Tun a farkon shigowa anguwar zaka shaida lallai ana biki, musamman da gidan da ake taron ya kasance shine na biyar a farkon shigowa layin.
Cike titin layin yake da yara da ƴammata harma da manya maza da mata. Musamman a cikin babban haraban massalacin dake manne da katafaran gidan da tun daga kallon gate ɗinsa zaka san ya wuce raini a gine da yalwar girma.
Rumfunane guda uku a tsaye, waɗanda gaba ɗayansu an cikasune da fararen kujeru bisa tsari. Rumfar farko cike take da manyan malamai masu faɗa aji a ƙasar dama wasu ƙasashen ƙetare musamman na musulmai. Rumfa ta biyu kuwa matane zalla a cikinta tundaga ƙanan har zuwa manya. Rumfa ta uku mazane suma manya da yara.
Babban abin birgewar da ƙayatarwar shine shigar kamala da mutunci dake tattare da jama’ar wajan. Duk da taron bikine kowa ya suturta jikinsa, babu wani mai shigar ALLAH wadai ta nuna tsiraicin da ake laɓewa da sunan biki.
Duk da cikar da wajen take da shi hakan bai hana yawaitar mutane a cikin gidanba shima. Lallai da gaske gidan babban gidane, dan a kallo ɗaya zaka fahimci gidan family house ne, dan kuwa yafi ƙarfin mallakar mutun guda kai tsaye. Daga jikin gate ɗin gidan zaka iya ganin dukkanin yawan ɓangarorin gidan da aƙalla zasu iya kai sashe biyar zuwa shidda, ginin iri ɗaya ne babu wani banbanci game kallo da ga nesa, saika shiga daga cikine ka fahimci kowa da kalar tsarin da yafi buƙata a nasa sashen.
Lokacine bana banbance minene a cikiba, ko mi aka tsara. dan haka nabi ayarin mutane masu kai kawo zuwa sashe na biyu da yafi ɗaukar jama’a. Kasancewar duk mutane na a harabar masallaci wajen da za’a gudanar da walima ya bani damar kutsa kai har cikin ɗakin da naji ana masa ishara da amarya na ciki.
Ƴammata ne da a ƙalla zasu kai goma zuwa sha a ciki, kowacce nata ƙoƙarin ƙimtsa jikinta dai-dai buƙatarta cikin doguwar riga milk color mai adon golden ɗin furanni da aka ƙawata da stones a gabanta da ƙarshen hannun. Hirarsu suke da dariya har baka iya jin mi wani yake faɗa.
“Oh ALLAH, Aure mai saka kowa hankali. Su o’e tunkan Yah Ab.. Yaci ƙaniyar bakin harya mutu haka?”. Ɗaya daga cikin ƴammatan dake naɗa ƙaramin golden veil a kanta ta faɗa tana ƙyalƙyalewa da dariya. Kusan a tare duk suka juya suna kallon wadda ke kwance saman gado ita kaɗai ta juya musu baya, kwance take rubda ciki da ɗaurin ƙirji sai ƙaramin hijjab a jikinta. “Hhhhh! Wlhy kuwa Iman, kinga dai bakin tsiwa tun jiya ya mutu”. Wata tabama mai maganar amsa tana dariya itama da ƙarasawa jikin gadon, yayinda suma sauran suke dariya suna nufar gadon. Sai da suka zagayeta sannan suka haɗa baki wajen faɗin “Gobe zata fashe!!!” tare da ƙyalƙyalewa da dariya suna tafawa.
Ƙaramin tsaki wadda ke zaune can gefen mirror tana kwalliya taja tare da taɓe baki, taɗan hararesu idanunta cike da ƙwalla, cike da fushi ta ajiye hodar da take shafawa ta fice daga ɗakin.
Bama susan tanayiba, dan sukam hankalinsu nakan amarya suna cigaba da mata ihun “Gobe zata fashe!! Gobe zata fashe!!!”. Faɗi suke da ihu sosai suna dariyar tsokana irinta ƙawen da ƙuruciya ke ɗawainiya da su, dan gaba ɗaya yarane ƙanana da bazasu wuce 16-17 ba.
Saurari Audio na littafin Saran BoyePart 1