*AUREN WATA UKU..!*
*45*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
Zame jikinta tai daga nasa tana mai goge fuskarta. Lokaci guda ta k’arasa saman sofa ta zaune tana mai ci gaba da goge hawayen da ya wanke mata fuska.
Ya d’anyi still a wajen yana dubanta kaman bazaice komai ba sai kuma ya zira hannayensa cikin aljihun wandonsa. Ya soma takowa a hankali zuwa yanda take. Har lokacin babu walwala a fuskar Ummul.
Haidar ya zauna daga gefenta ba tareda ya dubeta ba. Dak’ik’ai suka gifta. Ya soma tuno kalaman Mommy da tace he should own up to his mistakes. Ya dan lumshe idonsa kadan. Har Ta cire ran bazai ce komai ba ta sinkayo muryarsa “Are you.. Still mad..?”
Ta dan dube shi. Sai taji yace “Do you want me to apologise.?”
Nan ma batace komai ba sai d’an dubansa da tai.
Haidar ya dan furzar da huci wann karon yana janye idanunsa daga barin dubata “Oh no Khairy. You are not going to give me that silent treatment.”
Nan ma bata ce komai ba.
Sai ya mik’e a dan fusace “Ok fine.. Dama kawai baki dawo ba idan bazaki ce komai ba.!”
Mik’ewa tai itama cikin fushi “Da gaske, haka kace…?” Sai ta nufi k’ofa da zummar ficewa. Haidar yai saurin dawo da ita.
Ta d’an kalleshi “Ni ka sakar mun hannu.”
“Idan ank’i fah.?!” Ya fad’i yana tsareta da ido sosai. Sai ya dan sassauta rik’on da yai mata “Wai duk mema genesis na fushin nan ne .? Kan project d’in nan ne right.?”
Ta dan kallesa da wutsiyar ido. Kaman Wanda ya fama mata wani mik’i tace “Waye yake fad’a da mahaifinsa.? Waye yake d’aukan fansa kan mahaifinsa.!”
“Oh no please.. Not again.” Ya fad’i yana kame Kansa kad’an. Sai kuma ya dubeta a fusace “Maybe he pushed me into becoming this monster.. Don’t you think.!”
Sai ta girgiza Kai tana dubansa “A’a saidai idan hakan d’in ka zab’a. K’walla suka ciko idonta tana dubansa. Ta rik’o hannayensa cikin nata “Shin zakaci gaba da rayuwa a bayanka ne.? Meyasa zaka bar kanka rufe cikin kurkuku.. Wann k’uncin da kake ji cikin zuciyarka ba komai bane illa kasa karb’an k’addararka da kayi. A wasu lokuta Allah yakan saka mana jarabawar mu su zamto mutanen da suke da alak’a ta jini damu. Mutane mafi kusanci damu. Bamu ke zab’an ahalinmu ba, kuma hakan Rahamarsa ce.” Ta d’an numfasa kafin taci gaba. Allah ya jarabci salihan bayinsa Annabawansa da ahalinsu. Kaman Annabi Ibrahim (AS) Allah ya jarabce shi da Babansa. Kaman Annabi Yusuf (AS) Allah ya jarabce shi da ‘yanuwansa. Kaman Annabi Yaqub (AS) Allah ya jarabce shi da ‘ya’yansa. Kaman Annabi Nooh(AS) Allah ya jarabce shi da D’ansa. Kaman Annabinmu fiyayyen halitta(SAW) Allah ya jarabcesa da Uncles d’insa. Duka wad’annan Annabawa masu daraja sun fuskanci jarabawa daga cikin ahali. Ashe lallai muma zaa jarabcemu daga cikin namu ahalin. Wad’ann k’alubale da jarabawa suke k’arfafa imaninmu..Sann Allah shike shiryar da Wanda yaso..” Daga haka bata kuma cewa komai ba taci gaba da tattare kayyakin da take.
Haidar ya koma ya zauna had’ida zuba mata ido ba tareda ya kuma cewa komai ba. A hankali yasa tafukan hannayensa ya shafi fuskarsa.
**
Koda suka dawo gida maganganun Anisa suke yawo a kwanyarta, tayi k’ok’arin ta yakice tinanin amma ta kasa. A lissafi saura kwanaki uku kacal ta cika watanni uku da aure. Hakan na nufin alk’awarin da ta d’aukar ma mahaifiyarta yana gab da cika. Ya kamata ta waiwayi gida. Tana buk’atan sanin wani hali ahalinta ke ciki. Musamman majinyacin mahaifinta. Tinanin kalaman Anisa suka ci gaba da dukan kwanyarta. ‘Shin Mommy ta tab’a tambayarki wani abu gameda ahalinki.?’ Tai saurin rintse idonta ta mik’e da zummar ficewa taji muryar Haidar daga bathroom yana kiranta. Ta isa jikin closet din kafin ta d’anyi gyaran murya ta amsa. Haidar yaci gaba “Could you please pass me my towel.”
Ta shiga bin closet din da kallo tana duban yanda komai yake cikin tsari. Nan ta hangi towel d’in dan sama kad’an anyi folding an jerasu cikin open shelf cabinet. Ta ciro towel din mai dan girma tai knocking a k’ofan bathroom din “Ga.. Gashi nan na kawo maka.”
Muryarsa ta sinkayo “The door is open.. you can come in.”
Ta zaro ido waje jin abinda yace. Sai ta soma girgiza kai ita kad’ai “A’a.. A’a kawai ka karb’a.” Ta k’arashe tana mai tura hannunta dake rikeda towel d’in ta tsakanin k’ofar. Bata ankare ba saiji tai ya had’e da hannunta Ya janyota cikin bathroom d’in.
Ummul ta rintse idonta sosai sai ta fashe masa da kuka. ta shiga dukan k’irjinsa “Mai kake aikatawa ne.. Dan Allah ka… k’yaleni na fice. Please..!”
For the first time da taji sautin dariyarsa. Cak ta tsaya da abinda take still ta kasa bud’e idonta.
Haidar murmushi yake Har hak’waransa na bayyana “Okay.. Open your eyes now.. You are here already..!”
Ummul ta mak’e kafad’a tana kuma dukan k’irjinsa “A’a nidai bazan.. bazan bud’e ba.”
“Okaaaay.. Let’s see now..” “Trust me, I’m gonna make you open those eyes.” Har lokacin murmushi mai sauti mai bayyana hak’wara yake. Abinda Ya jima baiba na tsawon lokaci.
“Wai.. Mai kake k’ok’arin aikatawa.?”
Bai amsata ba yaci gaba da niyyansa.
A yayinda Ummul ke k’ok’arin zillewa bata ankara ba sai ji tai Haidar Ya janyota sun fad’a cikin jacuzzi tub d’in a tare.
Ummul ta ja numfashi tana mai fiddo kanta waje had’ida shafe ruwan da Ya jik’a mata fuska.
Ta kafesa da ido baki a ture kaman zata fashe da wani kukan.
Haidar ya kashe mata ido daya “See. I told you zansa ki bud’e idonki.”
Ta soma k’ok’arin mik’ewa yayi saurin kamo hannayenta “Ina kuma zakije bayan kin riga kin jik’e.”
Baki a ture tace “Ba kaine ka jik’ani ba... Kuma kasan Mommy ta gayyacemu cin abincin dare. Ya kamata naje sashenta da wuri dan na taimaka da wasu abubuwan..”
“Kar ki damu Mommy bazata ce komai ba..”
Ta d’an hararesa baki a ture “Kuma na riga na shirya.. kasa na jik’e gaba d’aya.”
Ya dan tab’e baki kad’an had’ida lifting shoulders d’insa “Shikenan sai ki sake wani wankan.” Ya matso saitin kunnenta yana mai rage murya “Let’s bath.. Together..”
Turasa tai da duka k’arfinta ta tashi . Murya na rawa ta shiga nuna masa forehead d’insa da hannunta “Kaga duba kaga.. akwai abu kusan idonka..” Yakai hannunsa goshinsa sai Ummul tai amfani da damar ta tashi a guje ta zille masa. Wann karon itake masa dariyar.
“Don’t worry, I’ll get you next time.” Ya k’arashe yana mai mata alama da yatsarsa.
Anisa da tin shigowarta sashen ta soma sinkayo kaman sautin mutane nan ta sad’ad’ kaman mai shirin satan wani abu. Ta lab’e yanda take sinkayo sautin. K’iris Ya rage Zuciyar Anisa bai buga ba. Kasa jurewa tai dole ta fice daga sashen.
Tana ficewa ta d’auki waya ta kirawo Hisham. Cikin tsananin huci take fad’in “No way Hisham. I can’t wait till that day.. I’m losing my patience here. Na tsani wann kucakar.. She’s driving me crazy.. Ji nake kaman naje na shak’eta.”
“You will not do anything foolish.”
Ta katsesa “Na gaji Hisham.. Bakaji yanda suke dariya cikin nishad’i ba. They were having a good time.” Ta saki kara tana fad’in “It’s so irritating.. Ka gane we can’t let those two be happy while we are stuck here.. just freaking miserable. We need to act fast.!”
Hisham dake ci gaba da sakin huci Ya katseta cikin tsawa “Just shut up Neesa.! Na gaya Miki bazaki aikata komai ba ba tareda umarnina ba. Na dan lokaci ne. Haidar bazai taba samun dama akan Ummul dita ba. So just trust me.!” Ya k’arashe idanunsa ba kuma kad’awa in rage.
A fusace ta katse kiran tana kuma ci gaba da zagaya d’akin zuciyarta naci gaba da tafarfasa. Sautin nishadin Haidar da Ummul Ya kasa barin kwanyarta da kunnuwarta. Ta saki k’ara kad’an tana durk’usawa wajen. A hankali take furta “I hate you.. I hate you Ummul.!”
*
Koda Ummul ta koma nata d’akin murmushi ne Ya kasa barin fuskarta. Ta Tina sanda sukai juyi cikin jacuzzi tub tare sai ta lumshe ido a hankali tana sauk’e sassanyar ajiyan zuciya. Wata doguwar riga silk kalan peach da ya zauna a jikinta sosai ta d’auko ta saka ta yane kanta da mayanin rigar. Ba makeup a fuskarta sai d’an man leb’e amma sosai tai kyau. Fatarta da bai cika haske ba sann bai cika duhu ba ya k’ara murjewa yayi kyau. Kwantattun sumarta irinta asalin k’abilar fulani da ta d’auko daga mahaifiyarta sun kwanta sunyi luf tin daga gaban goshinta Har zuwa gefen fuskarta. Kallo d’aya zaka mata kaso sake kallonta. Kalan rigar sosai ya tafi da Kalar jikinta. Abinda bata saba ba sai ta tsinci kanta da duban kanta a madubi. Kunya da dariyar kanta suka zo mata lokaci d’aya. Harga Allah zata iya cewa ta mance da wata damuwar gidan duniya da batun Anisa. Shi d’in kawai take hangowa a duniyar ta Wanda takeji tamkar su biyu ne ciki. Parlor ta sauko tana jiransa dan yace ta jirasa zasu shiga sashen Mommy tare.
A b’angaren Haidar kuwa bayan Ya d’auki file din ya jima yana juyawa yana tinanin maganganunta kai tsaye sashen mahaifinsa Ya nufa.
Daddy yana zaune study Haidar yai Sallama Ya shigo.
Daddy ya d’ago ya dubi Haidar da idanunsa dake rufe cikin farin gilashi na k’ara k’arfin gani ga wad’anda shekaru Ya d’an ja masu.
Tin daga yanda Daddy ya amsa masa Sallama jikin Haidar Ya d’anyi sanyi. Dan yanayin amsa masa da yai yasha bambam da irin yanda yake amsa masa a baya.
Sun d’auki lokaci suna duban juna kafin Daddy ya nuna masa kujera mai kallon table d’insa yace ya zauna.
Haidar ya k’arisa ya zauna.
Shiru Ya dan ratsa tsakani kafin Haidar yai k’arfin halin cewa “Daddy.. Barka da dare.”
Daddy ya amsa masa had’ida jinjina Kai.
Sai Haidar ya aje folder d’in saman table din Daddy.
Daddy ya girgiza Kai kad’an kaman Wanda yake avoiding k’wayan idon Haidar d’in “What’s this for.?”
Haidar yai clearing throat d’insa “Yarjejeniyar project d’in ne Daddy.. Tareda resignation latter.. Na janye ragamar kula da kwangilar.. Sann.. Na aje aikina na company.”
Daddy sai Ya d’ago yana dubansa sosai wann karon.
Haidar sai Ya mik’e kansa a kife “I.. I’m sorry idan ban kasance wann d’an da kake fata da buri na zama ba..”
Ya soma k’ok’arin ficewa daga study d’in mahaifinsa ya dakatar dashi.
“Aliyu.!” Daddy ya ambaci sunansa.
Ya d’ago Ya dubi Daddy.
Da ido Daddy yai masa nuni da kujeran “Koma ka zauna.”
Haidar ya komo ya zauna har lokacin Kansa a kife.
Cikin tsawa da fad’a kaman yanda ya saba masa a lokutan baya ya soma fad’in “Ni kake ce ma ka aje aikinka..?” How dare you.? Who do you think you are...! Kai har ka kai ka dubeni kace min ka aje aikinka.? Kai har ka isa.?!”
Da a lokutan baya ne da ya amsa ko ya maida ma mahaifinsa martani cikin daga murya. Amma ga mamakin Daddy sai yaji ya soma magana a natse “I’m sorry.. But I can’t do it Daddy.!” Ya fad’i k’walla suna ciko idanunsa. Cak mahaifinsa ya tsaya yana dubansa.
Haidar yaci gaba da girgiza Kai “I can’t destroy you.!”
Daddy ya koma ya zauna yana duban Haidar d’in sosai cikin tsanani shock.
“My plan was… To use this so called project and destroy you.. I wanted to show you the kind of monster you created in me.. But then I couldn’t.. I couldn’t destroy the hands that raised me koda ace mun kasance munada alak’a mai rauni cikeda tarin k’alubale.” Yaci gaba da girgiza kai. Sai murmusa kad’an wann karon “I just want to be free from this prison. I.. I don’t want to keep on living my life tied to all this rage and hatred.. I want live a normal life.. To start a family of my own..” Muryarsa yaci gaba da rawa “I.. I’m sorry Daddy.. I’m sorry idan ban kasance wann d’an dake fata da burin samu ba.. I’m sorry idan ban kasance wann D’an da zakayi alfahari dashi ba.. Believe me.. I truly.. am sorry..”
Baikai aya ba Daddy dake ta k’ok’arin danne hawayensa sai ya zame farin gilashinsa ya kauda fuskarsa kadan yana goge hawayen da suka mak’ale masa a ido.
Kaman daga sama Haidar ya sinkayo muryar mahaifinsa “Aliyu, my son..”
Da mamaki Haidar ke duban Mahaifinsa Jin ya ambacesa da D’ansa abinda bai taba ji daga mahaifin nasa ba.
“Shin ka tambayi kanka koda ka farka daga coma meyasa baka ganni wajenka ba.?”
Shiru Haidar baice komai ba.
Daddy yaci gaba da jinjina Kai har lokacin bai kalli b’angaren da Haidar d’in yake ba “Sabida bazan iya kallonka a ido ba.. Bazan iya ambatan kaina da mahaifinka because I.. I haven’t been a good father to you.. And I treated you badly..” Daddy ya kifa Kansa hawaye na gangaro masa “Fad’an da kaji ina maka a yanzu borin kunya ce kawai sabida ni d’in ban sauk’e wani nauyi da hakki na mahaifinka dake rataye wuyana ba. Hadisi ne guda cewa ko wannen mu mai kiwo ne kuma za’a tambayemu gameda wann amana na kiwo da aka dank’a mana. Bazan iya duban idanunka na nemi gafararka ba Haidar… Bazan iya ba..!” Saiga alamun kuka cikin muryar Daddy.
Haidar ya mik’e jikinsa a matuk’ar sanyaye ya tako har zuwa gaban kujeran da Daddy ke zaune bisa. Duk’awa yai gaban Daddy Wanda har lokacin Kansa na kife yana d’igar da hawaye.
Haidar ya daura hannayensa biyu saman hannayen Daddy dake bisa laps d’in Daddyn. Shiru ne ya ziyarci wajen baka iya jin alamun komai face motsin zuciya.
Daddy ya rik’e hannayen Haidar tsam cikin nasa “I’m sorry son.. I’m sorry.. Please forgive your Dad…”
Hawaye suka gangaro ma Haidar dake duk’e gaban Daddy hannayensu cikin na juna.
Mommy da ta nufo k’ofan dan ta sanar da mijin nata gayyatar D’ansu da matarsa dinner matsayin maraba da dawowa gida ma Haidar d’in koda bazai nuna kulawarsa kaman yanda ta tsammata ba, nan ta riski wann babban al’ajabi. Rana mai d’inbin tarihi.. K’afafun Mommy suka kusan gaza d’aukarta.. Hawaye suka shiga zarya a k’uncinta.. Sai Mommy ta fad’i k’asa tana mai sujada na godiya ga Ubangijinta. Tama rasa mafarki ne take kokuwa dai a farke take. Haidar dinta da mahaifinsa take gani cikin yanayi da bata tab’a tsammanin zata gansu ciki ba. Allah buwayi gagara misali. Mommy ta kuma yarda cewa lallai duk Wanda ya dogara ga Allah toh fah Allah ya isar masa. Itakam babu abinda zata ce saidai taci gaba da gode ma mahaliccinta Wanda ya yaye duhun dake cikin gidanta da ahalinta ya yalwatasu da haskensa. Ta saki turban boka da suka d’auko daga fari ta rik’e turba na gaskiya sai gashi komai yana gudana cikin sauk’i. Lallai wann wani rahama ne daga Ubangijinta. Lallai wann izna ce ga tababbu masu bin hanyar b’ata. Wanda ya gane Allah shi yake yi ba boka ko Malam ba shi keda babban rabo duniya da lahira. Bata san sanda ta koma da baya ba ta nufi d’akinta ta maida k’ofa ta rufe ta fad’a saman gado tana kuka sosai. Kukan farin ciki wann karon. Kukan da ya goge Wanda ta jima tanayi a baya Kama daga zuciya har k’wayan ido. Alkhairin Allah yaci gaba da haska gidanta da ahalinta.
Haidar yaci gaba da girgiza Kai yana rik’eda hannayen Daddy gam cikin nasa “Daddy ka daina bani hak’uri. We are all human beings.. We make mistakes. What’s important is that we learn from those mistakes.” Yaci gaba da jinjina kai a hankali “Ni yafi cancanta na nemi yafiya a gareka Daddy. Idan inada hakki akanka hakkinka dake kaina yafi girma. Duk yanda naje nazo banida madadinka.. I should’ve been more understanding with you. Cikin zuciyarsa yake tuno sanda Ummul take fad’a masa ‘A rayuwa wasu lokutan Allah yakan saka mana jarabawarmu ya zamto people that are tied to us by blood.’ Sai Haidar ya mik’a hannu ya d’auko folder d’in project da ya shigo dashi. Ya daura saman hannun Daddy suna kallon cikin fuskan juna. Murmushi gauraye da siraran hawaye saman fuskar Haidar yake fad’in “Daddy I can walkway from this Business because it’s my choice.. But I can’t walkway from you. Do you know why.?”
Sosai Daddy yake kallonsa yana hawaye. Haidar yaci gaba da jinjina Kai “Because you are my Father.. Allah chose you for me… We are tied to each other by blood because haka Yake so ya kasance.” Yaci gaba da jinjina Kai yana murmushi “Daddy jininka shi yake circulating cikin jikina daga farko.. A karo na biyu Kai ka bani jininka, you couldn’t walkaway from me either. Sabida ni d’in D’anka ne.”
Daddy sai ya janyo kan Haidar ya rungume cikin jikinsa. Muryarsa na rawa yake fad’in “Allah ya maka albarka Aliyu.”
**
A lambum dake bayan sashen Mommy aka shirya cin abincin daren. Hasken wutan lantarki ya karad’e ko ina tamkar ba dare ba.
An shirya teburin gwanin ban sha’awa ga barbecue stand daga gefe.
Suna cikin shirya plates saman teburin itada Anisa Anisa tai excusing kanta sakamakon kira da ya shigo wayarta. Nan Ummul ta hangosa na tahowa. Sassanyar murmushi saman fuskarsa. Ta shagala sosai da kallonsa kaman yanda shima ya shagala da kallonta dan sosai tai masa kyau.
Yana k’arasowa sai ya tsaya daga bayanta ya dan rungumota had’ida rank’wafo da kansa kusan kunnenta “You look.. Gorgeous.!” Ya fad’i cikin sigan rad’a.
Ummul ta soma k’ok’arin turesa daga jikinta tana ‘yan waige waige “Mai kake aikatawa ne wai.. Idan wani ya ganmu fah.?”
Bai saketa ba ya kuma rad’a mata “So what.! Can’t I hug my wife.?”
Ta waiga ta dubi Anisa dake can gefe tana amsa waya. Ta kuma duban ma’aikatan kitchen guda biyu dake gefe gaban BBQ stand.
Kaman zatai kuka tace “Dan Allah ka bari akwai mutane wajen nan fah nan..”
Juyawa yai ya dubi kitchen staff d’in. Sai ya dan murmusa “Is that problem.? fine. Zo muje.” Bai jira amsarta ba ya shiga janyo hannunta. Suka nufi yanda ma’aikatan ke gashin naman.
Haidar yace musu suna iya tafiya zasu kula da barbecue d’in.
Ma’aikatan suka amsa masa cikeda risinawa suna duban yanda Haidar ya janyo Ummul dake fad’in ita fah bata iya amfani da irin wann abin gashin ba. Yace kar ta damu tare zasuyi.
Sosai suka birgesu kaman kar su daina kallonsu. Abu ne da zasu iya cewa basu tab’a ganin ya faru gidan ba. Basu tab’a ganin Haidar cikin farin ciki irin wann ba. Su dai kam Sun shaida zuwan Ummulkhair gidan Alkhairi ne.
Anisa ta juyo baki sake tana duban ikon Allah Haidar da Ummul gaban barbecue stand sai zuba soyayya suke. Gwiwoyinta taji sun sake kamar wata maras laka. A haka Mommy ma ta k’araso wajen ta taddasu. Farin ciki maras misaltuwa ya kuma gauraye zuciyarta. Zuwan Mommy wajen yasa Ummul janye jiki ta kyale Haidar shi kad’ai.
Haidar na fad’in ta mik’a masa bbq cutting board sai sann ya kula ta silale ta bar shi shi kad’ai.. Ba kowa wajen ma sai shi kad’ai. K’ila Sun shige yin wani abin cikin gidan. Ya dan tab’e bakinsa kad’an.
Amma sai yaga wani hannu na mik’o masa abinda yake nema. Haidar yabi hannun da kallo. Ga mamakinsa Daddy ya gani. Kyakkyawan murmushi saman fuskar mahaifin nasa. Haidar yasa hannu ya amshi board d’in had’ida godiya ma Daddy. Jinjina Kai Daddy yai. Sai Haidar yaga Daddy na nad’e hannun long sleeve shirt din dake jikinsa alamun zai tayasa.
Sai Haidar ya girgiza Kai “No Daddy you don’t have to.. Ya kamata kaje ka zauna.. I.. I’ll serve you some.” Ya fad’i awkwardly dan abu ne da bai saba faruwa ba koma bai tab’a faruwa ba tsakaninsu.
Murmushi ne saman fuskar Daddy ya dafa kafad’an Haidar din “No Son, let’s do it.. Together.”
Haidar yai murmushi yana tuna lokacin yarantarsa wann shine mafarkinsa. To make memories with both his parents… To strengthen their bond. Ya samu kusanci sosai da mahaifinsa. To have some quality time together.. To build something together. To play sports, video games, go horse riding da dai sauransu. Sai ya murmusa yana duban mahaifin nasa sosai. Kaman mafarkinsa ne yake zama gaskiya. Yana k’ok’arin yanka naman saman board din Daddy ya dafa hannunsa wana hakan Ya dakatar da Haidar. Suka dubi juna sai Daddy yace “Be careful Engr, this is not a construction side.”
Su duka sai suka d’an dara kad’an. Daddy yace “You know Son, if I were to turn back time.. Da munyi aiki tare hand in hand.. Like professional Engrs.”
Jikin Haidar Ya d’anyi sanyi Ya fahimci abinda sukeyi a yanzu d’in Ya K’wadaitar ma mahaifinsa inama lokacin da sukeda damar kasancewa tare a company sunyi ayyuka tare tare babu tsangwama babu hantara. Gashi yanzu Ya sanar da mahaifinsa Ya aje aikin company meaning ba lallai su sami irin wann damar ba. Muryar Daddy ya kuma sinkaya “Bana so na tak’uraka. Da na rok’eka wani alfarma.”
Haidar yai saurin girgiza kai “No Daddy.. Ka wuce wann.”
Daddy ya murmusa “Haidar, I can understand you, if you… don’t want to manage the project due to.. your personal priorities.. But please kar ka aje aikinka.. Kar ka bar Kampanin… Let this be the last abu da zan buk’ata ka mun.”
Haidar yai saurin girgiza kai “No Daddy, I’m your son.. Hakkina ne matsayinka na mahaifina nayi maka biyayya cikin abinda bai sab’a ma mahaliccina ba. Kuma wann bazai zama abu na k’arshe da zan maka ba. Umarni kawai zaka bani a koda yaushe.. Kuma na maka alk’awari bazan aje aikina ba in sha Allah. Bazan bar company ba. Together we will take the company to greater heights.!” Ya k’arashe da murmushi saman fuskarsa.
Sai Daddy ya kamo k’afafunsa Ya rungume “Thank you son. Allah ya maka albarka.”
A haka Mommy ta k’araso wajen ta iskesu. Farin cikinta ya ninku. Itakam a halin yanzu tana jin babu sauran abinda zata nema da ya shige taita gode ma Ubangijinta da ya cika rahamarsa ga ahalinta.
Bayan cin abincin suna zaune itada Haidar a parlor. Haidar ya kuma murmusawa ya dubeta “You know Mommy, After all these years it's today that I feel like… I'm part of the family.”
Mommy ta rik’e hannayensa cikin nata. Kyakkyawan murmushi saman fuskarta “We gonna have some family bondings to makeup for all the time we've lost… Kuma.. Zamu fara da shagalin bikinka. Aurenka da Ummul ta cancanci biki na gaske irin na ‘yan gata.”
Ya dan girgiza Kai yana murmushi “Mommy na kasa yarda bisa yarjejeniyar Wata uku na amince da auren Khairy.. Dan kawai Daddy ya bani wann project d’in.”
“Shiii.” Mommy ta dakatar dashi “Babu wann maganar Haidar.. An rufe shi har abada. D’ago baya irin haka baida wani amfani. Bazaka sanar da Ummul wani abu mai suna auren yarjejeniya ko AUREN WATA UKU ba.”
Sai ya d’an dubeta can k’asar zuciyarsa yana jin zuciyarsa ta katsa samun natsuwa har sai ya sanar da ita.. Sabida a halin yanzu Aure yake so ya gina da ita bisa zallan gaskiya.
Ya d’an dubi Mommy “Mommy I want to build my marriage with her base on trust and transparency. Bana so daga baya tazo ta fahimci cewa na aureta ne bisa yajejeniya zuwa wani k’ayyadajjen lokaci. I want her to hear it from me first kafin taji daga wani waje.”
Mommy ta jinjina Kai “Na fahimceka Haidar.. Amma kafin nan ka d’an dakata har a gama wann bikin tariyarku can gidanku da na saka nan da kwanaki biyu kacal. Idan yaso sai ka sanar da Ummul yanda al’amarin ya kasance..”
Sai ya d’anyi jim kafin kuma ya jinjina Kai a hankali “Shikenan Mommy. Idan hakan kike so.”
Ta murmusa cikeda jin dad’i. Burin ko wasu iyaye shine su samu ‘ya’ya masu biyayya a garesu. Lallai mai rai kar ya cire tsammani daga rahamar Ubangijinsa. Who would’ve thought za’a zo lokacin da Haidar zai d’auki umarnin mahaifyarsa ba tareda jayayya ko nuna k’in amincewa ba.? Ya ke ‘Yaruwa da Allah ya Miki jarabawa da D’an da kika haifa, kar ki tab’a yanke k’auna daga rahamar Ubangijinki domin kuwa shid’in rahamarsa mai yalwa ne. Kar ki karaya, kici gaba da mik’a lamuranki ga Ubangiji. Duk Wanda Allah ya zama majib’icin al’amarinsa shi keda babban rabo.
Haidar ya mik’e da zummar mata sallama ta dakatar dashi.
“Yauwa nace ba sai abu na gaba..”
Haidar ya jinjina kai yana sauraron Mommy.
“Kanaji.. Ummul zata dawo nan sashena da zama har sai anyi bikin an kai maka ita.”
Wann karon zaro ido yai kaman wani abin tausayi ya langab’e kai “Haba mana Mommy does it have to be this way.. I just came out of hospital fah..I’m still a patient.”
“Mommy ko kin daina tausayina ne.” Ya kuma fad’i a marairaice.
Dariya yaso bata amma ta gimtse tace “Ba tausayinka na daina ba. So nake kai d’aukin d’iyata idan an kai maka ita.. Waima dakata shin kai ka biya sadakin nan ne.?”
Haidar ya sauk’e ajiyan zuciya kaman wani maraya “Shikenan Mommy.. Saida safe.. Amma please a k’yaleta ta kawo min coffee.”
“Naji… Just coffee..” Tai maganar tana jaddada masa. Ta k’arada “Jeka Allah bamu alkhairi.”
Haka ya fice duk jikinsa ba kuzari. Shi fah maganar gaskiya wann gadara da Mommy take masa da mata akan sadaki ya fara isansa. Shidai kawai gwara ya biya Mommy sadakinta ya huta.
Bayan ficewar Haidar shiryawa tai ta nufi sashen Daddy.
A parlor ta iske shi. Daddy ya dubeta da mamaki. For days yana k’ok’arin shawo kanta daga fushin da take dashi sai gashi yau ta kawo kanta har yanda yake. Murmushi yai cikin zuciyarsa yake ayyana lallai sai a bar uwa da D’anta. D’anta shine rauninta.
Ta k’araso kanta a k’asa. Kaman mai shirin zama sai kuma ta silale gabansa. Ta kifa kanta tana hawaye. Cikin rawar murya irinta mai kuka take fad’in “Engr ka yafe min.. Ka yafe mun duk abubuwan da nai maka.. Na shekarun baya da na kwanakin nan..” Kuka ya hanata ci gaba da magana. Daddy ya duk’a shima suna fuskantar juna. Sai ya rungumota zuwa jikinsa. Kamar wacce take jira kukanta sai ya k’aru. Shima ya saka d’an yatsarsa ya goge kwallan da ya mak’ale masa cikin ido.
“Is Ok Kwaise. Ya isa haka.. Dukanmu ‘yan adam ne masu kuskure. Mafiya alkhairi sune masu tuba. Bayan tsawon shekarun nan idan akwai Wanda yafi cancanta ya nemi yafiya ni ne. I supposed to be the head of this family.. Amma duk sai na bar Miki nauyin.. Kece kika jajirce Akan wann ahalin Kwaise.. You never give up despite the challenges.. Kin tsaya Akan k’afarki ganin cewa ahalinki bai watse ba. Kinyi abinda ni na kasayi Kwaise.. Thank you for not giving up on us..” Murmushi ne gauraye da hawaye saman fuskarsa. Sai suka rungume juna wani kukan na kuma zuwa ma Mommy.
**
A b’angaren Haidar kuwa koda ya koma sashensa zama yai shi kad’ai a balcony d’insa yana tunanin rayuwarsa. Da yanda shigowarta cikin rayuwarsa Ya canza komai lokaci guda cikin ikon Allah. Yana jin wani shauk’i can k’asar zuciyarsa Wanda bai tab’a jin hakan ga wata mace ba. He wants to build something special with her.. base on trust and transparency wanda hakan ke nufi dole ya sanar da ita wasu abubuwan daga past d’insa musamman abinda ya danganci personal rayuwarsa. Aurensa da Dareen Wanda ko family d’insa basu sani ba har ya faru ya k’are da kuma yanda nasu auren da ita Ummul d’in Ya kasance. Yarjejeniya sukai da mahaifiyarsa zata shigo rayuwarsa a matsayin matar wata uku dan kawai Ya mallaki project d’in da yai niyyan tarwatsa mahaifinsa dashi. Ya lumshe idanunsa a hankali yana furzar da huci.
Shigowa Ummul Tai rik’eda kofin coffee da ya buk’ata a hannunta. Ta mik’a masa cikeda risinawa.
Ya amsa yana mata godiya. Sai ya nuna mata gefensa “Come sit here... let’s talk.”
Haka kurum taji gabanta ya fad’i sai ta d’an girgiza kai kad’an “Magana kuma.?”
Haidar ya jinjina Kai bayan ya sipping coffee din “Kar ki damu yau magana zamuyi ba akan kowa ko komai ba... Magana ce akanmu.. Let’s talk.. about us.” Ya k’arashe yana kashe mata ido d’aya gajeren murmushi saman fuskarsa.
Bugun zuciyarta Ya dan karu musamman da taga yanda yake binta da kallo. sai ta k’arasa a d’an sanyaye ta zauna a yanda Ya nuna matan.
Dak’ik’ai suka d’an shige kafin Haidar Ya aje coffee din dake hannunsa bisa teburin gefensa. Ya gyara zamansa Ya karkato sosai yana facing dinta gwiwarsu na gogar juna.
Sai ta d’an sadda idonta kad’an ganin irin yanda ya tsareta. Hannayensa ya d’aura saman nata dake bisa laps dinta.
Ummul ta dubi hannayensa da Ya d’aura bisa nata dake bisa cinyarta. Sai ta d’ago ta dubesa a d’an sanyaye.
“Khairy..!” Ya ambace sunanta kaman yanda Yake kiranta.
“You came into my life to make it better.. You’ve changed all areas in my life..” Ta dube shi sai ta dan murmusa “Bani nayi ba duka yin Allah ne..”
Ya jnjina kansa “Kece sanadi...” Yaci gaba da jinjina Kai hannayenta cikin nasa “I.. know there’s still a lot.. to do.. But you showed me the way Khairy..” You made me want to be a better son… You made me wanna wake up and reflect. You made me wann be.. a better business man, take my brand far.. And above all, you made me believe,.That I can be a better person. Thank you.. For coming into my life.” Ya k’arashe labarin na neman sauya direction.
Jiki a sanyaye ta soma k’ok’arin zame hannunta sabida zuciyarta dake bugawa cikin sauri.
“Dare yayi.. Ya kamata ka kwanta ka huta… Kaifa patient ne.”
Ya kamo waits dinta ya zaunarta saman laps d’insa. Cikin sigan rad’a yake fad’in “Wa yace miki ni patient ne har yanzu.? Bari ma na nuna miki na warke.”
Ta zaro ido tana k’ok’arin turasa “Kaga.. Ni tafiya ma zan..” Bata kai aya ba ya rufe bakinta da nasa.
SameenaAleeyou📚
