AUREN WATA UKU.!*
*13*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
Akan idon su Mama Hisham yai ma Ummul sallama ya rakota har wajen Khulsum. Saidai bai sanar da ita batun tafiyarsa ba.
Mama da Azeema ko harma da Badi’a ko k’ifta idanu basuyi. Musamman da sukaga zankad’ed’en Saurayin dake tare da Ummul. Mama tace “Toooh shi kuma wann d’in wai waye.?”
Badi’a tace “Wa ya sani masu ne Mama. Amma kaman saurayin Ummul..”
Mama ta bige bakinta “A gidan uwar waye ya zama saurayin Ummul. Wann yafi k’arfin Ummul inaga dai yayi zaton mabaraciya ce ya taimaka mata musamman da yaga tana cikin damuwa.”
Badi’a ta harari Mama yayinda Azeema ke hararar Khulsum tana cika. Lokaci guda ta katse Mama da fad’in “Saurayinta ne mana shine yayi belin wancan k’aramar ‘yariskar a police station bayan ta mareni.. Wllhi bazata saku ba. Ai na biya kud’in kwananta a cell amma bata kwana ba.. Toh wllhi komawa zanyi ayi duk rikicin da za’ayi. Ni da kaina na lale kud’ad’e na bawa Habibu ya biya ‘yansandan cewa su rufeta ta kwana. Wllhi komawa zanyi ko su biyani kudina ko su sanar dani dalilin bud’eta. Ai ko Kotu akaje akwai kud’in mari. Idan har ba biyana akayi ba wllhi rikicin nan bai k’are ba ehe. Ta k’arashe tana mik’ewa fuuu.
Mama tai k’ok’arin dakatar da ita da fad’in “Ke ke.. Ke ina zaki Azeema..?”
Ko juyowa batai ba Azeema balle ta amsa ta. Saima dialing layin Habib da tai tana k’arawa a kunne.
Mama ta dubi Bad’ia bayan Azeema ta shige. Ta janyota suka keb’e “Yauwa Kinga d’aga waya ki kira Tasi’u yazo ayi maganar sayar da shagon Malam da d’an sauran abinda Ke ciki. Kinga naji d’azu likitocin nan suna bayanin aikin da za’ayi ma Malam mak’udan kud’ad’e zai lak’ume wanda ko gaba d’aya Kantin da kayan dake ciki aka sayar ba isa zasuyi ba. Kinga kafin Wann shago da abinda Ke ciki tsautsayin jinyar Malam ya hau kansu gwara mu dafe su tunda wuri dan bazai yuwu mu zuba d’an abinda zamu samu ma jinyar Malam ba wanda su kansu likitocin k’irdado suke amma ga dukkan alamu ciwon Malam ba na tashi bane.
Bad’ia ta jinjina kai “Kuma ma Mama ai wanda suka fi cancanta su nemo kud’in jinyar Abba wanda sukai masa sanadin ciwon ne. Ina nufin wancan annobar da uwarta.” Tai nuni da yandasu Ummul Ke zaune.
Mama ta jinjina kai “Alhamdulillahi ina jin dad’in yanda kike fahimta. Maza kirawo Tasi’un.”
Tuni Badi’a ta d’aga wa ta shiga dialing layin Tasi’u mijinta.
Khulsum ta dubi ‘yaruwarta Ummulkhairi cikeda tausayawa “Adda yau d’in fah duka baki saka komai cikinki ba. Dan Allah kiyi hak’uri ki tashi haka nan mu tafi gida yamma ta riga tayi.”
Ummul naci gaba da hawaye ta girgiza mata kai “A’a Khulsum bazan iya tafiya gida ba. Watak’ila Umma zata zo nan wajen Abba..!” Tai maganar cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka.
Muryar Mama suka sinkayo akansu “Au har yanzu Uwar taku bata bayyana ba. Ta tabbata dai Angulu ta koma gidanta na tsamiya.”
Suka d’ago suna duban Mama da Badi’a tsaye kansu sai aika masu kallon wulak’anci suke.
Ummul ta girgiza kai “Mama Umma b’acewa tai bamu san yanda take ba.”
Sai Mama ta shiga tafe hannaye tana salallami “Na shiga uku ni Tani. Ta nan Suwaiba ta b’ullo..? Ta rasa abinda da zatai sai ta guji Malam sabida jinya ya kamasa ya zama kaya. Watau Suwaiba bazata iya jinyar Malam ba dai shine ta guje ta k’yaleni da wahalar jinya.. Yanzu da zataji labarin Malam ya cika dik yanda take zata fito tazo amsa sunar matarsa dan ta amshi rabonta na gado.”
Sai sann Khulsum ta finciki hannunta daga rik’on da Ummul ke mata cikin k’ok’arin dakatar da ita. Sai huci take.
Badi’a ce ta janyo hannun Mama hango mijinta Tasi’u da tayi sai buga sauri yake ya nufosu “Muje Mama kar ma kiyi hayaniya dasu balle a ba ma masu gadi hujjar koranmu. Ganin Abba ne sai a k’iyama idan sunada rabon had’uwa a k’iyamar.
Khulsum ta kuma fincika zatabi bayansu Ummul ta kuma dakatar da ita.
Cikin kuka Khulsum ke furta “Haba Adda Ummul. Haba ke kuwa.. Wai dan Allah meyasa kike dakatar dani.? Mutanen nan fah yaren da kawai suke fahimta kenan.”
Ummul ta jinjina kai tana kuma share hawayenta “Abinda suke so kenan Khulsum kiyita biyesu kuna tashin hankali. Ki tuna Abba dake kwance cikin asibitin nan. Ki tuna halinda yake ciki. Sann ki tuna Umma da halinda take ciki. Dan Allah ki daina biyewa Mama da yaranta. Allah ya fisu Khulsum. Mu fawwala masa komai da sannu zaiyi ikonsa akan kowa. Da sannu zai ba ma Abba lafiya ya tashi kafad’unsa kuma suna kallo. Muci gaba da yi masu add’uan shiriya har kullum domin su d’in ahalinmu ne komin lalacewarsu. Muje Khulsum, mu tafi gida mu kai kokenmu ga Rabbil izza wanda shike yaye dukkannin damuwa ya kuma kawo sauk’i da maslaha.” Tana ida fad’in haka taji natsuwa ya sauk’a cikin zuciyarta. Jiki a sanyaye suka fice daga asibitin.
**
Tasi’u yau harda risinawa yake gaida Tani. A mutunce yau d’in ya fito masu dan batu ake na kud’i.
Mama kaw sai hura hanci take dan ba Wai ta masa afuwan musguna ma ‘yarta Badia yake bane. Yanzun ma dan Badi’an ta nace ne sai an sako Tasi’un cikin hidiman, ta tabbata amfani yayi da son da Badi’a Ke masa ya saye zuciyarta da kalamai har ta aminta dashi. Dan dai ita kam har yanzu bawai ta yarda da tubansa bane. Tasan tuban D’anmuzuru ne. So yake a bawa Badi’a kasonta su lak’ume tare da zaran kudi sun k’are yaci gaba da mata iya shege.
Ta dubi mai sayen shagon da Tasi’u yazo dashi dan tinda Badi’a ta sanar dashi cikin waya ya taho da mai cinikinsa dan dama tuni ya tanadi mai saye tinda aka soma batun.
Mama sai cika take tana batsewa tana ciniki da mai sayen shago. Tasi’u yana daga tsakiya a matsiyinsa na dillali sai gyaran waje yake. Mama ta narka masa harara ganin zak’ewarsa.
“Amma dai Tasi’u ka tab’a dillanci ko..?” Cewar Mama tana dubansa a dak’ile.
Tasi’u ya Washe baki “Yo Mama banda abinki meye ba’a tab’awa ai duk abinda aka samu bugawa ake baka san ta yanda wutan zai kawo ba.” Sai faman Washe baki.
Ita kaw Hajiya Badi’a sai karkad’a k’afafu take tana Jin kanta. Daga yanzu ta samu makamin rik’e Tasi a hannunta. Tinda zata samu kud’i abinda yafi naira dubu d’ari aiko sai yanda tai da Tasi dole ta zama itace mijin itace mai basa doka da order. Tin yanzu ma biyayya yake mata balle ta dafe kud’ad’enta.
Aka tsaida cinikin Kantin Abba. Mai saye yace gobe suzo da takardu a saka hannu.. Nan fah Mama ta soma zare idanu dan bata San yanda ya aje ba. Tasi’u yace wann ai ba abun tada hankali bane washe gari zaije yai sabbin takardu a gama komai. Yanda yake ladabi wa Mama da Badi’a kai ka ranste yaron gidansu ne
**
A can station Habibu mijin Azeema sun keb’e da sergeant d’in da suka tafi sukai arresting Khulsum dan dama budurwarsa ce, ta cika tayi fam sai hura hanci take “Ni fah ba matsala ta bace dan an mari matarka. Yo a kasheta ma mana ai banida asara. Ni wllhi ba don ka min alk’awarin aure ba wllhi kaji na ranste da bazanje nai arresting kowa ba. Kuma kafi kowa sanin sabida kai nai. Toh ya Oga na zai yanke hukunci tazo nan tana kawo mana hauka. Ce mata akayi nan tasha ne. Ko ka d’auki matarka ka tafi ko a banza na jefata cikin cell a lakad’a mata duka dan bazan bari ta mun sanadin aikina ba. We are talking about my superiors here. Ita har ta isa tazo nan tana mana zage zage da hauka. Tasan me ake kira hukuma ma kuwa. Na ranste maka Habib idan bakai controlling d’inta ba zata gane ita k’aramar mahaukaciya ce dan yanzu zata tabbata mahaukaciyar da Dawanau ma ya kasa mata.” Ta k’arashe tana jijjiga sai sakin huci take tana tsuma tana kad’a kulkin cikin hannunta.
Ya murmusa yana shafa hab’a lokaci guda yana lek’en bayansa kar Azeema ta k’araso wajen. Ya sassauta murya “Haba kurtuwata. Kema kinsan duk duniya babu macen da nake so sama dake.. Da kikaga ina biyeta amfani zata min. Yo banda abinki ni kaina sau nawa ina lakad’a mata d’anbanzan duka kuma duk akanki toh dan an mare Azeema har wani damuwa zanyi. Wllhi yanda kika san an mari wofi haka naji..” Ya kuma shafa fuskarsa yana lek’en bayansa irin yanda marassa gaskiya keyi kafin ya matso da fuskar nasa saitin fuskan ‘yarsandar “Kinga ita Azeema Ubanta na asibiti rai hannun Allah. Ta tabbatar mun mutuwa zai. Kuma da zaran ya Mutu aka raba masu d’an abinda zasu samu zan amshe komai nata. Tana mallaka min zan koreta da kud’in gadon Uban nata zan aureki Kurtuwata.” Ya k’arashe yana wani washe baki yana wani kashe mata idanu “Toh d’an yi mun murmushi mana na gani sahibata.. Inye kaga Kurtuwa Amaryar Habibi..” Ya k’arashe kaman zai rungumota.
Yatsine fuska ta d’anyi had’ida turasa baya “Easy mana Alaji wajen aiki na muke.. Shikenan tinda haka kace.. Amma wllhi idan Kai ga gangancin kawo mun bariki wllhi babu abinda zai hanani cin uwarku daga Kai har matar taka kasan sharri na karanta a banza zan maida police station gidan hutun matarka.”
Saurin toshe mata baki yai yana “Wllhi bama ta sanki ba har yanzu. Bata san wace budurwar tawa ba.. Kwantar da hankalinki kafin ma ta sanki ta tsufa gidan marigayin mahaifinta. amma sai na tabbata na amshe d’an abinda uban nata zai bari mata..”
Ta kuma yatsina fuska kafin ta tura k’ofar ta fito tana karkad’a sandan dake hannunta sai faman d’age hanci sama take. Azeema ta bita da kallo dan haka kurum hankalinta bai kwanta da ‘yarsandar ba musamman da ta hango Habibu ya fito daga bayanta yana fad’in “Nifa Rankidade Sam bazan yarda ba wllhi sai an shiga kotu an k’watarwa matata hakkinta..!”
Azeema ta k’araso gareshi ta shige jikin mijinta tana fad’in wllhi a tafi kotu kawai.
Sai ya fara kokarin kwantar ma Azeema hankali da fad’in idan yana a matsayin mijinta sai an tafi Kotu.
Sergeant d’in kuwa banda watsa ma Azeema wani wulak’antaccen kallo bata komai.
Da kyar Habibu ya shawo kan Azeema ta amince suka bar police station d’in da sharad’in case din bai k’are nan ba. Sai aika ma ‘yarsandar mugun kallo take dan ta kula da wani kallan k’asa k’asa da Habibu ke binta dashi.
**
A can b’angaren su Umma kaw d’aki maiji da lafiya aka sauk’eta. Umma ta zauna saman gado tana lotsawa tana jin taushin latifa ga sanyin AC na bugata. Ai sai Umma ta yab’e baki tace “Kai kaji taushi kaman ina saman gajimare. Tirk’ashi. Lallai masu kud’i suna sha’aninsu.”
Asshe dake lab’e daga k’ofa tana karantar duk wani motsin Umma waya manne kunnenta wanda ko shakka babu da Mommy take wayan. Sauk’owa k’asa tai dan upstairs aka sauk’i Umma.
Ta zauna nan parlorn k’asa tv na aikinsa waya manne kunnenta “Aunty Kwaise bakida wata matsala fah. Ni na fad’a miki na kuma yarda da aikin wann Malamin dan kaman tafiya muke da solution d’in matsalar mu. Matar nan dai da muka bige”
Ta d’anyi Shiru alamun tana sauraro daga b’angaren Mommy. Sai taci gaba “A’a Haba Aunty Kwaise nasan fah abinda nake. Ai tuni nasa Yunusa yaro na ya binciko mun komai kanta. Duk wani abinda Ke wakana tsakanin ahalinta. Yazo gidan sauki tinda nan cikin Kano ne. Ai bazai yuwu mu d’ibo ko wace iri mu jajib’a ma Haidar ba koda kuwa Auren na wata UKU ne kawai. Yanzu zuwa gobe idan Allah ya kaimu zakiji duk bayanan da Yunusa zai kawo mun dalla dalla duk yanda akai. Idan ta kama a miki scanning information d’in ne a tura miki ta mail duk za’ayi Aunty Kwaise. Haba abu ne za’ayisa cikin wayewar kai. A yanda na fahimta bakin aljihu ne kawai zai bayani wann kuma nasan ba matsala bane.” Ta d’an dara tana kuma kod’a Mommy da mata kirari irin na matan Manya. A haka sukaci gaba da tattaunawar tasu.
Bayan sun ida waya Asshe ta mik’e ta lek’a Suwaiba. Nan ta tadda Umma tuni ta baje saman gado bacci yayi awon gaba da ita harda su minshari.
**
Hisham yai Shiru yana sauraron mahaifiyarsa. Sai kuma ya girgiza kai kad’an “Hajja ba yanda na iya ne. Tafiyar ce ta taso mun babu shiri.” Ya d’an matso kusanta had’ida kamo hannayenta cikin nasa “Na bar amanan Ummul hannunki Hajja. Dama tare na ganku nai maku karambani ko nace zuciyata tai karambani…” Sai ya d’anyi fasali “I will come back for her Hajja.. Zan dawo, dawowa na musamman domin Ummulkhair.. Please kici gaba da kula da al’amranta har na dawo. Bazan d’auki lokaci ba wann karan in sha Allah.. Kinji Hajjata.” Ya k’arashe cikeda rauni.
Dubansa ta d’anyi duka duka yaushe yazo har zai tafi. Ita kam ta fara gajiya da wann aikin nasa.
A hankali ta jinina Kai “Shikenan. Allah yaci gaba da tsareka yayi maka albarka. Bazan dakatar dakai ba koda ina son yin hakan. Ummul kuma ka barta cikin aminci da yardar Ubangiji. Fatana Allah yasa kar ka d’auki lokaci mai tsawo.”
Hisham ya murmusa cikeda jin dad’i yana jin zuciyarta at ease. Fitan sassafe zai wanda ba lallai ya samu ya kuma ganinta ba balle suyi sallama. Amma yayi alk’awarin da zaran ya isa zai kira Hajja ta had’asu a waya.
SameenaAleeyou📚
