Rubutaccen Al'amari page 1 - 3

Rubutaccen Al'amari page 1 - 3

 Rubutaccen Al'amari page 1 - 3

*A TRUE LIFE STORY*


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


 *RUBUTACCEN AL'AMARI*


           Page  1⃣

      

                 *NA*

       *AYSHA ALI GARKUWA*


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇Copied By


VISIT www.novelselite.com.ng For More Novel.


NOVELS ELITE is website consists of hausa novels note, the reason of launching this site is to Entetain, Motivate, Enlighten and Educate our readers.
We provided hausa novels of many type,  Such Adventure, love, romance, fiction, non-fiction, mystry, fantasy, action e.t.c from hausa Authors 
We provided a new and old novels both softcopy and hardcopy from our Author with thier permission.
 NOVELS ELITE shafin yanar gizo ne wanda yake ɗauke da littattafan hausa, dalilin bude wannan shafin shine domin Kayatar masu karatu da kuma ilimantar da su.
*Gargad'i! Gargad'i! Gargad'i! dan  Allah kar a juya mi wannan labarin tako wacce siga har sai an nemi izinina dan Allah ko harafin (A)  kar a canza min bana so*

*Ina mik'a sak'on Barka da sallah na ga d'aukacin  al'ummar musulmai baki d'aya Allahu rabbi ya amshi ibad'un da muka aikata Allah ya maimaita mana shekaru masu yawa da al'bakar wad'anda ke k'asa mai tsarki Allah ya dawo daku cikin lafiya*
*Alhamdulillah lillahi ala kulli halin na godewa Allah da ya bani rai da lafiya da nitsuba da konciyar hankali har na samu damar fara rubuta wannan littafi cikin k'oshin lafiya ya Allah ka bani iko da damar gama shi lafiya kamar yadda na fara lafiya Ameeen ya rabbil izzati*

Suna iso kan layin uguwar tasu Usman ya dafa kafad'un abokin shi Nura dake jan motar tasu cikin dan fidda ido yace.

"Kai Nuru tsaya a nan ba sai ka shiga cikin gidaba zan sauk'a a nan!."

Kai Nuru ya juyo tare da k'are mishi kallon sai kuma yayi murmushi ganin yadda Usman sarkin surutu ya wani zaro ido cikin murmushin yace.

"Kai Usman ni wallahi Hamma Umar mamaki yake bani ji yadda yake wani tsareka a gida kamar mace! ji yadda kake wani zaro ido dan kasan yanzu yana harabar gidan yana duba marasa lafiyan dake zuwa gunshi."


Shi dai Usman balle marfin motar yayi ya fita yana hararan Nuru tare da cewa.

"Ban za kawai lailamajanun duk ka zama majanuni akan mace sai dare yayi kazo kace in raka ka kakuwa sani sarai Hamma Farouq zai nemeni dan zai bani magani na."


Shi dai Nuru dariya yayi tare da jan motarsa ya tafi.


Shi kuwa Usman cikin sand'a da d'an d'aga k'afa da lek'e-lek'e ya shiga cikin gidan,

gaba d'aya hankalin shi na can gefen wasu yan bukkoki da akayi da ginin zamani sai samansu kuwa da akayiwa rufi da ciyawa suka fita kamar bukkokin rigar Fulani sai fulawowi masu kyau da suka zagaye harabar gidan da haske tako ina cikin bukkokin da sukafi kama dana shak'atawa wani farin matashi ne mai cikar haiba da tsurawa wanda yafi kama da laraba Dr Umar Faruoq kenan shine yake  zaune kan kujerun dake zagaye a bukkokin sai mutane kusan 8 dake zaune daga dukkan alamu sunzo ya duba lafiyar sune gaba d'aya hankalin shi na kansu.


Shiko Usman ganin haka yasa cikin sauri da d'an d'aga k'afa ya zille yayi cikin gidan,

kai tsaye Parlour Nenne ya nufa cikin yana yinsa na fara'a yayi sallama,

tare da shiga cikin Parlour yana ta haki da d'an zare ido.

Nenne ce ta fito daga cikin bedroom cikin sakin fuska tace.


"Usman daga ina haka kaketa zare ido?."


Dariya ya d'an yi tare da zamewa ya zauna gefen Ummul dake ta binshi da ido sai ya Adam da ya Sadik dake zaune a gafe duk sun zubawa Usman ido cikin murmushi Ummul tace.

"Mugun ne ya koroka ko ya Usman?."


Kai ya d'an juya cikin sauk'e ajiyan zuciya yace.


"Tab Nenne  Hamma Umar yazo ya nemeni ko.?"

Cikin sauri da salon tsokana ya Adam yace.

"Ehh yazo k'afa 3 yana neman ka."


Ido ya kuma d'an zarowa yace.

"Toh ni fa ba wani wuri naje ba!

kawai na d'an raka abokina Nuru zance gun budurwar sane,

kuma yanzu nasan Hamma Umar zaice yawo natafi ban sha maganina ba."


Dariya Nenne tayi cikin kula tace.

"A a baizo bafa Usman."


Shima dariya yayi cikin sauk'e ajiyan zuciya yace.

"Ummul me kika dafa mana me? Dan wallahi yunwa nikeji." 


Ya Sadik ne yace.

"A a saidai ta tashi ta dafa maka ko indomi ne dan miyar ganye tayi kai kuma kasan an hanaka ci."


Fuska ya d'an tsuke cikin badda zancen yace.

"Ummul kawomin zanci na yau kawai bazai min komai ba."


Nenne ce ta kalleshi cikin kula tace.

"A a fa Usman ka kiyaye dokokin Doctors ko dan samun lafiyar ka."


Baki ya kuma turawa yace.

"Wallani ni nagaji da wannan dokokin ace duk wani abu green bazan ciba,

dan Allah Nenne yau kawai kinji ko?."


Ita kam Nenne gaba d'aya take jin tausan Usman a ranta sabida ciwon dake tare dashi gashi yaro matashi .


Shi kuwa Usman cikin dariya ya kalli Ya Adam yace.

"Ya Adam kasan me Nuru yakeyi in munje gun babynshi?."


Murmushi ya Adam yayi tare da cewa.

"Inako zan sani sai ka fad'a min dai."


Ummul ce tayi carab tace.

"Ya Usman me yake yi?."


Hannu yasa ya kamo na Ummul d'in cikin yanayin shi na abin dariya yace.

"Jeki kawo min abinci zan baku labari."


"Toh" tace tare da haura saman d'an steps d'in da zai sadata da kitchen d'in sauri-sauri tasa mishi abincin a pilet sannan ta dawo parlour stol tajawo gaban shi ta ajiye mishi abincin cikin son jin zancen tace.

"Toh ga abin cin bamu labarin."


Murmushi yayi cikin raha ya mik'e tsaye tare da cewa.

"Nenne kina jiko kullum Nuru zaizo yace na rakashi zance amman sam in munje ba abinda yake sai shirme."


Ido ya Adam ya tsura mai cikin gimtse dariyar shi yace.

"Kamar yayafa?."

Dariya ya kuma tare da cewa.

"kuna jiko Nenne kullum in munje muna zuwa k'ofar gidan su  budurwar tashi sai Nuru ya kalle ni cikin in inarsan nan yace min k.. k.. kai Bosho k.. katsaya a cikin motar nan karka fito,

ni kuma sai nayi dariya nace toh ,

in an aika ta fito sai yace ta zauna kan motar ,

ita kuma sai ta wani d'ale  saman motar ta zauna tana kallon shi."

Ajiyan zuciya tayi tare da cewa.

"Hmmmm Nenne kin san me Ruk'ayyan  take ce masa?."


Su ya Adam kam da ya Sadik tuni sun fara dariya itama Ummul sai dariya take .

Ita ma Nenne murmushi take yi tare da girgiza kai alamar a,a.


Shi kuwa Usman cikin nuna musu abin a zahiri ya jawo hannun Ummul ya ajiyeta kan hannun kujera shi kuma ya matso gaban ta gab da ita ya d'an sa k'afarsa d'aya a gaba d'aya kuma ya maidata baya sannan ya rink'a d'an sunkuyawa yana d'an d'agowa kamar maiyin wazifa sai kuma ya kalli ya Sadik yace.

"Ya Sadik Kunga haka ko?,

wallahi haka Nuru yake tsayuwa a gaban ta kamar mai jin bacci yayi ta layi ita kuma sai tayi ta wani mishi murmushi kamar sokuwa."

Sai ya kuma kalli Nenne yace.

"Nenne kin san me take ce mata kuwa.?"


Cikin dariya tace.

"Me yake ce mata?."


Dariya yayi tare da koikoyar muryar Ruk'ayya budurwar Nurun  yace.

"sai tace ,Nuru ina sonka."


Sai kuma yayi dariya yace.

"Nenne ba tace masa Nuru  ina sonka ba?."


Cikin dariya Ummul tace.

"Ehh".


Shima dariya ya kumayi tare da cewa.

" shi  kuma soko sai ya kalleta murya can k'asa yace.

"Allah ya d'aiyiba."


Sai kuma suka rink'a dariya cikin dariya Usman yace.

"Kijifa Nenne wai Allah d'aiyiba sai kace wad'anda akayiwa haihuwa Allah ko Nuru yana bani dariya shi yasa nake son rakashi zance,

 kumafa kullum haka suke hirar tasu ,tace 

Nuru ina sonka shiko gogan yace,

 Allah d'aiyiba."


Gaba d'aya dariya suke shiko Usman yaja pilet d'in abincin ya fara ci kamar bashi ya basu dariyar ba.


Autan gidan ne Aliyu  ya kalleshi cikin sanyi yace.

"Ya Usman ba doctor ya hanaka cin duk wani abu green ba kuma kake cin miyar ganye kasan   fa Hamma Umar zaiyi fad'a."


Harara ya cillawa Aliyu tare da cewa.

"Toh sai dai in kaine zaka gaya mishi naci miyar dan nasan ka ka iya gulma."


Haka yaci gaba da cin abincin suna ta dariya da hira da raha.


Yana cikin cin abincin ya d'ago kanshi da sauri jin k'amshin turaren Hamma Umar na ratso hancin sa,

da sauri ya ture pilet d'in kasan kujara sai kuma yayi zuru-zuru da ido yana sauraron ta ina Dr Umar d'in zai shigo.


Shi kuwa Doctor Umar dama sarai yasan Usman baya cikin gidan kuma ya ganshi lokacin da ya shigo cikin gidan haka yasa yana gama sallaman marasa lafiyan kai tsaye part d'in su ya nufa wonka yake sonyi amman bazai iya zama har yayi wonka baije ya bawa Usman maganin shi ba hakan yasa ya d'auko magungunan tare da goran FARO a hannushi ya nufi cikin gidan.


Sallama yayi tare da tsayuwa a bak'in k'ofar yana jin suna ta hira da dariya bai shiga ba har sai da ya kuma sallama Nenne ta amsa mishi tare da bashi izinin shiga.Shi kuwa Usman tuni ya tonk'oshi kai yayi kalan tausayi .

Ummul kuwa mik'ewa tayi ta koma gefen Nenne dan jin muryar Hamma Umar d'in dan ta sanshi sarai yanzu zai samo laifin da zai turama .


Ya Adam da Ya Sadik kuwa Usman suka tsurawa ido.


Shi kuwa Dr Umar kan shi a sunkuye ya shiga cikin parlon cikin girmamawa ya gaida Nenne amsawa tayi fuska a sake tare da cewa.

"Umar bak'in naka duk sun tafi kenan?."


Murya can k'asa yace.

"Ehh"

dan shi baida rakad'i irin na Usman kuma baya da yawan surutu bashi kuma da shiga sabgar wani baya kuma wasa da yara kasan cewarshi shine babba a family nasu baki d'aya gashi da iya horon marasa jin magana.


Usman ya kafe da ido cikin tsuke fuska da yanayin tuhuma.


Shi kuwa Usman a hankali ya tashi ya matso gaban yayan nashi cikin ladabi da tsantsar k'aunar juna yace.

"Afwan Hamma Umar bazan sake ba."


Ido Hamma Umar ya kawar sannan yasa hannushi ya rok'k'oshi kan Usman tare da kamo kunnen shi ya d'an matse cikin yanayin hukun tawa.


Hannu Usman ya rink'a d'an yarfawa yana d'an k'ara tare da cewa.

"Hamma na natuba kayi hakuri bazan kuma zuwa yawo ba."


Sake mishi kunnen yayi sannan ya ajiyeshi kan kujera yana kallon fuskar sa,

Magungunan ya b'abb'allo sannan ya mik'a mishi,

hannu Usman yasa ya karb'a tare da afasu a bak'in sa yana mai yamutsa fuska,

shi kuwa Dr Umar goran ruwan FARON ya b'alle cikin kula yasawa Usman  bak'in goran a bak'in shi,

shiko Usman ido ya rumtse sannan ya had'iye magungunan nashi.


Murya can k'asa Umar yace.

"Kaci abinci?."

cikin sauri Usman yace.

"Eh Hamma naci."


Kai ya gyad'a sannan ya tattara magungunan tare da rufe goran ruwan ya juya ya kalli Nenne da ta zuba musu ido cikin tausayin su da mamakin irin kauna da kulawan da Umar yake bawa k'aninshi Usman.


A hankali Doctor Umar yace.

"Nenne sai da safe."

cikin kula Nenne tace

"Allah ya bamu al'heri Faruoq,

 Allah ya biya ka hidiman da kakeyi da d'an uwanka,

 Allah ya bashi lafiya."


"Amin ya rabbil izzati."


Yace tare da ficewa .

Kai tsaye Bedroom d'in su ya wuce wonka yayi tsab sai k'amshi yake zubawa yana fitowa yasa wonddon shi 3 qtr sai rigarshi Mara hannu  turare ya d'an fesa sannan ya jawo woyarshi da laptop d'in shi,

Usman ya kira,

Shi kuwa Usman tuni ya biyo bayan Hamman nashi ganin ya shi ga wonka ne ya dawo parlour ya zauna yana kallo,

ganin kiran Hamma Umar d'in nashi yasa ya mik'e da sauri ya nufi cikin bedroom d'in,

yana shiga gefen shi ya zauna cikin son juna suka kalli juna,

a hankali Dr Umar Faruoq yace.

"Na had'ama ruwan zafi kaje kayi wonka."


"Toh" yace tare da mik'ewa   ya dawo gaban Hamma Umar d'in ya tsuguna yana mai kallon shi da yana yin shi yake jira.


Shi kuwa Dr Umar laptop d'in nashi ya d'an ture gefe sannan yasa hannu ya b'abb'ale boturan jikin rigar Usman d'in,

yana gama bud'e mishi boturan Usman d'in ya mik'e ya cire rigarsa,

 sai kuma ya matso gaban Hamma Umar d'in ya tsaya ,

kai Hamma Umar ya girgiza tare da b'allewa Usman d'in beld'in dake k'ugunshi sannan ya d'an sunkuyo ya  fara kuncewa Usman d'in igiyoyin takalman shi.


Shi kuwa Usman sai kallon hannun d'an uwan nashi yake yi.


Yana gama kunce mishi ya kalleshi a hankali fuska a d'an tsuke yace.

"Wai kai Usman yaushe zaka koyi kula da kanka ne? ,

ace kana namiji baka iya d'aure igiyan takalmin ka da kuncewa ba  bel d'in jikin kama baka iya. mannashi ba hatta botur bazaka iya sawa da cirewa ba komai sai nayi maka randa bana kusa da kai kuma toh ya za kayi?."


Dariya yayi tare da shigewa toilet yana cewa.

"Hamma Umar ai ko Aure kayi tare zamu tare a gidan bazan bari kayi nesa da niba."


Shi dai Hamma Umar kai kawai ya jinjina tare da bin d'an uwanshi da kallo.


Bayan ya fito wonkan ne,

Umar ya had'a mishi tea sannan ya bashi ya sha,

yana gamawa ya konta gefen Hamma Umar d'in nashi  dake ta lallatsa laptop d'in shi.


A haka har zuwa d'an wani lokacin sanna Hamma Umar ya rufe laptop d'in tare da jawo blanket ya rufe Usman d'in cikin kula yace.

"B'iyaye na Usman kayi Addu'a kayi bacci kasan gobe ma akwai zuwa office ko?."


Fuska ya d'an tab'e tare da d'ago hannushi zai fara Addu'ar yace.

"aikin bankin ko aikin jaraba ni wallahi na gaji da aikin ma fa Hamma."


Ido ya d'an tsura mishi tare da tsuke fuska yace.

"Bacci fa nace muyi ba surutu ba ,

dan na lura kai kafi son zaman banza."


Addu'a sukayi sannan suka  konta baccin su.


2:00 Am Doctor Umar ya tashi yayi ta nafilfili tare da karatu k'ura'ani yana mai nemawa d'an uwanshi lafiya a gun mai bada lafiyar.


Haka yayi ta karatu sai da aka kira assalatu sannan ya tashi Usman suka tafi masallaci..


Bayan sun dawo masalla cin ne Doctor Umar ya d'an koma bacci bayan ya fitarwa Usman kayan aikin shi tare da had'a mishi ruwan wonka, 

yana konciya

lokacin d'aya bacci ya saceshi ,

shi kuwa Usman bai tasheshi ba dan sanin yau sai azahar zai tafi hospital d'in su.

wonka  yaje yayi sannan yazo ya kimtsa  ya saka kayan shi,

shiru yayi tare da kallon Hamma nashi sai kuma ya matso gaban Dr Umar Faruoq d'in cikin kallon fuskarsa yasa yatsunsa biyu ya matse hanc.........By 

*GARKUWAR FULANI*

📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


 *RUBATACCEN AL'AMARI*


            Page  2⃣


                   *NA*

   *AYSHA  ALI GARKUWA*


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇Ya d'an matse saman hancin shi kad'an tare da tsura mashi ido,

cikin bacci Hamma Umar Faruoq ya d'an bud'e ido jin an rik'e mishi hanci yasan ba maiyi mishi haka sai B'iyayen shi,

idon ya tsurawa Usman yana kallon fuskarsa da hannushi dake rik'e da net d'inshi,

a hankali ya mirgino bakin gadon yayi rufda ciki tare da zuro hannayen shi k'asa,

shi kuwa Usman k'afarshi ya turo kusa da hannayen Hamma Umar d'in.


A hankali Dr Umar Faruoq yasa hannu ya d'aurewa Usman igiyoyin takal man nashi sannan ya d'an d'ago hannushi ya manna mishi bel d'in shi,

shi kuwa Usman duk abinda Hamman nashi ke mishi binshi da ido yake yana jin k'aunar B'iyayen nashi har cikin ranshi,

yana gama manna mai bel d'in ya mik'e tsaye tare da kamo net d'in wuyan Usman d'in ya gyara mai zaman shi sannan ya kalleshi cikin  muryar bacci yace.

"zo kasha tea."

Kai ya gyad'a cikin sauri yabi bayan shi a parlour suka tsaya shi Dr Umar Faruoq ya had'awa Usman d'in tea tare da mik'a mishi cup d'in,

karb'a yayi yana d'an kurb'a yace.

"Hamma zan shiga cikin gida."


Kai ya gyad'a mishi ba tare da yayi magana ba,

shi kuwa Usman murmushi yayi ya fita ya nufu cikin gidan,

Usman d'in na fita shi kuwa ya mik'a a hankali yayi mik'a tare da yin salati cikin takun bacci ya nufi cikin d'akin da nufin ya koma baccin har ya konta idonshi ya haggo mishi magungunan Usman dake kan mirror daga duk kan alamu Usman baisha maganin ba hakan yasa  Faruoq d'in mik'ewa da sauri ya d'auki magungunan tare da fitowa parlour goran Faro ya d'auka ya fito ya nufi cikin gidan.


Shi kuwa Usman a part d'in kakarsu Hajjajo ya samesu suna zaune a parlorn ta suna ta hira,

 cikin yana yinsa na sakin fuska ya shiga hannun shi rik'e da cup d'in tea yana sha yana d'an lumshe ido,

yana shiga Hajjajo ta kalleshi cikin k'aunar jikan nata fuska dauke da murmushi tace.

"Usumanu ka fito ne."

har yakai cup d'in bakin shi ya cire tare da yi mata kallon kinafa bata min suna fuska ya d'an tsuke yace.

"Allah ko Hajjajo kina b'ata min suna wai Usumanu kice min Usman na kawai inbaza ki iyaba kibar kirana."


Murmushi tayi tare da cewa.

"Zo ka zauna kaci abinci."


"Toh" yace sannan ya matso kusa da Ya Adam hannu ya mik'a mishi suka gaisa sannan ya gaida ya Sadiq,

sannan ya juya zai k'arisa gaban Inna yazo dai-dai gaban Ummul khairi dake zaune kan hannun kujera sai ya tsaya ganin yadda ta karya wuya ta tsura mishi ido tana murmushi gaban ta ya matso dai-dai lokacin Nenne da Aliyu kuma suka shigo parlour,

ita kuwa Ummul kai ta k'ara d'agowa cikin koikoiyar muryar Ruk'ayya budurwar Nuru tace.

"Ya Usman ina son ka."

Murmushi yayi tare da k'ara matso ta ya tura k'afa d'aya gaba d'aya kuma ya maida shi baya ya d'an rink'a sonkuyowa kanta sannan ya koikoiyi muryar abokinshi Nuru yace.

"Allah d'aiyiba ."


Gaba d'aya su Nenne da ya Adam da ya Sadiq kam sai dariya suke Aliyu harda rik'e ciki Hajjajo kuwa sai binsu tayi da ido tana murmushi dan tasan shek'iyan cin Usman yawa ne dashi.


Shi kuwa Usman ko a jikin sa sai tea d'in shi yaci gaba da  sha,

Itama Ummul sai murmushi takeyi ta zauna gefen shi tana sa mishi abinci.


dai-dai lokacin Dr Umar Faruoq kuma yayi sallama duk da yana jin yadda suke ta dariya,

 yana shiga ya gaida Nenne ya Adam da Sadiq kuwa suka gaida shi,

gefen Hajjajo yaje ya zauna tare da tonk'oshe k'afafun shi kanshi a sunkuye yace.

"Hajjajo an tashi lfy."

Juyowa tayi tana fuskan tarshi tare da zubawa kekkyawar fuskar sa ido,

shi kuwa bai bita kan ta amsa mishi gaisuwar ba ya sunkuyar da kai yana b'allo magungunan Usman d'in.


Ido Hajjajo ta lumshe cikin k'aunar jikan nata da takeji tamkar ranta donko ya kasan ce shine jikanta na forko da ta fara mallaka uwa uba ga tsananin kamar da ya keyi da mahaifin shi gashi takwaran mijin tane hakan yasa take masa wani irin so mai tarin yawa gashi da halaiyar girma Doctor Umar  Ibrahim  Umar shuwa kenan.


Cikin kula tace.

"Umaru sanda kafi mata yanga Umaru kafi k'arfin kab'i mace sai dai ta bik'a Ummaru sanda mai k'amshin al'miski sanda babuga mai taimakon na gida da woje ,

Ummaru tsiyar ka rigima da mishkilanci  ko maganar ka tsada gareta."


Kanshi a k'asa ya d'an lumshe ido har ga Allah shi wannan halin nashi halittar sa ce haka Allah yayishi bai san ya zaiyi ya canza kanshi ba haka yake, a ranshi  yace.

"Ya zanyi da Rubutaccen al'amari haka Allah ya halicceni bazan iya canza kaina ba".


Ita kuwa Ummul tuni ta tsuke fuska dan sam bata jin Hamma Umar Faruoq d'in nasu kamar jinin ta haka kuma ya samo asali ne da yanayin halin Faruoq baida shiga harkar da ba tasaba bayi da yawan magana baya kuma son raini da hayaniya yana da girmama na sama dashi har ranshi kuma yake jin son y'an uwanshi a ranshi yana kuma kula da yanayin tarbiyar k'annen shi a matsayin shi na babban yaya,

 suma kuma suna son d'an uwansu sai Ummul ce da sam bata ko son su had'a inuwa d'aya da shi.


Tsuke fuska Ummul ta kuma yi jin yadda Hajjajo ke wani bashi kula ta musamman shiko ya wani shareta.


Su Adam da Sadiq da Aliyu da Usman sai murmushi sukeyi.


Shi kuwa yana gama b'allo maganin ya mik'awa Usman tare da bud'e mishi ruwan ya bashi yasha sannan ya had'a maganin wuri d'aya tare da mik'ewa ya fita a hankali  yana zuwa bakin kofar woyarshi ta fara tsuwa cikin wani sautin wak'ar India kaal hoh nan hoh sautin ne da ya kasan ce ko ba,a ga Umar Faruoq a wurin ba matukar akaji sautin toh tabbas yana kusa da wurin sauti mai cike da sanyi da tausayi.


A hankali ya fito a barandar Hajjajo ya koma gefen baya kad'an tare da zauna wa kan kujerun dake jere a wurin.


Woyarshi ya zaro a hankali yayi picking ya fara magana a hankali.


Su kuwa a parlour Usman ne ya mik'e tare da cewa.

"Nenne bari in tafi gwadago."


Murmushi ya Sadiq yayi tare da cewa.

"Tab ai kai kam aikin wuya kam baka cikin kai da zuciyar ka take rabi ai sai dai kaje back kana shan rab'a."


Hannun shi yasa ya d'an dafe k'irjin shi cikin lumshe ido yace.

"Da kenan ya Sadiq yanzu nayi lafiya zuciya ta kamar taka take ko buhu zan iya d'agawa."


Adam ne ya d'an kalleshi yace.

"Sai dai buhun kam amman damuwa da firgicin da zuk'atan mu zasu iya jurewa taka zuciyar bazata iya d'auka ba."


Murmushi sukayi baki d'aya ita kuwa Ummul maya finta ta gyara cikin fara'a tace.

"Yauwa ya Usman dama zanje gidan Anty Sadiya dan tunda akayi sallah ban jeba."


Hannu ya mik'a mata tare da cewa.

"Zomu tafi yar k'anwata zan kaiki."


Aliyu ne ya kalli Nenne da sauri yace.

"Nenne kina ji wai zata tafi gidan Anty Sadiya kuma batayi girkin ranaba."


Da sauri Nenne tace.

"Ehh haka nefa Autana kaga har na manta,

kai kam Usman tafi kawai abinka kar ka makara,

Ita Ummul sai tayi girkin rana."


Lokacin d'aya idanun Ummul suka ciko da k'ollah tib hannu ta rink'a yarfawa a hankali tana d'an buga k'afafun ta tare da yin kan Aliyu tana cewa.

"Ma gulmacin yaro dan munafurci Aliyu duk k'asa min ido a rayuwa ta shi yasa wallahi na gomma ce ina school ba mai takura wa rayuwa ta."


Sai ta kuma juyowa gun Nenne cikin muryar lallashi tace.

"Ayyah Nenne na kiyi hak'uri ki barni naje wallahi zan dawo da wuri inyi aikin dare."


Kai Nenne ta girgiza alamun bazata jeba.

Sai hawaye car-car a fuskarta.


Shi kuwa Aliyu dariya ya fara yi cikin jin dad'in ya d'ana mata tarko.


Kanshi tayi a fusace tana.

"Munafuki wallahi sai na dokeka."


Cikin dariya ya zille ya fara gudu ita kuma tana binshi a baya ta kasa kamashi.


Shiko Aliyu gudu yake tare da cewa.

"Yoh ai laifin ba nawa bane tunda bani nace duk randa kika dawo Hutu ko weekend kece zakina yin girki ba,

Hamma Umar Faruoq ne ya fad'a, kuma kice ni zaki daka, kije ki ce mishi bazakiyi girkin ba mana,

 ni me nawa a ciki?."


Kuka ta farayi tana binshi tana cewa.

"Ai shima mugun tace kawai ya hanani hutawa a rayuwa ta, ga masu aikin Amman don mugunta yace ni zanke yin girki mugu kawai mai bak'in hali."


Dariya Aliyu ya kuma yi harda yi mata gwalo yace.

"Shifa Hamma Umar yana tausayawa mijin da zaki aurane shi yasa yace ke zakina aikin ,

 don karkije baki iya girkiba,

 a ga laifin iyayenmu."


Binshi tayi da sauri shi kuma ya nufi woje da gudu yayi gefen da ya hoggo Hamma Umar d'in nasu yana gudu yana juyowa yana kallon ko ta kusa kamoshi.


Shi kuwa Dr Umar Faruoq tun da ya katse kiran woyan da yake yin,

 yake jiyo hayani yarsu shi Aliyu a hankali yake tsokanar ita kuwa Ummul sai mita da kuka take yana jin tana ta cewa Aliyu munafuki,

 Kalmar da baya k'aunar yaji an suffanta mutun da ita.


Ita kuwa sam bata lura da Hamma Umar d'in a wurin ba.


Shi kuwa Aliyu ya zo dai-dai gaban Hamma Umar d'in ya sule yayi wani irin mugun  fad'uwa a k'asan tayis,

 gum ya buge bak'in shi a take sai ga jini,

cikin wahala ya saki kuka mai k'arfi, wanda yasa su Nenne fitowa a guje.


Shi kuwa Hamma Umar da sauri ya mik'e ya d'ago Aliyu ranshi a b'ace ya kalli yadda bak'in yaron keta zubda jini,

ita kuma  tsayuwa tayi jikinta nata rawa ganin yadda jini yake zuba a bak'in k'anin nata ga wani irin mugun kallo da Hamma Umar ke watsa mata.


Ganin su Nenne sun fito tayi maza tayi bayan ya Usman dan shi kad'ai ne mai kareta su ya Adam ma kullum fad'a suke mata da biyewa Aliyu da takeyi tayi ta  jibagarsa.


Ita kam Nenne da sauri ta k'arisa gaban Dr Umar Faruoq da ya tallab'e hab'ar Aliyu cikin fad'a tace.

"Ummul zaki kashe min yaro a banza ga yadda kika fasa mishi baki akan zuwa uguwa."


Ita dai Ummul sai hawaye hannun Usman ta rik'e da k'arfi ganin Dr Umar Faruoq ya kirata da hannunshi cikin rawan murya tace.

"Ya Usman dan Allah ka bashi hak'uri wallahi bazan sake ba Allah ban san zai fad'iba."


A hankali Usman yace.

"Hamma tace kayi hak'uri."


Fuska ya tsuke murya a fad'ace yace.

"Zo nan."


K'ara k'ak'k'ame hannun Usman tayi tana zubda k'olloh,

shi kuwa Usman hannushi yasa a hankali ya b'amb'areta a jikin shi cikin rad'a yace.

"In baki jeba zai k'ara hatsala kije ki k'arb'i hukun cinki."


Cikin zubda k'olloh tayi gaban shi a hankali take taku har zuwa gaban shi tana zuwa  ta durk'usa a gaban shi.


A hatsele yasa k'afa ya tureta tare da cewa,

" taso."

Da sauri ta mik'e ta tsaya a gaban shi.

Mari ya watsa mata cikin fad'a ya nunata da yatsa yace.

"Kika kuskura kika k'ara cewa wani munafuki wallahi sai na fasa miki baki,

 ke kullum bakya jin magana,

 kiyi ta munafurta mutane kuma kece mai halin muna fukan,

 kalli yadda kike kuka tun ba'a tab'aki ba, ko shi da kika fasawa bak'in baiyi wannan kukan ba,

kuma kiji daga baki na ba inda zaki je sai shegen son yawo."


Sai ya kuma watsa mata mari tare da cewa.

"Ki wuce kiyi cikin gida ki fara akin ki tun wuri."


Baki na rawa tace.

"Toh"


Ta fice ta tafi tana kuka Usman ne yabi bayan ta da sauri yana lallashin ta har saida ta d'an huce ya kalleta cikin kulawa yace.

"Allah ya d'aiyiba."

Murmushi tayi tare da cewa.

"Ya Usman Ina sonka." 

fuskarta ya shafa tare da koikoiyan muryar Nuru yace.

"Allah ya d'aiyiba


Dariya sukayi baki d'aya sannan ya fice ya tafi.


Hajjajo kuma da Nenne da su ya Adam parlour Nenne suka bita,

 Nenne da su ya Adam fad'a suke mata,

ita kuwa hajjajo lallashinta take yi.


Shi kuwa Dr  Umar Faruoq yana rik'e da hannun Aliyu har suka shiga parlour su,

 kan kujera ya kontar da Aliyu dressing na wurin yayi mishi tare da bashi maganin ya sha,

sannan ya kunna mishi A,C da TV.


 a hankali Aliyu ya rink'a sauk'e ajiyan zuciya tare da lumshe ido, 

lokacin d'aya yayi bacci,

shi kuwa Dr Umar Faruoq wonka yayi tare da kimtsawa ciki shigarsu irin ta manyan doctors sai k'amshi yake zubawa ya fito ya nufi katafaren chemist d'inshi  mai suna Baba aura chemist  dayake kusa dasu,

yana zuwa dai-dai bakin wurin yayi wani irin.......By

*GARKUWAR FULANI*

📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


 *RUBUTACCEN AL'AMARI*


              Page  3⃣


                    *NA*

   *AYSHA  ALI GARKUWA*


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*Wannan shafi d'ugguruggum dinshi naki ne ke kad'ai Mamyn Najmah ina al'fahari dake ina sonki har cikin raina Allah ya bar zumunci ngd da k'aunar ki gareni 😘😍🤝*
*A*jiyan zuciya tare da lumshe ido,

ganin mutane da suke cike a harabar bakin chemist d'in mata da maza manya da yara,

cikin ranshi yake fad'in,

"Allah ya bashi ikion dubasu baki d'aya".

Fitowa yayi cikin nutsuwa ya nufi wurin da ya kasance wurin zaman shi a ko wacce rana matuk'ar dai ya shigo potiskum toh shi baya samun hutun weekend d'in.


Yana isa yaranshi da ke aiki chemist d'in suka yi mishi barka da safiya,

sannan ya zauna ya fara duba marasa lafiyan d'aya bayan d'aya yana mai basu kulawa yadda ya kamata duk da ba sakin fuska yake yiba amman a fili za'a gane fuskarsa mai ciki da tausayi ne da jink'an marasa lafiyan,

 dan bashi da surutu maganar sa a k'aiyade take .


Haka ya yayi ta dubasu har zuwa azahar daga nanne ya tashi tare da sa yaran nashi suka rufe chemists d'in sannan sukayi alwala suka nufi masallaci dan yin sallan a jam'i.


Bayan an idar da sallah su suka koma bakin aikin su shi kuma kai tsaye gida ya nufa dan gaba d'aya ya gaji ga yunwa ga baccin da yake ji.Ita kuwa Ummul bayan ta shiga kitchen ta fara aiki kenan ,

woyarta ta fara suwa tun kafin ta d'aga tasan waye ne dan sautin kiran kawai ke shaida mata Mustapha ne ke kiran ta haka yasa cikin shauk'i da k'aunar juna suka fara magana a woyar,

gas d'in ta kashe sannan ta fita cikin takunta mai cike da nitsuwa,

kai tsaye ta nufi part d'in kakarsu Hajjajo bedroom ta wuce tana zuwa ta d'ale kan gadon ta mai rumfa cikin sanyin muryar da ko kana gefen ta a kan gadon bazaka ji abin da take fad'i ba,

Ido ta lumshe cikin  sauk'e ajiyar zuciya tace.

"Habeebi"

"Na'am."

Yace mata tare da cewa.

"Ummul kina sani d'imuwa soyayyarki tana cazamin kai da jinin jikina k'ok'olwata na cushe in banji muryar ki na awa 3 ba Ummul ki daure ki soni ko rabin yadda nake sonki."


Ido ta kuma lumshe wa cikin hura mishi iska a kunne murya can k'asa tace.

"Ya Habeebi ka kontar da hankalin ka Ummul taka ce jiki da jini da duk wani motsina kana cikin raina ko bacci nake fuskar ka itace k'awan yata."


Mustapha kam k'ara sakewa yayi kan kujerar da yake konce gaba d'aya tsikar jikin shi yana mik'ewa lokaci d'aya kalaman ta suka sakar mai wani kasala da shauk'i k'aunar ta yakeji na ratsashi har cikin k'ahon zuciyarshi,

yayin da ita kuwa Ummul  take jin duk duniya ba yanayin da take so da jin dad'in shi kamar kasan cewa a haka suna musayan zantukan so masu sanyi,

ji take matuk'ar babu Mustapha a rayuwarta toh gani take kamar ba nunfashi tare da ita.


Haka sukaci gaba da soyewa kamar su shiga jikin juna,

ita kuwa Ummul gaba d'aya ta manta da wani batun girkin da aka sata,

haka yasa tayi ta woyarta sune basu katse hirar ba sai 12:23 pm tana katse kiran kuma bacci ya kwashe ta,

bata farka ba sai yanzu da taji muryar Hamma Umar a parlour HaJajjo.


Ita kuwa Nenne dama ta shiga mak'o tansu duba mara lafiya so batasan me Ummul tayi ba.

  *Asalin dengar takan su,   Zuriya d'aya ce duk su jikokin Alhaji Umaru shuwa'arab ne*Alhaji Umaru Shuwa'arab asalin sa shi da matarsa Rabi'atu Hajjajo kenan su Shuwa'arab ne asalin ma zauna garin patiskum cikin unguwar tudun wada yamma da fce,

kowa yasan shuwa'arab kyewawane kuma masu jin larabci ne,

Alhaji Umaru da Hajjajo  suna da yaran su 3 duk mazane babban d'ansu Alhaji Ibrahim Umar shuwa sai k'anneshi biyu tagwaye ne Hassan da Husaini sun tashi cikin gata da tsantsanr k'aunar juna,

 Alhaji Ibrahim shine babba kuma ya kasan ce mutun mai tausayi da k'aunar k'annenshi yana musu so mai tsanani,

iyayensu kuwa sun basu tarbiya mai inganci tare da ilimin addini da na zamani

sun tashi cikin tsabtacecciyar rayuwa,

da kulawar iyayen su bayan sun girma ne Alhaji Ibrahim yayi aure ya auri matarsa Amina ba fullatanar potiskum d'in,

 mace mai mutunci da kara da sanin ya ka mata,

bayan anyi auren bada jimawa ba Allah yayiwa Alhaji Umaru Shuwa rasuwa,

daga nan ragamar gidan ya zama a hannun Alhaji Ibrahim yake ya rik'e k'anneshi  da amana ya basu dukkan abinda uba zai bawa ya ranshi sunci gaba da karatu su .


Yana zaune da matarsa da mahaifiyar shi a gidan shi da k'annenshi baki d'aya,


Ranar da Alhaji Umaru Shuwa ya cika shekara d'aya da rasuwa a ranar Amina matar Alhaji Ibrahim ta haifi d'anta fari tas kekyawa dashi mai kama da babanshi,

ran suna yaro yaci sunan kakanshi Umar Faruoq kenan.


Yaro ya tashi cikin gata da kulawan mahaifiyar shi da kakarshi da k'annen mahaifinshi Hassan da Husaini,

yaro mai farin jini da kwarjini.


bayan shekara 4 Alhaji Ibrahim,   yayiwa k'annenshi Aure rana d'aya,

suka tare a gida jen da ya gina musu a gefen nashi.


Bayan watannni 5 da auren Khadija matar Hassan ta fara laulayin cikinta na fari a lokacin kuma Amina matar Alhaji Ibrahim itama tana da cikin d'anta na biyu,

matar Hussani kuma bata da ciki tukun ,

Bayan wani lokacin Amina matar Alhaji Ibrahim ta haifi d'anta na biyu mai suna Usman a lokacin Umar Faruoq kuwa ya cika shekara 5 da y'an watanni, Khadija matar Hassan kuma ta haifi d'anta  na fari mai suna Adam wanda tsaka ninshi da Usman kwana 12 ne Usman d'in ya girmi Adam da kwana 12 haka yaran suka tashi cikin shak'u da juna ko mai tare akeyi musu,

 Umar Faruoq ya tashi da k'aunar k'annenshi.


Usman da Adam suna da shekara d'aya a duniya Allah yayiwa Alhaji Ibrahim maifin Umar  da Usman rasuwa.


Rashuwa da ta shiga jikin Hassan da Hussain da Hajjajo sunyi kukan rashin d'an uwansu wanda shine madadin mahaifinsu a garesu.


Amina matar Alhaji Ibrahim mahaifiyar su Umar wacce yaran ke karanta da Ammi tayi kukan rashin mijinta da rabuwa da yaranta dan tana gama ta kaba ta koma gidan iyayen ta,

Alhaji Hassan wanda suke kira da Abba ya karb'i Umar da Usman ya dank'asu a hannun matarsa Khadija wacce yaran ke kira da Nenne sannan kakarsu Hajjajo itama tana gidan suka taru suka raini  yaran cikin kulawa da tsantsar gata ta yadda su Umar basu san zafin maraici ba.


Nenne kuma bayan ta haifi Adam ta kuma haihuwa yaran 4  Sadiq sai Sadiya sai Rabi'atu wacce take takwarar Hajjajo ce amman suna kiranta da Ummul khairi sai kuma d'an autanta  Aliyu.


Yaran sun tashi cikin k'aunar juna baka gane cewa Nenne ba ita ta haifi su Umar ba,

Sai dai kowa da halinsa dan shi Umar mishkili ne baya wasa da yara kuma kasan cewarsa shine babba a family d'in su yasa k'annenshi suna girmamashi

shi kanshi Umar yana jin haushin yadda yake halinshi, yayinda hakan ya jamishi kiyeyyah a uzuciyar Ummul ita kuma gani take yana takura rayuwarta a, zahiri Umar yana jin zafin yadda wasu lokutan ake gaza gane cewa wannan halin fa ba yin kanshi bane Allah ne ya halicce shi a hakan.

 

Sun tashi cikin gata da kulawa inda Umar a yanzu haka shi babban doctor ne yana d'aya daga cikin yerdeddun governor damaturu shine doctor dake duba lafiyar governor nasu kuma shine babban doctor dake aiki a general hospital damaturu,

Usman kuwa shi accounter ne sai .


Sai 

Adam Airforce ne yanzu haka a Kaduna yake

sai in yazo ziyara.


Sai Sadiq shi kuma yana aiki a ministry of justice.


sai Halimatu Sadiya ita kuma nurse ce tana aiki anan cikin garin potiskum.


 Sai 

Ummul khairi ita kuma bayan ta gama primary school d'in ta aka jona mata secondary school GGC damaturu inda ta koma cikin damaturu da zama a cikin makaran ta,

yayin da shi kuwa Alhaji  Hassan Abban Ummul kenan shi yana aikine a offishin gwamna a damaturu hakan yasa Abba yana da gida a can inda yake zama yana aikin shi sai alhamis ya taho week end cikin garin patiskum d'in,

 hakan yasa idan anyi hutu Ummul takan zauna a gidan shi dake gidan jen maikata na ministry of works and housing dake gashua road damaturu dan  jira ya gama aikin sa sai su tafi tare su koma cikin potiskum tare.


A hakan ne wata rana Ummul ta fita ita da k'awayen ta suna d'an zagawa cikin uguwar,

anan  ta had'u da Mustapha  saurayin da suke soyayya a yanzu haka,

 shima yazo gun abokan shine a unguwar,

dan shi Mustapha gidan su na commissioners quarters  dake  Maiduguri road damaturu,

 haka sukayi ta soyeyya in sunyi hutu yana zuwa har gidan su  Ummul d'in dake potiskum,

Haka yasa 

 ya saba da ita ya saba da y'an uwanta suna yiwa juna so mai tsabta.


Shi kuwa Umar sosai ya zuba ido kan lamuran Ummul, gashi in Abba baya nan kusan shine uba a gidan,

 so yana tsanani sa mata ido dan kare tarbiyar ta ita kuwa hakan yasa ta k'ara tsanarsa da jin tsoronshi,

dan baya mata da sauk'i.


Usman kuwa mutun ne mai fara'a da sakin fuska yana watsa da kawo dan shi ko da Abba wasa yake mishi kamar kakanshi,

 haka yasa Usman ya kasance wani jigo na gidan in ya fita ko na awa d'aya ne sai anyita ceki yarshi,

 shi da Umar kuwa suna yiwa juna wani irin so mai tsanani Umar yana k'aunar Usman fiye da komai a rayuwarshi suna yawan kaiwa Amminsu ziyara a gidan kakannin su.


Usman tun yana k'arami ya tashi da ciwon zuciya mai tsanani inda Abba da Daddy Hussain in Abban kenan sukayi ta jin yarshi,

a haka abin tashi hankali da fari an gane cewa zuciyar Usman tana da d'an hujin dake sashi ciwon zuciya so anyi ta bashi kula,

amman kuma Usman na girma abin na k'aruwa haka yasa zuciyarshi ta zama ta tsage ,

dole aka fitar dashi Egypt so acan akayi mishi aikin tare da kulawar d'an uwanshi Umar Faruoq aikin da akayiwa Usman a cikin zuciyar shi aiki ne da yasa an bar wasu na'urori a cikin k'irjinshi d'an zuciyar tashi tayi  raunin da bazata iya harba jininshi ba sai da wannan na'uran  haka kuwa aka k'inda ya mishi dokokin aka hanashi cin duk wani abu green dan abubuwa green suna sa jinin d'an adam kauri shi kuwa zuciyarshi nada raunin harba tsinkekken jinima bare mai kauri sai na'urar ke iya harba jinin ,

haka duk bayan shekara 5  yake zuwa a canza na'urar,

ko kusa da kai Usman ya zauna zakaji yedde na'urarnan take aikin a jikin shi tana,

*cak-cak* yana harba amman sai ka matso kusa dashi sosai zakaji sautin a hankali.


Wannan larura da Usman yake da ita yasa gaba d'aya zuriyarsu suke tausayawa mishi duk wata kulawa suna bashi,

yayinda Umar Faruoq kuwa a duniya baida wata matsala sai  damuwar ciwon B'iyayen shi,

shi yasa duk wata kulawa ta duniya wacce uwa da una zasu bawa d'an su ya had'eta yana bawa k'aninshi Usman.


Ummul kuwa da Usman suna rayuwa tamkar abokai,

Anty Halima kuwa tana gidan mijin ta amman duk wata kulawa tana yiwa Ya Usman d'in nasu.


Ya Adam da Usman kuwa su tamkar tagwaye suke tunda dama kwana  12 Usman yake bawa Adam.


Ya Sadiq kuwa mutumin Hamma Umar ne.


Auta Aliyu kuwa abokin fad'an Ummul ce shima yanzu ya kusa gama secondary school d'in shi ita kuwa Ummul sune suka gama this year so yanzu tana gida ana  sama mata admission a FCE (T) potiskum  zatayi NCE d'in ta akan maths and computer.

toh fa a d'an wannan zaman da takeyi a gidanne take k'ara fuskantar takura fad'a da Umar ke mata hakan yasa ta k'ara tsanarshi.Haka Ita kuwa Ummul take da wani irin ciwon mara a duk lokacin da zatayi  al'adarta kasan cewar a makaran ta tafara ciwon cikin sai ba'a santa dashi sosai ba tana dai fad'a tana ciwon ciki amman Nenne bata san ciwon mai tsanani bane.....

*Tak'aitaccen labarisu kenan*Mun dawo kan labarin yanzu.Nenne na dawowa ta lek'a kitchen tana kiran Ummul tana fad'in.

"Ummul kin gama ne?."


Ido ta d'an zaro ganin ba abin da tayi a kitchen d'in cikin sauri ta fito parlour kan dinning table d'in ma ba komai agogo ta kalla da sauri ta fita ganin har 2:00 pm tayi.


Parlour Hajjajo ta nufa tana kiran Ummul d'in.

tana shiga Parlour ta kalli Umar Faruoq d'in cikin b'acin rai da fushi tace........

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post