*Page 18*
"Lubna Wai Mai hakane dan Allah dan Annabi so kike sai na kwanta jinya ko na kashe kaina kafin ki hakura"
Ya cigaba da jijjiga k'ofar daya dameni ma na kunna karatu a wayata bansan Mai yasa zuciyata ta k'ek'eshe ba mahfuz ganinsa na Yan mintina ma batamin rai yake abinda ko kusa bazan yarda ba shine yace zai tabani da sunan zai samu nutsuwa dani, bayan ya kwanta da Hadeeza da ita kanta bata San adadin mazan da suka nemeta Ina matarsa ta sunna ya tsallakeni ya tafi wajenta hmmm macen data Kama mijinta da laifin cin amanar irin na mahfuz kawai zata Gane mai nakeji a zuciyata,ko kishiya aka ma kana dadewa cikin Jin Haushin mijin ka ballantana Wai budurwa naja dogon tsaki na Kara gyara kwanciyata dan idan har zan tuna sai naji kamar a yanzu abin ya faru ina jinsa ya bar bugun k'ofar.
Bansan a Ina ya Kwanta ba har bacci yayi awon gaba dani.
Mahfuz
Yasan yayi wa Lubna laifi amma wulakanci da take Masa ya fara isarsa,ya bata hakurin yayi rarrashin yayi kukan,baisan Mai takeso yayi ba har rantse mata yayi akan ya rabu da Hadeeza duk abinda takeso zaiyi amma Sam Taki saurarensa k'arfi da yaji yake neman zaucewa rabonsa da wata ya mace tun lokacin daya sadu da Hadeeza,wata wajen biyu kenan da sati,tunda yayi aure,bai tab'a sati ba mace ba ko period lubna take takan Masa dabaru ya samu nutsuwa amma sai gashi Yana fama da matsanacin shaawa sai aukin Shan kanwa da yake,a dawowar nan da tayi ya d'auka zata barshi ya samu nutsuwa ko Yaya ne amma sai gashi ko ta kansa bata bi ba ta kulle k'ofar,ya balain saka Rai da samun nutsuwa da ita,Koda ya kwanta juyi kawai ya ringayi,yanda zai samu nutsuwa kawai yake nema, wajen daya ya Kara mik'ewa ya nufi d'akin Lubna ya hau bubugawa amma lubna ko kulashi batayi ba balle ma tasan ana kwankwasa sai gajiya yayi da bugun k'ofar ya koma dakinsa.
Hannunsa dafe a mararsa ya d'auko wayarsa shi kansa bai san dalilin dayasa ya dauko wayar ba.
Tsintar kansa yayi da shigar da lambar daya haddace a kansa ya hau Kira bugu daya yaji ta d'auka tare da Jan dogon ajiyar zuciya "MahfuZ Kaine ko mafarki nakeyi"?
Ta fada can kasan makoshi daya sa yaji ta kara daga Masa hankali Sam bai iya magana ba a ransa Yana tunanin dalilin dayasa ya kirata da bashida burin daya wuce ya yakiceta daga rayuwarsa amma a Yanzu gani yake tunda lubna taki sauraransa zai iya samun nutsuwa a wajen Hadeezan.
Cikin kukan kissa da shagwaba ta fara magana tana Jan numfashi Wanda hakan ya tilasta masa rub da ciki dan ji yayi kamar mararsa za ta fashe ba abinda yake dawo masa sai abinda ya shiga tsakaninsu a karshe, kafin ta bar gidan
Can kasan murya kamar Mara lafiya yace "Hadeeza banida nutsuwa kimin abinda zan samu na fitar da abinan dake marata pls"
Wani irin kuka ta saka mishi daya saka shi wawuro pillow ya kankame a kirjinsa,yanda Hadeeza keyi yasa shi imagination ya ringa wani irin abu,shima ya ringa yi gurnani kasa kasa,Hadeeza kuwa ta cigaba da zuba masa kuka dayasa cikin Yan mintuna ya fara vibrating dan Kamar Yana tare da Hadeezan haka yakeji.
(KUYI HAKURI BANSO
NAYI BAYANI DALLA DALLA KAMAR NAYI BATSA NIMA WANAN DIN KAMAR NAYI DIN NAKEJI🙂🙂)
Numfashi kawai yake mayarwa Yana Jin Hadeeza tana "Karka cutar da kanka ka cutar dani Mahfuz ka turo gidanmu muyi aure na ringa faranta maka nayi missing dinka mahfuz"
Sai daya dawo daidai yaji kamar ya rufe kansa da duka baiso Sam ya Kira Hadeezan ba duk da bata gama fita a ransa ba,amma bayajin zai iya aurenta,a yanzu yafisan ya samu ya rabu da ita cikin sauki,tunda dama bashida burin Kara Auren Lubna ta ishe shi rayuwa.
Bai san ma mai zai cewa Hadeeza ba dan lalura ce tasa ya Kira ta Kuma duk lubna ce ta jawo masa kashe wayarsa yayi gabad'aya batare da yacewa Hadeeza uffan ba.
Ya lumshe Idonsa dan sosai yaji shi sakayau kamar an cire masa nauyi a jiki.
A hankali ya fara tuno wayar da yayi da Hadeeza yanda ta ringa kuka Kamar suna tare da Sunan ita budurwa ce a Ina to koyo irin wadanan Abubuwan.
Dan lubna har yau bata iya nuna Masa wani abu idan Yana tarayya da ita Wai kunya takeji,sai da ya zaunar da ita ya nuna Mata hakan da zatayi ne zai saka yaji dadi,yasan tana Jin dadin tarayyarsu,a hakan ma ba sosai take iya yi ba,taya duk Hadeeza ta iya Abubuwan Nan,ya tuno ranar daya fara kusantarta,hadin kai ta bashi ba kadan ba,Taya ma zai soma aurenta,a yanzu ya riga da yasan ba a budurwa ya sameta ba Tama goge a harkar har Lubnar ma tafi ta gogewa,yasan a yanzu zata cigaba da addabarsa da waya gashi lubna ta dawo shi.yasan a duk ranar da lubna ta ga Hadeeza ta kirashi yasan komai zai fada mata ba yarda zatayi ba,Kiran nan daya mata duk lubna ce ta jawo Masa.
Haka yayi ta sake sake har bacci yayi awon gaba dashi ba dadewa ya hau mafarki da Hadeeza Wai a kwancen da yake ta shigo dakin da yake kwance har ya kwanta da ita, lubna ta fado d'akin da wuka a hannunta aguje tayo kansu ya farka a gigice.
Ganin mafarki yake yasa ya koma ya kwanta,ya zama dole yayi taka tsantsan dan a yanzu ma tsoron Lubnar yake.
Baccin da bai koma ba kenan har aka Kira sallah asuba ya Shiga toilet yayi wanka ya dauro alwala ya fito har zai kwankwasa wa Lubna Kuma ya fasa dan yasan tana tashi itama.
Lubna
Ina jinsa ya fita massallaci dan tun hudu na farka ban Kara komawa bacci ba sabida mumunan mafarkin da nayi wai Hadeeza ta shigo gidan ta window naje na rutsa ta a d'akin mahfuz,duk na dauka a gaske ne sai da na farka bansan Mai yasa Hadeeza ta tsaya min a rai ba,na balain tsanarta a dawowa nan da nayi so nake ko Yaya ne na kamashi ma Yana waya da Hadeeza a ranar sai mun rabu,nasan mace bata Isa ta tsallaka kaddararta ba,amma ko da mahfuz na da rabon Kara aure na gwammaci ya auri kowa Banda Hadeeza,a duk ranar daya auro Hadeeza na gama Zama dashi kenan har abada.
Wajen shidda naji shigowarsa sanin ranar asabar ne ba fita yake da wuri ba yasa na koma nayi kwanciyata.
Karar tv da na jiyo ya kunna yasa na san Yana palon na Kuma tuno tv nan yake kunnawa ya yaudareni na dauka Yana Palo Ashe yana can d'akin Hadeeza na cije lebbena dan takaici,Nima tuna Abubuwan Nan ma hawan jini yake neman doramin amma bansan ya Zan hana zuciyata tunawa ba.
Wajen karfe takwas na fada bandaki nayi wanka na fito na dan shafa Hoda da man lebbe sai parking da nayi, wani yellon doguwar Riga nasa da bai jemin har kasa ba ya kwanta a jikina sosai nayi kwalliya ne dan kaina ba dan wani mahfuz ba,ban fito daga d'akin ba sai da na yiwa mimi itama wankan na shiryata na sabota a kafadata na fito.
Ina bud'e kofa Muka hada Ido dashi Yana kwance a doguwar kujera sanye yake da farar jallabiya.
D'auke kaina nayi daga kallonsa na kwantar da mimi a 2 seater.
Nayi hanyar kitchen zanyi Masa komai amma bazan yarda ya tabani ba.
Sam banji shigowarsa ba sai ji nayi an rungumeni ta baya,so nake na fusge jikina daga nasa da sauri amma rukon da yamin ma bazan iya kwakwaran motsi ba yasa kansa a wuyana Yana "Haba Lubna haba matata shikenan mutum bazai yi kuskure a yafe mishi ba,kinsan halin da nake ciki kuwa nayi kewarki lubna dan Allah ki yafemin ya riga da ya wuce nasan nayi kuskure bazan sake ba ki manta da komai mu cigaba da rayuwar mu kamar da"
Duk maganar Nan da yake k'ok'ari kawai nake dan na fusge daga jikinsa,amma yaki bani damar sai wani lasar min dokin wuya yake, ada Yana min haka duk girman laifin da yamin sai na sauko amma bansan Mai yasa ko kad'an maganrsa bata shigeni ba,har idan Yana Sona bana Jin zai ci amanata nasan Mai yasa yake ta lallabani so yake kawai na barshi ya kwanta dani.
Tuni ya hau yamutsani.ya hadani da bango ya dagemin riga Sama ya hanani ma motsi idan ya kawo bakinsa bakina sai na cije shi.
Ganin ya dage gaske a kitchen yake san yamin dole yasa na handaka.dashi da balain k'arfi Ina "Dan Allah mallam rabu dani, Mahfuz Wai kana tunanin bayan abinda ya faru cikin sauki zan iya yarda dakai,taya zan yarda.da Kai bayan baka je kayi gwaji ka tabbatar da lafiyar ka ba"
"Lubna naje nayi gwaji fa kikace"?
"Eee kaje kayi gwaji nace dan bazan zauna ka shafamin cuta ba,tunda ita budurwar taka ba kai ka fara saninta ba,itama kanta bata san adadin mazan da suka nemeta ba to akan me zan bari ka tabani bakayi gwaji ba idan har kaga na bari ka tabani a gidanan wlh sai na tabbatar da lafiyarka"
"Lubna yanzu wulakanci naki har ya Kai haka zargina ma kike zan saka Miki cuta,shikenan dan shaidan ya rinjayeni nayi abinda zanyi sai kice Ina d'auke da cuta"
"Wnan kuma matsalarka ce kaje asibiti dan ka tabbatar da lafiyar ka dan kaima kasan budurwar ka karuwace zata iya yuwa tana da cuta"
Yanda idonsa ya Kada yayi ja yasa na tabbatar da yaji haushi ko a jikina na dauko doya na fara feraye wa ya gaji da tsayuwa a kitchen ya fice ya bani guri.
Ko kad'an banji a raina abinda nakeyi ba daidai bane ba
Har na gama soya doya da kwai na dafa Mana ruwan shayi.
Sai da na zuba nawa daban na Kai sauran palo,ban ganshi a palon ba.
Hakane yasa na samu waje na zauna na fara karyawa,har na gama ci bai fito ba dan Ina Jin motsinsa a d'aki.
Koda na gama ci wayata na d'auko ina lallatsawa naji motsin bude kofa ban daga kaina ba amma kamshin turarensa da naji yasa nagane wanka yayi,na dauka zaiyi zuciya yaki cin abincin ta gefen ido na ringa satar kallonsa ya zauna ya fara cin abincin.
Daga ni har shi ba wanda yayi wa wani magana har ya gama ci ya mik'e Yana "Ni Zan fita zanje gida daga nan zanje asibitin nayi gwajin kamar yanda Kika bukata idan har gwajin ne zai kwantar miki da hankali zanyi"
"Idan ma wajenta zaka je ba damuwata bace ba gwajin Kuma idan kayi dan lafiyarka ne ba nawa ba"
"Allah ya kyauta wanan halin da Kika tsiro dashi ba Mai kyau bane ba karki manta aljannarki na tafin kafata karki ringa daukar wa kanki zunubi lubna"
Wayata na cigaba da latsawa ya gama surutunsa ya fice ko fitar da yayi sai da naji kamar wajen Hadeezan za shi ni nasan mawuyancin abu ne ya rabu da ita,idan shi zai rabu da ita wanan mayyar yarinya bazata rabu dashi cikin sauki ba,a zaune da nake sai zuciyata take saka min sai ya biya ta wajenta ma ya ganta.
Mahfuz
Yana fita daga gida ya kunna wayarsa a fitar da yayi har layi yayi niyyar canzawa dan a yanzu baya san su samu sabani da lubna,yasan ya kirawa kansa ruwa jiya Kiran da yayi wa Hadeeza yanzu zata sake Sako shi agaba,wayar na kunnawa sai ga texes dinta yafi Goma a wayar Yana k'ok'arin bud'ewa ya karanta sai ga kiranta a wayarsa yasan zaa rina Kuma bazai dauka ba.
Hakane yasa ya saka wayar a silent ya jefa a aljihunsa, gidansu ya fara zuwa Koda ya gaida Ammi bata amsa gaisuwar da ya mata ba sai cewa tayi "ka dai rantse sai ka dawo da yarinya nan ko?ka rantse sai nayi azumin kaffara ka dage ban Isa da Kai ba ko"?
"Ammi dan Allah dan Annabi Mai lubna ta Miki da zafi haka ?Ammi ni.na mata laifi fa"
"Zaka ga mai ta min ba dai ka dawo da ita ba tom ka fara shirye shiryen aure dan wlh Tallahi sai ka Mata amarya idan bazata iya ba sai ta Kara gaba"
"Ammi banida halin Kara Aure yanzu ni lubna ta isheni rayuwa"
"Idan ma asiri ta maka zaka dawo hankalinka Zan nuna Mata na Isa da Kai ni na haifeka ba ita ta haifamin Kai ba MahfuZ ka fara shirye shiryen turawa gidansu yarinya Nan Hadeeza"
Gwallo Ido mahfuz yayi Yana "Ammi wlh bazan iya aurenta ba haba Ammi dan Allah ni bama nida niyyar aure"
"Bazaka iya aurenta ba amma zaka iya kaita gidanka ko toh wlh sai ka aureta mu zuba mugani"
Duk Yar muryar da mahfuz ya ringayi wa Ammi ko kulashi bata karayi ba haka ya mike ya bar gidan ransa a bace shi Kam rabonsa ma dayaji shi cikin kwanciya hankali da farinciki har ya manta.
Daga gidansu asibitin da suke zuwa yaje.
Da zuwansa ya fadawa likita gwajin da yake.so ayi.masa, Cikin awa daya aka Masa gwajin yasan bashida wani cuta ko Hadeezan ma bai zargi tana da wani cuta ba dama.
A hanyarsa ta komawa gida ya siyi layi Mai register ya saka a wayarsa ya cire tsohon layinsa dan yasan Yana kunna wayar Hadeeza zata kirashi.
Duk da yasan sai lubna ta fada Masa bakar magana haka ya tsinci Abubuwan da take so ya tafi dasu.
Wajen karfe uku ya Isa gidan.
Lubna
Nasan asabar ba office yake zuwa ba idan gidansu ne ma da asibiti yaci ace ya dawo,amma har na gama girkin rana Bai dawo ba,haka.kawai naringa Jin kila zance.yaje wajenta idona na zubawa agogo Ina kirga sakanni da mintoci,wajen karfe uku sai gashi ya shigo,ciki ciki na amsa sallamar da yayi Ina Jin idonsa a kaina.har ya samu waje ya zauna yana "Sannun ki da gida"
"Yauwa"
"Ammi tana gaisheki"
"Ina amsawa"
"Lubna naje asibiti nayi gwajin ga result din bana d'auke da kowane cuta"
"Toh yayi kyau"
"Ki karba ki gani Mana"
Ko kulashi banyi ba Ina jinsa ya saki murmushi Yana "ai duk ta Inda Kika biyomin daidai nake dake yau dai baki Isa ki gujemin ba sai kin bani hakkina lubna rabona dake fa tun ana washegari zaki haihu watan Mimi yanzu nawa ta tafi hudu fa"
"Rabonka Kuma da Hadeeza fa"?
"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Lubna Nagaji daga yau Kar na sake Jin sunan Hadeeza a bakinki wanan wane irin masifa ne Abu kad'an sai kice Hadeeza Abu kad'an sai kice Hadeeza ba dama nayi magana sai kin Kira sunanta"
"Da baka kawota gidanka ba Zan santa ne ai ba karya nayi ba da kake cewa rabona da Kai an dade.ai Naga Ina nan ka wuceni kaje wajen Hadeeza ai lokacin Ina da tsarki ko nawane baka marmari sai nata,dan haka.kaje wajenta ta cigaba da baka"
"Inaga dan banyi maganinki bane shiyasa kike kiramin sunan ta kafin na ankara ya iso wajena ya danne ni da k'arfi ya fara kokawar ciremin riga.
Karfinsa da nawa ba daya bane duk yanda naso na hanashi kasa wa nayi,haka ya hau jagwal gwalani,Yana dab da cimma burinsa na hau tuno abinda yamin da yanda ya binne kansa a kirjin Hadeeza "idan kasan Kai dan halak ne ka kyalleni idan Kuma ba dan halak bane Kai sai kayi amma inaso kasan ba abinda zakayi naji Dadi a raina bakin ka nake gani har yanzu Ina hango ka a kirjin Hadeeza
Tunda na fara magana ya tsaya cak Ina idda magana ya dagani idonsa yayi jajjur Kamar jini yace "Lubna ni dan halak ne Kuma Zan nuna Miki nidin dan halak ne"
Ya dauke gajeran wandonsa da sauri yayi hanyar d'aki....
Mg's cakes nd more
For the lovers of cake,Ina masu biki ko suna ko wani shagali na musamman ko dan jin dadinku da morewar ku ko kuma akwati kuke Shirin ansa zaku bayar matsayi tukwaici,tofa nesa tazo kusa domin kuwa zamu tabbatar mun fidda ku kunya mun kuma gamsar daku da hadaddun abubuwa kamar su,cake nd cupcakes,meat pie,fish roll da kuma egg rolls,to me ya rage muku ai kawai ku tuntube mu ta number nmu kamar haka 07067210195,08062991549 cika alkawari shine taken mu,adade anayi sai gaskiya
*WANAN NOVEL DIN NA KUDINE BIYA 500 zuwa 2029764071 first bank nafisa Nuhu sai a tura shaidar biya zuwa ga lambar Nan 08033719070 ko katin mtn mutanen Niger Airtel Kika min SHARING bansanki ba Allah Yana kallonki na barki dashi*
*Page 20*
Lubna
Koda na Kira Mummy na fada mata fitar da mahfuz yayi da girkin da na masa yaki ci cikin kuka na Kara da "mummy wlh mahfuz a yanzu baya sona hankalinsa ba'a kaina yake ba, shiyasa nace miki bazan dawo ba wlh dan biyan bukatarsa ya dawo dani, yau kwana biyu da dawowa gidansa har ya fara fita wajen budurwarsa wlh abinda na dauka a baya bazan iya dauka ba yanzu, tun daga lokacin da na kamashi da budurwarsa ya fice min a rai mai kaunarka bazai tab'a maka haka ba dan haka wlh mummy bazan iya zama ba zan hakura da aurensa yafimin alheri"
"Shikenan Lubna mijinki bazai fita ba sai kice zance yaje?wai wanan wane irin abune kinfi so tun kina karamarki a ringa kirga miki aure? Kin isa ki canja abinda ya faru ne? Idan kina haka zai goge abinda ya riga da ya farune?,shikenan dan kin kama shi da laifin cin amanarki duk wani motsi ko fita da zaiyi cin amanarki yake"? Lubna bazaki ki kwantar da hankalinki ba ko?bakya Jin magana ko?kinaso ki nuna ban Isa dake ba ko?to ki kashe auren naki tunda bazaki iya zama ba "
Kit naji ta kashe wayar.
Nabi wayar da kallo hawaye na zubo min mummy ta kasa fahimta ta ta kasa gane halin da nake ciki,duk abinan da mahfuz yamin taya zan iya mantawa da wuri,har na iya sakin jikina dashi,ko zan saki jikina dashi sai na tabbatar da rabuwarsa da Yar iskar budurwar sa da ni nasan bazai iya rabuwa da ita ba idan har yasan bazai iya rabuwa da ita ba ya aurota ya sakeni,dan bazan tab'a zama da Hadeeza da Sunan kishiyata ba,ko fitar da yayi ban yarda abinci yaje nema ba nasan wajen Hadeeza ya tafi,idan har Yana Sona dan nayi fushi akan abinda yamin,bai Kamata yayi fushi ba har yak'i cin abincina.
Haka bakin ciki ya cikemin zuciya Ina kallon agogo har tara ta wuce ko uwar abinci yaje ci yaci ace ya gama ci ya dawo idan ba wulakanci ba da Rana ai da yayi zuciya da abincin zuwa yayi ya dafa bai fita nema ba.
Tara da rabi na wucewa na mik'e naje na kulle k'ofar ba inda yaje sama da wajen Hadeeza dan me ya matsamin na dawo bayan Yana tare da ita.
Na dauki Mimi muka Shige daki muka kwanta ni kadai nasan bakin cikin da nake ciki,mahfuz ya Raina min hankali.
Ina kallon agogon har goma ta wuce da minti goma anan na yanke sai dai ya koma wajen Hadeeza ya kwana amma ko ya dawo bazan bude masa kofa ba Kuma sai ya bani takardar sakina ko yanaso ko bayaso gwara ya sakeni yaje ya karata,idan ya ga dama ya auri Hadeeza idan yaga dama ya kawota gidan ta zauna na dindin din wanan matsalarsa ce amma matsawar Ina amsa sunan matarsa ina zaune a gidanan wlh sai dai ya zabi Hadeeza ko zama dani tuna duk abinda nayiwa mahfuz daga lokacin da muka hadu zuwa na aure shi nayi hawaye ya hau zubomin,na tuna akwatin Aurena da ba kayan arziki ya zuba min ba haka kawayena sukayi tayi dani,ko damuwa banyi ba dan Ina kaunarsa,duk wani abu Kuma da nayi da mukayi Aure rabin hidimar mummy ke bani kudin dan duk wata inta dauki albashi haka take binmu da kudi ba iya ni kadai ba dani da Zainab dan tana d'aukar albashin da yawa gashi dagani sai zainab da yayata da nake bi.
haduwata da mahfuz yasa ban cigaba da karatu ba dan yace kishine dashi,haka nake zaune sai mummy ce ma take cemin na bari idan na haihu zata bani jari na kama Sana'a,ban tab'a b'atawa mahfuz rai da gangan ba,duk wani abu da nasan Mahfuz naso Ina iya k'ok'arina na Masa koda ni banaso amma sakayyar da mahfuz zaimin shine ya kawomin budurwarsa har gida ya munafirceni,ya fifitani akanta ya Kuma Sakani hidima da ita,dan Nagano shi nayi fushi shine zaiyi fushi shima,Mai amfanin zama da mahfuz, mutumin da hankalinsa ya koma kan budurwarsa da taki aurensa sabida bashida abin duniya,banma san Yana da rufin asiri ba sai da budurwarsa tazo gidan har ya iya bata Dubu ashirin kudin kitso da kunshi,har a yanzu dubu ashirin a dunkulle bai tab'a bani ba.
Na kara kallon agogon naga goma da minti talatin da biyar adaidai lokacin da naji bugun kofa na maida idona na rufe dan dagaske so nake ya kwana a waje idan gari ya waye yayi zuciya ya bani takardar saki na.
Duk bugun da yake Ina jinsa har Kiran da yake min a wayata da nasaka a silent.
Idona biyu bai fasa buga kofar da Kiran waya ba har daya na dare yayi.
Haushin karnuka kawai nake jiyowa a waje burina ma su cije shi buga kofar da naji ya daina na tsawon mintuna yasa na bud'e idona,wayata dake ta kawo haske na leka naga mummy ce take kirana,da sauri na mike zaune na daga wayar
"Lubna yanzu mijin naki Kika kulle a waje innalillahi wa Inna ilaihi rajiun dama haka kike a yanzu na tabbatar da kina da matsala a yanzu na yarda akwai mugayen Abubuwan da kikeyi dayasa yarinya nan ta d'auke masa hankali wlh idan baki so naci ubanki kije ki bud'e Masa kofar nan"
Kuka nasaka Ina k'ok'arin Magana ta kashe wayar.
Na duro daga kan gadon nayi waje a fusace na bud'e k'ofar na ja da baya Ina jiran ya shigo.
Sai daya dade kafin naji Yana kokawar shigowa da machine dinsa.
Ina tsaye har ya shigo fuskarsa a balain had'e,kamar yanda nima nawa yake a had'en.
Yana saukowa na fara shakar kamshin turaren Hadeeza daya saka kirjina wani irin bugawa na tabbata ko hauka nake ba'a hayyacina nake ba idan naji kamshin turaren Hadeeza nasani.
Dagaske mahfuz wajen Hadeeza yaje daga dawowa ta bai ma iya daga kafa na kwana biyu ba tunda na hanashi kaina gwara yaje wajenta ta bashi,nama bashi yaje wajenta ballantana yanzu da na hanashi.
Wani irin zafi naji kirjina namin daya kusanto wajen da nake tsaye a fusace ban bari ya karaso ba na daka tsalle na isa wajensa na cakumo wuyan rigarsa sosai yake kamshin turaren hadeeza
"Bani takardar sakina mahfuz na balain tsanarka cutar da kayimin Allah ya Isa ban yafe maka ba bani takarda sakina mahfuz"
Wani irin fincike hannuna yayi daga rukon da nayi masa cikin hucci yace "Ni kikayi wa laifi amma zaki zo ki cakumi wuyan riga na kice na sakeki"
"Mahfuz mai yasa ka dawo dani gidanan bayan kasan bazaka iya rayuwa ba Hadeeza ba? yau Zan kwana biyu da dawowa amma mahfuz har ka koma wajenta idan har kasan kana santa haka Mai yasa ka dage min na dawo"?
"Ke fa dama idan Kika tashi haukarki bakya lissafi da tunani ni nace miki wajen Hadeeza naje"?
"Ko baka fadamin ba mahfuz ga kamshin turaren ta nan a jikinka ga Jan baki nan a kwalar rigarka dan Allah bakaji kunya ba Mahfuz na tsaneka ka sakeni kaje ka aurota idan Kuma dawo da ita gidanan zakayi sai ka dawo da ita mahfuz amma ni lubna na gama zama dakai ka rubuta min takarda ta mahfuz wlh na gama aurenka"
Nace cikin ihun kuka tare da Kara cakumo rigarsa Mara gaskiya ko a ruwa yake gumi yakeyi Ina cewa Yana kamshin turaren Hadeeza ya hau zare Ido,gumi na tsatsafo masa ya jawo kwalar rigarsa ya hau dubawa bai kalleni ba ya runtsa idonsa na cigaba da jijjiga shi Ina ya sakeni
"Ki yarda dani ba wajen Hadeeza naje ba abokina ne ya fesa irin turarenta yarsa da na dauka yasa na goge janbakin bakinta"
"Kutumar uban abokinka da yarsa baka ma iya karya ba mahfuz,yaushe maza suka fara fesa turaren mata mahfuz bana kaunarka bana San ganinka idan baka so na tara.maka jamaa ka bani takardar sakina gobe da safe na bar.maka gidanan kaje kayi duk abinda kaga dama da Hadeeza"
"Lubna dan sakeni dan Allah dan annabi karki manta dare yayi mu Shiga ciki muyi magana"
"Bazan sake ka ba sai ka bani takarda ta mahfuz wlh dak'yar nake numfashi sabida ganinka da nakeyi mahfuz ka bani takardata"
"Lubna na rantse da Allah bazan iya sakinki ba Ina kaunarki dan Allah ki tsaya mu fahimci juna wlh indai Hadeeza ce zan rabu da ita wlh sabida na faranta miki rai na canja layin wayata yanzu ma na saka layin ne dan na kwafi lambobi dan Allah kiyi hakuri ki cikani"
"Mahfuz idan kaga na cikaka wlh ka furta kalmar saki a gareni mahfuz yau kwana daya da wuni duk abinda kayimin duk baka ga girmansa ba daga dawowa ta ka Kara koma Mata,Ina san da kake min yake mahfuz ka daina yaudarar kanka,Hadeeza kake so ba lubna ba dan haka Zan hutashe ka ka bani takarda ta ka aurota ko kuyi zaman daduron duk abinda ka yanke yayi daidai nidai ka sakeni"
"Toh ki cikani mu Shiga ciki na rubuta miki"
Da sauri na sake shi yayi hanyar palo da sauri nabi bayansa Ina Jin kamar na shako shi dagaske ba abinda nake burin gani sama da takardar sakina
Muna Shiga palon ya shige d'akina na bishi har d'akin da shigarsa ya daki ya duka a kasa duk wani abu da mahfuz zaiyi yanzu bakinsa nake gani,ba abinda zai fadamin da zai Shiga kunnena duk rokon nan da ya ringayi na dawo ashe na munafirci ne daga dawowa ta ya tafi wajen budurwa bazan zauna mahfuz ya saka min hawan jini ba,ban damu da durkusawan da yayi ba na hau dube duben inda Zan samu takarda da biro,drawers din dake gefen mudubi na nufa da sauri,na hau watso da tarkacen ciki jikina sai rawa yake tamkar yanda na kamashi da Hadeeza zuciyata ta ringa Kuna haka nakeji a yanzu dan Koda bangansu a taren ba kamshin turaren da yake da dan janbakin gefen wuyansa ya tabbatar min da wajenta yaje babu ma ja
"Lubna dan girman Allah ki nutsu muyi magana Lubna ko kasheni zakiyi bazan iya sakinki ba Ina kaunarki lubna wlh sanki bai tab'a raguwa a zuciyata ba daidai da second guda"
A zabure na jawo drawer na jefa masa cikin ihu Ina "Karya kake Yi mahfuz da kana sona bazaka ci amanata ba,da kana sona bazaka kawomin budurwarka har gida ka ringa kwanciya da ita,da kana sona bazaka fifita budurwarka a kaina ba Ina matarka ka wuceni ka barni a gida kaje wajenta dan kawai na hana ka kaina bayan duk abinda kamin mahfuz,kwana biyu da dawowa ka Kara koma mata Ina San yake anan ka fadamin mahfuz ka maidani shashasha ka wulakantani kaci mutuncina ka nunawa budurwar ka banida wani matsayi a wajenka har gidanku ka kaita mahfuz sabida tsananin san da kake mata duk abinan daka min ka dage na dawo daga dawowa ta ka Kara komawa wajenta,Mai na maka dana cancanci haka daga wajenka mahfuz,dame na rageka da ka fifita budurwarka a kaina laifi ne dan na soka na aureka har yanzu ba muyi shekara biyu ba mahfuz"
Kukan da yaci karfina yasa na kasa cigaba da magana sosai nake Jin ciwon abinda mahfuz yamin
Zafin da kirjina yakemin yasa na dafe kirjina da hannu biyu bansan lokacin daya iso ba sai ji nayi ya kamkameni cikin rawar murya Yana "Baki rageni da komai ba Lubna wlh duk abinda ya faru sharrin shaidan ne bansan Mai ya hau kaina ba Hadeeza shuuma yarinya ce bansan ya akayi ta ja raayina har na kawota ba wlh ba wai bana kaunarki bane Ina sanki wlh Allah kiyi hakuri ki yafemin ki bani dama na gyara kuskure na nayi alkawari duk abinda kikeso shi zanyi a gabanki zan karya layin Nan da Hadeeza ta sani dashi"
Rashin kwari yasa bama zan iya kwace kaina daga rukon da yamin ba kamshin turaren Hadeeza da nake Shak'a a jikinsa yasa nake Kara Jin zuciyata na zafi
"Wane irin kalamai ne baka min kafin na dawo ba wane irin ban hakuri ne baka bani ba kafin na dawo daga dawowata mahfuz ka koma gareta mahfuz ka daina wahalar dani kana wahalar da kanka ka sakeni kaje ka zauna da Hadeeza dan Allah ka daina azabtar dani ka rabu dani na bar Mata kai duniya da lahira"
"Bani naje wajenta ba lubna ita tazo ta sameni a wajen da naje cin abinci"
"Shine ta danneka ta maka fyade ko mahfuz"?
"Dan Allah kiyi hakuri Lubna ki tausaya min ki kwantar da hankalinki"
"Kwanciyar hankalina shine ka bani takardata dan bazan iya zama da fasiki ba"
"Toh naji ki kwanta gobe da safe sai na rubuta miki"
"Bazan iya kwanciya ba sai ka bani mahfuz babban burina ka bani takarda ta"
"Wlh Lubna Zan rabu da Hadeeza duk abinda kikeso wlh Allah zanyi na Miki na farko na Miki na karshe idan kin Kara kamani da ko waya Ina Yi da ita nayi Miki alkwarin Zan sakeki"
Haukace masa nayi akan lailai sai ya sakeni,ya dage da magiya kaina danajin Yana baranazar rabewa biyu yasa na samu waje a gefen gado na zauna,
Yana k'ok'arin nufoni na daka Masa tsawa akan ya fice min daga d'aki.
Ya fita da sauri na koma na kwanta
Banida burin da ya wuce garin Allah ya waye na hada kayana,mahfuz ya Saba da Hadeeza ko min daidaita bazai fasa nemanta ba banga amfanin zamana dashi ba.
Sam bacci bai ga idona ba sai wajen karfe hudu bacci yayi awon gaba dani.
Mahfuz
So yayi tana bude k'ofar ko bai dauketa da Mari ba zai jijjigata har shi zata kulle a waje , sam dabaran Kiran mahaifiyar lubna bai fado masa na sai dayaga dagaske Lunbna ta shiryawa ya kwana a wajen hakane yasa ya Kira Aunty nurse duk da bashida tabbacin zata dauki wayar ga mamakinsa a kira na biyu ta dauki wayar bayan ya gaisheta ya fada mata kulleshi da lubna tayi a waje a san ya kara Kare kansa yace Mata abinci ya tafi nema kafin ya dawo ta kulle tunda lubna ta dawo take masa rashin mutunci jiya ma koroso tayi daga d'akin,daga yanda take sallati yasan ta fusata hakuri ta bashi akan bari ta Kira lubna Yana zaune ba dadewa yaji an bud'e k'ofar.
Ransa a b'ace ya shiga gidan so yayi ya zubawa lubna rashin mutunci Yana parking ya doshi wajen da take tsaya ga mamakinsa kafin ya Isa wajenta ta iso wajensa tare da cakumar rigarsa tana ya bata takardar sakinta haka kawai yaji gabansa ya Fadi har ga Allah inta furta sakin nan sai yaji hankalinsa ya tashi
Dakewa yayi ya mata martanin ita ta Masa laifi amma itace zata ce ya saketa
Kamshin turaren Hadeeza data ce yanayi da Jan bakin da tace Yana kwalar rigarsa yasa gabansa faduwa ya Kai hancinsa jikinsa ya kuwa shako kamshin turaren Hadeeza ya kuma ga jan bakin da bai san garin yaya ta shafa Masa ba duk wani kwarin gwiwar daya shigo dashi ya sace wani irin kunya ya lullube shi bazai yi saurin shiru ba ko yayane gwara ya Kare kansa
Hakane yasa ya yanko mata karya
Amma baiga alamar karyarsa ta Shiga ba hakane yasa ya yanke bata hakuri duk hakurin da ya ringa bata haka ta ringa botsarewa akan dole ya fito daga d'akin ya shige nashi d'akin duk hankalinsa a tashe, idan har baiyi dagaske ba zai iya rasa lubna bai Kuma shirya rabuwa da ita ba lubna ta riga da ta Zama Rabin jikinsa baisan Mai yasa baya iya danne kansa akan Hadeeza ba,Sam baiyi niyyar komawa Hadeeza ba tunda bashida niyyar aurenta zafin da lubna ta hada masa yasa ya kirata a waya gashi turaren da ta fesa ya tona Masa asiri ya zama dole ya Kira mahaifiyar lubna ya fada mata abinda ke faruwa ya Kare kansa
Haka yayi ta sake sake sallah asuba akan idonsa,sai a lokacin ya Shiga bandaki yayi wanka ya daura alwala ya fito a hankali wai Kar ma Lubna taji motsinsa.
Ana iddar da Sallah ya fito daga massallaci ya samu waje ya zauna ya Kira Aunty nurse a waya Yana Kira ta d'auka bayan ya gaisheta cikin marairaicewa ya hau bata labarin abinda ke faruwa a tsakaninsa da lubna ya hada rantswar shi bai hadu da Hadeeza ba tazo ta taimaka Masa ta bawa lubna Baki ya rantse ya rabu da Hadeeza.
Aunty nurse kuwa ranta ya balain b'aci da abinda lubna tayi inda ta bawa mahfuz hakuri akan tana nan zuwa"
Sai a lokacin mahfuz ya samu kwanciyar hankali ya koma gida karfe bakwai daidai sai ga sallamar Aunty nurse.
Mahfuz har kasa ya duka ya gaisheta yayi kasa da murya yana "Dan Allah mama banaso ki mata fada sosai so nake ki kwantar mata da hankali ta daina furta kalmar saki mutuwa nakeso ta rabamu mama,wlh Ina kaunarta bansan Mai takeso nayi ba na riga da nayi kuskure na Bata hakuri amma ta dage sai na saketa wlh na rabu da yarinya nan mama bansan Mai lubna take so na mata ba
"Jeka kiramin ita"
"Wlh tsoron zuwa d'akin nake mama"
A fusace Aunty nurse ta mike tana a wane daki take
Mahfuz yayi sauri ya nuna Mata ta nufi d'akin lubnar da k'arfi ta tura k'ofar tayi Ido biyu da lubna dake zaune akan sallaya idonta ya kumbura gefenta ga akwatin kayanta
Lubna
Nayi matukar ganin mummy da sassafe yanda ta had'e rai nasan Mahfuz ne ya kirata,banason yanda Mahfuz ke neman hadani da mahaifiyata
A hankali na Mik'e nayi waje Dan muna hada Ido ta juya ko gaisuwar da na mata bata amsa ba ta rufeni da fada har tana k'ok'arin kawomin duka,da wane zanji kuka kawai nake idan Ina k'ok'arin Magana sai ta tareni,a karshe sai ta saka kuka akan batasan Mai yasa nakeson dora Mata hawan jini ba idan na Kara yiwa mahfuz ba daidai ba bata yafe min ba idan na kashe Aurena Kar nazo Mata gida.
Bata tsaya taji ta bakina ba ta mike da sauri tayi waje mahfuz ya mike ya bita a baya........
*Page 21*
A ganina mummy kawai ce zata iya gane halin da nake ciki mummy ta d'auka kishi ne yasa na kasa kwantar da hankalina,bana jin ko aure mahfuz zai Kara ko yayi zai jefani a cikin tsananin bakin ciki haka, tsanar mahfuz nake ji a kowane sassa na jikina yanzu mummy ce kawai nake ganin idan nayiwa bayanin halin da nake ciki zata karfafa min gwiwa tace na hakura da aurensa tunda har ya kasa rabuwa da budurwarsa bazai daina fasikanci ba mummy da ta barni nayi mata bayani abinda ya faru amma Sam taki saurarana,Allah ne yasan kalar karyar da mahfuz ya mata,da har zata min Allah ya isa idan ban kyautata masa ba har yaushe iyaye zasu gane gaskiya su daina danne yayansu akan su zauna a gidajen mazajen su Idan basajin dadin auren,akwai cutuwa a zamana da mahfuz,dan nasan bazan iya Kara Masa biyayya ba,zan tayin abun da zan jawowa kaina zunubi ne.
Ina nan a zaune hawaye na zubo min har Mahfuz ya dawo palon Yana satar kallona,Allah yasan ko ganinsa bansan yi balle har mu zauna waje daya.
Mik'ewa nayi na nufi dakina Ina shiga ciki naji motsin sa a bayana gefen gadona na zauna na sunkuyar da kaina kasa har lokacin hawaye nake,da zalincin mahfuz zanji ko da hadani fadan da yayi da mahaifiyata.
"Lubna dan Allah kiyi hakuri wlh nasan na miki ba daidai ba,dan Allah ki tsaya mu fahimci juna ki cire komai a ranki insha Allahu bazaki Kara kamani da laifi irin haka ba,bana Jin dadin irin zaman da kikeso muyi wlh gwara ki hukuntani kowane irin hukuncine indai zamu koma yanda muke ada"
Mai zancewa mahfuz babu dan ba sabon kalma a maganarsa maimaici ne,kafin na dawo yamin kalamai da suka fi haka amma duk da haka bai fasa koma Mata ba ko dan daga kafa baiyi ba.
Mike'wa nayi na shige bandaki banasan ma jin muryarsa.
Har a yanzu kirjina zafi da ciwo yake min, wanka nayi dan naji sanyi a jikina bansani ba Yana bandakin ko baya nan, towel din dake rataye a bandakin na daura na fito ko ban kalli mudubi ba nasan fuskata a kumbure yake,Yana nan a zaune a gefen gadon ya dora mimi a cinyarsa ban nuna nasan Yana d'akin ba a nutse na shafa mai na zura doguwar riga na bar masa d'akin idan ya ajiye mimi sai na dauketa na mata wanka.
Tunda har ya dage bazai rabu dani ba bazai ji dadin Zama dani ba,kwanciya nayi a 3 seater dan karfe tara nake san Shiga kitchen,na samawa kaina abinda zanci tunda jiya yaki cin abincina na Sha alwashin bazan sake girki dashi ba.
Fitowarsa daga d'akin yasa na lumshe idona sai nake hango shi a kirjin Hadeeza,a jiya Abubuwan da yake min yake mata rudewar da yakeyi idan muna tarayya haka yakewa Hadeeza ba aurenta yayi ba jiya ma Allah ne yasan iya abinda sukayi ahaka mahfuz yakeso na share komai mu cigaba da Zama Kamar ba abinda ya faru.
Nayi saurin goge hawayen daya zubomin ta gefen idona bansani ba Yana palon ko baya palon dan idona a rufe yake,
Saukar numfashinsa naji a fuskata kafin na bud'e idona ya kamo bakina da nasa ya tsotse lebbena kafin na Mik'e ya hau ruwan cikina Yana "Dan Allah Lubnata ki taimaka min komai ya wuce wlh banasan ganinki cikin damuwa wlh tallahi zan rabu da Hadeeza ga wayata nan ki kirata duk abinda kika ga dama ki fada mata na miki alkawari bazan sake kulata ba"
So nake na saka ihu na tureshi huccin numfashinsa a jikina kamar garwashin wuta haka nake ji amma kalmar mummy ke dawo min na bata yafe min ba idan na kara Masa ba daidai ba hakane yasa na Kara runtse idona,shi kuwa hakan da yagani yasa ya cigaba da min magana Yana bin fuskata da sumba, na d'auka zan iya daurewa ya kashe kishinsa a kaina na riga da nasan jikina yake yiwa nasan abinda yake so ya samu kenan,bama zai iya hakurin a kwana biyu ba,ko zuwa lokacin zan daina Jin zafin da nakeji a kirjina,kansa kawai yasani bai damu da halin da nake ciki ba,bansan mai yasa idan har zai tabani sai na Tuno yanda na gansa da Hadeeza da Kuma yanda ya shigo jiya Yana kamshin turaren ta idan har yasan Ina da matsayi a wajensa ai ba yanda zaayi yaje wajenta jiya.
Wani iirn hankada na amsa adaidai lokacin da yake kokawa da wandona
A gigice ya taso yana "lubna karki min haka wlh idan na sama miki nutsuwa Zaki yafemin komai zai wuce a wajenki dan Allah kibari mu farantawa juna,ki barni na gwada miki kaunar da nake Miki wlh Zaki yafemin lubna"
Ya Kara yowa kaina gadan gadan
Sai a lokacin na dago idona na kalleshi "Mahfuz ka rabu dani idan kana so na sauko mu daidata dan Allah ka nisanceni har zuwa na samu nutsuwa ka riga da ka dage sai ka zauna dani bazaka bani takarda ta ba,kaje ka hadani da mummy Mahfuz har tana ikrarin bazata yafemin ba idan na maka ba daidai ba mahfuz kamin adalci kenan?mahfuz aure anayi ne dan Jin dadin,a yanzu bata ni kake ba ka samu wacce ta fini ka sakeni Mana ka koma gareta ka samu nutsuwa nima na samu sabida me kakeso kaga kayi ajalina ta hanyar doramin hawan jini,jiya da kamshin turaren ta.ka shigo gidanan"
"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun lunbna dan Allah kicire komai a ranki idan kina tuna baya wlh bazaki iya yafemin ba karki manta Allah ma muna masa laifi mu nemi yafiyarsa ya yafe Mana haba lubna mai yasa kike da ruko haka dan Allah ki manta da duk abinda ya faru wlh na Miki alkawari na rabu da ita har abada"
Haka kacemin a gida jiya Kuma ka koma wajenta mahfuz da aurenka kake aikata zina,ban rage ka da komai ba sabida rashin godiyar Allah, ka bar matarka ta suna ka tafi wajen da zaka kwasowa kanka zunubi inaso na yarda shaidan ne ya rinjayeka daka kawota har gida jiya Kuma fa"?
"Wlh ban yi komai ba jiya lubna wlh bacin rai ma yasa na kirata muka hadu turarenta nada k'arfi shiyasa kikaji kamshinsa a jikina"
Mik'ewa nayi fadar ma ya hadu da ita bai san.mai hakan ke haddasa min bane.
Na shige kitchen sai gashi shima ya shigo kitchen din,bai bar kitchen din ba har na dafa farar taliya na yanka cabbage dan mai da yaji nakeso naci.
Koda na zubo haka ya saka hannu ya fara ci,so yake ya ringa abinda Zan tanka shi hakane yasa ko kulashin banyi ba Ina gama cin abincin na dauki Mimi nayi daki da ita na mata wanka.
Zamansa a palon yasa nayi kwanciyata a d'aki.
Ban Kara Jin motsinsa ba har bacci ya saceni bansan tsawon lokacin da na dauka Ina bacci ba sai ji nayi ana hura min iska a kunne na bud'e idona a hankali sai da na wartsake na kalli gefena da alama wanka yayi sai kamshin turare yake
D'auke kaina nayi daga kallonsa na matsa sabida Rabin jikinsa ya kwantar a jikina.
"Lokacin sallah yayi ki tashi kiyi sallah ga abinci nan na siyo mana yau ba sai kin wahalar da kanki wajen girki ba daddare sai mu fita"
Da a baya yace zamu fita inaga sabida doki bazan ma iya cin abincin ba dan a rayuwata Ina balain san naga mun fita,irin rayuwar nan na matukar burgeni,ban ce masa komai ba na sauka daga kan gadon na shige bandaki na dauro alwala na fito.
Kafin na iddar da Sallah ya fita daga d'akin ya dauko plate da cokali
Ina sane nayi zamana akan sallaya bazan cutar da kaina ba zanci dashi nake fushi bada cikina ba.
Ina satar kallonsa har ya zuba Miya akan sakwaran dake a mulmule yasan Ina balain San sakwara inaga hakane yasa ya siyo,duk abinan fa da yake yi da wata a zuciyarsa na girgiza Kaina Ina danne zuciyata dake san bijiromin da tunanin Hadeeza.
Yana gama zuba miyan ya kawo sakwaran ya ajiye a gabana ya dauko ruwan wanke hannu da ruwan roba ya zauna tare da tankwashe kafarsa Yana "Bismillah"
"Na koshi"
"Lubna dan Allah ki bari, fushi da zuciya bazai canza abinda ya riga da ya faru ba dan Allah ki sauke fushin nan haka haba lubna"
Ya yanko sakwaran ya kawo bakina na kau da kai
K'arfi da yaji ya dage sai ya bani a baki hakane yasa na wanke hannuna na fara cin sakwarar Kamar ana min dole,har ga Allah Kuma yamin dadi,fuskata a hade har na gama cin Wanda Zan iya ci Yana Jana da hira nidai ban tanka masa ba har na wanke hannuna na Mik'e na dauki mimi nayi Palo na zauna.
Shi ya kwaso kwanukan ba jimawa yazo palon shima ya zauna shi kadai ya ringa hirarsa da eee Aa kawai na ringa binsa bana san fushin mummy ya tabbata a kaina.
A haka har aka Kira sallah la'asar yayi alwala ya fita massallaci nima nayi sallah na sake wanka tare da canja kayan jikina nayi zamana daki na dauko wayata na kunna data na hau WhatsApp.
Grps na Shiga nake dan bin hirar mutane har ya Kuma shigowa d'akin ya zauna Yana yiwa Mimi Wasa Ina latsa wayata Ina satar kallonsa idonsa na kaina sai sauke numfashi yake, na riga da nasan duk abinda yake yiwa bana san na cigaba da dorawa.kaina zunubi Addu'a nake Allah ya bani ikon daurewa idan ya sake nemana.
Bai bar dakin ba sai da aka fara kiraye kirayen sallah magriba da ya fita bai sake dawowa ba sai da aka yi sallah Isha.
A Palo ya tarar dani a zaune idan ta nice a koshe nake,sai dai ya nemowa kansa abinda zaici.
Yana shigowa yace na tashi mu dan fita baa machine zamu fita ba a machine Mai kafa uku zamu fita ya hada da na tayashi da Addu'a akwai kudin da yake sa rai idan ya shigo zai siyi mota.
"Idan ma aure zakayi wanan damuwarka ce ba inda zani sai ka dawo"
Ya dawo gefena da sauri ya zauna Yana "Lubna ba dan halina ba dan Allah ki tashi mu tafi"
Banza na bawa ajiyarsa ya cigaba da magiya yanda ya dagemin yasa na shige daki na canza kayan jikina zuwa doguwar Riga na yane mayafin akaina.
Shi ya goya mimi da jakar goyo ta gaba sai kallona yake ni kuwa na hade rai nasan so yake yace mayafin dana yafa yayi kadan ban saurare shi ba nayi gaba har muka fita titi ya tsayar Mana da abin hawa ya fada mishi inda zai kaimu.
Wayata nake latsawa har muka iso wajen da ake Shan ice cream yasan ni mayyar ice cream ce rabon ma daya siyomin tun Ina amarya.
Nidai binsa nake kawai a baya har muka iso wajen zama na zauna, ya miko min Mimi yaje ya fada musu kalar ice cream din daya keso a kawo daga Inda nake zaunen na ringa Kare Masa kallo.
Shigar kananan Kaya na balain yi Masa kyau so nake naga muninsa,amma na shagala da kallonsa Yana k'ok'arin jiyowa na d'auke kaina da sauri ya dawo ya zauna.
Muka hada ido ya sakar min murmushi na d'auke kaina aka kawo Mana ice cream din.
Ya mik'o hannu Yana na bashi Mimi naji dadin Shan ice cream din
Ban musa masa ba na mika masa Mimi na fara Shan ice cream din a hankali,har ga Allah naji dadi a raina, amma ban nuna hakan a fuskata ba sai ma Sha da nake a hankali kamar yamin dole,da alama masoya Nan suke zuwa har nawa namiji zai kashe ya kawo matarsa nan ya faranta Mata,mazan mu basa Mana adalci haka suke ajiyemu a gida su fito nan da Yan matan su waya sani ma ko ya kakawo Hadeeza nan take na hade rai naji ice cream din na neman fita a raina.
A hankali na saci kallonsa naga yana kallon wani waje hakane yasa na juya dan naga mai yake kallo,mace da namiji ne zaune macen ta bani baya yanayin jikinta Kamar na Hadeeza take naji gabana ya Fadi,na maido da kallona Kan Mahfuz da har lokacin yake kallonsu na Kara juyawa na kallesu,a daidai lokacin da namijin yake bawa yarinya ice cream a baki hannu daya mika yasa nagane a baki yake Bata amma banga fuskar macen ba,na Kara dawo da kallona Kan Mahfuz daa yanzu yake juya cokalin ice cream din ba Kuma Sha yake ba ni kuwa na zuba masa Ido Ina karantarsa hada Ido da mukayi yasa ya sakar min murmushi da a idona na yak'e ne yace "Kiyi ki gama mu tafi dare yanayi ko Kar Mimi ta kamu da mura"
Juyawa nayi na kara kallon wajen da dazu yake kallo sai dai har lokacin namijin kawai nake gani,macen bata jiyo ba,bansani ba ko hancina ne sai naji kamar kamshin turaren Hadeeza.
Kishi wata mahfuz keyi a gabana kenan take naji raina ya b'aci Yana k'ok'arin Magana nace "Sabida kaga Hadeeza da wani shine ka hade rai Mahfuz"
Ya gwallo Ido waje Yana "Kamarya lubna akwai wacce zanyi kishinta bayan ke ne ai babu dan Allah ki daina kiramin sunan ta ki gama Sha mu tafi"
"Na Gama"
Na juya na Kara kallon bayan yarinyar da Zan so ta juyo ba ma ja Hadeeza ce kamar na kwalla Mata Kira ta juyo Wanda kake kauna kake kishi,mahfuz ganin ta da wani ne yasa ya kasa Shan ice cream din,take naji zuciyata na min zafi daya barin Kuma sai naji dadin ganin daya Mata da wani duk abinan dai ban tabbatar da itace ko ba ita bace.
"Kaje wajenta Mana mahfuz Zan jiraka a waje"
"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun haba lubna"
Ya dan fada da karfi idona na Kan yarinya dan burina ta juyo na ganta aikuwa muryar mahfuz da taji yasaka ta juyo, gabana yayi wani irin faduwa.
Bana Jin tagani ganin mahfuz yasaka ta mik'ewa tare da gwallo ido tana mahfuz gadan gadan tayo wajen mu har lokacin bata gani ba,
Kafin ta karaso mahfuz ya daka mata wani uban tsawan daya saka ta tsayawa cak
"Karki sake ki matso kusa dani,ki fita daga rayuwata Hadeeza daga yau bani bake, matata ta isheni rayuwa ki rabu dani Hadeeza idan Kuma kika k'i duk abinda na miki ke kika jawowa kanki"
Bansan Mai yasa naji sanyi da Dadi na ratsani ba,Koda baa har zuciya MahfuZ ya fadi haka ba ya faranta min dan ya disgata a gaban katon Alhajin da tazo dashi haka ma a gaban mutane.
Ido muka hada da ita idonta ya ciciko da hawaye na sakar mata murmushi na tsinci kaina da karasawa wajen da take tsaye Ina "Idan ke din ba jaka bace Kuma karuwa mai bin mazajen mutane sai ki hakura ki daina bibiyar mijina haka banza balagaza karuwa"
So nake tayi magana na d'auke ta da mari batayi magana ba har Mahfuz yazo ya janyeni
Muka bar wajen muna fita na fusge hannuna Ina "Wlh duk kishi yasaka kayi maganar da kayi,mahfuz ni ba yarinya bace wlh kana san yarinya nan ka sakeni kawai ka aurota"
"Lubna bansan Kuma Mai kikeso na miki bayan wanan ba agaban idonki dai kina ganin kashedin dana mata duk sabida na faranta miki rai haba lubna"
Ya kuwa faranta min din banaso na nuna masa ne ban Kara ce masa komai ba har muka Isa gida.
Da isarmu gida ya ajiye ledojin da ya dan yi siyayyarsa a ciki har dasu balangu a palo ni kuwa daki na shige na canjawa Mimi Pampers na bata abincinta ta Sha ta koshi
Kafin na Shiga bandaki nayi wanka na saka kayan bacci na haye gado raina fes dan na fara yarda mahfuz dagaske yake zai rabu da Hadeeza.
Shigowarsa yasa nayi saurin lumshe idona yace "bazaki ci balangun ba"?
" A koshe.nake"
Bai Kara cemin komai ba ya fice daga d'akin ba dadewa ya dawo d'akin Ina jinsa ya rufe kofa yazo ya kwanta a gefena a hankali ya matso kusa dani yamin rada a kunne "Ina bukatar ki pls kimin wanan taimakon dan Allah"
Ban motsa ba ya juyo dani,jiki da jini Ina karbar sakonsa amma haka na kwanta kamar ruwa na d'auka yi zaiyi sai ji nayi ya dagoni idona a rufe yake Ina k'ok'arin bude Idona naji jikinsa a bakina Yana shafa kaina.
Har ga Allah abinan amai yake Sakani nayita tofe tofen yawu har garin Allah ya waye janye kaina nayi na koma na kwanta,hakane yasa ya hakura jikinsa sai rawa yake kamar Wanda tab'a sanin mace ba har ya samu nutsuwarsa naji bacci ya d'auke shi nima Ina rufe Ido bacci yayi awon gaba dani...
MG'S SKINCARE
In akaji gangami labarin kidane,sun shahara sun tumbatsa sunkai sunwuce tunanin duk wani meson Adama dashi aharkar gyaranfata d walwalinta,
Yar uwa haske ko qyalqyale kikeso kiyi Abu yaci tura?
Kyan fuskarda ko yar uwarki mace kance dama dama kikeso?
Kokuma ke kuraje d tabbuna suka lahanta mki fuska har ake ganinki d wani idon n daban,
Nankarwace tayimiki zanen kura a kyakyawar fatarki?
Kokumade Mai kikashafa be amshekiba yasa duk kika koma ruwa biyu Nan fari Nan baqi?
To duk kuzo insha Allah kudai naku y qare gdan kukazo,
Munkawo shahararrun kayangyaran jiki
Sabulu,
Man shafawa,
Man fuska,
Scrub,
Cleanser,
Glow oil,
Dukdan qawarmaku d matsaltsalunku,
Da 11k kachal zatasa kihaske kizama kalar madara qirar models,
Set 11k
Sabulu 3k
Student package:7k
Munakuma bayarwa in pieces duk afarashin mesauki.kayanmu bbu fariya ko tutiya angwada andawo,ankumayi farinciki d hkan,Kuna iya samummu d wadannan numbobin,
WhatsApp,
08062991549 or 07046881166 or 07067210195
Call only
08064532391
Instagram: glow_with_mgs
Facebook:mg's skincare
Idanba wadannan numbobinba to gaskiya b mg's bane, available in Kaduna and Kano only, thanks for always trusting us,our returning customers we really do appreciate wadanda sukeda burin Siya munamaku fatan alkhairi ubangiji ybaku yenda zakuyi,Allah Kuma yqaro mna dukiya me amfani ta hanyar halalinmu
*WANAN NOVEL DIN NA KUDINE BIYA 500 zuwa 2029764071 first bank nafisa Nuhu sai a tura shaidar biya zuwa ga lambar Nan 08033719070 ko katin mtn mutanen Niger Airtel Kika min SHARING bansanki ba Allah Yana kallonki na barki dashi*
*Page 22*
Dagani har shi makara mukayi sallah asuba sai a gida yayi sallah asuba.
Sanin zaije aiki tunda ranar Monday ne yasa ban koma bacci ba na fara k'ok'arin zuwa kitchen na sama Masa abinda zaici.
Sai dai Ina zuwa na gansa a kitchen Yana soya kwai Ido da muka hada dashi yasa ya kanne min Ido Yana "Na hutasheki farin cikina jekiyi kwanciyarki kiyi baccinki"
Ina karya Zan wuce na Kulle Miki gidan idan bazaki iya girkin rana ba Zan siya na Aiko miki dashi"
Hmm kawai nace tare da barin Kitchen din nasan duk Yana hakane dan na manta abinda yamin,nima zanso na manta din amma bansan Mai yasa nakeji kamar bazan iya sakin jikina dashi kamar a baya ba,ban koma d'aki ba na zauna a palo,ya fito daga kitchen din da plate din kwai da kofin shayi.
Ya zauna a gefena yana ci Yana min hira nidai biyesa kawai nake har ya gama ya jawoni ya Kara jagwalgwalani san ransa banda ma naki nasan karawa zaiyi ya shige daki ba dadewa ya fito a shirye Yana kamshin turare ya ajiyemin Dubu biyu a gefena Yana "bari naje kar na makara"
"A dawo lafiya"
Ya sunkuyo yamin kiss zai juya nace "Idan har ka sake cin amanata Allah ya isa ban yafe maka ba idan bana kallonka Allah na kallonka"
Murmushi yayi Yana "Mahfuz bazai ci amanarki ba mahfuz nakine ke kadai ki kwantar da hankalinki a gabanki dai jiya kina kallon irin gargadin da nayi mata"
Yarda daya ce amma ba abinda mahfuz zai cemin yanzu na yarda da Ido na bishi har ya fice daga gidan.
Na Mik'e na koma daki na kwanta bacci ya Kara awon gaba dani.
Mahfuz
Sosai yaji shi cikin farinciki dan a yanzu yasan ya samu ya shawo Kan lubna zaiyi iya kokarinsa wajen gujewa duk wani abu da zai saka su samu sabani.
Take yaji shi cikin b'acin rai daya tuno ganin da yayiwa Hadeeza da wani jiya,tunda yake da ita bai tab'a ganinta da wani ba baisani ba ko hakane yasa jiya yaji ransa ya b'acin da ganinta da wani,Ashe karya take da tace masa bata kula kowa Ashe karya take da tace shi kadai ne saurayinta,a yanzu ya Kara tabbatar da zarginsa akan fuska biyu gareta,dama hanya yake nema da zai yakiceta,dama hanya yake nema da zai ce Mata bazai iya aurenta ba, a yanzu Kuma ya samu hanyar tunda ya ganta da wani jiya.
Sai da ya isa office ya dan kammalla wasu ayyukan kafin ya Nemo lambar Ammi ya kirata dan su gaisa,dan ba mai wanan sabon layin nasa.
Sai dai Ammi na Jin muryarsa ta rufeshi da fada tana "Wulakanci ne yasa ka kashe wayarka tun jiya nake neman layinka a kashe"
'canja layi nayi Ammi shiyasa na kiraki da sabuwar Dan na daina amfani da wancan"
"Sabida me ka canja layin da tun kana Saurayi kake amfani dashi"?
"Haka kawai na canja layin Ammi"
"Karya kake yi kace min matarka ce ta saka ka canja layi sabida Kar mu ringa samun ka a waya mahfuz kasan dai ba ita ta haifamin Kai ba ko"Anya yarinya nan ba asirice ka tayi ba naga alama so take ta rabaka da kowa ta hanaka muamalla da kowa to wlh wanan ne bata Isa ba dan ko dawo da ita da kayi bada yawuna ba,amma tunda ka dage wlh sai ka Kara aure Ina nan akan bakana Kuma kafin na Saba maka ka mayar da layin nan da kowa yasanka dashi,ba ruwana da wanan sabon layin jibi kazo Ina san ganinka"
Kit ta kashe wayar yabi wayar da kallo,ya riga da yasan halin Ammi idan baiyi abinda tace ba kadan da aikinta tace zata maka baki, mayar da layin nan da tace yayi zai iya haddasa Masa matsala da Lubna yasan halin Hadeeza da azababben naci ko yayi blocking dinta sai ta kirashi da wani layin ba Kuma lalai duk bayanin da zai yiwa Lubna akan ita take nace Masa ba ta yarda,zancen Karin Aure Kuma da ta dage sai yayi sam bai shiryawa wani aure ba,Koda zaiyi ba yanzu ba Hadeeza ce dama ta matsa Masa yaji Yana San ya Kara auren,a yanzu Kuma bazai tab'a iya aurenta ba.
Layin ya mayar a karamar wayarsa dan yasa a babbar wayarsa sai Hadeeza ta kusa cika mishi waya da magana ta watsapp.
Yana sakawa ko minti goma baayi ba sai ga Kiran Hadeeza a wayarsa ya riga da ya haddace lambarta a kansa baiyi wata wata ba ya danna Mata blocking sai yake hango ta a idonsa yanda ta dame ko'ina a jikinta wani katon da a haife ya haifeta ya ringa bata ice cream a baki.
Texes ne sukayi ta shigowa da wani lambar zain ko bai bud'e ba yasan itace tayi amfani da wani layin
Duk message din na ban hakuri ne da bayanin ba saurayinta bane wani dan uwansu ne ya bata dama su had'u bata ji dadin wulakanci daya mata ba jiya ko bacci batayi ba,Kar ya manta irin san da take masa,Kar ya manta irin dukan da ta Sha a hannun matarsa bai dace ya Mata haka ba.
Tsaki yayi ya goge duk messages din ya Nemo lambar lubna a waya dan so yake ya goge komai a zuciyarta sai da Kiran ya kusa katsewa kafin yaji ta d'auka hira ya hau janta dashi amma daga yanda take amsa wayar yasan ba so take ba,dariya ma yanzu take bashi ita a lailai fushi take dashi,bayan yasan balain San shi take dannewa kawai take katse wayar yayi ya tutura Mata text ya ajiye wayar.
Kiransa da Hadeeza ke tayi da layin zain din da ta ke ta Masa texes ya danna a block Yana Jan dogon tsaki,har yanzu hangota yake da wanan katon yana bata ice cream ya rasa ma mai yasa yake Jin haushi idan ya tuna.
Wajen karfe daya ya mik'e dan so yake daga massallaci ya biya ta restaurant yayi take away guda biyu ya aikawa lubna daya shima yaci daya.
A bakin k'ofa ya ci Karo da Hadeeza da ta sha bak'ar doguwar Riga har kasa kamshin turare kawai take.
Da sauri yaja da baya cikin mugun hade rai,Yana "Mai ya kawoki office dina ban hanaki zuwa wajen aikina ba Wai Mai yasa bakida hankaline wane kallo kikeso a ringa min ne bana ce miki ki rabu dani ba"
Ba ko alamar fushi a fuskarta ta rufe k'ofar tana "Mahfuz taya zan rabu dakai bayan Ina sanka nasan kaima kana Sona, Mahfuz Ina duk alkawarikan da kayi min,na zaka aureni,duk wahala da na sha da dukan da naci a hannun matarka ya tashi a banza kenan a yanzu zaka ce na rabu da kai,bayan kasan banida kowa Wanda ka gani dashi a jiyan cousin dina ne ba saurayina bane"
"Hadeeza ada ni nace zan aureki a yanzu Kuma na fasa ba Kuma ki isa kimin dole ba,har ni zaki rainawa hankali kicemin wanan katon da na ganki dashi jiya cousin dinki ne?cousin dinki ne yake baki ice cream a baki?wane irin rantsuwa ne bakimin akan bakida saurayi ba ni kadai gareki,nasan irin wayanda kike hulda dasu taya zan aureki kina biye biye wlh Hadeeza Sam ban yarda dake ba na dade Ina zargin badani kawai kike muamalla ba jiya kuwa idona ya gane min dan haka a yanzu ban yarda da ke ba bazan iya aurenki ba ki daina kirana a waya Hadeeza karki hadani fada da lubna inasan matata"
Akan gwiwarta ta zube hawaye na zubo Mata Tana "Wlh mahfuz dakai kawai nake hulda ka yarda dani ba komai tsakanina da wanan da kagani dashi jiya,san da nake ma yasa nake ma duk abinda nakeyi bawai dan halina bane ba Zan iya maka komai dan na faranta maka rai"
Kamar an fusgo maganar daga bakinsa dan ya dade Yana san ya mata tambayar "Hadeeza bani na fara saninki ba wa Kika fara bawa kanki"?
"Fyade aka min a lokacin Ina secondary mahfuz shiyasa kaji haka amma wlh ba na muammalla da kowa"
Tasan ta hanyar da take Kama mahfuz hakan kuwa yasa ta cigaba da kuka cikin kirsa tunda taga yayi shiru ta cigaba da kuka cikin shagwaba taja gwiwar ta zuwa wajen da yake tsaye ta mike tsaye tare da rungumeshi.
Har zai janyeta ta Kara kankame shi.
So take ko Yaya ne ta rinjayeshi tunda ya fara botsare mata hankalinta ya tashi bata da wata hanya da zata samu ya fito ya aureta sai ta wanan hanyar da idan ta samu cikar burinta ya gama zuwa hannunta,so take ta nunawa lubna tayi kad'an bata Isa ta hana aurenta da mahfuz ba,so take ta nunawa lubna iyakarta a jiya ko runtsawa batayi ba burinta kawai mahfuz ya aureta.
Yanda ta fara kunna shi yasa mahfuz janye jikinsa da sauri Yana "Dan Allah ki tafi gida Hadeeza nan karki Manta wajen aikina ne"
"Bazan tafi ba sai ka tabbatar min da zaka zo gidanmu idan ba haka ba wlh haka zan ta zuwa nan"
"Hadeeza Dan Allah ki bari na samu nutsuwa zanzo ki daina kirana a waya bana so ki haddasa min wata fitinar har yanzu ban gama shawo Kan lubna ba Kuma kinsan duk abinda ya faru ke Kika jawo min,kema kinsan bazan samu wani kwanciyar hankali ba har nayi tunanin wani aure idan bana zaman lafiya da lubna"
Kamar ruwan zafi yake watsa mata haka ta ringa ji amma haka ta daure tana "toh idan ban kiraka ba kai zaka kirani"?
"Eee karki sake ki Kara kirana a waya Hadeeza da kaina Zan kiraki Kuma Dan Allah ki daina fesa wanan turaren yanzu lubna tasan kamshin turaren ki idan har kinaso mu cigaba da muamalla ya zama dole ki kiyaye Abubuwan da na fada miki na Kuma gaya Miki gaskiya a yanzu banida halin aure idan har matsuwa kikayi da auren sai dai ki nemi wani idan Kuma Zaki iya jirana toh sai ki bini a hankali"
Murmushi ta sakar Masa tana "Duk yanda kace ayi haka za'ayi Ina kaunarka Mahfuz"
Ta Kara rungumeshi,mahfuz da kyar ya Kai zuciyarsa nesa bai biye mata ba amma har kasan ransa yaji yana san kasancewa da Hadeeza dan wani irin salo take masa dake gigita shi.
A haka ya samu ya Koreta yana maida numfashi sai yake ganin kamar Lubna zata gane ya had'u da Hadeeza wayarsa ya d'auko ya Kira lubna Koda ta d'auka hira ya ringa janta dashi da alama ta fara saukowa dan ta dan biye Masa har take tambayarsa mai zata dafa mishi daddare sosai yake jinsa cikin farinciki saukowar da tayi hira Suka dan tab'a kafin ya kashe wayarsa ya sake alwala a bandakin office d'insa yayi sallah Koda ya iddar cire rigarsa yayi ya wanke a bandakin ya rage daga shi sai vest da dogon wando dan gani yake Yana zuwa gida lubna zata ji kamshin turaren Hadeeza a jikinsa a yanzu tsoro yake lubna ta gano Yana tare da Hadeeza bai san Mai yasa zuciyarsa taki bashi hadin Kan ya rabu da ita ba tana da tsara shi shikenan.
LUBNA
Tunda mahfuz ya kirani a waya ban Kara komawa bacci ba na tashi na nemawa kaina abinci naci na gyara ko'ina nayi wa mimi wanka na dawo Palo na zauna haka kawai nake Jin wani irin kadaici da ace a wancan unguwar muke da yanzu na Shiga gidan mmn Iman mun Sha hira.
Wayata na dauka dan na kirata Ina kuwa kiranta tace min yanzu takeso ta kirani akan ta shigo layin gidana.
Kasa hakura nayi ta shigo na fita waje na tsaya har ta karaso cikin farinciki na rungume ta mmn Iman nada wani irin matsayi a zuciyata Ina kaunarta sabida tana kaunata duk wani abu da ya shafeni tana daukarsa da mahimmanci damuwata damuwarta ce, duk da ta girmeni ko jinina ce ita sai haka.
Hira muka barke dashi ta hau tsokana ta akan nayi fresh anya daga dawowata mahfuz bai yiwa Mimi kanwa ba,nariga da nasan halinta ban biye mata ba
Na Shiga kitchen na dora Mana abincin muna hira Ina girkin har na sauke na zubo Mana muna cikin ci nake bata labarin duk abinda ya faru daga dawowata gidan har ganin da mukayi wa Hadeeza jiya da wani ban b'oye mata komai ba
Cokalin hannunta ta ajiye tana "Lubna ki ajiye duk wani fushi ki cire komai a ranki a yanzu ya Kamata ki zage wajen kyautatawa mahfuz wlh yarinya nan shaidaniya ce,duk da kince ya mata kashedi a gabanki zata yi duk abinda zatayi dan ta dawo rayuwarsa ke Kuma kisan yanda zakiyi ki hana hakan faruwa,yanzu balain da ake ta fama dashi kenan wlh shekaranjiya Abban Iman ya bani lambar wata da ta sako shi a gaba yace na kirata na nace mata ta daina kiransa a waya bakiga zagin da nayiwa yar iska ba,yau ma Yana Kira a wayarsa ya mikomin yace min itace tanajin muryata ta kashe"
"Toh mmn Iman ke mijinki Yana Sanki baya iya Miki boye boye,mahfuz bazai tab'a bani wayarsa na zagi Hadeeza ba wlh nasani,wane irin kyautata wa ne banyiwa mahfuz ba mmn Iman a karshe dai sai da yaci amanata har gida ya kawomin budurwarsa wlh ko yanzu na tuna sai naji zuciyata namin zafi, fushin mummy ne banaso shiyasa na bar shi ya samu nutsuwa dani,amma wlh na kasa manta abinda yamin"
"Idan har kina tunawa dole kiyita Jin zafi amma Ina shawartarki da ki manta da komai wlh mijinki na kaunarki shuumar yarinya ya hadu da ita"
Shawarari mmn Iman tayi ta bani ta bud'e Jakarta ta fito da lodin magunguna mata akan na ringa amfani dasu,na jawo mijina jikina na yafe Masa abinda yamin tariga da tasan bazan iya mantawa ba amma na daure.
Muna taren mahfuz ya kirani, ita ta ringa min rada har na biyewa mahfuz muka tab'a hira har na tambayeshi abinda zan dafa yace na dafa koma mene zaici.
Ina jin farinciki a muryarsa har ya kashe wayar sai ga text dinsa nan a wayata
Zuwan mmn Iman da shawawarinta ya faranta min sosai hakane yasa na cire komai a raina na Kuma dauki shawararta akan na sake karkato da hankalin mahfuz kaina.
Magungunan da ta kawomin wayanda zan iya sha na Sha na matsewa na matse nayi abincin da yake so karfe shidda ya dawo da kwalliya ta yazo ya Sameni.
Sakin fuskar daya samu da tarbar da na mishi yasa sai da ya samu nutsuwa dani har mamakinsa nake dan kamar karo jarraba yayi.
A ranar guduwa ne banyi ba dan sai daya kusa fanshe watani da baiyi ba.
A wanan gabar na Kara jawo mijina jikina duk wani abu na kyautatawa Ina masa,lokaci zuwa lokaci shaidan kaso bijiromin da cin amanar da yamin sai nayi saurin yakicewa balle idan naga bai dawo da wuri ba.
Wayarsa kuwa Yana ajiyewa zan d'auka na hau Masa bincike duk binciikena dai ba abinda nake gani hakane yasa na saki jikina Ina tunanin dagaske ya rabu da Hadeeza.