*AUREN WATA UKU..!*
*26*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
Ko motsawa ta kasa. ‘Yan hanjin cikinta tuni Sun kad’a. A hankali ta zame wayar daga kunnenta bayan ta katse kiran. Muryarsa ta kuma sinkayowa Ya daki dodon kunnwanta a karo na biyu.
“I think I ask you a question. Who were you talking to on the phone. Who the hell is Shadow.?!”
Juyowa tai tana dubansa yanda ya tsareta da rikitattun idanunsa. Alamun yana jiran amsarta.
Abinka da gogaggiya sai tai murmushi “Shadow.. Inuwa.. Asalin sunansa Inuwa.. He’s.. He’s my cousin.. My cousin that I told you about lokacin auren mu.. Ka tuna..?” Ta k’arashe tana tsaresa da ido.
Kansa ya soma juyawa. Sai yaji ya soma wani tunani wanda bazai iya cewa ga specific abinda yake son tunowa ba. Sai ya zama lost and confused. Dan shi bazai iya cewa ga abinda ya faru lokacin auren nasu ba. Iyakacin abinda yakeda tabbaci akai shine sunyi aure. But baya iya tuna komai in detail.
Dareen taci gaba “Cousin dina da na baka labari. Wanda yake so na ni bana sonsa. Because my heart belongs to you tun kafin mu had’u.” Ta kuma murmusawa “Yaron Uncle dina. Shine ya kira wai mu gaisa har kaji ina kiransa Shadow ina kuma ce masa ya daina damuna because ina tareda lovely husband d’ina, enjoying our third honeymoon.” Ta k’arashe tana d’aura duka hannayenta saman kafad’unsa makirin murmushi saman fuskarta.
Kansa ne Ya kuma Ji ya cunk’ushe sai ya rasa wane tunani yake guda d’aya. Wani abu yake son tunawa amma bai sani ba. Ya kuma kasa tuna komai. Tinda Dareen ta d’aura hannayenta saman kafadunsa sai ya kuma Ji ya zama confused. Sai ya zama baya tunanin komai cikin kwakwalwarsa baya kallon kowa cikin k’wayar idonsa sai ita.
Dareen ta karkatar da kai tana dubansa har lokacin murmushin ne saman fuskarta “Shall we go now.?”
Girgiza mata kai yai cikin rashin fahimta “To Where.?”
Ta kuma murmusawa tana mai tallafo fuskarsa da tafukan hannayenta “You seem to forget things easily nowadays My love.. Har ka mance. Jiranka nake ka fito mu tafi Spa and fitness.. I thought kace zaka gym.”
Shiru yai kaman mai nazari sai Ya karisa saman drawer ya d’auki wayarsa had’ida jefata cikin aljihun wandon three quarter dake jikinsa.
Har ya soma takawa ya juyo ta dubeta “Don’t answer his calls again.” Ya fad’i cikeda gargad’i.
Saurin jinjina masa kai tai “I’m blocking his number right this instant.”
Baice da ita komai ba yasa kai ya shige ba wai dan ya aminta da labaran da ta basa ba sai don Ya k’asa tuna komai.
Bayansa tabi da kallo murmushin saman fuskarta ‘Bazaka tab’a sanin waye Shadow ba Haidar.. Shadow has been shadowing you for a long time now.. Maybe tun kafin na shigo rayuwarka. But one thing I’m sure of shine Shadow made a huge mistake da har ya bari na shiga rayuwarka. Because I’ll protect you from him. Kuma bazan tab’a bari ya cutar dakai ba for as long as we are together..’ Ta k’arashe zancen zucin nata tana take masa baya dan tuni Haidar ya fice.
Motsa jiki yake da iyaka kuzarinsa da k’arfin sa ko zai iya tuna wani abu amma ya kasa. Why couldn’t he remember a thing.? Meyasa yake ji kaman brain d’insa na barazanar tarwatsewa.? Meyasa yakeji kaman chest d’insa ya masa nauyi. Meyasa yakeji like he’s lost in his own world. Rintse idanunsa yai yana kuma tuk’a keken motsa jikin da iyaka k’arfin sa.
**
Abuja..
Suna fitowa Leenah ta mik’e a birkice tana duban fuskar k’awarta da ya koma jazir abinka da farar fata. Fuskar tayi rod’i rod’i duk tayi jazir kaman k’osan da ya sha wuta cikin mai.
“OMG.! Girl.. What happened to your face…?” Leenah tace tana zaro ido waje.
“Just shut up Leenah..! This is all your fault..” Anisa tace tana sakin huci. Lokaci guda tasa kai ta nufi mota.
Daidai lokacin Ummul ta fito fuskarta ta k’ara kyau sai wani shek’i na musamman da fuskar nata keyi. Sosai gyaran ya amsa fuskarta.
Leenah ta saki baki tana duban Ummulkhairi.
“But..But.. Wait.. How’s this possible..?” Leenah tace cikin rashin fahimta.
Murmushi Ummul ta sakar mata kafin tasa kai ta shige ta nufi mota.
Leenah tabi bayan k’awarta Anisa cikin sauri tana tambayarta me Ya faru.
Juyowa Anisa tai tana dubanta da toyayyan fuskarta “You know what Leenah, I don’t want to listen to you. Just get in the car and let’s get out of this place..!” Ta k’arashe tana furzar da huci had’ida rausayar da ido.
Saurin rik’ota tai ta dawo da ita baya “Hey hey easy.. Wai mai ya faru ne.. For as far as I know ba ma Ke na zuba cream din ba. How did it end up on your face..?”
Anisa ta rausayar da ido “Because She outsmarted you Leenah.. Isn’t it obvious..? You are so useless.!” Ta k’arashe cikin huci tana juya ido.
“Hey easy don’t take it out on me. She’s the culprit. She switched the bowls.” Cewar Leenah tana nuni da Ummul dake zaune cikin mota.
Anisa ta rausayar da ido “That’s because you are stupid. You know what Leenah, I feel like punching your ugly face.”
Leenah ta shafa fuskarta “Hey don’t be mean. I spent so much on this beauty..” Ta k’arashe tana Shafa fuskarta da murmushi.
Rausayar da ido Anisa tai tana sakin huci. Zata shige Leenah tai saurin kamo hannunta. “Girl, if she can do something terrible like this, with that innocent looking face. Then believe me she’s dangerous.. She’s a wolf in sheep’s clothing. You need to eliminate her out of the picture.. As soon.. As possible..!” Ta k’arashe tana firfito da ido waje.
Tururi kurum Anisa take “Believe me Leenah. I won’t play fairly this time around..She wants battle? then I’ll give her war..Just watch and be amazed.!” Ta k’arashe tana sakin huci.
Leenah ta girgiza kai “You need to change your ways Neesa. Ki fito mata a musulma. Make sure you win her trust first before you make your move.”
Anisa ta rausayar da ido “I don’t think I have that kind of patience. I can’t stand her one bit.”
“You have to Neesa. You must put up with her. That is idan har kina so ki kawar da ita cikin sauk’i.”
Anisa tai Shiru without saying a word.
Murmushi Leenah ma ta saki amma sai murmushin ya rikid’a Ya koma dariya dan sosai fuskar Aminiyar nata ya bata dariya yanda ya sauya halitta lokaci guda.
“What’s got you laughing..?” Anisa ta tambaya a hasale.
Leenah ta soma k’unshe baki tana nuni da fuskar Anisa “Seriously Girlfriend you look like a monster.” Ta dubi Ummul da ko kallon yanda suke batayi tace “Ita kuma makirar tayi kyau jibi yanda take glowing.. Awwn I’m jealous of her skin..” Ta k’arashe tana dafe fuska.
Tsawa Anisa ta darara mata tana fad’in ta shige mota su tafi ko ta tafi ta barta nan wajen.
“Oh hey. Easy girl, I’m just joking.. You are still more beautiful than her.” Leenah ta fad’i tana take ma k’awarta baya.
Haka suke tafe Mota Leenah na kuma tunzurata da surutanta har dai aka sauk’e Leenah a destination dinta shak’e da kayyayakinta da sukai shopping.
Mota ya rage saura Ummul da Anisa. Ba mai ce da kowa komai har suka iso gida.
Ummul ta dubi Anisa Tai mata godiya wann murmushin Wanda sam Anisa bata k’aunar gani saman fuskarta.
Suna shigowa cikin gidan suka tadda Mommy zaune da wasu mata masu sanye da rigar kampani na tailoring a first parlor.
Ma’aikatan gidan da kusan ko yaushe suke cikin shiga ta uniform suka soma amsan kayyakin hannunsu suna masu sannu da zuwa cikeda girmamawa had’ida ladabi.
Ita dai Ummul duk ba wai ta Saba da irin wad’ann abubuwan bane. Musamman idan taga manyan mutane suna girmamata suna gaisheta koda kuwa masu aiki ne. Sam batajin dadin irin abun. Sosai abun ya bata mamaki da safe kafin su fita yanda Anisa ta dinga masifa ma babban mata dake kitchen wai dan kawai bata kawo mata abinda ta buk’ata kan lokaci ba. Tana jin wacce ta amsa Kayan hannunta tana tambayarta “Ma’am, should I take these to your section..?” Kasancewar akasarin ma’aikatan gidan hiring d’insu akai daga registered company na masu aikace aikacen gida da Office ba hausawa bane ba sosai suke hausa ba.
Sai Ummul tai sakare tana dubanta. Ba wai dan bataji mai tace bane, kawai sabo ne da irin rayuwar da Sam batai ba. Rayuwar da gaba d’aya ya banbanta daga irin rayuwar da ta girma ciki tai wayo ciki.
Mommy ce ta bata amsa da fad’in ta kai mata su side dinta. Wato b’angaren Haidar.
Maid din ta amsa da “Yes Ma.” Cikeda risinawa.
Mommy ta k’araso ga Ummul wacce tuni ta risina tana gaisheta.
Bata amsa gaisuwar ba sai kamo hannunta da Tai tana fad’in suje ga masu d’inki zasu gwadata su d’auki measurement dinta. zasu d’inka mata atamfofi da laces daidai size d’inta.
Anisa ta saki baki tana kallon ikon Allah musamman da ta ga babban tailoring company da Mommy ta kira Wanda a garin ma ba ma kowa suke d’inki ba sai ka cika elite. Ko ita kanta Anisa basu tab’a mata d’inki ba sai gashi wai zasuyi ma wann kucakar. Zuciyar Anisa ta kuma tunzura. Tsanar Ummul ya kuma cika mata zuciya. Ko ta kanta fah Mommy bata bi ba balle taga abinda ya samu fuskarta. Cikin k’unan rai ta nufi d’aki tana tuanin sabon hanyar da zata bi ta b’ullo ma Ummul dan bata tunanin zata iya hak’uri da Ummul d’in kaman yanda Leenah ta bata shawari.
**
Kano…
Da kyar Mama ta amince ta fito wajen ganawa da mutane yanda Umma ke jiranta a nan police station da akai detaining dinta.
Umma ta zuba tagumi tana duban Mama yanda ta jeme ta rame duk tsawo da jiki irin na Tani duk ta lalace cikin k’ank’anin lokaci ta zama abun tausayi.
Banda Uwar harara Mama bata aika mata komai.
“Kinzo ne kimin dariya Suwaiba.? Kinzo ne dan kiji dadin ganina a k’ask’ance..?” Muryar Mama ya soma rawa “Ki amsa min Suwaiba. Kinzo ne dan ki min dariyar abubuwan dake faruwa dani..? Ina nufin ‘Ya’yana Sun jirge gida. Badia miji ya gudu Ya barta ita kuma Azeema miji ya koreta.. Ni kuma gani a nan cikin k’ask’anci da tozarci.. A yayinda ke Allah ya cika miki burinki. Ummul d’inki tayi aure.. Aure na gani a fad’a irin Wanda nawa ‘ya’yan basu samu ba.. Mutanen unguwa sun bar nunaki da baki sun koma nuna ni nida nawa ‘ya’yan.. Mijinmu kuma yanzu na k’ark’ashin kulawarki.. Ya zama naki ke kad’ai.. Haka ne Suwaiba..?” Ta k’arashe kuka na b’alle mata yayinda Umma ma kukan take. Cikin zuciyarta cewa take Allah sarki Yaya baki san tashin hankalin da kike ciki mai sauk’i ne gaban Wanda nake ciki. Baki san wani irin aure Ummul Tai ba. Baki san cewa Aure ne mai k’ayyadadden wa’adi ba. Baki san Aure ne da aka k’ullasa bisa yarjejeniya na tsawon watanni uku.. Aure mai gib’i auren da zan jima ina d’an dana sanin yi ma Ummul irin wann auren Har tsawon rayuwata. Sann Mijinmu banida ikon taka yanda yake.
Muryar Tani ya kuma katseta cikin karaji sanda ta soma janyo Umma tana fad’in “Tashi ki tafi Suwaiba. Ki tashi nace ki tafi kuma kar ki sake takowa yanda nake.!”
Kuka Umma take tana girgiza kai “A’a Yaya.. Dan Allah ki saurareni.. Wllhi ko d’aya banzo nan dan abubuwan da kika zayyano ba.. Yaya ki saurareni..” Sai Umma ta rungume Tani tana kuka.. Su duka biyun kuka suke Wanda yafi kama da kukan nadaman rayuwa.
Mama ta fincike jikinta daga rik’on da Umma tai mata. Zata sa kai ta shige Umma ta kuma rik’o hannunta “Yaya dan Allah ki saurareni.. A halin yanzu bamuda kowa sai mu biyun..”
Mama Tani ta goge hawaye da bakin zaninta Wanda yai duk’un duk’un “Yayane Suwaiba..? Ki sanar Dani yayane..?”
Umma ta goge hawayenta da bakin mayafi “Yaya yanzu ba lokaci bane da zamu rik’e juna abokan gaba. Lokaci ne da zamu fahimci dukkanmu masu kuskure ne.. Kuma Allah yana sonmu da ya nuna mana kura kurenmu tun a nan gidan duniya.. Saura ya rage namu mu d’auki darasi ko mu bijire.”
Jikin Tani ya kuma yin sanyi wasu hawayen na zubo mata yayinda Umma taci gaba “Yaya babban abinda ya jefa mu cikin halinda muka tsinci kanmu shine son kanmu, rashin tawakkali da yin abu dan mu burge mutane Wanda Har yasa mun mance su waye mu. Mun mance auren mu, mun mance ‘ya’yanmu da Allah ya dank’a mana amanarsu. Mun mance mijinmu da yakeda girman hakki akanmu.. Sabida son zuciya irin namu.. Mun mance mu masu kiwo ne kuma za’a tambayemu bisa abinda aka bamu kiwo.. Yaya duk mun mance wad’ann mun saka son zuciya a farko.. Wanda shi ya kai mu ga halinda muka tsinci kawunanmu.” Ta kuma jinjina kai tana hawaye “Watak’ila Ummul tayi aure.. Amma ba irin auren da naci mata buri ba.. Dije ta rabani da Khulsum kaman yanda ta rabani da mijinmu.. Nida ke bamuda wani maraba Yaya. Yanda kike rufe a nan babu walwala nima a b’angare na haka take.. Kullum ina kulle ne cikin d’aki Babu walwala.” Ta kuma share hawayenta yayinda Tani ta katseta “Wani irin aure ne Ummul Tai Wanda baki ci mata buri ba Suwiaba.?”
Tambayar da ya haifar ma Umma fad’uwan gaba. Koda Ummul AUREN WATA UKU Tai bazata so ta sanar da Tani ga irin auren ba. Hasalima bazata iya ba. Batada wann k’warin gwiwar.
Girgiza mata kai tai “Ki yarda dani Yaya na tapka babban kuskure..” Tai maganar cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka.
Mama ta jinjina kai “Na yarda da duka abubuwan da kika fad’a Suwaiba.. Mun tapka kuskure.. Kuma idan bamu had’e kawunanmu yanzu ba bazamu tab’a k’wato mijinmu daga hannun Dije ba. Tazo Har nan ta min d’iban albarka ta kuma jaddada min tinda naci amanar d’anuwanta dake kwance nida fita a gidan yari sai Randa jakin Baba yayi k’aho. Zata tabbata ban samu wani k’ofa da zan tsira ba. Sann yarana sun guje ni. Salima ce kawai ke zuwa nan ta dubani. Amma Azeema da Badia Wanda nake gark’ame nan sabida su sun wofantar dani Suwaiba..” Ta kamo hannayen Umma “Suwaiba dan girman Allah ki taimaka min kafin a tafi Kotu. Sunce cikin satin nan za’a shiga Kotu da mutumin k’auye mai kudi. Dan girman Allah Suwaiba ki taimaka ki nemo kud’d’en nan a fitar dani.. Naga Sirakan Ummul masu hannu da shuni ne. Ki taimaka min Suwiaba ko wajensu kije ki nemo kud’ad’en nan ki fitar Dani a nan..” Ta k’arshe tana tsare Umma da ido. Zuciyarta na tabbatar mata hanyar da zata bi kenan ta samu ta fita daga wann tuggun. Ta nuna ma Suwaiba nadamarta a fili Har dai Suwaiban Tai mata hanyar fita..
Dum!! Haka k’irjin Umma ya buga dan ita kanta bata isa tace ga kalan sirakan Ummul ba. Uwa uba rabuwar da sukai da Asshe Wanda Asshe tai mata iyaka da gidanta.
Tani ta tsare Umma da ido. Cikin zuciyarta take ayyana tinda na sauko da kaina Suwaiba dole kimin abinda nake so. Ta haka ne kawai zan samu na fito har na fahimci mai kike b’oye min gameda auren Ummul.
“Ke nake sauraro Suwaiba, zaki min wann alfarmar.?” Mama tace tana tsareta da ido.
Zuciyar Umma ya kuma tsinkewa. Ta d’ago tana duban Mama cikin sanyin jiki…
SameenaAleeyou📚
*AUREN WATA UKU..!*
*27*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
Umma ta girgiza kai a hankali “Kiyi hak’uri Yaya.. Bazan iya Miki alk’awarin komai ba a halin yanzu.” Tai maganar ba tareda ta iya duban fuskar Mama Tani ba.
A dak’ile Mama ke dubanta “Suwaiba.. Kina nufin bazaki taimake ni ba..? Kenan kema kin zab’i a tura ni kurkuku kaman Dije.?”
Umma tai saurin d’ago kai tana girgizawa alamun a’a.
Tani ta gyara zama “Toh idan ba haka ba yaya ne.? Bakida wani maraba da Dije Suwaiba.. Banyi zaton haka daga wajenki ba Suwaiba..” Sai ta fara hawaye “Bayan ke banida kowa Suwaiba.. ‘Ya’ya na Sun guje ni.. Mijina na kwance jinya ta cinyesa.. Ke da nake zaton zamu taru mu rufa asirin juna kema kin juya mun baya Suwaiba.?” Sai ta fashe da kuka tana fad’in bata zaci haka daga Umma ba.
Lokaci guda Mama ta mik’e tana huci “Tinda haka kika ce Suwaiba.. Shikenan kije abinki.. Kije kici arzikin sirakanki ke kad’ai. Ni kuma in sha Allahu babu ni babu Ke Suwaiba. Kar ki sake tako inda nake idan har ba taimako na zakiyi ba.” Tasa kai zata shige Umma tai saurin mik’ewa ta tareta “A’a Yaya. Dan Allah kar kice haka.. Ni ahalin yanzu banida kowa nima sai ke. Bamuda kowa sai mu biyun.. Amma..”
Katseta Tani tai “Amma me Suwaiba.?” Tai maganar tana tsare Umma da ido.
Gaba d’aya Umma ta daburce bata San mai zata sanar da Mama Tani ba. Bata san ta yanda za’ayi ta sanar da ita cewa itama ta riga ta k’are mata ba. Tai saurin jinjina kai “Toh. Toh.. Yaya.. In sha Allah zan nemo hanyar da zaki fita..”
Mama ta jinjina kai “Yanzu naji batu Suwaiba. Kar ki mance fitowa zanyi muyi yak’in k’wato mijinmu daga hannun azzalumar ‘yar uwarsa wacce babu komai cikin zuciyarta face burin fansa dan nayi imani ba tsakani da Allah Dije ke ma Isubu jinya ba. Shi kansa yasan halin Dije Shiyasa tun yanada lafiya ya mata iyaka da yanda yake. Ko dan wann Suwaiba bazamu bari Dije ta rab’esa ba. Ki nemo kud’ad’en bak’auye a biyasa na fito mu k’wato mijinmu uban ‘ya’yanmu. Ta haka ne kawai ahalinmu zai kuma samun daidaito. Kin fahimta.”
Umma tai Shiru kaman mai nazari sai kuma ta shiga jinjina kai “Na fahimta Yaya. Nima zanso muyi jinyar mijinmu mu samu ladansa. Kuma kuskure ne mun riga Munyi amma munyi nadama. Kuma Allah mai afuwa ne mai yawan gafara.”
“Yauwa dai Suwaiba ko ke fah. Nasan kinada fahimta Shiyasa munafukai basu tab’a samun nasaran shiga tsakaninmu ba. Ni ‘yaruwa na d’auke ki Suwaiba ba kishiya ba. Kuma ‘yan sa’insa da sab’ani da muke samu a baya zama ne Ya kawo haka. Dama shi kansa rayuwar zo mu zauna ne zo mu sab’a. Harshe da hakori ma suna samun sab’ani ballantana mu ‘yan adam.”
Umma ta jinjina kai “Haka ne Yaya. Zanyi iyaka kokari na in sha Allahu. Allah ya mana jagora.”
Mama ta murmusa had’ida amsawa da “Yauwa yanzu naji batu Suwaiba. Ina nan ina saka tsammani. Na d’aura duka yardana akanki Suwaiba.” Ta k’arashe cikin yanayi na tausayawa.
A hankali Umma ta jinjina kai duk jikinta a mace haka sukai Sallama da Tani. Tana ficewa Tani ta kece da dariya. A fili take furta “Saidai ba Suwaiba matar Malam Isubu ba. Muje zuwa, da kanki zaki fiddani ni kuma na fidda ‘yar naki a gidan auren nata. Tinda ‘ya’yana basu zauna d’akin miji ba naki ‘yarma bazata zauna ba. Abun yazo gidan sauki dan da alama akwai abinda kike b’oyewa gameda auren. Bazan yi k’asa a gwiwa ba har sai na shak’a iskar ‘yanci dan na cimma burina.” Ta kuma murmusawa daidai sanda wata ‘yar sanda tazo maidata cell dinta.
Umma tana tafe tana lazimi da tinanin ta yanda zata b’ullo ma al’amarin Tani. Zatai iyaka yinta dan ta taimaki Tani tinda ta tabbata idan yau mijinta ya farka Ya gansu sun had’e kawunansu kuma sunyi nadaman duk abubuwan da suka aikata a baya zaifi kowa farin ciki kuma Watak’ila fushin da yake dasu ya gushe. Watak’ila hakan ya zama silan yafe masu duk wasu kurakuren da sukai sanda yake kwance. Toh amma ina ta nufa..? Ina zataje .? Wajen waye zata je ta samo kud’ad’en da za’a fidda Tani.? Asshe kawai ta fad’o ranta. Dan idan ba Asshen ba bata kuma san wajen waye zataje ba. Toh amma sanin irin rabuwar da sukai da Asshe sai ya kuma haifar mata da sanyin jiki. Asshe ta bada umarni ma masu tsaron gidanta cewa ko mai kamanninta suka gani kar su bari ta shiga. Uwa uba had’e kan da Dije da Asshen sukai mata kafin a tafi da Ummul. Ta tabbata idan Har Dije ta k’ulla aminta da Asshe zuwa wajen Asshe had’ari ne. Dan idan har Dije ta fahimci Matan Isubu Sun had’e kai. Wato ita Suwaibar da Tani wani sabon wuta zata kunna masu. Snn abinda take k’ok’arin b’oye ma Tani gameda auren Ummul kuma shikenan ya tashi daga sirri. Dan tayi imani Dije bazata so taga wann had’in kan ba Wanda yake nufin rugujewar shirin duk wani fansarta akansu. Dole tai taka tsantsan. Dole tabi komai a tsanake idan har tana so ta taimaki abokiyar zamanta Tani ta fita daga kurkuku. Da wann tunanin ta sallami mai adaidaita ta shigo gida. Saidai tana shigowa abinda Tai karo dashi ne Ya mugun bata mamaki. Dije ta gani tsaye tsakar gidan ga kayan abinci da kwanaki Suwaibar ta kawo lokacin sunayi da Asshe lokacin yak’in auren Ummul jirge gaban Dije ta kirawo yara tana fad’in maza su fidda mata kayayyakin su kai mata cikin adaidaita dake jiranta k’ofar gidan.
Umma ta saki baki tana kallon ikon Allah “Dije.. Lafiya mai nake gani haka..? Ina zaki kai mana kayan abincin.?”
Kallonta Inna Dije Tai daga sama zuwa k’asa “Makauniya ce ke.? Bayan shahshanci kuma idonki Ya rufe ne Suwaiba.? Tafiya dasu zanyi. Tinda na tabbata da kud’ad’en da kika saida d’iyar D’anuwana kika sayi kayan abincin nan. Ko ma ince su suka baki. Kaman yanda kika sani da zaran an sallamesa daga asibiti ko gidan nan bazai taka ba balle yayi karo da wani tashin hankalin da tsautsayi. Dutse zan wuce dashi ya samu hutu da jinya a can. Kayan abinci kuma zamu buk’ata.” Ta k’arashe tana d’aura ma yaro guda kwalin taliya akai.
Umma ta girgiza kai “Amma Dije mai zamuci.? Kar ki mance ba ni kad’ai ce a gidan nan ba. Akwai Badi’a sann akwai Azeema. Idan kika kwashe komai mai zaki barmu dashi.?”
Dariya Inna Dije tai harda shewa kafin tace “Lallai Suwaiba. Yau kece mai fafutakan abinda yaran Tani zasu ci.? Saikace ba kece Tani ke hana naki yaran abincin da ubansu Ya kawo ba. A cewarta bazata girka ma k’artan banza Wanda suka ki aure abinci ba.? Ikon Allah sai gashi yau ke Suwaiba kece kika nemo abinci kika ba ma yaran Tani da suka k’i zaman aure harma girka masu kike. Yaran da ko ganin mutuncinki basayi. Lallai na yarda kin tabbata shashasha Suwaiba.”
Umma ta girgiza kai “Dije rayuwar duka nawa take. Ciyar da rai lada ne dashi balle ‘ya’yan mijina Wanda jarabawar rayuwa ya fad’a kansu suka baro gidan mazajensu. Babu mahaifinsu a gidan Babu mahaifiyarsu. Gatansu Allah sai ni kad’ai da na rage masu cikin gidan kuma in sha Allahu bazan wofantar dasu ba. Idan Allah ya bani dama da iko na zama mahaifiya a garesu zan zama. Idan ban samu daman gyara kura kuran da nai a baya kan nawa ‘ya’yan Ummulkhairi da UmmuKhulsum ba zan kwatanta gyara akan Azeema da Badia cikin yardar Ubangiji Dije. Ki kirani da duk sunan da kikaga dama amma in sha Allahu ni Suwaiba bazan sake maimaita kura kuren da nai a baya ba.”
Inna Dije ta murmusa ta matso kusan Umma sosai “Idan dai Tani da iyalanta ne gaki gasu. Sai ki fita ki nemo ki dafa ki basu. Idan ma aikatau zakiyi ki nemo masu wann ke ta shafa. Amma kinga wann abincin Ya haramceku daga ke Har su.” Ta k’arashe tana sunkuman kwalin taliya. Kaman daga sama taga Azeema da Badia kanta ko wacce tana sakin huci. Shigowarsu gidan kenan.
Azeema ta nuna mata kwalin taliyar “Ajiye.” Ta fad’i cikeda gargadi.
Inna Dije ta dubeta da mamaki “Ke Azeema ni zaki ma rashin kunya.”
“Zaki ajiye ne ko zaki jira na tayaki ajewa.” Cewar Badia tana shan d’amara.
Inna Dije ta saki baki da mamaki “Ke Badi’a.. Ni zaku ma d’iban albarka ina kanwar Ubanku.?”
“Allah yasa k’anwar uban kikace ba uban ba. Rashin kunya kuma ai mai sauk’i ne wann. Billahillazi akan abincin nan sai mu tara Miki na jaki a nan mu bama idon mak’ota abinci dan kinsan dai wann ba bak’on abu bane a wann k’ofar.” Azeema tace tana kuma shan d’amara.
Har lokacin mamaki take baki bud’e “Ni Dije zaku daka ke Azeema.! Eh Lallai! Ai idan bakuyi ba baku cika jinin Tani ba. Ba laifinku bane Kunsha a nono.”
“Wllhi Inna Dije zakici bugu a banza dan kin fad’a da bakinki nida kunya dama munyi hannun riga. Ke d’in banza tinda na tafi na tari fad’a da budurwar Habibu mai tak’ama da uniform da bakin bindiga banga uban da bazan taresa ba. Ke mu fah fad’a ma rancenta muke ko ya kikace Badia.?”
Badia ta dubi Inna Dije da bakinta ya gaza rufuwa sabida mamaki “Inna billahillazi idan baki kira yaran nan sun maido da abincin da suka fitar ba wllhi Kinji na ranste Miki kaf takaicin duniya da Tasi’u Ya juye mun zan juyesu akanki. Dan wllhi yanzu a haka hannayena k’aik’ayi suke.!”
Inna Dije ta jinjina kai “Eh na yarda dole ku kasa zaman gidan aure dan babu Wanda zai zauna da shed’anu Irinku. Me za’a tsammata daga wajen yaran da uwarsu ke tsare a gidan gyaran hali.”
“Saki nawa aka Miki.? Yaji sau nawa kikayi da wayonmu kafin ki zauna gidan auren.?da wayonmu muna rakaki kome. Naga gado mukai wajenki” Badia tace tana fincikan kwalin taliya dake hannun Inna Dije.
Inna Dije ta jinjina kai tana duban Umma da ta zuba ma sarautar Allah ido. K’wafa tai tasa kai zata wuce Badia da Azeema suka shiga janyota suka nufo waje suna fad’in saita maido kayan abincin da ta sace ta saka a keke napep.
Haka Azeema da Badia suka tirsasa ma Inna Dije ta dawo masu da kayan abinci.
Suka k’araso da kayan suka jirge gaban Umma. Har lokacin ko waccensu da d’amara a kunkuminta. Azeema taci gaba da nuna ma Umma kayan abincin “Kema kiji da kyau bamu k’wata abincin nan sabida Ke ba sai don yunwar cikinmu. Kici gaba da girkawa kina bamu.”
Umma bata ce komai ba har suka gama maganganun da zasuyi. Dan tun bayan abubuwan dake faruwa kaman abun nasu k’aruwa yai. Cikin Zuciyarta tabi su da addu’ar shiriya. Ta d’au alwashin zatai hak’uri dasu kuma bazata fasa masu nasiha ba har lokacin da abubuwa zasu daidaita da taimakon Allah.
**
Abuja…
Anisa taci gaba da juya kwalaben turare da Mommy ta bata tace ta kaisu ma Ummul.
Waya ta d’aga ta kira Amminta. Asshe na ganin wayar Anisa Tai saurin d’agawa “Ina sauraronki Anisa meke faruwa.? Shin Haidar yazo gidan.?”
Anisa ta rausayar da ido “No Ammi he hasn’t shown up until now. And I don’t think zaizo gidan anytime soon.”
Asshe ta jinina kai “Toh ina sauraronki, wani abun ne Ya faru.?”
Anisa taci gaba da juya kwalban turaren “Ammi Kince duk abinda ake ciki na dinga sanar dake.”
Asshe tace “Eh K’warai. Remember you are my eyes there.”
Anisa taci gaba “Ammi Mommy ta bani wasu kwalaben turare guda biyu.. Kaman turaren black khumra amma banaji suna k’amshin khumra.. Tace na bama Ummulkhair.. Lallai Lallai na bata na kuma sanar da ita had’in khumra ne na musamman Mommyn Tai mata kyautar su.”
Ai Asshe bata San sanda ta mik’e daga zaunen da take ba. Ta soma tuna lokacin zuwansu wajen boka sanda za’a masu aiki akan makarin asirin Haidar. Boka Ya basu wani turare mai launin bak’i ya kuma ce lallai lallai duk matar da za’a karya asirin jikin Haidar da ita sai ta zamto tana amfani da wann turaren domin kuwa turaren tamkar shine kuran k’arfe da zai janyosa zuwa gareta Har dai sihirin Ya lalace. Idan kuwa haka ne bazata bari Ummulkhairi Tai amfani da turaren ba tinda ita d’in barazana ce ga rayuwarsa.
Baki na rawa Asshe tace “Turaren humra.? Kar ki bata su Anisa..!”
Anisa tace “Meyasa Ammi.?”
“Na fad’a Miki no asking questions Anisa. Just do as I say. Ki zubar ki zuba turaren Khumra cikin kwalban ki bata. But koda wasa kar ki bata wann turaren idan har kina son ki mallaki Haidar.”
Anisa ta kuma juya ido “But Ammi what if Mommy ta ba ma Bagidajiyar nan turaren da zata mallaki Haidar ne since she wants her for her son. What if I use it instead.. Kinga sai ya soni bai sota ba..”
K’iris Ya rage Asshe bata kurma kururuwa cikin waya ba jin nata ‘yar zata zama makarin asiri “Ke Anisa. Zan tsine miki albarka idan kikai amfani da turaren nan.. Wai ke wace irin shashasha ce. Nace duk abinda nace kiyi kawai kiyi zan miki bayanin komai daga baya.. Just dispose it and replace with natural Khumra. Kin fahimceni.?” Ta k’arashe cikeda gargadi.
Anisa ta furzar da huci dan ta gaji da wann mysteries d’in “Ok fine Ammi. As you wish.” Ta k’arshe tana katse kiran.
Taci gaba da juya turaren kafin ta nufi d’aki ta nemo wani kwalban ta juye turaren ciki ta wanke kwalban kafin tai yanda Amminta tace. Can k’asan kayanta ta b’oye turaren da Mommy ta bata Wanda zuciyarta ke raya mata turaren da zaisa Haidar yaso Ummul Mommy ta bayar a kai ma Ummul d’in tinda tana mata makahon so. Idan kuwa Har hunch dinta ya zama gaskiya ita ce wacce zatai amfani da wann turaren dan Haidar ya so ta.
**
Gaba d’aya Ji take bata kyauta ba tin bayan abinda Ya faru tsakaninsu da Anisa. Musamman da taga yanda fuskar Anisar Ya b’aci. Ita a halin yanzu ba abokin fad’a take nema ba. Hasalima Tun farko batada abokin fad’a dukda kuwa masu nemanta da fad’an sunada yawa kama daga cikin gidansu har izuwa mutanen unguwa. Khulsum ce ta fad’o ranta wacce a ko yaushe idan an taresu da fad’a ita ke d’aukan fad’an. Tayi nata Tai na Ummul d’in. Ta murmusa a hankali. A fili ta furta “Nayi kewar ki fitananniyar ‘Yaruwarta.” Ta share hawayen da Ya gangaro mata. tunanin mahaifinta ne Ya fad’o mata sai ta tuna alk’awarin Inna Dije gareta a lokacin da suka kawota cewa kar ta saka damuwan mahaifinta a ranta domin kuwa zata kula dashi cikin yardar Ubangiji. Umma ta fad’o ranta. Sai ta lumshe ido a hankali tanajin kuka na zuwa mata. Kalaman Umma na k’arshe a gareta su take tunawa cewa kar ta nemeta kar ta nemi kowa cikin danginta Har na tsawon watanni uku koda kuwa a wayan salula ne. Meyasa Umma zata yanke mata hukunci mai tsauri irin wann. Shin ko haka take a al’adarsu idan anyi aure sai bayan watanni uku kai magana da ahalinka.? Bata jin hakan ne. Ta lumshe idonta wasu hawayen suka kuma gangaro mata.
Tana a haka taji ana knocking a b’angaren ta. Ta mik’e Tai k’ok’arin kintsa kanta kafin ta nufi k’ofa.
Ga mamakinta Anisa ta gani tsaye tana sakin huci.
Ummul ta sakar mata sassanyar murmushi had’ida bata hanya “Bismillah shigo.”
Anisa ta watsa mata harara kafin tasa kai ta shigo. Sai faman yatsina yank’wanannen fuskarta da bai Ida warkewa ba take.
“Ba zama nazo yi ba. Ban kuma zo dan na rama abinda kika min ba dan naga kin sha jinin jikinki. Sak’o Mommy ta bayar a kawo miki.” Tai maganar tana mai aje turaren saman centre table.
Ummul ta katseta “Ni ban miki komai ba Anisa. Ke shaida ce keda k’awarki ku kuka shirya abunku.”
Ganin Anisar ta tsareta da ido Ya sanyata samun k’warin gwiwar ci gaba “Ni bana nemanki da fad’a. Kuma ki yarda dani har cikin zuciyata banji dad’in abinda Ya sameki ba.”
“Oh please shut up! Spare me your false sympathy.” Taci gaba da takowa gaban Ummul. Tana huci take nuna fuskarta. Muryarta ya soma rawa alamun kuka “Just look at my face.. Look at what you did to me. Kalli yanda fuskata ta lalace.. This is what you want right.? Farin ciki kike ko..? Na sani tun farkon zuwanki gidan nan baki sona.. Amma ban tab’a tunanin zaki min abinda kika min ba. Leenah ita ce ta zuba miki cream din ba ni ba. Meyasa kika zab’i b’ata nawa fuskar… It was Leenah’s plan and not mine. Bansan ta shirya Miki haka ba amma ki zab’i cutar dani. Look duba kiga abinda kika min.” Ta k’arashe cikin kuka.
Jikin Ummulkhairi yai sanyi. Ta soma girgiza kai “Anisa ki yarda Dani banji dad’in abinda ya samu fuskarki ba. Amma ki sani shi rayuwa abinda ka shuka fah shi ke dawo maka. Idan khairan khairan idan sharri sharri. Ya kamata ki d’auki darasi cikin abinda Ya faru.”
“You are not in a position to dictate to me what I should do with my life. Idan kuma shawari ne ban nema ba. We are not even friends to begin with.” Ta k’arashe tana juya ido.
Ummul ta kuma girgiza kai “Ni bance mu zama k’awaye ba. Amma ki sani bana neman abokin fad’a.”
Anisa ta kafeta da ido sai kuma ta marairaice fuska ta k’arasa saman kujera ta zauna tana Shafa fuskarta. Ta d’ago tana duban Ummul da idonta masu zuban ruwa “You are right you know. Duk abinda ka shuka a duniyar nan shi yake dawo maka. At first I hate you Ummul.. Bazan b’oye Miki ba. Ina kishinki musamman ganin yanda daga zuwanki gidan nan hankalin Mommy da soyayyarta gaba d’aya ya koma kanki.” Ta mik’e Tai tsaye gaban Ummul da idonta masu zuban ruwa “I’m not a bad person Ummulkhair. I’m so sorry for everything I did to you.. I don’t want us to fight anymore.. Ko bamu zama kawaye ba I believe we can get along and live in peace..” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta. Ta mik’a ma Ummul d’in hannu murmushi saman fuskarta “Mu mance komai mu zauna lafiya.”
Sosai Ummul tasha mamaki da sabon sauyin Anisar. Amma sai ta murmusa ta mik’a mata hannu sukai musabaha. Anisa Tai saurin hugging d’inta tana fad’in fad’a tsakaninsu Ya k’are tayi alkawari.
Ta dubi saman dining table yanda abinci suke nan a jere alamun tinda aka kawo ma Ummul d’in bata ko tab’a ba.
Ta murmusa ta dubi Ummul “Don’t tell me you still haven’t eaten. Koda yake zaman kad’aici Babu dad’i. Come zo muje. Barin tayaki cin abincin.”
Ta janyo hannun Ummul suka nufi dining table. Anisa tace da Ummul ta zauna ita zatai serving d’insu. Ta zuba abinci ta shirya table.
Nan suka zauna suna facing juna itada Ummul d’in. Ganin Ummul ta matsar da table knife gefe yasa Anisa murmusawa tace “Ya kamata ki koyi cin abinci to our level. You must keep your table manners. And that includes the use of utensils. Kar ki mance ke sirkar gidan nan ce a yanzu. Hakan na nufin, your social status has changed. You should learn how to mingle with upper class people. Mijinki Haidar mutum ne da ya girma cikin wayayyu sann yake hulda da wayayyun mutane, so you must adopt our lifestyle.” Anisa ta k’arashe tana gyara zamanta ta d’aura napkin saman laps d’inta. Sai faman kwarkwasa take.
Ta dubi Ummul tace tai irin zaman da Tai.
Murmushi Ummul Tai had’ida yin yanda Anisa tai.
Anisa tace “Good. Haka wayayyun mata ke zama bisa table especially in public. Yanzu ki d’auki fork and knife muga.”
Ummul ta kuma murmusawa dan harga Allah dariya Anisa ke bata. Nan tai yanda Anisar tace. Anisa ta girgiza kai “No, fork should be in your left and knife in your right. Like this.” Ta k’arashe tana nuna mata.
Murmushi Ummul ta kuma yi. Sai ta girgiza kai wann karon “ Amma addininmu harma da al’adarmu basu koyar damu cin abinci da hannun hagu ba. Shed’an shi yake cin abinci da hannun hagu.”
Anisa ta kauda fuskarta gefe tana juya ido. She had no other option than to put up da wann Bagidajiyar.
Sai ta juyo ta murmusa “Of course you are right. Kinyi gaskiya. Na gode da kika tunasar dani.” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta. A haka sukaci abinci Har Ummul Tai mata rakiya sanda zata tafi.
Sai mamakin canzawar Anisar Ummul d’in take. Amma cikin ranta taji dad’i da suka shirya da Anisar dan harga Allah bata neman abokin fad’a.
Anisa tana shigowa ta tadda Mommy zaune a parlor alamun tana jiran shigowarta.
“Mai ya tsaidake can.? Shin kin bata turaren da na baki ki bata ko kin tsaya shashancinki ne.” Mommy ta tambaya tana duban Anisar .
Murmushi Anisa tai “Na bata Mommy. Tace ta gode sosai. Taji dadin kyautar dan tin kafin na bar wajen ta shafa.” Annurin fuskar Mommy ya k’aru jin tayi amfani da turaren. Anisa taci gaba “Na tsaya na tayata cin abinci ne Mommy. Sai kuma na mata hira..” Ta k’araso ta zauna kafin taci gaba “Da alama kad’aici na damunta. Dan ko abinci bata wani iya ci. Kar kiga yanda taci abinci sosai da muke tare..” Ta kuma muskutawa “Em Mommy nace why not gobe Ummul ta shigo muci abinci gaba d’aya tare. Zata d’an rage kewa kuma zata k’ara samun daman sakewa damu tinda har yau Haidar baizo ba..”
Mommy ta murmusa “Da alama ku biyun Kun fara sabo sosai. Sai ki samu ma’aikatan kitchen ku shirya komai.”
Anisa ta murmusa “Okay Mommy..” Ta mik’e tana murmushi. Har ta soma tafiya ta juyo “Em.. Mommy nace, can I invite my friend over..?” Sanin ba ko wani shirgi Hajiya Kwaise ke bari a kawo mata cikin gida ba Shiyasa ma ta tambaya.
Mommy ta jinjina kai “Of course you can..” Tai maganar tana murmushi zuciyarta fari sol tinda Anisa ta sanar da ita Ummul tayi amfani da turaren da ta bata. burinta Ya kusa cika. Haidar d’inta zai dawo gareta.
**
Saida Anisa tai shirin kwanciya kafin ta d’aga waya ta kira Leenah. Tana tsaye gaban mirror tana cleansing soyayyan fuskarta da auduga taci gaba “I told you Leenah. Yarinyar nan sai tayi nadaman soyan fuska da tai. Zamanta a gidan nan yazo k’arshe. Kedai kizo da wuri ki sha kallo. Kar ki damu na karba Miki katin gayyata daga wajen Hajiya Kwaise Maitama dan kinsan da k’a’ida ake shigar mata gida. Matsalar kawai I need someone who can help me to carry out my plan .”
Leenah ta murmusa “Girl I’ve got your back. Just say the word kiga aiki da cikawa.”
“Oh shut up Leenah! As if your tiny brain is capable of helping me out.. last time I checked stupidity dinki ne yasa fuskata ta soye.”
Leenah ta murmusa “Haba Neesa trust me we re not going to repeat the same mistake.. You need me. After all, I’m the only one you can count on.”
Shiru Anisa tai “Fine. But wait , if you screw up my plan Leenah. I swear I’m going to kill you myself.”
Leenah ta murmusa “I’m on it girl. Kar ki damu zamu shirya komai ta yanda yarinyar zata bar gidan a gobe. I give you my word.”
Jinjina kai Anisa take tana sakin murmushi lokaci guda tana duban fuskarta a mirror. A fili take furta “Tomorrow I am going to get rid of my problem. Goodbye to you. Ummul..!” Ta k’arashe tana mai fashewa da dariya had’ida duban kanta cikin mirror.
**
Bayan ta Ida shirin baccinta alwalwa ta d’auro ta soma jero nafilfili tana kai kokenta ga Rabbil Izza. Kama daga kan sabon rayuwar da ta tsinci kanta ciki zuwa ahalinta da ta baro Har dai izuwa kan wann k’addararren aure da Ubangijinta Ya jarabceta dashi. Auren da batada tabbaci akan makomarsa auren da har kawo wann rana bata san kalan mijin ba bata kuma da tabbacin mijin Ya san da ita. Dan dik kyautatawa da d’imbin alherin mahaifiyarsa gareta bata tab’a jin a ranta ta samu sukuni cikin fargaban abinda ka iya zuwa yazo cikin auren. Addu’a ta dingayi Allah ya shiga al’amarinta. Idan har akwai alheri a cikin auren. Idan har zamanta alheri ne a gidan Allah Ya kawo mata komai cikin sauk’i. Haka zalika idan Babu wani alheri Allah Ya sauk’ak’a mata ya kawo hanyar da zata bar gidan cikin sauk’i. Ta jima sosai tana kai kokenta wajen Ubangijin da Babu abinda yafi k’arfin buwayarsa. A nan kan sallayarta bacci yai gaba da ita.
**
Cuba..
Bacci yake yana jin Kansa na juya masa cikin baccin. Nan kuma ya soma mafarki da mahaifiyarsa. Mommy ya gani durk’ushe gabansa tana kuka hannunta rik’eda farin takarda. Tana fad’in mahaifinsa yayi canceling project d’insa. Saurin amsar takardan yai daga hannunta saidai yana ware takardan yaga sab’anin abinda Mommy tace. Domin kuwa takardan sakin mahaifiyarsa ya gani wai Daddy ya saki Mommy. Juyowa yai bayansa yana huci kaman zai shak’e Daddy yana fad’in maiyasa zai saki mahaifiyarsa. Daddy bai basa amsa ba saima nuni da yai masa da bayan wata mace tana tafe tana jan akwatinta. Jikin Haidar yai sanyi sanda Daddy ke fad’in ‘Mahaifiyarka ita ta saka nata Auren cikin had’ari dan wanzuwar AUREN WATA UKU. Ka tuhumi kanka Aliyu.!’
Daga haka ya farka daga baccin duk ya had’a zufa. Nan yaga yamma ne sosai a agogon Cuba. Around karfe shida na yamma. Ya shafi fuskarsa da tafukan hannayensa yana mamakin baccinsa a daidai wann lokaci. Ba bacci bane yafi basa mamaki kaman mafarkin da ya tsinta kansa da yi cikin barcin. Meyasa hankalinsa ya tashi sanda yaga Mommy na kuka a cikin barcinsa. Baya son ganin hawaye. Baya so yaga ana kuka amma ya sani hawayen Mommy bai tab’a damunsa ba. Meyasa ya tsinci kansa yana mai damuwa da hawayenta cikin barcinsa. Meyasa zuciyarsa tai zafi da yaga mahaifinsa ya rabu da mahaifiyarsa.? Wann shine abinda yake fata yake buri tsawon rayuwarsa ahalin ta ruguje ta lalace. Meyasa hankalinsa zai tashi bayan abinda yake buri ne Ya faru cikin barcin nasa. Ya furzar da huci a hankali yana kuma shafan fuskarsa. Can k’asan zuciyarsa ji yai yana son kiran Mommy amma wani b’angare na zuciyarsa na kuma tunzurasa gameda al’amarin iyayen nasa. Why would he even care. Toh su rabu mana for all he cares. Yai gajeren tsaki kafin ya mik’e yana neman Dareen yanda ya hangeta cikin pool tana waving d’insa tana fad’in he should join her.
**
Washe gari ta kama Alhamis hakan yasa Ummul ta tashi da azumi dan dama azumin litinin da alhamis basa wuceta hasalima Sun zame mata jiki.
Anisa ce ta shigo Tai inviting b’angaren Mommy kaman yanda Mommyn ta buk’ata a Cewar Anisa. Ummul ta shirya tsaf kafin suka jera suka nufo b’angaren tareda Anisa.
SameenaAleeyou📚
*AUREN WATA UKU..!*
*28*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
A parlour suka tadda Mommy. Tana ganinsu ta fad’ad’a murmushinta. Ummul ta k’araso ta zauna daga can bakin carpet ta gaida Mommy. Bayan Sun gaisa Mommy ke ce da ita ta dinga shigowa b’angaren tana cin abinci tare dasu duk sanda take son hakan sabida zaman kad’aicin babu dad’i. Murmushi kurum Ummul tai dan harga Allah sosai take jin nauyin Mommy dukda k’ok’arin janta jiki da take. Nan take mata godiyan turaren da Anisa ta kai mata injita. Mommy ta murmusa tace Babu komai. Cikin zuciyarta kaw dad’i ne ya mamayeta. Daga k’arshe burinta yana gab da cika. Haidar ya gama gudunsa duk yanda zaije amma tanada yak’inin aikin Malaminsu zai tasiri akansa.
Anisa ce ta janyo hannun Ummul tace ta taso su duba ma’aikatan a kitchen. Aiko kaman wacce take kan k’aya ta mik’e tabi bayan Anisa.
A kitchen d’in ma saida ta janyo Anisa suka keb’e ta d’an mata nasiha kan wulak’anta d’an adam koda na k’ark’ashin ka ne. Musamman da taga yanda duk ta birkita ma’aikatan da tsiwa.
Anisa ta kauda fuska tana rausayar da ido. Cikin zuciyarta fad’i take ki gama duk wani kilibibinki bayan abinda na shirya Miki kin zama tarihi a gidan nan. Zuwan Leenah yasa Anisa barin kitchen d’in dan security personnel sun kira daga can gate sun sanar Anisa tanada bak’uwa. Hakan yasa bata bi takan Ummul ba ta fice.
Ummul na tsaye gefe ta hangi madara kan wuta yana gab da zuba. Cikin sauri ta isa ta d’auki abun motsawa tana juya dan hanasa zuba.
Chef d’in da bata jima da barin wajen ba ta k’araso da sauri tana bama Ummul hak’uri da fad’in urgent call ta samu daga gida Shiyasa ta tafi amsa kiran.
Ummul ta murmusa had’ida girgiza mata kai “Laa babu komai kar ki damu nima nayi kewan aikin ne. Ban Saba zama haka nan bana aiki ba. Duk sai ina jin ba dad’i.” Ta k’arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarta. Dan ta lura cikin ma’aikatan wann wacce ta d’an manyanta mai kula da sauran ‘Yanmatan dake kitchen din ita kad’ai taji tana hausa sosai.
Matar ta d’an murmusa “I’m the chief chef here. I’m the one supervising and monitoring the kitchen staff. Kar ki damu munada yawa a nan.. Zamuyi komai kan lokaci in sha Allah.”
Ummul ta murmusa kad’an “Amma zan d’an iya tsayuwa a nan na tayaku da wani abun..?”
Matar ta kuma murmusawa “I’m afraid you can’t. Idan Madam tazo taga mun baki aiki zai iya shafan namu aikin musamman ni.. Kar ki damu zamu kula da komai a nan.. Kije kawai.”
Ba don Ummul taso ba ta jinjina kai ta nufi k’ofa matar sai sakar mata murmushi take.
Tafiya take a katafaren gidan tana waige waige. Tabbas batada tabbaci idan bata b’ace hanya ba. Tana tafe tana tinanin ta ina zata bi nan ta hangi wani k’ofa tabi k’ofar. Wata ma’aikaciyar gidan mai sanye da uniform ta gani.
Budurwar ta tambayi Ummul “Ma’am, are you looking for someone.. Do you need something..?”
Ummul ta dubeta sai tace “Hanya nake nema dan Allah.”
Budurwar ta murmusa “Oh that’s the way to the main house Ma’am.” Ta k’arashe tana nuna ma Ummul b’angaren dama.
Ummul ta jinina kai a hankali kafin Tai mata godiya tabi hanyar da budurwar ta nuna mata. Tana tafe taga wani k’aton hoto manne a wani madaidaicin parlorn mai kaman waiting. Ta gane Mommy a hoton dukda k’uruciya da ya nuna a fuskar Mommyn. Gefe da Mommy wani mutumi ne mai Kamala da bata tantance ba amma tanada tabbacin shine mai gidan kenan. Tsakiya dasu wani yaro ne Wanda duka duka bazai gaza shekaru 10 ba. Kansa an tara masa suma irin mai laushin nan da cika. Ga kamannin iyayensa d’auke a fuskarsa. Yanda yaron ya b’ata rai cikin hoton ga fuskarsa da Ya buya cikin sumar kansa sosai abun yaso bata dariya musamman da taga kaman ita yake harara. Kai da gani kasan camera yasha harara kaman dai Wanda aka masa dole.
Muryar su Anisa da ta soma jiyowa ne Ya janyo hankalinta. Ta nufi hanyar da take sinkayo muryoyin. Nan ta kuma cin karo da wani hoton a wani dogon corridor. Saidai wann hoton matashi ta gani tsaye gaban wani k’atoton zanen gine gine hannunsa rik’eda wani k’aramin abu kaman kara yana nuna ma mutanen dake zaune saman kujeru bayansa zanen dake gabanshi. Ko ba’ace ba zaka fahimci ma’aikata ne. Matashin yana sanye da suit saidai fuskarsa bai bayyana cikin hoton ba sakamakon Ya bada baya alamun yana bayani gameda hoton dake gaba gareshi. Bata san dalili ba amma kallo guda Tai ma mutumin dake cikin hoton zuciyarta ya yanke. Ta tsinci kanta da fad’uwan gaba dukda ba wai ganin fuskarsa tai ba.
A haka tana nan tsaye su Anisa suka k’araso suka taddata. Anisa da Leenah suka dubi juna kafin Anisa ta k’araso murmushi saman fuskarta. Tai tsaye gefen Ummul dake duban hoton.
“Aliyu Haidar Maitama. D’a d’aya tilo ga Engr Aliyu Maitama da kuma Hajiya Kwaise Maitama.” Abinda Anisa kenan tace Wanda ya kuma haifar ma Ummul fad’uwan gaba. Kenan wann shine Aliyu.. mijinta.? Sai ta kuma jin zuciyarta na bugawa da sauri. Musamman da Zuciyar nata ta ambacesa da mijinta wanda ko shakka babu da kokonta zuciyar nata ta raya mata.
Anisa ta murmusa tana ci gaba da kallon hoton “Mutumin da manyan mujallu ke rubibin hasko fuskarsa yana guje masu. Da matuk’ar wahala kiga hotonsa koda cikin mutane saidai a bazata.” Ta kuma murmusawa “But If you read papers definitely zaka iya sanin fuskarsa. Dan bana tunanin wann d’anuwan nawa has any social media account.” Ta kuma murmusawa tana girgiza kai “I guess my cousin is allergic to camera. He is the weirdest person with high standards I’ve ever known.” Ta juyo ta dubi Ummul “Shall we.. Abinci is ready ke muke jira ranki dad’e.”
Ummul ta murmusa kad’an “Saidai ni Ina azumi yau d’in..”
Anisa da Leenah suka dubi juna. Anisa tace “Azumi ba cikin watan azumi ba.”
Ummul ta kuma murmusawa “Yau d’in alhamis ne akwai falala cikin yin azumi a wann ranar.”
Leenah ta kauda fuska gefe tana rausayar da ido cikeda k’osawa yayinda Anisa ta murmusa “Wow. A gaskiya kin burgeni Ummul. Zan so na koya daga wajenki.”
Batace da Anisa komai ba sai murmushi da tai. Anisar ta janyo hannunta tana fad’in suje she can wait in her room idan bazata zauna a table din ba. Nan d’akin Anisa suka baro Ummul d’in yanda Anisar da Leenah suka nufo teburin cin abinci.
Mommy ke tambayarsu ina Ummul d’in.
Anisa ta waiga kaman wacce take nemanta “Oh mun fito tare daga d’akina.. But where has she gone.?” Tai maganar fuskarta d’aukeda alamun tambaya.
Leenah tace “I think naga komawarta cikin d’akin. Maybe ta mance wani abun.. Or she’s Probably using the bathroom.”
Mommy bata ce komai ba taci gaba da cin abincinta. Can wayarta yai ruri ta tashi daga table din tabi wani k’ofan tana amsa kiran.
Leenah da Anisa suka dubi juna suna murmushi daidai lokacin Ummul ta fito. Su biyu ta tadda a table d’in.
Anisa ta fad’ad’a murmushi sanda taga fitowarta “Har kin fito. Sorry we left you alone. Gashi na mance ban kunna miki Kayan kallo ba. You must be bored.”
Ummul ta girgiza kai “A’a kar ki damu babu komai. Ina so na koma ne naga garin da hadari na bar wasu Windows a bud’e.”
Leenah ta girgiza kai “Haba Ummulkhair kan wann zaki wahalar da kanki. Umarni kawai zaki bawa ma’aikata su miki.. Wai ko Har yanzu baki gane matsayinki bane a gidan nan.? Kinga koma abinki kiyi zamanki yanzu zamu shigo nasan kunya kikeji. Bazaki iya zama ki saka surkarki gaba tana cin abinci ba dikda ita Mommy normal ne wajenta abinki da civilized woman.” Ta karkato sosai tana duban Ummul “Kinada babban sa’a Ummul. Mata da yawa suna burin ina ma ace sune a matsayinki. Wayayyun mata Wanda suka had’a komai na rayuwar duniya. If I were you, bazanyi wasa da wann damar ba.” Ta kuma murmusawa “Kar ki damu a hankali zaki koyi irin rayuwar.” Ta k’arashe tana sakar mata murmushi kafin Ta mik’e tana fad’in “I’ll ask one of the maids ta rufe windows din.” Bata jira Cewar Ummul d’in ba ta wuce b’angaren ma’aikatan cikin sauri Kai kace itace ‘yar gidan. Anisa ta dubi Ummul d’in da murmushi.
Ummul Tai tsaye kaman mai tunanin wani abu. Magaganun Leenah take kuma nanatawa cikin kanta. Sai tanaji tamkar wani sak’o Leenar ke son bata a dunk’ule. Allah sarki da ace Leenah tasan ita wann auren ba da son ranta akai ba. sadaukarwa ne kawai ga ahalinta da bata fad’i abinda ta fad’i ba.. Ta d’anyi still a wajen sai kuma ta juya ta koma d’akin Anisar dan gabatar da sallar la’asar da aka soma kira.
Bayan Sun gama cin abinci suna zaune suna hira nan d’akin Anisa gaba d’ayan su ukun. Da alama harta Leenah ta saki jiki da Ummul. Har kana iya jiyo shewan Leenah da Anisa alamun hira ta masu dad’i. Ita dai Ummul saidai tai murmushi idan an fad’i wani abun bakajin muryarta.
Suna tsaka da hiran suka soma sinkayo muryar Mommy tana doka kira ma ma’aikatan gidan.
Anisa Tai shiru tana fad’in “Kai ku saurara kuji.. Meke faruwa.? Kaman muryar Mommy nakeji cikin fad’a.”
Gaba d’aya suka saurara aiko nan suka sinkayo muryar Mommy tana fad’in kaf ma’aikatan su hauro parlornta.
Anisa tace maza su tashi suje suji abinda ke faruwa.
Suka mik’e gaba d’ayansu suka nufo parlorn Mommy yanda suka tadda ta had’a assembly ma gaba d’aya ma’aikata tana tambayar waye ya shigar mata d’aki cikinsu.
Wann ya dubi wancan wancan Ya dubi wann. Kowa yace bai shiga ba tin gyaran safe.
Mommy ta d’ago wani d’an box hannunta. Cikin tsimewa taci gaba da fad’in ta tadda jewelry drawers d’inta a bud’e kuma an d’auki sark’ar dake cikin box d’in hannunta. Waye ya d’auka.?
Anisa ta zaro ido waje “Mommy sata cikin gidan nan..? This is something unusual.. Abu ne da bai tab’a faruwa ba.”
Mommy taci gaba da jinjina Kai “If there’s one thing I hate shine rashin gaskiya. Abu ne da akayi shi a cikin gida. And that’s why dole a fito da koma waye yayi satan. If it takes ayi searching every angle na cikin gidan nan ne za’ayi. Kayan kowa cikinku kaf sai an bincika.” Ta k’arashe tana duban ma’aikatan.
Anisa ta jinjina kai “K’warai Mommy a duba ko ina cikin gidan nan. I’ll search the employees section myself.” Mommy ta dubi babba cikin ma’aikatan wacce tafi aminta da ita Tai assigning d’inta da suje su duba su caje kaf b’angaren ma’aikatan. Daga b’angaren ma’aikata Anisa tace su nufi b’angaren Ummul tinda Mommy kaf gidan tace a duba.
Su Mommy da Ummul suna tsaye tareda sauran ma’aikatan a parlor wayan Mommy yai ringing. Anisa ce mai kira duk jikinta a sanyaye.
Mommy tace “Ehen I’m listening to you. Kun samu sark’ar.?”
Anisa ta jinjina kai a hankali kaman Mommy na kallonta “Eh mommy mun samu..”
Mommy taci gaba da jinina kai “Cikin kayan waye kuka samu tsakanin maids d’in. Ki sanar da security guda d’aya a kira ‘yansanda. Wacce duk tai satan must be punished kuma zata bar gidan nan a yau.”
Anisa ta kuma fad’i a sanyaye “Mommy you need to come see it yourself.. Ban san yanda zan sanar dake ba.. Amma Ya kamata ki gani da idonki.. I’m still in shock..”
Mommy ta girgiza kai kad’an “Anisa.. Ban fahimceki ba.. Mai kike nufi.?”
Shiru ne Ya biyo baya alamun Anisa na sanar da ita abinda ke faruwa.
Ta juyo ta dubi Ummul wacce damuwar abuja ke faruwa Ya nuna a fuskarta “Kin tabbata da abinda kike fad’a Anisa.?”
Jinjina kai Mommy tai a hankali kafin ta nufo k’asa.
Sosai taji mamakin ganin sark’ar cikin d’akin Ummul. Toh amma Ya hakan ta kasance.?
Ma’aikaciyar ta girgiza kai “Hajiya gaskiyar kenan. Nima naji mamaki sosai da abinda muka gani.”
Mommy ta girgiza kai “Ummulkhair bata jima da zuwa gidan nan ba. Amma inada tabbacin bazatayi abu makamancin wann ba.”
Anisa Tai Shiru kaman mai tunani “Nima dai Mommy ban zaci haka daga wajenta ba. Dukda yau ce rana ta farko da ta jima b’angarenki..”
Shiru Mommy tai tana juya maganganun Anisa. Tabbas yau ne rana na farko da Ummul ta jima irin haka a b’angaren ta. Sann lokacin da suke cin abinci batazo teburin cin abinci ta zauna tareda su ba.
Anisa ta kuma duban Mommy kafin tace “Mommy bazanso hakan ta kasance ba.. Yarinyar nan ba saninta mukai ba. Ammi ce kawai ta Santa da background d’inta.. I’m sorry to say kinsan talakawan nan gold diggers ne. Ammi used to tell me this.” Ta kuma duban Mommy sosai “What if Ammi batai bincike mai zurfi kan ahalin Ummul ba.. Kuma d’azu da naje zan shigo da Leenah na ganta ta fito ta hanyar parlorn ki na sama. I thought kece kika aiketa wajen or something. Kuma one of the maid ta sanar damu taga Ummul wandering around the house.”
Shiru Mommy tai tana juya maganganun. Sai kuma ta girgiza kai “I still find it hard to believe Ummulkhair zata iya aikata abu makamancin wann. But koma menene we’ll find out about it. Je ki kira Ummulkhair da ita da maid din da tace miki ta ganta tana zagaya gidan.”
Anisa ta jinjina kai “Yes Mommy.” Lokaci guda tasa kai ta fice tana sakin muguwan murmushi zuciyarta fal nishad’i.
Ba’a jima ba Ummul da maid d’in da Tai mata kwatancen hanya harma da Leenah suka k’araso. Anisa na tafe gaba garesu.
Zuciyar Ummul yaci gaba da tsinkewa ba don tsoro ba sabida tasan akan gaskiya take ba abinda zai bata tsoro saidai a duniyarta ba abinda ta tsana irin a danganta ta da sata. Sata abu ne mai ciwo ace an danganta ka dashi. Koda ace ta fito gidan da basuda arziki Allah ya masu arziki da wadatan zuci wanda shine babban arziki. tayi imani basuda abinda zata sata. Sanda Mommy ta d’ago sark’ar tana nuna mata sai taji kuka yazo mata.
Mommy ta k’araso ta dafata “Bance kin d’auka ba Ummul. So nake kawai ki amsa min tambayata dan haka ne zai wanke ki. An samu sark’ar a cikin d’akinki.. Ta Ya haka ya kasance.?”
Ummul ta girgiza kai “Ki yarda Dani Mommy. Ni ba b’arauniya bace. Ban kuma d’auka ba. Sann bansan Ya akai ya zo d’akina ba. Gaba d’aya ranar ina zaune cikin gida ban ma shigo b’angarena ba.”
Leenah tai kaf tace “But wait kince zaki zo ki rufe Windows d’inki sabida hadari da kika gani gudun kar ruwa ya shiga miki.. Kodai lokacin ne kika fito kika kawo sark’ar kika ajiye a d’akin ki.”
Ummul ta dubi Leenah cikeda mamaki dan ta ma kasa cewa komai yayinda Anisa Tai karaf tace “A’a Leenah. Ai Ummul bata zo ta rufe Windows d’in ba.. D’aya daga cikin ma’aikata ne tazo ta rufe Windows d’in.”
Leenah ta tab’e baki “But samun sark’ar a nan proves otherwise.”
Ummul taci gaba da girgiza kai tana hawaye take fad’in ita ba b’arauniya bace.
Leenah tace “Prove it then.. So kike a d’aura ma wani sharri bayan ga abinda aka gani.”
Mommy ta aika ma leenah wani kallo ganin irin kukan da Ummul keyi.
Hannayen Ummul Mommy ta kamo tace “Idan kina son sark’ar Ummul zan baki ita kyauta. Kar wann yasa ki d’aga hankalinki. Ni ban kawo a raina zaki min sata ba. Duk abinda kika d’auka nawa tamkar naki ne. Ke matar Haidar ce idan har zance kin min sata kaman nace Haidar ya mun sata ne. Duk abinda kika d’auka gidan nan ba sunansa sata ba. Case closed.” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta tana goge ma Ummul d’in hawayen dake gangaro mata. Cikin zuciyarta cewa take ke d’in makarin asirin d’ana ne ko mai zaki min zan shanye har na samu Haidar ya dawo gareni.
Da mugun mamaki Anisa da Leenah suke duban juna baki sake. Wai shin wane irin makahon so Mommy ke ma yarinyar nan Wanda hankali bazai d’auka ba. Wai Hajiya Kwaise ce ta zama very soft haka. Matar da sunyi imani irin sanin da suka mata yanda ta kama b’arawon nan sai Ya d’and’ani kudarsa. Matar da sam bata yarda da wani shit ba.
Ummul ta girgiza kai ba don bata d’auki maganganun Mommy da mahimmanci ba sai don bazata bari a mata shaidan sata ba. Amma ta ya zata wanke kanta. ta ina zata fara hakan.? D’agowa Tai tana dubansu gaba d’aya da idonta mai zuban ruwa. Sai ta dubi Mommy ta kuma girgiza kai “Ban d’auka ba. Kiyi hakuri Mommy ban raina k’ok’arin ki na kula dani da bani duk wani kariya ba. Amma hankalina zaifi kwanciya idan har aka tabbatar banida laifi.”
Leenah da Anisa suka kuma duban juna suna mamakin ta Ya za’ai ta fidda gaskiyar.
Ummul Tai tsaye tana k’are ma gidan kallo. Cikin zuciyarta kaw addua take ‘Ya Allah banida wani wayo sai abinda kayi dani. Ya Allah ina tawassili da azumin dake bakina Wanda nakeyi dan neman yardarka. Allah ka wanke baiwarka mai rauni daga wann sharri da aka k’ulla mata.’
Anisa ta katseta da fad’in “Ummul Mommy ta aminta dake inaga ya kamata ki bar zancen a haka. I think You don’t need to prove your innocence.”
Mommy ta girgiza kai “No, if she wants to prove her innocence bazan dakatar da ita ba. After all, I want to know who the real culprit is.”
Zuciyar Anisa Ya kuma tsinkewa. Leenah ta dubeta a tsorace itama. Nan ta fara wak’an tafiya gida. Mommy tace babu mai tafiya sai gaskiya ya fito. Ta dubi Ummul tace suna sauraronta. Ta bayyana gaskiyarta.
Ummul ta jinjina kai a hankali kafin ta d’aga kai tana k’are ma gidan kallo.
Can k’ofan shigowa sashen ta hangi security camera.
Leenah ta rausayar da ido tace “Ummul bakida wani hujja please don’t waste our precious time here. I really need to leave now. Is getting late already.”
Juyowa Ummul tai ta dubi Leenah tana murmushi “A’a inada hujjar da zan kare kaina.”
Leenah ta girgiza kai “So.. Where is your proof then.?”
Ummul ta girgiza kai “Kiyi hak’uri ban fahimci mai kike nufi ba.”
Leenah tai murmushin rainin hankali tana duban Ummul a wulak’ance “Common English bakiji har kina tunanin kinada wani intelligence da zaki iya canza abinda idonmu ya gani.? Is this a joke or something.”
Jinjina mata kai Ummul Tai “K’warai inada shi koda harshena bai iya furtawa ba.” Ta d’aga hannu Tai mata nuni da cctv camera. Taci gaba “Na tabbata shi zai tantance na fita daga sashen Mommy ko ban fita ba. Haka ne.?” Leena tai Shiru sai muzurai dan batai zaton wann bagidajiyar zatai tunanin cameras ba. Batamayi zaton tasan da zaman cameras din ba. Ta juyo ta dubi Anisa cikeda tsoro. Sai Anisa ta kashe mata ido alamun ta kwantar da hankalinta she had everything under control.
Mommy ta jinjina kai “K’warai akwai cameras a wasu hanyoyi da zai sadaka da d’akuna cikin gidan nan. Shi zai tabbatar mana idan Ummul ta shiga d’akina ko bata shiga ba.”
Anisa ta jinjina kai tace k’wari a duba footage.
Saidai koda aka duba cameras na cikin k’waryar gidan kawai aka duba kuma da alama duk Sun samu fault dan haka ba’a ga waye ya shiga d’akin ba.
Leenah ta rausayar da ido cikeda k’osawa tana fad’in Ummul batada sauran hujja.
Ummul ta girgiza kai tace “Na cikin k’waryar cikin gida kawai aka duba mai zai hana a duba na waje. Shi zai tabbatar ya kuma tantance waye ya kawo sark’ar b’angarenta.
Leenah ta dubi Anisa wacce izuwa lokacin ta gama razana dan zallan cameras na cikin gidan Tai tampering banda na haraban gidan tinda bata kawo abun zai kawo haka ba.
Mommy ta jinjina ma tunanin Ummul dan koda aka duba footage na haraban gidan Ya hasko wata maid din gidan sanye da uniform dinta ta nufi bangaren Ummul da sark’ar rike hannunta saima juyasa take tana waige waige.
Leenah ta rausayar da ido “See, this doesn’t prove you innocent Ummul. It could be an alibi so that no one would suspect you. I’m sure this is pretty mandated. Bakinku d’aya kawai bata mana lokaci kike a nan.”
Mommy ta daka mata tsawa da fad’in Tai masu shiru. Sai kuma ta juyo sosai tana duban Leenar dan ta kula zak’ewarta da k’ok’arin ganin ta d’aura laifin kan Ummul yayi yawa. Mommy ta girgiza kai kad’an tana kuma duban Leenah “Waye ya baki daman saka hancinki cikin al’amarin gidan nan.?”
Leenah ta sha jinin jikinta. Ta dan matsa gefe tana bama Mommy hakuri.
Take Mommy tasa akai mata kiran maid din.
Ba’a jima ba Maid din ta bayyana gaban Mommy wacce ta tsareta sosai da ido. Sai rawa jikinta keyi dan tsoro.
Cikin murya mai tsoratarwa Mommy ke tambayarta waye ya bata umarni da ta kai sark’ar d’akin Ummul.
Maid din taci gaba da sunkuyar da kai tana girgiza kai. Ta d’ago tana dubansu a tsorace. Anisa ta Zare mata ido. Sai ta girgiza kai ta shiga nuna Ummul d’in tana fad’in ita ta bata umarni taje ta b’oye mata sark’ar a b’angarenta bayan ta d’auko. Cikin harshen turanci mai aikin tai maganar.
Leenah ta murmusa “My hunch was right, after all. Gashi Ummul Vicky ta bada shaida akanki. Bakinku d’aya. Shin har yanzu kinada sauran hujja.?”
Mommy ta kuma tambayar Vicky tabbata Ummul ce ta bata umarni. Vicky tace eh haka ne.
Girgiza kai Ummul take tana dubanta kafin ta k’araso gabanta “Kika ce ni na baki umarni.?”
Sai ta d’ago tana duban Ummul d’in dan bataji mai tace ba sabida ba hausa take ji ba. Ummul ta kula mai aikin bata jin hausa. Sai ta murmusa a hankali tana hamdala cikin zuciyarta dan da alama duk yanda mugun zaibi yaga Ya kulleta sai Allah ya bata k’ofan fita sabida batada hakki.
Taci gaba da duban Maid din tana mai ci gaba da furta “Amma baki jin yaren da nakeyi. Haka zalika nima bana jin yaren da naji kinyi magana dashi. Shin ta Ya akai har na k’ulla cinikayya dake.? Ta ya akai har kika iya d’aukan umarni daga bakin wacce baki jin mai take fad’i.?”
Shiru sai kallon Ummul da take cikin rashin fahimtar mai take cewa.
Mommy ta jinjina kai cikeda gamsuwa da yanda Ummul ke fayyace komai dalla dalla.
Mommy ta dubi Leenah tace “Yanzu kika mana proving a nan cewa Ummul bata jin turanci haka ne.?”
Cikin sanyin jiki da daburcewa Leenah ke duban Mommy ganin table na k’ok’arin turning.
Mommy taci gaba da jinjina kai “Idan haka ne bana tsammanin zata iya dogon magana har su shirya wani plan da Vicky wacce sam ba hausa take ji ba.”
Kowa ya shiga jinjina al’amarin yayinda zuciyar Ummul Ya cika da hamdala.
Anisa ta sake baki tana kallon ikon Allah yanda Bagidajiyar nan zata kamasu gidadancin da suka raina.
Leenah ta janyo Anisa gefe tana mata k’usk’us “Oh Girl, this is not happening.. What’s she doing.? My goodness! Is she a detective now.? I never imagine zatai irin wann tunanin maiyasa kika bada aikin ma wann maid d’in da batajin hausa.” Tai maganar tana satan duban Ummul. Kafin ta kuma kwantar da murya daidai kunnen Anisa “I thought you said you’ve everything under control.. looks like it’s gonna backfire.. Hajiya Kwaise bazata yafe mana ba Neesa. Oh no.. I’m scared. Mai zai faru idan tasa ‘yansandan su tafi damu.? This is all your fault Neesa. I shouldn’t have involved myself in your plans.”
Anisa ta furzar da huci Har lokacin k’usk’us suke yayinda Mommy ta tistiye Vicky tana tambayar sai ta sanar da ita waye ya bata order.
Leenah ta kuma tambayar Anisa “Girl what do we do now.? Your grand plan turned out to be brainless. Are you that stupid Neesa. Didn’t it occur to you hakan zai iya faruwa.?”
“Oh shut up Leenah.! Banyi tunanin haka ba. You know why.? Because your stupidity is contagious.. Ke kika shafa mun shashancinki.”
Ta k’arashe daidai lokacin da idon su Mommy gaba d’aya yayo kansu dan Vicky direction d’insu take duban sanda Mommy ta titsiyeta.
Mommy taci gaba idonta kan su Anisa “Tell me Vicky. If you don’t want to go to jail alone. Who’s your accomplice. Who ordered you to frame my daughter in-law.? Tell me now.!” Mommy ta k’arashe cikin tsawatarwa.
Ganin haka yasa Anisa yin alama ma Vicky da yatsarta tana nuna mata Leenah cewa tace Leena ce.
Hannu na rawa Vicky ta nuna Leenah “It’s her.. She payed me to do a clean job. But believe me madam, I only accepted her offer because I desperately needed the money.. Please don’t fire me. Have mercy on me.!” Ta k’arashe cikin kuka tana duk’awa gaban Mommy.
Leenah ta saki baki cikin tsananin shock jin yanda aka aza mata laifin komai tashi daya. Ta soma girgiza kai tana duban Vickey “Me.? Hey excuse me.! What crap are you talking about.? Why would I do such a thing.. What could be my motive. I have nothing against her..!” Tai maganar tana duban mutanen dake wajen cikin k’ok’arin kare kanta. Leenah ta tafi ta shiga jijjiga Vicky tana fad’in ta bud’e baki ta fad’i gaskiya cewa ba ita ta sakata ba.
Vickey ta nuna credit alert da Leenah tai mata dan dama da account d’in Leenah akai payment d’in sabida account din Anisa yak’i transfer kuma ba cash a hannunta. Leena tace akwai kud’i cikin account d’inta bari ta tura ma Vicky. Nan Anisa tace Tai payment d’in 100k zata bata daga baya. Hakan yasa da Vicky ta nuna kud’in da ya shiga account d’inta sunan Leenah ya fito. Vicky taci gaba da fad’in ta tura kud’in ne zuwaga mahaifiyarta dake jinya dan sayen magani. Shiyasa ta amsa tayin da Leenah Tai mata cewa taje ta aje sark’ar a d’akin Ummul.
Leenah ta saki baki ta juyo tana duban Anisa wacce Tai kaman batasan meke faruwa ba.
Zata kuma magana Anisa ta dakatar da ita da fad’in “Oh shut up Leenah.! Bansan haka halinki yake ba. Bansan zaki k’ulla ma Ummul irin wann sharrin ba I shouldn’t have invited you here in the first place.”
Leenah ta saki baki tana duban ikon Allah jin yanda k’awarta Anisa Tai incriminating dinta ta kuma aza mata laifin komai tashi guda.
Leena baki na rawa take furta “But.. But wait..”
“Oh Leenah kowa yaga evidence da sunanki. Ke kika biyata Tai aikin without my knowledge. Amma nasan dalilin da yasa kikai haka k’awata. You did it out of your concern for me. A tunanin ki zaki rama min abinda Ummul ta mun a SPA ne Shiyasa kikai haka, right.?”
Leenah ta kasa cewa komai sai duban k’awarta Anisa da take da tsananin mamaki.
Anisa ta juyo ta dubi Mommy “Mommy dan Allah kiyi hak’uri. I know Leenah.. I know my friend is not a bad person. Misunderstanding aka samu.” Tai briefing Mommy kan abinda Ya samu fuskarta duk akan Leenah ta d’aura laifin Har abinda ya faru a spa. Sam bata nuna ma Mommy tasan da plan d’in Leenah na k’ona fuskar Ummul ba Wanda ya juya nata fuskar.
Anisa taci gaba “Mommy Leenah thought she was doing it for me. Ta zaci hakan da Tai tamkar ta rama mun ne. Kinsan kishi irin na k’awaye. Kishi take da Ummul zata k’wace mata k’awancenmu. Musamman da yau da tazo taga yanda nake da Ummul d’in.” Ta kuma duban Ummul “Ummulkhair please forgive my friend.”
Muryar Mommy ta sinkayo tana fad’in “Dama nasan za’a rina. A yanda taketa k’ok’arin d’aura laifin ma Ummul. She’s the real perpetrator. I dont care if she’s your Friend. Criminals are not welcome in my house. And this won’t go unpunished. She must pay for what she did to my daughter.”
Ta dubi d’aya daga cikin ma’aikatan gidan tace ta kira mata ‘yansanda. Matar ta jinin kai “Right away Madam.”
Vicky sai kuka take tana fad’in a mata rai. Yayinda Leenah mamaki ya hanata katab’us.
Sai jan k’afafun Ummul Vicky take tana fad’in ta yafe mata.
Tsawa Mommy ta daka ma Vicky da fad’in “Shut your mouth and get up from there! You are leaving this house right this instant. I don’t have room for criminals like you in my house.” Ta kuma jaddada mata sai ta fara mik’asu ma hukuma daga ita Har Leenah.
Duk sai jikin Ummul yai sanyi. Yarinyar ta bata tausayi. Da alama cikin ma’aikatan tafi kowa k’arancin shekaru. Sann taji cewa da tai kud’in da ta amsa wajen Leenah ta aika wa mahaifiyarta dake jinya ne. Sai ta tuna nata mahaifin dake kwance yana jinya. Ta tuna mak’asudin zuwanta gidan itama yarda da auren da Tai sabida ta ceci mahaifinta dake jinya ne itama. Sann sadakinta shine kud’in jinyar mahaifinta. Tabbas kowa zai komai dan ya ceci iyayensa. Sai taji kaman batada wani maraba da Vicky.
Cikin sauri Ummul ta juyo ta dubi Mommy kaman zata fashe da kuka take fad’in Mommy tai hakuri ita ta yafe masu kar a kirawo ‘yansanda.
Da kyar Mommy ta hak’ura da kiran ‘yansandan sabida rok’on da Ummul Tai mata. Amma kam ba don Ummul d’in ba da daga Leenah Har Vicky sun kwana ofishin ‘yansanda.
Mommy ta bada umarni ma babba cikin ma’aikatan gidan cewa a raka Vicky waje da kayanta ta koreta. Ita kuma Leenah ko me kamanta securities suka kuma bari ta shigo gidan a bakin aikinsu.
Harda Anisa akaima Leenah rakiya waje. Sai kallon mamakin cin amanar da Anisa Tai mata take ma Anisar.
Anisa ta dubeta bayan Sun rage saura su biyu “Let me call you a cab for you..”
D’aga mata hannu Leenah tai alamun dakatarwa “Ki barshi bana buk’ata. You know what Neesa ban tab’a zaton zaki ci amanata irin haka ba. Ta ya zaki d’aura min laifin da banyi ba. You planned the whole thing. Sann kin d’aura min laifi kaman wata sakarai. You know what? I think you’re right. I’m stupid and that’s why I remain loyal to you.” Tana gama fad’in haka tasa kai ta shige kaman zata tashi sama ba tareda ta kuma bi takan Anisa ba.
Juya ido Anisa Tai had’ida furzar da huci kafin ta koma cikin gida.
Nan ta tadda Mommy ta had’a kaf ma’aikatan gidan tana kafa masu warning. Ta dafa kafad’an Ummul tace “She’s my Son’s wife. I expect each and everyone of you to treat her with absolute respect, Including you Anisa.” Tai maganar tana duban Anisa da shigowarta kenan kafin taci gaba “The same respect da zaku bama D’ana Haidar. Bana so makamancin abinda ya faru yau Ya kuma faruwa. Do I make myself clear.?”
Gaba d’aya suka jinjina mata kai hadida amsawa cikeda risinawa
**
Bayan Ummul ta koma sashenta tana zaune saman darduma Ida sallarta kenan Anisa ta shigo da murmushi saman fuskarta.
Ummul bata nuna mata komai ba dan itama wann sassanyar murmushin wanda a baya Anisa ta d’aukesa shashanci da gidadanci a halin yanzu shakkar wann murmushin take shine dai saman fuskar Ummul.
Ta zauna tana tambayarta an sha ruwa lafiya.
Ummul ta amsa mata da sakin fuska. Nan Anisa ta soma bata hakurin abinda Leenah Tai tana mai kuma tabbatar mata Lallai Babu hannunta cikin abinda Leenah da Vicky suka k’ulla mata.
Murmushi Ummul ta kuma yi “Babu komai Anisa kar ki damu. Suma ban k’ullacesu ba. Daga k’arshe Allah Ya bayyana gaskiya. Ba wayona bane ba kuma dabarata bace. Allah ne Ya dube ni da rahamarsa Ya wanke ni daga k’agen da aka so min. Na kuma gode masa da Ya wanke sunana daga k’agen sata. Ina kuma fata ya shiryi duk masu tunani irin nasu damu baki d’aya.”
Anisa ta jinina kai “You are a good person Ummul. You have a clean heart that’s willing to forgive and forget. Yanda kika wanke kanki cikin hikima ya burgeni. I wish zan zama kaman ke.”
Ummul ta murmusa “Duk wanda ya dogara ga Allah Allah ya isar masa. Kuma duk wanda yaji tsoron Allah Allah zai samar masa mafita. Ba yin kaina bane Allah yakan wanke bayinsa da akai masu k’age ba tareda sun aikata laifin ba. Kaman yanda Ya wanke Ummuna Aisha (RA) daga k’agen da azzalumai suka mata. Kaman yanda Ya wanke Annabi Yusuf (AS) daga k’agen da aka masa. Kaman yanda Ya wanke bayinsa muminai da dama daga k’agen da aka masu. Kaman haka yanke wanke bayinsa da basuda hakki. Na gode masa da ya wanke ni daga k’agen da aka min ba tareda hakki ba. Amma ni Ummulkhair banida wani wayo. Saidai Inaso mutane irinki da Leenah su fahimci English is just a language and not a means to measure one’s intelligence or education. Snn duk wani wayewar da yai karo da koyarwar addininmu da d’abi’u da kyawawan al’adunmu ba sunansa wayewa ba.” Tai maganar murmushi saman fuskarta.
Baki sake Anisa ke kallonta “So you can speak English.?”
Ummul ta murmusa “Ba sosai ba abinki da Wanda taje makaranta na gwabnati.”
A hankali Anisa ke jinjina kai “Na yarda da duk abubuwan da kika ce. A yau kin kuma tabbatar min da haka. “ Ta kamo hannayen Ummul “Mommy tayi zaton ni zan koya miki abubuwa musamman zamantakewan rayuwar civilized world. But it turned out ni ce wacce ke koyo wajenki. Yau na raina duk wani exposure na Ummul.”
Ummul ta girgiza kai “A kullum ko wani shafi na rayuwar mu darasi yakan bude mana dan mu koya. Kullum cikin koyo muke a duniyar nan. Kaman yanda muke had’uwa da mutane iri daban daban.” Ta d’an murmusa “Nima ina koyo daga gareki Anisa.”
Shiru Anisa Tai sai kuma ta saki murmushi da yafi kama da yak’e.
Tin daga wann rana Ummul ta samu sanyin abubuwan da Anisa ke mata. Sai ta koma kaman tana shakkan Ummul d’in koda bata nuna a fili ba. A kwanakin da alama Anisa ta maida makaman yak’inta.
**
Kano…
Batai k’asa a gwiwa ba dukda fargabn abinda ka iya zuwa yazo ta nufi gidan Hajiya Asshe. Juyin duniya Umma tayi amma masu gadi sun hanata shiga sabida dokan da Asshen ta basu tin kwanakin baya.
Asshe na kitchen tana had’a ma maigidanta abinci kasancewar ranar yake dawowa daga tafiya kuma gidanta yake. Mai gadi yai Sallama ya sanar da zuwan Umma wacce babu yanda basuyi ba amma tak’i barin bakin gate din tace sai ta gana da Hajiyar.
Zuciyar Asshe ya tsinke yanzu idan matar nan ta tada mata hargitsi a k’ofan gida har mijinta ya iso ya tadda wann al’amari mai zata ce masa. Oh! Ita kam dai ta d’ebo ruwan dafa kanta. Wann wasu irin ahali ta kwaso masu ne wai ita Asshe. Bata gama da fitinan Dije ba ga Suwaiba da tai tunanin ta ajeta yanda ya kamaceta yanzu ta dawo. Toh uban mai ta dawo zata mata.?
Fuuu ta nufo gate tana huci dan wllhi bazata bari d’aya daga cikin watsatsun matan nan su mata sanadin aurenta da take lallab’awa ba.
Tana fitowa ta shiga janyo Umma tana fad’in yau hukuma ce zasu mata iyaka da ita muddin bata bar mata k’ofan gida ba.
Umma bata tafi ba bata fasa rok’on Asshe tana fad’in ta dubi girman Allah ta saurareta.
Hilal daga sashensa yake jiyo haniya yak’i k’arewa daga gate. Babu shiri ya bar abinda yake ya nufo gate d’in.
SameenaAleeyou📚..
*AUREN WATA UKU..!*
*29*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
Asshe taci gaba da janyo Umma tana fad’in kodai ta bar mata k’ofar gida ta mik’a mata ma ‘yansandan dan ta gaji da fitinan fitinannun mata Irinsu. Wanda tin had’uwar ta dasu Masifan yau daban na gobe daban.
Umma taci gaba da girgiza kai “Idan kina ma Allah ki tsaya ki saurareni Hajiya Asshe.”
“Na saurareki na saurari mi inyi.? ‘Yarki ce nace Miki akwai wa’adin da na d’ibar Wanda zan dawo da ita gareki. Amma a halin yanzu ni Asshe banida wani sauran alak’a dake da sauran zuri’arku. Na gode ma Allah da yasa auren Ummul ba mai d’orewa bane. Mi za’ayi da zuri’arku dangin masifa dangin mayu dangin matsafa.. Zo ki wuce.. Idan kika kara minti d’aya k’ofar gidan nan ki kwana ofishin ‘yansandan” Ta k’arashe tana hankad’a Umma da iyaka k’arfinta Wanda saida ta kaita k’asa.
Daidai nan Hilal Ya fito ya taddasu. Ya isa da sauri yana ma Umma sannu had’ida tambayar bataji ciwo ba.
Umma ta d’ago tana girgiza masa kai alamun a’a.
Da tsananin mamaki yake duban mahaifiyarsa “Ammi what’s the meaning of this.? Kan wani dalili zaki aikata abu makamancin haka..? Mai yayi zafi..? Wai meke faruwa ne ma.?”Ya k’arashe damuwa saman fuskarsa.
Asshe na huci take furta “Babu ruwanka Hilal. Ba abinda ya had’aka da Matar nan zo ka shige gida.”
Hilal ya girgiza kai “Ammi matar nan sirkar Haidar ce.. ‘Yarta Haidar ke aure.. We are practically family now.”
Bai kai aya ba Asshe ta k’araso a guje ta toshe bakinsa “Allah tsari gatari da saran shuka. Allah mana tsari da had’a iri da wann zuri’a.. Shige gida kar na sake jin bakinka.” Ta k’arshe tana nuna masa k’ofa.
Girgiza kai Hilal Ya kumayi “Ammi I’m sorry. Bazan iya barin Umma a nan ba har sai na san abinda ke faruwa.”
Baki sake Asshe ke dubansa “Umma.?” Ta nanata a fili. “Umma ka kirata.? Toh sunanta Suwaiba. Kanwar uwarka ko na ubansa da zaka kirata da Umma.?. Ka sake kiran mahaukaciyar nan Umma sai naci maka. Zo ka shige kafin Abbanka Ya k’araso.” Ta k’arashe tana janyo Hilal yana tirjewa haka Har ta shigar dashi cikin gidan ta janyo k’ofa tana fad’in masu gadi kar su bari Suwaiba ta zo koda kusan gate din ne.
Mamaki Ya cika Hilal. Shi Ya kasa gane wann irin al’amari ne wann da kuma abindake tsakanin mahaifiyarsa da da Umma.
After some hrs da faruwan hakan. Tsaye yai bayan mahaifiyar tasa sanda take lek’e daga window ko zata hango Umma. Cikin zuciyarta tana addu’an Allah yasa mayyar ta tafi dan bata fata mijinta ya dawo ya tadda Suwaiba kofan gidan balle asirinta ya tonu.
Ya girgiza kai kad’an yana kuma takowa kusan mahaifiyarsa. Aiko a firgice ta juyo tamkar maras gaskiya. Ta dafe k’irjinta tana fad’in “Haba Hilal, halin Anisa na lab’e ka koya kaima. K’iris zuciyata bata buga ba.” Ta k’arashe har lokacin hannunta dafe da k’irji. Sai kuma ta canza maganan da fad’in “Lek’e nake naga ko Abban naka Ya iso.. Gashi dai da alama har yanzu bai iso ba.. Lallai da alama zai dare.” Ta kuma duban Hilal tana tsimewa “Waima mai ya shigo da Kai nan ne. Mai kake nema.?”
“Dama na shigo ne na fad’a Miki zan d’an kwanta kafin la’asar tinda naga har yanzu Abban bai iso ba.”
Ta jinjina Kai tana dubansa “Idan ya iso zan tada Kai.” Ta fad’i tana nufan k’ofa yayinda Hilal ya take mata baya.
*
Fitowan Hilal sallar la’asar bayan an Ida sallah a masallaci a hanyar sa ta dawowa gida ya hangi Umma tana sallah jikin wani gini dake manne da karantar gidansu. Kasancewar akwai interlocks wajen. Mamaki ya cika Hilal. Ikon Allah yanzu dama ashe matar nan bata tafi ba. Lallai ba k’aramin Abu ya zaunar da ita ba.
Ya k’araso gefenta daga can ya tsuguna kan k’afafunsa har ta Ida addu’arta. Hilal ya tayata shafawa.
“Umma.” Ya ambaci sunanta daga nan yanda yake tsugune kaman dai yanda yaji Khulsum na kiranta.
Umma ta d’ago ta dubesa sai ta sakar masa murmushi “Hilal d’an albarka.” Ta fad’i tana dubansa dan bazata tab’a mance alkhairan yaron ba koda kuwa ita mahaifiyarsa suna buga dabi. Kaman yanda nata yaran basuyi halinta ba haka zalika Hilal baiyi halin mahaifiyarsa ba a cewarta.
Hilal ya gaisheta kafin ya k’arada “Umma mai kikeyi a nan.? Mai ya zaunar dake nan.?” Ya dan numfasa kiyi hak’uri da tambayar da zan Miki “Shin akwai wani matsala ne tsakaninki da mahaifiyata.? Meke faruwa tsakanin ku biyun.?”
Umma ta girgiza Kai kad’an “Babu komai Hilal. Amma Kai hakuri bazan bar k’ofar gidan nan ba har sai mahaifiyarka ta saurareni.”
Hilal ya zuba ma sarautar Allah ido yana tuno yanda sukai da Amminsa. Ya d’an kuma girgiza Kai “Amma.. Kiyi hak’uri da tambayarta da zan Miki.. Wani abu ne kike nema wajen mahaifiyata.? Ki sanar dani dan Allah idan wani Abu ne da zan iya taimakawa.”
Umma ta kuma murmusawa “A’a Hilal. K’arshen abinda zanyi shine na saka ka cikin matsalolinmu. Kai d’in kanada zuciya mai kyau. Ina rok’on Allah yasa D’anuwanka dake auren Ummul d’ina ya zama mai kyaun hali da d’abi’u irin naka..” Ta k’arashe cikin rawar murya irin na mai kuka hawaye na gangaro mata dan a koda yaushe cikin tunanin Ummul d’inta take da halinda zata iya kasancewa ciki. A gaggauce tai k’ok’arin goge fuskarta kafin ta kuma duban Hilal tace “Mahaifiyarka nake son magana da, sabida wajenta nazo. Domin dani da mahaifiyarka munada alak’a mai kyau.” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta.
Mamaki ya kuma cika Hilal. Kansa ya kuma k’ullewa. Tabbas wad’ann mata wato Amminsa da Umma al’amarinsu abin dubawa ne sann yanada rikitarwa. A b’angare guda mahaifiyarsa tana ikirarin datse alak’a da Umma da ahalinta. A b’angaren Umma tana fad’in itada mahaifiyarsa sunada alak’a mai kyau. Shin na waye zai d’auka cikin su biyun.?
Juyin duniya Hilal yayi Umma ta hakura ta koma gida amma fir fir tak’i ta kafe lallai lallai sai Asshe ta saurareta. Ganin yamma nayi yasa Hilal d’aukan mota ya fice daga gidan. Dan yasan watak’ila maganarta kawai Umma zata saurara ta amince ta bar k’ofar gidansu.
A bakin ward din ya hangeta tana k’ok’arin shiga. Sauri sauri ya k’arasa ya cimmata.
Kaman Wanda aka jefo shi haka Khulsum taga Hilal gabanta.
Da mamaki take dubansa.
“It’s a good thing that I found you here. You need to come with me.” Abinda kawai Hilal yace kenan.
Khulsum ta girgiza Kai cikeda mamaki “Malam lafiya.?”
Yai gajeren tsaki “Wai ke ko yaushe haka kike ne. Abun fad’a baya Miki kad’an ne.?” Ya kuma girgiza Kai “I need you to come with me right away. And please you alone. You don’t need to inform that aunt of yours… She might stop you.” Dan bai mance ba kwanakin can da suka shige ita ce ta hana Khulsum bin Umma Akan idonsa. Daga haka sa Kai yai ya soma tafiya yana fad’in tai sauri ba lokaci.
Takaici ya cika Khulsum, mai wann D’an rainin hankalin ya d’auketa da zaice tazo ta bisa. Ina ma zata bisa.? Mai ya maidata.?
Ganin ya soma tafiya ya nufi mota yasata bin bayansa da sauri tana fad’in “Kai Malam.. D’an dakata.? Kana tunanin kai waye.? Mai ka d’auke ni.. Mai ka maidani da zaka tako har yanda nake kace nazo na bika kuma kar na sanar da Innata.. Ce maka akai..”
Bata Kai aya ba Hilal ya kaikaito yana dubanta cikeda takaicin kuskuren fahimtar da tai masa “Hey cut it out will you.!” Ya katseta da fad’in haka kafin yaci gaba “Seriously, is that what you think of me.?” Har lokacin da mamaki yake dubanta kafin yaci gaba “If that’s what I wanted I’d have gone straight to a hotel or club, and not a hospital.” Ya dan girgiza Kai “Look, ni ba irin wad’ann mutanen bane. And I’m not kidnapping you.. Idan na zo nan kawai nazo ne sabida mahaifiyarki dake zaune k’ofar gidanmu through out the day. Idan Ammi na ta fito ta taddata wajen it would be a disaster. Idan akwai girman mahaifiyarki da kike gani kike ji a cikin Zuciyar ki koda kad’an ne zaki taho tare Dani dan na tabbata ke zata iya sauraronki.” Ya k’arashe yana bud’e motar.
Jikin Khulsum yai sanyi ta dubesa da mamaki “Umma ce take k’ofar gidanku.?”
Hilal ya zuba mata ido yana dubanta. Baice komai ba sai tada motar da yai “Zakije ne ko nai tafiyata.?”
Ta hareresa sai kuma tai still a wajen kaman mai tunani. Shin ta sanar da Inna Dije ne.? Toh amma idan ta sanar da Innah Dije wani wutan zata kunna tinda tasan Ummanta da Inna Dije basa jituwa. Sann Inna Dije zata iya hanata zuwa. Tana tsaka da tunanin taji sautin horn ya cika mata kunne alamun Hilal na jiran decision dinta. Harara ta b’alla masa kafin ta bud’e marfin motar ta shige.
Ya soma driving babu mai ce da kowa komai cikin su biyun har suka iso k’ofar gidansu Hilal. Can Khulsum ta hangi Umma rakub’e jikin gini tana lek’en gate din gidansu Hilal kaman wata mabaraciya. Sosai abin ya mata ciwo ganin mahaifiyarta a haka. Hilal na Ida parking ta fito ta nufi Umma.
“Umma.!” Khulsum tace daga nan yanda take tsaye kusan Umma.
Umma ta d’ago tana dubanta. Khulsum tai saurin k’arasowa ta duk’a gaban Umma “Umma Mai kike a nan. Dan Allah mai kike haka a nan.? Umma wann fah zubda mutunci ne. Dan Allah ki tashi ki bar k’ofar gidan nan. Duba fah kiga mutane masu shigewa suna kallonki.. Umma dan Allah ki tashi haka nan.”
Hawaye Umma ta soma tana girgiza Kai “A’a Khulsum bani tafiya sai Hajiya Asshe ta sauraren.”
Khulsum ta juya ta dubi Hilal dake can jikin motarsa yana tsaye. Shid’in ma su yake duba. Ko ba’a ce ba damuwan halinda Umma ke ciki ne saman fuskarsa dukda baya iya sauraron mai uwa da ‘yar ke cewa.
Khulsum ta maidoda dubanta ga mahaifiyarta “Umma matar nan tareda ita ina nufin keda ita kuka k’ulla auren ‘Yaruwata. Bansan dalilinta na juya Miki baya ba. Bansan meye ku biyun kuka bisne ba. Bansan meye a tsakaninku ba. Amma ke mahaifiyata ce kuma bazan so ki walak’anta ba. Dan Allah Umma ko mai kike nema wajen matar nan kiyi hak’uri ki bar k’ofar gidan nan.”
Umma ta kuma girgiza Kai tana hawaye “Khulsum idan na tafi mai zanje nace da Tani. Na mata alk’awarin zan nemo kud’ad’en belinta. A nan ne kawai nake da yak’inin zan samu kud’in fiddo Tani Khulsum.”
Baki sake Khulsum ke dubanta. Da mamaki tace “Umma wai dama kan kud’ad’en belin Mama kike nan.?”
Umma ta jinjina mata Kai alamun eh.
Shiru Khulsum tai na d’an lokaci kafin ta dubi mahaifiyar tata tace “Umma kece zakiyi belin Mama. Wai Mama Tani dai da ta saida shagon Abba.?”
Umma ta kuma jinjina mata Kai “Dukkanmu masu kuskure ne Khulsum. Tani ta salwantar da dukiyar Malam ni kuma na salwantar da rayuwar ‘yarsa. Cikin mu biyun idan akwai Wanda tafi girman laifi toh ni ce Khulsum. Ni yafi cancanta na tafi gidan kasu ba Tani ba. Idan har zan zuba ido ni ina shak’an iskan ‘yanci yayinda Tani ke gark’ame kurkuku bana tsammanin nayi ma kaina adalci. Sann bana jin ‘yancin iskan da nake shak’a a mak’oshi na. Tani ta tuba Khulsum. Dukanmu mun gane kurakurenmu. A halin yanzu bamuda wani buri da ya wuce mu koma ga mijinmu mu kula dashi mu masa jinya mu samu aljannarmu.” Ta k’arashe cikin rawar murya irinta mai kuka.
Jikin Khulsum yai sanyi. Tasan mahaifiyarta tanada zuciya mai kyau Wanda da yawan mutane suna amfani da wann damar su shashashantar da ita. Kaman dai yanda takeda kokonto Akan tuban Mama Tani. Dan tasan kad’anda aikin Mama ne ta shashantar da mahaifiyarta ta samu ta fito daga prison.
Muryar Umma ta kuma sinkayo sanda ta tallafo fuskar Khulsum d’in cikin zuban hawaye take fad’in “Nayi kewarku Khulsum daga ke har ‘yaruwarki. Ina zaman kad’aici a gidan.. Babu ke.. Babu Ummulkhair.. Babu mahaifinku.. Tani ma bata nan.” Tai shiru tana tinanin daga ita sai su Azeema Wanda suka maidata wofi cikin gidan barikinsu kawai suke bugawa. Su fita sanda suka so su dawo sanda suka so. Idan tai masu abincin da bai musu ba su mata tatas. Har wankin kaya Badia ke sakata. A cewarsu idan batai ba zata fice ta bar masu gidan uba tinda gidan na ubansu ne.
Ganin tayi shiru ta tsunduma tunani yasa Khulsum kamo hannayenta “Umma.” Ta kirawo sunan Umman a hankali.
Umma ta d’ago tana duban Khulsum.
“Zaman kad’aici yasa kike so ki fiddo Mama Tani.?”
Shiru Umma bata ce komai ba sai hawaye dake kuma gangaro mata.
Khulsum ta janyo mahaifiyarta ta rungume sai dukansu biyun suka fashe da kuka.
Cikin muryar kuka Khulsum ke fad’in “Umma kiyi hak’uri ki koma ki zauna. Nayi ma Abba alk’awari bazan sake barin kusansa ba bayan abinda ya faru.” Cikin rawar murya taci gaba da fad’in “Umma ba zama da Inna Dije na zab’a ba. A’a zama da Abba na na zab’a. Inna Dije bazata kuma barinki kije kusan mahaifina ba Umma. Zanfi kowa so naga ahalinmu ya kuma cika amma a halin yanzu Abu ne mai matuk’ar wuya Umma. Ki koma kici gaba da addua ma Abba har Allah ya bashi lafiya iyakacin soyayyar da zaki nuna masa kenan a halin yanzu. Da sannu Allah zai duba Zuciyar Wanda yai tuba na gaskiya ya yaye masa matsalarsa kinji Umma na.” Ta k’arashe cikin rawar murya.
Umma ta shiga jinjina mata Kai a hankali har lokacin tana hawaye. Cikin zuciyarta kaw cewa take ita kanta bazata so ta bar Malam k’ark’ashin kulawar Dije kawai ba. Gwara ace Khulsum d’in na tare dasu. Zatai hak’uri kuma zataci gaba da addua kaman yanda ‘yar nata ta shawarceta.
Hannunta Khulsum ta kamo suka nufo Motan Hilal. Hilal na ganin su ya isa ya bud’e back seat Khulsum suka shige tareda Umma hannayensu rik’e cikin na juna suna Jin d’umin juna da suka jima basu samu hakan ba.
Ta mirror Hilal yake dubansu yanda suka shige jikin juna. Kan Khulsum na kwance gefen kafad’an mahaifiyarta yayinda Umma ta rik’e hannun Khulsum d’in k’am cikin nata tamkar kar wani Abu ya rabasu. Murmushi ne yaji out of nowhere na zuwa fuskarsa. Shi a duniyar sa duk yanda yaga shak’uwa da soyayya mai tsafta tsakanin iyaye da ‘ya’yansu ba kowa yake hasashowa ba face D’an Uwansa Haidar. A kullum addu’arsa kenan yaga irin wann bond d’in tsakanin Haidar da iyayensa.
Har gida Hilal ya kawo Umma. Khulsum ta fito taima Umma rakiya zuwa cikin gida ta kuma tausarta had’ida kwantar mata da hankali amma fah dukda haka bata ji cikin zuciyarta zata iya baro Abba ta dawo ta zauna da Umma musamman idan ta tuna abinda matan Abban nata suka masa.
Tana fitowa ga mamakinta ta tadda Hilal na nan na jiranta.
Daga can yanda take tsaye ya zuba mata “Rankidad’e jirana ake gida muje mana.”
Ta had’e fuska sosai “Toh ce maka nai ka jirani. Kai tafiyarka mana.” Tace tana canza hanya.
Furzar da huci yai kad’an ga wayarsa da ta kasa shiru sakamakon kira da Mahaifiyarsa ke jero masa. Yasan bazai wuce Abbansa ne ya iso ba. Baisan mai zaice mata ba dan shi dai bai iya k’arya ba amma muddin ya sanar da ita Umma ya kawo gida ya taro match ne tsakaninsa da Ammi.
Ya k’arasa da mota gaban Khulsum yai rolling glass “Zaki shiga ne ko sai na fito na shigar dake da k’arfi.? Be thankful, albarkacin Umma kikace idan na maidake.alk’awari na daukar mata zan maidaki yanda na d’aukoki.” Yace a mugun tsare.
Khulsum ta dubesa dan yanzu gadararsa da k’arfin halinsa ya daina bata mamaki. Bata son dogon hira dashi dan kaf zuri’arsu haushi suke bata. Sann ga magarib ya k’arato hasalima batasan yanda za’ai ta koma ba tinda ba kud’in abun hawa wajenta. Ta kauda fuska gefe cikeda takaici zata bude backseat ya saka motar a lock.
Fitowa yai daga mazauninsa yana fadin “You must be kidding. D’azunma albarkacin Umma kikaci na barki kika zauna baya.” Ya bud’e mata front seat “Shige muje.”
Ta hararesa kafin ta shige.
Tana shiga ya sakar mata murmushi had’Ida kashe mata ido kafin ya zaga ya shige. Takaici ya kuma cika Khulsum.
Suna tafe babu mai cewa komai. Khulsum ta saci kallonsa. Yanzu wai godiya ya kamata ta masa ko hakurin kuskuren fahimtar da tai masa zata basa.? Kai ina ita dai bazata basa hakuri ba dan bataga laifin da tai masa ba. Ta saci kallonsa suka had’a ido.
Sai ta wayance dan bata so ya fahimci tana dubansa. tai kaman bata kalli b’angaren da yake ba. Saida tai gyaran murya da kyar kafin tace “Idan kana jira na baka hak’uri ne kan abinda ya faru ni dai bazan baka ba. Abinda Kai kuma shima Kai ka saka kanka shima bazan maka godiya ba.” Ta k’arashe tana kauda fuska.
Hilal ya murmusa “Guilty conscience.? Kar ki damu na yafe miki.” Yace idonsa naga kwalta.
Bata amsa shi ba sai kuma tace “Toh mai za’a tsammata daga wanda yake sallah babu alwala.?”
Ya kuma murmusawa “Allah yasa dai ba kece mai karb’an tuba ba balle ki k’i karb’an nawa tuban.”
Ta kuma hararsa “Ka fad’a ma wann D’anuwan naka mai sallah babu alwala ‘Yaruwata musulma ce bazata zauna dashi ba. Ni Khulsum sai na datse wann auren.”
Hilal ya jinjina Kai “Why not ask your sister to tell him. After all su biyun sunfi kusa a halin yanzu.”
Ya d’an dubeta a kaikaice kafin ya k’ara “And remember they say, Wanda ya shiga tsakanin mata da miji shi zaiji kunya.”
Ta hareresa musamman da taga murmushin dake bisa fuskarsa.
Yana ida parking tasa hannu ta bude marfin motar a fizge ta fice. Ko kallon yanda yake bataiba balle tai masa sallama balle ya samu arzikin godiya.
Bayanta yabi da kallo yana murmushi. Cikin zuciyarsa yake jin yanzu yanada k’wakk’waran dalilin da zaisa ya k’ara delaying lokacin komawarsa makaranta koda hutunsa ya k’are. Bazai tafi ba har sai ya tabbata baida wani pending matters. Saida ta b’ace ma ganinsa kafin yaja motarsa ya bar wajen.
**
Cuba…
Waya manne b’angaren kunnensa na dama. Dareen na hankalce dashi tinda ya soma wayar.
Daga d’aya b’angaren Hisham yaci gaba “You know I still can’t get over her. I don’t know why.. But I find it difficult to forget about her. Dukda cewa mun hadu ne na d’an wani lokaci. Nayi tunanin zan cireta a zuciyata cikin sauk’i kaman yanda na cire sauran. But then I realise she’s different. So different.” Ya d’anyi fasali “Haidar na kasa hana zuciyata tunanin matar wani. I dream about her every night. And worse part d’in shine zuciyata tak’i ta karbi k’addaran. Haidar ji nake zata dawo gareni.. Astagfirullah.” Ya k’arashe jikinsa duk a mace.
Sosai Haidar yaji tausayin abokin nasa. Shi ire iren abun nan ba layinsa bane. Hasalima bai tab’a soyayya ba. Dareen ma bazaice ga yanda akai har ya fara sonta ya aureta ba. So baisan wani shawari zai ba ma abokin nasa ba. Ya d’an numfasa kafin yace “Just.. Just try to distract yourself.. Engage in activities that require your full attention… Like work.. Zaka gani in no time zaka mance da ita. And you’ll find someone better than her.”
Hisham ya d’an furzar da huci “What if my mind gets stuck here Haidar.? What if I couldn’t move on.? What if banida wani future dangane da abinda ya shafi Aure.? What if this is my destiny.?”
Haidar yai shiru cikin sanyin jiki ba tareda ya iya cewa komai ba.
Hisham yai murmushi mai ciwo “Sorry I shouldn’t be telling you all this. Kayi tafiya ne dan ka rage damuwar dake kanka bai kamata na k’ara maka da nawa ba. Anyways, I guess this is life for us. Ba ko yaushe muke samun abunda muke so ba.” Ya d’an murmusa kafin yace “Let’s talk business maybe this will keep me busy.” Yai maganar da gajeren murmushi kafin yaci gaba “Ya kamata ka dawo haka work is getting hampered because you are not here. Komai so yake ya tsaya. And kasan lokaci baya jiranmu.”
Ya d’anyi gajeren tsaki “I’m still on my vocation. Zanje Pennsylvania daga nan.”
Daga d’aya b’angaren Hisham Ya girgiza kai “Wai kana nufin hutun naka bai k’are ba.. Ko wani business d’in kakeda a can US d’in.?”
Gajeren tsaki ya kuma yi “Ka kira ne dan ka bani haushi.? What business kuma.?”
Hisham Ya murmusa kad’an “Alright fine. Yanzu dai Ya kamata ka dawo. Kaga we need to meet up. Ina nufin our team members. We’ve got a lot of things to discuss.”
Tsakin ya kuma yi dan ya kula da gangan Hisham ke son tunzirashi “Maiyasa zan dawo. Mai zan dawo na maka when you can schedule a zoom meeting. I just hope ba shirme da shiririta bane cikin meeting d’in ba. Because you know my time is precious.”
Hisham ya murmusa kad’an “Look Haidar, you and I both know dawowarka nada mahimmanci. Magana muke kan project d’in da bamu tab’a handling babba kaman shi ba. Kuma a matsayinka na Wanda ragamar kula da aikin ke k’ark’ashin ka ya kamata ace by now ka ziyarci site not just once or twice. Cikin k’ank’anin lokaci zamu fara. Sann any moment any time Dad dinka zai iya dawowa k’asar nan. Mai kake tunani idan ya dawo Ya tadda baka nan.? The story will definitely change. And all our hard workings will go to waste.. Haidar you need to forget about your tour to America and come back as soon as possible.”
“I don’t take orders from you Hisham. Let Aliyu Maitama do his worse. I do not give a damn.!” Yana ida fad’in haka ya katse kiran kafin yasa kai ya fice cikin huci saikace Hisham d’in na ganinsa. Zuciyarsa na masa zafi dik sanda aka ambata masa mahaifinsa. Sunan da dik sanda aka ambata sai yaji k’una cikin zuciyarsa at the same time babu yanda ya iya wann sunan dai yake amsawa. Babban kuskuren da mahaifiyarsa Tai shine saka masa sunan wann mutumi da Tai Wanda duk duniya babu Wanda Ya tsana sama dashi.
Dareen ta fito daga mab’oyarta tana bin bayansa da kallo Har ya b’ace ma ganinta. Zama tai tana k’ok’arin figuring out maganganun da taji ya tattauna cikin waya.
A b’anegarn Haidar kuwa can bakin beach yaje ya zauna tunanin duniya na damunsa. K’iyayyan mahaifinsa ne zalla cikin zuciyarsa. Lokaci guda maganganun Hisham na yawo a kwanyarsa. If he wants to take his Dad down dole yaje yayi aikin koda baya son komawa. Rashin komawarsa na nufin zai iya rasa chance d’insa na k’arshe akan mahaifinsa. Dan kaman yanda Hisham yace ne idan har Dad d’insa ya rigashi komawa Nigeria toh fah zaiyi replacing d’insa da wani ne. He promised to make his Dad swallow all his words sann baya jin zai janye wann k’udirin nasa.
Gajeren tsaki yai yana tunanin abun yi. Mommy ce ta fad’o ransa. Yai scrolling kan sunanta. Kaman mai tunanin wani abu ya jima sosai kan lambarta had’ida k’ura ma sunanta ido. Saida ya furzar da huci kad’an dan baida wani option kafin yai dialing layin.
Sunanta Ya fara ambata tana d’aga wayan in the way he does sanda yake k’arami. Sai Mommy taji hawaye ya ciko idonta. Idan Ya kirata da wann sigan lokacin k’uruciyarsa ta kullesa ne a d’aki taurin zuciyarsa bazai bari Ya rok’eta ta bud’e sa ba sai ya ambaci sunanta da wann sigan. Tai k’ok’ari Tai ta maza ta share hawayen da suka gangaro mata “Haidar ina ka shiga tsawon sati biyu.? Mai kake nufi Dani Haidar..? Mai kake nufi da Amaryarka dake zaman jiranka tsawon sati biyu. Shin ka cika alk’awarin da ka d’aukar min.?”
Da ta ambaci amaryarsa sai yaji abun Ya masa wani banbarak’wai. Girgiza kai yai kad’an “Alk’awari d’aya na d’aukar miki Mommy shine bazan saketa ba sai ta cika wata uku kaman yanda yake a Yarjejeniyar. Amma ban miki alk’awarin zama da ita cikin watanni ukun ba.”
Mommy ta zaro ido waje kaman yana ganinta. Idan baizo ba ai Babu amfanin auren. Ya zama wofi kenan.
Katse shirun Tai da fad’in “A’a Haidar kar mu fara wann wasan dakai. I mean what about the project.? Muddin mahaifinka ya rigaka saka k’afa cikin gidan nan kasan sauran Haidar. All our efforts and sacrifices zasu tafi ne a banza . Haidar ka tuna na k’ulla auren nan ne dan mahaifinka ya amince ya baka project din nan.”
Katseta yai da fad’in “To hell with everything Mommy.”
Mommy ta mik’e tsaye tana jin zufa na keto mata. Sai muryarta Ya soma rawa “A’a Haidar.. Haidar kar kace haka.”
“You know what Mommy, you are too demanding. Yes na yarda zan auri yarinyar chan or whatsoever da kika kawo kika ce na aura because I wanted to manage the project. But zama tareda ita under same roof ban miki wann alk’awarin ba. It’s suffocating already da na amince da auren.”
Mommy taci gaba da girgiza kai jin duk sadaukarwan da tai da duk wasu k’ok’arin ta zasu tashi a banza. Sai ta soma hawaye “Yanzu da gaske ka hakura da aikin Aliyu.? Mai zai faru Dani Haidar.? Mai zai faru da nawa auren.? Yanzu bazaka amince da AUREN WATA UKU dan ceto auren naka mahaifiyar ba.”
Cikeda k’osawa yake tattare naman goshinsa “Quit the act Mommy. Your victim card won’t work on me. You brought this to yourself. You should blame yourself.”
Cikin kuka Mommy ke fad’in “Haidar cikin satin nan Mahaifinka zai dawo k’asar nan. Na tabbata idan Har ya rigaka dawowa zaka dawo ka tadda bana nan. Idan har ni na haifeka zaka dawo Aliyu.. Zaka dawo ka ceci Aurena kafin mahaifinka ya sauk’a k’asar nan..” Tana ida fad’in haka ta katse kiran ba tareda ta jira cewarsa ba.
Ya lumshe idonsa kad’an yana tuna mafarkin da yai tareda iyayen nasa a kwanakin baya.. Yai gajeren tsaki wani b’angare na zuciyarsa na fad’a masa mafarki is the opposite of reality. Ya kuma yin gajeren tsaki zuciyarsa na kuma tunzura shi gameda al’amarin iyayen nasa. Meyasa yakeji gaba d’aya shidai baida wani alk’ibla a rayuwarsa. Like his life’s a complete messed up. Baisan mai yake son yai ba. Baisan mai yake ji ba. A haka ya mik’e yana tafiya baisan wani direction zaibi ba.
**
Abuja..
Mommy yau din mafarki tai Haidar ya dawo suna zaune parlor Kansa kwance saman cinyarta suna hira na d’a da uwa da basu tab’a irinsa ba. Tinda tai wann mafarki ta tashi da farin ciki ga dukkan alamu shirinta mai tasiri ne Akan Haidar din. A b’angare guda ga Daddy ya mata waya ya sanar da ita nan da kwanaki biyu zuwa uku zai dawo da izinin Allah. Gaba d’aya sai tana ji kaman lokacin dunk’ulewar ahalinta ne yazo. Burinta yana gab da cika. Tuni tasa akai mata kiran Ummul ta sanar da ita Mijinta na nan tafe. Yacce kasan wacce takeda tabbacin dawowar Haidar d’in ta dauko mai gyara na musamman irin nasu na shuwa aka soma yi ma Ummul sabon gyara. Wani sabon kula na musamman Mommy ke bawa Ummul.
Hankalin Anisa idan yayi dubu ya tashi. Babu shiri ta fita ta nufi gidansu Leenah dan bazata iya kallon wann kayan tashin hankali ba. Bazata bari Haidar ya dawo gidan ya cimma Ummul ba.
Leenah ta dubeta a dak’ile “So da kika taso kika zo nan mai kike so na miki.?”
Anisa tace “Leenah let’s forget about everything. Nasan ban kyauta ba amma dole ce ta saka ni d’aura miki laifin. Da ace na d’auki laifin da yanzu bana gidan. Leenah I have no one to turn to but you. You just can’t abandon me you know.” Ta k’arashe tana duban kawar tata kaman zatai kuka.
Shiru Leenah tai na d’an lokaci kafin tace “Neesa I’m not doing this. I won’t allow myself to fall into your trap again. I’m not that stupid.”
Anisa ta kamo hannayen Leenah “Girlfriend please mana. Zamu bari wann low class d’in ta shiga tsakanin abotanmu ne.? Tayi mana guda biyu bazamu bari tayi na uku ba. Think, yanzu idan muka kyaleta ji zatai tayi nasara akanmu. And remember, we never back off for a fight.”
Shiru Leenah tai kafin tace “This is your battle Anisa. You should fight it alone.. Kin gane.”
Sai kuma ta faurzar da huci kad’an ganin Anisa ta tsareta da ido “Fine, naji.. What do I get in return dan wann karon shiri babba zamuyi wanda bazata iya tsallakewa ba.”
Anisa ta jinjina Kai tana murmushi “Idan har kika taimaka min na zama matar Haidar komai mai sauk’i ne Leenah. I promise not to let you end your life Washing clothes with bleach just to keep them white.”
Leenah ta jinjina Kai tana murmushi “Lokaci yayi da zakiyi abinda kike tsoro Anisa.”
Anisa ta dubeta cikin rashin fahimta “Kaman yaya..?”
Leenah tace “Your ultimate goal is to get rid of her for good. Right.?”
Anisa ta jinjina Kai “K’warai kuwa.”
Leenah ma ta jinjina Kai “Good..! Then make her disappear for good..”
Anisa ta kuma girgiza Kai “But how.?”
“Kill her Neesa.! Poison her once and for all.”
Anisa ta zaro ido waje “A’a Leenah.. What what if our plan fails again..? Kaman dai sauran..?”
Leena ta dubeta “Anya da gaske kin shirya Anisa..?”
Anisa ta dubeta a d’an tsorace “Mai a zai faru idan bataci poison din ba.?”
Leenah ta murmusa “Ba ko wani poison bane ake ci Anisa. Wani shak’ansa ake a iska. A hankali yake lalata lungs kafin a ank’ara sai gawan mutum. Kinga irin wann babu wanda zai zargeki.” Ta k’arashe da murmushi saman fuskarta.
Anisa ta murmusa “Yayi. Yanzu ya za’ayi mu samu.?”
Leenah ta murmusa “Wann mai sauk’i ne ki bar min komai a hannuna. Nasan kudi bazai zame miki matsala ba.”
Anisa taita murna tana mata godiya. Akan haka suka rabu washe gari suka had’u a mahad’a.
Leenah ta ciro wani mistitsin kwalba cikin jakanta ta mik’a ma Anisa. Anisa hannu na rawa ta amsa dan kwalban da wani ruwa mai kaman acid ciki.
Anisa na juya kwalban Leenah ke mata bayanin yanda zatai amfani dashi.
“Cikin turaren da take yawan amfani dashi zaki zuba kad’an. Muddin tana shak’an wann turaren bazata wuce kwanaki uku tana numfashi ba.”
Murmushi Anisa tai. Cikin zuciyarta take fad’in Yazo gidan sauk’i dan ta kula Ummul tana yawan shafa turaren humra da ta kai mata a kwanakin baya Wanda ta sauya turaren da Mommy ta bata dashi. Tabbas zata zuba mata a ciki.
Leenah ta dubi Anisa had’ida gyara zamanta “A baya nayi zaton Hajiya Kwaise bazata tab’a bari D’anta ya auro d’iyar talakawa ba. Nafi tunanin iyayen Haidar zasu nema masa aure ne daga babban ahali. A well known and influential family. Like business partners d’insu ko d’iyar manyan ‘yan siyasa kodai d’iyar masu mulki. Amma na sha mamaki yanda ta auro ma d’anta wann yarinyar.”
Anisa ta jinjina Kai “Ba ke kad’ai kike mamaki ba Leenah. Shiyasa zuciyata ke tabbatar min akwai wani Abu a k’asa k’ark’ashin wann auren. Massive love d’in da Mommy ke nuna ma yarinyar yafi komai d’aure min kai. Ko ni nan da nake tamkar ‘yarta sann mahaifina is a successful businessman banyi zaton zata bari d’anta ya kawo mata ni matsayin sirka ba sanin ko wacece ita. Nafi zaton zata tafi da nisa sai gashi ta k’are a ‘yar talaka. Ke da ganin wann al’amari kinsan akwai lauje cikin nad’i. And believe me I vow to find out whatsoever she’s hiding.”
Leenah ta jinjina Kai “Ta haka ne kawai zaki fahimci komai Neesa. Idan kika kashe yarinyar.”
Anisa ta jinjina Kai tana tabbatar da kalaman Leenar.
Daga bisani godiya tai ma k’awarta Leenah sukai sallama Leenah na fad’in sai taji result.
Koda Anisa ta koma gida cikin hikima da dabara ta zuba wann ruwan lungs poison da Leenah ta bata cikin turaren Ummul.
Ta dawo d’aki tai relaxing tana sakin murmushin nishad’i. Nan da kwanaki biyu zuwa uku mataalarta zai kaw. Saidai a fidda gawan Ummul daga gidan. Dan ta tabbata wann karon Ummul bazata haye tuggunta ba.
A fili take furta “Mommy ki gama duk wani shirin da zaki mata. Haidar gawar Amaryarsa zai dawo ya tadda.” Tana Ida fad’in haka ta fashe da dariya.
SameenaAleeyou📚
*AUREN WATA UKU..!*
*30*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
Tinda jirginsu tai landing a Nigeria Dareen ta rasa sukuni. Ta kula akwai mihimmin abinda yasa suka yanke hutun nasu suka dawo gida Nigeria. Toh amma rashin sanin mak’asudin dawowar tasu shi yafi komai d’aure mata kai. Da fari tayi zaton project d’insa yasa ya dawo amma daga bisani ta kula kaman dai abun nada alak’a da ahalinsa ne musamman ma mahaifiyarsa. Meyasa duk irin aikin da suka tabbata anyi kan Haidar d’in da iyayensa kaman bai wani tasiri tsakaninsa da mahaifiyarsa ba. Kaman dai Har yanzu shid’in koda bai nuna ba can k’asar zuciyarsa yana kwad’ayin Ya mata biyayya. Dan taga call history nasu a wayarsa shida mahaifiyarsa. Kuma tinda sukai wann wayar ya yanke decision d’in dawowa gida. Tabbas ya zama dole ta koma wajen Dodon kobuku ta sanar dashi halinda ake ciki. Tana so aimata aiki na musamman akan mahaifiyar Haidar wacce take ji a jikinta ita d’in nema take ta zame mata barazana. Sann wann zuwan da zatai bazata bari Shadow ya sani ba. Aiki ne da za’a mata ita kad’ai. Ya kamata ta saka rana ta tafi gida Ilorin dan ta gana da Dodo Kobuku. Ta k’arashe tunanin tana kallon fuskar Haidar dake kwance yana baccin gajiyan hanya. Fuskar tasa tayi fayau tamkar Wanda baida wata damuwa. Ta murmusa zallan k’aunarsa takeji na bin duk wani vein na jikinta. Ta Shafa fuskarsa a hankali. Can k’asar zuciyarta take furta ‘You are mine Haidar Maitama. Ni kad’ai na. I won’t allow anybody to come between us. Not Shadow, not even your own parents. Idan shiga tsakaninku is not enough zan b’ullo maku ta wani hanyar. Idan ta kama na kashe rai ne akan ka zan kashe. Koda mahaifiyarka ce dan na kasance dakai zanyi Haidar. Kaid’in nawa ne. Ni kad’ai.!’ Ta k’arashe tana tsura masa ido.
**
Tin farar safiya take gidansu Leenah, ta kasa zaune ta kasa tsaye. Zuciyarta ya cika da tsoron abinda ka iya zuwa ya zo. Yau kwanaki uku kenan da ta zuba poison din cikin turaren Ummul. Ta tabbata izuwa wann lokaci komai zai iya faruwa dan gaba d’ayan ranan ma bataji d’urin Ummul d’in ba. Ta dubi Leenah dake zaune hankalinta kwance tana kallon American movie ta k’araso ta zauna kusan Leenah zuciyarta sai tsinkewa yake “Hey.! What if she’s dead by now.? Ko kuma ta shirya min wani makircin tinda kinsan makira ce ta gaske..!” Anisa tace duk a tsorace.
Murmushi Leenah tai tana jefa popcorn a bakinta “You know what Neesa, you should stop being paranoid idan ba haka ba a banza zaki sa ko wani Abu ya sameta a zargeki. And if that happens believe me I won’t come to your aid. So ki kwantar da hankalinki ki tashi ki koma gidan ki tabbatar da abinda ya sameta.” Ta k’arashe tana duban Anisa.
Jikin Anisa har lokacin a mace yake sanin ko wacece Ummul d’in tinda ta tsallake tuggunsu har guda biyu. Idan ta tsallake wann din ma ba abin mamaki bane. Babban abinda yafi bata tsoro shine wann ya k’unshi kisan kai ba kaman sauran ba. Bata kuma cewa komai ba sai zama da tai can gefe tana ci gaba da tunanin abin yi. Dan tsoronta d’aya ji take kaman idan ta koma gida Ummul zata kamata, reshe zai kuma juyewa da mujiya kaman ko yaushe. Da kyar ta iya tashi tai Sallama ma Leenah ta nufo gida duk jikinta a mace.
Daga can nesa tai tsaye tana hangen sashen Ummul amma bata shiga ba dan har lokacin zuciyarta bai daina bugawa ba. Sauri sauri ta nufi nata d’akin tana tambayan maids ko Ummul ta shigo. Nan wata maid ke sanar da ita bataga shigowarta ba. Da haka Anisa ta nufi d’aki duk a tsorace take. Tana shiga ma kwanciya tai saman gado ta sanar sa maid d’aya ko Mommy ta neme ta tace mata ta dan kwanta bata Jin dadi.
Kwanciyarta da kad’an ta hango mota bak’a k’irar Mercedes GWagon. Gabanta yai wani irin tsinkewa dan wann motar tasan ta Haidar ce. Yaushe Ya dawo.? Da gaske shine ciki.? Kodai idonta ne ke mata gizo.? Da gaske Haidar ne Ya dawo.? Take taji jirin gaske na neman kada ita sanda ta diro daga saman gado. Ta isa jikin window a guje dan tabbatar ma idonta.
Shid’in ne dai looking handsome as always a cewarta. Gani tai ma ya k’ara k’warjini da kyau. A hankali ta furta “Haidar… Mai ka dawo yi..? Meyasa bazaka jira ta cika ba.? Meyasa zaka dawo yanzu..?” Ji tai tana son sanin halinda Ummul ke ciki kafin Haidar Ya cimmata. Sauri sauri tai nufin fitowa daga d’akin sai kuma taja ta tsaya kaman wacce ta tuna wani abu zuciyarta na kuma bugawa. A hankali ta koma da baya ta zauna zuciyarta bai daina bugawa ba.
A b’angaren Haidar kaw tsaye ya hange mahaifiyarsa gaban tsohon hotonsu Wanda akai tun yana k’aramin yaro d’an shekara 10 Wanda bayan shi baya tunanin sunada wani family picture tare.
Hawaye take tana Shafa hoton, at same time tana ci gaba da furta “I want nothing but the best for you.. I know I’ve never been a good mother to you.. But please give me a chance Haidar.. Ka bani dama na gyara kurakuran da nai a baya. Just this once..” Kuka ya hanata ci gaba da magana.
D’an kauda fuskarsa yai cikeda k’osawa dan yasan hakan bazai wuce d’aya daga cikin acting d’inta ba. Yasan bazai wuce ta hangi motarsa ne ko taji shigowarsa shine tazo gaban picture d’insu take wann wasan kwaikwayon nata in order to gain his sympathy.
“Nice performance Mommy.! I’m here already. I guess the show is over.” Yace yana k’arasa shigowa parlorn.
Mommy ta juyo cikeda mamaki tana dubansa. Ta kuma mutsuka idonta. Sai taji murmushi na zuwa saman fuskarta.
“Haidar.. My Son..!” Ta furta cikin rawar murya hawaye basu daina ambaliya a fuskarta ba.
Sai Ta isa da sauri ta rungume shi kukanta na k’aruwa. Tsam ta rik’e sa cikin jikinta. Tana hawaye take furta “I knew it.. I knew You’d come back to me.. To your family. Nasan zaka dawo garemu Haidar.. Nasan bazaka bani kunya ba. Sabida kai d’in D’ana ne..”
Duk sunbatun nan da take ji yake ta cika masa kunne. Yai k’ok’arin cireta daga jikinsa da k’arfin gaske.
“Don’t get it wrong Mommy. Idan na dawo na dawo ne kawai sabida project d’in amma ba sabida ke da k’udirinki ba.” Yace yana duban mahaifiyar tasa dake tsaye gabansa tana kuka cikin sanyin jiki.
Mommy ta jinjina kai “Even so Haidar. I’m glad ka dawo sabida project d’in. Nafi kowa farin cikin dawowarka. Your wife is waiting for you Aliyu.. She’s been waiting for you for the past two weeks..”
Bata kai aya ba suka soma sinkayo hayaniyar wata ‘yar aikin gidan tana ihu tana kiran Mommy.
Gaba d’aya Haidar da Mommy suka juyo a tare sanda maid din ta shigo tana haki.
Anisa da hayaniyar ya sanyata fitowa ba shiri ita ta tari maid din da tambayar meke faruwa ta shigo haka tana ihu.
Cikin haki take sanar dasu ta shiga kai abinci section d’in Ummulkhair amma ta tararta a kwance lifeless.
Mommy da taji batun bagatatan saurin k’arasowa tai tana jijjiga mai aikin tana tambayarta mai take cewa. Mai aikin ta kuma nanata binda tace.
Babu shiri Mommy ta fice ba tareda ta bi takan kowa cikinsu ba ta nufi sashen Haidar.
Yayinda Anisa taji kama an yaye mata duka damuwarta. Daga k’arshe dai burinta Ya cika.
Yanda Mommy taga Ummul kwance k’asa tamkar maras numfashi sai ya kuma gigitata. Ta shiga jijjigata tana ambaton sunanta.
Mik’ewa tai cikin kuka tana fad’in ma’aikatan gidan su kira ambulance amma kafin tai wani aune sai ganin Haidar tai ya ciccib’i Ummul d’in Ya nufi motarsa da ita yana Anisa ta isa ta bud’e mata bayan motar.
Mommy ta biyo bayansu cikin sauri Har lokacin hawaye take.
Anisa jikinta duk a mace ganin Haidar ya d’auki kucakar nan ya sakata motarsa harma cewa yake ta bud’e masa motar. ‘Kan uba toh wllhi ka d’auki wofi domin kuwa fanko ce wajen gawa ce Babu rai.’ Ta fad’i haka cikin zuciyarta.
Mommy ce ta shiga bayan motar ta d’aura kan Ummul saman cinyarta yayinda Anisa tai maza ta shige gaban Motar Haidar ke driving.
Yanda hankalin Mommy ya tashi dole ta baka tausayi. Dan kuka take da gaske tana fad’in Ummul ta tashi kar ta tafi ta barsu ga mijinta Ya dawo gareta.
Daga Anisa Har Haidar d’in sumbatun Mommy ya cika masu kunnuwa cikin motar. Allah Allah suke a isa asibiti ko sun huta da sunbatun Mommy.
Suna isa Ya kuma d’aukanta suka nufi cikin asibitin da ita. Take Likitoci suka amsheta aka nufi ER da ita.
Nan suka zauna suna jiran ba’asi daga Drs. Har lokacin Mommy kuka take yayinda Anisa ke addu’an Allah yasa a fito da sakamako mai dad’in sauraro a kunnuwarta ma’ana ta mutu.
Ganin Mommy bazata daina kuka ba yasa Haidar mik’ewa Ya zira hannayensa cikin aljihun wandonsa. Kukan da Mommy take irritates him musamman idan yaji tana ambaton yarinyar ta tashi mijinta ya dawo gareta. Gaba d’aya ji yake zuciyarsa a cunk’ushe. Meyasa ma bazai tafi ba.? Zaman me yake a asibitin.? He did what he had to do sanda yaga yarinyar kwance lifeless. Ya kawota asibiti. Toh zaman mai zaici gaba da yi.? Yai gajeren tsaki sanda ya kuma duban Mommy dake ci gaba da matsan hawaye. Wani b’angare na zuciyarsa na sanar dashi ka zauna ko dan mahaifiyarka. Ya kuma yin tsaki wai shi Haidar ke yin abu dan mahaifiyarsa matar da bata da wani buri bayan taga ta k’untata masa. Ya kuma yin gajeren tsaki yana mai duban k’ofan ER din.
Can gefe ya matsa dan baya son sauraron kukan da Mommy take.
Anisa sai satan kallonsa take da duk wani motsinsa.
Wayarsa ce ta soma ruri Ya fito da ita daga aljihu nan yaga Dareen ke kiransa. Bai amsa ba sai Ya maida wayar aljihu Har ta k’arashi ringing d’inta.
Hankalin Anisa sosai ya kuma tashi ganin Haidar baibi takan wayarsa ba sann ga damuwa k’arara Ya nuna saman fuskarsa. Mai hakan yake nufi .? Ba dai Haidar damuwa yai da wann kucakar ba Wanda ko wayarsa Ya kasa amsawa. Dan ita duk a nata tunanin damuwar halinda Ummul ke ciki ne ke d’awainiya da Haidar d’in tsaban abinda ta raya ma ranta kenan. Zuciyarta sai wani irin k’una yake mata tana ci gaba da addu’an Allah yasa a fito masu da gawan Ummul kowa ya huta.
A can gidan Haidar d’in kuwa hankalin Dareen yayi dubu Ya tashi. Haidar d’inta ne ke ignoring calls dinta yau. Mutumin da ko important meeting yake zai excusing kansa ya d’aga kiranta musamamn da taga an d’auki lokaci bai returning call din ba. Ita kad’ai sai safa da Marwa take tana jin zuciyarta na mata d’aci. Tana a haka taga wayan Shadow na shigo mata.
SameenaAleeyou📚
