haka ya tuk’a su suka nufi gida tareda Matar dasu Ammi suka bige wacce ta zamto bak’uwar Ammin tasa.
Suna isa gida Hilal ya tareta “Ammi Wai meke faruwa ne. Meyasa kika taho da matar nan.. Ammi I thought danginta za’a nema.. Nowadays fah mutane ba abun yarda bane. This whole thing zai iya zama shiri bigeta da kukayi, kaita asibiti da duk wani maganganun da zata sanar dake. Ammi yanzu fah har gida ake ture a sace mutane. Ammi Abba sanannen mutum ne a garin nan. Iyalansa zasu iya zama target.”
“Kai dallah rufe min baki. Duka duka yaushe ka sauk’a k’asar balle ka fad’a min abinda Ke faruwa cikinta. Nafika sanin meke faruwa. Ina zuciyar taimakon taka? Inji kai ka fara cewa we shouldn’t abandon her. Toh Shiyasa na taho da ita. Kuma ko mahaifinka yazo gidan nan ba ruwanka kar ka sanar dashi komai kaji na fad’a maka.”
D’an girgiza kai yai “Fine, yanda kikace Ammi.” Hilal yasa kai yai shigewarsa.
Yana shigewa ta d’aga waya tai dialing wani layi. Ana d’agawa ta soma fad’in “Hello Yunusa kanajina. Zan turo maka information kan wata mata. Yanda take zama sunan mijinta da sauransu. Inaso ka gudanar min da binciken k’wak’waf kan ahalinta da abinda Ke faruwa dasu. Bana so a d’auki lokaci. Ayi komai cikin gaggawa.”
**
A can b’angaren su Ummul kuwa hankulansu yakai matuk’a wajen tashi. Dik yanda ake tunanin za’a sami Umma anje ba’a sameta ba. Hisham kaw da shi ake aiwatar da komai tuni sun bada cigiyan Umma.
Yai k’uri yana duban Ummulkhairy dake ci gaba da kuka da gaske wann karon. Duk k’ok’arin ganin bata d’aura alhakin iftila’in dake faruwa cikin ahalinsu akanta ba saida zuciyarta ta raya mata hakan.
Da wanne zasuji? B’acewar mahaifiyarsu ko kuwa mahaifinsu dake kwance gadon asibiti wanda har wann lokacin bai san yanda yake ba. Ga likitoci sun tabbatar masu idan har treatment d’in da ake masa yaci gaba da failing jikinsa ya kasa amsa then he must have to undergo Cardiac surgery wanda zaici mak’udan kud’ad’e ga had’arin dake tareda hakan.
Hisham ya d’anyi gyaran murya cikin k’ok’arin kwantar mata da hankali. Amma kaman cewa yai ta k’ara. Ringing d’in wayarsa yaja hankalinsa.
Abokin aikinsa ne kuma amininsa Haidar me kira. Ba tareda ya bar wajen ba dan baisan barinta ita kad’ai farfajiyan asibitin suke yayinda Khulsum ke can wajensu mama sun hanata koda lek’a Abba ne.
Daga d’aya b’angaren Sautin kuka ne yai Sallama ma Haidar. Ya d’anyi still kafin yace “Wait..What’s that noise.. Where exactly are you..?”
Hisham ya dubeta sanda take k’ok’arin mak’ale kukan nata bayan taji alamun yana amsa waya “You seem to forget things easily nowadays Engr. Ka mance na tafi gida ne.”
Haidar ya d’an d’aga gira yana mai jinjina kai “I hope dai lafiya ka samu gidan. I mean lafiya ka samu Hajja..?”
Hisham yace “Yeah lafiya..” Ya k’arashe yana mai d’an jan kalamansa.
Haidar ya kuma tambaya “So who’s making that noise.?”
Ciki Zuciyar Hisham ke ayyana isa da jin kan Haidar. Wato bazai iya tanbayarsa wacece ke kuka next to him ba shine wai hayaniyar me yake ji. D’agowa yai Ya dubi Ummul wacce ke k’ok’arin tsagaita kukan nata. Ya d’an mik’e ya matsa gefe kad’an . Ya saki murmushi mai kyau yana mai d’an rage murya “Let’s call her Someone.. Someone Very special.. Ka gane I’ll call you back.”
D’an tab’e yai “Let’s talk business.” Yace cikin katse Hisham d’in.
Hisham ya d’an kuma satan kallanta sanda Haidar ke sanar dashi sunada ganawa ta musamman gobe a Kampani. Ya zama dole ya katse hutunsa.
Hisham ya girgiza kai kad’an “Wait what meeting Haidar.?”
“Tomorrow by 9:00am.. Design Architect Hisham.!” Abinda kawai Haidar yace kenan.
Hisham ya soma girgiza kai cikin rashin yarda “You know I can’t make it to the meeting Haidar.. I mean I’m not the only design architect in your team...” Bai tsaya d’aukan excuse d’in Hisham ba ya katse kiran.
Furzar da huci Hisham yai yana shafan fuskarsa da tafukan hannayensa. Jiki a matuk’ar sanyaye ya dawo yanda ya baro Ummul.
Ta ya zai barta ya tafi a lokacinda take tsananin buk’atarsa. He needs to stay.. But what about aikinshi.. Baiso wani yai taking place d’insa. Sun jima suna aiki tuk’uru kan wann project din wanda yake da tabbacin idan ya zama a successful one ba darajan Kampaninsu kawai zai d’aga ba. Zai taimaka wajen daidaita relationship d’in Amininsa da mahaifinsa wanda a kullum yake burin faruwan hakan. Bayan haka Haidar is counting on him. Abokinsa needs him now. Amma kuma Ummul fah. Shin zai iya barinta ya tafi.? Shin waye zai kyale ciki su biyun.
SameenaAleeyou📚
.jpg)