Amaal Bugun Zuciya page 4

Amaal Bugun Zuciya page 4

 

Amaal Bugun Zuciya page 4

*AMAAL*

*BUGUN ZUCIYATA ๐Ÿ’”*


*๐Ÿ’ซ๐ŸŒŸ Labarin soyayyane mai ban tausayi, tsoratarwa, fadakarwa,  tunatarwa da kuma nishadantarwa ๐ŸŒŸ๐Ÿ’ซ**๐Ÿฆ…๐Ÿฆ…WRITTEN BY FANDI๐Ÿฆ…๐Ÿฆ…*


*Da sunan Allah mai rahama mai jin Kai*


*FREE BOOK๐Ÿ˜ป๐Ÿ”ฅ*


*PAGE 4*

Wani dan saurayi da alama shine wanda ya bugeta da motar sa cikin sauri yazo ya tsayar da mai keke napep din... yace wa suraj bawan Allah in ba damuwa mu kaita Asibitin da motata, Suraj ya kallesa yace a'a ba damuwa zamuje a keke napep mai keke dan Allah muyi sauri jinin sai zuba yake! Yana magana yana mai cire dankwalin dake kanta, yana cirewa ya hau goge mata idanta da hancinta da jinin ya bata... Garkuwa hospital mai keken ya kawo su... Yana kokarin daukar ta Amaal ta farka ta rintse idanunta saboda ciwon da taji kanta na mata... Yace Alhamdulillah kin tashi sannuh bude idanunta tai ta kalleshi ta nuna masa kanta tace kaina kaina yana min ciwo... Yace munzo asibiti insha Allah zaki samu lfy zaki iya tafiya ko in kira Nurse's? Zan iya tafiya... Are you sure? ta gyada masa kai alamar eh tashi tai ya rike ta suka fara takawa har suka shiga cikin Asibitin wata nurse ce  ta hango su tai saurin zuwa ta rike mata hannu ta shiga da ita wani dan madaidaicin guri kamar daki, ta zaunar da ita akan dan karamin gado sannan ta dauko First aid box ta ciro auduga ta zuba Dettol kadan ta goge mata inda taji ciwo Amaal tasa kuka tace tabarshi haka ya isa, Nurse cikin tausayawa tace ki kwantar da hankalinki yanzu zamu gama... Gurin ta cigaba da treating  sannan ta shiga yi mata wasu tambayoyi, wasu Amaal ta bata amsa wasu kuma tayi shiru... tana gamawa ta tambayeta ko akwai inda ke mata ciwo? Amaal tace eh kanta na mata ciwo...  Bayan shifa? Inji Nurse, bb ta bata amsa a gajarce... Wayan sane yayi ringing yana dubawa yaga Abdallah yasa wayar a silent... Ya kalli Amaal yace sannuh... fita Nurse din tayi  bayan kamar minti biyu tazo tare da doctor tace ma. Nayi mata treating gurin saidai tace kanta na mata ciwo... Bayan shifa ba inda yake mata ciwo? Doctor ta tambayi Nurse tace eh... Ok sannuh baiwar Allah ษ—an tashi ki tafi gurin dustbin dinnan... Tashi tai da zummar zuwa gurin dustbin dinda likitar ta nuna mata amma sai taji  jiri da wata azabaษ“ษ“iyar ciwon kai... ku rikeni zan fadi ta fada cikin sanyin Muryar ta saurin riketa nurse din tayi... Doctor ta kalli suraj tace zamu kwantar da ita na kwana uk.. ahm doctor taji ciwo sosai ne amma kuma naga inda taji ciwon ba sosai bane, eh ba sosai bane zamu kwantar da itane sbd jirin da take ji da kuma ciwon dan idan muka sallameku a haka gsky zataji jiki sosai... Ok doctor ba damuwa kuyi duk abinda ya dace... 

Da taimakon nurse din yaje ya biya kudin komai... ya ciro  phone dinsa a aljihunsa dan duba time yaga miscalls din Abdallah da dad dinsa yayi sauri ya kira dad din nasa but is not reachable... sai ya kira  Abdallah yace hello Abdall... Wai ina ka shigane? tun dazun nake ta kiranka amma baka picking... wllhy accident mukai Amma banji ciwo ba sai wata da muke keke napep daya da ita shine na kawo ta asibiti... Sbhnllhy ya sunan asibitin? Bansan sunan saba... ka tambayi wasu su fada maka sunan asibitin gani nan zuwa na daukeka kamin test ok ya fada ya katse wayar wani ya tambaya ya fada masa sunan asibitin sannan ya turawa Abdallah text kamar yanda ya fada...

Bayan ya tura masa test ya fita dan yaje yayi alwala yayi Sallah sai yaga me keke napep dinda ya kawo su ya dafe kai yace dan girman Allah bawan Allah kayi hkr wllhy gaba daya na manta kana kirana... Ya ciro 3k ya basa me napep yace ai kudin ku ko dubu daya bai kaiba eh nasani ka rike saboda bata ma lokaci da nai... Godiya me keke yai masa sannan ya shige cikin napep dinsa har zai wuce ya tsaya ya bawa suraj takalmin Amaal da school bag dinta karba yayi ya masa godiya sannan ya shige cikin Asibitin ba tare da yayi sallahr ba... Koda ya shiga ya tarar da ansa mata drip ta kwanta tana bacci... Ajiye mata kayan ta yayi sannan ya daga kiran da Abdallah ke masa yace Suraj ka fito Ina bakin asibitin... Fitowa yayi  Abdallah ya masa hon ya karasa inda yake... Ya bude motar ya shiga, suraj yace ya naga kamar kana cikin damuwa? A'a lfy nake gajiyan aikine muje in ganta mu wuce gida... No ni ba yanzu zan tafi ba saboda ko yan gidan su basu san halin da take ciki ba... Kamar ya basu san halinda take ciki ba? Bangane ba! Eh toh bata bada numbern gidan su ankira an sanar dasu halin da take ciki ba... Kuma kaga bai kamata na tafi na barta ba... goge zufa Abdallah yayi yace kasan me?  A'a... Bacci take ko idanta biyu? Bacci takeyi.... ok bari na baka paper da pen ka rubuta contact Dinka da sunan ka idan mun  shiga sai ka aje mata mu wuce gida idan ana bukatar wani abu in tafarka sai ta kiraka... Abdallah akwai wani abin da yake faruwa ne? A'a nace ma babu kawai gajiyace... Abdallah amma kamar yanayin ka ya nuna kana cikin damuwa... Bude kofar motar Abdallah yayi ya fita ba tare da bashi amsar tambayar saba... Koda suraj yaga haka sai shima ya fita daga motar yabi bayan Abdallah... Nurse dinda tayi treating Amaal Suraj ya sama yace mata zaije gida ya fadawa iyayen su dan yana da kiran layinsu baya shiga ga contact dinshi idan ana bukatar wani abu... Nurse din tace dan Allah karka dade ka jamin matsala to ngd inji sa... Basu shiga dakin da take ba suka juya  suka fita daga Asibitin✍๐Ÿผ


Shin wanene SURAJ?


*ALKALAMIN FANDI CE✍๐Ÿผ๐Ÿฆ…*


07066554340

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post