*AUREN WATA UKU.!*
*21*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
Jikin Asshe Ya kuma yin lak’was dan gani take kaman Kwaise ta riga ta san komai. Cewa Ajalin D’anta zata kai mata matsayin makarin asirinsa.. Har wayar ta kusa tsinkewa kafin Asshe ta iya tattara daidai gwargwadon natsuwan da yazo mata a wann lokacin. Murya a raunane ta d’aga kiran “Aunty Kwaise..”
Daga d’aya b’angaren Mommy ta kaste ta “Asshe duk yanda za’ai Amaryar wata uku ta iso Abuja a gobe.. Asshe a yanda na hango tsananin k’iyayya a idon Haidar Ya kuma haifar min da tsoron rasa D’ana. I can’t afford to lose him Asshe. Haidar shi kad’ai ne D’ah na zanyi komai zan sadaukar da komai nawa dan na kub’utar dashi da ahalina daga sharrin shed’aniyar can. Asshe bana so a sami wani mishkila. Ki kula da matar wata uku da kyau tamkar k’wai a hannun yaro tinda kinsan amfanin ta wajenmu. Rayuwar d’ana tamkar yana had’e ne da nata rayuwar. Har sai lokacin da zata karya wann asiri da aka jefesa dashi. We need to make sure ta iso a gobe cikin k’udurar Ubangiji.”
“Amma.. Amma.. Aunty Kwaise..”
“Asshe Babu wani Amma.. I cant afford to lose my son completely… Just do as I say.. The house is set. Everything is ready. Isowarta kawai ake jira na rik’e Haidar a gida kaman yanda yake bisa yarjejeniyar mu dashi. Engr ma cikin satin nan zai tafiya, Business trip. Akan Auren Haidar na hana kaina bin mijina tafiyar da zai d’aukesa makonni kinga kuwa na shirya ma wann aure. Na shirya karya asirin da akai ma Haidar.” Mommy ta k’ark’are wayar nata tana kuma jaddada ma Asshe lallai lallai kar a samu wani matsala.
Asshe Tai sakare tana duban wayar. Zama Tai gijif cikin gado zuciyarta naci gaba da tsinkewa. Shikenan.. Ta faru ta k’are wai anyiwa mai dami d’aya sata yanzu mi zatayi..? Ba tada ikon canza komai a halin yanzu. A dole ta nad’e Ummulkhairy ta kaita ma Yayarta Kwaise. Yanzu ita meye abinyi. Anisa ce ta fad’o zuciyarta. A fili ta furta “Anisa.. Anisa zata taimaka min na aiwatar da komai ba tareda Haidar Ya cutu ba sann ba tareda ‘Yaruwata ta fahimci komai ba. Lallai zaman Anisa a can shine kawai rufin asirina. Toh amma idan Anisa taje ta tafka wani shashancin fah.? Kuma kenan zaki sanar da Anisa komai.?” Ta soma girgiza kai a hankali “A’a Anisa doesn’t need to know about everything. Kawai umarni zan dinga bata daga nan.” A hankali ta shiga jinjina kai kafin ta nufo k’asa.
Nan Asshe ta tadda Inna Dije ta titsiye Umma sai ta fito mata da Ummulkhairy ta tafi da ita. Umma sai kuka take tana rok’on Mama Dije ta rufa mata asiri kar ta tona mata Auren Ummul ya mutu tun a daren aurenta kafin tafiyarta. Cikin gunjin kuka Umma taci gaba “Dije ki dubi girman Allah ki rufa mun asiri.. Wanda kika tona min ma Ya isheni wllhi.. Yanzu idan auren Ummul Ya Mutu Tun a daren yau da wani idanun zan kalli mutanen unguwarmu da dangi baki d’aya… Dije idan kina ma Allah kar ki d’auki Ummul.. Kar ki tafi da Ummul..”
Kaman daga sama muryar Asshe ya katse su “Babu yanda za’a tafi da Ummul domin kuwa a halin yanzu mutum d’aya keda iko da Ummul shine mijinta..!”
Gaba d’aya suka juyo suna dubanta, daga Umman Har Mama Dije.
Asshe taci gaba da sauk’owa daga bene cikeda k’asaita. Ta k’araso gaban Inna Dije dake tsaye gaban Umma wacce ke duk’e kaman mabaraciya tana Koke Koke.
Dije ta zuba ma Asshe idanu. Su duka biyun suna duban juna. kowacce tana sak’awa cikin zuciyarta.
Murmusawa Dije Tai tana kuma duban Asshe da kyau “Da gaske..? Bayan duk abubuwan da kika ji… Kin amince a kaima D’anki ajalinsa..? Oh! D’an ‘yaruwarki..? Haka ne..?!”
Asshe ta murmusa tana ma Dije irin duban da biri yake ma Ayaba “Ko mai zai faru a halin yanzu.. Ummul tana k’ark’ashin ikon mu ne.. Sadaki D’anmu Ya biya Wanda Ya tabbatar da wanzuwan igiyoyi Har guda uku da suka mallaka masa cikakken dama da iko akan Ummul. Duk wani abinda zai biyo baya, hukunci zai zamana yana wajenmu.!”
Sosai Mama Dije ta tsareta da idanu tana ji akwai wata a k’asa. Dan ta tabbata wann aure ba auren Allah da Annabi bane.. Duk yanda akai akwai wata shiryayya. Idan auren tsakani da Allah ne bayan duk abinda ta sanar ma Asshe a gaban Suwaiba wacce take mahaifiya ga Ummul ba yanda za’ai Asshe ta amince akaima D’ansu mace irin Ummul.
Umma harda sujudusshukur tayi dan farin ciki. Ta shiga d’aga hannaye sama tana mik’a ma Allah godiya “Alhamdulillah..! Alhamdulillah Allah abin godiya.. Allah gatan bawansa.. Kai amma dai annamimi baiji dadi ba.. Zakaran da Allah ya nufa da cara ko fah ana Muzuru ko ana shaho sai yayi.. Kuma wllhi idan rana ta fito tafin hannunki bata isa ta rufesa ba Dije..! Tani ma ta buga Dani ta barni balle ke..!” Ta k’arashe tana mik’ewa tsaye harda rangad’a gud’a.
“Bada garaje ba Suwaiba..!” Muryar Asshe ya dakatar da ita.
Umma ta waro idanu waje dafe da k’irji tana duban Asshe. Sai kuma ta soma girgiza Kai “A’a dan Allah.. Ki rufa mun asiri Hajja Asshe.. Ki dubi girman Allah kar ki bari mak’iya suyi dariya.. Wllhi duk abinda kikaji daga bakin Dije ba komai bane face sharrin mak’iya..”
Asshe ta dafa Umma tana murmushi “Kin yarda cewa aure rai ne dashi..?!”
Umma ta jinjina kai tana duban Asshe.
Asshe taci gaba “Bazai Mutu ba sai kwanakin Sa ya k’are.. Haka ne..?”
Nan ma a sanyaye Umma ta jinina Kai.
Asshe ta juya ta basu baya daga Umma har mama Dije lokaci guda tana taka parlorn nata a hankali take ci gaba da fad’in “Bari muce auren Ummul zai rayu ne na wani d’an lokaci..!”
Dummm! Haka k’irjin Umma ya buga. Jiri ne taji na neman aikata k’asa. Ta dafe garu tana furta “Ban ban.. Ban fahimceki ba Hajja Asshe.. Mai Kike nufi da cewa auren Ummul zai rayu ne na wani d’an lokaci..?”
Assshe ta juyo tana dubansu “Ina nufin zai rayu ne na tsawon watanni uku kacal.!”
Dije ta gyara tsayuwarta sosai tana duban Asshe makirin murmushi kwance saman fuskarta. Cikin zuciyarta take furtawa ‘Eh Lallai.. Da alama yanzu ne wasan zai d’au zafi.. Bari dai mu gani..!’
Muryar Umma ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi.
“Ban.. Ban gane tsawon watanni uku kacal ba.. Me kike nufi Hajiya Asshe..? Me kike nufi da auren Ummul zai rayu ne na tsawon watanni uku kacal..? Ki min magana dan Allah.. Ki sanar Dani mai kike nufi..?!”
“AUREN WATA UKU..! Ina nufin AUREN WATA UKU kawai mukayi ma D’anmu da ‘yarki.. Bayan wata uku.. ‘Yarki zata dawo gareki.. Sai ki shirya mata wajen zama bayan wata uku..!”
Duniyar Umma ya shiga juyawa sama na koma mata k’asa… Ta girgiza kai tana jin hankalinta na neman gushewa da gaske. Cikin rawar murya Umma ke furta “Amma.. Amma meyasa haka Hajiya Asshe.. Shin wani irin aure kukai ma D’anku da ‘Yata… Meyasa na wata uku kawai..?”
“D’an ‘Yar uwata yana aiki ne k’ark’ashin Kampanin Mahaifinsa. Mahaifinsa zai basa wani k’wangila ne na tsawon watanni uku kawai idan yayi aure.. Bayan wata uku zai gama wann kwangilar.. Daga nan kuma bamuda buk’atar ‘yarki dan kwangilar ta k’are.. Kin fahimta..?” Ta k’arashe tana duban Umma sosai.
Umma na girgiza kai cikeda rashin yarda take duban Asshe “Amm.. Amma.. Amma.. Bamu yi haka dake ba.. Wann zalunci ne.. ‘Yata ta jima, ta d’auki lokaci batayi aure ba.. meyasa kuka zab’i cutar mun da ‘ya.. Ummul.. Ta wahala a rayuwa, ta fuskanci k’alubale na gujewan manema.. Ta fuskanci k’alubale da dama.. Bata cancanci irin wann auren ba.. ‘Yata ta cancanci aure na gaske.. Aure mai d’orewa ba mai rabewa ba.. Shin Auren Kwangila kukaima D’anku da ‘yata..? Hajiya Asshe kin cuceni.!”
“Ban cuceki ba hasalima taimakon ki nayi.. Idan baki mance ba sadakin ‘yarki shine kud’in jinyar mijinki.!”
“Wani irin taimako ne wann..? Wane irin taimako ne haka.. Wann zalunci ne ba taimako ba..”
A zuciye Asshe ta katseta “Kar ki sake cewa na cuceki.. Ke kika cuci kanki.. Magana akan cuta.. Shin tsakanin ni da Ke waye ya cuci wani..? Ni da naima D’ana auren cikan buri da ‘yarki ko kuma keda kika cuceni kika sakani a tsaka mai wuya, nai jagoranci wajen aura ma d’an ‘Yaruwata wann ‘yar taki mai lullub’e da Illan asiri da farar k’afa.. shin ki fad’a mun… Tsakanin mu biyun waye ya cuci wani..? Rayuwan d’ana yana tsaka mai wuya a nan.. Idan Haidar Ya Mutu ‘yarki ce Sila.. Shin banyi adalci ba da nace zata zauna na tsawon watanni uku..?!”
Umma taci gaba da hawaye tana duk’e wajen.
Asshe taci gaba “Ki gode ma Allah.. ‘Yarki bazata fuskanci tozarci na mutuwan aure a daren aurenta ba.. Ki gode ma Allah bayan duk abubuwan da kikayi ‘yarki zata zauna k’ark’ashin Inuwan aure na tsawon watanni uku.. Ki gode ma Allah bazaki fuskanci dariya da gori harma da wulak’anci idan har auren ‘yarki Ya Mutu a daren yau ba.. Domin kuwa duk wani Sirrinki da naji sai na bankad’e.. Kuma Kinsan me..?” Ta k’arashe tana mai duk’awa gaban Umma dake duk’e tana hawaye “Zaki amar da duk wasu kud’ad’en da na kashe wajen nema ma D’an ‘Yaruwata auren ‘yarki. Kaf ko kobo bazan bari yai ciwon kai ba.. Kin shirya biya.?” Ta k’arashe tana tsare Umma sosai da ido.
Inna Dije ta k’arada “Daga nan kuma sai kiyi bankwana da Mijinki Suwaiba bayan kin rasa yaranki. Dan bayan abinda Ya faru ki sani zan d’auke D’anuwana na masa jinya bazan barshi tsakanin mata guda biyu da Babu Allah cikin zukatansu ba..!”
Umma ta d’ago idanunta masu zuban ruwa tana duban Dije da Asshe “Dan Allah.. Kar ku jefa rayuwata cikin garari.. Kuji tsoron Allah.. Kuji tausayin rai.. Ku tuna kuma iyaye ne.. Kuma burin ko wace uwa ta kai ‘yarta d’akin miji.”
“Kar kiyi mana maganan zama iyaye a nan.. Domin kaw baki tab’a zama uwa ga ‘ya’yanki ba Suwaiba.. Kuma yau zaki fara girban duk abinda kika shuka..!” Dije ta k’arashe tana sakin huci.
Asshe ta gyara tsayuwarta “A tsakanin watanni ukun ma inada sharud’a.. Dan Kinsan a daren nan zan iya kashe auren ‘yarki Suwaiba haka ne..?!” Ta k’arashe tana duban Umma kannare da idanu.
Umma ta share hawayenta tana kuma jinjina kai a hankali kaman marainiyar mage.
Asshe ta jinjina kai “Shradina shine bazakiyi magana da Ummul ba har na tsawon watanni Uku. Ina nufin iyakacin wa’adin zaman da zatai da D’anmu. Keda had’uwa da ita kuma sai kwangilar D’ana Ya k’are randa Ya cika aikinsa ya warware auren.. Ni kuma zan d’auko ‘yarki da kaina na kawo miki ita cikin mutunci. Kin amince..?”
Umma ta d’ago a raunane tana duban Asshe jin da gaske dai Auren wutin gadi Ummul tayi ba kaman yanda taci mata buri ba. Sann ga wasu dokoki da sharud’a Wanda aka gindaya na datse alak’arta da ‘yarta “Dan Allah kar kiyi haka.. Kiyi hakuri… Kar ki rabani da Ummul.. Wllhi Ina son ‘Yata..”
“Na zata kinfi so tayi aure tayi nesa dake… Ko ba haka bane..?” Asshe ta katse ta.
Umma ta kuma rintse idanunta tana hawaye.
Muryar Inna Dije ya katseta “Burinki Ya cika Suwaiba.. Mata mazan ‘yarki tayi aure.. Amma aure mai gibi.. Wanda bada jimawa ba angulu zata koma gidanta na tsamiya..” Ta murmusa kafin taci gaba “Inama zanga Tani na bata wann babban Albishir..!”
Umma ta shiga d’ago hannaye daga duk’e tana rok’on Dije “Dan girman Allah ki rufa mun asiri Dije.. Kar abinda Ya faru yau ya fita ko ina.. Dan Allah Ku rufa mun asiri.. Wllhi na amince zanyi duk abinda kukace.. Amma kafin nan dan Allah ku barni nai Sallama da Ummul.. Ku barni nai Sallama da ‘Yata..!”
Dije da Asshe suka dubi juna kafin Asshe ta jinina kai “Kinada minti talatin kacal kiyi Sallama da ‘yarki.. Sann ki aje wann a ranki.. Kaman dai yau nan da watanni uku zaki sake had’uwa da ‘yarki.. Watak’ila had’uwa ta Har abada..”
Umma ta shiga jinina kai tana godiya. Jiki Babu laka ta mik’e ta nufi sashen da aka aje Ummulkhairy.
Umma tana shigewa Dije ta juyo tana duban Asshe duban irinta gogaggu. Dukansu biyu suka tsare juna da idanu. Kai da gani zaka fahimci wann ta naima wann kallon biri ne waccan tanai ma d’aya kallon ayaba. Ko wacce irin duban da take ma juna kenan.
Dije ta murmusa tace “Kin d’auki kasada mai girma ma d’anki dukda na sanar dake ga abinda Ya samu nawa d’an.. Meyasa..? Meye dalinlinki..?”
Asshe ta murmusa irinta gogaggun wayayyu “Aw.! Baki yarda da hujjata bace..? Cewar auren kwangila na tsawon watanni uku mukai da ‘yarku.?”
Murmushi Inna Dije Tai “Kar kiyi zaton wayewarki zaisa ki shashashantar Dani kamar yanda kika shahsantar da Suwaiba.. Ni ba Suwaiba bace.. K’ar nake kallonki.. Dan haka Ki sanar dani meye asalin dalilinki.. Dan babu wanda zaiji abinda na fad’a Ya kuma amince D’ansa ko wani nasa yai tarayya da Ummul.. Bayan jifa na asiri dake jikinta ita d’in barazana ce ga rayuwarsa.. Anya akwai wacce zata amince wani nata Ya zauna da Ummul matsayin matar aure..? Ko da yake ba d’anki da kika haifa bane.. D’an ‘Yaruwarki ne.. Tabbas akwai banbanci.!” Ta k’arashe shu’umin murmushi saman fuskarta.
Asshe ta murmusa “Jifa na asiri..? Toh kodai kece kikai jifan.. Dan idan Har Zan amince D’an ‘Yaruwata ya auri ‘yarku mai tawaya na asiri.. Bana jin akwai wacce zata tona ma ‘yar D’an uwanta asiri irin haka.. Kaman dai yanda kikai ma Ummul.. Da ni dake dukanmu ‘Yanuwa ne ga iyayen Ummul da kuma Haidar.. Haka ne..?”
Dije Tai shiru tana duban Asshe. Ta kula su duka biyun Sun k’ware a iya buga wasan. Tabbas kuskure kad’an zatai gaban matar nan ta sha k’asa.. Koda wasa bazata bari hakan ta kasance ba. Gwara ta gyara d’amararta da kyau.
Murmusawa Dije tai tace “Af! K’warai haka fah.. Magana ake na gwaggwani da Innoni.. Wanda yafi nuna kula ga nasa.. Tabbas shi zai d’auki kambin.. Mai zai faru idan na tafi na samu ‘yaruwarki na sanar da ita ga abinda kika shirya ma D’anta… A bayan idonta..?” Ta k’arashe tana tsare Asshe da idanu ga muguwar murmushi saman fuskarta.
Asshe ta d’an d’auki lokaci tana dubanta. Dukda bugu da zuciyarta keyi bai hanata tattaro natsuwarta ba dan bata so ta bama Dije k’ofan da zata d’ago rauninta. ta murmusa tace “Wai ance da D’an gari akanki gari.. Kin tab’a jin an shiga gari yak’i Anci yak’in ba tareda taimakon D’an gari ba..? Ina nufin kinada masaniyar wace irin yarda ce tsakanin ‘yanuwa biyu.?” Ta k’arashe tana tsare Dijen da idanu itama..”
Su dukansu biyu suna duban juna. Asshe ta murmusa ganin Dije bata bata amsa ba. Ta k’araso ta dafa Dije kad’an “A shawarce “Kowa ya tsaya a masarautarsa , Ina nufin kiyi yanda kikaso da Suwaiba harma da D’anuwanki.. Kar ki shiga tsakanina da ‘Yaruwata.. Dan nasan bazaki so yin wasa da wuta ba..”Ta k’arashe murmushi saman fuskarta.
Dije ta murmusa “D’iyar mak’eri bata shakkan wuta.. Hasalima ta saba wasa da wuta.. Kiyi tunani kan abinda na sanar dake. Domin kuwa kaman yanda kika amshi bak’oncina cikin gidanki ba tareda kin gayyaceni ba. Toh ina mai tabbatar Miki zan kai ziyara ma ‘yaruwarki ta birnin tarayya.. Ina nufin mahaifiyar surkinmu.” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta.
Shiru Asshe tai zuciyarta na kuma bugawa. Lallai wann matar babbar barazana ce a gareta. Dan tabbas idan ta tafi ta samu Kwaise ta sanar da ita abinda ke faruwa toh fah tata ta k’are. Sosai tai nisa cikin duniyar tunanin yanda zata b’ullo ma wann Dijen wacce ta zamto babban threat a gareta.
Inna Dije ta gyara zaman mayafinta “Kiyi tunani da kyau.. Ni zan tafi.. Dare yana yi.. Amma kafin na tafi ki zuba mun lambobinki a nan.. Sabuwar k’awata..” Ta k’arashe tana duban Asshe da ta zama deep in thoughts.
Asshe ta dubeta irin duban baki kai ki shiga jerin matsayin kawayena ba.. Sai kuma ta murmusa abinka da gogaggiya “K’awa..? Oh haka ne… Ta bayan fage..!” Ta k’arashe maganar tana Shafa kwantattun gwalgwalan dake zube wuyanta zuwa kunnuwanta da hannayenta. Dije sai dubanta take tana jinina barikin matar nan. Watau bazata fad’a mata matsayinta da baki ba saidai yanayin shigarta da suturan dake jikinta Ya tantance hakan.
Lokaci guda ta d’auki wayarta ta mik’a ma Inna Dije “Zuba min lambobinki a nan..”
Inna Dije ta murmusa kafin ta dubi wayar kaman zata amsa sai kuma ta tabe baki tace “Baki tunanin ban Saba da rik’e irin wayoyin nan naku ba.. K’awa..!” Ta k’arashe tana juya mata gajiyayyar wayar dake rik’e hannunta harda d’aurin robber ring jiki.
Asshe ta murmusa tace “Gashi Ba hand sanitiser kusa, bara na sanar dake da baki sai ki juye a naki wayar.. Ya Miki..”
Dije ta jinjina kai “Kar ki damu.. matuk’a bazaki lank’wasa harshe ba.. Anyi alimantari an samu na zama cikin Al’umma.. Kar ki mance lambobin gaske zaki bada dan idan ba haka ba. Zan riga ki isa wajen ‘yaruwarki.” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta.
A haka dai sukai exchanging phone numbers kowa tana watsa ma juna bak’ar magana da sako a dunk’ule.
Inna Dije zata fice Asshe ta dakatar da ita “Ina Miki ta’aziyar D’anki.. Ina kuma fata hakan bazai faru da nawa D’an ba..”
Inna Dije ta murmusa “Fata mai kyau.. Allah yasa.. Idan kuma fatanki bai amsu ba.. Sai ki tanadi farin k’yalle nan da watanni uku.. Watak’ila akwai cin gumba gidan k’awata..”
Suka sakar ma juna murmushi Wanda yafi kama da yake. Kafin daga bisani suka kuma yin Sallama. Asshe ta juya idanu cikeda k’osawa Har Inna Dije ta fice.
Zama Tai cikin kujera tana mai furtawa a fili “Oh ni Asshe wasu irin mutane na jajib’o mana ne wai.. Ita Suwaiba nayi zaton abin nata a shashanci da wauta kawai ya tsaya ashe Shegiya wawiyar gangance ‘yar boka. Ga Tani daga can gefe mai cinye gadon miji yana raye.. Ita kuma wann Dijen da alama itace tafi kowa hatsabibanci cikin ahalin domin kuwa idan har banyi da gaske ba zata zame min babban barazana..!”
Ta mik’e cikin sand’a ta nufi d’akin da Umma ke ban kwana da Ummul d’inta. Jikin k’ofa ta mak’ale tana sauraron tattaunawar ‘ya da Uwan.
Umma tai k’ok’arin saita kanta tana duban Ummul dake dubanta cikin rashin yarda hawaye kwance saman k’uncinta. Sosai Umma ta sha mur kaman ba ita ba. Cikin zuciyarta kaw k’ok’arin danne raunin nata kawai take dan k’arfafa gwiwar ‘yar tata. Cikin kakkausan murya ta ambato sunan Ummulkhairy snn taci gaba “Ina so ki mun alk’awari guda d’aya Ummulkhairy.. Watak’ila shi kad’ai ne alfarmar da zan nema daga wajenki.!”
Ummul ta kuma duban mahaifiyar tata jiki a matuk’ar sanyaye. Murya na tsananin rawa take furta “Umma kin wuce ki nemi alfarma wajena.. Kar ki mance ke mahaifiyata ce.. Ko me kike so nayi matuk’a bai sab’a wa Ubangijina ba zanyi… Dan cikan burinki… Zan zan Miki Umma..!” Ta k’arashe cikin sautin kuka.
Dukda kuka da yazo ma Umma amma sai tayi k’ok’arin danne kukanta “Ummulkhairy kar ki neme ni… Kar ki tako yanda nake Har na tsawon watanni uku.. Ko a waya kar ki kirani.. Ki min alk’awarin.!”
Da tsananin mamaki Ummul ke duban mahaifiyarta. Ta shiga girgiza kai cikin rashin yarda “Umma.. Mai hakan yake nufi..? Umma zaki yanke duk wata alak’a dani ne..?”
Umma ta jinjina mata kai alamun eh “K’warai Ummul.. Kuma kema kimin alk’awarin yanke alak’arki damu.. Ina nufin da d’aukacin ahalinki na tsawon watanni uku.. Kimin wann alk’awarin..!” Ta k’arashe tana duban Ummul d’in.
Girgiza kai Ummul keyi tana duban mahaifiyarta “Umma.. Kin kaw ji abinda kike fad’i mun..? Umma yanke alak’a da iyayena harda mahaifina dake kwance yana jinya..? Umma Anya..”
Katseta Umma tai “Na tsawon watanni uku kacal.. Dan Allah ki mun wann Ummul..!” Ta k’arashe tana kamo hannayen Ummul d’in alamun rok’o hawayen da taketa k’ok’arin dannewa na kwaranyo mata.
A hankali Ummul ta zame hannayenta tana girgiza kai “A’a Umma.. Baki tunanin Kin tafi da nisa Umma.. Bazan iya ba.. Bazan iya abinda kike nema daga wajena ba.. Bazan iya yanke alak’a da ahalina ba.. Menene dalilinki Umma..?”
Umma taci gaba da matsan k’walla. Sai kuma ta mik’e tana huci “Wann Shine kad’ai abinda na nema daga wajenki Ummul.. Kar ki nemeni, kar ki tako yanda nake Har na tsawon watanni uku.. Idan kuma kika nemi ni ko kika tako yanda nake kafin wata uku ban yafe miki ba.!” Tana ida fad’in haka tasa kai ta fice kuka na kuma b’alle mata.
Ummul Tai zaune tamkar wacce aka dasa. Ta nemi kuka ta rasa. Sai ta shiga tambayan kanta Wacece ita..? Meyasa rayuwa yazo mata a haka..? Shin ita kad’ai ce take fuskantar k’alubale irin nata..? Shin Anya Umma itace ta haifeta..? Anya uwa takan haifi ‘ya tayi watsi da ita irin haka.. Tin daga tasowarta Umma bata tab’a damuwa da al’amarin rayuwarta ba. Ta mata aure a wulak’ance. Daga k’arshe ta datse alak’a da ita ba tareda dalili ko hujja ba.. Anya ana samun irin wann uwar.. Anya ko a labarai ta tab’a cin karo da uwa irin Umma..? Ta shiga girgiza kai tana duban d’akin da aka ajeta. Lokaci guda ta mik’e tana takawa a hankali. Daidai gaban madubi taja ta tsaya tana duban kanta cikin madubin.
Take zuciyarta Ya shiga karanto mata wacece ita. Tin daga lokacin k’uruciyarta har kawo girmanta. Duban kanta take cikin mirror hawaye na zurarowa daga cikin idanunta d’aya na bin d’aya.
A hankali ta silale a wajen cikin kuka maras sauti tana jin tamkar bata a duniyar.
**
Umma ta kusan ficewa kenan taji an damk’o hannunta an janyota wani d’akin.
Asshe ta gani tsaye tana sakar mata murmushi “Kinyi abinda ya kamata.”
Jinjina kai Umma tai tana duban Asshe “Ki sani da ace nasan irin auren da zakuyi ma D’anku da Ummul kenan tun farko da ban amince ba. Amma saidai idona Sun rufe Allah Ya barni da iyawata a lokacin da na Shafa’a da neman zab’i daga gareshi. Watak’ila wann shine hukunci na.” Ta share hawayen da suka zubo mata kafin taci gaba “Nayi abinda kuke so.. Na yanke alak’a na wucin gadi da Ummul kaman yanda kukai auren wucin gadi da ita.. Alak’ata da ‘yata zai dawo ne bayan sharud’anku Sun cika.. Wann lokacin kuma.. Nayi alk’awarin sabanta alak’ata da ‘Yata.. Nayi alk’awarin bata kulan da ban bata ba tsawon rayuwarta.. Nayi alk’awarin nuna mata soyayya irin Wanda na hana mata a matsayin uwa tsawon rayuwarta… Na..” Kuka ya hanata ci gaba da magana.
Da k’yar ta iya saita kanta kafin taci gaba “Iyakacin abinda zan rok’a daga wajenki shine ki kula mun da Ummul .. Dan Allah kar kici amanata Asshe.. Ke kad’ai na sani cikin ahalin da Ummul zata shiga na watanni uku… Dan Allah Ki kular mun da ita.. Kuma ki rike amanata kar ki tab’a tona sirri na ma Ummul… Kar ki sanar da ita AUREN WATA UKU tayi kuma inada masaniya. Dan Allah kimin wann..!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka hannayenta had’e waje guda alamun rok’o.
Asshe tab’e da baki take duban Umma babu ko alamun tausayi. Cikin zuciyarta take ayyana dan ma baki san dalilin auren ‘yar taki shine ta karya sihiri ba. Sann auren yana nufin ajalinta. Ki gode ma Allah itama ta zama barazana ga rayuwar Haidar Wanda hakan zaisa ki sake had’uwa da ‘yarki bayan wata uku. Dan bazan tab’a bari Haidar ya kusanci wann ‘yar taki ba. Ta murmusa kad’an “Kin kware wajen iya wasan kwaiwayo Suwaiba.. Ban Miki alk’awarin komai ba… Dan bayan amanata da kikaci bansan mai zai faru a tsakanin wata uku ba..!”
Cikin zuban hawaye Umma ta shiga jinjina kai tana k’ok’arin mik’ewa. Jiki a matuk’ar sanyaye tasa k’afa zata fice Asshe ta kuma dakatar da ita.
Umma taja ta tsaya Har lokacin hawaye take.
Asshe ta k’araso tana duban Umma daga sama zuwa k’asa. Lokaci guda tasa hannu ta shiga janyota da k’arfin gaske . A haka suka isa gate.
Suna isowa gate tai jifa da Umma gaban securities. Asshe ta shiga nuna masu Umma “Ko me kamannin matar nan kar ku bari ta kuma shigowa gidan nan..”
Umma dake watse k’asa kaman kayan wanki ta d’ago idanunta da kyar tana duban Asshe dan yanzu ta daina mamakin abubuwa.
“Asshe…”
“Shiiii..!” Asshe ta dakatar da ita tana mai d’ora yatsa ta guda saman labb’anta “Duk draman da akayi mijina baida masaniya Suwaiba.. Ni Ina son mijina kuma ina daraja aurena.. Ni ba irinki bace wacce ta watsar da mijinta dake kwance yana jinya sabida cikan burinta. Bazan bari mace irinki ta lalata mun aure ba.. Dan haka bake ba ni. Dama kema kinsan hanyar jirgi ba daidai bane da na mota. Ni da Ke ba d’aya bane. Ciniki Ya had’amu kuma ta k’are. Babban goro sai magogin k’arfe bayan wata uku zaki sake haduwa da ‘yarki idan d’anmu Ya gama kwangilarsa dan ita ba ajinsa bane. Zaren ba kalar yadin bane. Tashi ki fice kafin nasa su fitar dake..!” Ta k’arashe tana nuna mata k’ofa.
Jiki Babu k’wari Umma ta mik’e tana ganin duhu na gauraye mata k’wayan idanu. Ta shiga had’e hanya tana takawa da kyar tana jin wani abu mai zafi na yawo cikin k’irjinta.. A haka Umma ta fice daga gidan ga duhun dare ba tareda tasan ina take zuwa ba.
SameenaAleeyou📚
*AUREN WATA UKU.!*
*22*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
A b’angaren Inna Dije kaw koda ta fice sai ta tadda Khulsum a yanda tace ta zauna ta jirata. Dan dama lokacin da Umma ta kori Khulsum daga wajen Ummul Inna Dije ta had’u da ita a k’ofan gidan tana kuka. Nan take sanar da Inna Dije ga yanda sukai ita da Ummanta hakan yasa Inna Dije Tai mata umarni da ta jirata Har ta shiga ta fito zasu tafi tare.
Basu zarce ko ina ba sai asibiti wajen Abba.
Inna Dije ta k’ura ma D’anuwanta dake kwance idanu. Ta shiga jinjina kai tana mai furtawa a fili “Lallai Yaya ka gamu da jarabawan shed’anun Mata.. Amma da izinin Allah ba macen da zata saka samun damar cutar dakai cikinsu.. Bazan bari hakan ta kasance ba.. Na maka alk’awari D’anuwana.” Ta k’arashe tana dafe hannunsa guda.
Khulsum dake zaune gefe ta goge hawayen da suka gangaro mata tana jin ciwon abinda mahaifiyarta da abokiyar zaman mahaifiyar nata sukai ma mahaifinta Wanda Babu mijin da Ya cancanci mata Irinsu.
Mama Dije ta matso ta rungume Khulsum tace “Kar ki damu Khulsumu. In sha Allahu mahaifinki zai samu lafiya, zan d’auke shi daga nan.. Zamu tafi gaba dayanmu.. Zamu fara sabuwar rayuwa gaba d’ayanmu tare.. Su kuma Suwaiba da Tani ko waccensu zata girbi abinda ta shuka ne..”
Khulsum bata iya cewa komai ba sai kauda fuskanta gefe da Tai tana mai kuma goge hawayen dake zubo mata. Dan Allah ya gani dukda Umma ta kasance mahaifiyarta sai taji sam bata ko k’aunar a ambato mata sunan mahaifiyar tata musamman bayan rabuwar da sukai a daren yau d’in.
Mama Dije sai duban Khulsum take tana sak’a abubuwa cikin zuciyarta ‘Tabbas sai ta cika Zuciyar Khulsum da tsanar mahaifiyarta.. Suwaiba zata rasa yaranta gaba d’aya.. Bayan ta rasa Ummul zata rasa Khulsum ma. Zata rasa ahalinta gaba d’aya dan mijin ma ta rasa shi kenan rashi na Har abada.. Sai ta tabbata rayuwa yayi k’unci ma Suwaiba, k’uncin da sai ta gwammaci mutuwa da wann rayuwar… Kaman yanda ta rasa Fa’iz d’inta D’anuwanta tilo Ya kuma k’ullaceta sabida soyayyan Suwaiba da ya rufe masa ido. Ta rasa soyayyan D’anuwanta na tsawon shekaru zata tabbata tayi amfani da wann damar ta dawo da shak’uwa da soyayya dake tsakaninta da D’anuwanta.. Snn zata rattaba Auren Ummul ya Mutu kafin wa’adinsa ya cika. Bayan auren ya Mutu ta bi ta sanar da Ummul irin auren tozarci da Suwaiba tai mata. Sai ta kwance ma Suwaiba zani kasuwa gaban ‘ya’yanta. Dik irin biyayya da Ummul ke ma Suwaiba sai ta tabbata ta masu farrak’u bayan ta kashe wulak’antaccen auren da tai ma Ummul. Suwaiba zata zama batada tsuntsu batada tarko. Zata rasa kowa tin daga kan Yayanta Isubu da zata masa jinya a yanzu wanda makahon soyayyan da yake ma Suwaiba ya hanasa ganin aibun Suwaiban har dai suka sami sab’ani mai muni duk sabida Suwaiba har izuwa kan yaranta guda biyu Ummulkhairy da kuma Ummulkhulsum.. Wann alwashi ne da ta d’auka ma kanta. Ta saki murmushi a hankali tana jin zuciyarta na mata sanyi al’amara suna tafiya mata yanda take so.
**
Ikon Allah ne ya kawo Umma gida. Tana isowa ta hangi fitilan d’akin Tani a kashe. A nata tunanin Tani ta kwanta bacci tinda tasan kaman yanda Dije tace bazata kuma barin d’aya daga cikinsu ta kusanci Abba ba tasan bazata bar Tani ta zauna can asibiti wajen Abba ba. Hakan yasa ta shiga sand’a a hankali alamun bata so Tani taji dawowarta.
Kaman Wata b’arauniya haka ta shige d’akinta cikin sand’a tana addu’an Allah yasa ta tadda Khulsum na bacci. Saidai koda ta shige d’akin babu Khulsum Babu alamunta. Umma ta silale ta zauna da kyar tana duban gadon yaran nata da angle din da ko wacce ta Saba kwanciya.. Sai ta tuna irin rabuwar da sukai da Khulsum duk Akan Auren Ummul. Datse alak’a tai tsakaninta da ‘yarta Khulsum. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un tana cikin hayyacinta ta aikata makamancin wann abu. Sai ta soma tunanin toh ina Khulsum ta shige.? Take zuciyarta ta bata amsa da fad’in tana wajen mahaifinta a asibiti kaman yanda kika koreta daga gareki. Khulsum bata da wajen zuwa da ya shige wajen mahaifinta. Umma ta silale a hankali hawaye na kuma b’alle mata. Sai tana jin wani abu da yafi yanayi da tashin hankali na ziyartarta… Yau dai Babu Ummul a cikin gidan, wacce a kullum idan ta bud’e idanu ta ganta cikin gidan Babu aure zuciyarta ke mata ciwo, hankalinta ke tashi. Haka zalika taita kausasa harshenta Akan k’addarar ‘yar tata. Meyasa bataji ciwon ya tafi ba..? Meyasa duk tulin damuwar da Tai a baya Wanda a nata zaton ganin Ummul ne a gida ba tareda aure ba ya haddasa mata. Meyasa taji babu abinda ya ragu a k’uncin da takeji cikin ranta sai ma abinda ya k’aru..? Meyasa..? Meyasa abubuwa suka kwabe meyasa auren Ummul da tai zaton zai zamto mabudin farin cikin ta da na ahalinta meyasa bai zama haka ba.. Meyasa auren Ummul ke barazanan zama mabudi da Mafarin tarwatsewar Ahalinta.. Ta rintse idanunta wasu hawayen masu tsananin ciwo suna zubo mata. Saida Umma tai kuka mai isanta ita kad’ai cikin d’aki with no shoulder to lean on. Babu wanda zaiji sautin kukan nata balle Ya lallasheta.. Ita kadanta cikin d’aki tasha kukanta. Dakin ya mata girma, daren ya mata tsayi… Haka Umma taci kukanta a d’aki cikin dare tamkar marainiyar kenwa.
**
Washe gari sassafe ake shirin tafiya da Amarya Ummulkhairi gidan mijinta dake Abuja.
Asshe ta fito taci uwar gayu yayinda Ummul ta kasa fitowa sai shesshek’ar kuka take Wanda ya riga ya zame mata jiki. Tin Daren jiya take aikin abu d’aya Akan dole Asshe ta tilasta ma cin abinci ma saida tai da gaske kafin ta saka ruwan shayi a cikinta. Kallo guda zaka mata ta baka tausayi. Asshe sai sababi take tana fad’in haka za’a Kai amarya a k’anjale jiki duk yunwa kaman wata kazar mayu. Cikin ranta kuwa addu’a take Allah yasa Ummul tafi haka lalacewa ko dan kar idon Haidar da hankalinsa ya sauk’a kanta.
A haka suka fito da k’yar bayan Asshe ta sanar da Ummul kar ta mance kud’in Aurenta shine kud’in jinyar mahaifinta dan haka tafiya gidan Miji ya zame mata dole idan har ba so take su janye komai ba.
Ummul na hawaye take janyo k’afafunta. Tabbas wann auren sadaukarwa ne ga illahirin ahalinta. Bayan datse alak’a da ita da Umma tai a daren jiya na tsawon watanni uku na farkon aurenta bata jin Umma zata tab’a yafe mata idan tace ta fasa wann aure. Ta rintse idanunta zuciyarta na tausarta da cewa irin nata k’addaran kenan. Watak’ila hakan shine alkhairi ga d’aukacin ahalinta. Idan tai nesa dasu Watak’ila farin ciki da kwanciyar hankali zai wanzu cikin ahalin irin Wanda basu samu a baya ba.
Fitowar da zasuyi da zummar shiga mota kenan suka sinkayo wata murya.
“Ku dakata ku dakata. Direba a dakata ga pasinja d’aya.!” Ta k’arashe tana kuma mak’ale k’aramar jakar Ghana must go d’inta a hammata sai faman buga sauri take.
Asshe ta zaro ido tana duban matar nan shaye da tsananin mamaki “Dije.!” Ta furta da k’arfi.
Inna Dije taci gaba da sakin murmushi tana duban Asshe “Haba k’awa ban gane wasa tare ci banban ba. Haka kika shirya tafiya da ‘yarmu babu wani nata. Ce Miki akai batada dangi ko tsawa akai ta fad’o da zaki rufeta ki kaita kamar wata maras gata.”
Ummul tai saurin yaye rufin kanta hawaye na kuma b’alle mata “Inna Dije.” Ta furta a hankali tana duban Dije. Dije tai saurin k’arasawa ta rungumi ‘yar D’anuwanta “Ni ce nan Goggonki Ummul.. Innarki Dije, bazan bari a kaiki gidan miji kamar maras gata ba. Shige muje.!” Ta k’arashe tana mai shigar da Ummul cikin mota.
Har lokacin mamaki Ya kasa sakin Asshe. Watau matar nan ta ranste sai ta tona mata asiri. Inaa bazata bari hakan ta kasance ba.. Kafin Tai aune taji Inna Dije ta janyo hannunta ta jefata cikin mota. Fad’i take “Direba tada mota muje birnin tarayya ba nan kusa ba.”
Asshe ta matse hannun Inna Dije da k’arfi tana k’ok’arin fiddota waje amma sai taji Inna Dije ko gizau bata motsa ba. Saitin kunnen Asshe take rad’a mata “Kar kiyi wann ganganci dan tsaf zan kwance Miki zani a Kasuwa. Kama daga kan mijinki da kishiyoyinki Har izuwa kan ‘yaruwarki. Dan haka cikin salama ki shige mu tafi.!” Ta k’arashe tana firfito da idanu waje.
Asshe ta had’iyi abinda Ya tsaya mata a mak’oshi da k’yar. Cikin sigan rad’a take tambayarta “Fad’a mun nawa kike so.?”
Inna Dije ta murmusa, cikin sigan rad’a ta bata amsa da fad’in“Ki bari mu isa can zamuyi ciniki a tsanake.” Sai ta murmusa tana k’are ma Asshe kallo harda kashe mata ido “Kar ki damu k’awalliya zamu sha hirarmu ta k’awaye a mota.” Ta k’arashe tana d’aka ma Asshe bugu a cinya harda kecewa da dariya. Ta dubi driver tace yaja mota su tafi kar rana yai masu a hanya. Driver kaw yai yanda tace dan dai Asshe kam ta kasa katab’us cikin motan. Abun matar Ya koma bata tsoro. Ta d’auki Suwaiba shashasha amma wann kam ko shakka babu gogaggiya ce . Tanaji tana gani suka d’auki hanya tareda Dije babu kuma yanda ta iya. Abinda take tsoro ne yake gab da aukuwa. Mai zai faru idan wann matar da ta zame mata k’arfen k’afa ta bud’e baki ta sanar da uwar Haidar komai. Ta tabbata Kwaise zata iya d’aureta Har igiya yayi saura sann asirinta gaban miji da kishiyoyi harma da yaranta Ya tonu. Lallai Ya zama dole ta san yanda zata b’ullo ma wann matar. Idan ta kama ta b’atar da ita tun akan hanya ne kafin su isa zatai hakan. Dole ta canza salon yanda zata tunk’ari wann mahaukaciyar Matar da burin fansan ran D’anta Ya rufe mata ido. Haka dai Asshe taita sak’awa tana kwancewa cikin mota. Gaba d’aya kallo d’aya zaka mata ka gane a birkice take.
**
A b’angaren Umma kaw sassafe da rabon fad’an yaran Mama ta tashi. Badia da Azeema sai tona ma juna asiri suke Azeema na fad’in sai Badia ta nemo B’arawon mijinta yanda ya shiga ya fita. Yayinda Badia ke fad’in gwara nata mijin a sata Ya tsaya ita kaw Azeema ba Wanda baisan Habibu k’aton kwarto bane Wanda baya raina mai d’ankwali. Nan dai akaita fad’a Umma na k’ok’arin rabiya amma inaa saida dai akai chaa a k’ofan b’angaren nasu kaman ko yaushe ana bama ido abinci.
Azeema taci gaba da fad’in “Oho dai gwara ni mijina baiyi sanadin rufe uwata a police station ba. Hasalima fad’i tashi yake ba dare ba rana dan ya fidda mahaifiyarmu da wann macucin mijin naki ya jefata ciki.. Kuma wllhi idan Har baki fito da Tasi ba zan tona miki asiri wajen Jami’an tsaro dan ba Mama bace kawai ta saka hannu a takardun bogin da mijinki ya kawo na saida Shagon Abba harda ke macuciya azzaluma.!”
Haba nan fah Badia ta janyo Azeema dambe ya kaure tsakaninsu. Umma ta shiga tsakiya tana k’ok’arin rabiya aikaw akai jifa da ita gefe. K’um kakeji jini ya b’alle a goshin Umma. Ta dafe kanta dake juya mata tana shafan jinin dake zubowa daga goshinta. Da rarrafe Umma ta bar wajen ta shige d’aki dan ba mutan gidan kawai ba har mak’ota lek’ensu suke suna Allah wadai irin wann ahali. Saikace ba jiya akai auren Ummul ba wacce kowa yake tunanin sabida ita ahalin suka gaza samun kwamciyar hankali. Sai gashi yau an wayi gari babu Ummul da akai mata lak’abi da annoba cikin gidan amma da tashin hankali suka wayi gari kaman dai ko yaushe.
Umma ta matse bakinta tana jin kukan gaske mai k’arfi na taso mata musamman da taji abubuwan da mutane ke fad’i. Ta kuma shafan goshinta taga jini. Ta rintse idanunta tana tunanin ‘ya’yanta a daidai lokacin da jini ke fitowa daga goshinta. Ta aurar da Ummul bisa son zuciyarta sann ta kori Khulsum. Ummul take hangowa tana share mata jinin goshinta cikin tsananin nuna soyayya da kulawa yayinda take hango Khulsum tsakiyan Azeema da Badia tana k’ok’arin k’watar wa mahaifiyarta hakkin rauni da sukai mata a goshi.
Umma ta fashe da wani irin kuka mai ciwo. Lallai mutum baya gane kiman wani ni’ima da Ubangiji yai masa baiwa dashi sai ya rasa wann abun.
A haka Umma taci kuka da suntumemmen goshi ita kad’ai a d’aki.
Rayuwa kenan ko babu rabuwa akwai mutuwa. Mu zama masu godiya ga d’imbin rahamomin ubangijinmu garemu tun kafin daman hakan ya kufce mana. Tomorrow is not promised. Mu so juna muyi hakuri da juna. Mutanen da Allah ya albarkace mu dasu cikin rayuwarmu. Walau iyaye, ‘ya’ya, miji, mata abokan zama da sauransu. Rayuwar duka batada tsawo. Abinda hak’uri bai kawo shi ba tashin hankali bazai bayar ba. Allah ya mana muwafak’a duniya da lahira. Ameen.
**
A can b’angaren Mama Tani kuwa yanda taga rana haka taga dare a police station. Fuskarta ta kumbura suntum sakamon Mari da tasha hannun tsagerun ‘yanmatan da aka had’asu cell d’aya. Sallah ne kawai yake ceton Mama daga bugun da take sha hannun tsagerun nan.
Saiga Mama tana sallah cikin cell harda nafilfili. Har bata fatan ta ida sallah gudun kar su ci gaba da cutar da ita. Yara k’anana Har tausa suke sa ta masu idan batayi ba taci bugu.
Ta kula ko neman agaji take wajen ‘yansandan basu kawo mata d’auki musamman wann matar da ta gansu da Habibu.
Ta nemi a fitar da ita zataje fitsari. Da k’yar da sid’in goshi aka fitar da ita tinda bata jima da fita alola ba. Addu’a take Allah Ya had’ata da Habibu Ya sanar da ita yaushe za’a fiddata. Kaman daga sama ta bayan d’akin da aka kaita fitsari yanda band’akin suke a jere ta soma jin maganganun ta wata ‘yar window. Muryar Habibu takeji daga window d’in yana kwantar ma ‘yarsandar hankali da fad’in shi fah ba taimakon Mama Tani zai ba. Dama yayi zaton zai cimma Tasi’u ne kafin abubuwa su lalace. Dan haka bazai jefa kansa a uku ba dan wann bakwaiye Ya rantse har kotu sai an tafi. K’arshe gidan Kasu Tani zata tafi babu ranar fita. ‘Yarta kuma babu amfanin da take masa saima cike masa d’aki da tai dan haka a yau d’in nan zai rubuta mata takarda tinda Tasi’u Ya gudu da kud’ad’en. Aure zaiyi Ya saka amaryarsa a d’akin.
Sai ga Mama tana sakin fitsarin jikinta. Ta kama k’arfen window ta d’ale tana dubansu “Habibu.. Irin cin amana da yaudara da zakai ma Azeema kenan..! Amma Habibu Allah Ya tsine maka albarka. Ka cuceni ka cuci Azeema. Habibu Allah bazai barka ba. Kan wann kilakir ka wulak’anta Azeema.?”
Kafin takai aya taji sauk’an tagwayen Mari a fuskarta. ‘Yar sandar Habibu ce tai mata Marin “Ki iya bakinki kisan a ina kike.” Cewar budurwar Habibu Yayinda Habibu ke mik’a mata farar takarda “Tazo gidan sauk’i tinda kina kusa. Ga wann ki bawa ‘yarki idan gantalinta Ya d’ebota ta nan tinda ba mutuncinki suke gani ba balle suzo dubiyanki. Kar na koma gida na tadda tsummokaranta cikin d’akina. Sak’o na baki ki sanar da ita. Gyara zan fara a gaggauce dan amarya ta zan aje ciki.” Ya k’arashe yana kashe ‘yarsandarsa da murmushi.
Mama sai Tai mutuwar tsaye tana juya takardan da Habibu Ya mik’a mata cikin hannunta. Bata san meke wakana ba har saida ‘yarsandar da tai mata rakiya fitsari ta tasa k’eyarta.
Fitsarin da ta juyesa jikinta kenan ba tareda taje band’aki ba. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un. Meke faruwa da ita da yaranta? Daga wacce miji Ya bata sak’on sakinta ta hannun mahaifiyarta sai wacce miji Ya cuta ya kuma gudu Ya barta. Sann a dalilinsa aka kame uwarta aka gark’ame. Shin wann wace irin rayuwa ce. Sai ga Mama tana kuka shar shar da hawaye hannaye biyu aka “Wayyo ni Tani naga takaina.! Habibu kaji tsoron Allah. Ka tuna ko mutuwa na kunyar idon uwa. Yanzu da wani bakin zan goranta ma Suwaiba ni Tani. ‘Yar Suwaiba ta tafi d’akin Miji ni nawa yaran Sun dawo a jere. Wllhi bazata saku ba. da na koma na fuskanci tozarci yo gwara na Mutu a nan.!” Ta kuma kurma kururwa.
Tsawa budurwar Habibu ta daka ma abokan aikinta cewa su shige da Tani cikin cell d’inta su gark’ame.
**
Abuja
Tsaye suke a can construction site d’insu, yanda zasu gudanar da babban project na Kampaninsu.
Dukansu sanye suke da kaya irinta k’wararrun Engrs. Reflective safety jacket kalan d’orawa mai ratsin bak’i sai safety helmet mai d’aukeda tambarin kamfaninsu daga gaban *MB*
Su kusan hud’u sunyi tsaye gaban wani tapkeken sketch. Design Architect Hisham sai kwararo bayani yake yayinda sauran ke jinjina Kai kowa yana fad’in abinda ya k’ware akai.
Hisham na hankalce da Haidar Wanda Sam hankalinsa bai tare dasu. Excusing Kansa yai ya k’araso yanda Haidar ke tsaye jingine jikin mota. Shima d’in cikin shiga irin tasu yake saidai shi babu jacket saman rigarsa sai ko helmet.
Hisham yai masa k’uri hannayensa zube cikin aljihun jeans d’insa. D’an k’arasowa yai kusan Haidar d’ in had’ida jingina jikin motar. Ba tareda ya dubi Haidar d’in ba ya soma fad’in “This is not like you Engr. Ban Saba ganin ana aiki jikinka a mace ba.. I expect to see Haidar mai jajircewa da na sani dan ban tab’a tsammanin Dad d’inka zai mik’a maka ragamar aikin nan cikin sauk’I ba.. Snn kaji yanda abokinsa yake yabawa team d’inmu baice komai ba baiyi yunk’urin dakatar dashi ba kaman yanda ya saba a baya. Kawo yanzu sun hango future ma Kampanin tareda kai. Zan iya ce maka na hango yau d’in a k’awayar idanunsa. Ko bai furta maka ba he’s proud of you..”
Furzar da huci kad’an Haidar yai yana mai gyara tsayuwarsa hannayensa zube cikin aljihunsa yake duban masu tonon k’asa daga gefe “But unfortunately I’m not a perfectionist, a workaholic like my Dad.” Ya karkato yana duban Hisham sosai “Ban damu ba yayi alfahari dani ko kar yayi. I don’t give a damn..”
Hisham ya d’an girgiza Kai yana duban Haidar d’in “So tari mukan kasa ganin blessings da Allah ya mana baiwa dasu har sai mun rasa. Ka gode ma Allah Haidar ka girma da iyayenka biyu a raye kuma suna tareda kai. In my own case is a different story. Ban samu daman sanin mahaifina ba. Ban samu daman had’uwa dashi ba.” Ya d’anyi fasali kafin ya murmusa “But it’s fine I’m not complaining. Alhamdulillah, At least I have my Mom with me. And to me she’s more than enough you know.” Ya kuma murmusawa yana jinina Kai “Bazamu iya k’irga d’inbin ni’imomin Ubangijinmu garemu ba.”
Dukda sanyi da jikin Haidar yai sai ya kauda Kai gefe dan shi gani yake da mahaifinsa da babu shi duk d’aya ne gwara ma ace babun Watak’ila bazai masa irin k’iyayyan da yake masa a yanzu ba. Duban abokan aikinsu yai kana ya kauda zancen da fad’in “Komai ya kammala saura fara aiki. Soil test ya rage. You take care of the report while I’m away..”
Hisham ya zuba masa ido shaye da mamaki. Ya d’an girgiza kai “While you are away.? What does that mean..? What do you mean by that.?”
Murmushi Haidar yai “It’s good to take a break, don’t you think.”
Har lokacin dubansa Hisham yake da mamaki “Seriously.! Ina zaka Haidar.?”
“To Cuba. Jirgina gobe da safe ne in sha Allah..”
“Business trip.?” Hisham ya tambaya yana dubansa.
“Am I using business terms here.? Bakaji mai nace maka bane. Vocation zan tafi of course.”
Hisham ya d’an Ware idanunsa. Kafin ya soma magana Haidar ya dakatar dashi “Don’t even start.”
Hisham ya jinjina Kansa a hankali “Bazaka saurareni ba na sani. But why Cuba.? Jiya fah nake gani a labarai Hurricane killed at least 6 people there… Couldn’t she think of a better place.” Ya tambaya yana duban Haidar d’in tinda yasan wann bai wuce aikin Matarsa Dareen ba wacce yayi imani tarayyarta da Haidar d’in Babu wani alheri tinda aure ne da Har yau iyayensa basuda labari.
K’ok’arin bud’e motarsa ya soma “Zamuyi magana kaikam..”
Har ya bud’e motar zai shige Ya juyo ya dubi Hisham murmushi saman fuskarsa “C’mon haka zaka barni na tafi bazaka min fatan alheri ba. What if this is the final goodbye. What if hurricane ya ritsa dani a can.?”
Hisham ya k’araso ya d’an punching muscle d’in Haidar guda “You shut up jerk.!”
Dariya sukayi su duka biyun kafin suka rungume juna Hisham na fad’in zasuyi aikinsu tareda nasara cikin yarda da ikon Ubangiji. A haka sukai sallama kowa naji a cikin zuciyarsa zasuyi kewan juna.
Hisham yai tsaye yana bin bayan motan Haidar da kallo. Murmushi ya saki yana mai ayyanawa cikin zuciyarsa tinda ba wani aiki mai tsanani da zasu fara yanzu zai tafi Kano. Ya kuma sakin murmushi sanda yake hango beautiful innocent face d’inta a k’awayar idonsa. Ya shirya tafiya neman aurenta wann karon. Ya shirya sanar da ita abinda yakeji gameda ita. Even though he’s not expert a wann b’angaren but zaiyi iya k’ok’arin sa ya tabbata bata kufce masa ba. He’s been rejected so many times wanda hakan yasa neman aure da ‘yanmatan suka fita Kansa. But wann karon ya shirya yak’in Neman auren Ummulkhairi da duka k’arfinsa. Ya kuma sakin murmushi mai kyau zallan k’aunarta na d’awainiya dashi.
**
Yanda Mommy keta faman shiga da fice saida abun yai mugun d’aure ma Anisa kai. Mommy fah tarba na musamman taketa faman shirya ma masu kawo Amaryar Haidar. Jikin Anisa gaba d’aya ya mace, zuciyarta ta karaya ganin yanda Mommy keta d’aukin wann aure. Ta tabbata ko wacece matar Haidar ta gama samun gurbi mai girma cikin zuciyar Mommy dan sosai take son wann aure. Ita gani take Ammi b’ata lokacinta kawai take dan Mommy bazata bari Haidar Ya rabu da matar nan ba cikin watanni k’alilan kaman yanda Ammin nata ta sanar da ita.
Suna jin shigowar Mota Mommy tai saurin mik’ewa tana fad’ad’a murmushinta. Lokaci guda ta dubi Anisa tace maza su sauk’a k’asa ga matar Haidar ta iso.
Saurin rik’o Mommy Anisa tai tana murmushi da yafi Kama da yak’e “A’a haba Mommy. D’an dakata mana kefa uwa ce. Ki bari ni na sauk’a. Ma shigo miki da ita.”
Bata jira cewar Mommy ba ta nufi k’asa tana mai rausayar da ido had’ida furzar da huci dan wani mugun takaici ne Ya cika mata zuciya yacce kasan ‘yar gwal za’a kawo gidan.
SameenaAleeyou📚
*AUREN WATA UKU.!*
*23*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
Mommy ta gaza zaune ta gaza tsaye. Zuciyarta sai harbawa yake, ta rasa sukuni ne zuciyar nata ya samu sakamakon kawo makarin asirin Haidar da akayi kokuwa yarda da amincewan Haidar Wanda batada tabbas akai ne. Koma dai tsoron abin ya k’unshi rasa rai ne. Sai ta fara tuhumar kanta anya bata kasance mai son zuciya ba. How could she kill another person’s child for her own to survive. Saurin girgiza kai tai dan bata son irin tunanin nan su shige kanta. Dole ne yasa tayi hakan. Ance so so ne amma son kai yafi. She needs to save her only son no matter the cost, koda kuwa Ya k’unshi rasa rai ne. Da wann tunanin zuciyarta ya samu natsuwa. Tai zaune cikin kujera tana jiran shigowarsu.
Inna Dije na rik’e da hannun Ummul gam take k’are ma katafaren gidan kallo Wanda ta masa lak’abi da fadan shugaban k’asa.
Suna shigowa wani irin k’amshi ne da zatace hancinta bai tab’a karo da irin shi ba tsaban dad’i shi ya daki hancinta, nan ta hangi wata hamshak’iyar mace wacce kallo guda zakai mata ka tabbata tayima babu bugun girma. Tana ganin Asshe jik’akk’iyar mace wayyaya sai taga ashe gaban Hajiya Kwaise Asshe ba komai bace. Kama daga yanayin suturan dake jikinta muhallinta harma da gogewar fatar ta. Dije ta jinjina kai tana kuma tabbatarwa. Waima Tani bataga wann daula da Ummul ta shiga ba kenan koda kaw ace na wutin gadi ne. Dole Tani ta zauce ta haukace.
Mommy ta fad’ad’a murmushinta tana fad’in su k’araso su k’araso bismillah.
Yayinda Zuciyar Ummul yaci gaba da tsinkewa. Har lokacin kanta rufe yake cikin mayafi.
Daga yanda take zaune saman carpet tana jin yanda su Inna Dije dasu Aunty Asshe suke gaisuwa da muryar wata mata mai yanayi da shige dana Aunty Asshe. Nan gaisuwar tasu ta sauya salo zuwa yaren k’abilar shuwa arab tsakanin Asshe da ‘yaruwarta.
Ita dai Inna Dije tinaninta da k’wak’walwarta sun gaza tantance tsananin kyau da tsarin gidan. Sai juye juye take tana mamakin koda ace auren kwangila na wata uku d’ansu zai da Ummul meyasa sai Ummul a wann irin arziki da suke dashi. Meyasa basu nemo mace da Babu aibu tattare da ita ba sai Ummul. Itafa wann aure Sam bata amince iyaka cin gaskiya Asshe ta sanar dasu ba. Dik yanda akai akwai wata a k’asa. Tunaninta ne Ya katse sanda taga matar ta k’araso gaban Ummul murmushi fal saman kyakkyawar fuskarta.
Zuciyar Ummul yaci gaba da tsinkewa sanda taga hannun matar saman nata.
Lokaci guda Mommy ke ci gaba da fad’in “Welcome my daughter. Sannu da zuwa cikin ahalinmu. I can’t believe this is happening.. Finally Matar Aliyu na ta iso.” Sai ta k’arashe tana rungume Ummul daga zaune.
Anisa da Tai mutuwar zaune tana dubansu. Sai ta rausayar da ido cikeda k’osawa tana mai aika ma Amminta wani kallo wacce itama jiki a sanyaye take duban Mommy dake rungume da Ummul tana ayyana farin cikinta a fili.
Mommy kaw cikin zuciyarta take ayyanawa ‘Zan kula dake a tsawon watanni uku da zakiyi damu. Sabida kin cancanta. You are my son’s savior. Kin sadaukar da rayuwarki dan rayuwar nawa d’an Ya inganta koda ace bakida masaniya akan hakan. This is the least I can do for you bayan sadaukarwa mai girma da kika mana. Zan baki dukkan soyayya da kulawa Har kawo lokacin da zaki warware mugun k’ullin da akai ma D’ana harma da ahalina.’ Ta k’arashe tinanin nata idanunta harda guntun k’walla. A hankali ta saka hannu ta yaye rufin da akai ma Ummul. Wani ikon Allah Sai Zuciyar Mommy ya kuma karaya. Fuskar yarinyar take kallo.. She looks so innocent and totally naive. She couldn’t help but to feel guilty.. Meyasa rauni Ya cika zuciyarta a kallon farko da Tai ma fuskar yarinyar a zahiri. Tai k’ok’arin saita kanta tana fad’ad’a murmushinta “Barka da zuwa Ummulkhairi, d’ago ki kalleni.. Sabuwar Mamanki..!” Ta k’arashe tana mai tallafo fuskar Ummul wacce ta kasa d’ago idonta ta dubi matar amma jin kalamanta na k’arshe yasa ta soma k’ok’arin d’ago idonta masu cikeda rauni hawaye tab cikinsu.
Dubanta Mommy take Har lokacin tana rik’eda hab’arta murmushi saman fuskarta.
Sai Ummul taji kuka da gaske na zuwa mata musamman da taji matar ta ambaceta da sabuwar Mamanta. Shin tasan Ummanta ta datse alak’a da ita ne..?
Mommy ta soma girgiza mata kai alamun banda kuka. Ta shiga share mata hawayen tana fad’in ta daina kuka ta saki ranta kaman tana cikin Ahalinta.
Mik’ewa Anisa Tai cikeda k’osawa tana rausayar da ido. Ta dubi Amminta ta furta a hankali “I’m tired of this drama.!” Tana fad’in haka tasa kai ta shige.
Su Inna Dije Anci an sha an masu tarban girma ta kuma yarda Lallai Ummul gidan girma ta arziki ta shigo dan ko matar nan bata masu tarba da kayan arziki ba tarban fuska da ta masu da yanda ta amshi Ummul kawai sun isa ta shaida gidan girma da arziki Ummul ta shigo. Koda yake amma Asshe ta sanar da ita Auren na wata uku ne sann ga dalilin auren cewa kwangila suke so a bama d’ansu a kampanin mahaifinsa mahaifin nasa yace bazai bada ba har sai ya kawo masa mata ma’ana Har sai yayi Aure. Shin duk akan AUREN WATA UKU matar nan tai masu irin wann tarba ta kuma karb’i Ummul hannu bibbiyu kaman ‘yarda ta haifa.. Anya kuwa..? Ita fah duka abubuwan dake faruwa Sun fara kwance mata kai. Ji take ta gaza fahimtar komai. Koda sukazo tafiya da Ummulkhairi b’angaren Haidar Mommy ce ta rik’e Ummul da kanta tace ita zatai ma ‘yarta rakiya. Kan Inna Dije Ya kuma d’aurewa. Suka dubi juna itada Asshe. Asshe ta k’ifta mata ido alamun kar tace komai.
A haka dai aka bama Inna Dije ma nata masauk’in nan cikin gidan da nufin washe gari idan Allah yakai rai zasu koma Kano itada abokiyar tafiyarta Asshe.
Ita kad’ai a d’aki sai sak’awa da warwarewa take. Ta d’au d’amarar kafin su bar gidan kafin su koma garin Kano sai tayi yanda tasan ta fahimci duk abubuwan dake wakana. Batai ma Ummul rakiya zuwa garin ba sai don su koma tare da Ummul d’in. Amma yanda taga Uwar mijin Ummul na kaffa kaffa da ita tana nan nan da ita bata tsammanin Auren zai Mutu a sauk’ak’e. Abu guda ne zai kashe auren nan shine kawai ta bud’e bakinta ta sanar da matar cewa ajalinta D’anta Asshe ta kawo mata cikin gida.
Ta mik’e da zummar fitowa nan taga Asshe tsaye gabanta.
Girgiza mata kai Asshe Tai tace “Koma ki zauna Tun muna mu biyu.”
Inna Dije ta dubeta da mamaki. Sai kuma Tai ‘yar bazawarar murmushi “Aw baki so mu kasance mu uku ne. Ina nufin ni da Ke da kuma ‘yaruwarki wacce kikai mata rufa rufa ki aura ma D’anta ajalinsa. Kar ki tausareni da abun duniya dan yanzu na fahimci kema gaban ‘yaruwar taki almajira ce. Sunan mijinki ne kawai kike tink’aho da tak’ama dashi amma da alama Babu abinda auren naki ke tsinana Miki. Da alama yayinki ya k’are wajen miji dole ki nemi hanyar neman kud’i kota halin k’ak’a.”
A zuciye Asshe ta dakatar da ita “Kar ki kuskura ki bada shaida kan abinda bakida masaniya. Ina shawartanki kar kiyi gangancin shiga tsakanin ‘yanuwa guda biyu. Ina nufin nida ‘yaruwata.” Ta k’arashe maganar nata tana sakin murmushi kamar ba itace ta sha mur ba.
Lokaci guda Asshe ta k’araso ta dafa kad’an Inna Dije guda tana sakin murmushi “Ki kwanta a saman gado irin Wanda baki tab’a mafarkinsa ba. Ki yada gajiya, kafin ki d’auki hanyar gida gobe dan ba Lallai ki sake karo da irin wann gadon ba. Kar ki mance ‘yarku wata uku kacal zatai a gidan nan.!” Ta k’arashe tana k’irga uku da yatsunsa. Lokaci guda ta zaunar da Dije saman gado sai itama ta zauna a gefenta “Ya kamata mu tab’a hira ta k’awaye kafin safiya.. Baki tunani.?” Ta k’arashe tana kashe ma Dije ido. Daidai lokacin Anisa ta shigo da tea cups guda biyu.
Asshe ta fad’ad’a murmushinta “Yauwa ‘yar albarka. Kin kawo mana shayin nida k’awata.”
Anisa ta jinina kai tana mai ajewa gaba garesu.
Asshe ta d’auko ta mik’a ma Dije “Ga shayin gidan shugaban k’asa. Irin wann ganyen shayin a gidan shugaban k’asa kawai kike gani ki sha ki kafa tarihi ki goranta ma sirakanki ina nufin Tani da Suwaiba.” Ta k’arashe tana kurb’an wanda ke d’aya hannun nata.
Ganin Dije ta k’ek’ashe ido tana dubanta Ya sanyata sakin murmushi “Aw na zaci k’awa kika d’aukeni. Kindai san k’awar arziki bazata baki guba ba. Ko dama k’arya kike da kika kirani k’awa.?” Ta murmusa tana kurban shayinta hankali “Ashe k’aryar gogewa kike Dije.” TaI maganar tana kuma kurban shayin. Harda lumshe ido tana fad’in “Wani abu sai a fadan shugaban k’asa.” Ta shanye nata tana k’ok’arin janyo na Inna Dije da niyyan shanyewa Inna Dije Tai saurin rik’e hannunta ta amshe tea d’in.
Inna Dije na murmushi tace “Yo Dije nake muricin kan Dutse . Idan baki sani ba ban fito ba saida na shirya. Ba wani barikinki da gogewarki da zai bani tsoro.” Ta k’arashe tana kafa kai ta soma kurb’an shayi tana lumshe ido.
Kan kace me Inna Dije ta zube kan gado bacci yayi awon gaba da ita. Asshe ta kece dariya tana jinjina k’ok’arin ‘yarta Anisa da ta kawo wann plan d’in. Lokaci guda ta gyara ma Inne Dije kwanciyarta tana furta “K’awata ki sha bacci lafiya. Keda bud’e ido kuma sai gobe da safe in sha Allahu.” Ta k’arashe tana kuma kecewa da dariya.
A haka Anisa ta kuma shigowa ta tadda Amminta “Gobe da safe jirgin Daddy zai tashi. Mommy zata masa rakiya zuwa airport. Sai kiyi amfani da wann dama Ammi ki fitar da matar nan daga gidan nan da zaran Mommy ta fice. Kinga hakan na nufin bazata samu zarafin sanar da Mommy abinda kike tsoro ba wanda kika kasa sanar dani.” Ta k’arashe tana tab’e baki had’ida rausayar da ido Wanda d’abi’anta ne.
Bakin Asshe Ya gaza rufuwa dan farin ciki bata tab’a tsammanin zata samu solution na yanda zatai da matar nan cikin sauk’i ba. Ta dubi Anisa tace “Ni yau kin gama min komai. Ina Miki kallon marar wayau ashe zaki iya had’a plan irin wann. Lallai na yarda banyi ganganci ba da nace You’d become my eyes here.”
Anisa ta murmusa “I’m your daughter after all, Ammi.”
Asshe ta jinina kai “K’warai yau kin gama tabbatar min. Kuma na yarda zakiyi kaman yanda nace. Koda wasa kar ki bari D’anuwanki Haidar Ya samu kusanci da yarinyar nan. Kiyi duk irin makircin da kikaga Ya dace ki tabbata basu samu kusanci ba a tsakanin watanni uku.”
Anisa ta girgiza kai kad’an “Amma Ammi meyasa kika canza ra’ayinki akan yarinyar bayan da kince mun na zama mabudin k’ulla shak’uwa tsakaninsu da Haidar.. Ammi what’s with all the mystery behind this marriage.. Ke yanzu kin nuna baki so amma a b’oye ba tareda kin bari Aunty Kwaise ta fahimci haka ba. Ita Aunty Kwaise tana son auren tana son yarinyar da duka zuciyarta. And at the same time baki so wann matar tayi magana da Aunty Kwaise..” Ta k’arashe tana nuna Inna Dije dake zube saman gado tana bacci. Ta kuma girgiza kai “Ammi wai menene b’oyeyyen al’amarin gameda Auren Haidar.?”
Asshe ta sauk’e ajiyan zuciya ta kamo hannayen Anisa “Ki yarda dani Anisa. Zan fayyace miki komai amma ba a daidai wann lokacin ba. Akwai lokacin da zaki fahimci duk abubuwan da nayi. Iyakacin abinda zan fad’a Miki a k’arshe shine zaki mallaki Haidar da izinin Allah. Amma fah sai kinyi aiki tuk’uru Anisa. Kar ki bari Ya kusanci yarinyar nan. Daga k’arshe zamu nemo mafita.”
Anisa ta sauk’e ajiyan zuciya “Shikenan Ammi zanyi yanda kikace. After all, bana son auren tin daga farko. Yanzu zan d’auko makaman yak’i na da kika sa nai watsi dasu daga farko.” Ta kuma murmusawa kafin tace “Tinda inada ke Ammi, I know I’m not fighting a losing battle.”
Suka sakar ma juna murmushi a tare kafin Anisa tasa kai ta fice zuciyarta na mata sanyi. Zatai whatsoever it takes dan ta tabbata yarinyar nan ta fita daga rayuwar Haidar duk tsananin son da Mommy ke mata kuwa. Ta kuma rausayar da ido kafin ta shige.
Asshe ta janyo ma Inne Dije k’ofa kafin ta fito daga b’angaren bak’in ta nufi wajen ‘yaruwarta daketa faman neman layin Haidar bata samu.
Zama tai gefenta ganin damuwa ya nuna k’arara saman fuskar Mommy.
“Aunty Kwaise, ya na ganki haka. Allah sa dai lafiya.?”
Mommy ta furzar da huci kad’an “Na gaza samun layin Haidar Har yanzu. Ga amaryarsa ta iso.”
Asshe ta jinina kai kad’an “Relax Aunty Kwaise. Ki kwantar da hankalinki.. Yarinyar nan tana nan a gidan nan har tsawon watanni uku. Ki basa space kar ki tak’ura masa da batun a yanzu. Tinda an samu Ya amince kuma yarjejeniya akai dashi so I believe zai zo Har nan kan k’afafunsa.”
Mommy da har lokacin ta gaza samun sukuni girgiza kai take “What if ya janye fah Asshe.? What if wancan makirar ta kuma jifansa da wani mugun asirin fah..? Asshe what if Malaminta yafi namu..? Asshe I’m scared.. Tsoro nake kar duk efforts d’ina su tafi a banza.”
Asshe ta kamo hannun Mommy ta zaunarta saman gado “A’a Aunty Kwaise ke uwa ce. Da izinin Allah k’ok’arin ki bazai tafi a banza ba. Haidar zai dawo gareki. D’anki zai dawo gareki. Munyi komai kaman yanda Malam yace. Inada yak’inin hak’armu zata cimma ruwa. Just relax, ki zama calm kuma ki tunk’ari Haidar a tsanake. Yanda kike ta rawar k’afa akan yarinyar zai k’ara tunzura Haidar ne. Kinsan halinsa hasalima kinfi kowa sani tinda ke kika haifesa. Ki bashi gobe zuwa jibi koma satin nan. A hankali sai ki tunk’aresa da batun.”
Mommy ta girgiza kai “Sati Asshe..? Toh me zaman me yarinyar zatai a gidan nan idan Har babu wanda tazo domin shi.. Asshe no sati yayi yawa. Kema uwa ce ya kamata kifi kowa fahimtar mai nake ji.”
Asshe ta jinjina kai “Na fahimceki Aunty Kwaise. Shiyasa nake k’ok’arin fahimtar dake abinda na hango.”
Mommy ta jinjina kai a hankali tana duban Asshe wacce gaba d’aya batada wani kuzari “Asshe.” Ta kirawo sunanta in a serious tune.
Zuciyar Asshe Ya tsinke. Kai da ganinta kaga maras gaskiya.
Mommy taci gaba “Akwai abinda ya kamata na sani ne..? Ina nufin, tinda kuka kawo yarinyar nan kin canza. Kaman akwai abinda ke damunki ba kaman lokacin da muka soma shirya auren nan ba. Tell me, is there something I should know.?”
Asshe tai Shiru zuciyarta naci gaba da yankewa sai tanajin tamkar ‘yaruwar tata ta riga ta fahimci komai abinka da maras gaskiya.
“Asshe.!” Mommy ta kuma ambato sunanta su duka biyun suna duban juna.
Sai Asshe ta fashe da kuka tana girgiza kai.
Hakan yai mugun tada hankalin Mommy. Bata San sanda ta mik’e ta k’araso wajen ‘Yaruwar tata ba. Ta dafata tana tambayarta meke faruwa.
Asshe na hawaye take bama Mommy hak’uri tana girgiza kai.
Cikin rashin Hajiya Kwaise ke girgiza kai “Asshe meyasa kike kuka irin haka. Kuma meyasa kike bani hak’uri.. Wani laifi ne kika min..?”
Cikin zuban hawaye Asshe taci gaba “Na miki laifi mai girma Aunty Kwaise..”
Mommy ta girgiza kai “Laifi.. Wane irin laifi..?”
Anisa da isowarta jikin k’ofan kenan nan tai tsaye ta kasa kunne tana sauraron wani laifi ne mahaifiyarta ta aikata ma Mommy. Cikin zuciyarta Addu’a take Allah yasa taji amsoshin duk tambayoyin da takewa mahaifiyarta gameda wann murd’add’en aure da sukai ma Haidar.
Muryar Amminta ta sinkayo tana fad’in “An sace komai Aunty Kwaise. Kayan lefe na gani na fad’a da kika sa akai ma yarinyar. A lokacin da kayan ya dawo gidana bayan an kai gidansu yarinyar.. A lokacin b’arayi suka biyo dare suka kwashe komai.. Maganar millions of Naira ake.. Shiyasa kikaga dik jikina yayi sanyi ko zarafin fad’a ma yarinyar ma ban samu ba balle danginta.”
Shiru Mommy tai tana dubanta. Sai ta jinjina kai a hankali “Kan haka kika tada hankalinki.. Idan dan wann ne Babu wani matsala tinda kwalliya ta biya kud’in sabulu yarinyar ta riga ta shigo hannunmu. Akan auren nan har property na na d’aga na sayar a garin nan.. Kwabon Aliyu Maitama baiyi ciwon kai cikin yak’in neman auren nan ba. So ko nawa zan kashe akan yarinyar nan bazan Ji ciwo ba Asshe because it worth it. Gobe idan Allah Ya kaimu sai ita yarinyar su fita da Anisa ta tayata da shopping kafin mu shawo kan shi gogan. Kinga fitan nasu da Anisa ma zai d’an sa ta kuma sakin jiki sann Anisa ta koya mata wasu abubuwan yanda zamu samun daman shawo kan Haidar Ya amince ya zauna da yarinyar matsayin mata a sauk’ak’e.
Jin haka yasa Anisa sakin tsaki tana juya idanu cikeda takaici tasa kai ta shige dan batai tsammanin abinda za’a ce ba kenan. Ji yanda Mommy keta rawar k’afa kan wann yarinyar. Ita taji ta tafi taje ta k’are mata kallo taga me take dashi haka da Har Mommy ta kasa hangowa tattareda ita.
A b’angaren Asshe kuwa sauk’e ajiyan zuciya Tai dan dama kaya hayansu ta karb’o ta coge kud’ad’e. Dan a wann auren Ummul da Haidar da ta had’a ba k’aramin jari taja ba tinda a halin yanzu mijinta baya yayinta amaryarsa yarinyar Sa’ar Anisa ke cinye kud’in harta da yawon k’asashen waje ya daina yi da ita da amaryarsa yake. Abin sosai yake mata ciwo musamman idan ta tuna yanda tayi nata zamanin kafin ya auro yarinyar. Da alama bokan yarinyar da iyayenta yafi nata aiki ne inji Asshe. Hakan yasa ta buga business d’inta da auren d’an ‘yar Uwar nata. Dan haka koda wasa bazata tab’a bari Kwaise tasan gaskiyan al’amari ba.
Sanda Anisa ta tafi sashen Haidar sai cika take tana batsewa ita kad’ai. Ji take tamkar cin fuska ake mata da matar Haidar. Ta ya ma za’a kawo wata kucakaa ajiye gidan da sunan matar Haidar. Gidan da ita da kanta ta shirya komai to her taste wanda takeda tabbacin Haidar d’inta zaiso. Bata hango Haidar tareda wata cikin gidan ba. Gida ne data shirya masu su biyu take kuma hangosu da kalolin soyayyar da zasu sha a cikin gidan harma da yaran da zasu haifa. Ta kuma rausayar da ido tana furzar da huci kad’an kafin ta nufi sama.
Ga mamakin Anisa zaune ta tadda Ummul a parlor har lokacin kanta rufe cikin mayafi. Ta saki baki tana kallon ikon Allah kafin ta girgiza kai had’ida juya ido “Seriously.! Da gaske kina nan kina k’unk’ume a wajen. Kina jiran miji yazo ya bud’e fuskarki.. Lallai kuwa zaki jima kina rufe kaman kwab’in cincin dan ba mijin da zai bud’e wann fuskar naki.!” Ta k’arashe tana fincike rufin fuskan Ummul.
Damm! Haka k’irjin Ummul ya buga sanda taji mai maganar ta finciki mayafin da Mommy ta rufa mata bayan sun kawota sashen.
SameenaAleeyou📚
.*AUREN WATA UKU.!*
*25*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
Ya girgiza Kai kad’an disbelievingly “Hajjah.. Ban.. Ban fahimceki ba. Aure.? Ummul tayi aure..?” Ya kuma girgiza Kai “Ina nufin, wane irin aure kuma.?”
“Zauna.” Ta fad’i tana nuna masa kujeran dake gefensa.
Jiki a matuk’ar sanyaye Hisham ya ja k’afafunsa ya isa ya zauna had’ida zuba ma mahaifiyarsa ido.
“Hisham, ba wann karon bane ka fara Neman aure baka samu ba. Ka kai sadaki, har an saka rana a wasu lokutan amma daga k’arshe an hanaka. Toh ina so ka saka ma ranka wann bazai zama na k’arshe ba. Kuma shi aure da kake gani nufi ne na Allah. Matar mutum kuma bazata wuce shi ba. A kullum hud’ubar da nake maka kenan. Kar ka saka damuwan rejecting d’inka da akeyi cikin zuciyarka. Lokaci ne kawai baiyi ba amma idan lokaci yayi zakayi Aure. Abinda yasa na maka sha’awan Unmulkhair ba komai bane face aminta da nayi da hankalinta, tarbiyarta da kuma addininta. Kaman yanda yazo cikin hadisin Abu Hurayrah Wanda bukhari ya rawaito ‘Manzon Allah (SAW) yace ana auren mace sabida abubuwa guda hudu, sabida dukiyarta, sabida nasabarta, sabida kyaunta ko sabida Addininta. Sai Manzon Allah SAW yace Na horeku da ma’abociya addini hannunka zai samu riba.’ Wann yasa nai maka sha’awar Ummulkhair.” Ta kuma daidaita zamanta cikin kujeran kafin taci gaba “Bugu da k’ari kaida Ummul kunada k’addara mai kamanceceniya. Dukanku Kun fuskanci k’alubale na lalacewar neman aure kafin akaiga auren. Toh amma a ko yaushe shi mutum ya zama mai d’aukan k’addara da hak’uri da jarabawar Ubangiji a yanda tazo masa. Duk iyaye burinsu kenan. Farin cikinsu kenan suga ‘yarsu ta natsu a gidan aure. Haka zalika idan namiji ne suga yayi archiving a rayuwa sann ya zama mutum mai cikan kamala yayi aure. Shi aure abun so ne ba abun gudu bane ba abun k’i bane. Hasalima ya inganta a hadisin Anas dan Malik wanda Bukhari da Muslim sukai ittifak’i akai. Cikin hadisin Manzo SAW ya tabbatar Aure sunnarsa ce kuma wanda ya k’yamaci sunnarsa baya tare dashi. Toh kaga kuwa aure sunnah ce mai girma kuma koyi ne da Manzo SAW. Yayi umarni ma samari da suyi aure ga Wanda Allah ya bama ikon yi. Domin shi aure yana tsare gani da kuma kamewa. Ga Wanda baida hali kuma yayi azumi domin shi azumi garkuwa ne. Hadisin Abdullahi bn Umar wanda Bukhari da Muslim suka rawaito shi.” Ta d’an numfasa “Toh kaga duk wad’ann hadisan suna nuni da aure ba abun k’i bane aure ginshik’i ne na ko wani Al’umma. But you can’t force it. Kuma ka nemi zab’in Allah cikin duk abinda ka sa gaba. Kana so kana buri kana kuma fatan kayi. Cikin aure akwai tarin albarka kuma ibada ne. Allah ya halicci ‘yan Adam jinsu biyu domin su samu natsuwa da juna. Kaga wann natsuwar sai ta hanyar aure za’a samu. Kai hak’uri d’ana, Kai hakuri da jarabawarka. Kai hak’uri da Ummulkhair. Ka cireta a zuciyarka ka nemi wata daban. Allah yasa haka shi yafi zama maka alkhairi da mu baki d’aya.”
Sauk’e ajiyan zuciya Hisham yai yana mai shafe fuskarsa da tafukan hannayensa. Sai ya kifa Kansa na d’an lokaci. Ya d’ago yana duban mahaifiyarsa broken “Hajjah.. Hajjah wanene Ummul ta aura.?”
Tambayar da ya haifar mata da fad’uwan gaba. Ta girgiza Kai kad’an “Shin baka d’auki k’addara bane.? Are you having doubts kan abubuwan da na sanar dakai.?”
Girgiza mata Kai yai a hankali ba tareda da ita cewa komai ba.
Hajjah Fannah ta jinjina Kai “Sanin waye Ummul ta aura baida wani alfanu wajenka. She’s someone’s wife now. Ka cireta gaba d’aya a ranka kuma kar ka waiwayi baya.. Ka min wann alk’awarin D’ana.”
D’agowa ya kumayi ya dubeta. Sai yai murmushi mai ciwo “Kamar yanda kika ce Hajjah.. Zanyi kaman yanda kikace..” Ya mik’e yana kuma shafa fuksarsa “Inaga zan koma bakin aiki ko zuwa… Gobe idan Allah ya kaimu. If that’s with you.” Ya k’arashe jiki a mace.
Sosai tausayin shi ya cikata. A hankali ta jinina masa Kai “Hakan yayi D’ana.. Allah ya tsareta da tsarewarsa ya baka dukkan kariya. Ya saka maka albarka cikin duk abinda ka sa gabanka.”
Ya k’ak’aro murmushi ya sakar mata kafin yasa kai ya shige.
Sauk’e ajiyan zuciya tai tana jin ciwon da D’an nata ke ji har cikin zuciyarta. Shin har yaushe zata ci gaba da b’oye masa.? Shin sai yaushe zata sanar dashi gaskiyan lamari gameda mahaifinsa.? Shin rufe masa da tai tayi daidai..? Shin yaushe zata sanar dashi gameda Ahalinsa.? Shin Anya wann ba alama bace a gareta na cewa ya kamata ta fayyace ma D’anta komai. Musamman da yanzu d’an uwansa ya auri Ummul.? Anya ba baya bane yake hunting d’inta..? Bayan ta datse duk wani alak’ar da take da tabbacin zaisa su waiwaya.. Meyasa kwatsam abubuwa ke neman sauyawa..? Shin Ummul zata iya kasancewa dalilin da zaisa su waiwayi baya.? Ta kuma girgiza kai cikin sauri. A fili take furta “Bana fatan hakan. Allah ya gani tsakani da Allah naso Ummul tamkar ‘yarda na haifa a cikina. Watak’ila iyaka lokacin da zamuyi kenan a tare. Tabbas ya zama dole na datse alak’a da Ummul da duk wani abinda zai had’a d’ana da Aliyu Maitama.”
**
Abuja…
Tsaf suka fito cikin shirin fita. Doguwar rigar abaya Anisa ta bata ta saka. Da shike kaf dogayen rigunan Anisa ta rage fad’insu hakan yasa ya kama Ummul sosai sai yafi kyau a jikin Ummul d’in saidai tsawo da ya d’an mata yawa sakamakon Anisar ta fita tsawo.
Sai faman yatsina fuska Anisa take tana mata kallon wulak’anci.
Mommy kaw suna fitowa ta mik’e ta isa ga Ummul wacce tuni ta sadda kanta k’asa.
Murmushi saman fuskar Mommy take fad’in “Ki saki jikinki ‘Yata. Ki zabi duk abinda kike so. Ko menene.” Ta dubi Anisa “Ki tayata ta zab’i kaya masu kyau Wanda zasu k’ara fito da kyaunta. And make sure you take good care of her.”
Anisa ta kauda Kai gefe tana rolling ido. Kuji Mommy fah wani wai ta kula da ita saikace watchdog d’inta or something.?
“I’m talking to you Anisa kina kallon wani wajen. Kinsan bana san shashancin nan naki..” Mommy tace ba walwala.
Anisa ta juyo fake smile saman fuskarta “Ok Mommy. Kaman yanda kikace .. I’ll take good care of your daughter in-law for you. I promise.”
Mommy tace “She’s my daughter, not daughter in-law..”
Anisa ta kuma kauda Kai tana fuzar da huci. Sai yanzu ta yarda da kalaman Haidar idan ya kira Mommy good actress. Tayi imani ba a banza take ma wann kucakar makahon so irin haka ba. Yarinyar da gaba d’aya duniyarsu ya banbanta. Su d’in gaba d’aya ma ba d’aya bane. Wai Hajiya Kwaise Maitama ke treating ‘Yar talaka haka. Wllhi idan za’a Mutu bazata tab’a yarda auren nan na Allah da Annabi akayi ba. Kuma ko menene ke rufe cikin auren she vowed to find out about it. Sai ta binciko to the core.
Credit card Mommy ta mik’a ma Anisa bayan ta tambayeta zatai driving ko driver ya kaisu. Anisa tace no zata tuk’asu.
Murmushi Anisa ta sakar ma Ummul harda bud’e mata front Seat gaban Mommy. Dan Mommy ta tabbata zata kula mata da sirkarta. Cikin zuciyarta kaw cewa take ‘I’ll play your little game Mommy har na gano bakin zaren komai.’
A haka suka d’auki hanya.
Suna tafe Anisa ta d’aga waya ta k’ara a kunne “Hello Girlfriend kina ina..?” Ta murmusa “Toh ki bar duk abinda kike let’s go shopping.” Ta kuma darawa “Ok just wait there yanzu zaki ganni.” Tana Ida fad’in haka ta katse kiran.
Tai parking ta dubi Ummul “Ke koma baya zan d’auki k’awata”
Ummul ta dubeta sai ta murmusa. Kaman zata fita sai kuma ta fasa. Ta juyo ta dubi Anisa “Amma ba a gidan baya Mommy tace na zauna ba. Kiyi hak’uri bazan iya sab’a umarninta ba.” Ta k’arashe murmushi mai k’untata ma Anisa saman fuskarta.
Hararta Anisa tai kafin taja motar. A haka suka k’arasa kusan wani k’aton gini mai gidaje iri guda a jere.
Can wata budurwa ta fito cikin shigar Wando sai top bajajje wanda bai matseta ba sai d’ankwali d’aure kanta.
Tana k’arasowa Anisa ta bud’e motar ta fito suka tafi a guje suka rungume juna suna kiran juna Girlfriend.
Da mamaki budurwar ta tsaya tana kallon wacce ke zaune gaban motar.
Ta juyo ta dubi Anisa “Neesa wacece kuma wann..?”
Anisa ta rausayar da ido “Kinsan a duniya ba abinda ke burge bakauye irin zaman gaban mota. Kedai shige muje Leenah we gonna shop the entire city..” Ta k’arashe tana d’aga mata card d’in mommy dake hannunta.
Leenah ta shige backseat sai labari suke itada k’awarta Anisa. Tanata k’are ma Ummul kallo wacce batabi ta kansu ba.
Can Leenah Ta bangaji Ummul ta mik’a hannunta jikin radio na motar ta k’ure kid’a. Har lokaci Ummul batabi ta kansu ba. K’arshe hannu tasa ta cikin mayafi ta toshe kumnuwarta dan ita dama ba mai sauraron irin wad’an wak’ok’in na turawa bane.
Sanda suka isa ma gaba sukai suka barota baya. Har sun d’an yi nisa kafin Anisa ta rausayar da ido ta juyo ta dubeta. Nan ta hange Ummul na kokawan d’alewa escalator. Sai kuma ta dubi Leenah “I can’t believe this is happening to me. I can’t believe we are hanging out da bagidajiya irinta. Dubi abinda take neman wani ya mana video yace tare muke. Anjima mu ganmu ana tagging d’inmu. Nidai yau Mommy ta kashe ni. Wann da kyar idan ba daga kauye aka d’aukota ba dan ba dai cikin birnin Kano ba.” Ta k’arashe tana furzar da huci. Daidai sanda Ummul ta k’araso “Kuyi hakuri takalmin ne nakeji kaman zai kadani.”
Leenah da Anisa suka dubi juna suka dara a tare. Kafin Anisa tace “Malama karkiji Mommy ta ce na kula dake. If you go missing babu wanda zai b’ata lokaci wajen nemanki dan da alama this is your first time in a place like this.”
Leenah ta tab’e baki sai kuma ta nufi wani wajen cikin sauri tana ambaton sunayen designers.
Anisa ta rausayar da ido tana duban Ummul da Leenah ta barsu nan tsaye tare “Baiwar Allah. We are here already. Select what you want.. Ko shima sai na tayaki.?” Ta k’arashe tana kuma rausayar da ido had’ida furzar huci.
Tuni Anisa ta tafi wajen k’awarta Leenah. Suka kyale Ummul ita kad’ai.
Saida suka jida kaya nik’i nik’i suka tadda Ummul tsaye da wasu dogayen riguna da basu wuce uku ba.
Duban juna suka kuma yi kafin Anisa tasa hannu ta finciki Kayan dake hannun Ummul. Ta d’aga kayan sama ta Ware tana gani Leenah na tayata “What.! Are you kidding me..? Wann shine iyakacin abinda kika iya zab’a tuntuni.?” Ta girgiza Kai tana kuma duban Kayan.
Leenah tace “Wai zallan jallabiya ta zab’a. Ina zata dasu.. Ba azumi ake ba balle nace ittik’afi zata shiga.”
Anisa ta girgiza Kai tana duban Ummul take d’aga rigunan “Baiwar Allah. We are shopping with Hajiya Kwaise Maitama’s card, we can buy the whole mall if we want.. And hello! You are married to Haidar Maitama. So get used to spending a lot.”
Leenah baki sake take duban Anisa Jin ta kira budurwar da suke tare matar Haidar. Saurin janyota tai suka matsa daga kusan Ummul.
Leenah ta dubi Anisa “Wait, did I hear that right..? Wann d’in matar Haidar.. Haidar Maitama da na sani. Our long time crush..?”
Anisa ta juya ido “You heard it right. Wai wann d’in matarsa ce. Amma bana tunanin auren mai d’orewa ne dan dai tin jiya da aka kawo masa ita gidan he didn’t show up. Mommy ce kawai mai son Auren Amm Wanda akai domin shi baisan anayi ba da alama.”
Leenah ta jinina Kai “No wonder. Dan dai wann hanyar da Haidar yabi ma bata isa bi ba.” Sai ta kuma gyara tsayuwarta tana duban Anisa “But what about you girlfriend. I know you love your cousin so much. Does that mean.. You give up..”
“Giving up is not in my vocabulary Leenah. You should know better. Kawai lokaci na d’ibar masu. I have to study my target well before I strike.! But trust me sweetheart hakan zai faru ne kafin ta samu kusanci da Haidar.” Ta k’arashe makirin murmushi saman fuskarta.
Leenah ta murmusa “Then do it fast sweetheart. Kinga irin wadnn makiran babu wuya sun saye Zuciyar namiji.”
Dubanta Anisa take fuska a yatsune. Tai nuni da Ummul wacce mata me kula da kantin keta faman nuna mata wasu kalolin designs din. Anisa ta murmusa ta kuma duban Leenah “Haidar Maitama ya fada soyayya da wann bagidajiyar. You know what Leenah. I hate to burst your balloon but what you’re imagining is never ever going to happen.” Ta k’arashe tana kuma rausayar da ido.
Leenah ta murmusa “Lallai Neesa toh barikiji na fad’a miki. You’ll remember this moment idan baki tashi tsaye tun yanzu kin kawar da ita ba. Ina nufin tun kafin Haidar ya zame Miki k’alubale wajen kauda ita.”
Shiru Anisa tai sai kuma tace “I don’t want things to reach the point where I have to stain my hands.”
Leenah ta murmusa “Then hire someone to do the job for you.. I can’t wait to get my hands dirty..” Ta k’arshe tana kashe mata ido.
Juyawa tai ta kalli wani cream yanda aka rubuta do not apply on face. It contains strong fragrances that might irritate your facial skin. Ta murmusa ta kuma duban Anisa “Hey Girlfriend. Daga nan ya kamata mu ziyarci beauty Spa.” Tai maganar tana d’auko cream d’in ta nuna ma Anisa. A tare suka dara kafin suka k’arasa wajen Ummul suka ci gaba da tayata shopping kaman babu abinda ke faruwa. Har cewa Anisa take ita tasan taste d’in Haidar so zata zab’a ma Ummul kaya to taste d’insa. Ita dai Ummul bata tankasu ba amma jikinta ya bata wani abun suke shiryawa.
Daga nan Beauty Spa suka tsaya. Ummul ta dubi Anisa “Mai zamuyi a nan.”
“Face treatment sweetheart.” Ta bata amsa tana unbelting kanta daga cikin kujeran.
“Amma ba abinda ya samu fuskata ni..” Ummul ta bata amsa.
Gajeren tsaki Anisa tai “Beauty treatment ake magana ba sai kinji rauni ba. Dan Allah bani son stinginess naku na talakawa. Mommy card ta bayar mu k’arar dashi akanmu idan munso.”
Ummul ta murmusa had’ida girgiza Kai ganin Anisa ta fice zata rufeta a mota.
Koda suka shiga Ummul na hankalce dasu. Anisa da Ummul ake ma gyaran fuskar yayinda Leenah ke tsakani tana jira ta cika aiki kaman yanda suka tsara itada k’awarta Anisa. Ana fara face massage cikin dabara Leenah ta dauko wann cream din ta zuba cikin bowl din da aka kwaba kayan gyaran fuska na Ummul. Tana gama zubawa ta fice dama idon Anisa a lumshe suke sakamakon abinda aka daura mata saman idon.
Ummul ta murmusa a hankali dan taga sanda Leenah ta matse tube din ciki. Aiko nan Ummul ta soma kokawan mik’ewa a birkice jin ana juyata mata fuska alamun bata saba ba. Aiko nan bowls d’in suka fado k’asa saidai basu zube ba. Ummul tai saurin d’aukan na Anisa wacce idonta ke lumshe sai faman tsaki take Bagidajiyar nan na bada ita. Ummul ta mik’a ma mai mata gyaran fuskar robar gyaran fuskan Anisa yayinda mai gyaran fuskar Anisa ta Sunkuya ta d’auki na Ummul dake k’asa tana ce da ita ba komai ta daina basu hakuri.
Anisa ta rausayar da kwayar idonta dake rufe. Takaicin Ummul fal zuciyarta wani b’angare na zuciyarta kuma cikeda farin ciki zata toya ma Bagidajiyar Amaryar Haidar fuska tun kafin ya ganta.
Bata Ida tunanin ba taji wani k’aik’ayi mai gauraye da k’una saman fuskarta. Aiko nan Anisa ta saki k’ara tana tsalle tana ihu tana tambayarsa mai suka saka mata a fuska.
**
Royalton Cayo Santa Maria resort. Cuba…
Tana kwance tana facing view na ruwa. Zuciyarta na mata sanyi. Rayuwar Jin dadi da bata fata wani abu ya katse mata shi. Nan ta bud’e WhatsApp dinta da ta kwana biyu bata waiwaya ba. Sak’onni ne sukaita shigo mata daga wani number da tai saving da . *Shadow.* Kaman jira yake ta kunna nan k’ira ya soma shigowa. Dareen taja garen tsaki. Tasan babu abinda zai tambayarta face mai suke Cuba a daidai wann lokacin bayan kwana biyu bata basa wani update kan Haidar d’in ba. Ganin bazai daina kiraba yasa ta d’aga ba don taso ba.
Tana d’agawa ta fara da “Shadow shadow. Looks like kana biye damu dik yanda muka je. Just like your name.. Before you ask. We are here on our third honeymoon. Oh! I forgot to put my cellphone on DND mode.”
Muryar Haidar ta sinkayo daga bayanta “Who is Shadow.?!”
Zuciyar Dareen yai wani irin tsinkewa tamkar statue haka ta kafe ko motsawa ta kasa.
SameenaAleeyou📚
