*AUREN WATA UKU..!*
*46*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
Da kyar ta samu ya k’yaleta yai mata rakiya har k’ofan parlorn Mommy. Suna isowa ta zame jikinta daga nasa. Sai ya mik’a mata k’aramar paper bag d’in dake hannunsa.
Ta d’an girgiza Kai “Ta mecece.?
Dont open it yet sai kin shiga. Ya fadi yana kashe mata ido daya . Bai kuma tsayawa sauraronta ba ya soma tafiya yana waving dinta kaman kar ya tafi ya barta.
Ta girgiza Kai kurum tana binsa da kallo a haka har ya shige.
Anisa tana nan ta kasa ta tsare tana jiran dawowarta dan kusan komai Akan idonta ya faru.
Sam Ummul batasan da mutum a parlorn ba sai muryar Anisa da ta sinkayo. Batada lokacin sauraron maganganun Anisa hakan yasa tuni tasa kai ta nufi upstairs ba tareda ta tsaya sauraron maganganun Anisa ba. Amma sai Anisa ta bude murya tace Auren Haidar Maitama might seem to you like a golden opportunity na samun nasarori da Jin dadin rayuwa.. Musamman duba da irin rayuwar da kika baro cikinta But what if, this golden opportunity comes at a very high price.?
Ummul taci gaba da kokarin dannar kanta. Dan a yanda ta tsara ba a wann lokacin zata fuskanci Anisa ba. Ta gama shirya lokacin da zata tunkari Anisa da kalamanta. Sai ta bude lumsassun idonta a hankali taci gaba da tafiya ba tareda ta juyo ta dubi Anisa ba.
Anisa ta take mata baya tana ci gaba da fadin Abinda yasa kikaga na dage miki Ummul dan inada gaskiya ne. Bana so ki saki jiki cikin auren da zakiyi danasani a gaba. Kuma ciwon ya mace ta ya mace ce.. Ba komai cikin wann auren face kaskanci.
Ummul ta dubi Anisa da murmushi saman fuskarta. Sai kuma ta maida kofan daki ta rufe ba tarda tace komai ba. Dan Sam bazata bari ta bata shirinta ba.
Anisa taci gaba da sakin huci dan ta tsani wann silent treatment din da Ummul ke bata dan bata mance karonsu da Ummul din ba. Tasan shes sharp and smart dik yanda akai wann shirun da take tana murmushi wani abin take shiryawa tinda Tasha lalata mata shiri ba daya ba. Taci gaba da sakin huci ita kadai.
Ummul tana shigewa daki ta lumshe idonta tana karanto adduoin samun sauki da sukuni cikin zuciyarta dan sosai take Jin maganganun Anisa har cikin kahon zuciyarta da bargonta.
Ta isa saman gado ta zauna gijif sai ta dubi yar jakan da Haidar ya bata. Ta soma kokarin budewa.
Nan taga wayar salula ce ta yayi mai dankaran kyau. Da alama komai an saka cikin wayar. Kaman daga chaji har zuwa simcard.
Taita juya wayar kafin ta kunna. Sako ne ya fara mata Sallama _I've bought a new book.. and open a brand new page together with you_
Taita karanta sakon yayinda jikinta ya kuma mutuwa. A bangare na kunnenta guda kalaman Anisa ke mata yawo a daya bangaren sakon Haidar cikin yanayin muryarsa na mata yawo. Ta rasa wanne daya zata saurara sai ta toshe duka kunnuwanta biyu kuka na zuwa mata. Ganin koke koke da tunanin bazasu fishheta ba kawai sai ta mike ta dauro alwala ta soma Kai kukanta ga Mabuwayin Sarki da babu kaman shi.
Tana bisa darduma tayi lamo tana duban wayar kira na shigowa Wanda tasan kiransa ne tinda lambarsa ne kawai kan wayar. Bata bi takan wayar ba haka akaita kira har dai ya hakura. Karshe ya tura sakwanni Wanda suma batabi takansu ba.
Duk Haidar sai ya damu ya fara tunanin ko bataji dadin kyautar da yai mata bane. Kodai ya mata wani abin ne.
Washe gari da safe Fashion designer tazo har gida da manyan bridal dress catalog dan amarya Ummul ta zaba yanayin rigar da zaa mata. Anisa ita ke tayata zabe. Ummul sai duban Anisa take tana mamakin wai wacce ke mata gargadi da kashedi da auren Haidar sai gashi itace mai zakewa wajen zaba mata Kayan da zata saka.
Aka nuno wani farin gown mai dankaran kyau Anisa tace Yauwa perfect. I think this one is ok.
Kaman daga sama suka sinkayi wann muryar nasa daga bayansu This is too revealing.. My wife cant wear this. Ya fadi cikeda gadara hannayensa sakale cikin aljihun jeans dinsa yasa kai ya shige upstairs gaida Mommy ba tareda ya dubi ko yanda Ummul din take ba. Ta bisa da kallo duk jikinta a sanyaye. Toh ko dai fushi yake da ita sabida yayita kiranta a Daren jiya bata daga ba har sakwanni ya turo bata amsa shi ba. Gaba daya sai taji babu dadi.
Anisa na hankalce da ita da Haidar din. Lokaci guda tana mamakin wai Haidar ke cewa kaya is too revealing dik girma da tasowa cikin gogaggun wayayyu da yai. Lallai ta yarda ya fara nisa cikin soyayyar wann Bagidajiyar. Idan batai sauri ta rabasa da wann Bagidajiyar ba haka zata maida mata Haidar dinta Bagidaje irinta.
Haka har aka gama zaben rigunan ita dai bama tace ga rigar da aka tsaida ba. Duk tunaninta na kan Haidar.. Bata san ta damu da fushinsa har haka ba. Abinda yafi bata mamaki shine ko ta kanta bai sake bi ba.. Bai nemeta bata ma sake saka shi a idonta cikin gidan ba. Ta dauki wayar kaman zata kira layin sa amma sai ta kasa. Haka kaman wasa har ranan da ake saka ran ranan ne Mommy ta tsaida dan shagalin bikinsu bata saka Haidar idonta ba. Wani abinda ya kara bama Ummul mamaki shine Anisa batai kasa a gwiwa wajen shirya komai ba. Ita Mommy tasa ta kaita saloon aka gyara mata gashi sann ta dauko mai lalle da makeup artist har gida. Kaman wata maid of honor haka Anisa ta zake tana mata komai. Ummul bata daina karantarta ba.
Cikin wata farar doguwar riga da dinkin ya zauna jikinta ta shirya. An mata dauri na zamani da irin fabric din rigar Wanda da gani zaka san an barar da kudi wajen sayensa da dinkasa. Baa cika mata kwalliyar ba amma tayi kyau har ta gaji. Duk Wanda ya kalle ta sai yaso sake kallonta. Haka masu kwalliyan da shiryata sukaita santin kyaun da tayi. Ita dai Ummul gaba daya ranan ta kasa gane kanta gaba jinta take ba daidai ba. Something feels wrong. Sai kawai ta danganta hakan da fushin da Haidar keyi da ita.
Koda akace ta fito su dauki hoto da Haidar sai rashin nutsuwar da take ciki ya ninku. Zuciyarta yaci gaba da bugu. Yanda kasan bata taba sanin shi ba haka takeji. Da kyar ta iya fitowa kirjinta sai bugu yake.
Tin daga saman bene masu camera ke haskota har zuwa saukowarta parlorn basu daina daukarta hoto ta ko wani angle ba.
Anisa ta dubeta ta saki murmushi Relax Ummul, ki natsu a Miki hotuna masu kyau dan wadann hotunan a manyan mujallu zasu fito.. Mrs Haidar Maitama. Ta kashe mata ido guda tana fadin a dauke su tare.
Mommy ta karaso tana dubanta kwalla kaman zai zubo mata ta karasa ta rungumeta Kinyi kyau daughter.. May yours be among the best. Ta karashe murmushi saman fuskarta. Nan aka dauke su hoto. Kwallan da Ummul take makalewa ya gangaro. Mommy tai saurin goge mata tana girgiza Kai Aa Ummul, yau fah ba ranan kuka bane.. Bana so hawayen nan ya bata Miki kwalliya. Ta waigo cikin kokarin danne nata kukan tana tambayar wai ina Haidar din ne.?
Anisa da takaicin acting Mommy ya isheta sai ta juya ido tana furzar da huci. Tana kokarin barin wajen ta hango Haidar na shigowa cikin shiga ta farar shadda kal babbar riga harda hula. Shigan da zata iya cewa bata taba ganinsa ciki ba. Sosai ya amshe sa dan ba Anisa kawai ba harta ita Ummul din saida ta shagala da kallonsa.
Ya karaso aka musu su uku da Mommy. Ta shige tsakiyar su ta rungumesu su duka biyun akaita kashe musu pictures.
Daga bisani aka soma yima amarya da ango. Masu hoto suna bada direction. Aka ce ta daura hannunta guda saman chest dinsa sai ta dan dago tana dubansa. Duban irin na mai yake nufi.? Ita fah har kawo wann lokacin bai mata magana ba gashi duk yanda aka ce ya rike jikinta kafin ma ace yayi. Wann fah shine mutumin da a baya hes allergic to cameras. Ummul bata Ankara ba saiji tai ya dago hannunta ya daura saman chest dinsa.
Anisa taji wani katutun bakin ciki ya tokare mata makoshi. Ga wani kallo da suke bin juna dashi. A hankali take calming kanta cikin zuciyarta Patience Neesa.! Patience.!! Na yau ne kawai.. Daga rana mai kaman ta yau ta zama tarihi a rayuwar Haidar dinki. Ta kuma murmusawa I cant wait for things to get chaotic.
**
A can waje kuwa zabga zabgan bakaken jeep din sukai parking. Motar farko Hajiya Asshe ce ta fito sai Inna Dije daga daya bangaren. Dayar motar kuwa daga can seat din yanuwan Ummul guda biyu ne Badia da Azeema yayinda Umma da Mama Tani ke daga tsakiya. Suka neri suka fito sahu sahu.
Kallo guda zakai ma Umma ka fahimci tsananin tashin hankalin da take ciki. Tayi tsuru tsuru da ido ko motsi mai kyau bata iyawa. Badia da Azeema kuwa kasa rufe baki sukai ganin irin gidan da Ummul wai take aure ciki.. Ummul fah. Wacce kowa ke gudunta cikin ahalin su. Wann maras saan.. Wacce ake mata lakabi da mai farar kafa.. Wann wacce maza da yawa ke guje ma Aurenta.. Allah mai iko. Gashi daga saukan su wasu maaikata masu uniform suka taho suna masu sannu da zuwa cikin harshen turanci cikeda ladabi suna amsan jakkunansu. Daya daga ciki tai directing nasu zuwa masauki. Sukaja suka tsaya wann ya dubi wancan wancan ya dubi wann. Asshe ta furzar da huci kadan ganin duk sunja sun tsaya suna duban tsoro ma juna Ku taho muje mana. Wai ko Baku gaji bane.?
Sai Inna Dije ta murmusa da shike ita ta taba zuwa lokacin auren Ummul. Tace Kunga ba masu yankan kai bane ko Shan jini. Ku taho muje..
Sai Mama Tani wacce ta kasa gasgata wata duniya ma tukunna take ta janyo Inna Dije tana rada mata Ke Dije.. Da gaske kike.? So kike kice min nan shine gidan da Ummul take ko kuma dai matar nan ta shanshantar damu ne gaba daya Kama Suwaiba. Dije nan fah fadan shugaban kasa ne. Kurani shine a talabijin nake gani.! Ta karashe harda dangwala yatsa saman harshe.
Inna Dije taci gaba da janyo Mama Tani tana fadin Kin dai gani da idonki.. Na tabbata bazaki so ki bar Ummul cikin wann daula ba. Duk balain da zaayi bazamu fice daga gidan nan ba saida Ummul. Cikin sigan rada suke ma juna magana.
Duk maganar da sukeyi ita dai Umma bama tasan mai ke faruwa ba jefa kafafunta kawai take tana tuna kalaman Asshe a gareta tana tuna a daidai wann rana sukai AUREN WATA UKU da tai ma Ummul da dansu zaizo karshe.
Azeema da abin ya fara bata tsoro ta dan jada baya tana janyo yaruwarta Badia. Tai kasa da murya Badia nifah wllhi naga gidan zama.. Wllhi bazan koma Kano ba ina nan tareda Yaruwata.!
Badia ta dara kadan tace Toh kiyi yaya da Habibinki kuma idan ya dawo miki.?
Azeema ta galla mata harara Aa Makiyi dai ba Habibi ba. Ai ni idan kinga na fice a gidan nan saidai idan fadan shugaban kasa zan tafi..
Badia ta kuma darawa daidai sanda suka isa guest section din.
Asshe ta dubesu tace su saki jiki su huta ga abinci dama tuni an jere musu idan da akwai abinda suke bukata ga maaikata zasuji dasu. Zata shiga cikin gida ta sanar da isowarsu. Inna Dije ne kawai ta amsa mata yayinda Mama Tani ta rakata da harara duk cikin acting ne da suke dan su shashantar da Umma. Badia da Azeema kam basu tsaya sauraronta ba suka tashi suka soma zaga gida suna kallon aljannar duniya a cewarsu.
Bayan ficewar Asshe jikin Umma yaci gaba da rawa. Ba tareda ta dubesu ba take fadin Yau ne.. Yau ne tai alkawari.. Waadin auren zai cika.. Yau dansu zai sakar mun Ummul dita.. Zan dauki Ummul dita mu tafi.. Shine kawai abinda ya kawoni..!
Mama Tani da Inna Dije suka dubi juna.. Tani tuni shiga bude buden kayayyakin abincin da aka jere musu Wanda da yawa ma bama ta taba ganin irinsu ba. Da ta ga dai bata gane wasu abun ba sai ta dauki Wanda takeda tabbacin naman kaza ne ta soma gwagwiya dama Tani da kaza. Tana ci tana Zare ido kaman zaa kwace. Ta dafa Umma Shiyasa na rakoki Yaruwata. Kinga wann mata mai zubin akwati (Wai Asshe) kina ganinta kinga makira.. Wani abin take shirya Miki.. Ni da tuni kin sanar Dani ga yanda auren Ummul ta kasance ai da tuni anyita da wajewa an gama komai.. Haba Tani fah nake.! Ta karashe tana kurban wani abu da bata tabbata kunu ne ko madara mai yanyan itatu ciki ba. Ta lumshe ido tana fadin Dole ace masu kudin nan kunci rabonku na Aljannah ehe.!
Inna Dije ta harareta sai ta dafa Umma tace Suwaiba mu duka muna nan tare da ke bazan bari aci zarafin yardanuwana ba. Kafin su wulakanta Ummul zamu dauketa mu tafi dan kinsan masu kudin nan su wulakanta Danadam ba komai bane wajensu. Tinda auren ma a wulakance suka nema dan haka a wulakance zasu nemi rabuwa bacin haka meye dalilinsu na gayyato mu a wann rana da sukai alkawarin kashe Auren. Kinga Suwaiba tashi ki shiga bandaki kiyo alwala.. Muje na nuna miki yanda ake amfani da irin bandakinsu kinsan ni na taba zuwa. Ta karashe tana mai kamo Umma suka nufi bandaki. Ta nuna mata yanda zatayi kafin ta dawo ga Tani. Ta kafe ta da ido Ke kuma Tani ba sallah ba salati kin fara ciye ciyen abubuwan da cikinki bai saba da irinsu ba.. Idan cikinki ya tsure kika kasa zuwa wajen shagalin bikin tozarta Suwaiba da yarta saidai na kulleki a dakin nan dan nidai billahillazi bazaki bata min shiri ba ehe..
Mama Tani ta saki gyatsa mai karfin gaske tace Yo ka iya ibada ciki bai dauka ba. Ibadanki ma maje ina Dije.. Yo naga keta ce da fansa ya kawo ki nan..
Inna Dije ta galla mata harara yayinda Mama Tani ta sheke da dariya.
**
Jikin Mommy ya danyi sanyi. Ta kuma duban Asshe Asshe kika ce harda Mahaifiyar Ummul akazo..? Asshe ina Jin nauyi.. Ina matukar Jin nauyin bayin Allahn nan.. Mu ya kamata mu fara zuwa musu ba su ba.. Kuma a yanda na shirya da anyi bikin tariyar zamu dunguma mu tafi gaba daya mu gaida iyayen Ummul da danginta musamman iyayenta.. Mu kuma musu godiya sann a kulla alaka da zumunci mai kyau.. Munada shirin zuwa gaba dayamu.. Ni, Haidar harma da Engr da Kansa. Sun cancanci haka Asshe.. Dama kawai na bukaci wasu daga cikin danginta suzo ne dan itama taji dadi kar taga ba danginta ko daya wajen shagalin. Dan farin cikin Ummulkhair. Duk jikin Mommy a sanyaye take maganar.
Asshe ta furzar da huci kadan tana mamakin dan dai Mommy batasan waye Suwaiba ba. Da bazata daga hankalinta kan wann shashasahar matar ba.
Ta dan girgiza Kai Aunty Kwaise ke ya kamata ki musu godiya ko su ya kamata su Miki godiya.? Yau kece zaki duka kiyi godiya ma talaka Aunty Kwaise.? Aunty Kwaise Anya kece kuwa baa canza ki ba.? Asshe ta karashe tana binYaruwar tata da kallon mamaki.
Sai Mommy ta dubeta ta shiga jinjina Kai Kwarai kuwa ni ce Asshe. Saidai ba Kwaisen da kika sani a baya bane.. Wancan Kwaise da kika sani capitalist, maison mulki, izza da dagawa ta tafi kuma bazata sake dawowa ba. Wann Kwaise ce da ta fahimci duniya da rayuwa. Kwaise ce mai Neman dacewa da tsira duniya da lahira.
Asshe ta furzar da huci kadan sai kuma tace Aunty Kwaise nidai.. Da an kashe auren nan kawai mu basu diyarsu kaman yanda muka tsaro daga farko kawai a huta.. Aunty Kwaise waadin ya cika.. Kawai mu basu yarsu kawai and save Haidar.. Ta karashe cikin rawar murya.
Mommy sai ta dan girgiza Kai kadan cikin rashin fahimta Save Haidar kuma Asshe. Kaman ya save Haidar.. If theres someone to save here is Ummul. Balle ma boka makaryaci ne kinga dai yanda Alamra suka kasance bayan mun bar hanyar bata mun kama hanyar gaskiya. Kinga bana ma so ana dago wann maganar kije ko da akwai abinda suke bukata sann kizo kimin iso na gaishesu.
Asshe ta kuma fruzar da huci Wai Suwaibar zakije gaisarwa Aunty Kwaise.? Matar nan fah ko a yar aikatau dinki bata isa tazo ba.
Izuwa lokacin Zuciyar Mommy ya soma tunzura. A fusace ta dubeta wann karon Matar da ta haifo Ummulkhairi idan ta kama na duka gabanta na mata godiya ne zanyi haka Asshe. Domin kuwa tinda Ummulkhair ta shigo rayuwarmu banda alkhairi babu abinda muke gani. Ke shaida ce a gabanki komai ya faru Asshe.. For years ina kuka kan ahalina.. Ahalin da na ruguza da hannu na.. Akan idonki Haidar da baisan hawa ba baisan sauka ba ya dauki burden din da ba nasa ba tsawon rayuwa. Shin ba Akan haka bane muka tassamma kauce hanya.? Yau sai gashi cikin ikon Allah Haidar ya zauna da iyayensa lafiya. Ahalin da na jima ina mafarki ya dunkule waje daya. Ummul ta shigo ta farfado da duk wasu kyawawan dabiu da muka mance dasu ta cika gidan da nargartanta da alkhairanta.. Kinga kuwa ko dukawa nai na mata godiya ban fadi ba. Mahaifiyar Ummul ko wace iri ce Asshe tanada kima da mutunci a idona. Danginta ko yaya suke mun zama daya irrespective of our social differences. I expect you to do the same with them. Kin fahimta.! Ta karashe cikeda umarni like a big sister.
Zuciyar Asshe yaci gaba da tafasa. Ta kula Aunty Kwaise tsaf zata iya zaben dangin Ummul ta mance ita ce danginta ta asali. Gaba daya itakam kaman an canza mata Yaruwa.
Magana nake Miki Asshe..! Mommy ta kuma tsawatar mata.
Sai Asshe ta jinjina Kai da kyar tana kokarin kwakulo hawaye. Cikin muryar kuka take fadin Aunty Kwaise yanda kike magana kin fara bani tsoro.. Aunty Kwaise karfa kwarin gwiwar da kike dashi Akan yarinyar nan yasa ki mance komai.. Aunty Kwaise ni fah amana ce wajenki.. Iyayenmu Sun bar Miki amanata.. Banida wacce ta fiki kaf fadin duniya.. Aunty Kwaise dan Allah kar ki taba mance hakan.. Idan kika rabu dani bansan ya zanyi ba Duk abinda nakeyi kawai dan na damu dake ne.
Jikin Mommy ya danyi sanyi. Sai taji dan dafa Asshe Haka ne Asshe. Idan ba mutuwa ba babu abinda zai rabamu Yaruwata. Likewise banida wacce ta fiki. A lokacin kuka da lokacin dariya duk muna tare. Ta dalilinki Ummulkhairi ta shigo rayuwarmu Asshe.
Bata karasa sauraronta ba zuciyarta ya shiga tafarfasa. Dole dai sai ta ambaci wann mayyar yarinyar. Gaskiya ta fara yarda da batun su Dije yarinyar mayyace dan gashi ta lashe Zuciyar yaruwarta.
Sauri sauri Asshe ta nufi kiran Dije da Tani. Suka kebe tana sanar dasu tsarin yanda zasu tarwatsa wann biki.
Asshe ta rike kunne tana duban Tani da Inna Dije alamun kashedi Kunaji biki ne na manyan mutane. Biki ne da zai samu halartan manema labarai. Dole Yan jarida zasu sanin yar gidan wane hamshaki tilon Dan Aliyu Maitama yake Aure. Inaso da zaran manema labarai sun soma jefo muku tambayoyi ku fara amo duk abinda muka shirya.
Tani ta chabi zancen da fadin Zan fede musu daga buzu Har fata. Zasuji wacece Ummul da kuma yanda auren Ya kasance. Wayyo wayaga Tani cikin talabijin tana bayani.
Asshe ta furzar da huci hadida yin gajeren tsaki. Ta dubi Inna Dije alamun tana jiran nata baasin.
Dije ta murmusa Ita ce tayi sanadin mutuwan tilon Da na Faizu sabida balain farar kafarta. Maza bila adadi sun mutu ta dalilinta.
Asshe taci gaba da jinjina kai tana sakin murmushin cin nasara.
**
Su Badia tuni Sun nufi cikin gidan suna fadin a kaisu wajen Ummul. Da kyar Anisa ta kyale su suka shige wajen Ummul din a Cewar Anisa ana gyara mata kwalliyarta dan tuni ta canza zuwa wani shigan.
Sai kallonsu take tana yatsina fuska tana toshe hanci wai dik warin talauci suke.
Azeema tana hankalce da ita jira take su fito daga wajen yaruwarsu Ummul suji da ita.
Suna shigewa katafaren bedroom din suka tafi a guje suka rungume Ummul.
Ummul wacce ta gansu a bazata sai ta mike cikin tsananin shock tama rasa mafarki take ko gaskiya. Yanuwanta take gani. Sai ta rungumesu ta kankame tana mai fashewa da kuka.
Saida tai mai isarta suna bata baki suna fadin kar ta bata kwalliyarta.
Ummul ta kuma dubansu dan ta kasa yarda Azeema, Badia.. Wai dan Allah kune.?
Azeema ta murmusa tace Kwarai kuwa mune Yaruwa. Kawo hannunki ma ki kuma tabbatarwa. Ta hade hannuwansu su duka uku waje guda. Ummul ta murmusa tana share guntun hawayen da ya digo mata da tissue Ina Abba na.. Ya jikinshi..? Ina Khulsum da Anty Salima.? Meyasa basu biyoku ba..? Ina Mama da Umma.?
Azeema da Badia suka dubi juna sai Badia ta kamo hannun Ummul tace Abba jikinsa da sauki sosai Ummul.. Yana tashi yana zama saidai maganar ne da sauki. Sann har fita dashi waje yasha iska anayi. Abubuwa ne dai har yanzu ba kasafai yake ganewa ba. Likitoci sunce sai a hankali..Kinsan ciwo idan ya hadu da shekaru.
Ummul ta jinjina Kai a hankali tana adduan samun lafiya ga mahaifinta.
Azeema taci gaba Anty Salima tana tana gidanta yaranta ba lafiya kyanda suke gaba dayansu. Amma tace muce Miki tana tayaki murna kuma taso zuwa Allah bai nufa ba. Mun taho da Mama da Inna Dije.. Da..
Sai Badia ta dan dubeta dan Umma ita ta rokesu cewa ko sunga Ummul cikin gidan kar su sanar da ita zuwanta tukuna. Basu kawo wani abu ba dan Umman ta kwana biyu cikin wane irin yanayi.
Ummul sai bata tambayesu Umma ba dan tinda sukace Mama ta taho sai tayi tunanin Umma ke tare da Abbanta.
Khulsum fah.? Meyasa batazo ba..? Har yanzu tana fushi dani koh.? Ta tambaya jikinta a sanyaye.
Murmushin da yafi kama da yake sukai.
Badia tace Aa ko kadan bata fushi dake Ummul Ta danyi fasali sai kuma tace Ummul ki yafe mana duk abubuwan da muka Miki a baya..
Azeema ma ta saka baki suna rokon Ummul yafiya.
Dadi gauraye da farin ciki Ya mamaye Ummul. Ta kamo hannayensu tana fadin komai Ya wuce Allah Ya yafesu gaba daya.
Nan ta soma tambayarsu labarin gida.
Badia ta dan numfasa tace Abubuwa da dama Sun faru a lokacin da baki nan.. Kedai sai mun samu lokaci kawai.. Yau ranar ki ce bani so wann hawayen yaita bata Miki kwalliyarki na yan gayu. Cewar Badia tana kokarin gyara mata fuskar.
Azeema tace Wai Ummul kece kika zama haka.? Kin ganki kuwa.? Saikace wata shahararriyar yar gayu irin Wanda muke gani wayoyin mutane ana turawa.. Ta mike tana zaga dakin Wanda Ya amsa sunansa wajen kyau da girma Dankari makari wani aikin sai amale. Rayuwa kenan Ummul kiga yanda Allah Ya sauya miki rayuwa lokaci guda.. Tabbas kinyi hakuri kuma kinga ribar hakuri.. Sai na tuna Zubairu dasu Hajiya Dudu irin tijaran da suka zuba lokacin da suka amshe lefenki dashi Zubairun. Ai wllhi yanzu kam saidai Zubairu yazo a direbanki. Ta karashe suna darawa daga ita Har Badia.
Ummul ta murmusa hadida girgiza kai Aa Azeema ni duk wadann kayan kyalekyalen basu dameni ba matuka akwai kwanciyar hankali da zaman lafiya..
Chab ai kudi sune kwanciyar hankali wllhi.. Yo ina cikin wann daular karyar bakin ciki Ya tunkareni ai. Azeema tace tana mai hayewa saman gadon.
Anisa ce ta banko kofa ta shigo tana fadin maza su fice zaa karisa shirya Ummul.
Azeema ta kuma harararta Tai kwafa.
Ummul ta kamo hannayen yanuwanta tana sanar dasu kar su koma masauki su jirata nan parlor tana fitowa.
Koda suka fito parlor Azeema dai bata zauna ba sai zagawa take tana bama idonta abinci a cewarta.
A haka Anisa ta karaso daidai sanda Azeema take taba wani katon flower vase. Anisa ta rausayar da ido tana fadi a fili Dealing with Ummul is already giving me a headache. Now I had to deal with these local champions.? Ta rausayar da ido tana furzar da huci.
Excuse me.! Ta darara ma Azeema tsawa.
Azeema ta juyo da mamaki tana dubanta.
Anisa taci gaba da nunata a wulakance That flower vase worth your entire family.. Tell me, idan kika fasa zaki iya biya ne.?
Badia ta danyi kasa da murya taceda Azeema tazo ta zauna su jira fitowar Ummul. Ta dubi Anisa tace Kiyi hakuri bazata fasa ba.
Hararsu take daga sama zuwa kasa kafin taja dogon tsaki ta shige tana toshe hanci.
Azeema ta yunkura zata bi bayanta Badia Tai saurin rikota.
Ki kyaleni na shayar da wann mai kirar zabon mamaki Badia.
Badia ta girgiza kai Aa Azeema yau ranar farin cikin Ummul ne bazaki bata mata da wani abu ba. Musamman fada da dangin mijinta.. Ki kyaleta kawai karma ki kulata.
Azeema Tai kwafa Wllhi darajar Ummul taci da nayi wasan kura da ita dan dama hannuna kaikayi yake kwana biyu. Ban saba da wann salihancin ba.
Badia tace Naji dai bazakiyi ba.. Ta karada inata so na tambayi Ummul ina surkin namu mu gaisa.
Daga can Azeema ta hango Haidar na tahowa dukda bata sanshi ba amma kallo daya ta masa ta gane shine angon. Sai ta shiga taba Badia tana fadi a hankali Ke wllhi gashin can yana zuwa.. Shine ango. Shine surkinmu.. Na shiga uku Badia kiga irin mijin da Ummul ta samu bayan duk kalubalen da ta fuskanta saikace tauraron fina finan Hindiyan nan. Ummul ta hada komai Badia kawai ta nemi lahira. Gaskiya na yarda da karin maganar nan da ake cewa Wani JINKIRIN alkhairi ne. JINKIRIN Ummul ya zama Alkhairi Badia. Wllhi ta amsa sunanta Ummulkhairi.
Jin Azeema duk ta zauce yasa Badia take mata kafa kadan dan ya kusa karasowa yanda suke. A hankali take furta Ke meye haka wai. Ni dan Allah ki natsu saikace wacce kikai gamo sai sunbatu kike. Ki mata fatan alkhairi kawai.. Kinga gashi nan ya iso da alama dakin da Ummul take zai shige.
Kafin Badia ta rufe baki Azeema ta mike ta hau daga masa hannu Sirkinmu.!
Haidar ya juyo da mamaki sai ya shiga yan waige waige yana tunanin kodai ba dashi ake ba.
Azeema ta kuma nunasa da yatsa kaidai sirkinmu. Ta karaso yanda yake bata daina washe baki ba Mu yanuwan Ummul ne.. Ni kanwarta ce.. Waccan kuma dake zaune Yayarta ce Babanmu daya ai da Ummul..
Badia dake zaune daga saman sofa takaici ne ko kunyar abinda Azeema take ta ma rasa wanne ne daya take.
Sai sukaga Haidar Ya murmusa ya fasa shigewa dakin Ya nufo yanda suke. Anisa da karasowarta wajen kenan mamaki kaman ya kasheta ganin da gaske Haidar Maitama kema kucakan nan sannu da zuwa kuma fah ransa a sake. Wai anya baa canza shi ba kuwa. Tana tsaka da tunaninta ta sinkayo muryar Azeema tana fadin Sunana Azeema. Ni ce ta hudu wajen Abbanmu ai.. Daga Ummul sai ni ke biye mata..
Haidar Ya jinjina kai har lokacin da murmushi saman fuskarsa. Ya nuna Badia yace And.. you are..?
Sai Badia da Azeema suka dubi juna. Azeema ta karaso da sauri tana rada ma yaruwarta Adda Badia, kinsan dai mudai boko rakiya mukayi dan na tabbata Har yau ko shakeki zaai da kyar ki iya rubuta sunanki. Su Ummul da Khulsum ne masu kwakwalwar ganewa. Turanci fah yake miki.. Tambayarki yake Ya kike.. Kice masa you are fine. Haka nakeji ake fada. Kar ki masa shiru zaki disga Ummul.
Badia tace You fine.
Sai Ya dan murmusa kawai yace Ill check on.. Khairy.. Sannunku da zuwa once again.
Azeema taci gaba da waving dinsa har ya shige. Badia ta fuzgota tana fadin Ke dan Allah wai meye haka ne.? ki kama kanki mana.
Mutanen da muke gani a tv mun gansu a zahiri Har gaisar damu yake kice na kama kaina.. Ke Nifa yanzu ko unguwarmu na koma wllhi ba ma kowa zanke magana ba ehe Kiji wani sunan yan gayu da yake kiran Ummul dashi.. Kai wllhi na Miki murna yaruwa Kekam taki adduar ta amsu.
Badia ta girgiza kai Allah Ya baki lafiya Azeema.
Azeema ta kyalkyale da dariya tana amsawa da Ameen.
Anisa da takaici Ya cikata furzar da huci Tai tana barin wajen. Dik yanda zatai bazata bari sunan wadannan Almajiran ya shiga guest list ba tin daga waje zata sa securities suyi watsi dasu.
Ana shirin fita wajen event Anisa tai kicibis da Azeema a dan wani lobby. Sai kawai ta kara wayarta a kunne alamun tana amsa kira I need to double-check the guest list because ba ko wasu shara bane zaa barsu su shiga. You know is a high class event. Ta karashe tana aika ma Azeema harara.
Zata wuce Azeema ta cakumo wuyarta ta dawo da ita baya Toh ya ne.! nace ko kinada abin cewa ne.? Ta karashe tana tunkuda drink din dake hannun Anisar ai kaw ya zube ma Anisa a jiki ya bata mata expensive gown dinta.
Mamaki ya hana Anisa rufe baki ganin bata ko tanka Azeema ba amma tai mata wann dibar albarka.
Girgiza Kai Anisa take tana fadin No this is not happening.. Not my dress..! Ta dubi Azeema dake nade hannu riga Kai kace zata daga wani abin ne tace You ask for it.! Tai maganar tana sakin huci tana kokarin Kai ma Azeema Mari amma sai caraf Azeema ta rike nata hannun ta kuma dauketa da maruka har biyu masu kyau.
Anisa ta kuma zaro ido cikin mamaki. Saima Azeema ta soma bata tsoro ta fara tunanin jada baya zata gudu Azeema ta kuma jawota tana fadin Ashe karyar tashanci kike karamar maras kunya ba yanda zakije.
Anisa taji rikon manyan yan dambe ta soma kokawan kwace kanta tana fadin Let go.. let me go.. What are you doing you witch.. I said let me go.
Wani daki mai kaman store Azeema ta turata ta janyo kofar da karfin gaske Wanda taga har wani dan haske ya kawo daga wajen rikewar mai daukeda alamun wajen danna yatsa, sann harda wasu lambobi jiki. Bata taba ganin irin kofar ba. Sai ta dan matsa da baya ganin kofan na haske.
Anisa ta fara girgiza Kai tana bugun kofan tana fadin ta budeta. Kara Anisa ta saki tana Kama Kai sanin cewa da tai kofan Smartdoor ne. A fili take fadin a taimaketa tana buga kofan.
Azeema kuwa shekewa da dariya tai jin Anisa tanata ihu daga cikin dakin sann ta kasa fitowa. Sauri sauri Azeema ta bar wajen tana kyalkyale dariya ga wayar Anisar da ya fadi nan wajen sanda take kokarin turata dakin. Tasa kafa ta kuma cilla wayar a gefe tai wucewarta abinta. Sai nishadi takeji tayi maganin zabuwar can.
Anisa taci gaba da bugun kofa tana neman dauki ga wayarta can a gefe Hisham sai kira yake no response.
SameenaAleeyo
