Auren Wata Uku Page 14-20 complete na Sameena Aleeyou

*AUREN WATA UKU..!”*

*14*

*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*

Mommy ta kuma duban Daddy Wanda fitowarsa kenan cikin shirin fita Squash game. Hannunsa rik’e da jakan kayan motsa jikinsa d’aya hannun Racket ne na buga wasan. Sunada private court d’insu da suke bugawa da abokansu. 


Ta d’an sauk’e ajiyan zuciya a hankali “Engr, kan maganar namu..? Nasan idan har na bari sai ka dawo ce min zakai ka gaji.” Ta k’arashe da d’an shagwab’a cikeda kissa.


Tab’e baki yai kad’an had’ida girgiza kai “Kwaise I thought mun gama magana. Kinga wann D’an naki na cire hannuna cikin rayuwarsa. So yayi aure ko kar yayi aure is non of my business. The only thing I care about is my company tareda ci gabanta.. “ Har ya d’an soma tafiya ya juyo “My tea should be ready kafin na dawo.. Please.” Ya k’arashe yana mai ficewa. 


Mommy ta furzar da huci tana girgiza kai “A’a Kwaise bazaki karaya ba. You need to do this.. You must.. Ya zama miki dole. Ta k’arashe tana neman layin Asshe. 


Shi kuwa Daddy zaune suke a court d’insu shida Alhaji Gimba suna hutawa daga motsa jikin da sukai. 


Alhaji Gimba Ya d’an girgiza kai kad’an “Engr Ya kamata kaji maganar iyalinka.. Nima na jima da wann tunanin, inaga Aure shi ya kamata a masa.. Shi zaisa ya tara hankalinsa waje d’aya. Kasan meye idan bazaka iya zuwa ka nemar masa Aure ko ka karb’ar masa ba. I can represent you then. Zaka iya wakiltani nai komai ma Haidar. After all, nima uba ne a gare shi.”


Daddy ya d’an dubesa, baice komai ba saima k’ok’arin bud’e bottle water dake cikin hannuna da yake. 


**



Washe gari Umma ta karya da karin kumallo mai kyau. Ga kaya na alfarma da Asshe ta aiko mai aiki ta kawo mata. Tai wanka ta cancand’e cikin atampar da bata tab’a mafarkin saka irinta ba. Ta dubi kanta jikin madubi tana mamaki. Ta mik’e ta shiga zaga d’akin ta yaye lalube tana kallon kyaun gidan da aka sauk’eta. 


A haka Asshe ta shigo ta taddata. Ta saki murmushi tana dubanta “Maman Ummul har kin shirya abinki… Na aiko Marka ta tambaya ko akwai abinda kike so..” Tai maganar tana shigowa d’akin.


Umma ta girgiza kai tana washe baki “A’a babu abinda nake buk’ata.. Kin ganni na d’age labule kallon Aljannan duniya nake. Ire iren gidajen nan saidai kaita hangosu daga kwalta ashe Inada rabon bacci cikinsu.”


Asshe ta murmusa tana jinjina lamarin Umma “Ai wann gidan ba komai bane gaban gidan ‘yaruwata Hajiya Kwaise dake birnin tarayya. Wann saidai a kirasa da gidan sauk’an bak’insu ko ma nace miki na ma’aikatansu.”


Umma ta zaro ido waje “Gida kaman wann za’a kira gidan Ma’aikata..?”


Asshe ta kuma murmusawa “K’warai kuwa.. Kinga kalli nan..” Tai mata nuni da fuskar wayarta. Umma tai k’uri tana duban hoton matar da Asshe Ke nuna mata wacce tai mata lak’abi da Matar manya cikin zuciyarta. 


Asshe tace “Da wa ta miki kama.?”


Kafin Asshe ta rufe baki Umma tace “Da Matar marigayi tsohon shugaban k’asa Maryam Abacha.”


Asshe ta jinjina kai tace “Toh wann sunanta Hajiya Kwaise Maitama. ‘Yaruwata ta ce da muka fito ciki guda. Ke da ganinta ba sai ance miki Matar manya bace.”


Umma ta jinina Kai “K’warai kuwa babu shakka.”


Asshe ta jinjina kai tana mai kuma gyara zama “Kaman yanda na fad’a miki Aure take so d’anta yayi kuma ta bani wuk’a da nama na zab’ar masa Matar kirki a nan gida Kano dan bata son ya auri matan dake rubibinsa a bariki wanda akasarinsu girman Turai ne. Ni kuma a yanda kika bani labarinki na tausaya miki. Dake da ‘yarki kuna cikin yanayi na k’unci da damuwa. Watak’ila Allah ne ya dubi halinda kuke  ciki. Da duk abubuwan da kuke  fuskanta kama daga kan kishiryarki har izuwa jama’an unguwa. Ya share miki kukanki. Zanso ‘yarki tayi Aure na gani a fad’a.. Auren da za’a bigi k’irji a kirasa Aure. Auren da duk masu jifanku da munanan kalamai sai sunyi d’an da na sani. Domin kuwa Ummulkhairinki ta amsa sunanta Uwar Alkhairi.. Ta kawo miki alheri da ma danginku gaba d’aya. Dan nayi imani katafarin illahirin danginku Ke harma da jama’an layinku babu budurwar da tayi irin Auren da Ummul zatayi. Babu wacce tai dacen miji irin na Ummul d’inki. Yaro d’an gata d’a d’aya tilo ga Attajirin d’an kasuwan da kasuwancinsa ya zaga gida Nigeria da ma k’asashen k’etare.” Ta kuma gyara zama “Ke Maman Ummul duk yanda zan miki bayanin dacen da ‘yarki tayi bazaki fahimta ba. Ke kanki guje gujen rab’arki za’a fara yi ba ma Ummul da ake gudunta ba. Domin kuwa kin zama sirkar Manyan mutane. Mutanen da ake haskosu a manyan mujallu da talabijin. JINKIRIN Ummul d’inki ya zame maku alheri. Ke fah Maman Ummul wllhi Kakarki ta yanke sak’a.”  


Ta d’an numfasa “Amma fah ni taimako nai niyyan yi sann tun had’uwa na farko naji na yarda dake na aminta dake. Bugu da k’ari labarinki da kika bani ya tab’a min zuciya dole duk mai imani ya tausaya miki daga Ke har ‘yarki. Kuma yanda Ummul d’inki ta juri kyara da tsangwama baisa ta lalace ba ko ta bijire ma iyayenta na kuma aminta ta cika yarinyar kirki wacce kowa zaiso ta zama Matar d’ansa. Amma idan kinaga kunada wani zab’i ko ita Ummul d’in tanada wani bazan tak’ura ki ba sai na nemasa wata dukda na masa sha’awar Ummul.”


Ai kafin Asshe ta rufe baki Umma tai tsalle ta toshe mata baki “A’a haba Hajja Asshe.. Har wani zab’i Ummul kedashi.. Ina laifin wanda yaso taimakon ka ya tasamma rufa maka asiri. Ni damuwana Allah yasa ‘Yaruwar taki da d’anta su amince idan sukaga hoton ita Ummul d’in. 


Asshe tai murmushin cin nasara. Lallai wann matar ta tabbata shashasha yanzu take kuma gasgata duk bayanan da Yunusa ya kawo mata akanta da ‘yarta. Wann ko ta fad’a mata mak’asudin auren ba damuwa zatayi ba. Ta murmusa a fili kafin tace “Karki damu ‘yaruwata batada matsala ita burinta kawai D’anta ya samu mata ta gari ba wad’ancan ‘yanmatan dake sonsa dan kwad’ayin abin hannun iyayensa ba. Shima D’an nata yaron kirki ne mai biyayya mai bin umarnin iyayensa. Na miki alk’awari baza’a sami matsala daga b’angarenmu ba. Amma saidai kinsan ance Aure d’an bincike ne, yanar gizo kawai zaki d’ale ya tantance Miki komai. Kinsan su manyan mutane a yanar gizo ake bikcikosu.” Ta k’arashe tana kuma dulmiyar da Umma. 


Umma ta shiga girgiza kai “Wllhi ni na yarda dake d’ari bisa d’ari na aminta dake sabida a zamanin nan samun mutanen kirki irinku yayi k’aranci.. Da ace Ke mai cutarwa ce tin a lokacin da kuka bigeni da mota da kunyi tafiyarku Kun barni wajen. Bakiyi haka ba kika d’aukeni kika kaini asibiti kikayi d’awainiyata kika kuma kawoni gidanki. Idan ba kin aminta dani ba na tabbata bazakiyi haka ba.”


Asshe ta murmusa “Alhamdulillah, na d’auki haka matsayin yarda da amincewarki. Yanzu ki sake kwana ki sake samun sauk’i da hutu. Mu kuma ci gaba da tsara abubuwa da yanda zasu kasance.”


Umma ta katseta “Ko dan sabida idon masu ido da hassadan masu hassada”


Asshe ta jinina Kai “Kinga zuwa gobe ko jibi idan na tuntub’i ‘Yaruwar tawa aka samu matsaya sai muje asibiti a biya duk wasu kud’ad’en jinyar mijinki. Sai ki kaini kuma naga surkata Ummulkhairi. Cikin satin nan da yardar Allah magabata zasu taho daga can Abuja sai ayi maganar tsaida ranar Aure. Nafi so ayi komai a gaggauce kafin masu mugun ido su kuma jifan al’amarin da idonsu.”


Umma tai Shiru kaman mai nazari sai kuma tace “Tooh amma Hajja Asshe wani hanzari ba gudu ba. Kinga shi mahaifin Ummul yana kwance asibiti baisan yanda kana yake ba. Anya baza’a jira ya farka daga wann jinyar nashi ba.”


A dak’ile Asshe take dubanta kafin tace “Haba Maman Ummul ya kike magana haka saikace ba k’arni na ashirin da d’aya muke ba. Na Miki ta bakin bature yace 21st century. Shin ita Ummul batada dangin mahaifi ne da zasu iya bada aurenta. Yaushe za’a tsaya jiran tashin mahaifinta dake tsananin jinya. Waye yasan yaushe Allah zai tada shi. Yarinya ta samu miji shikenan sai ace sabida mahaifinta ba lafiya bazatayi aure ba. A ina ake haka. Yanzu fah mazan wahala suke Shiyasa da zaran an samu gwara a kauda. Baki ganin akasarin Auren da ake yanzu daga zuwa tambaya ba bakin kowa sai kiji an d’aura ai duk sabida gudun masu neman jifanka da sharri ne balle wani abu ya gifta a fasa auren. Kinga ‘Yaruwata yanzu take so D’anta yai aure dan a cewarta yaro da kudi hannunsa ba mata had’ari ne. Kinga bazai yuwu mu tsaya jiran mahaifin ‘yarki dake jinya Ya samu lafiya ba kafin ayi auren. Kinga bazamu bari namu yaron ya lalace ba. Kawai idan wann aure bazai yuwu ba..”


Saurin mik’ewa Umma tai ta daka tsalle ta tumu gaba Asshe. Ta d’ago hannaye biyu “Ki rufa min asiri kar ki k’arasa maganarki. In sha Allahu fashin auren Ummul ya k’are. An daina k’irga mata fashe fashen aure. Za’ayi aure da zaran magabata sunzo. Ayi tambaya take a d’aure tun kafin mak’iya suji labari.” Sai kuma ta fashe da kuka wiwiwi babu k’akk’autawa. 


Asshe ta dafata kad’an “Lafiya Maman Ummul Ya da kuka kuma keda zakiyi farin ciki burinki zai cika Ummul d’inki zatakai ga d’akin miji.”


Umma ta d’ago tana murmushi ga hawaye na bin k’uncinta “Kukan farin ciki nake Hajja Asshe. Burina zai cika Ummul d’ita zatayi Aure. Zata bar gidan mahaifinta. Zan daina kwana kullum ina tashi na ganta gabana.. Wayyo ni Suwaiba Ashe wann rana zaizo..?” Taci gaba da rera kuka. 


Asshe ta zuba ma sarautar Allah ido ganin yanda Umma ke sunbatu tana fad’in Yaya Tani zakici goron Auren Ummul. 


**


A b’angaren su Mama kuwa Tasi’u yazo da wasu takardu yanda ya gabatar masu matsayin sabbin takardun shagon Abba. Harda sabbin makullai. Kai da ganinsa kaga maras gaskiya. 


Ya dubi Mama da Badi’a a yanda suka keb’e daga can k’asar wani bishiya wajen asibtin. 


“Yauwa nace mu had’u a nan sabida ‘yan sa ido. Mai saye zai iso yanzu da kud’ad’ensa naira dubu d’ari uku kaman yanda muka tsaida magana. 


Badi’a tace “Haba Tasi dubu d’ari uku saikace na sata.?”


Tasi’u yace banda abinki abu ne ake a sirrance kuma ko ina kikaje kayan magada karyawa ake. Ku gode ma Allah ma da muka samu mai saye dan na tabbata shima rahusa yaji shiyasa bai tsnanta bincike ba amma da zaran yasan Mai shagon na numfashi bai cika ba kinsan bazai sayi gaibu ba. Ni fah taimako nake a nan.”


Mama tace “Kyaleta me ta sani wann. Ni fah da kike gani so nake ayi komai a gaggauce kafin Suwaiba ta bayyana. Dan na ranste kwandala bazasu samu ba daga ita har yaran nata.”


Tasi’u yace “Ah toh magana kenan.. Yauwa gashi can ya k’araso.”  Yai masu nuni da mai sayen shagon Wanda Tasi’un bai jima da masa kwatance yanda zai samesu cikin waya ba. 


Yana k’arasowa Tasi’u ya warware takarda “Wann takardan yarjejeniyar mallakar fili ne..” Ya saka yatsa a baki ya dangwali halshensa kafin ya d’aga d’aya takardan “Wann kuma takardun fili ne Wanda local government ta saka hannu akai, ga saka hannun sarkin Kasuwa. Kunsan ko wace kasuwa tana k’ark’ashin local government d’in da take ne.” 


Ya dubi Mama “Yauwa Mama nan wajen shine wajen saka hannun magada watau masu sayarwa kenan. Nan kuma wajen saka hannun mai saye ne. Nan kuma wajen saka hannun shaidu.”


Badi’a ta katsesa “Amma shi mai sayen baizo da shaidu ba.”


Tasi’u ya Washe baki “Wani aiki sai Badidi ta. Banda abinki meye amfani na. Ai duk dai a rubuce ne kawai ake abin ni duk zan iya saka hannu na zame maku shaidu.. Eh ai duk abun a rubutu ne kawai.” 


Ya dubi mai saye yace “Mutumi na ai sai ka saka hannu ko..” Mutumi Ya amshi takarda Ya saka hannu.


Tasi’u Ya kuma Washe baki yace “Ai shikenan ka mallaki shago a garin Kano.. Burinka Ya cika.. Allah yasa ma kasuwa Albarka.” Sai Washe baki yake dan dama mutumin k’auye ne irin Wanda ko cirani basa fita cikin kauye suke kasuwancinsu burinsa Ya mallaki nasa shagon cikin garin Kano nan yai gamo da Tasi’u. 


Tasi’u ya dubi su Mama “Yauwa Mama ga wajen da zaki saka hannu.” 


Mama ta dubesa a dak’ile “Banida hankali ne zan saka hannu banga kud’ad’e ba.” 


Tasi’u yace “Banda abinki Mama Tani waye yake yawo da kudade masu yawa irin haka. Ai sai b’arayi su bi mu. Haba shi fah kud’i d’an sirri ne.”


Mutumin Kauyen yace “Wann gaskiya ne. Daga nan zamuje tareda shi surkin naki Ya amsa kud’in.”


Tasi’u yace “Ahtoh tare zamu tafi takardu suna hannuna bani damk’a masa takardun Har sai ya dank’a min kud’ad’en. Ko nima baki yarda dani bane. Na tabbata da baki yarda dani ba da baki bani ‘yarki Badi’a ba.”


Mama ta jinina kai “Shikenan..” Ta dubi Badi’atu tace ta nuna mata yanda zata saka hannun. Tasi’u kaman zai kamo hannayenta yake nuna mata. Yace Badi’a ma ta saka duk suka saka. 


Tasi’u yace su koma asibiti wajen Abba shi zai k’arisa ji da komai. Zuciyar Mama ba wai ya kwanta ba suka nufi cikin asibiti. Sam rawar k’afan da Tasi’u yake ba wai ta yarda dashi bane. Sai ta soma tunanin anya batayi gangancin barin Tasi’u su tafi su biyu da mutumin amsar kud’ad’en ba. Koda yake ya Santa ya san halinta ita ba Badi’a bace tsaf kwabo yai ciwon kai sai ta tatse. Da wann tunanin suka shige cikin asibiti. 




(Rayuwar Duniya kenan. A wann babi munji yanda Matan Abba Wanda ke kwance gadon asibiti sukai cinikin dukiyarsa  da kuma ‘yarsa. Mama dai tayi cinikin dukiyarsa yayinda Umma tayi cinikin ‘yarsa. Fad’in Manzon Allah S.A.W cikin hadisin Abdullahi ibn Amr . ‘Duniya jin dad’i ne kuma mafi alkhairin jin dad’inta shine samun mace ta gari.’ Sahih Muslim 1467. Tabbas babban rahama ne Allah ya baka Matar kirki wacce zata tsare maka mutuncin kanta iyalanka da kuma dukiyarka Wanda suke amana a hannunta. Allah kasa mufi k’arfin zukatanmu. Ameen).



SameenaAleeyou📚

*AUREN WATA UKU.!*





*15*






*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*





Mama dai ta gaza zaune ta gaza tsaye tin bayan tafiyar Tasi’u da mai sayen shagon Abba. Ta dubi Badi’a dake shafen shafen waya tace “Ke kira min Tasu’u shirun nan nashi yayi yawa.. Karb’an kud’i saikace karb’an bashi.. Maza kirasa naji ina ya makara ne wai.”


Badi’a ta d’an girgiza kai “Haba Mama ko fah awa d’aya baiyi da tafiya amma kin d’aga hankali a kirasa. Nasan halin Tasi barsa da shaye shayensa amma banda sata.”


Zuciyar Mama yai wani irin bugawa. Ta dubi Badi’a a zabure tace “Badi’atu ina hankali na da tunani suka tafi Har na mance Tasu’u Ya tab’a shaye shaye.. Yo ina ake dank’a amanan kud’i hannun d’an wiwi Bad’ia..!”


“Mama mijin nawa ne d’an wiwi..? Ya tuba fah.” 


“Idan ba d’an wiwi ba d’an uwarki ne..!” Mama tace tana danna mata dak’uwa.. Zufa ya shiga keto mata ta ko ina “Na shiga uku.. Na kashe kaina ni Tani. Wani b’atan basira ne ya d’ebeni na dank’a amanan dukiyar nan hannun Tasu’u.”


Badi’a tai tsaki “Yo tsaban kina sauri mana a kauda shago kar ya shiga jinyar Abba ko Umman su Ummul ta dawo amsan hakkinta da na yaranta..”


Mama taci gaba da safa da Marwa “A’a Tasu’u bazai tab’a min wann gangancin ba. Wllhi akan kud’in nan sai na cajesa daga hula har takalmi ba abinda ya shalleni ehe. Bayani d’aya na sani na kud’ad’ena..” Ta kuma duban Badi’a “Ki sake kiransa nace.. Ungo kirasa da nawa wayan..!”


Badi’a taja dogon tsaki tana mitan Mama ta isheta. 


Wasu nurses suka fito suka tambayan iyalan Malam Isubu. Mama ko takansu batabi ba ita dai damuwarta kud’inta. D’aya nurse d’in da ya ganesu Ya k’araso yana fad’in “Hajiya ashe kuna nan. Muna can munata nemanku a ward.”


Mama wacce gaba d’aya take a daburce ta dubesa a harzik’e tace “Toh gashi ka ganmu ai me akayi..?”


Nurse d’in ya d’an tab’e baki ganin yanda ta hayayyak’osa “Dama wasu magani da drip za’a saya shine akace a sanar daku..”


Bai kai aya ba Mama ta katsesa “Da uwar me za’a sayi maganin inyi.. Kai kaga mun maka kalan masu bada kud’i.? kuje ku masa abinda zaku iya mu nan bamu maganin k’wandala ehe..!” 


Ta dawo kan Badi’a tana fad’in ko batir d’in wayar mutuwa zai kar ta fasa kiran Tasu’u. 


Nurse d’in Ya kuma bud’e murya yace “Ku fah muke jira Dr zai iya shigowa round..”


“Kai bana son fi’ili wai bakaga tashin hankalin da muke  ciki bane?”


Nurse yace “Wann matsalar ku bari idan Kun bar nan sai ku warwareta dan Allah. Yanzu dai ku sayi abinda aka ce ku saya dan a samu a ceci rayuwar majinyacin.”


Muryar Badi’a yaja hankalin Mama alamun ta samu Tasi a waya. Badi’a ta juyo tana duban Mama da murmushi saman fuskarta “Ki kwantar da hankalinki Mama barin saka miki shi a speaker kiji.”


Daga d’aya b’angaren Tasi’u Wanda daga jin yanda yake kana iya sauraran k’aran ababen hawa alamun yana bisa kwalta kenan. Fad’i yake cikin d’aga murya irin na Wanda ke bisa abin hawa musamman babur “Mama ina bisa hanya ne shiyasa bani iya d’aga kiran. Gasu na karb’o su.. Go slow ne ya tare mu kinsan ana fashe fashe sabida k’ara manyan titi.. Eh gani na ma kusa k’arasowa kenan.”


Mama saida ta silale ta zauna dirshan a k’asa tana dafe k’irji “Yauwa yanzu naji batu” Ta marairaice murya tunanin yanzu kud’inta na hannun Tasi’u dole ta bisa a sannu kafin ta dafesu “Ayya ayya Tasu’u na.. Sannu da k’ok’ari kaji d’an albarka.. Muna nan muna jiranka.. Allah iso da kai lafiya.”


Nurse da ya zuba ma sarautar Allah ido ganin Ya zo masu da muhimmin batu amma hankulansu na kan wani abu daban yace “Amma Hajiya kun saurari abinda na fad’a kuwa.?”


“Mun saurara mana. Meye.? Ko so kake mu maimaita maka ka tabbatar mu ba kurame bane.”


Ya d’an girgiza kai “Hajiya gaskiya ina ganin girmanki kuma ni aikina nake k’ok’arin yi a nan. Ya kamata ki dinga tantance kalamanki.”


Mama ta tab’e baki dan a halin yanzu hankalinta ya kwanta taji labarin kud’ad’enta “Kaga k’aramin likita wllhi fah saidai ku k’yalesa mai aukuwa Ya auku dan nan da kake gani bamuda abinda zamu bada.”


Nurse d’in yace “Ban gane mai aukuwa Ya auku ba. Ya kukeso ayi yanzu.? Kunsan cewa kud’in kwanakin da aka biya masa ma sun kusa cika. Kwanan nan za’a buk’aci k’arin kud’i musamman duba da irin jinyar da majinyacin ke fama dashi. Jinya ne babba kuma mai cin kud’i..” 


Mama ta dubesa galala “Au dama ba gwamnati bane Ke biyan kud’in jinyar nasa.?” Dan ita a nata zaton alfarmar gwamnati Abba ke ci tinda dai tasan tin zuwansu kwabo ba’a amsa wajensu ba. 


Nurse ya girgiza kai cikin rashin yarda gajeriyar dariya na neman kufce masa “Mama kenan, a K’asar mu ta gado kike fah ko kin mance ne na tuna miki. Nothing is free in this country.”


Mama ta tab’e baki “Kai kasan me kace. Ni dai na fad’a maka gaskiya bamu maganin fici ehe.”


Nurse yace “Amma ina wann mutumin da yai settling bills d’inku yake.. Ina nufin ina mutumin da ya biya kud’ad’en..?”


Mama ta dubesa da mamaki “Wane mutumi kenan..?”


“Wanda na ganshi nan ya rako wasu ‘yanmata biyu.. Ina tsammanin ‘ya’yan majinyacin ne..”


Mama tace “Toooh..” K’irjinta na bugawa “Kar dai ace wai su Ummul kake nufi. Uban wa ya biya kud’in toh..?”



Badi’a ta katseta “Wann mutumin mana da suke tare wanda har Azeema tace Miki saurayin Ummul ne kuma shine yaje yayi belin Khulsumu a police station. Ta tabbata dai saurayin Ummul ne.”


Mama ta dafe k’irji cikeda mamaki. idan har Wanda aka ambata da saurayin Ummul ya biya tulin kud’ad’en nan watau mai kud’i kenan wann karon Ummul ta samo. Toh wllhi bazata saku ba wai bindiga a ruwa. Yanda sauran batun auren suka lalace shima wann haka zai lalace yabi iska. Bari ta gama da batun kud’ad’enta ta tabbata sun shiga lalitarta. Ya zama dole ta bincika tasan waye shi daga ina yazo dan tasan yanda zata b’ullo ma al’amarin amma bazata zuba ido Ummul ta k’are a gidan maik’o ba dukda wann canfi da aka mata. 


Nurse yace “Ku nake sauraro.”


Mama tace “Yo ina kaw zaku gansa. Dama yaran karuwai ne yaje yayi abinda zaiyi dasu ne shine ya biya ladan jinyar ubansu. Sai ku jira su zo su baku dan nasan yanda Uwarsu ta tafi nata  yawon suma ba zama zasuyi ba qila sun had’e a bayan gari. Ku jira Zasu zo  so su kuma biyanku wasu kud’ad’en. Idan Har kuma basu samu ba sai Malam ya jira har ta Allah ta cimmasa. Idan kuma lokacinsa baiyi ba har wa’adin kwanciyar sa saman gadon asibitin ya cika sai a maidasa can gida saman katifarsa ya cika a can.” 


Badi’a tace “Ahtoh magana kenan..”


Mamaki ya cika nurse d’in. Wai dama a duniya akwai mutane irin haka. Shikam yasha cin karo da mutane daban daban a aikinsa na asibiti amma bai tab’a cin karo da mutane irin wad’ann ba. Girgiza kai kurum yai yasa kai ya shige zuciyarsa fal tausayin Malam Isubu.


**


Abuja.



A fusace Daddy Ke dubanta “Wai meyasa kike son b’ata mun rai ne Kwaise. How many times do I have to tell you this.. Duk abinda ya danganci wann D’an naki bai shafeni ba..”


Mommy ta soma girgiza kai “Why.? Meyasa..? Aliyu D’anka ne Engr.. He’s your flesh and blood.. Meyasa kake masa irin wann k’iyayyar haka..? Su waye suka shiga tsakaninka dashi har haka..?!”


Cikin tsawatarwa Daddy ya katseta “Har sai kin tambaya waye ya shiga tsakani na dashi Kwaise.. Meyasa a kullum kike son tuna mun baya.! Kinfi kowa sanin wann D’an naki only reminds me of my sin. He reminds me nothing but my past Kwaise. Kuskure mafi muni da na tafka a baya… All because of you and your selfishness..!”


Mommy na hawaye take girgiza kai ganin hannun mijin nata Har na rawa yake nunata. Cikin kuka take furta “Ni ce na maka laifi ba Haidar ba. Amma ka daina hukunta Haidar kan laifin da baida masaniya akai..” Muryarta yaci gaba da rawa “Haidar Ya taso cikin k’unci da tsangwama. A baya Nayi zaton izuwa wann lokacin zaka k’aunace sa kuma ka mance komai sann ka zama mahaifi a gareshi kaman yanda ko wani uba yake. He’s your only son our only son…”


Katse ta yai ta hanyar d’aga mata hannu “This family can never be like a normal family Kwaise.. Kinfi kowa sanin haka. Farin ciki bazai tab’a wanzuwa cikin wann ahalin ba..”


Cikin rawar murya tace “Nayi zaton ka yafe mun.?”


Ya jinjina mata kai “Na yafe miki amma idan Har zanga d’anki sai na tuna Kwaise!”


Mommy ta girgiza kai hawaye na kuma zubo mata. Tabbas an shiga tsakanin D’anta da mahaifinsa. Dan idan ba aikin asiri ba ba yanda za’ayi Ya d’auki laifinta Ya d’aura kan d’anta Wanda baida masaniyar laifin har yai masa irin wann k’iyayyar. 


Ta kuma share hawayenta  “Meyasa kake zaune damu ni da Haidar.. To build your image a duniyar kasuwancinka.?” Taci gaba da huci  “Fine.. Mun cika maka wann burin.. Kanada iyali da duniya zata d’aga ido ta kalla ta kirasu da ahalinka. Amma babu komai cikin ahalin face k’arya da k’unci.. Nothing is real here..!”


“Kwaise.!!!” Ya ambaci sunanta cikin d’aga murya.


Mommy na hawaye taci gaba “Eh kasuwancinka shine kawai gaskiyarka.. But your family..”


“You are right… I only care about my business because it’s the only thing that keeps me moving bayan tarwatsani da kikayi years back..!”


Ta lumshe idanunta hawaye na kuma gangaro mata. Sai kuma ta sassauta murya “I endured everything.. I even lost my own son without even realizing it. Thinking maybe wataran zaka k’aunacesa.. But than… I failed..! I failed as a mother and I failed as a wife..!” Kuka yaci k’arfinta sanda ta duk’a k’asa tana mai isarta.


Ta d’an d’auki lokaci a haka kafin taji hannun Daddy saman kafad’unta. A hankali ya d’agota. Kaman wacce akace ta k’ara kuka. 


Ya d’an shafi fuskarsa ganin yanda take kuka sosai tana fad’in ta gaza ta ko wani b’angare. Ta gaza protecting ahalin. Rungumeta yai ta b’angaren jikinsa kad’an yana fad’in Ya isa ta daina kuka. A haka yai masu masauk’i suka zauna saman kujera.


Saida suka d’ibi lokaci a haka kafin ta soma fad’in “Bazan tilasta maka ka so Haidar ba. But please just this once.. Alfarma nake nema.. Be a father to him..”


Ya d’an dubeta sai kuma ya kauda kansa kad’an “Ban tab’a cewa ni ba mahaifinsa bane Kwaise. D’anki shi ya zab’i ya cire kansa daga cikin ahalin nan.”


Ta d’an sauk’e ajiyan zuciya kafin ta mik’e sosai tana gyara zamanta “Aure nake so a masa..”


Daddy ya dubeta da mamaki “Aure.? Cikin yaran Business partners dina kike so na nemar masa matan.?”


Ta girgiza kai alamun a’a “Na riga na samar masa mata a garin Kano. ‘Yar gidan mutunci wacce bata da bud’ewan ido da wayewa da yawa balle a samu matsala along the way. Ba babban Aure nake so ba, ba auren da za’a wallafa a mujalla ko a gayyato manyan mutane ba. No aure nake so ayi a sauk’ak’e. Kawu na dake can Maiduguri zai iya wakiltanka dan shi na wakilta akan komai. Ga Asshe ma a can Kanon. So dik wani necessary bincike da Ya kamata a gudanar an gudanar..”


Dakatar da ita yai ta hanyar d’aga hannu “Idan keda ‘yanuwanki kun gudanar da duk abinda ta kamata kuyi so meye nawa kuma. Ni dai kin sani bazan tab’a karb’ar ma D’anki Aure ba Kwaise. Kuma abinda ya shafi rayuwarsa ba damuwata bane. The only alak’a dake tsakanina dashi shine abinda ya shafi Kasuwancina. Kampanina da ci gabanta.”


Mommy ta rintse idanunta tana jin wani zafi na ratsa cikin  k’irjinta. Tasan za’a Rina haka tinda dai ta jima da sanin duk wani abinda ya danganci Haidar wofi ma ya fisa mutunci a idon mahaifinsa. Ya zama dole ta tabbata anyi auren nan at all cost. Tinda tasan wann ba komai bane face sharrin mugun asirin da aka jefesu dashi. Ta tabbata tinda Malaminsu ya sanar dasu da zaran anyi auren matsalan dake cikin ahalin zaizo k’arshe gwara tayi komai domin ta tabbata auren ya yuwu. 


Ta numfasa kad’an “Auren bazai yuwu ba saida yarda da amincewarku.. Ina nufin kaida Haidar..”


Ya kuma dubanta da mamaki “What exactly do you mean.?”


“Ina nufin Yarda da amincewarka shine kawai zai karkato Haidar Ya amince da wann Auren. Kasan halinsa za’a iya masa auren mu daina ganinsa har abada, bazai yarda ya zauna da matar ba. Yanzu haka ma Gaba yake damu  tinda gashi ya daina zama gidan nan.”


“Wanda  yafi k’arfin zaman gidan iyayensa ne zai zauna ma Auren da zaki masa.? Ke kanki kinsan D’an naki baida mutunci bai ganin kowa da mutunci daga ni har Ke.”



“Amma yana mutunta aikinsa.!” Mommy ta dakatar dashi da fad’in haka.


Daddy ya tsareta da ido.


Taci gaba da jinjina kai “Musamman project d’in nan da yaketa kai komo akai. Naga yanda ya dage yake matuk’ar so Ya jagoranci aikin.. Idan har muna so ya amince da auren zamu iya amfani da wann damar. Ina nufin zaka amince ya jagoranci aikin matuk’a zai amince da Auren. Daga baya na tabbata zai so Yarinyar kuma zasu gina family tare. Zai tara hankalinsa waje guda. A yanda matsalar..”


Bata kai aya ba ya katseta “A’a dakata dakata Kwaise amma ba dani Aliyu Maitama za’ayi wann shiriritar ba..”


“Engr dan Allah ka min wann alfarmar a rayuwa.. Just this once..”


Ya gyara zama sosai yana dubanta cikin rashin yarda “Seriously.. Wann ai hauka ne.. Kwaise a ina kika tab’a jin anyi abu makamancin wann..? Are you asking me to put my company at risk here.?”


Mommy ta silalo daga saman kujera ta duk’a gaban Daddy saman gwiwoyinta. Ta shirya sadaukar da komai domin ta ceto ahalinta.



Cikin muryar kuka take furta “Zanyi ko menene Engr.. Zan duk’a a gabanka na rok’eka sabida inada yak’inin Auren nan zai zama silan shiriyar Haidar da kuma kwanciyar hankalin ahalin nan cikin yardar Ubangiji..”


Saurin d’agota yai yana fad’in “You don’t need to do this Kwaise.”


“A’a ka kyaleni na duka gabanka idan har hakan zaisa ka amince da buk’ata ta.”


Daddy ya soma girgiza kai “Kwaise, babu abinda zakiyi da zaisa na damu da d’anki ko na damu da al’amarin shi.. Kaman yanda ban d’auke shi da mahimmanci ba haka ban d’auki wann auren da kika dage sai kin masa da mahimmanci ba. Amma idan har haka kika zab’a ki sani I won’t get myself involved cikin nema ma d’anki aure.” Sai ya d’auki wayarsa ya shiga dialing layin Haidar. Haidar yana d’agawa Daddy ya sanar dashi yazo gida ya samesa yana jiransa. 


Koda Haidar Ya k’araso zaune ya taddasu a parlon. Iyayensa guda biyu. Yayi zaton magana zasuyi da Ya shafi Kasuwanci shida mahaifinsa tinda har wann ranar baice komai ba gameda proposal da Haidar ya kawo masa the other day. Har k’uri’a akai a company kan waye ya kamata ya jagoranci aikin wanda yake har kawo wann lokacin pending matter sabida shugaban kampani baiyi nasa zab’en ba. Idan Har mahaifinsa a matsayin shugaba a Kampanin Ya zab’esa ko shakka babu ya lashe k’uri’u mafi rinjaye. Idan  har mahaifin nasa ya hau kujerar nak’i dole haka yana Ji yana gani aikin ya tafi k’ark’ashin kulawar waninsa. Duk shirinsa na son ganin bayan mahaifinsa da Kampanin zai tashi a banza. 


Like always he’s not welcome. Ya bud’e murya Ya gaishe su cikin rashin tabbacin za’a amsa masa ko baza’a amsa ba.


Daddy ya jinjina masa kai had’ida nuna masa kujerar gefensa “Have a seat.”


Ba musu ya k’rasa ya zauna yana satan duban b’angaren mahaifiyarsa dan a yanda Ya gansu jikinsa ya basa wani abun ake shiryawa akanshi. Ya jima da sanin su biyun tarayya suke wajen k’untata ma rayuwarsa.



Daddy ya dubesa “Are you sure you can handle the project.?”


Haidar yaji tambayar a bazata. Ya d’ago yana duban mahaifin nasa. Maimakon ya basa amsa kai tsaye sai ya girgiza kai yace “Do you still have your doubts.?”


Mommy ta tsaresu da idanu jin Daddy ya tambayi Haidar amma sai Haidar d’in Ya amsa masa da tambaya. A cikin zuciyarta tace like father like son. 


Daddy ya jinjina kai “The project is to be commenced in three months time. Idan har ka shirya kuma kana so kayi da gaske zan sauk’a daga kujeran veto and give you and your team the green light… But on one condition.”


Haidar ya dubesa da mamaki sai kuma ya dube mahaifiyarsa wacce tin shigowarsa ta kafesa da idanu. Ya maidoda dubansa ga mahaifinsa “What’s your condition.?”


Daddy ya dubi Mommy “Go ahead Kwaise. Tell your son the condition.”


Mommy da idanunta Ke a k’ek’ashe kaman ba ita ce taci kuka a while ago ba tace “Sharad’in shine Aure.. Zaka auri matar da muka zab’a maka kuma ka zauna da ita matsayin matarka.!”


Tamkar sauk’an aradu haka Haidar yaji batun. Ya dubi mahaifiyarsa da tsananin mamaki Ya kuma dubi mahaifinsa. Lokaci guda yake girgiza kai alamun maganan tana kuma ringing cikin kwak’walwarsa “Unbelievable.! This is unbelievable..  What is this.. Aure.. Sharad’in Aure..? Mommy seriously..?!” Ya k’arashe yana duban mahaifiyarsa. Har lokacin ya kasa yarda.


Mommy ta jinina kai “Eh Haidar.. Aure shine sharad’in idan har da gaske kana so ka jagoranci aikin..”


Ya kuma juyowa yana duban mahaifinsa yana jiran ya k’aryata amma sai yaji Shiru bai ce komai ba.


“Wann shine kiran.?” Ya tambaya yana duban mahaifinsa.


“Abinda mahaifiyarka take so kenan. If it was to me kaima ka sani da yin aurenka da rashin yin Aurenka duk ba matsala ta bane. Talkless of wacece zaka aura. ‘Yar waye.? Daga ina take.? Duk wann ba matsala ta bane.”


Meye yake ji kaman hawaye na neman cika idon shi.. Anya wad’ann mutanen sune suka haifesa? Anya akwai iyayen da zasuyi ma d’ansu mugun k’iyayya irin wann.? Abinda yakeda mahimmanci a cikin ahalin kasuwancin ahalin ne kawai Wanda za’a yi komai domin bunk’asarta. Amma duk wani abinda ya shafi ahalin baida mahimmanci musamman ma shi in particular. 


Muryar Mommy ya kuma katsesa “Idan an maka aure a yanda ka d’auke mu nasan zaka iya cewa an d’aura ma wofi ba lallai ka zauna da matar ba tinda yanzu ma ba ganinka muke ba. Wann dalili yasa muka zab’i gindaya maka sharud’a.


“Ki gyara zancenki Kwaise kika zab’ar masa dai. Amma bani Aliyu Maitama ba. And one more thing.. I can’t gamble my company away. Idan kuma har company na zai shiga ki sani naki AUREN ma zai shiga.”


Mommy ta dubesa da tsananin mamaki “Aurena kuma Engr.. Mai hakan yake nufi..?”


“Hakan yana nufin it will be the end of our marriage if things go wrong with my company.. Kuma wann fake family d’in zai watse… Ina nufin babu sauran ahali.. So think carefully for the repercussions of what you are about to decide.!”



Zuciyar Mommy yai wani irin bugawa kaman an sauk’e mata guduma jin irin hukuncin da mijinta Ya yanke. Yayinda Haidar ke ci gaba da dubansu cikin tsananin mamaki. 


Mommy ta nuna kanta tana duban Daddy “Kana so kace my marriage and the family that I spent years Ina iyaka k’ok’arin naga bai ruguje ba zai lalace..?”


“Of course yes.!” Mijinta ya bata amsa. Yaci gaba “So before you make your final decision sai ki tantance wanne ne yafi mahimmanci wajenki.. Auren D’ank’i ko naki Auren.!”



Haidar yaci gaba da girgiza kai yana dubansu. This is unbelievable! Ya kasa aminta wad’ann mutanen sune wai iyayensa. Ya tsaida idanunsa wanda suka rine zuwa ja kan Daddy “Really Daddy.. Is this what’s like to be born into wealthy and influential family..? Everything is about business and making money..? Da gaske Daddy..? Shin ba wani abinda yakeda mahimmanci ne cikin ahalin..?” Ya d’an d’aga murya wann karon “What are we to you..? Is that what you think of your family..? Like we are some sort of business ventures..?” 


Ya mik’e tsaye jijiyoyinsa na kuma tashi yana duban duka iyayen nasa “Are we supposed to..”


“Shut up!” Mahaifinsa Ya katsesa kafin yaci gaba “Don’t you dare raise your voice at me.. Da kai da rayuwarka babu guda da yakeda mahimmanci wajena. If I take your proposal into consideration, it’s because your Mom insisted.. Now get out..! Get out of my sight.!”


Haidar yaci gaba da girgiza kai yana duban mahaifin nasa disbelievingly. A haka ya juya ya nufi k’ofa a fusace zuciyarsa na masa mugun d’aci. 


Mommy ganin damarta na k’arshe zai kufce mata Ya sanyata bin bayan Haidar a d’ari tana k’ok’arin dakatar dashi.


Anisa ta mik’e tana lek’en window jin irin kiran da Mommy ke ma Haidar. Nan ta hangesu sun fito daga side d’in Daddy. Haidar na tafe kaman zai kifa yayinda Mommy ke take masa baya. 



Mommy ta rik’esa sosai “Haidar don’t do this.. Just listen to me.. Bazai yuwu ka rasa project d’in nan ba..”



Yai murmushi mai ciwo “Oh Shiyasa kika tareni ranan a nan.. Kike cewa ni da Ke zamu had’a kai.. Wann shine had’in kan naki da d’anki.. C’mon Mommy.. I always knew baki tab’a yin abinda bazakiyi benefiting a ciki ba.. What I don’t understand here shine Auren kike so nayi ko kuma dai wann project d’in ne a ranki..?”


Mommy ta jinjina kai “Both Haidar.. But my top priority is the project.. Idan har baka amince da auren ba bazai tab’a baka project d’in ba. Think about it Haidar you are his only son. Tilon magajin shi. bazan tab’a bari wani Ya d’auki place d’inka a wann Kampanin ba.”


Ya murmusa yana dubanta “Na sani to him I’m his failed investment. And to you… Your weapon.. Rayuwana baida wani amfani a wajenku..”


Zai shige Mommy ta dakatar dashi da fad’in “Three month marriage.. AUREN WATA UKU Haidar.. Project d’in zai fara nan da watanni uku. Idan ya riga Ya d’auraka akai ka riga ka fara aikin he can’t cancel the agreement. Zaka iya rabuwa da yarinyar.. Ni dai kawai damuwata shine ya baka wann project d’in..!”


Yai Shiru yana duban Mommy. Watau akan abinda take so zata iya zuwa ko wani mataki. Ya matso sosai yana dubanta “Har haka kike son project d’in Mommy..? Shin yakai ki saka naki Auren cikin had’ari ma AUREN WATA UKU. Kawai dan ya bani wann project d’in.?”


Ya kuma girgiza kai “But Mommy this doesn’t make any sense. Ke kikayi kid’anki kikayi rawarki. Da kunnuwanki Kinji ya fad’a. Idan a nasa ra’ayin ne bai damu nayi Aure ba ko kar nayi. Duk ba  matsalarsa bace. Kece kike son Auren kaman yanda yace.. Toh meyasa Auren Ya zama hujja.?”


Mommy ta jinjina masa kai “I couldn’t just sit back and watch you lose your chance. Na kula abinda yake so kenan. Koda bai fad’a ba deep inside yana so kayi auren ne.. Kaima kasan ba don yana so kayi Auren ba bazai tab’a saka Kampaninsa on the line ba. Kayi tunani Haidar we are talking about your Dad here.. Mutumin da zai iya bada rayuwarsa ma wann Kampanin. Rana tsaka dan ina so kayi Aure sai ya amince cewa ka jagoranci aikin.. Aikin da future na Kampanin Ya ta’allak’a akansa. Think Haidar. Wllhi da ace mahaifinka baison kayi wann aure bazai tab’a yarda da sharad’in ba. Mahaifinka yana sonka Haidar kawai bazai iya nuna maka bane ko kuma lokacin nuna maka d’in ne bai ba..”


“Well I don’t give a damn..!Ya soni ko kar Ya soni.. Ban damu ba kuma bana ma so naga ranar da zai so ni..”


“In that case ka yarda ka amince kai AUREN WATA UKU. A lokacin da zaka fara project d’in sai ka rabu da matar ba tareda mahaifinka ya fahimci komai ba. Tinda dama Auren yake so kayi d’in. Toh kayi a wuce wajen. Dan ka rabu da matarka bazai ce meyasa ka saketa ba. Since we all believe ana aure ana rabuwa. Sann bazai tab’a yuwa A amshe aikin daga hannunka ba tinda abu ne base on agreement Wanda Ya k’unshi saka hannu daga duka b’angarorin.”


Shiru Haidar yai yana dubanta. Yasan mahaifiyarsa akan abinda take so. Sann shid’in tamkar makaminta ne da take amfani dashi wajen kare kanta. Idan Har ya amince da wann Auren za’a basa project d’in and everything he’s long been planning for zai samu damar aiwatar dasu. He can finally have the chance to ruin his Dad and his so called company. After all, the marriage is just for three months. Sann idan komai Ya wargaje auren iyayensa ma zai wargaje kowa zai kama gabansa a wann ahali da babu komai cikinsa face k’unci da k’arya. Zai d’auki matarsa Dareen suyi nesa da wann ahalin Wanda basuda hurumin saninta ko rashin saninta because bai d’auki ahalin matsayin ahali ba. Kaman yanda suma baida mahimanci a wajensu.  Haka zalika bai damu yaji waye zasu aura masa ba. Dan yayi imani da zaran an basa jagorancin wann project d’in sun aura ma banza ne da wofi dan ko kamanninsa bazai tab’a bari matar ta sani ba. 


“Fine Mommy.. Na amince,na amince da AUREN WATA UKU kaman yanda kikace.!” 



Mommy jin abun tai a bazata. Wai Ya amince zaiyi wann Auren Wanda bata sanar dashi k’udirinta da mak’asudin Auren ba. Ta tabbata a nasa tunanin ta zab’i yayi wann Auren ne sabida project d’in da yake matuk’ar so ya jagoranta. Ta tabbata kafin ya saki Matar tama riga ta jima da rabuwa dashi idan har aikin Malaminta ya cika. Zuwa wann lokacin kuma asirin ya karye hankulan ahalinta zai dawo jikkunansu. Daga nan sai su bud’e sabon babin rayuwa mai dad’i ita da ahalinta. 


Ta k’araso ta rungume Haidar tana hawaye tsananin farin ciki da Ya lullub’eta. 


Anisa dai sai lek’ensu take, tana mamakin yau Mommy ce harda rungumar Haidar haka. Lallai something’s going on.. She needs to find out. Saurin sauk’owa tai sanda Mommy da Haidar suka kuma shigewa sashen Daddy.


Mommy bakinta har kunne take duban mijinta “Engr, Haidar Ya amince.. Ya amince da sharad’inmu. Ya amince da batun Auren.”


Zuciyar Anisa dake daf k’ofan katafaren parlorn yai wani irin tsinkewa. A fili ta furta “Aure.? Aure kuma..?”


Daddy ya d’ago yana duban Haidar Wanda ke tsaye gaba gareshi cikin parlorn Ya nad’e hannayensa kansa a karkace. Shid’in ma mahaifinsa yake duba. Irin duban nan na your days are numbered. 


Cikin zuciyarsa yake furta ‘ This is the beginning of an end for you Daddy.. K’arshenka and your so called company.. Komai zaizo k’arshe a tsakanin wata uku. This project will turn out to be a great disaster for you and your company. On the day of launching the project, a wann ranan zan gayyato maka manyan bak’i Daddy..  I’ll make sure to invite EFCC for you.. All your assets will be seized. Ba a nan zai tsaya ba. You will fall in front of everyone.. I’ll make sure they sue you and your company for poor Workmanship.. Zan tabbata they impose sanctions for your company ta yanda zai zama ba kai ba shigo da wasu manyan kayan gine gine na zamani cikin k’asar nan. After all this Daddy. Ni, Aliyu Aliyu Maitama, your never wanted son will personally charge you for a series of discriminations while working under your company. Duk wasu cin mutuncin da ka mun a wann Kampanin naka sai nasa ka cinyesu gaba d’aya. I’ll make you lose everything. Alk’awari ne.!’ 


Muryar mahaifiyarsa Ya sinkayo tana fad’in irin farin cikin da take ciki burinta yana gab da cika. Sai kuma ya hango Daddy wanda tuni ya nufi study d’insa. Cikin sauri yabi bayan mahaifin nasa. 


Daddy ya d’ago yana dubansa. Haidar ya shigo cikin study d’in sosai. Su duka biyun suna duban juna. Daddy yace “What now.? Mai kuma kake nema.?”



Zama Haidar yai saman kujeran dake gaban table d’in Daddy. Ya d’auki pen ya zara plane sheet mai d’aukeda alama, adireshi had’ida sunan company dake bisa table d’in. Ya mik’a ma Daddy. Lokaci guda yake furta “You and I are both businessmen Daddy. And we know how things work a duniyar kasuwanci. Since everything here is about business Daddy. Zamuyi shi a rubuce, sann mu saka hannu to avoid business pitfalls..”


Daddy ya tsaresa da idanu yayinda Haidar yaci gaba “We will both sign this agreement tabbacin babu janye yarjejeniya daga baya.”



Daddy ya amsa takardan kafin ya ketata gida biyu “Na riga na gama yarjejeniya da mahaifiyarka. Bana magana biyu. If things go wrong, believe me your Mom will face the consequences.” Yana ida fad’in haka Ya nuna masa k’ofa.


Haidar yai Shiru yana mai jinjina kansa. Har cikin ransa yake jin babu abinda zaisa Ya janye duk wasu k’udirinsa gameda wann wofin ahalin. 


**

A b’angaren Mommy kuwa ta kira Asshe ta sanar da ita yanda sukai da Daddy harma da Haidar.



Asshe tai Shiru kaman mai nazari “Amma Aunty Kwaise na fara tsoro da lamarin nan. Ta ya zaki saka aurenki on the line..?”


“Ta ya bazan saka nawa auren at risk ba Asshe.? Har yaushe zan jira na gyara ahalin bayan ga dama ya sameni. Asshe na shirya sadaukar da komai domin ceto ahalina.”


Asshe ta furzar da huci “Aunty Kwaise I find it strange wai Haidar Ya amince tashi guda. Shin har haka yake son wann project d’in.. Anya son da yake ma aikin yakai yai making huge decision irin wann..? Kuma shi Engr yasan Auren wata kika shirya yi ma d’ansa.?”


Ta girgiza kai kaman Asshe tana dubanta “Ta Ya zai sani Asshe..? Haidar ma na fad’a masa zai iya rabuwa da matar a wata uku ne dan na samu amincewarsa a sauk’ak’e. Amma kinsan su duka biyun Babu Wanda yasan mak’asudin auren. Dukkansu kafin su ankare aikin gama ya gama.”


Asshe ta kuma jinjina kai “Ciniki ta fad’a kenan. Yanzu zamu iya zuwa asibiti mu biya kud’in jinyar mahaifinta..”


Mommy ta kuma jinjina kai “K’warai.. Bana so a d’auki lokaci Asshe. Kawu Bana da mutanensa zasu zo su sameki ku tsara komai. Su karb’i auren a nad’o makarin asirin a kawota. Kud’i ba matsala bane Asshe. Zan kashe ko nawa ne domin wann buri nawa Ya cika.”


Asshe ta kuma jinjina kai “Shikenan Aunty Kwaise. Bakida matsala, zan tsaya ra’ayin daka Har Allah ya shige mana gaba.”


Mommy suna ida wayan ta fito parlor yanda ta tadda Anisa ta kifa kanta sai kuka take. 


Mommy ta k’araso a birkice tana tambayarta meke faruwa.


Anisa ta d’ago tana dubanta dan tinda taga Haidar yazo gidan gashi taji ana batun Aure. Bugu da k’ari akan idonta Mommy ta shige d’aki tana magana da Amminta a waya Wanda ta tabbata bazai shige zancen auren suke ba. Shin iyayenta basu fahimci irin son da take ma Haidar bane. Idan har ba auren Haidar zatayi ba toh ma zaman me take a gidan. Take ta mik’e tana kuma fashewa da kuka ba tareda tace da Mommy komai ba. 


Mommy tabi bayanta da kallo kafin ta tab’e baki tace “Sangarcin sun motsa kenan.” Bata kuma bi takan Anisa ba taci gaba da sabgoginta dan yau Ji take tamkar kaf damuwarta na gidan duniya Ya yaye. 



**


Asshe ta dubi Umma wacce ta cakare cikin tsadaddan leshi d’anubansu, Tai far da idanu “Wow Umman Ummul kinga kuwa yanda kika fito kikai kyau.. Kyaunki na asalin k’abilar Fulbe Ya kuma bayyana.. Gaskiya kud’i zasu amshe ki.. Kin ganki kuwa wa zaice kin haifi Ummul..”


Umma ta ci gaba da wahse baki tana juyi gaban madubi tana duban kanta “Allah ko Hajja Asshe.. Toh ai gwara kar na Saba tinda ba samun irin wann tufafi zanyi kullum ba.”


Asshe ta kuma murmusawa “Inji waye.. Ai saidai ki dinga kyautan su ma. Ke ai yanzu kin girmi irin wad’nn ma saidai na order daga k’asar waje.. Kekam fah yanzu kin zarce sa’anninki ‘Yarki taci sunanta Uwar alkhairi ta bud’e Miki k’ofofin alkhairi.. Ke fa yanzu da matan gwamnoni zaki dinga jerawa..”


“Na shige tsaran Yaya..” Umma tace tana kuma  washe baki.


Asshe tace “Waye kuma Yaya..?”


“Tani kishiyata..” Umma ta bata amsa.


Gajeren tsaki Asshe tai tace “Saidai ta soma kiranki da Yaya daga yanzu dan kin Riga kin amshe girman. Ummul d’inki ta k’wace Miki girman..” Ta aje mata hanshak’in handbag shak’e da kud’i ‘yan dubu dubu ciki tace “Wann naki ne ki razani Tani dasu.”  Dan tinda Asshe ta gane Suwaiba ba kwad’ayayya bace burinta kawai shine ta burge kishiyarta harma da sauran jama’an dake tsangwamar ‘yarta su shiga taitaynsu  sann Ummul d’inta Tai irin auren da yaran Tani basuyi ba ta k’udiri niyyan cika ma Umma wann buri nata. Dan sosai matar ke sakata nishad’i. 


Asshe ta fice tana fad’in bara ta duba Hilala ko ya shirya dan shine zai kaisu.


Umma ta jinjina Kai tana kuma murmusawa. A fili take furtawa bayan Asshe ta fice “Tani kenan.. Dake da ‘ya’yanki Kun gama mana wulak’anci.. Yau idanunki zasu gane Miki abin mamaki.. Yau zakiyi nadaman duk wasu abubuwan da kika jima kina min cikin gidan nan.. Ummulkhairy da kike aibatawa Har kina ambatonta da Ummulsharri toh yau sharrinki zai koma kanki Tani.. Ki jira bayyanata.!”




SameenaAleeyou📚

*AUREN WATA UKU..!*




*16*







*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*






Safiyar Washe gari gidan Hajja Fannah suka fara nufa ko an samu wani bayani gameda Umma. Saidai har kawo wann ranar babu Umma babu labarinta babu wani bayani tak’amaime da ita. Ummul sai juya wayar Umman take cikin hannunta nokia k’irar 3310 duk taji jiki ta kod’e. Hawaye suka kuma gangaro mata. Gashi sun tadda Hajja Fannah ma bataji dad’i ba kwance take lik’is dan tin bayan tafiyar Hisham jikinta ba dad’i k’ok’ari kawai take. Ummul ta dubeta tace “Hajja ko dai asibiti zamuje.?”


Hajja Fannah ta murmusa cikeda jin dad’in yanda Ummul ta damu da damuwarta “A’a Ummul, ba sai naje asibiti ba.. Zuwa anjima zazzab’in zai sauk’a in sha Allah.”


Ummul ta jinina kai suna masu mata fata da addu’an samun lafiya itada Khulsum. 


Khulsum ce ta soma mik’ewa yayinda Ummul ma ta mik’e suna mata Sallama da fad’in zasu biya Asibiti wajen Abba su dubasa daga can zasu k’ara komawa police station ko an samu wani batu gameda mahaifiyarsu. 


Ummul ta d’an dubeta “Hajja zamu iya barinki ke kad’ai naga kaman yau jikin naki da d’an nauyi.”


Hajja Fannah ta murmusa tana mai mik’ewa zaune sosai dan hankalin Ummul d’in Ya kwanta “Kinji Ummul nifa zazzab’i ne ke damuna nasan kuma bazai shige typhoid d’in nan da ya sakani gana kwana biyu ba. Banison zuwa asibiti ne su tara min magani dan bana shiri da had’iye k’waya Shiyasa ko Hisham ban sanar dashi ba dan nasan yanda kika dage naje asibiti haka shid’inma zai dage. Toh kafin ku min taron dangi gashi can na dafa ruwan zogale ma inata sha dan nafi gane wann.” Ta k’arashe cikin k’ok’arin nuna jarumta irinta maras lafiya.


Ummul ta murmusa kad’an. Sosai take jin Matar har cikin ranta. Sun mik’e suna kuma mata Sallama ta k’araso hannunta rik’eda ‘yan kud’ad’e ta mik’a masu “Ungo nan kuyi kud’in abun hawa.”


Dukansu biyu girgiza kai suke suna fad’in a’a ta barshi.


Ta d’an b’ata fuska tana fad’in “Au baku d’aukeni uwa ba kenan idan har zan baku abu kuk’i karb’a.” Ta dubi Khulsum “Ungo nan karb’a maku ita Ummul ai tasan karonmu. Idan bata amshi kyauta na matsayin malamar ta ba ai ta amsa matsayin ‘Yata.” Can k’asar zuciyarta kuwa Matar D’anta ta kirata.


A dole dole suka amsa dukda dama basuda ko sisin da zai kaisu asibiti wajen Abba balle Har su tafi police station maganan case d’in Umma. 



Suka kuma mata godiya had’ida fatan samun lafiya kafin suka fice. 



Suna tafe cikin adaidaita Khulsum ta dubi Ummul “Adda mai zai hana mu fara zuwa police station d’in tinda kinga asibiti ko munje ba Lallai Mama da yaranta su bari mu shiga wajen Abba ba.”


Ummul ta girgiza kanta “A’a Khulsum, koda zasu hanamu mu je d’in dai. Muji ya jikin nasa Ya kwana tinda idan muka tafi maganan neman Umma ba Lallai mu dawo da wuri ba har sai munji yanda al’amarin Ya kwana. Kinsan ofishin ‘yansanda cases da yawa. Inaji a jikina da izinin Allah yai za’a samu Umma.” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya irin na Wanda Ya gama karaya amma tawakkali Ya hana furta hakan.


Khulsum ta jinina kai tana amsawa da Allah Ya sa a samu Umma ya kuma bawa mahaifinsu lafiya. Ummul ta amsa da Ameen daidai sansa mai adaidaita Ya diresu k’ofan asibiti.


Suna dosowa haraban ward d’in suka hango Mama da Badi’a. Ga Azeema a gefe harma da mijin Azeemar Habibu. Sai wallahi tallahi suke baka ma gane mai suke fad’i dukda wai k’asa k’asa sukeyi basa d’aga murya kar ajisu a fatattake su. 


Azeema fad’i take “Wai kuna so kuce mun tun yammacin jiya kud’ad’en suke hannun Tasi’u kuma wayansa a kashe.?”


Habibu yaci gaba da salati yana tafa hannu. Ya dubi Mama wacce ko iya cewa komai batayi. Huci kurum take. Fuskar Tasi’u ne kawai ke mata gizo cikin ido. Allah ya gani da zataga Tasi’u yanzu a gabanta zata iya shak’esa Har sai an k’wacesa. 


Cikeda zak’ewa Habibu yaci gaba “Wann ai zancen banza kenan.. Ta Ya za’a ce kun kira shi Tasi’u kun dank’a masa ragamar komai irin haka. Mai zai hana baku tuntub’i ita Azeema ta kirawo nata mijin matsayin shaida ba..Wann ma ai ba magana bace tinda kud’in nan ba kud’in Bad’ia bane ita kad’ai.. Ehe kud’i ne na magada.. Kuma shago da ba shagon sata ba ya ma za’ace an sayar cikin rahusa haka. Nawa kowacce zata samu cikinku.?”


Badi’a dake aika masa mugun kallo tace “Toh wai kai Malam naka a wanne.. Ko harda kasonka ne cikin gadon.?”


Azeema ta katseta “Ai naga gadon na uban Tasi’u ne da kika gayyatosa Ya kwashe kud’ad’en Ya gudu. Toh wllhi na ranste da Allah bazata tab’a sakuwa ba wai bindiga a ruwa. Wllhi yanzu zan kirawo Yaya Salima tinda duk abinda ake itama bata sani ba. Na ranste da Allah sai an mana kashin hakkinmu ehe. Ko kuma wllhi na gayyato maku hukumar hisba nace Kun saida gadon mahaifinmu dake kwance gadon asibiti.!” Ta k’arashe sai huci take. 


Habibu sai bud’e hannaye yake yana kuma ingiza Azeema. Fad’i yake  Ahtoh magana kenan a fito masa da hakkin matarsa.


Azeema ta Ciro waya da zummar kiran Salima kenan suka sinkayo kukan Mama. Ta kamo bakin mayafi tana matse idanunta “Ni Tasi’u zai tona ma asiri a garin nan.. Na rufa masa asiri yana d’an wiwi na d’auki ‘ya na basa a tunanina zaiyi hankali ashe ni ce ‘yar wiwi.” 


“Mama ba fah kuka zakiyi ba, nemo Tasi’u Ya kamata kuyi yanda ya shiga Ya fita dan wllhi muddin Tasi’u baizo ba daga nan ofishin hukuman hizba na nufa na zayyane masu komai. Kun raba gadon mahaifinmu da ransa.!” Azeema tace tana huci.


Habibu yai saurin shiga tsakiya kaman wani alk’ali “A’a a’a baza’ayi gaggawan gayyato hukuma ba tinda abin duka na gida ne. Kamata yayi a binciko yanda Tasi’u yake duk rintsi. Yanzu zan tafi yanda shi Tasi’un ya cika zama na tuntub’i abokansa tinda dai baza’a samesa a gida ba. Na tabbata baiyi nisa ba.” Ya k’arashe yana mai wucewa cikin sauri. 


Ummul da Khulsum suka dubi juna cikin tsananin shock. Mama da Badi’a saida shagon Abba sukai kenan ko mai hakan yake nufi.? Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.


Suna a haka aka zo neman kud’in magungunan Abba wanda kusan kwana biyu kenan yana skipping wasu treatments d’in masu matuk’ar mahimmanci.


Mama sai ta hayyayako ta soma bala’i tana fad’in ta gaji da zaman asibiti ma jinyar da yak’i ci yak’i cinyewa.


Nurse yace “Yanzu babu kud’in da za’a masa jinyar.?”


Azeema tace “Kurma ne kai baka ganin tashin hankalin da muke ciki ne.. Damfararmu fah akayi..”


K’arasowan su Ummul suna tambayan mai ake nema gameda jinyar mahaifinsu yaja hankulan su Badi’a. Ita kam Mama har yanzu fah bata wani gane mai ake ciki ba hankalinta kacaukam naga Tasi’u da kud’ad’enta. 


Badi’a tace “Kud’in jinya ake nema ko zaku biya ne tinda wancan karan ma ku kuka biya. Sai aje a sake saida jiki a kawo kud’i. Ko mazan ne babu.?”



Khulsum ta dubeta Har lokacin mamakinsu bai saketa ba “Da dai a kiramu b’arayi marassa imani masu saida k’addaran mahaifinsu da ransa gwara ace jikinmu muka saida muka biya kud’ad’en jinyarsa. Kin fahimta B’arauniya matar b’arawo.!”


Badi’a ta nufota a zafafe tana fad’in “Ke ni sa’anki ne dan ubanki.. Sai na gurje bakin ki yanzu a nan..!”


Saida aka shiga tsakanin Khulsum da Badi’a. 


Nurse yace “Yanzu haka Dr zaizo babu abinda aka buk’ata.. Shin ba hanyar da za’a bi a samu a saya magungunan..?”


Kaman daga sama suka sinkayo wata murya “K’warai akwai hanyar da za’a saya!”


Mama dake shirin barin wajen dan batada lokacin cecekucen rashin kudin jinyar Malam da malaman asibiti burinta kawai ta isa ta cimma Tas’u. Nan tai birki jin wann murya dai tai ma me muryar farar sani. A hankali take k’ok’arin juyowa har dai ta karkato gaba d’aya. 


Mama ta daskare. Ta shiga mutsuka idanunta tana duban wacce take gani gaba gareta “Suwaiba.!” Ta furta cikin tsananin mamaki. 


Suwaiba ce fah.. Suwaiba Amaryar Malam Isubu nata take gani sanye cikin tufafi na alfarma. A gidan Uban wa Suwaiba tayi arziki dare d’aya. Karfa hausar nan da ake cewa dare d’aya Allah kan yi bature ta tabbata kan Suwaiba. Ta kuma mutsuke idanunta dan har lokacin gani take kaman gizo ne ba gaskiya ba. Wai Suwaiba shashashar matar Malam Isubu ce haka kaman wata matar shugaban k’asa ko gwamna.


Khulsum da Ummul ma da mugun mamaki suke duban mahaifiyar tasu wacce kaman an canzata. Suka dubi juna suka kuma duban Umma shaye da tsananin mamaki, cikin tsananin shock suka furta “Umma.!”


Umma taci gaba da takowa gaba garesu. Azeema da Badi’a ma da mugun mamaki suke duban Umman.


Kai tsaye nurse d’in Umma ta nufa tace “Nawa ake nema..?”


Nurse d’in Ya d’ago takardan na list d’in abubuwan da ake buk’ata Ya soma karantowa.


Kafin Ya gama karantowa Umma ta d’aga masa hannu alamun dakatarwa lokaci guda ta bud’e tsadadden handbag d’in dake rik’e hannunta ta Ciro sabbin kud’ad’e ‘yan dubu dubu sai walk’iya suke. Mama ta zaro ido waje ganin dubabe bugun habuja suna walk’iya suna kashe mata ido. Wai Suwaiba ke fiddosu. 


Ko k’irgawa batai ba ta mik’a ma nurse d’in “Ungo nan.. A saya duk abinda ake buk’ata, idan yayi canji ka rik’e canjin idan kuma akwai abinda bai isa ba ka sanar Dani.. Ko menene..” Ta k’arashe tana gyara zaman tsadaddan mayafin dake bisa kanta.


Nurse ya murmusa “A’a Hajiya saidai na Miki jagora ki biya da kanki.”


Umma ta jinjina kai yayinda Umma ta take masa baya. 


Tin daga k’afafu Mama ke dubanta Har zuwa tsadadden leshi da yan kunne da sark’a dake kwance wuyanta. Wann ko taron manyan matan gwamnoni Suwaiba taje a haka ai ta cinye taro.


Akan idonsu Umma ke gudanar da komai da taimakon nurse d’in kafin daga bisani ta amso receipts ta dawo yanda ta baro ahalin mijin nata Wanda kowa shock Ya hanasa aiwatar da komai. Baga Mama da yaranta ba baga Yaran Umma ba wanda zasu iya cewa Har yanzu basu tabbatar idan mahaifiyarsu bace. 


Ko takan Mama batabi ba ta dubi su Ummul wacce suma kansu ta koma masu tamkar bak’uwa. Kallon rashin sani ne ko na mamaki suke bin mahaifiyar tasu dashi. Tsakiyan yaranta ta shiga wato Ummulkhairi da Ummukhulsum ta kamo hannayensu tace “Mujenku kuga mahaifinku..” 


Tamkar rak’umai da akala haka Umma ke janyo su Ummul da Khulsum. A haka suka zo suka shige gaban Mama da yaranta wanda suka koma kaman an dasa su.


Har suka shige cikin ward d’in Mama da yaranta basu daina binsu da kallo ba.


Suna shigewa Mama ta dubi Azeema tace “Ke wanke ni da mari dan ubanki.” 


Azeema ta dubeta a yatsine “Ban gane na wanke ki da mari ba Mama..”


“Nace ki mareni na tabbata ba mafarki nake ba.. Ba Suwaiba bace Ke min gizo ba. Inji ba itace yanzu ta shige gaba na ba ko.? Ku amsa min mana.. Na shiga uku ni Tani..” 


Bata kai aya ba taji zafi Ya tsunkuri ‘yar yatsarta na k’afa. Badi’a ce ta take mata ‘yar yatsar cikin k’ok’arin dawo da Mama hayyacinta. 


Mama ta saki k’ara tana d’ingile k’afarta “Wayyo kunama ta cijen.!”


Badi’a tace “Ba kunama bane ta cijeki, take maki k’afar nai ki tabbata ba mafarki kike ba..”


Azeema tace “Mama wllhi Umman su Ummul ce. Amma nima nafi zaton canzata akai.. Mama ina ta samo kud’ad’e irin haka dare d’aya.. Kinga Har fari da shek’i ta k’ara dare d’aya. Mama kin kaw ga suturan dake jikinta. Wllhi iriinsa matar Gwamna ta saka ranan da za’a rantsar da mijinta.. Mama Ina matar nan ta samo kud’i haka wai.?”


“Yo Ina zan sani ina tareda ke a nan..” Mama tace tana kuma lek’en bayan Umma a tsarace. 


Badi’a ta tab’e baki tace “Kar canzawarta ya zautar daku. Abu ne a bayyane matar nan dama barikinta kawai take son yi auren mahaifinmu ya taka mata burki.. Yanzu da take ganin zai Mutu shine ta baje kolinta da kyau zatai barikinta mai dalili..”


Azeema tace “Kai wllhi amma fah ta mun kyau, kinga shegen mayafin da ta watsa.  Irin mai  walwalin nan fah da ake talla online.. Inama ta bani aro naje dashi Bikin k’anwar Habibi na yak’i shegun danginsa.”


Bata kai aya ba Mama ta hamb’are bakinta “Kud’in shan jini da tsafin zakije a baki.. Toh Idan shaye shaye kike kije Azeema.. Kije Suwaiba ta shanyeki.. Ni nayi imani itace ta asirce Ummul mazan dake nemanta ke gudu sabida Allah Ya rufa masu asiri da sauran kwanakinsu. Shi Fa’izu dake kwanansa Ya k’are gashi ta lashe kurwansa. Yanzu kuma abun yazo kan Malam Shiyasa data mik’a sa gashi a kwance kafi gawa.. Kuma yanzu ba sai anjima ba zan fiddata daga cikin asibitin nan..”


Fiuuu Mama ta shige ta nufi ward d’in yaranta na biye da ita.


Bata damu da majinyata dake kwance wajen ba Mama ta shiga kururwa tana fad’in Suwaiba mayyace yar K’ungiya asiri ne na shan jini.. Ta tsafe ‘yarta Ummul tana amfani da ita tana cinye mutane kaman yanda Fa’izu d’an ‘yar uwan Malam Isubu ya mutu. Bai isheta ba yanzu ta mik’a mijinsu zata cinye.. Sai dukan k’irji take tana fad’in wllhi bazaayi ma mijinta amfani da dukiyar ‘yar shan jini irin Suwaiba ba. 


Sauri sauri wasu nurses da cleaners suka tafi kiran securities. Hango securities d’in da Mama tai ya sanyata had’iye kalamanta. 


Securities suka k’araso suna muzurai suna fad’in waye zasu fidda. 


Take Mama ta shiga masu nuni da Umma tana fad’in “Ga Suwaiba ita zaku kama ita zaku fidda.. Yar shan jini ce..” 


Ai sai Mama taga securities sun isa gaban Umma suna duk’awa suna kwasan gaisuwa lokaci guda suna tambayar ko da abinda kike so a miki Hajiya. 


Mama sai ta saki baki tana duban ikon Allah. Suwaiba.? Suwaibar ne Hajiya..?


Umma ta murmusa tana gyara zaman mayafinta “A’a babu komai Kar ku damu. Haukar wancan Matar ne Ya motsa inaga b’allewa tayi daga b’angaren masu jinyar hauka.”


Mama jin an ambaceta da Mahaukaciya ya sanyata kuma hayyak’owa. Jikinta Har rawa yake. 


Sauran mutanen dake wajen Wanda dama fitinan Maman a ishesu sukace da gaske ne batada saiti kullum fama ake da ita. 


Aiko nan take securities suka fidda Mama da k’arfin gaske sai ihu take tana tsine ma Umma. Yaranta suka bi bayanta a guje suna ambato sunanta.


Umma ta zuba masu idanu har aka fice dasu kafin ta sauk’e ajiyan zuciya ta juyo tana duban yaranta Khulsum da Ummul Wanda Har lokacin kallon mamaki ko muce kallon tsoro suke binta dashi musamman bayan da Mama ta gama fad’e fad’enta.


Umma ta kuma dubansu sai ta k’arasa ta rungumesu. Basu iya maida mata martanin rungumar ba.


“Ummul, Khulsum.. Ni ce fah mahaifiyarku Ummanku.. Meyasa kuke dubana kaman bak’uwar fuska. Shin ko baku shaida mahaifiyarku bace.?”


Girgiza mata kai Ummul tai “Mun shaida kamanninki Umma amma yanayi ki yafi kama da bak’uwar Fuska.. Umma mai ya canza ki cikin kwanaki k’alilan..?”


Murmushi Umma ta saki kafin ta dafa Ummul “K’addararki itace ta canza ni cikin kwanaki k’alilan Ummul.. K’addaranki Wanda a baya naita Allah wadai dashi shine ya zamto mabud’in Alherinmu..”


Girgiza kai Ummul tai cikin tsananin sanyin jiki “Umma ban fahimceki ba..”


Umma ta kuma murmusawa “Kar ki damu ‘Yata da sannu zaki fahimci komai.. Kuzo muje..” Ta shiga janyo hannuwansu suka nufo waje yanda suka hangi Mama har lokacin huci take bayan an tilasta mata yin shiru.


Mama ta zabura zata nufo Umma amma sai taga wata jibgegiyar jeep taja tayi parking gaban Umma. Mama taja wani wawan birki tana dafe k’irji. 


Mamaki da sanyin jiki Ya kuma sauk’ar masu Ummul.


Umma ta dubesu “Toh yarana ni zan tafi,  in sha Allah zan kuma dawowa nan bada jimawa ba.”


Da tsananin mamaki suke duban mahaifiyarsu. Tasa kai kenan zata shige mota Ummul tai saurin kamo hannunta. Hawaye na gangaro mata take girgiza kai “Umma.. Ina zakije ki bar Abba cikin halinda yake ciki..? Umma ina kikaje kika barmu mu nata nemanki.. Shin Kinsan abubuwan dake faruwa a nan.. Umma wai meke faruwa.. Umma meke faruwa ne..?”


Dafata Umma tai “Da sannu zaki fahimci abinda ke faruwa Ummul.. Zan rok’i alfarmarku. Kar ku bar kusan mahaifinku.. Ku zauna ku kula dashi.. In sha Allah daga yanzu duk wani abinda za’a kashe sabida jinyar mahaifinku bazai zama matsala ba. Na barku lafiya yarana..” 


Ummul na kuka ta kuma kamo hannunta “Umma shin kinsan kalan tashin hankalin da muka shiga na rashin ganinki.. dan Allah kar ki tafi ki barmu.. Umma..” saidai tuni Umma ta cire hannunta daga rik’on da Khulsum tai mata ta shige mota. Ummul ta kuma yunk’ura tana ambato Umma amma saiji tai Khulsum ta rik’on hannunta had’ida dakatar da ita “K’yaleta Adda.. Wann ba Umman mu bace.. Idan ma itace banida haufi an canzata dare d’aya.” 


Fad’awa jikin Khulsum Ummul tai wani irin kuka na kufce mata.


Mama kaw zuba masu idanu tai tana mai kuma tabbatar da zarginta cewa Suwaiba dai K’ungiyar asiri ta fad’a.



Umma tana shigewa cikin motan ta dubi Asshe dake zaune gefe. Ta d’an yi adjusting mayafin  “Hajja Asshe  Ya kikaga k’warewata..? Kinga kaw yanda na razana Tani na haukata ta na gigitata.? Gaba d’aya fah ta birkice..”


Asshe ta murmusa tace “Ai ma fah bama ayi komai ba, wann ai sharan fage ne. Sai randa aka kai lefen Ummulkhairi, ranan ne zaki kashe kishiyar ki da k’unci. Dan ina mai tabbatar miki sai ta had’iyi ranta. Kaf abinda ta miki kan Ummulkhairi sai kin rama. Ranan biki kuma a fice da gawarta.”


Umma ta zaro idanu “Na shiga uku, bazan so Yaya ta Mutu ba ai…”


Asshe ta d’an murmusa kad’an had’ida dafe kafad’ar Umma guda “Bazata Mutu ba ma sai taga Nasaranki da na Ummul. Kuma ko yanzu kin tauna tsakuwa aya kuma taji tsoro.. Ni so nake ki kece raini a kamfatanin layinku.. Duk masu aibata Ummul d’inki sai Sun shaida auren gata da za’a mata..”


Nan fah Umma ta shiga wage baki zuciyarta na mata dad’i. Karfa ku mance mijin Umma na kwance gadon asibiti tsakanin rayuwa da mutuwa. Amma Har yanzu burin Umma shine Ummul d’inta tayi aure kota halin k’ak’a ko ba dan komai ba sai dan ta birge Mama da sauran jama’an unga sabida abinda suka jima suna mata kan Ummul. 


**


A b’angaren su Ummul kuwa tinda Umma ta shige bak’ar Jeep d’in nan mai lullub’e da tint suka kasa komawa cikin asibiti wajen Abbansu dan haka su Mama da Azeema sukai caa a haraban asibiti suna nunasu suna cewa ga ‘ya’yan mayya. A dole suka fice daga asibitin suka dawo gida.


Ummul ta zuba tagumi Khulsum ma da kalan nata tagumin.


“Adda anya ba gaskiya Mama take fad’i kan Umma ba.. Anya Umma ba wani k’ungiyar asirin ta shiga ba..!” Tai maganar kaman mai tsoron furtawa.


Ummul tai saurin d’agowa tana dubanta “Haba Khulsum ta ya zakiyi irin wann tunanin..?”


“Adda abinda idanun mu suka gane mana fah kenan… Ina Umma ta samo dukiya irin wann tsakanin kwanakin nan..? Sann meyasa ta tafi ta k’yalemu..? Meyasa bata damu ta bar Abba cikin halinda yake ba.. Adda kifa duba kiga yanayin da Abba yake ciki amma Umma tana a matsayin matarsa ta saka k’afa ta tsallake shi har da shigewa shirgegiyar Jeep d’in nan. Ga ado da tayi irin wanda bata tab’a yi ba. Wata matace zatayi wad’ann abubuwan alhalin mijinta na kwance cikin tsananin jinya. Wllhi ko baki fad’i ba Kema kanki nasan zuciyarki bai kwanta ba Adda kuma akwai irin tambayoyin da nakeyi kwance cikin zuciyarki.”


Sauk’e wani irin ajiyan zuciya Ummul tai sai kuma ta jinjina kai tace “Kinyi gaskiya… Akwai tarin tambayoyi k’unshe cikin zuciyata Wanda zanso Umma ta amsa min su.. Amma ko ma menene kar muyi gaggawan yanke hukunci da abinda idanu mu ka iya gani.. So tari abubuwan da idanun mu ke iya gani a zahiri ba haka suke a bad’ini ba.. Mu tsaya Har muga gudun ruwan Umma mu kuma ji abinda ke faruwa.”


Khulsum taja wani irin gauron numfashi ba tareda ta kuma furta komai ba. 


**


Abuja.


Laptop ne gabansa waya manne kunnensa yana duban wasu  sketches na manyan bridges iri daban daban. Ko ba’ace ba da Hisham yake wayan. Da alama shi ya turo masa sketches d’in da suke tattanawa akai. Bayan Sun gama magana shiru yai yana nazarin abinda ke gabansa. Sai kuma ya rufe laptop d’in ya k’ura ma waje guda idanu. 


Dareen da waya ke mak’ale kunnenta ta kuma lek’ensa kafin ta koma da baya tana rage murya had’ida matse wayar jikin kunnenta sosai  “How would I know.. He’s been acting strange lately..”


Daga d’aya b’angaren muryar mutumin ya katseta “What are you there for idan har bazaki iya karantar yanayin da yake ciki ba..?!”


Ta d’an rausayar da idanu had’ida furzar da huci “Look, I see him everyday but I can’t grasp his mood. Ba ko yaushe asiri yake tasiri ba. Kar ka mance Shi mutum ne Wanda tun kafin sihiri ya jefesa yakeda wahalan sha’ani.”


Mutumin yace cikin tsawatarwa “Kalla Dareen. Ban kawo ki cikin rayuwar Haidar dan kiyi holewarki dashi ba. Kinfi kowa sanin dalilin da yasa kike tare dashi. Idan Har bazaki min amfani ba. Zan tarwatsaki da kaina.. Kinsan inada makamin da zan tarwatsaki a hannuna tinda har yau baki san yanda na bisne sirrin da Ya rufe Aurenki da Haidar ba.”


Lumshe idanunta tai had’ida bud’esu “Fine, zanyi iya k’ok’arina na fahimci mai yake shiryawa. Amma karkayi gangancin rabani da Haidar domin zan tashi wutan da kaima baka isa kashewa ba.!”


Ya murmusa “Kar ki mance I’m the one calling the shots here. Kibi umarnina ki zauna lafiya.!” Yana ida fad’in haka ya katse kiran.



Furzar da huci ta kumayi kafin tai k’ok’arin kintsa kanta ta fito parlor yanda Haidar ke zaune. 


Murmushi saman fuskarta ta zauna gefensa “Love..” Ta fad’i tana shigewa jikinsa. Sai kuma ta d’ago fuskarta tana dubansa “Is something bothering you..? You seem preoccupied… Is it about work..? Ko kaje duba Mommy ne..?”


Tambayan da ta masa na k’arshe yasa ya dubeta sai kuma ya maida dubansa wani b’angaren “I’m fine..” Ya fad’i a tak’aice ba tareda ya kuma cewa komai ba. A ‘yan kwanakin ta kula magana ma sai ya zama dole yakeyi. Ya koma mata tamkar bak’o cikin gidan dukda dama a iya zamansu bata isa tace ta sansa kaman yanda tasan tafin hannunta ba dukda kuwa Auren sihiri da tayi dashi. Mik’ewa yai ya nufi sama ba tareda ya kuma ce mata komai ba. Hannayensa sakale cikin aljihun sweatpants d’in dake jikinsa. 


Tabi bayansa da kallo har ya haye sama kafin tai saurin janyo laptop d’in ta bud’e. Sannu a hankali take bin duk wasu abubuwan dake fuskan computer d’in tana karantawa. 

Aiki yake sosai kan project d’in da takeda masaniya yanata fad’i tashi akai. Toh kodai mahaifinsa ya basa go ahead ne.? Idan har mahaifinsa ya amince ya jagoranci aikin dole akwai wani abu a k’asa. Ba yanda za’ayi mahaifinsa ya amince masa cikin sauk’i.. She needs to find out meke faruwa. 


**

Yau kwanaki biyu kenan Umma bata kuma waiwayowa ba. Hankalin Mama kaw gaba d’aya ya gaza kwanciya. Damuwarta kawai shine tasan yanda Suwaiba ta samo irin wann arziki da ta gani tareda ita. Gaba d’aya ta ma mance da batun Tasi’u da halinda kud’ad’en shagon Abba ke ciki. 


Yau d’in ko asibiti wajen Abba ta gaza komawa. Tare take da yaranta Badi’a da Azeema  yayinda suka baro Salima can wajen Abba. Tunanin Mama d’aya idan ta fice  Suwaiba na iya zuwa gidan wajen ‘ya’yanta Shiyasa ko k’ofa ta gaza fita. 


Mama da yaranta Azeema da Badia Suna tsaka da aibata Suwaiba ‘yar k’ungiyar asiri gaban su Ummul suka soma jiwo hayaniya daga waje. Wann Ya dubi wancan wancan ya dubi wann.


Azeema tai saurin tare wani yaron cikin gidan da ya shigo a guje rik’eda gudan dubu a hannunsa yana ihun murna. Azeema ta rik’esa tana tambayarsa meke faruwa waje.


Yaron yace “Umma ce.. Umman su Khulsum itace tazo da k’atotuwar mota tanata rabon kud’i a waje..”


Mama dasu Azeema suka dubi juna. Babu shiri suka nufi waje a fujajan yayinda su Ummul ma duban junan sukai itada Khulsum. Take suma suka take ma su Mama baya. 



Mama da yaranta suka wani irin birki Har saida ya rage saura k’iris Mama bataci tuntub’e da wani yaro da ya nufo gida a guje yana ihu yana d’aga kud’insa sama.


Daskarewa Ummul da Khulsum ma sukai suna duban kayan al’ajabi. Ikon Allah. Da gaske Umma ce ta fito cikin wann bak’ar shirgegiyar mota tana rabon kud’i ma Al’umman unguwar. Mutane kaw sai fitowa suke kusufa kusufa daga lungu da sak’o suna amsan kud’ad’en da Umma ke rabawa.


A haka Umma ta k’araso gaban Mama. Ta murmusa tana dubanta “Tani ya muka sameku..”


Mama ta kuma bud’e baki tana duban Umma jin irin gaisuwan rainin da tai mata. Wai Tani ya muka sameku.. Tani fah.. yau Suwaiba bata kirata da Yaya kaman yanda ta saba ba. Tani fah ta kirata dashi gatsau. Waima Yaushe Suwaiba ta sami ‘yanci cikin gidan. Dan lokacin da aka aurota daga rugarsu babu kalan uk’uban da bata gallaza mata ba ga wauwauta ga shashashanci had’ida mugun k’auyanci da sukai mata dabaibayi.. Wai har Suwaiba ne ta waye yanzu.. Lallai ta yarda da hausar nan da ake cewa Shege na k’auye.. Idan bak’auye ya samu faraga yafi d’an birni iya shege.. Eh Tabbas yanzu ta shaida wann da idanunta.. Dan barikin da Suwaiba take a yanzu ko goggan d’an birni Wanda aka haifesa tsakiyar wayayyu bazai ba. Ko ita kanta bata tasa k’afa ta tsallake mijinsu dake kwance yana jinya ta tafi ta barsa ba. Sai yanzu take ganin ashe ita jaririya ce a bariki tinda ita saida shagon Isubu kawai tayi, tanata kumfan baki tana fad’i tashi ta raba gadon Isubu tun yana raye dan kar Suwaiba da yaranta su samu. Ashe Suwaiba kallon k’aramar ‘yar iska take mata. Ita a daidai wann gab’ar ma ta baje Rumfar barikinta.


Muryar Umma ne Ya kuma dawo da ita daga duniyar tunanin da yai nisa ciki “Yauwa Tani nace ba ga wann ki kula da Abban Ummul sosai.. Naga Salima wajensa. Bansan mai kike a nan ba da har yanzu baki tafi wajensa ba. Idan akwai abinda ake buk’ata kina iya sanar Dani dukda dai duk wani abinda ya kamata a bayar an bayar. An canza masa d’aki ma ya koma b’angaren kud’i. Kira Salima zata sanar dake komai tinda tareda ita akayi duk wasu sauye sauyen. Tai maganar tana mai Ciro kud’ad’en cikin hamshak’in jakanta. Yacce kasan matar gida na bawa ‘yar aikinta sak’o. 


Mama tai sakare tana duban Suwaiba. 


“Ungo amshi mana..!” Umma tace tana mai kamo hannun Mama had’ida damk’a mata kud’ad’en ciki.


Lokaci guda Umma tasa kai tana taku d’add’aya sai juya ma Tani mazaunai take. 


Kusan silalewa wajen Mama tai har saida Azeema ta tallafeta. 


Kasa motsawa Khulsum tai har Umma ta shige ta nan gabanta rik’eda hannun Ummulkhairi wacce ke biye da ita tamkar rak’umi da akala. Bata iya dawowa hayyacinta ba saida ta sinkayo muryar Mama na fad’ida Azeema ta rik’eta sosai bata iya tsayuwa kan k’afafunta.


Cikin sauri Khulsum ta nufi bayansu Umma k’afafunta Har hard’ewa suke. 


Tana shigowa ta sinkayo muryar Umma dake rik’eda hannun Ummulkhairi tana fad’in “Ba sai Kin d’auki komai ba.... Maza tashi muje direba yana jiranmu..”


Katseta Khulsum tai da fad’in “Ina zaki Kai ‘Yaruwata  Umma..?” 




SameenaAleeyou📚


*AUREN WATA UKU..!*




*17*




*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*






Katseta Khulsum tai da fad’in “Ina zaki kaita Umma..?” Muryarta Ya soma rawa sosai sanda take ci gaba da furta “Umma shin abinda mutane ke fad’i gaskiya ne..? Umma dan Allah wacece ke..? Ina asalin Ummanmu da muka sani..?”


“Banida lokacin Miki bayanin komai a yanzu Khulsum.. A halin da ake ciki ‘yaruwarki nazo d’auka..” Ta k’arashe tana mai janyo hannun Ummulkhairi.


Cikin azama Khulsum ta rik’e Ummulkhairi tana girgiza mata kai tana hawaye “A’a Adda kar ki bi Umma.. Adda dan Allah kar kije..”


Dubanta Umma tai a yatsine kafin direba ya bud’e mata owners corner saida ta dubi yaranta na d’an lokaci kafin taceda Ummul idan kin gama kya shigo muje.” Daga haka ta fad’a mota kayanta.


Khulsum ta kuma share hawayen da suka gangaro mata. Hannayenta cikin na Ummul take fad’in “Adda dan Allah kar ki bi matar nan.. Bamu san Ina zata kaiki ba.. Watak’ila rad’erad’in da mutane suke da gaske ne Adda.. Kinga Umma dai an canzata gaba d’aya bamu San Wacece ita ba a halin yanzu.”


Khulsum na hawaye take girgiza kai lokaci guda taci gaba “ Adda Ummul, Mai zai faru idan da gaske wajen matsafa zata kaiki.. Mai zai faru idan wani abun ya sameki.?”


Ummul ta zame hannunta daga cikin na Khulsum tabi bayan Umma aka bud’e mata mota ta shige. Tana kallon Khulsum dake tsaye wajen hawaye na gangaro mata yayinda itama Ummul d’in hawaye ne ke gangaro mata. Ta rintse idanunta cikin zuciyarta take furta ‘Kiyi hak’uri ‘Yaruwata. Ya zama dole nayi wann. Babu abinda zai sameni face Allah ya k’addari faruwan hakan.. Dani dake mun San yanayin Umma a d’abi’a da halayya. Munsan matsalan mahaifiyarmu, Abu ne mai sauk’i a rud’eta.. mahaifiyarmu ce, ya zama dole na bita na gano hak’ik’anin abinda ke faruwa da ita. Domin kaw bazamu bari ta auka ma halaka ba munaji muna gani. In sha Allah komai zai daidaita K’anwata..’ Ta k’arashe tuanin nata wasu hawayen na kuma gangaro mata. 


A daidai gate d’in wani gida mai matuk’ar kyau da tsari  motar tai horn. 


Khulsum da tuni ta d’ale acab’a tabisu a baya ba tareda saninsu ba. Tana ganin gidan da akai parking tace ma me mashin ya ajeta daga can nesa dan sai ta karanci gidan kafin ta danna kai ciki. Allah ya gani bazata bari mahaifiyarsu ta bada ‘yaruwarta ayi tsafi da ita ba. 


Driver na Ida parking Ya fito ya bud’e masu k’ofofin. Zuciyar Ummul sai tsinkewa yake tana duban Umma wacce ta koma mata tamkar bak’uwa. 


Umma ta dafata tana murmushi “Ki saki jikinki Ummul d’ita. Ban kawo ki yanda za’a cutar dake ba. Domin kaw ni mahaifiyarki ce. Tin haihuwarki burina shine rayuwarki ya cika da d’imbin alkhairai kaman dai yanda sunanki yake.” Ta d’an numfasa kafin taci gaba “Kinga nan gidan.. Gidan da za’a share mana hawaye ne.. Gidan da za’a cika mana burinmu da yardar Ubangiji. Kukanmu yazo k’arshe Ummul.. Taho muje..” Ta k’arashe tana mai janyo hannun Ummul. Amma sai Ummul ta tarje.


Umma ta juyo tana dubanta “Ummul ya kika ja kika tsaya, kinga nasan damuwarki bai wuce tafiya da mukai muka k’yale ’yaruwarki Khulsum ba. Sanin halinta, sanin duk abinda aka saka da ita sai ya lalace shisa bamu taho da ita ba.. Shige muje kinji.”


Hawaye sukaci gaba da gangaro ma Ummul. Cikin rawar murya take furta “Umma gidan da za’a cika mana buri fah kikace… Umma Ashe har akwai mahaluk’in da zai cika ma wani mahaluk’i burinsa..? Umma idan kinga burin d’an adam ya cika ya bar duniyar nan ne..”


Bata Kai aya ba Umma ta hanb’are mata baki “Ke ke meye haka.. Daina kira mana mutuwa a nan.. Nidai bazan Mutu ba sai burina ya cika in sha Allahu. Shiyasa nace da yardar Ubangiji. Kuma burina shine na ganki a d’akinki dik rintsi.. Koda k’arshen abinda zan aiwatar kenan a rayuwana..”


Jikin Ummul ya kuma yin sanyin Jin kamar mahaifiyarta ta riga ta zauce. Cak tai tsaye tana duban mahaifiyarta, ta rasa tausayin kanta ne ko tausayin mahaifiyarta take. Muryar wata mata ce ya dawo da Ummul daga duniyar tunanin da ta tafi “Ummul d’inmu ta iso..!” Ta fad’i kyakkyawan murmushi saman fuskarta.


Ummul ta karkato tana duban matar wacce keta faman fad’ad’a murmushinta. Kafin tai wani aune ta k’araso ta rungumeta tana fad’in finally sun had’u. Lokaci guda kuma ta shiga janyo Ummulkhairy tana fad’in maza ta shigo ta shirya mai hoto yanzu zai iso bada jimawa ba. 


Tambayarta kanta take Wacece wann matar..? Ina Umma ta santa..? Hoto kuma..? Wane irin hoto..? Meke faruwa ne wai..? Anya zata iya jurewa..? Anya batai gangancin biyo Umma ba kaman yanda Khulsum tace.. Amma idan mutanen suka cutar da mahaifiyarsu fah.. Zuwanta shine daidai ko dan tasan wani hali Mahaifiyarsu ke ciki. 


Jikin Ummul sai rawa yake yayinda Asshe taci gaba da janyota Har suka shige cikin gidan Umma na biye dasu baki har kunnenta.


*

A b’angaren Khulsum kaw tinda ta shigo gidan ta rasa wani b’angare suka shige. Nan ta hangi wani section daga farko. Ganin k’ofan wajen a bud’e Ya sanyata nufan k’ofan cikin tunanin nan su Umma suka shige. Saidai tana shiga wayam bataga kowa ba. Shiru alamun babu kowa. A hankali cikin sand’a ta soma jada baya zata fice. Saidai tana cikin sand’an da baya da baya taji ta bangaji mutum. A tsorace ta juyo zuciyarta na tsinkewa dukda bata bari tsoron Ya nuna saman fuskarta ba saima sauk’e huci da take. 


Wani matashin saurayi ta gani ya zuba mata ido, hannayensa hard’e. Yana binta da kallo mai d’aukeda alaman tambaya. 


Taci gaba da huci tana hura hanci basu daina duban juna ba.


“Ina ‘yaruwata.. Mai kuka mata.. Su waye ku.?”


Hilal ya girgiza kai kad’an “Excuse me, what are you talking about..? Wait, Who are you..? And what exactly are you doing in here.?”


Gajeren tsaki tai had’ada sa kai zata shige. Hilal ya kuma tare gabanta Yana girgiza yatsa alamun bazai barta ta fice ba har sai ta amsa masa tambayoyin sa “Oh wait. Dakata dakata. Ai bazaki fita ba sai kin sanar dani wacece ke. Daga ina kike..? Kuma mai ya shigo dake b’angare na.?”


Ya d’an girgiza kai ganin har lokacin hararsa kurum take. A tunaninsa sabuwar mai aikin Amminsa ce a gidan. Ya katse shirun da fad’in “You must be new here? Basu fad’a miki masu aiki basa shigowa b’angarena ba saida izinina.?” 


Kallonsa tai daga sama zuwa k’asa jin ya kirata da mai aiki “Kaga Malam ka bani hanya na wuce. Banida lokacinka balle na tambayoyinka. Watak’ila ba kai nazo nema ba.!” Ta k’arashe kaman zata bangajesa ta shige.


Ya d’an matsa Ya bata hanya ganin da gaske bangajesa zatayi. Lokaci guda yabi bayanta da kallo “Who’s she.? She doesn’t sound like mai aiki.” Ya d’an girgiza kai har lokacin yana duban k’ofan “She’s so tough.” Ya fad’i yana mai tab’e baki had’ida girgiza kai. 

*


Suna shigewa d’akin Ummul ta juyo ta dubi matar amma bataga Umma tareda ita ba. Nan fah tsoronta Ya ninku. 


Asshe ta murmusa ganin har lokacin jikin Ummul bai daina rawa ba “Ki kwantar da hankalinki Ummulkhairi. Ki saki nan gidanku ne kinji.. Ga bathroom ki shiga kiyi wanka duk abubuwan buk’ata zaki samu cikin band’akin.” 


Asshe tasa kai zata fice kenan Ummul tai saurin kamo hannunta “A’a dan Allah kar ki cutar dani.. Dan Allah kar cutar da mahaifyata.. Na San tanada nata irin matsalar amma ita d’in ba mai kwad’ayin abin duniya bace.. Bansan mai ya sameta ba har ta mance damu da mahaifinmu dake kwance gadon asibiti ta zab’i wann rayuwar.. Kiji tsoron Allah kar ki cutar damu.. Na rok’eki..!” Ta k’arashe tana mai duk’awa gaban Asshe tana kuka sosai.


Tallafota Asshe tai ta d’agota cikin k’ok’arin kwantar mata da hankali take fad’in “Ki kwantar da hankalinki Ummul banida wani k’ulli cikin zuciyata taimakonku nai niyya.. Kar ki min mummunan fahimta..”


Ummul taci gaba da kuka har lokacin jikinta rawa yake “Dan Allah kar ki cutar damu kar ki cutar damu..”


Ganin gaba d’aya ta birkice yasa Asshe daka mata tsawa da fad’in “Ke ki mun shiru.. Yi mun shiru dallah.. Kar ki mun shashashanci a nan.. Shige maza kiyi wanka kafin masu kwalliya da mai hoto su iso..” Tai maganar tana k’ok’arin tura Ummul cikin bathroom Ummul tana tarjewa tana fad’in “A’a dan Allah.. Dan Allah a’a..!”


Daidai lokacin Khulsum ta k’araso ta finciki hannun Ummul daga rik’on da Asshe tai mata “Sakar mun ‘Yaruwata.!” Ta fad’i da k’arfin gaske tana fincikan Ummul.


Asshe tai tsaye tana duban Khulsum wacce tuni ta soma tambayar Ummul koda abinda ya sameta “Adda sun Miki wani abu ne.. Muje zo mu gudu.. Zo mu tafi..!”


Kaman daga sama suka sinkayo muryar Umma tana fad’in “Babu yanda zaki kaita.. Sakar mun ‘ya..!” 


Da mamaki Khulsum da Ummul suke dubanta.


Khulsum tace “Umma Allah bazai baki damar cutar da ‘Yaruwata ba sabida tin tasowarta biyayya take Miki. Dani da ‘Yaruwata zamu tafi.. Zamu fice daga rayuwarki Umma idan Har haka kike so..” Muryar Khulsum ya soma rowa sosai “Umma me ya sameki..? Su waye wad’ann..? Menene gaskiyan rad’e rad’in da mutane suke akanki.. Umma shin kin manta da k’alubalen da ahalinmu suke fuskanta..? Shin har akwai abinda Yafi Miki ahalinki mahimmanci..? Umma Abba yana kwance a asibiti tsakanin mutanen da suke mafarki da burin ganin bayansa.. A daren da kika zab’i ki tafi ki barmu Har kusan kwana nayi a police station.. Duk ina kike Umma.. Ina kike sanda mahaifinmu yake tsananin buk’atarki kusan shi.. A kullum muna fita mu fuskanci mutane da maganganun da suke jifanmu dasu.. Yanzu kin zagayo kin d’auke ‘Yaruwata kin kawota nan ayi tsafi da ita.!”


Bata kai aya ba taji sauk’an mari a k’uncinta. Ta d’ago tana duban Umma dake sakin huci.


Lokaci guda take nuna Khulsum hawaye na gangaro mata “Ke baki san komai ba.. Baki san abinda ke faruwa ba.. Zo ki fice… Shiyasa tin farko ban gayyatoki ba dan nasan ke dai kam ba’a k’ulla alkahiri dake.. Zo ki fice..” 


Muryar Asshe ne ya katse su. Ta dubi Khulsum tace “Kar ki Fad’i abinda baki Sani ba yarinya. Duk fad’i tashin da mahaifiyarku keyi akanku ne da mahaifinku. Ina kuke a lokacin da kishiyar mahaifiyarku ta koreta tace taje ta nemo kud’ad’en da za’ayi ma mahaifinku jinya..?”


Khulsum ta kaikaito tana mata wani irin duba “Wacece ke..? Me kike nema daga wajen mahaifiyata..?”


“Ki kirani Sirkar ‘yaruwarki Ummul.. Domin kaw nan bada jimawa ba Ummulkhairi zata zamto matar D’ana.!”


Da mugun mamaki dukansu suke duban matar da kuma Umma.. suka kuma juyowa suna ma Umma wane irin duba Wanda su kansu basu san duban me suke mata ba a halin yanzu. 


“Sirka..! Matar D’ah..!” Khulsum ta nanata tana duban Asshe da Umma kafin ta kuma juyowa ta dubi Ummul wacce ita kanta cikin rud’ani da duhu take.


Umma ta jinjina kai “K’warai kinji da kyau.. Wann matar da kike gani k’anwa take wa mahaifiyar mijin Ummul d’ita.. Wnn karan bazan bama wani k’ofa Ya lalata auren Ummul d’ina ba, ba ke ba Khulsum ba Tani da ‘ya’yanta ba ba kuma sauran munafukan mutanen layinmu ba.. Dan haka zo ki fice..!”


Ta k’arashe tana k’ok’arin rab’a hannun Khulsum dana Ummul amma sai taji wann karon Ummul ta rik’e hannun ‘yaruwarta k’am tak’i saki hawayen dake idanunta sun kafe sun daina zuba.


Ummul ta girgiza kai tana duban mahaifiyar tasu cikin rashin yarda “Har yanzu wann ne damuwarki Umma.. Ki aurar Dani kota halin k’ak’a..? Shin Umma rashin aurena ne kawai k’alubalen da muke fuskanta a rayuwa..?” Muryarta Ya soma rawa sosai “Abba yana cikin wann yanayi.. Ahalinmu suna cikin wann jarabawa amma ke damuwarki har yanzu guda d’aya ne Umma.. Shin Umma bakida sauran matsaloli na rayuwa ne sai wann..? Umma iyakacin kiman da nake dashi kenan a wajenki a matsayina na ‘yarki..? Iyakacin kiman da mahaifina yake dashi kenan a wajenki matsayinsa na mijinki.. Umma ina zaki kai girman hakkin Abba.. Ta Ya zaki shirya aurar da ‘yarsa yana kwance cikin wann hali.”


Khulsum na hawaye ta katseta “Ta Ya zata shirya sayar masa da ‘Ya dai.. Adda dan Allah kizo muje.. Muje mu nemi agaji daga hukumar hisba wllhi Umma bata a hayyacinta..” Ta k’arashe tana kuka sosai.


Ummul na hawaye take girgiza kai “kiyi hak’uri Umma.. Ki yafe mun amma.. amma Bana tunanin wann karon zan iya Miki biyayya.. Kiyi hak’uri zanbi ‘Yaruwata mu tafi.!” Tana ida fad’in haka ta janyo hannun Khulsum “Muje Khulsum..!”


Umma ta dubi Asshe hawaye na k’ok’arin ciko idanunta “Kin gani ko kinga abinda nake fad’a Miki.. Wann ‘yaruwar tata ta kora mata mazan aure  sunfi abinda suka fi da wann bak’ar Zuciyar nata. Kin gani hassada take da ita.. Toh wllhi wann karon ban shirya jin kunyan duniya ba.!” Tana huci take duban su Ummul da k’iris Ya rage basu fidda k’afafunsa daga cikin d’akin ba. 


Umma ta bud’e murya tace “Ummulkhairi.! Idan kika saka k’afa kika fice daga d’akin nan.. Ki mance kinada mahaifiya Suwaiba..! Wllhi wllhi idan Har ki kai sanadin da mutanen nan zasu ce sun fasa auren nan toh Babu ni babu Ke kuma ke ba ‘Yata bace daga wann lokacin.. Ki nemi wata mahaifyar amma ba ni ba..!” Ta k’arashe tana sakin huci.


Cak Ummul ta tsaya ta kasa koda motsa k’afarta guda.


Gani haka yasa Asshe bud’e murya “Ba sai kin mata baki ba! Baza kuma a mata dole ba. Yardarta da amincewarta shi zaisa ayi wann Auren.” Ta maidoda dubanta ga Ummul “Har yau ba’a biya kud’in surgery da za’ayi wa mahaifinki ba. Anyi masa komai, an canza masa d’aki. Yana samun duk wani kulawa saidai kud’in aiki ne kawai yai saura.. Kinsan dalili..?”


Ummul ta dubeta cikin tsananin sanyin jiki “Sadakin ki shine kud’in da za’a biya ai ma mahaifinki aiki Ummulkhairy..” 


Asshe taci gaba da takowa gaban Ummulkhairy, su duka biyun suna duban juna “Nasan za’a iso wann gab’ar. Shiyasa ban bari an biya kud’in aikin ba. Har sai nida Ke mun gana da juna. A halin yanzu, ki sani Aurenki shi kad’ai ne zai ceci mahaifinki. Domin kuwa sadakinki da zamu biya shine kud’in da za’a masa aiki a ceci rayuwarsa.. Wuk’a da nama na hannunki... Yanzu idan kika ce baki amince ba. Ni kuma zan janye komai ku nemi wani hanyar da za’ayi wa mahaifinki aiki..”


Umma ta kuma bud’e murya ganin Asshe tayi nasaran dakatar da Ummul.


“Wacece matsalar ahalinmu Ummul. Kece matsalar mu. K’addararki shi yai silan kwanciyar mahaifinki.. Idan Har akwai wacce tafi cancanta tai sadaukarwa mai girma wa mahaifinku.. Toh ki sani kece kika fi cancanta Ummul.!”


Khulsum ta soma girgiza kai tana duban Ummul “A’a Adda, dan Allah karki amince.. Akwai na gari da yawa. Na Allah basa k’arewa.. Dan Allah kar ki amince da wann auren na rashin galihu Wanda ko sanin mijin bakiyi ba.” Ta k’arashe tana ci gaba da janyo hannun Ummulkhairy alamun tazo su tafi. Amma sai taji Ummulkhairy ta doge. Lokaci guda take girgiza kai tana duban Khulsum “Kiyi hak’uri Khulsum.. Na zab’i ceto rayuwar mahaifina koda shine abinda zanyi na k’arshe a rayuwata. Zanyi auren.. Zan auri ko waye Umma ta kawo dan na ceci rayuwar mahaifina.. Gaskiyar Umma ne. Watak’ila idan nayi auren komai zai zo k’arshe. Watak’ila matsalar ahalinmu zai k’are. Watak’ila ni ce matsalar kaman yanda Umma tace.” 


Khulsum na hawaye take girgiza mata kai alamun a’a. 


Cikeda k’osawa Umma ta dubi Khulsum. Kinji abinda tace “Ita d’in ’ya mai biyayya ce ba irinki ba. Sakar min hannun ‘ya kafin ki mata sanadin abun alheri da ya sameta.”


Khulsum ta girgiza kai tana duban Umma. Lokaci guda ta soma jada baya. Tana duban Ummul hawaye na gangaro masu su duka biyun. 


**


A can gida kaw Mama tana zaune tsakar gida ta rapka tagumi ga su Azeema da Badia sai dadd’age Kayan masarufin da Suwaiba ta kawo suke. Yaran Salima suna gefe an had’asu da Kayan mak’ulashe. Babu yanda Mama batayi  ba kar su tab’a Kayan Suwaiba Kayan Shan jini amma babu wacce ta kula mama cikinsu sai Salima wacce ta tayata da tagumi. Gashi Salimar ta basu labarin irin kud’ad’en da Umman ta kashe a asibiti. Amenity ma aka maida Abba executive room kula ake basa na musamman. Su Azeema kam har so take washe gari yayi ko Umma zata sake zuwa ta rok’eta Aron tufafin kece raini taje bikin dangin mijinta da suke dashi a satin. 


Mama ta kuma sauk’e kakkauran ajiyan zuciya tana tuna Suwaiba a baya Suwaiba fah data maidata bora cikin gidan farkon aurota wai itace yanzu duniyar nan ta juya akeyi da ita. Gashi har ‘ya’yanta na cikinta sun fara son Suwaiba da tarayya da ita. Ikon Allah Lallai ta yarda babu mayaudariyar aba irin duniya. Yanzu zata rud’eka ka zata tanayi dakai anjima kad’an ta sake ta Kama wani a Barka bakin Tasha. Ita yanzu haka tanaji tana gani Suwaiba zata ci gaba da zuba mata bariki a gida. Lallai bataci ta zama ba. Ya zama dole ta san abinyi.


**


Abuja



Saukowa yai cikin shirin fita waya manne kunnensa “Family dinner?” 


Ya d’an girgiza kai yana ci gaba da sauk’owa “This is not part of the agreement Mommy. You know we can’t stand each other.” 


Shiru yai alamun yana sauraro daga mahaifiyarsa  “Fine, I’m on my way there. Amma wann zai zama na k’arshe.” Daga haka katse kiran yai.


Dareen ta k’araso tana dubansa “Going somewhere.?” Tace tana mai kamo hannayensa murmushi saman fuskarta. 


“To my Mom’s” Ya fad’i a tak’aice sai kuma ya k’ara da “Don’t wait for me for dinner.. Maybe I’ll be back late.” Ya fad’i yana shafan b’angaren fuskarta guda. 


Ta d’an jinjina kai “Haidar, don’t you think it’s high time you introduce me to your family. After all, we’ve been married for months now.” 

 

Hannayenta ya kamo cikin nasa “I don’t think it’s necessary. Those people mean nothing to me. I don’t even consider them family.. Na rubuta yarjejenyar rabuwa dasu. Rabuwa ta har abada.”


Tai masa k’uri tana dubansa, Ya d’an janyota cikin jikinsa suna fuskantar juna sosai “You.. And only you.. You are the only family I have.” 


Murmushi ta saki zuciyarta zallan k’aunarsa. Ta shafi gefen fuskarsa tana fad’in “And I’ll love you till my last breath.”


Ya murmusa had’ida manna mata light kiss. Lokaci guda Ya kuma mata Sallama kafin ya fice. 


Tabi bayansa da kallo cikin d’aurewar kai. This is not like him. Ya canza gaba d’aya. Mutumin da ya tsana ai masa zancen iyayensa shine yanzu yake zuwa wajensu akai akai.. Sann mai yake nufi da ya rubuta yarjejeniyar rabuwa dasu..? Shin Wai meke shirin faruwa ne..? Haidar ya canza gaba d’aya wani sabon kusanci na neman shiga tsakaninsa da ahalinsa.. At the same time yana cewa ya kusa datse duk wata alak’ar dake tsakaninsu. What exactly is going on..? Kasa nemo amsar da Tai ya sanyata k’arasawa saman kujera ta zauna tana kuma fad’awa duniyar tunani. 


**


Ita dai tana Jin yanda makeup artist d’in keta faman zuzuta kyaun da tai amma bata tanka ba. Dan physically ne kawai take wajen amma tinaninta da hankalinta basu a wajen. Duban fuskar nata take cikin madubi Wanda dukda makeup d’in ba mai tsanani bane. Amma abinka da wacce bata saba ba sai take ganin kaman an canza mata kamanni ne . Dama tin can ita ba gwanar kwalliya bace balle yanzu da take tsaka mai wuya. Bata tab’a tsammanin Umma zata tafi da nisa har haka ba. Tana jin sanda su Umma da Aunty Asshe suka shigo sai faman zuzuta kyaun da tai suke. Lafaya ne Wanda kallo guda zaka masa ka tabbata Ya amsa sunansa kalan peach Wanda Ya dace da skin color d’inta da bai cika haske ba haka nan kai tsaye baza’a kirata bak’a. sai black long sleeve shirt daga ciki, an kwantar da lallausar bak’ar sumarta da Ya sha gyara daga gefe. 


Asshe ta k’araso da sauri ta mik’ar da ita tsaye “Wow! lallai za’a haifo mana Fulata shuwa. Yauwa ‘yar albarka Uwar alkhairi.. Maza muje masu hoto suna parlor suna jiran fitowarki.”


Ummul ta d’ago ta dubi Umma amma sai taga Umma ta kauda kanta gefe alamun bazata saurare ta ba. Cikin sanyin jiki ta soma jan k’afafunta tana biyeda Asshe wacce ke rik’e da ita. Can k’asar zuciyarta bata komai sai ambaton Allah domin ya shiga lamuranta.


Suna fitowa parlorn suka tadda masu d’aukan hoto har kusan mutum uku. Tai tsaye tana duban masu hoton wanda k’arasowarta kawai suke jira komai nasu ya zama ready. Ji tai kaman kar ta k’arasa wajen amma sai maganar Aunty Asshe ya fad’o mata “Kud’in Aurenki shine kud’in aikin mahaifinki” Ta d’an d’aga k’wayan idanunta sama cikin k’ok’arin hana hawayenta zuba. Tamkar kazar da k’wai ya fashe ma a ciki haka take takowa cikin parlorn. Ta k’arasa ta zauna yanda masu d’aukan hoton ke nuna mata. Lokaci guda zuciyarta na karanto mata ‘Komai da kike gani na faruwa akwai dalilin faruwarsu Ummulkhairi.. Ita rayuwa jarabawa ce gaba d’ayanta. Allah yayi tanadi wa masu hak’uri kaman yanda yayi alk’awari.. Watak’ila kasancewar Umma a matsayin mahaifiya a gareki shine babban k’alubalenki a rayuwa.. Kiyi hak’uri kiyi mata biyayya.. Har abada bazaki tab’e ba.’ Da wann batu na zuciyarta taji k’warin gwiwa na d’an zuwa mata. 


Umma ce mai nuna mata styles d’in da zatayi har gyara mata zama take tana fad’in tai murmushi kyaunta ya bayyana. Kuji fah. 


Izuwa lokacin Ummul ta daina mamakin Umma sai addu’a da take wa mahaifiyar nata cikin zuciyarta. 


Aka d’auki hotuna aka gama dikda cikin idanunta akwai alamun hawaye a duka hotunan amma kam tayi kyau TabarakAllah ma sha Allah inji Aunty Asshe. Fad’i take d’ansu yayi dacen mata. 


Bayan Asshe da Umma sun keb’e Umma tace “Toh yanzu meye abu na gaba Hajja Asshe.?”


Asshe tace an tura ma mutumin da zai wanke hoto can Abuja ya kai ma ‘yaruwata. Yau zasuga  Amaryarsu  Ummulkhairy a hoto kafin su ganta a zahiri. 


Umma ta lumshe idanu had’ida sauk’e ajiyan zuciya. Lokaci guda ta d’aga hannuwa sama “Ubangiji kasa an dace.. Allah yasa Ummul d’ina ta dace.. Allah na rok’eka ka jefa k’aunarta cikin zukatansu a kallon farko..”


Asshe ta murmusa ta dafa Umma “Anma dace in sha Allahu. Kinsan dai ance wai gani ya kori ji Shiyasa za’a aika masu hotunan Ummul su gani su shaida amma ‘Yaruwata da D’anta basuda matsala. Yanzu Abu na gaba sai maganan kai lefe da saka rana.. Inaso duka ayi su a gobe ne. Amma kafin nan dole mu samu magabatan Ummul ayi magana.. Kinaga dangin mahaifinta zasu amince su bamu aurenta.?”


Umma tai shiru kaman mai nazari. Cikinta ya bada wani sauti k’uuu.! Ita sai yanzu ma ta Tina da za’azo wann gab’ar. Ta soma ‘yan kame kame. Sai kuma ta nusa tace “‘yanuwansa basa jituwa dashi abinki da gidan da ‘yanubanci ya raba kai. Yaruwarsa mace ce guda d’aya tak, kuma itama Sun raba gari tinda jimawa. Kuma mace ai bata bada aure. Kaf ‘yanubansa ne gidan Wanda ba wani ganinsa da gashin ido suke ba..” Idanun Umma suka kawo ruwa murna na Neman komawa ciki take duban Asshe “Toh.. toh.. Yanzu mai zai faru idan suka k’i amincewa su bada auren Ummul..?” 


Saurin katseta Asshe tai “Haba Suwaiba kin faro abu da zafinki kar ki badani mana… Keda kike da babban makami.. Bakiga yanda kika aje Kishiyarki a yanda ya Kamaceta bane..? Ai kud’i Sune jigon rayuwar nan Suwaiba. Idan kud’i na aiki toh na tabbata Miki zasu bada auren Ummul ba tareda wani b’ata lokaci ba dan nayi imani kaf d’insu fama suke da rayuwar nan ta yau..”


Umma ta jinjina Kai “Kuma fah kince wani abu dan ko yau d’in nan da naje nai rabon kud’in ina ganin Baballe ya amshe Wanda na bawa D’ansa ya soke a aljihu.. Kunya ce ta hanasu nasan suma da Sun shiga layin rabon kud’in..”


Asshe tace “Ah toh kin gani ko. Ke fah yanzu sai abinda kika ce a wann gidan.” Ta k’arada “Ita kuma Ummul zata zauna a nan a mata ‘yan gyare gyare na amare.. Mai gyara na musamman na d’auko daga can gida Maiduguri.Kuma kinga dai  yaro ne d’an gayu Wanda rabin rayuwarsa turai ne Ya saba cin karo da matan turawa da wayayyun mata da suka goge. Kinga kuwa dole duk wacce zata je matsayin matarsa ta wanku da kyau ta kuma k’ara samun gogewa gudun kar a samu matsala dukda ko a haka aka kai masa Ummul na tabbata baza’a samu matsala ba amma kinsan ance idan kanada kyau ka k’ara da wanka. Kinsan sha’anin d’an yau.” Ta d’an gyara tsayuwarta “Sann zamanta a can gidan naku wani tsautsayin na kuma giftawa Wanda bazamuyi fata ba. Kinga Har kawo wann lokacin kishiyar ki batasan abinda ake shiryawa ba.”


Umma tai karaf tace “Ai Kinga wann ‘yaruwar tata da ta fice ko bala’inta kad’ai Ya isa ya iya jawo wani matsalan tinda kinga a nan take ce mata su gudu. Toh kafin ta koma can na shafa cikin dare naji sun gudu gwara ta zauna a nan asiri na a rufe a kula da ita idon masu ido bai ganta bakin masu baki bai tofa ba.”


Asshe ta jinjina kai “Cikin kwanaki k’alilan komai zai kammala da yardar Ubangiji Ummul d’inki ta shige d’akin aurenta mafarkin ki ya zama gaskiya.”


Umma sai ta fara hawayen farin ciki tana fad’in shikenan burinta yana gab da cika. Allah zai cika mata wann buri nata daga k’arshe. 


Asshe ta girgiza kai kafin ta fice ta bawa Umma waje tai mai isarta.



A haka Ummul ta k’araso ta tadda Umma wacce itama hawaye ne kwance saman fuskarta. 


Ta k’urawa mahaifiyarta ido. Sai kuma tasa bayan hannunta ta share hawayen dan taji kaf tattaunawar da su Umma sukai.


“Alfarma d’aya zan rok’eki Umma.” Ta fad’i cikin rawar murya. 


Umma ta dubeta wann karon hawaye ne saman k’uncinta.


Ummul taci gaba “Ki kaini wajen Abba na gansa nai masa Sallama kafin ku killaceni a wann gidan.”


Umma ta jinina mata kai tana sakin murmushi ta kamo hannayen Ummulkhairi “Zamuje Ummul. Zamuje kiga mahaifinki. Sann zan baki labarin duk abubuwan da suka faru dalla dalla tin daga lokacin da Tani ta fatattake ni naje na nemo kud’ad’den jinyar mahaifinku.”


Bayan Umma ta labarta komai dangane da had’uwarsu da Asshe da irin duk wani taimako da Asshe Tai mata. Da buk’atan Asshen na nema ma d’ansu aurenta. Jinina kai Ummul tai ba tareda tace komai ba dan kalamai sun k’are saman harshenta. Abinda yai mata saura hawaye ne Wanda suma d’in batada tabbaci idan basu kusan k’arewa ba. 


Driver ne ya d’aukesu Ya kaisu Har asibiti wajen Abba. 


Mama dake zaune a haraba tana hangosu ta mik’e cikin sauri ta nemi wajen b’oyo ta b’uya yayinda Ummul da Umma suka shige d’akin.


Umma ta dubi Ummulkhairy tace “Zan barki ki gana da mahaifinki Ummul. Ku biyu.”


Ummul ta jinjina mata mai tana goge hawayen da suka kwararo mata. 


Ummul zaune gaban gadon mahaifinsu Wanda idanunsa ke lumshe, ta saka bayan hannunta ta share hawayen da suka gangaro mata, abubuwan da suke faruwa da ahalinsu sai gifta mata suke a k’wayar idanu. Ta d’aura hannunta guda saman na Abba. Cikin rawar murya take furta “Abba tinda ka kwanta komai bai k’ara daidaita ba.. Umma ta canza Abba..” Sai kuma tai shiru tana share hawayenta “Abba koda bana nan… Ban sani ba  ko zamu sake had’uwa ba ko bazamu sake had’uwa ba. Abba ka yafe wa mahaifiyata a bayana. Dan Allah ka yafe ma Umma.!” Kuka ya hanta ci gaba da magana. 


Da k’yar kukan nata Ya tsagaita kafin taci gaba “Abba bazanso wani wanda ba kai ba ya aurar dani. Watak’ila Umma ta hana maka wann damar ne domin ceto naka rayuwar.” 


Muryarta yaci gaba da rawa “Abba banida wani zab’i.. Rayuwarka na kan gab’a a nan.. Watak’ila wann shine maslahan ahalinmu. Watak’ila komai zaizo k’arshe. Watak’ila ni ce matsalar. Watak’ila idan nayi nesa daku zaman lafiya da kwanciyar hankali zai wanzu tsakanin ahalin. Abba zanyi duk wata sadaukarwa sabida ahalina. Ka yafe mun Abba. Kuma ka yafe wa mahaifiyata .” Ta k’arashe tana mai kifa kanta gefen Abba hawaye na kuma kwararo mata.


Mama dake lab’e bayan window ta waje taji duk abinda Ummul tace. Wato Suwaiba ta shirya aurar da Ummulkhairi ne a sirrance..? Shin wann shine dalilin canzawan Suwaiba..? Aiko idan haka ne sai taga ta yanda za’ayi wann aure.. Idan Suwaiba tasan wata bata San wata ba. Toh amma ta ya zata b’ata auren tinda Suwaiba bata nuna masu mijin Ummul d’in ba.? Kar dai Suwaiba ta samo attajiri ne ma Ummul d’inta.. Idan har al’amra sukaci gaba da tafiya a haka kenan fah Suwaiba zata zamto sarauniya a gidan. Sai abinda tace. Harta ‘ya’yan cikinta su Azeema sai Sun gagareta. Tin yanzu ma komai ya canza balle abubuwa suci gaba da tafiya a haka.. Uwa uba Har kawo wann lokacin basu saka Tasi’u a idonsu ba... Dawowan Suwaiba dik shi ya karkata masu hankali ta kasa aiwatar da komai gameda b’cewan Tasi’u. Toh inaga Abubuwa sunci gaba da tafiya a haka.? Yanzu ita fah zata tashi a tutan babu kenan ga Suwaiba ta dawo da sabon sauyi..


Mama ta koma gefe saman benci ta zauna had’ida buga uban tagumi. Kallo d’aya zaka mata ka fahimci duniyar tai mata atishawan tsaki. Sai faman sauk’e tagwayen ajiyan zuciya take tana canza salon tagumin ta. Babu babban abinda ya bata takaici kaman da ya kasance yanzu dik abinda suke ci daga wajen Suwaiba ya fito.. Shikenan Suwaiba fah ta amshe girman nata. Abinda yai saura kawai shine Suwaiba ta umarceta ta soma kiranta da Yaya.


Saiga Mama na hawaye tana fad’in har abada bazata bari Suwaiba tai nasara akanta ba. Idan abinda zata aiwatar k’arshe shine hana yuwan auren Ummulkhairi ta shirya yi. Da dai ta bari Suwaiba tai galaba akanta gwara tai komai dan nasara nata ne da yaranta ba na Suwaiba da nata ‘ya’yan ba. Da wann tunani ta mik’e tagajan magajan domin kaw zama bai ganta ba. 


*

Kan Ummul na kife gefen mahaifinta tana ci gaba da cazgan kuka mai ban taisayi. 


Umma ta k’araso ta dafata. 


Ummul batace komai ba Har Umma ta ta k’araso wajen. 


“Tashi kije Ummul direba yana jiranki. Ki sani bazan bari ki koma gidan mahaifinki ba har sai ranan Aure gudun kar wani abu ya gifta. Kindai san matsalarki da abubuwan da mukaita fuskanta a baya na fashe fashen Aurenki. Wann karon ban shirya ba ma wani k’ofa ya lalata Aurenki ba. Naga Tani bata nan a nan, zan zauna wajen Abbanku Har Tani ta dawo. kuma zan karanto masa komai koda bazai bud’e idonsa ba na tabbata kunnuwansa da zuciyarsa zasu saurareni.”


Ta murmusa tana duban Ummul “Na tabbata a yau mahaifinki ya farka ya ganki a d’akin Aurenki zaifi kowa farin ciki sann wann kad’ai Ya isa ya zama silan yaye damuwar dake k’unshe cikin zuciyarsa.”


Dubanta kurum Ummul Tai ba tareda ta iya cewa komai ba. Har yanzu dai a idon Umma itace matsalar ahalinsu da k’addararta. 


Ta kuma juyowa ta dubi Abba hawaye suka kuma gangaro mata. A hankali ta isa ta tofa masa addu’o’i kafin tasa kai ta fice jiki a mace. 

**


Abuja..


Zaune suke gaba d’aya a nan lambun dake farfajiyan gidan. Mommy Daddy harma da Anisa. 


Mommy dai bata sama bata k’asa gaba d’aya kana ganinta zaka hango tsantsan farin cikin da take ciki. 


Ta dubi Anisa tace maza ta sami one of the mades su shirya wajen cin abincin mutum guda. 


Daddy ya dubeta “Are you expecting someone.?”


Mik’ewar da Anisa zatai ta hango shi ya nufo garden d’in. Looking handsome as always. Zuciyarta yai wani irin yankewa. 


Mommy ta fad’ad’a murmushinta tana nuni da Haidar dake k’arasowa “Oh! He’s here already.” Ta maido da dubanta ga mijinta “Ya kamata mu rinka samun lokaci irin haka na musamman domin ahali. After all, amarya za’a kawo mana very soon.”


Baice komai ba yaci gaba da abinda yake. Dan yanzu ya kula Kwaise batada zance sai na auren D’anta. 


Haidar ya k’araso Mommy na masa sannu da zuwa. Sai nan nan dashi take. Wani sabon kula da soyayya take nuna masa abinda bata masa a baya ba. Kaman tayi ma wofi haka ya d’auki abun tinda yasan ba dan Allah take ba. 


Koda Anisa ta kawo plate karb’a Mommy tai tana k’ok’arin serving d’insa sai haba haba dashi take tana tambayarsa me za’a zuba masa.


Cikeda k’osawa Haidar Ya rik’e hannunta Ya amshi plate d’in “Mommy please that’s enough, I can do it myself. I’ve been doing it since childhood.” 


Jikinta ya d’anyi sanyi ta soma Tina ita dai tin tasowarsa tin yarinta bata tab’a tambayarsa yunwan cikinsa ko lafiyarsa ba. Masu aiki da Nannies Sune suka San lafiyarsa, cinsa ko shan sa. Har yayi ciwo ya gama bata san yayi ba kuma ba matsalar ta bane. The only abu da take tambaya ta kuma tada hankali akai shine karatunsa na boko da sakamakon da zai birge mahaifinsa. Idan kuwa bai kawo sakamakon da zai birge mahaifinsa ba ranan zai wuni ne a d’aki mai duhu kuma a kulle cikin tsananin horo. 


Mommy ta gyara zama ganin table d’in Ya b’ata shiru sai sautin cutlery dake tashi cikin plates. 


Ta d’an murmusa tana duban Haidar “Ya labarin aiki.. Ina nufin sabon project d’in naku.. Kun fara ne.?”


Yasan so take tai creating hiran da zai had’asa magana da mahaifinsa. Ya d’an girgiza kai kad’an “Still ironing out the details..”  Ya d’ago yana dubanta sosai tinda yasan tasan komai “In a couple of months, Mommy. Let’s say two to three months.” 


K’arasowar wata mai aiki rik’eda k’aton frame a rufe Ya katse Mommy. Mai aikin ta k’araso cikeda ladabi ta tsaya nan bayan Mommy rik’eda  frame d’in tana sanar da ita security ne Ya shigo dashi. 


Mommy ta jinjina Kai tana mai nuna mata yanda zata ajiye. 

Ta maidoda dubanta ga Ahalinta tana kuma fad’ad’a murmushinta “Na had’a mana wann cin abincin ne a tare domin na gabatar mana da wani mihimmin abu. Musamman gareka Haidar.” Ta k’arashe tana mai isa jikin frame d’in. 


Ta shiga bud’ewa sannu a hankali tana mai furta “Kyakkyawar Amaryar mu. Matar D’anmu Haidar. Sirkarmu wacce zata zamto silan dunk’ulewar ahalinmu.” 


Cak ya tsaya da abinda yake. Lokaci guda yana mai matse fork and knife dake rik’e cikin hannunsa. Bai iya janye idanunsa daga saman plate d’in ba haka nan bai dubi hoton da mommy ke nuna masa ba wacce ta ambaceta da matarsa. 


Girgiza kai Daddy yai yana tunanin matarsa ta zauce da wann auren da take yunk’urin yima d’ansu. Ya d’auki tissue had’ida goge bakinsa. Ya dubi Mommy kafin yace “Are you in your right state of mind. What’s the meaning of this Kwaise.?”


Mommy tace “Gani ya kori ji Engr. Matar Haidar ce. Idan ba a hoto ba nasan bazaije ya ganta ba har sai Randa aka kawo mana ita gidan. So kafin a kawota yak’i amincewa yace gaibu na auro masa. Gwara na samu dalilin kafa hujja. Look kalla kaga, zasu dace da Haidar.. Asshe ta iya zab’e.” Ta k’arashe sai duban hoton take tana murmushi. 


Daddy dai kallon wacce ta samu matsala yake mata. Lokaci guda ya girgiza Kansa “I’m done here.” Yai maganar yana mai barin wajen. 



Zuciyar Anisa yaci gaba da bugawa tana mai duban hoton. Cewa da Mommy tai Asshe ta iya zab’e shine keta yawo cikin kumnuwanta. Mai kenan hakan ke nufi.? Amminta ce ta zab’o wa Haidar mata.? Mahaifiyarta ta turota gidan ne dan taci amanarta ta nema ma Haidar auren wata daban a garin Kano.? Ko kuwa mai Ammi take  nufi da ita.?




SameenaAleeyou📚

*AUREN WATA UKU.!*




*19*







*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*




Ruwa aka kawo za’a yayyafa ma Umma Asshe ta dakatar dasu ta bud’e bakin jaka ta shiga lik’a ma Umma kud’i had’ida umartan matan da ke gefe da su rangad’a ma Umma gud’a cikin kunne. 


Aiko firgit Umma ta mik’e tana tambayan da gaske ne an d’aura auren Ummul, Ummul d’inta dai. Sai kuma ta fashe da kuka tana fad’in bata tab’a tsammanin zataga  wann rana nan kusa ba. 


Masu lallashi nayi masu tausayi nayi masu murna nayi harma da masu takaici. 


Toh komai akace d’an lokaci ne, shi kuma aure baka tab’a yinsa sai lokacin da Allah Yace. No matter how hard you try or how many relationships make. Zai faru ne kawai a lokacin da Allah ya nufa. Yau dai Allah ya k’addari za’a d’aura auren Ummulkhairi bayan tulin fad’i tashi da mahaifiyarta taitayi dan dai taga ‘yar tata tayi aure. Dukda irin kawo sadaki ana janyewa saka rana ana d’agawa harma da amshe lefe yau Allah ya nufa ya kuma k’addari za’a d’aura auren. 


‘Ya’ya musamman mata tamkar k’wai suke hannun iyayensu. Babu Iyayen da zasu so wani abu na k’i bisa tsautsayi ko tilastawa ya fasa wann k’wai da suke rik’e dashi cikin kula da kaffa kaffa. Tabbas burin ko wata uwa koma iyaye in general shine da zaran ‘yarsu ta Kai gab’an aure su kaita d’akin mijinta cikin salama da aminci. Saidai wasu lokutan insecurity yakan rinjayi confidence da muke dashi akan yaranmu  Wanda hakan ka iya zama babban threat a garemu. Tsoron zamansu a gabanmu babu aure, tsoron maganganun mutane da abinda ka iya zuwa yazo yakan sa mu mance wani b’angare mai mahimmanci Wanda yake tamkar foundation idan babu shi tamkar anyi gini bisa iska ne . Shine neman zab’in Allah da fawwala masa lamra. Idan tsoron ya rinjayi raunin har aka mance wann gab’a mai mahimmanci hakan ka iya jefa rayuwar yaran cikin had’arin da yafi zamansu gaban Iyayen. Wani auren death sentence ne iyaye suka jefa yaransu ciki ba tareda sunyi la’akari ba. Da yawa auren yayi ajalinsu. Wasu ma anyi tsafi dasu sabida ba’a nemi zab’in Allah ciki ba tun farko. 


‘Ya’ya amana ne hannun iyaye sann sunada hakkoki Akan iyayensu kaman yanda iyaye keda hakkoki Akan nasu ‘ya’yan. Mu fara k’ok’arin sauk’e nauyi da hakkokin yaranmu Wanda shine tarbiya na farko da zamu basu ko dan nan gaba su sauk’e namu nauyin hakkin dake kansu. Bazai yuwu ka haifi d’a ka wofantar dashi ba kai tsammanin zai girma da tausayinka. Da yawan yaran da muke ji muke gani suna zama abin gudu cikin Al’umma mu bincika yaya tarbiyansu ya samo asali. Wasu tun suna yara iyayen sun d’ebe masu albarka da harsunansu. Wasu iyayen basu san cin yaran ba basu san karatunsu ba balle maganinsu Wanda duk nauyi ne da ya rataya kan iyaye. Ko a d’abi’ance Yaron da ya taso cikin kula da soyayya ba daidai yake da yaron da aka wofantar dashi ba. Akwai jarabawa. Idan kayi iya naka Allah ya jarabceka wann kuma jarabawa ce da yake jarabtar bayinsa dashi.


Ba’a yarda ka d’auki ‘yarka ka bada aurenta ma ko wane irin mutum ne yazo Neman auren nata ba dan kawai kana hanzarin ka kauda ita gabanka. Shiyasa addini ya bada tsare tsare cikin Neman auren Kansa kafin aje ga auren. Uwa uba a nemi zab’in Allah cikin duk abinda ake nema. Allah ya shirya mana zuri’a ya azurtamu da yaranmu da samun abokan rayuwa na gari. Ameen. 



Umma naku fah kan kace me ta ware. Har wani cakarewa tai cikin tsaddan leshi da Hajja Asshe ta kawo mata a d’inke. Kayan da Ummul zatai fitan biki ma Hajja Asshe ta kawosu a d’inke masu d’an karen kyau da tsada. Dik wani buk’ata da amarya zatai amfani dasu Asshe da k’awayenta Sun kawo. 


Hajiya Hadiza k’awarta ta dubeta bayan Sun keb’e “Amma fah kawata kin bani mamaki, ko a mafarki ban tab’a hasashoki tsakankanin talakawa ana damawa dake ba. Wai fisabilillahi ya akai kuka amince da wann aure tinda nasan duk yanda tsiya yake ba’a ganinku wajen.”


Murmusawa Asshe tai tana duban Umma yanda taketa shige da fice cikeda farin ciki. Ta kuma duban k’awarta Hadiza “Hadiza kenan, kin fad’a daidai. Duk yanda tsiya da talauci yake bana zuwa wajen. Toh amma babu yanda muka iya ne. Dole ce ta Kama sai anyi auren.”


Hadiza ta girgiza Kai kad’an “Toh amma gida bai k’oshi ba yaya za’a kawo waje. Ina nufin ga Anisa ‘yarki dan me baki had’a auren da ita ba tinda tana zaune itama ba mijin har yanzu.?”


Asshe ta kuma murmusawa “Tinda kikaji na Miki amfani da kalmar dole ki amince kawai dolen ne. Ni fah kaza ce Hadiza bani k’wai na saida zakara. Ke kinfi kowa sanin haka. Yanzu dai ki bari a gama hidiman nan idan mun natsu na sanar dake komai.”


Hadiza ta jinjina Kai a hankali har lokacin mamaki bai saketa ba ganin yanda Asshe ta shiga cikin talakawan nan ana damawa da ita. K’awarta ce tun secondary school ta Santa farin sani. Asshe da zuri’arta worshiping money suke inji su Hadiza. Mutane ne da zasuyi komai Akan duniya da abinda ke cikinsa. Shiyasa ta sha mamakin ganin wann al’amari. Kaman yanda Asshe tace da ita akwai dalili ta tabbata akwai dalilin.


**



A can police station kuwa motar ‘yan sanda na shigewa na Hilal ma ya sako kai. 


Sauri sauri Hilal ya take mata baya ganin ta nufi hanyar da aka shige da Mama sai kururuwa Maman take tana fad’in wllhi bata ci kud’ad’en ba. 


Mama taci gaba da fad’in “Wayyo Khulsum ‘Yata ki cece ni ki ceci Mamanki kar a rufeni. Idan aka rufeni babu mai kula da Abbanku dake kwance gadon asibiti Khulsum.”


Khulsum ta samu zarafin dakatar da ‘yansandan ga bak’auye a gefe yana fad’in kwarankwatsa sai an karb’ar masa hakkinsa. Baici nanin ba nanin bazata cisa ba. Takardun bogi suka kawo masa ya saka hannun. Sarkin kasuwa yace baisan da zancensa ba. Idan sama da k’asa zasu had’e sai an fitar masa hakkinsa. 


Police ya dubi Khulsum yace “Ke kuma fah.?”



Mama tai saurin bud’e murya tace “‘Yata ce. “


Tsananin mamaki sai ya hana Khulsum furta koda kalma. Wai yau Mama ce ke kiranta da ‘yarta. Ikon Allah, Ashe har akwai ranan da Mama zata danganta kanta da jinin Ummanta. Bata kaiga furta kalma ba ta hango Habib mijin Azeema da police woman d’in da kwanaki suka kawota nan police station d’in. Sai wani mannewa take jikinsa. Mama ganin Khulsum tayi shiru ya sanyata duban yanda Khulsum d’in ke duba. 


Ta zaro ido waje tana kuma mutsukesu. Waye take gani haka.? Habibu ne mijin Azeema Sun fito daga wani ofishi yana faman gyara kwalan rigarsa sai washe baki yake ga wata ‘yarsanda gefe sai kashesa da kallo take kaman zata shige cikinsa. Ta dafe k’irji tana furtawa da k’arfin gaske “Na shiga uku mai nake gani.! Habibu..!”


Hankalin Habibu da ‘yarsandarsa ya dawo kansu. 


Mama ta soma nunasa da yatsa “Habibu mai zan gani mai kake a nan..? Amanan Azeema kake ci da wann ‘yarsandan.?”



“Madam ki iya bakinki police station kike ba Tasha ba.” ‘Yarsandan ta fad’a cikin dakatar da Mama wacce tai sokoko tana kallonta. 


Habibu ya wayance “Haba Mama ya kike magana haka.? Nan fah police station ne. Zuwa nai inata fafutuka ina fad’i tashin yanda za’a samu a kamo mana Tasi’u mana Mama..”


Ya dubi mutanen dake wajen ya kuma dubi ‘yansandan da suka kamota “Meke faruwa a nan.. ya na ganki da ankwa.?”


Sai Mama ta soma kuka “Habibu ka ceceni.. Kamo ni sukai.. Ka fad’a masu waye yaci kud’in shagon Malam. Kai shaida ne wllhi banci ba. Habibu kar ka bari a rufe ni.”


Kaman daga sama suka sinkayo muryar Khulsum “Ni kuma zan bada shaidan kece kika sayar da shagon koda kuwa Kotu za’a je na shirya zuwa.!” 


Mama ta kaikaito tana duban Khulsum “Fitsara zaki min a nan Khulsum.? Inji kin biyo ni ne dan ki taimakeni ki bada shaida kaina.”


“K’warai kuwa Mama. Zuwa nai dan na bada shaida akanki na kuma tabbata kin biya abinda kika aikata wa mahaifina Wanda yake kwance baida ikon kare kansa balle dukiyarsa.”


Mamaki ya cika Hilal. Ya dubi wann ya dubi wancan “Wait. D’an dakata, wai dama ba zuwa nan kikai dan ki taimaki matar nan ba.. I thought I heard you call her Mama or something.. Is she not your Mom.? Ba naji ta kiraki ‘yarta ba. Ta ya kike bada shaida mai muni kan mahaifiyarki.. Are you going to let them arrest your mother just like that..? Don’t tell me we came all the way here just for you to make sure anyi arresting Mamanki..”


“Malam kar ka sake kiran wann matar Mamata. Ni ba uwata bace. Kuma ka fad’i daidai zuwa nan nai na bada shaidan abinda ta aikata kafin wancan surkin nata yayi amfani da damarsa ya fiddata.” Ta k’arashe tana nuni da Habib dake tsaye gefen budurwarsa ‘yarsanda wacce ya kawo ta kama Khulsum d’in lokacin da ta mari Azeema. 


“Amma nafi uwarki da ta saida ‘yar Malam Isubu yana kwance. Gwara ni shago kawai na saida.” Mama tace tana huci.


Hilal ya kuma duban Khulsum da mamaki Wanda kalaman Mama ya haifar mata da sanyin jiki. 


Bakauye ya kafe sai an rufe Mama idan ba kud’ad’ensa aka lalo aka basa na. Haka  dole aka jefata cikin cell Habib na kwantar mata da hankali da fad’in zai iya k’ok’arinsa yaga ta fita. 



Khulsum kaw bata kuma fahimtar komai ba tun bayan maganan da Mama ta fad’a mata. Take taji wani irin kuka na zuwa mata. Tabbas Mama ta fad’i gaskiya gwara ita Akan Umma. Ita abun duniya kawai ta saida amma Umma fah mutum ta saida. ‘Yarta da ya kamata ace ta zamto tamkar lu’ulu’u a hannunta. Abu mafi daraja fiyeda shago da abinda ke cikinsa Umma ta sayar. Ko kusa baza’a had’a laifin Mama da Umma ba. Bata San yanda take jefa k’afafunta ba tafiya kawai take tana kuka. Tana Jin wani abu mai kama da k’iyayya Wanda shine zata iya cewa iyakacin alak’arta kenan da mahaifiyarta. 


Tana tafe gefen kwalta Hilal na biyeda ita cikin mota. Yaci gaba da fad’in “You know you are unbelievable.. Da nasan Akan wann dalilin kika taho all the way to police station da ban b’ata lokaci na na kawoki nan ba. Because of you na rasa d’aurin auren d’an uwana.”


“Malam idan baka Kama gabanka ba duk abinda na maka Kai ka saya da kud’inka.. Da ace baka b’ata min jiki ba Watak’ila da ban tsaya na b’ata lokacina wajen ji da kai ba balle har nayi gamo da Mama. Watak’ila da na samu damar dakatar da auren zalunci da ake yunk’urin yima ‘Yaruwata..”Ta fad’i tana ci gaba da sakin huci ga hawaye dake ci gaba da gangaro mata. 


“Blame your step mother then.” Hilal ya bata amsa Kai tsaye.


Khulsum taci gaba da tafiya tana hawaye. 


Hilal yai parking ya fito ya tare gabanta “No I can’t just leave you here. After all, Ni na kawoki nan. Idan wani abu ya sameki I’ll blame myself for the rest of my life. Please get in the car. Ki bari na maida ke yanda na d’aukoki. At least.” 


Bata amsa shi ba sai kukan da take ci gaba da yi dan mugun takaicinsa take. 


Ya d’an waiga yana duban mutane masu giftawa sai kallonsu suke.


Ya d’an kuma gyaran murya “Look, I don’t want people to think that I hurt a girl. Dan Allah ki shiga.. At least ki bani dama na fitar dake daga nan.. Dare ya soma yi duba ki gani.. And is not safe for you to walk alone a babban kwalta irin haka.”


Cikin kuka Khulsum ke dubansa “Na tsaneka.! Na tsani mugayen ahalinka da sukai amfani da raunin mahaifiyata suka sayi ‘Yaruwata da sunan aure.!”


Hilal ya zuba mata ido “Look, bansan meke faruwa tsakanin ahalinmu ba. But the only abu da zan fad’a Miki shine my cousin is a good person.. He has his faults as human. But I can assure you he’s a good person.” Ya d’an tab’e baki “Idan yar uwarki ta kasance matarsa abun kiyi mata murna ne.”


Takaici ya hanata furta koda kalma tasa kai tana ci gaba da tafiya. Hilal ya kuma tareta “Yamma yayi sosai ki shiga na kaiki gida. That’s idan Kinaso ki cimma ‘yaruwarki kuyi Sallama kafin a tafi da ita. Dan na tabbata kawo wann lokacin an d’aura auren. Tinda bakiyi nasaran dakatar da auren ba. Watak’ila zakiyi nasaran samun dama kuyi Sallama idan har kika shiga mota ta.” Ya k’arashe yana nuni da motar.


Bata k’aunan abinda zai kuma had’ata da d’aya daga cikin wann ahalin. Toh amma gaskiya ya fad’a idan batai saurin cimma Addanta ba Watak’ila bazata samu suyi Sallama ba za’a tafi da ita. Saida ta rakasa da harara kafin ta nufi motar.


Hilal ya d’an tab’e baki yana bud’e mata marfin motar “Sorry to say a daidai yanda na d’aukeki zan ajiyeki. Kinga ko ba komai na rage Miki hanya.”


Ta kula nema yake ya dad’a tunzurata hakan yasa bata kuma bi takanshi ba balle ta amsa shi. 


Saidai suna isowa bakin babban kwalta da zai shigar da kai layinsu suka hango motocin amarya na ficewa. Alamun Sun makara amarya ta riga ta hau hanya.


Hilal ya tab’e baki kad’an “Looks like someone didn’t make it on time. Unless zaki bi bayansu.” 


“Ajiyeni a nan.” Ta fad’i tana k’ok’arin bud’e motar.


“Are you serious.?” Hilal ya fad’i yana k’ok’arin juya kan motar cikin k’ok’arin bin bayan motocin.


Da mamaki Khulsum ke dubansa ta kuma jan marfin motar ta jita a rufe alamun ya rufe daga wajensa.


“Malam ka ajiyeni a nan nace ko na maka ihun b’arawo.!”


“You and I both know this is what you want. Kiyi Sallama da ‘yaruwarki. Just admit it.” Ya d’an dubeta sai yai murmushi da gefen bakinsa “Don’t worry, I’ll do you a favor and take you to your sister. After all, Nima can na nufa..” Ya maida idanunsa ga kwalta “Kar ki damu ba sai kin biya kud’in abun hawa ba. A simple thank you will be okay.” 


Bai kuma cewa komai ba yaci gaba da tuk’a motan. 


Izuwa lokacin ta rasa ma mai zatce ma wann d’an rainin hankali. Shiru tai tana duban titi yanda Hilal taketa fifila gudu da ita. 


**


Abuja..



Zaune yai gaban mahaifinsa yana sauraronsa yanda Daddy yaci gaba da fad’in “I will be meeting with our international clients in Nairobi.. Daga can zan wuce Cape Town, southAfrica gameda business alliance da muka fara a can months back.” Ya gyara zaman glasses d’in dake mak’ale idonsa kafin yaci gaba “Maybe it will take me two to three weeks before I return..” Ya k’arashe yana ci gaba da duba documents d’in dake gabansa. 


Haidar ya jinjina Kai yana duban mahaifinsa “So why are you telling me all these Daddy.? Are you.. Do you want to hear from my own perspective.? I mean regarding the alliance.?”


D’agowa yai had’ida d’an zame glasses d’insa yana duban Haidar d’in sosai. “I did not send you to those expensive schools dan kawai ka dawo na saka ka a gaba naita kallonka. But unfortunately it is unfolding.. Watak’ila ba kai bane wann D’an da zanyi alfahari dashi. By now ya kamata ace na huta. Ya kamata ace Kai ke wakiltana a tafiye tafiye irin wann. Saidai Kai d’in banida k’warin gwiwa akanka. It is enough da na amince ka jagoranci project d’in cikin gida..!” Ya kuma dubansa sosai kafin ya k’arada “You are a complete failure to my name Aliyu!” Ya k’arashe yana maida glasses d’insa.


Haidar yai murmushi mai ciwo yana jinjina Kai “Is this the kind of legacy you wish to leave behind for your Son.?” Ya jinjina Kansa zuciyarsa na kuma masa d’aci kafin yaci gaba “I wouldn’t be surprised of course. But You know what Daddy. No matter how insignificant you keep insisting I’m to you.. You can’t deny the fact that your company needs me.. And you need me too.. Kuma shine dalilin da yasa ka kirani kake sanar Dani duka shirye shiryenka.. So Daddy, deny it all you want. But the truth is that I’m very much important to you.. And your company is nothing.! Absolutely nothing without me.!” Yana ida fad’in haka ya mik’e zuciyarsa na masa zafi. 



A daidai k’ofan fita daga sashen ya had’u da Alhaji Gimba na shigowa. Alhaji Gimba na ganinsa ya fad’ad’a murmushinsa. Bai damu ba idan Haidar bai gaishesa ba. Shi dai bazai tab’a cire hope Akan Haidar d’in ba. Alhaji Gimba yaci gaba da fad’in “Congratulations to you and your team. Naji dadin wann al’amari kuma inada yak’inin company bazatayi danasanin zab’en gwarazan da zasu jagoranci wann aiki irinku ba..I trust you and your team.” Ya d’anyi fasali kafin yaci gaba “Wann aikin kampani ne so ina shawartanka kar ka bari wani matsala da kake dashi tsakaninka da mahaifinka yasa kai ma aikin rik’on sakainan kashi ko ka yanke hukunci cikin fushi. Na yarda da Kai amma tunasarwa yanada kyau. The company’s future relies on your hand Aliyu. And we have high expectations of you.. Let’s set our differences aside so we can reach our common goal. Ko dan mu ba ma abokan Adawa kunya.” Ya k’arashe murmushi saman fuskarsa.


Tinda ya soma magana Haidar da hannayensa ke sakale cikin aljihu yake dubansa lokaci guda yana nazarinsa “Trust me, it’s just a matter of time before we find out who the real traitor is.” 


Murmushi Alhaji Gimba ya kuma sakar masa kafin yai nuni da parlorn “Baringa mahaifinka. Have a good evening.” Ya fad’i yana mai shigewa cikin parlorn. 


Lumshe idanunsa kad’an Haidar yai had’ida furzar da huci “Fake life fake people. Everything around this family is fake nothing is real.” Lokaci guda yasa kai ya shige cikin sassarfa zuciyarsa na masa wani irin k’una. 


Ya fito daga sashen mahaifinsa  kenan ya hangi k’atuwar mota ta shigo cikin gidan shak’e da kaya ta nufi nasa b’angaren. Yabi motar da kallo kafin ya nufi hanyar sashen nasa. Nan ya hangi Mommy da Anisa sai nuna ma masu interior d’in yanda zasu jera kayayyakin suke. Ga tsaffin Kayan duka an fito dasu.


Yai tsaye yana dubansu da mamaki. Can Anisa ta hangosa. Sai ta matso kusan Mommy tai mata rad’a a kunne “He’s here Mommy.”


Mommy ta d’ago tana tambayan wane kenan. Ganin Haidar ya sanyata fad’ad’a murmushinta. Ta k’arasa da sauri ta kamo hannunsa “Haidar my son, today is the happiest day of my life.. An d’aura aurenka yau Haidar.”


Sai yaji abun banbarakwai. Shi ya ma mance da wani batun aure da yarjejeniya. Wani irin duba yake mata irin na da gaske take.? Da gaske auren suka masa sabida son zuciya irin nasu. 


Mommy taci gaba da fad’in “Wann shine Mafarin had’in kan ahalinmu da yardar Ubangiji. Cikin ikon Allah komai zai daidaita.” Bakinta ya gaza rufuwa har mamaki Anisa take yanda Mommy ke matuk’ar d’aukin wann aure. Taci gaba da nuna ma Haidar kayayyakin “Look duba kaga. I know you have high taste so I ordered everything to your taste.” Ta saka hannu ta tallafo fuskarsa “Yau d’in ina Jin na cika wani gurbi na zama uwa a gareka D’ana. Burin ko wata uwa kenan taga D’anta yakaiga cikan kamala.”


K’ok’arin cire hannun Mommy daga fuskarsa yake Jin tana wasu irin sunbatu “Mommy will you please stop.! Enough of this drama.” Ya dakatar da ita kafin yaci gaba “Quit the act already! Stop acting like you care.. Like you are responsible.! Like you are doing your motherly duties wad’anda kika makara bakiyi ba tun a baya. It doesn’t suit you at all Mommy.!” Ya k’arashe jijiyoyinsa har fitowa suke. 


“Haidar.” Ta ambaci sunansa kaman mai shirin kuka. 


Dakatar da ita ya kumayi “Mommy you and I both know ba auren tsakani da Allah bane. Ba don ci gaban rayuwana matsayina na d’anki kikai ba. You are doing all this for your own advantage.” Ya d’anyi fasali “Mommy my day is bad enough, thanks to my Dad. bazan bari ki k’ara mun wani akai  ba.!” Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice daga gidan a gaggauce.


Jiki a matuk’ar sanyaye Mommy ta juyo. Anisa ta k’araso ta taddata.


“Mommy seems like ke kad’ai kike son auren nan a gidan nan. Shin bazaki hak’ura da auren nan ba kawai tinda Wanda akayi dominsa baya so. Kawai ki d’aga waya ki kira Ammi ki sanar da ita an fasa tin kafin a kawo matar cikin gidan nan. Dan na tabbata wann auren ba mai d’orewa bane.”


Mommy ta harereta “Ke dalla rufe mun baki. Bansan shashanci, Wann aure da kika gani mutuwa ce kawai zata raba matar da Aliyu. Idan kinga auren ya Mutu ki tabbata matar ta Mutu ne.!” Tana ida fad’in haka tasa kai ta shige tana neman layin Asshe dan Jin mai ake ciki.



Anisa ta tab’e baki tana mamakin wann irin al’amari. 


**


Kano…



Dik maganganun da Hilal keyi cikin motar ba sauraronsa take ba. Hasalima bazata iya tantance mai yake cewa ba da za’a tambayeta. Damuwarta kawai su isa ga ‘yaruwarta tai k’ok’arin shawo kanta su gudu tinda babu idon Umma. K’aran bud’e gate ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da tai nisa ciki. Zuciyarta sai tsinkewa yake tana addu’an Allah ya bata ikon shawo kan Addarta Ummul cikin sauk’i. Tana ji a jikinta wann aure babu wani alheri cikinsa. 


Hilal yana Ida parking tai saurin kama handle tana kokawan bud’ewa.


Ya tsareta da idanu “Easy kar ki balla min marfin mota bayan kin b’ata min da tab’o..” 


Bata amsa shi ba dan bata da lokacinsa. Tana Jin sanda motar ta fita a lock tai saurin bud’ewa ta fito. Sauri sauri ta nufi cikin gidan har kaman zatai tuntub’e.


Hilal ya bita da kallo had’ida tab’e bakinsa kad’an kafin ya nufi bangarensa. 


A daidai mashigar gidan Khulsum taji ance da ita “dakata..!”

 

Cak taja ta tsaya sakamon muryar taji ya dakatar da ita. 


Umma ta gani ta tsaya tayi k’ebebe rik’e da kunkumi tana duban Khulsum d’in.


“Umma..!” Khulsum ta fad’i mamaki kwance saman fuskarta.


Umma ta jinjina kai “K’warai ni ce nan.!” Tai maganar tana kuma k’obarewa bakin k’ofa.


“Umma.. Me kike a nan..?” Khulsum ta tambaya cikeda mamaki.


“Ke zan tambaya mai kike a nan..? Wani munafuncin ne Ya kawoki..? Awho kinzo ne ki kashe mata auren Tun kan ta tare ko..?”


Mamaki Ya hana Khulsum furta koda kalma sai duban Umma da take. Da k’yar ta iya furta “Umma a ina uwar amarya ta tab’a yima ‘yarta rakiya d’akin miji.. Haba Umma fisabilillahi, bayan auren rashin galihu da kikai ma ‘Yaruwata shine saida kikai mata rakiya. Shin baki gudun maganganun mutanen ne Umma..?”


“Allah tsari gatari da saran shuka.. Aure auren gata nai ma d’iyata irin Wanda kaf lungun ku ba’a tab’a samu ba. Ki koma ki tambayi ‘yan lungun naku kiji wani irin aure akaima Ummul. Aure na bajinta auren da na tabbata bazaa daina kambabasa ana labarinsa ba. Ke harta da masu shigewa saida suka shaida.. Kuma ban rako Ummul ba saida zuciyata ta tabbatar min zaki iya zuwa… Gashi kaw kin zo d’in kaman yanda nai tunani.. Zuwanki na sani ba Alheri bane.. Dan na tabbata kaman yanda nai alwashin aurar da Ummulkhairi haka Kikai alwashin lalata mata aure. Tinda ba yau kika saba korar mata maza ba. .Ke ni fah akan auren nan wllhi Khulsum sai mu raba gari dake.!” Ta k’arashe tana sakin huci.


Khulsum ta jinina kai a hankali tana duban mahaifiyar tata “Umma kin kaw ji abinda kike fad’i..?” Tai maganar cikin rawar murya.


“K’waraiii kuwa.. Wllhi sai kiyi yamma nai gabas muddin kikai yunk’urin lalata auren ‘Yaruwarki Wanda Babu kalan fad’i tashi da banyi ba dan ya tabbata. Tsaf zan yafeki Khulsum muddin kika kawo mishkila.”


Hawaye suka gangaro ma Khulsum “A’a Umma. Abun bai tsanani haka ba. Har kullum ke mahaifiyata ce banida tamkar ke.. Bazan b’ata auren Adda Ummul ba.. Na Miki alk’awari Umma.. Amma dan Allah alfarma d’aya nake so kimin..”


Yanda Umma ke dubanta a dak’ile sai ka rantse ma wata tsararta take  jifa hararan.


“Umma dan Allah ki bari nai Sallama da Adda.. Na rok’eki..!” Ta k’arashe tana had’e tafukan hannayenta biyu waje guda alamun rok’o.


Umma bata amsa ba sai k’ofan waje da ta shiga nuna mata “Fita.. Wuce ki fita.. Wllhi idan ni na haifeki kuma na haifi Ummul bazakiyi Sallama da ita ba.. Shige ki fita nace kar na bud’e idanuna na ganki..”


Khulsum ta dubi mahaifiyarta da mamaki “Umma kin Sallamanin kenan..?”


“Idan haka kika d’auka.. Kije duniya da yawa..”


Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un Khulsum ke nanatawa cikin zuciyarta. Wai mahaifiya ke fad’a ma ‘yarta haka.. Anya Umma ita ta haifesu..? Anya akwai iyaye irin Umma..? Anya mutum zai d’auki D’ah a cikinsa tsawon watanni tara Ya haifosa duniya yaci gaba da rainonsa rana tsaka Ya k’isa sabida wani buri nasa na duniya..? Anya akwai irin wad’ann iyayen..? A iya saninta harta dabba yasan dadin d’ansa. Meyasa tasu mahaifiyar ta zama haka..? Shin dama ana jarabtan bawa da iyayensa..? Ashe ba iyaye bane kawai ake jarabtarsu da yaransu ashe Yaran ma akan jarabcesu da nasu iyayen.. Ta lumshe idanunta hawaye suka gangaro mata. A hankali take ja da baya hawaye na gangaro mata tana duban Umma. 



Umma kaw bayan ta tabbata Khulsum ta fice cikin gidan ta koma harda ce ma maigadi idan wann yarinyar ta dawo ya koreta. 


Suna zaune parlor itada Asshe bayan k’awayen Asshe Sun watse. Asshe ta dubi Umma tace “Yarinyar nan taki akwai fitina, sam batai halin ‘yaruwarta Ummul ba.”


Umma ta tab’e baki “Ai mutane biyu ne mabanbanta halayya. Fitinanniya ce ga taurin kai tsiya da masifa yacce kikaga k’anwar Ubanta. Bata rage ma Dije komai a d’abi’a ba.”


Asshe tace “Wacece Dije..?”


Kafin Umma ta kaiga bata amsa  suka sinkayo wata murya daga k’ofa “Ni ce nan Dije k’anwa d’aya tilo ga Isubu..!”


Daram.! Daram!! Daram.!!!


Haka k’irjin Umma ya bada wann sauti cikin sakan guda.




SameenaAleeyou📚

*AUREN WATA UKU.!*





*20*







©️Sameena Aleeyou…✍🏽*







Inna Dije taci gaba da takowa cikin parlorn. Yayinda Umma keta faman k’ifta idanu, zuciyarta bata daina tsinkewa ba. 


Daidai saitin Umma Inna Dije ta k’araso ta tsaya. Umma ta kasa d’ago idanu ta dubi Dije.


“Dole ki kasa d’ago idanu ki dubeni Suwaiba. Idan Har kinada sauran kunya  bazaki dago ki dubeni ba..”


Umma ta soma girgiza kai hawaye na zubo mata Har lokacin bata d’ago idanunta ba.


Fincikota Dije tai tana fad’in “zo nan.. Yau sai naji uban da ya tsaya miki a garin nan Suwaiba har kike buga wasanki da sunan wauta da shashancin gangan..!”


Ta kuma janyo Umma a zafafe. Hajja Asshe tai saurin raba tsakaninsu “Inaga dai ya kamata ayi komai gaban idona.!” Ta k’arashe tana duban Inna Dije data cakumo Umma.


Umma ta k’walalo idanu waje Jin zaa kwance mata zani gaban Hajiya Asshe. Ta had’e hannu biyu waje guda alamun rok’o “A’a Dije.. Kar kiyi haka.. Wann matsala ne da ya danganci ahali..”


Inna Dije ta murmusa tana duban Umma “Dole kice matsala ce da ya danganci ahali Suwaiba.. Sabida bakiso a bankad’o sirrikanki gaban sirakanki ko..? Kin masu rufa rufa kin aura masu ‘yarki da lak’anin mahaifinki ya fad’a kanta cewa ita d’in bazata tab’a aure ba.. Sabida wani babban Dalili Wanda nida ke muka binne hakan tinda jimawa..!”


Umma ta zaro idanu waje tana duban Inna Dije da Jin wani batu Wanda ta kasa fahimtar ina ya dosa..


Asshe ma idanu waje take duban Umma da Inna Dije cikin tsananin d’aurewar kai  “Wa.. Wani batu kenan..?!”


Dije ta murmusa cikeda cin nasara. Cikin zuciyarta take ayyana lokaci yayi lokacin d’aukan Fansan rasa tilon D’anta Fa’iz da tai a dalilin Ummulkhairy.


Umma ta kuma girgiza Kai “Dije wa.. Wani dalili ne wann.. Kuma.. Wani magana muka tab’a binnewa mu biyun Wanda ni ban sani ba.?”


Dije ta murmusa “Suwaiba kar ki fara mana dramarki a nan.. Dan kinsan tar nake kallonki.. Kin shashantar Dani Karon farko na rasa Fa’iz dalilin ‘yarki bazan kuma bari ki shashantar Dani ba..!”


Umma ta kuma girgiza Kai hawaye na Neman b’allo mata.. Zatai magana Asshe ta dakatar dasu “Wai meke faruwa ne..?”


“Abinda yake faruwa shine D’anku ka iya zama gawa na gaba kaman dai yanda Fa’iz d’ina ya mutu..!”


Asshe ta mik’e tana kuma zaro idanu dafe da k’irji “Na shiga uku gawa fah..! Haidar ne zai zama gawa na gaba..?!”


Dije ta dubeta sosai tace “K’warai kuwa.. Domin Ummulkhairy da kike gani ba mace bace..!”


Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.! Shine abinda Asshe take nanatawa tana ganin duniyar na Neman juye mata “Ba mace ba..? Mecece toh..?! Na shiga Uku ni Asshe me na aura ma D’an ‘Yaruwata..?!”


Umma na kuka take girgiza Kai tana duban Inna Dije jin irin sharrin da ake ma ‘yarta akan idonta  “Dije kiji tsoron Allah..!”


“Idan banji tsoron Allah ba tsoronki zanji ko tsoron mushurikin mahaifinki wanda ya maida Ummulkhairy yanda take a yanzu..!”


Izuwa lokacin kan Asshe ya gama k’ullewa.. Ta dubi Umma dake duk’e wajen tana hawaye tace “Ke Suwaiba..! Fad’a mun.. Meke faruwa..? Wacece ‘yarki..?”


Umma bata iya cewa komai ba sai kuka tana girgiza Kai.. 


Inna Dije ta kuma murmusawa “Ai bazata iya sanar dake komai ba domin kuwa batada amsar baki.. Amma ki tambayeni ni zan sanar dake komai.. zan sanar dake Wacece Suwaiba da badak’alan data k’ulla a doron k’asa..!”


Asshe ta d’ago tana duban Inna Dije cikin tsananin shock.


Lokaci guda Inna Dije taci gaba “Yarinyar da kuka aura ma D’anku ba mace bace.. Domin kuwa a lokacin da Suwaiba ta samu cikinta ba cikin ‘Ya mace tai fatan samu ba.. Mahaifin Suwaiba ya kasance gasunkumin malamin tsubbu ne Suwaiba ta tafi wajensa amsar taimako a lokacin tana d’auke da cikin Ummulkhairy kan cewa ya bata lak’anin haifo d’a namiji... Sabida  Sun mance Allah shi kad’ai yake halitta mahaifinta bai isa ya sauya halitta ba.. Wann dalili yasa aka haifo Ummul a idon duniya mace ce mai kyau son kowa k’in Wanda ya rasa.. Amma a zahiri ne kawai. A magana ta auratayya namiji bazai tab’a amfana da Ummul ba domin kuwa ita d’in an tsafeta tun a ciki.. Hakan na nufin Ummulkhairy bazata tab’a aure ba.. Idan kuma tai toh fah duk mijin da ta aura zai mutu. Idan bai Mutu kafin ta kaisu ga aure ba kaman dai yanda Fa’iz d’ina ya mutu toh zai mutu idan wata alak’a ta auratayya ta gifta tsakaninsu.!” 


Duniyar Asshe ya shiga juyawa.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.. Meke shirin faruwa dasu.. Shin ta yaya zata sanar dasu suma auren warware asiri kawai na watanni uku sukai da Ummulkhairy Wanda sai ya mu’amulamceta wann sihirin da aka masa ya karye.. Ta ina zata soma sanar da ‘Yaruwarta abinda ke faruwa.. Lallai tana tsaka mai wuya..!


Muryar Umma ne ya katse mata tunanin yanda take fad’i cikin kuka “Haba Dije..! Dije kiji tsoron Allah.. Ki tuna akwai mutuwa.. Dije har zaki iya tsara wann babban k’arya kan D’iyar D’anuwanki.. Dije baki tsoron hakki.. Baki tuna yau idan babu mahaifin Ummul ita amanace a gareki..?!”


“Rufe mun baki annamimiya..! Ke Har akwai maci amana irinki ne Suwaiba.. Kin mance Ya aurenki ya kasance ne na tuna miki Suwaiba..?”


Umma ta kuma kifa kanta a k’asa kuka na kuma zuwa mata. Lokaci guda Dije  taci gaba “Talla  kike kawowa cikin gari a lokacin Tani da mahaifiyarmu wato sirkarta kenan basu jituwa mahaifiyarmu tana so Yayana Isubu ya k’ara aure kafin ta bar duniya sabida yara mata da Tani ke haifa masa. Mahaifiyarmu tana son samun jika namiji daga wajen D’anuwana Isubu.. Ke Suwaiba kika yaudari Tani kikace a garinku  mahaifinki malamin zaure  ne kuma yana bada lak’anin mallaka, Tani ta biyeki kika kaita Har rugarku da sunan tana neman lak’anin mallaka. Shakuwa ya shiga tsakaninku kika d’auki Tani tamkar Yaya. Tani ta daukeki tamkar k’aramar k’anwa ta baki dukannin yardarta. Kika zamto mata ingiza mai kantun ruwa.. Kika zaga Tani kikaci amanarta. Maganin bakin jini keda Ubanki kukaita tura ma Tani Wanda zaisa mijin Tani ya tsaneta ya soki. Haka ne..?”


Idanun Umma suka kuma firfitowa waje tana jin sirrikanta kaf Dije na fito dasu. Dan wann b’angare da Dije take fad’i bata da haufi gaskiya ne. Cikin rawar murya irinta mai kuka take furta “Amma nayi nadama kuma mahaifina ya daina wann aikin kafin ya bar duniya Dije. Ke shaida ce mahaifina bai Mutu yana wann mummunan sab’o ba. Dije Allah Algafur ne kuma mai rahama.”


“Ke yimin shiru! yau ne kika san Allah  Suwaiba.? Ashe kinsan da haka kika rufe ido kika doge sai kinga auren Ummul kaman lokacin baya da kika doge wajen ganin kin haifo d’a namiji.? Kaman yanda burinki na farko bai ta bata ba Suwaiba haka burinki na biyu ina nufin ganin ‘yarki  Ummul a d’akin aure kaman ko wace ‘ya mace bazai tabbata ba.!”


 Dije na huci taci gaba “Kusanci da yarda da Tani ta baki da shi kikai amfani kika aure mata Miji. Mahaifiyarmu babu irin soyayyar da bata Miki ba Dik a tinaninta zaki haifo mata jika namiji.. Wanda hakan yasa kukaje kukaita tsibbace tsibbacenku keda mahaifinki dan ki haifo d’a namiji..Idan kin mance na sake tuna miki da cikin Ummul mahaifiyarmu ta bar duniya bataga abinda kika haifa ba Wanda ta k’wallafa ran D’a namiji zaki haifo.. Bayan mutuwar Inna wato mahaifiyarmu mahaifinki ya Mutu shima. Daga nan ne Tani ta fara cuzguna Miki… Kika koma mata tamkar baiwa.. Duk abubuwan da kikai a baya basu isheki ba Suwaiba har saida kika saka mutanen da basuda hakki ciki.. Idan ni na rasa Fa’iz Watak’ila sabida tsanar da na Miki a baya.. Su wad’ann mutanen mai suka Miki kika jangala masu Ummul...? Suwaiba dole ki haukace da son ganin ‘yarki tayi aure kota halin k’ak’a tsoron kar tsafin da mahaifinki ya jefi ‘yarki dashi a lokacin da kike d’auke da cikinta ya tabbata.!”


Girgiza Kai kurum Umma take tana hawaye ganin Dije ta d’aureta ko ta ina.. Babu bayanin da zatai ta wanke kanta. Dije taci gaba “Ke fah  akan cikan burinki Suwaiba babu Wanda bazaki ci Amanansa ba. Koda kuwa wann mutumin ya Miki halarci kaman yanda Tani ta Miki..!”


Asshe ta shiga jinina Kai bakinta yana furta “Tabbas haka ne..! Sai yanzu nake fahimtar  komai.. Tani taso nusar Dani gaskiya na rufe idanuna.. Ashe ita ce mai gaskiya.. Tabbas na Miki rana Suwaiba.. Babu abinda ban Miki amma kika zab’i ki b’oye mun wann bala’i dake k’unshe jikin ‘Yarki.. Da niyyan taimako na nema ma D’an ‘yar uwata auren ‘yarki.. Ashe ke akwai k’ulli cikin zuciyarki.. Kin cika butulu Suwaiba.!” Muryar Asshe ya soma rawa hawaye na gangaro mata “Ki sanar Dani mai zan fad’a ma ‘Yaruwata da ta aminta Dani Akan Tilon D’anta ta mallaka min wuk’a da nama.! Ki sanar Dani Suwaiba..!” Ta k’arashe kuka na kuma b’allo mata.


Umma na girgiza Kai tana hawaye take fad’in “Ki yarda dani Hajiya Asshe.. Wllhi cikin maganganun Dije akwai Wanda sam ba gaskiya bane.. D’anta had’arin mota shine ajalinsa amma ba auren Ummul d’ina da Ya tasamma bane.!”


“Wani gaskiya kike dashi da har  zan yarda dashi..?” Asshe ta katseta cikin d’aga murya.

Lokaci guda taci gaba “Wann auren babu yanda zaije..! Bazan saka rayuwar D’an ‘Yaruwata Akan layi ba.. Za’a Warware wann aure tun kafin ‘yarki ta bar gidan nan.. Zan kira ‘Yaruwata na sanar da ita komai.. Ita zatai umarni ma D’anta ya datse auren Amaryar da aka aura masa wacce ko saninta bai ba..!” Tana ida fad’in haka ta mik’e zata nufi sama.. 


Umma ta bita a guje ta duk’a gabanta ta kamo k’afafunta tana kuka sosai take fad’in “Ki rufa mun asiri dan girman Allah Hajja Asshe.. Dan Allah kar ki bari a warware wann aure.. Dan Allah kar ki bari a maida sadaki.. Wllhi Ummul mace ce kaman ko wace ‘ya mace.”


Asshe ta fuzge k’afarta “So kike na kashe D’ah na Akan cikan makahon burinki Suwaiba..! Aure dole a warware..!” Tana ida fad’in haka ta kuma fuzge k’afar ta ta nufi sama a fujajan kaman zata kifa.


Hannu biyu Umma ta saka aka tana kuka maras sauti tsoron kar Ummul taji muryarta tasan abinda ke wakana. A fili take furta ta shiga uku ta Mutu ta lalace.


Daga yanda Dije ke tsaye tana dubanta murmushi ta saki. Cikin zuciyarta take furta “Da kyau Dije.. Fansan ran Tilon D’anki kike d’auka.. Aima baki shiga uku ba tukuna Suwaiba.. Dan yanzu ne aka fara buga wasan.. Ba ke kad’ai bace kika iya buga wasa.. Saima kin ci karo da duk tanadin da na miki..



Asshe tana haurawa zama tai gijif saman gado tana jin wani irin tashin hankali na ziyartarta. Yanzu ta ina zata fara b’ullo ma wann al’amari..? Mai zata soma sanar da ‘yar uwarta bayan d’inbin kud’ad’en da ta asma daga wajenta..? Ta sanar da ‘yaruwarta d’iyan mutane masu mutunci mai irin matsalar da boka yace a aura ma Haidar ta samu dukda kasancewansu talakawa amma sunada dattako. Sabida Hajiya Kwaise bata amince D’anta ya kasance da d’iyar matsiyata marassa dattako k’ark’ashin kalmar aure ba koda kuwa na tsawon watanni uku ne kacal. Shin ta yaya zata soma gabatar da wann ahali masu dabaibaye da matsala Wanda tashin hankali yai ma rayuwarsu marfi, dangin tsiya dangin matsafa. Ba’a nan ta tsaya ba Ita kanta yarinyar an tsafeta tin a ciki.. Sann ita d’in barazana ce ga rayuwar Haidar. Ta rintse idanunta tana jin tashin hankalinta na kuma ninkuwa.. Meyasa Tai komai a gaggauce..? Meyasa bata saurari Tani ba..? Meyasa Tai zaton kishi ne kawai da Hassada yasa Tani gaza zaune wajen ganin auren bai tabbata ba..? Ta Ware idanunta sanda zuciyarta ke ambato mata . ‘Mutuwar Kwasko kenan Haidar zaiyi da wann yarinyar da kika aura masa. Shin AUREN WATA UKU zaki ambaci auren ko Auren ajali.? Tabd’ijam! Wann shi ake kira cuta ta d’au cuta.!’ 


Ta kuma mik’ewa tsaye zufa na kuma tsartsafo mata. Zuciyarta ta shiga amsa mata d’imbin tambayoyin da sukai karan tsaye cimma Zuciyar nata ‘Me kike tunani a auren da aka faro bisa umarnin boka..? Me kike tunani a auren da ba’a nemi zab’in Allah cikinsa ba..? Me kike tunani cikin auren da ba’a d’aukesa umarni daga Allah ba..? Me kike tunani cikin auren da ba’a ginasa bisa ginshik’in auren ba..? Ma’ana ba’ayi sa domin cika sunnar ma’aiki (SAW) ba. Dole abubuwa su biyo baya.. Dole bazaku ga da kyau ba. Kaman yanda kika rufe ido kikai ma ‘yar mutane auren Mutuwa da D’anku haka nan wann matar da kika d’auketa shashasha tai auren mutuwa ma d’anku da nata ‘yar. Tirk’ashi. Lallai yau akeyinta.


Asshe taja wani irin gauron numfashi tana mai kuma mik’ewa tsaye daga zaune. Lokaci guda take furtawa a fili “Me zan aikata ni Asshe.. Me zan sanar da ‘Yaruwata..? Zata fahimci k’arya naita shera mata kenan ina amsar mak’udan kud’ad’e hannunta..? Shin waye zai fanshe kud’ad’en da na amsa hannun Kwaise da sunan AUREN WATA UKU ma d’anta. Shin ma ta ina zan iya mayar mata da kud’ad’en da ta bani na yak’in nemo ma Haidar matar wata uku..? Dan nayi imani nawa mijin ba biya zaiyi ba dan shi mutum ne da mata bata cin kud’insa sai wacce yake yayinta. Nida ‘Yaruwata kuma k’ar tasan k’ar ne akan kud’i. Zamu iya samun matsala ta tarwatsewar ahali akan kud’ad’en da ta tafka asara ba tareda ta samu biyan buk’ata ba. Uwa uba taji auren mutuwa na shirya ma tilon D’anta Wanda ita kanta ta saka nata Auren cikin had’ari domin ta ceto sa daga mugun asirin da aka jefesa dashi. Mijina will come to know everything. Duk abubuwan da na aikata harda zuwa wajen boka da AUREN WATA UKU da na k’ulla Wanda Ya k’unshi kisan kai. Zai rabu dani rabuwa ta har abada. Even my children will leave me. Kowa zai gujeni na zama banida tsuntsu banida tarko. Kishiyoyina su samu abun yawo Dani. Lallai ina tsaka mai wuya ni Asshe. Suwaiba ni ta cuta a duka wann al’amari. Gashi garin k’ok’arin gyara ahalin ‘Yaruwata ni zan tarwatsa nawa ahalin da farin cikina. Toh amma rayuwar Haidar ake magana a nan.” Ta shiga girgiza kai tana mai furtawa a hankali “A’a.. A’a bazan bari hakan ta kasance ba.. Haidar’s life is at stake here.. Bazan bari a kai masa ajalinsa ba.. I need to do something immediately.. I need to come up with something… I just.. Can’t sit back and do nothing.. Amma me zanyi..?”



Batakai aya ba wayarta ta soma ruri Hajiya Kwaise ke kira. 




SameenaAleeyou📚..


Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post