Alkawarin Allah page 1&2

Alkawarin Allah page 1&2

Alkwarin Allah page 1&2

ALKAWARIN ALLAH

Na

HUGUMA

0️⃣1️⃣


        "Allah ya taimakeki" lafazin da ya shiga kunnenta kenan,lafazin da a bakin mutum daya take jinsa,furucin da ko mutuwa tayi ta dawo bata jin zata kasa tantance daga bakin wanda yake fitowa dare da rana,a hankali ta waiwaya fuskarta qunshe da murmushi,yana tsaye daga bayanta kamar koda yaushe,wannan annurin data saba gani kan fuskarshi kowanne lokaci na nan shimfide saman fuskarsa,kwarjini cikar zati da haiba cakude saman kyakkyawar fuskarsa,batasan me ya shigeta ba,sai taji bacin rai ya sauko mata a take,b'acin ran daya sanyata ta dinga ja da baya,ja da bayan daya zama silar data soma ganinshi dishi dishi,yana tsaye hannayenshi goye a k'irjinsa,dubanta yake ba tare daya tsaidata ko yace mata komai ba,saidai annurin fuskarshi ya ragu cikin kaso d'ari zuwa kaso ashirin cikin d'ari.        A firgice ta farka,sa'annan tayi zumbur ta miqe tayi zaman dirshan saman gadon nata,dukka hannayenta ta sanya ta dafe kanta dasu bayan ta dora gwiwar hannunta saman cinyoyinta,gashinta mai tsaho da sulbi ya sako ya rufe fuska da hannayen nata gaba daya,inda zaka ga fuskarta a sannan zazzafan hawaye ne ke layi saman kuncinta,inda ace tana da iko data hana kanta mafarkinsa,da ta isa data hanashi bayyana a duniyar mafarkinta,sam ko kusa ko alama bata da buqatarsa a duniyar mafarkinta kamar yadda bata da buqatarsa a zahiri

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" idan ka kasa kunnenka da kyau zakaji tana fada cikin muryar kuka.


      Ta jima cikin wannan yanayin kafin ta iya lallashin zuciyarta,kanta ta dago sannan ta sanya hannayenta guda biyu ta tattare gashinta baya ta daureshi,kyakkyawa kuma sassanyar fuskarta datayi jajur ta kuma tasa saboda kukan data yi ta fito fes duk da qarancin haske da d'akin keda shi,a hankali ta zuro qafafunta qasa sannan ta yunqura ta miqe,kai tsaye ta nufi wata qofa dake kallon gadonta ta murda ta shige.


     Mintuna biyar kyawawa tayi ta fito daure da alwala,ta bude ma'ajiyar kayanta ta fidda after dress da hijabi ta sanya,sannan ta nufi wani kebantaccen waje dake daura da gadonta tahau saman abun sallar dake shimfide a wajen ta kabbara sallah.


       Ita kanta batasan adadin lokutan data kashe zaune saman abun sallar ba,don sam bata marmarin sake komawa barcin da tayi mafarkinsa a ciki,saidai shi bacci ba wanda yafi qarfinsa,saboda haka sanda yazo yayi awan gaba da ita bata shiryawa hakan ba,sai jingina da tayi da jikin gadon,carbin hannunta kuma ya silale ya fadi nan saman dardumar.


 *******  ****   ********


       Qarfe takwas na safiya ta kammala shirinta tsaf,tsaye tayi kawai tayi gaban mudubin tana qarewa kanta kallo,tayi kyau iya kyau,irin kyan nan mai sanyi,saidai wasu abubuwa da suka soma mata yawo akai take suka d'auke duk wata sauran walwala da taketa yunqurin d'orawa fuskarta,qarar kira daya shigo wayarta yaso janye hankalinta,saita zubawa wayar dake gefan mudubin ido tana kallonta ba tare data tabata ba gudun zuciyarta na qaruwa,bata kuma da niyyar hakan ma gaba daya,har ta qaraci b'urarinta ta katse,tamkar mai jira kiran ya katse din kuwa tayi gaggawar surar wayar ta kasheta gaba daya sannan ta jawo locker din madubin ta jefata ta maidata ta rufe.


          Cikin kasala kamar wadda tayi wani babban aiki ta koma da baya ta zauna gefan gadonta tana ci gaba da kallon fuskarta cikin mudubi,ko kad'an bata qaunar ta raba wani abu ajikinta da zai sata tayi kyau,don dai kawai bata k'aunar bata ran anty zubaida ne,amma da bata ga dalili ko alfanun kasancewarta a haka ba.


       "Auntyyyyy...." Muryar huda ce ta ratsa kunnenta,firgigit tayi tana dubanta kafin ta samu qaqaro murmushi wa fuskarta

"Anty ina kwana"

"Lafiya huda ta,kin shirya kenan?" Ta furta tana janyo yarinyar kusa da ita tana gyara mata daurin jelar rigar makarantar dake jikinta

"Ummi tace ki fito karmu makara"

"Muje na gama ai,fitowa kawai xanyi" ta fada tana miqewa,ta qarasa ma'ajiyar jakankunanta ta ciro daya daga ciki da zata dace da shigarta,sannan ta dauko wata daban ta zuge,ta fiddo da tarkacen ciki ta maida wadda zata fitan da ita sannan ta kama hannun huda suka fice.


        A kitchen suka tadda  anty zubaida tsaye tana shirya lunch box din huda,sanye take da rigar bacci da qaramin hijabi,kallo daya anty zubaidan tayi mata ta karanci yanayin data shiga,don haka bayan sun gama gaisawa ta shigar da qorafinta

"Yauma kinyi halin ne?" Murmushi kawai tayi wanda ya fito da ciwo tun daga zuciyarta zuwa labbanta,maimakon ta amsata saita shigo da wata maganar

"Yanzu anty dan Allah ta yaya zanci gaba da kwanciya kina tashi kina girki bayan kula da uncle aby da kike?"

"In kinason komawa kitchen sai kiyo qoqarin maida mode dinki yadda yake....." Cikin seriouse ness ta waiwayo tana dubanta

"Cikin shekaru biyu mun soma yin nasara shahida....saidai bansan meke neman tarwatsa nasarar da muka samu muka yi ta tsahon shekara biyun ba" ta fada cikin nuna damuwa,shuru shahida tayi tana k'okarin kokawa da damuwar data taso mata,tun lokacin data san cewa suna rayuwa ne ashe cikin gari d'aya da anwar bata sake samun peace of mind ba,murmushin yaqe kawai ta jefi anty zubaida dashi,don bata son dukkan abinda zai sake jagula nutsuwar da take ta yunqurin samarwa kanta,shuru ne ya ratsa tsakani,ganin bata da niyyar magana anty zubaidan ta saki hannayenta tana dauko lunch boxs din huda ta miqa mata gami da cewa

"Shikenan,ku wuce ku karya karku makara,amma dai.....kota halin qaqa karki bari abinda ya riga ya gabata a rayuwarki ya bata future dinki,koda anwar ko babu ki baiwa kanki qwarin gwiwar xaki rayu,rayuwa mai inganci...."

"Zan rayu babu shi ne anty rayuwa mai inganci,babu batunshi ma cikin babin rayuwata" ta fada wani radadi na tasowa tun daga cikin zuciyarta har saman fuskarta,murmushin da ita kadai tasan ma'anarsa anty zubaida ta sako,shahida mutum ce me confidence,tana da qwarin gwiwa saidai har zuwa yau kaman hakan yaqi tasiri ga wannan lamarin,duk da koda yaushe tana yunquri da fadi tashin baiwa kanta wannan qwarin gwiwar,da idanu ta bisu har suka fice daga kitchen din ita da huda sannan ta saki ajiyar zuciya tana yiwa deejan addu'a a fili da zuciyarta.


        Suna gama karyawar abby ya fito,sanye yake da jallabiyya,mutum d'an kimanin shekara arba'in da takwas,mai cikar kamala da fara'a,cikin girmamawa shahida ta gaidashi,ya amsa fuskarsa qunshe da fara'a yana fadin

"Teacher uban karatu....baku wuce ba kenan?,hala yau keda dalibar taki tare zakusha bulalar latti" murmushi ta fidda,tana mamakin abbyn sau da dama,wuta ne shi a wasu lokutan,amma wani lokacin yafi xuma dad'i

"Yanzun nan zamu wuce abby" ta fadi tana sab'a jakarta

"Gwara kam,don qila hadi(mai adaidaitan dake kaisu makaranta)yana waje yana jiranku na sanshi da himma" dai dai sanda anty zubaida ta fito daga kitchen din sukayi mata sallama suka wuce.


        A bakin k'aton gate din   *NOOR INTERNATIONAL ACADEMY* ya saukesu

"Daganan zan kai adaidaitan wajen gyara....amma zanyi qoqari in sha Allahu na dawo na d'aukeku"

"Karka damu,yauma muna shirye shiryen wasu abubuwa da za'a gudanar a makarantar,ina zaton ma zamu d'ara lokacin tashi,zamu bi ta haya mu koma"

"To na gode,amma du da haka idan na gama akan lokaci zanzo" bata sake ce masa komai ba ta kama hannun huda suka ratsa gate din makarantar zuwa ciki.


       Dukansu ita da hudan sashen 'yan nursery da primary suka nufa,saboda a nan ne deejan ta zabama kanta ta koyar,duk da tarin ilimi da Allah ya bata,wanda tana da cikakkiyar damar da zatayi lacturing amma bisa wani dalili nata ta zabi koyarwa a qaramin mataki na 'yan nursery da primary,tun daga bakin section din yara ke gaidata cikin nuna qauna da soyayya,yayin da ita kuma take amsa musu cikin fara'a da jansu a jiki,sai da zata shiga staffroom sannan suka rabu da yaran,suka wuce azuzuwansu ita kuma ta shiga ofishin malamai.


        Office ne madaidaici mai girma da tsari,duk da girman office din su uku ne kacal a ciki,makaranta ce da kallon farko.idan kayi mata zakayi tsammanin private ce irin mai tsadar nan,saidai sam ba haka abun yake ba,makaranta ce da wani shahararren d'an kasuwa ya ginata saidai akwai sa'ido da kulawar gwamanti akanta,duk da cewa shike dauke da duk wani nauyi na makarantar,kama daga school unifoarm,littafan karatu,abincin da yaran zasuci na break da dai sauran dukkan wasu lalurori,aqidarshi ce haka,yakan gina makarantar a duk inda yaga hakan ya dace,ya kuma hada hannu da gwamnatin garin donta tayashi lura da makarantar,bawai lura na su bada wani abu ba,a'ah,tsarin gudanarwa tsaro da sauran abubuwan da ya kamata,kusan kowacce qasa dake africa ya gina makarantu d'aya,saidai a inda makarantun suka fi yawa a nigeria ne yankin arewa,duk dalibin dake karatu cikinta yana farinciki haka iyayensa farinciki da kasancewar dansu a cikinta,saboda ta tsaru da tsari mai kyau,hakanan tana da dukkan wani qualities da akeson makaranta dashi.


       Hidaya kawai ta samu cikin office din tana hada littafan dalibai da tayi marking,da alama tana da ajine qarfe takwas,murmushi suka yiwa junansu

"Kinso makara yau malama shahida"

"Yau da gobe hidaya...." Ta fada tana zaman kan kujerar teburinta.

"Sai Allah..." Hidayan ta qarasa mata kana ta gyara yafen mayafinta

"Mun tashi lpy...."cewar hidaya

"alhmdlh....mun godewa Allah"

"Ma sha Allah....zan wuce aji don Allah idan kausar ta iso kice mata ga kayan nan ta duba"

"Babu damuwa" cewar shahida,tana kallon hidaya ta bude office din ta fice sannan ta maida qofar ta rufe musu,saita maida kanta a hankali ta kwantar saman teburin dake gabanta,idanunta a lumshe,batason tuna komai,batason tunanin komai,tanason ta saita kanta kafin lokacin shigarta aji yayi,don nan da minti goma sha biyar periode dinta zai shiga.


***********************


     "Dukkanin takardun na cikin wannan file din,sauran takardun da za'ayi amfani dasu a d'akin taron ma gab suke da kammala,na shiga dakin buga takardun na musu magana sunce nan da mintina goma da izinin Allah....engine ne yaso basu matsala" mutumin d'an kimanin shekara arba'in dake zaune saman d'aya daga cikin qawatattun kujerun dake shirye a qayataccen office din ya fada,yana bayanin ne ga dogo kuma tsayayyen matashin dake tsaye tsakiyar office din yana kai kawo a hankali,hannunshi riqe da dan madaidaicin glass cup,yayin da d'aya hannun nasa yake riqe da wata zungureriyar takarda yana dubawa,sanye yake da suit masu azabar kyau da d'aukar idanu,wankan tarwada ne shi,dogo wanda ke tafe da tsaho da kuma 'yar qiba kadan,wadda kai tsaye ba zaka kirata da qiba ta zahiri ba saidai ace murjewar jiki,doguwar fuska gareshi wadda take cikakka,lumsassun idanu mai kama da wanda kejin bacci,saidai da girmansu idan ya budesu sosai aduk sanda yaso hakan,bashi da cikar gashin gira can,saidai gashin idanunshi a cike suke,siraran labba masu taushi,da qawataccen qasumba da aka gyarata aka rage mata yawa da fadi,ta zagaya ta hade da habarsa da kuma qasan hancinsa,kanshi saisaye ne wanda ya qawata fuskarshi saboda gyaran fuska da aka yi masa,kana kallonshi kasan tsafta hutu da iya dressing sun kama gida a wajensa,kana kallonshi kasan ba ma'abocin fara'a bane,sosai ya bada hankalinsa kacokam kan takardar hannunsa da gani kasan abune mai muhimmanci yake dubawa,yayin da ta wani b'angaren daban ya bada hankalinsa ga wanda ke masa bayanin

"Ina imran?"

"Yana sashen aje tsaffi da sabbin qarafa" kai ya gyada yana ci gaba da takawa sannu a hankali,har yanzu hankalinsa na kan takardar hannunsa

"Amma ba tuni na bada umarnin a cire wancan a sanya sabon da mukayo order ba?"

"Sorry sir.....engineer din ake dako,yaudai yayi alqawarin zuwa ya hada" ya fada cikin nuna tsantsar ladabi,bai sake cewa komai ba har na tsahon wasu mintina,sannan ya isa gaban teburinshi ya aje kofin hannunsa,ya taka zuwa gaban matashin dake zaune ya bude files din dake gabansa ya sanya takardar ciki ya rufe,sai a sannan ya dubeshi

"Karku wuce qarfe biyu ba'a gama kammala komai ba,bana son delay...."kafin ya gama fada qofar office din nashi dake aiki da lantarki ta bude da kanta,wanda hakan ke nuna muhimmin mutum ne zai shigo ciki,don ba kasafai take budewar da kanta ba sai bayan sakatariyarshi ta sanar masa ya bada umarni sannan ta bude din.


      Dukkansu maida idonsu sukayi kan qofar,tun kafin ta qarasa shigowa ya fahimci wacece,hakan ya sanya ya maida idanunsa kan yaqub,don bashi da tabbacin yanayin da zata shigo dashi,don haka ya sallameshi

"shikenan....zaka iya tafiya" a bakin qofar sukayi clashing da ita tana shigowa,cike da girmamawa ya rusuna yana miqa mata gaisuwa,kaman yadda aka saba haka ta amsa a daqile,cike da izza,shan qamshi taqama da isa,yaqub ya wuce ita kuma taci gaba da takowa cikin office din.


       Fuskarta qunshe da murmushi,hakanan idanunta na kan fuskarshi,taku take d'ai d'ai harta kusa cimmasa,yayin da shi kuma yake kallonta yana nazarin shigarta,babu laifi shigar tata tayau,doguwar riga ce mai wrapper,saidai kuma gajeran hannu ce,tayi rolling mayafi qarami a kanta,high hill ta saka a qafafunta,hannunta ba komai daga waya sai key din motarta

"It seems kamar bakayi farinciki da ganina ba M.A" ta fada a shagwabe tana kallonshi

"Uhummm....who told you?"

"Ba kowa....kawai yau nayi missing ganin cute face dinka,ka fita tun da sassafe ban samu ganinka ba,me yasa baka yi break fast ba yau a gida?" Takawa yayi zuwa d'aya daga cikin kujerun wajen yayiwa kanshi mazauni,itama yayi mata nuni da yatsa yana nufin ta zauna,sai data zauna sannan yace

"Me yasa zaki fito a irin wannan lokacin?" Farrr tayi da ido,tana jin wani dad'i na ratsata,a duk sanda ya nuna kulawa a gareta takanji babu ya ita a fadin duniya,sai data saki murmushi sannan tace

"Kai kadai na fito don na gani,kasan bazan iya wuni ban ganka ba" shuru yayi yana dubanta,can qasan ranshi yana jinjina wanne irin so nafisa ke masa?,kalamanta sunyi shigen kama da na wata,wadda ya soma qoqari da kokawar badda ta daga ranshi a yanzun da takeson taso mishi,don ko kusa bashi da sha'awar hakan,itama kallonshi take,tasan cewa wannan plan din nata ya d'anu,tanason dukkan wasu kalamai nata da yanayin kulawa yayi kama dana waccar da tasan ta taba wanzuwa cikin rayuwarshi,duk da tana baqinciki da cewa kwaikwayonta shine zai sama mata wani gurbi data dauki tsahon lokaci tana neman samu a zuciyarsa,duk da irin baqin fenti da qin jini da yayyabe tarihinta a zuciyarsa,amma duk da haka kishinta take fiye da komai a rayuwarta

"Naso na iso tun dazun sai aka samu akasi" ta katse kallon kallon da sukema juna,dan muskutawa yayi kadan,cikin muryarshi dake nuna halayyarshi yace

"Akasi?,name fa?" Sai data d'an jaa fasali sannan ta sake cewa

"Wallahi wasu 'yammata ne suka so yiwa motata b'arna..."

"Me ya gamoki dasu?" Ya tambayeta kai tsaye yana ci gaba da dubanta,kafad'a ta daga sannan tace

"No,karka damu,na musu uzuri saboda a make suke,kana ganinsu kasan sunsan sirrin shan syrup,har zan hadasu da police sai kuma na wuce don bai kamata na b'ata lokacina akansu ba" sexy eyes dinshi ya lumshe gaba dayansu,yana jin wani abu mai ciwo na sauka saman zuciyarshi kamar ana d'iga masa wuta,wani boyayyen murmushi ta saki sannan cikin shagwaba tace

"Karka damu nawan....ba abinda ya faru dani,am safe..." Bude idanun nasa yayi kaman zai kalleta saiya kalli wani sashe na daban,yana sauke ajiyar zuciya a boye,a duk sanda yaji ko yaga labari irin wannan babu wadda yake tunawa sai ita,hakanan haushi tsana da qyamarta yakan sake ninkuwa a ransa.


     "Yaya" ta kirashi tana son kauda damuwar data ziyarceshi,tunda haqarta ta cimma ruwa

"Yaune fa zamuje yaya?,don Allah karki sake cewa kana da wani uzurin"

"Saura minti goma sha biyar mu shiga meeting....saidai bayan mun kammala kuma" ya fada yana miqewa a hankali kai tsaye ya wuce bandakin dake cikin office din nashi ta bishi da idanu tana tantamarsa.


      A hankali ya tura qofar bandakin sannan ya maidata ya kulle,gaban dan fanfon dake maqale a bango mai hade da madubi dake manne a samanshi ya isa,yasa dukka hannayenshi ya dafe sink din tangaran dake qasan famfon,qirjinsa na zafi haka zuciyarshi,ya jima a haka kanshi a duqe yana kokawar maida yanayinsa yadda yake sannan ya dago yana duban kanshi a madubin kamar baisan halittar kansa ba saiyau,maganganu yake da zuciyarshi,magana yake gayawa kansa wanda shi kadai yasan meke kai kawo a ranshi harna tsahon wasu lokutta sannan ya zare 'yar samam suit dinshi ya daura alwala bayan ya tattare dogon hannun ta ciki,sai daya saka dan qaramin towel ya tsane ruwan jikinsa sannan ya maida rigar ya fito.


          Da sauri ta jiyo a firgice suka hada idanu dashi,tana tsaye gaban wani dan qaramin akwatinsa da ake budeshi da lambobin sirri,wanda ta budeshi ta kuma soma fiddo wasu kayayyaki dake ciki,dauke idonsa yayi daga kallonta ya maida kan d'an akwatin dake zaune dirshan daga can wani saqo na office din,baya taja cikin rawar murya muryarta can qasa tace

"Am sorry" baice mata uffan ya taka a hankali zuwa wajen,inda ta janye jikinta ta rabe a bango,ya durqusa ya dinga daukan kayan d'aya bayan d'aya yana maidasu muhallinsu,duk abu guda idan ya dauka yana jin kaman yana qarawa zuciyarsa nauyi ne.


      Har ya saka wani abu ya sake cirosu ya kalla,suna nan kamar yadda ta bashi su,hatta da ledarsu itace dai wadda ta qullesu a ciki,d last thing data bashi a tarayyarsu,da hanzari ya maidasu ya rufe sannan ya sauya lambobin sirrin ya miqe zuwa gaban teburinsa ya amsa wayar daketa burari,sai daya kammala a nutse sannan ya aje,ya kalli nafisa data tsarki kanta tare da ala wadai da shegen qwaqwqwafinta da yakeson ya bata mata dukka plan dinta

"Ki wuce gida,saina qaraso" daga haka ya soma diban wasu files,dai dai sanda P.A dinshi ya shigo suka soma yunqurin barin ofishin,hakan ya sanya dole tabi bayansu jiki a sanyaye,a wajen elevator suka rabu,su suka hau wadda zata kaisu third floor ita kuma tayi qasa don barin companyn.*GA MAI BUQATAR WANNAN LITTAFI ZAI BIYA NAIRA  KACAL 200 YA SAMESHI,WANDA KE BUQATAR DUKKA ZAFAFA BIYAR DUN KUWA ZAI SAMESU NE AKAN FARASHIN NAIRA 500*


πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DINπŸ‘‡πŸ‘‡_*2260792279

_MARYAM SANI_

_ZENITHBANK_


saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layinπŸ‘‡πŸ‘‡

*07067124863*


*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*πŸ‘‡πŸ‘‡

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuΙ—i gida masoyan asaliπŸ˜‰πŸ˜»πŸ₯°πŸ₯°πŸ˜πŸ˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ‘ŒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»_*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*


07067124863


*Ko kuma*


09032345899

ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING 

Ga Shafin kamar haka MASU GARI TV***

0️⃣2️⃣     Qarfe biyu na rana suka shigo gidan ita da huda,a falo suka tadda anty zubaida gabanta plate ne dauke da alala guda uku tana ci

"Wash" kadija ta fada tana zama saman kujerar dake falon,sannan ta zame dankwalin kanta don tasha iska,dogon gashinta da bashi da cika saboda santsi da tsahonsa ya bayyana

"Ina kuka jima haka yau?" Muskutawa shahida tayi,muryarta dauke da alamun gajiya tace

"Kin manta na gaya miki muna shirye shiryen ziyarar da mai makarantarmu zai kawo mana next week?"

"Af,na manta haka ne fa....amma da alama ba qaramin shiri kukewa zuwan nasa ba,ga dalibarku nan ta kasa zaune ta kasa tsaye" inji anty zubaida tana duban huda dake zare safarta tana dariya,yatsina fuska shahida tayi cike da qosawa

"Nima abun duk ya soma ginsata anty,duk sun d'aga hankalinsu duka malaman makarantar.....amma hakan qila baya rasa nasaba da halayyarsa,don a yadda kausar ke gayamin bashi da sauqi sam,kuskure kadan zai gani da bai masa ya dauki mataki,don bai qaunar abinda zai taba students din,last year yazo lokacin ban soma koyarwa a makarantar ba"

"To Allah ya taimaka yayi jagora...kece ma,da kin amshi aikin kamfaninsu abban huda da duk wannan jigilar kin huta da ita,har mota zasu baki kyauta saboda matakin da aka baki aiki akai yakai a bakin" murmushin gefan baki kawai tayi,sannan tayunqura ta miqe tana tattara mayafinta zuwa dankwalinta da jakar makarantarta

"Au....kinga naso na manta...nuraddin ya bada saqo,yayita kiran wayarki wai bai samu ba" cak shahida ta dakata da abinda take ba kuma tare data juyo ba,fitar furucin daga bakin anty zubaida zuwa kunnuwanta jinsu take kamar harbin bindiga

"Waima....ina kika aje wayarki?,nayita kira ni dinma ban sameki ba......anya shahida anya?,sai yaushe zaki saki ki koma dai dai?,saboda nuradden ne kika kashe wayarki?,nuradden kuwa deeja ya cancanci haka kuwa?" Batasan idanunta sun soma fidda hawayen da suka cikasu ba sai data ji saukarsu kan hannunta dake cukuikuye da mayafinta,kasa jure tsaiwa tayi saitayi gaba cikin sassarfa.


      Da kallo anty zubaida tabita harta bacewa ganinta sannan ta girgiza kai tana furta

"Allah ya kyauta" bata sake tankawa ba saita maida hankalinta kan alalanta da take ci.


     Ganin har huda ta gama komai shahidan bata sake ko leqowa ba,sai anty zubaida ta bawa hudan saqon tace ta shiga ta kai mata,sannan ta gaya mata ta fito taci abinci.


   Qarfe hudu na yammaci ta fito a shirye tsaf cikin doguwar riga abaya wadda ta wadatu da adon duwatsu,tayi rolling da wadataccen mayafinta,tayi kyau duk da babu ko digon hoda fuskarta bare akai ga kwalliya,hakanan idanunta tarwai suke babu kwalli ko d'aya a cikinsu.


    Ci gaba da kallonta anty zubaida tayi harta kammala tsakurar alalen sannan tace

"Zanje na dubo umma"

"Saikin dawo,Allah ya tsare,bari na baki saqo" ta fada tana miqewa zuwa cikin dakinta,mintina qalilan ta fito da leda ta miqa mata

"Gashi kikai mata" hannu biyu ta saka ta amsa sannan tayi mata sallama ta fice daga gidan,don 'yar rakiyar tata huda yau akwai islamiyya ta riga data wuce kuma,tilas ta wuce ita d'aya.


    A hankali take takawa zuwa bakin titi,jikinta a mace yake kamar yadda take jin zuciyarta sam babu wani qwarin gwiwa ko karsashi tattare da ita,tun daga can nesa ta hango shigowar motar,kallo d'aya tayi mata ta gane motar kota wace,hakan yasa ta sake tsananta d'aure girarta gami da kau da fuskarta tamkar bata ga motar ba.


      Ilai kuwa yana zuwa dab da ita ya rage saurin motar,saidai yadda ta dauke kai tare da qara saurin tafiyarshi ya hanashi damar ce mata komai,tana jinsa ya qara yin gaba,hakan ya nuna mata reverse zaije yayi ya dawo,don haka ta qara sauri,cikin sa'a ta cimma titi kafin ya juyo ta samu abun hawa ta shige ko waiwayenshi ma batayi ba bare ta san ya iso ko bai iso ba.


       Tsam tayi da ranta cikin abun hawan lokacin da yake sake kusantata da ainihin unguwarsu,wadda anan komai na rayuwarta ya samo asali,a nan duk wani babu na quncinta ya bude,anan komai ya wanzu ya kuma wakana cikin shafukan rayuwarta.


      Tafiyar mintina talatin suka iso,ya gangara da ita cikin layinsu kamar yadda ta saba aduk lokacin da tazo unguwar tasu bata sauka a titi saita dangana da qofar gidansu,kanta ta dauke gefe guda lokacin da sukazo gifta wani katafaren gida,bata maida kanta ga kallon gabanta ba har sai da suka isa qofar gidansu,sauka tayi ta sallami mai motar tana cusa kai cikin gidan gami da yin sallama.


       Fakadeden tsakar gidan nasu wanda ada can zamanin quruciya takejin babu wajen daya kaishi dadin xama da dadin yin wasa,kafin wasu murd'addun al'amura su zama silar da zaman tsakar gidan ya zame mata tamkar zama kusa da ramin maciji,babu kowa a tsakar gidan saidai a share yake sarai fes cikin tsafta da kulawa,batayi mamakin ganin babu kowa din ba don tasan a irin wannan lokacin saura qannenta na islamiyya.


       Daga falonta ta amsa mata sallama,shahida taci gaba da takawa har zuwa qofar falon ta sabule takalmanta ta shiga tana sake maimaita sallamarta.


       Cikin sanyi ta amsa mata kamar kowanne lokutta,wanda hakan kusan ya zame musu jiki ita da umman tata

"Yanzu kike tafe?" Umman tata ta fada cikin jin nauyin d'iyartata wanda har yau ya kasa barinta

"Wallahi umma,na manta yaune ranar da nake zuwa sai wajen uku na rana na tuna"

"Da kin bari sai gobe ai,tunda yamma tayi.....mubina ma ta riga da tayi wankin harsun bushe ta shanya,tunda taga rana ta soma baki zoba tace wataqila yau yaya ba zata samu zuwa ba"

"Me yasa?,da ta jirani ai ina kan hanya" gaida ummantata tayi ta amsa tana tambayarta anty zubaida huda da mai gidan,ta miqa mata saqon da anty zubaidan ta bata wanda itama batasan meye a ciki ba,bayan umma ta gama godiyarta ne kuma shuru ya biyo baya,shahida ce ta dinga qoqarin sako hira jefi jefi,ko kusa a yanzu batason yadda umman take qin sakewa da ita,kaman ba ummanta ba?,komai ya canza tsakaninsu tun shekarun baya da suka shude.


     Qarfe biyar ta shiga kitchen ta soma dorawa ummantata abincin dare da taga tana niyyar daurawa,ita kuma tana daga tsakar gida zaune kan tabarmar da suka shimfida,duk wani motsin rahama na kan idanunta,itama rahaman ta ankara da hakan saidai ta nuna bata kula ba,irin wannan kallon umman tata ta saba binta dashi da dadewa,kallon tausayi,kallon nadama,kallon kaicon biyewa son rai da son zuciya da sukayi ita da mahaifin rahama shekarun baya da suka shude,har hakan yaso jefa diyar tasu cikin hallaka,da tuni yanzu bayan shudewar mai gidan ita daya zata ci gaba da kurbar baqinciki da bacin ran abinda suka aikatawa rayuwar rahaman.


        Qarfe shida qannenta nata suka shigo,ta bisu da kallo sanda suke shigowar cikin jin dadi tare da musu addu'a cikin ranta,koda yaushe tana jin dadi har cikin ranta na yadda rayuwarsu ta banbanta da tata rayuwar a sanda take da shekaru kamar nasu,kallo daya zakayi musu kasan suna samun kulawa da tarbiyyar data dace,mubina ke bin rahama(shahida),sai khadija,faruq,sajid sai qaraminsu nasir.


     Dukkansu fuskarsu qunshe da walwala suka iskota,ta jima cikinsu yayin da mubina ta amshi aikin girkin,tana yi suna hira da yayarta da sauran qannunta.


      A nan kan qatuwar tabarmar suka ci gaba da zama,suka gabatar da sallar magariba,sannan mubina ta zuba abinci cikin babban tray.


    Gaba dayansu kowanne ya sanya hannunshi suka soma ci,suna hira lokaci lokaci,har cikin ranta tana jin dadin kasancewa cikin 'yan uwanta,saidai wannan kallo da duba da umma ke mata tana qaunar ya gushe daga idanunta,ta manta da faruwar komai,ya zama tarihi kamar ma bai taba faruwa ba.


     Sallamar usman d'an maqotansu shi ya katse hirar tasu,ya gaida ummansu sannan yace

"Ana sallama da anty shahida" hada idanu sukayi da umman,yayin da kowa abinda ke yawo a zuciyarsa ya tashi daban da na d'an uwanshi,qas da kanta shahida tayi tana kokawar hadiye lomar tuwon data riga ta saka abakinta,batakai ga hadiyewa ba saqon usman ya shiga kunnenta,sai taji gaba daya abincin bai mata dadi a bakinta,ya kuma gagara wucewar,hakan ya sanya ta miqe tsam ta isa bakin rariyarsu ta zubda tuwon sannan ta wuce dakin umman ba tare data bi takan aiken da akayo mata ba.


      Suya kawai qirjinta yake,waye wannan yakeson mata kutse ne cikin rayuwarta a sanda bata shiryawa hakan ba?,waye shi da zai tunkari rayuwarta a sanda bata da dukkan wani tsari akan kowanne d'a namiji?.


       Shigowar umma dakin shiya katse mata tunaninta,ta yunqura ta miqe ta zauna sosai daga kasalalliyar kwanciyar da tayi,wani mummunan tashin hankali ya ziyarceta sanda ta dubi idanun umman taga hawaye na biyo kuncinta,cikin matuqar rudewa da gigita tace

"Um....umma...hawaye fa kike umma meya sameki?,don Allah kibar kukan,kiyi shuru kice wani abu"

"Dole nayi kuka shahida....bazan daina kuka ba harsai sanda abinda yake damuna ya gushe,tashin hankalin da kika shiga kadai sanda aka aiko kiranki ya tabbatarmin akwai sauran rina akaba,kuma hakan ke nunamin cewa dafin da muka zuba a zuciyarki har yau bai gama wankewa ba" zamowa tayi daga saman kujerar tayi gurfane a gaban umman tata itama hawaye na sakko mata cikin tashin hankali

"Ko kad'an umma,kufa iyayena ne,kune kukayi silar zuwana duniya,umma....ba tun yauba na gayamiki ki goge duk wani abu daya faru daga ranki,ki daina alaqanta duk wani yanayi da zaki gani tattare dani da cewa laifinku ne"

"Indai kinason hakan ta faru shahida ki koma yadda kike....ki amshi wani cikin masu sonki kiyi aure,anwar bashi kadai bane namiji da don ya miki wani abu zai zama silar da zaki maida kanki wata aba daban ba,indai ina ci gaba da ganinki a haka baki sauraren kowa bare akai ga batun aure bazan daina zargar kaina ba har na koma ga mahaliccina,kamar yadda mahaifinki bai daina zargin kanshi ba har ya koma ga mahaliccin......" Maganar tata saita riqe,kuka sosai ya qwace mata,tana tuna abubuwa marasa dadi da suka faru a rayuwarsu,tana tuna komai tar cikin kwanyarta,qaruwar kukanta ya qara dasa tashin hankali a zuciyar shahida,wadda ta miqe ta figi mayafinta cikin rawar murya tace

"Zanje,zan fita umma indai hakan shi zai sanya farinciki da walwala a cikin zuciyarki" bata qara second guda ba tayi waje,kai tsaye kuma ba tare da saurarar komai ba ta wuce zuwa qofar gidansu.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post