Tsintacciya Hausa Novel page 6-10


Health College

Tsintacciya Hausa Novel page 6-10

Tsintacciya Hausa Novel page 6-10

 *🌈TSINTACCIYA🌈*

FITATTU HUƊU🔥


Http://wa.me/+2348119237616


EPISODE6️⃣

Ƙamshin haɗaɗɗan turarensa ne ya daki hancinta wanda ya sanyata saurin janye shanyayyun idanunta tare mai dasu ta rufe,

Wani irin harbawa Zuciyarta keyi tana jin wani matsananci tsoro na shigarta, gata dai male male a jikin mutum amma ta kasa wani ƙwaƙƙwarar motsi bare tayi tunanin zame jikinta.

Yana zaune saman kujera 1 seater yana sanye cikin wani tattausan wando 3gauter sai farar singlet wacce ta kama jikinsa sosai ta fito da 6pack na jikinsa idanunsa a lumshe yana sauke numfashi, yayinda gudun da zuciyarsa ya ƙaro fiye da baya,

Idanunsa dake a Lumshe ya buɗe a hankali ɗan taune bakinsa yay jin yadda take masa sukur sukur a jiki kamar wata macijiya.

Hannunsa ya miƙa ta gefen lafaffan cikinta yana jin yadda take sauke ajjiyar zuciya cup of coffee ɗin sa ya ɗauka, gently kuma yay baya tare da kwanciya a jikin kujerar.

A hankali yake spending coffee ɗin a bakinsa ya ɗauki wajan 10minute kafin ya shanye coffee ɗin domin daman ƙa'ida ne sai ya sha Wannan coffee ɗin na Subhi da cikin dare kamar wani buzu ko labarabe.

Ajjiye cup ɗin yay cikin nutsuwa kuma ya sanya tafin hannunsa duk biyun tare da zurasu ta tsakiyar hammatar ta caraf ya ɗaga ta tsaye yana yatsuna fuskarsa.

Tsaye Akeela tayi kanta a ƙasa, kunya duk ya kamata through ba taga fuskar wanda ta zauna a cinyarsa ba, amma dadɗan ƙamshin parfume ɗinsa ya sanya tasan cewa shi ɗin daban yake ko a cikin maza.

Musamman yadda taji Physique chest ɗinsa dake cike da ƙwantaccen gashi lub! lub!!..

A razane ta sauke ajjiyar zuciya tare ƙanƙame Jikinta waje guda, naman jikinta ya wani irin rawa da ɓari dalilin saukar wani masifafan ruwan sanyi da taji tun daga tsakiyar kanta har ƙasan ƙafafuwanta, da alama ma ruwan daga cikin fridge aka ɗauko shi.

Idanunta da sukai wani irin juyewa suka ja ta buɗe da niyyar ganin wanda ya zuba mata ruwan.

Amma kamar walƙiya tuni Akeem ya haura upstairs babu mai cewa Shine yay punishing ɗin ta da wannan ruwan sanyin domin babu wani sign daya bari a wajan.

Abinka da mai ciwon ciki wanda jininta yake double SS tuni jininta yay wani daskarewa, tare da tsaya mata waje guda, a hankali kuma wata ƙwaya ta tsaya a tsakiyar jijiyar ƙafarta tare da lanƙwashewa kamar laushe.

Cikin ƙaramin lokaci ƙafarta ta fara wani irin matsanancin ciwo kamar ana sanya gatari ana datsa ɓargo da ƙashin ƙafarta haka ta keji.

Tsananin azabar da yay mata yawa ne yasa ko kuka ta kasa sai wani irin fitinannan numfashi da take gumi na yanko mata.

A hankali ta sulale tare zubewa a saman carpet ɗin parlon cikin wani irin wahalallan sabon yanayi ta kwanta tare da ɗura ƙafarta a saman kujera ta shiga jujjuya kanta tana sakin wani gigitaccen kuka iya zuci mai bala'in cin rai.

Gashi babu Folic acid da paludrine a kusa da ita bare tasha ko taji sauƙin abin.

Dukkan hannunta ta sanya a ƙafarta ta riƙe gam "ɗib! ɗib!! ɗib!!" Haka jijiyoyin ƙafarta suke harbawa alamar ciwo yayi ciwo a hankali kuma ciwo ya fara yawo a jikinta daga ƙafa zuwa kwankwasonta bata samu bacci ba sai wajan kiran sallar farko na Subhi.



A hankali yake sakkowa daga strains ɗin benen part ɗinsa, yana sanye da Embrodiery Islamic jallabiya white colour, wacce ta kasance mai santsi da taushi tana da half hand daga gaban ƙirjin kuma a ɗan tsage take..

A hankali yake tafiya kamar bai so cikin nutsuwa bakinsa ke motsawa alamar tasbihi yake ga Ubangiji.

Hannunsa a goyo da bayansa yana taka ƙafafuwansa dake sanye cikin Mon mule slippers masu kyau..

A tsakiyar parlon ya tsaya idanunsa a rufe  babu jimawa Abbu ya fito daga part ɗinsa shima sanye da jallabiya milk irinta Akeem.

Babu wanda yay magana a haka suka jera zuwa masallacin dake cikin estate ɗin nasu.

Rutse idanunsa yay da tuni su uku ne suke tafiya amma waccan shigiyar Yarinyar mai siffa da aljanun ruwa taja masa a rasa mafi muni a rayuwarsa.

Bayan an idar ya zauna zaman azkar ƙarfe 6 dai-dai suka fito daga cikin masjid ɗin zuwa gida.

Kai tsaye Akeem kitchen ya nufa yana zuwa ya samu Ummi a ciki sanye da ƙaton hijab har ƙasa, kallonsa tayi tana Murmushi, a sanyaye murya can ƙasa yace.

"Sabahul khair Ummina"

Mug ɗin hannunta dake cike da coffee ta ajjiye a hankali ta ƙarasu wajansa yana ganinta ya ɗan zube a ƙasan gwiwoyinsa tare da zame wular kansa, hannunta ta ɗura a saman sumar kansa kafin tace.

”Sabahul khair Hero”

Murmushi Yay irin Murmushin nan da idan ba ita ba ko Abbu babu mai ganinsa sai Md Adnan.

Addu'a ta shiga yi masa kafin gently ya miƙe, ganin yadda take kallonsa yasa ya ɗan kwaɓe fuska yana lumshe idanunsa cikin narkakkiyar murya yace.

“Ummi”

Hannu tasa ta ja dugun hancinsa tace "Allah ya kyauta maka, ƴarka tayi taɓara kai ma kayi"

Shi dai bai ce komai ba, maimakon ya fita daga kitchen ɗin sai yay zamansa akan kujera yay hakanne kuma saboda bai son fita yaga Akeela.

Fita Ummi tayi sam bata kula da Akeela ba kai tsaye part ɗinta ta shige.

Abbu da ya tsaya da Bala driver yana bashi hqr ne ya shigo cikin parlon kai tsaye kuma idanunsa ya sauka akan Akeela wacce take baccin wahala a saman carpet..

Da sauri ya nufi inda take  yana faɗin.

"Ya Salam Babyna bacci a Parlo a ƙasan carpet why?"

Ya faɗa yana tsugunawa tare da sanya hannunsa gaba ɗaya ya ɗauke ta zuwa jikinsa, Ajjiyar zuciya ya sauke yana ƙara kallon fuskarsa wacce tai jajirr idanunta ya kumbura sosai.

Cikin tausayinta da kuma masifafan sonta dake ƙara zautar da Abbu a hankali ya manna bakinsa a saman goshinta tare da sumbatar wajan karaf a idanun Akeem taɓe baki yay da kuma sauri ya juya tare da komawa kitchen ɗin.

"Sorry nine ko, sorry Babyn Abbu muje na goyaki kiyi bacci sosai, i promise to you cewa ba zaki kuma kuka ba, I'll be your side kinji Babyn Abbu na" ya faɗa yana ƙara shafa fuskarta tare dayin part ɗin yaransa da ita.



  http://wa.me/+2348119237616

*_wannan book ɗin na kuɗi ne biya 500 a saki a vip ko kuma 300 a nrml grp_*


Abbu na shigewa Akeem ya fito fuska kamar hadari babu walwala baki ɗaya, kai tsaye wani room ya shiga yana shiga ya kunna hasken ciki, ɗakin karatu ne yana shiga wajan kujera yaje ya zauna tare da lumshe idanunsa yana sauke numfashi.

Not too long da zamansa a buɗe ƙofar a hankali aka shigo, Amani ce ƙyakkyawar Yarinya mai fuskar Akeem.

Washe bakinta tayi da gudu ta nufi wajan Akeem tana faɗin "Hero na" ware gajiyayyun idanunsa yay tare da mai da idanunsa kan Amani kallon da yay mata yasa ta tsaya tare da juyawa da sauri ta fita tana dawowa tace "Salamu Alaika" wani fitinan Murmushi Yay mata yana jin wani sanyi a ransa yace "Wasalamu alaiki Amani Abdul-hakeem Bukar Bello" ya faɗa yana lumshe idanunsa tare da ware mata hannayensa cikin jin daɗi ta faɗa jikin Mahaifin nata tace.

"Azunnu annaka bikhair?"

Shafa bayanta yay tare da sumbatar goshinta yace.

"Lafiya lou and you"

Murmushi tayi tana sumbatar goshinsa tace "Ana bikhair"

Lumshe idanunsa yay yana ƙara rungome ta a jikinsa yana jin wani so da ƙaunar Yarinyar nasa na shiga zuciyarsa, zameta yay a jikinsa yace "sit" Zama tayi tana kallonsa sosai kamar bazai magana ba sai kuma yace "biya haddarki" a hankali tai rufe idanunta kamar yadda taga yanayi kafin ta fara karanta masa inda yay mata, tana cin karatun ne Afaf da Aleema suka shigo sanye da manyan hijabai, nan da nan walwalar fuskarsa ya ɗauke zubewa sukai bakinsu na rawa suka fara gaida shi.

Suna tsaye ko Kallon su bai ba yaci gaba dayiwa Amani karatu.

Bayan ya gama ya kallesu har zai magana sai kuma ya fasa.

Hadda suka bashi kana ya ɗura masu da karatu.

Suna cikin karatun ne Aka buɗe ƙofar Abbu ne ya shigo cikin tashin hankali ganin hakan yasa duk yaran nasa suka kallesa a kiɗime yace.

"Dr Saboda Allah ba danni ba kazo ka duba Yarinyar nan she's in critical condition ciwonta ya tashi bana son yay worse da yawa"

Shiru Akeem yay tare da ƙara haɗe fuska ganin hakan yasa Abbu faɗin "saboda Allah, saboda matsayina na mahaifi please Abdul-hakeem Bukar Bello" Miƙewa tsaye yay ba tare da yace komai ba ganin hakan yasa Abbu yabi bayansa, Akeem kam ji yake kamar ya zunduma hannu aka yay ihu dan baƙin ciki.

A bakin ƙofar ya tsaya Murya a can ciki yace "Kaje Abbu I'll check her" yana faɗin hakan ya buɗe ƙofar ɗakin ya shiga tare da rufewa girgiza kai kawai Abbu yay ya juya.

Tana kwance saman bed ɗin sai juyi take domin a yanzu bata iya tantance inda yake mata ciwo a sanadin ruwan da Akeem ya sheƙa mata..

Hannunsa ya harɗe a ƙirjinsa cike kuma da tsanarta ya ƙarasa inda take tsaye yana jin kansa na wani irine sara masa zuciyarsa na harbawa sosai.

Ganin bata hayyacinta gaba ɗaya yasa gently ya zaune a gefen gadon tare da sanya hannunsa ya wani irin fincikar ƙafarta wata razananiyyar ƙara ta saka jikinta na kyarma da sauri ta tashi zaune tana cije bakinta tare da yarfar da hannayenta Jikinta sai ɓari Yake gaba ɗaya rigar jikinta ya zame gashinta ya hargitsa sosai..

A karo na farko ya ƙara Kallonta kafin ya daka mata wata gigitacciyyar tsawa ƙarfin tsawar da kuma rashin sabon jinta ga halin ciwo da kuma matsanancin tsoron daya shigi Akeela yasa gaba ɗaya tai wani irin juyi tare da faɗawa jikinsa ta wani irin cusa fuskarta a tsakiyar ƙirjinsa jikinta duk rawa yake domin dam bata saba da kind of this abubuwan ba.

Tsaki Akeem yaja yana taune bakinsa kafin a hankali yasa hannunsa yay cilli da ita daga jikinsa, kanta ya daki frame ɗin gadon wani irin runtse idanunta tayi azaba biyu ta haɗe mata.

Bayan ya fita daga bedroom ɗin ne Akeela ta fashe da wani irin kuka, gashi ita magana sam bata tsarinta bai dame ta ba, wani irin zafi da ciwo ta keji a ranta, wanne irin mutum ta haɗu da shine? Me tayi masa da har zai dinga cin mutuncin ta har haka? She don't even know him balle tai wani abu na rashin dai-dai amma yana nuna ko ina kula infact ma shine yaja mata wannan masifar na tashin ciwon nata.

A yanzu ba ciwon ke sanyata kuka ba, domin idan da ana sabawa da zafi da kuma raɗaɗin ciwo da yaci ace ta saba dashi, amma a kullum idan ya tashi a sabo ta kejinsa, ciwon sikila ya wuce tunanin dukkan mai tunani ko mai haihuwa ba lallai taji azabar da suke ji ba.

Kifa kanta tayi a tsakiyar cinyoyinta tana wani irin kuka mai cin zuciya.

Akeem na fita derect wani side ya shiga ashe ƙaramin clinic ne, wata injection ya haɗa guda biyu fuskar nan nashi babu walwala sam.

A haka ya gama haɗawa ya fito yana fitowa ya tsaya idanunsa akan Didi wacce ta ciko plate da farfesun naman cow head.

tsareta yay da idanu domin mamakin naman data kwasa yake amma fuskarsa sam bata bayyana yanayinsa ba, harara ta maka masa tace "to ba sai dai kaci kanka ba, ai dai lalura ce bata shige kan kuwa, jiya jiyan na dakta ya gama gayawa Bukari naci nama na ƙoshi, to wallahi nidai li'ilafi ƙurash kaci kanka nama na kurr aniya bil aniya ato"

Girgiza kai kawai yay tare da nufar part ɗin su Aleema.

"Ɗan banza fuska kamar karas in sha Allah sai Ubanka yay maka auran dole, masifa sai cin yaro take shi kenan shan lemun tsami" 


_(shan lemon tsami baya rage sha'awa sai ma amfani da yake wajan inganta Mani, more impormation kiyi attending class ɗin we are all Women wanda zan gabatar da grp na Vip ɗin Tsintacciya 500 kacal)_


Parlo ta koma lokacin Abbu ya fito cikin wata dakakkiyar shampoo dark blue anyi masa ɗinkin jamper da babbar riga.

Ya haɗu sai ƙamshi yake zubawa, Didi na ganinsa ta fashe da kuka tana faɗin.

"Sai a gaya min cewa bani na haifi Bukari na kawosa duniya ba, da za'a dinga yi min gori a gidan ɗan dana haifa"

Kallonta yay yana zama dai-dai nan Mami ta fito cikin wata milk ɗin valisco sai ƙamshi take zama Abbu yay yace "Gori kuma Didi?"

Bakin zani ta cire ta face majina tace "A'a to ba dole nace gori ba gashi nan Audil yana cemin kura bani da aiki sai cin nama, kuma dai ai naga lalura ce ko ba gaskiya ba? Babu ruwana fisabilillahi nidai na basshi da Allah bance ka faɗa masa masifar sa ta ƙare masa akai wallahi" 

Akeem a hankali ya tura ƙofar ɗakin ya shiga tana cure waje guda lokacin su Aleema sun gama shiryawa tuni Drive ya tafi kaisu makaranta su da Amani.

A ɗan fakaice ya kalleta dugun gashinta wanda yake zube har saman bed ɗin ya kalla taɓe baki yay aransa yana faɗin "har ƴan ƙauye sun iya ƙarin gashi mtwss"

Gently ya ƙarasa inda take zaune tana sauke ajjiyar zuciya har yanzu jikinta ɓari yake.

Baya jin zai ɓata lokacin da wajan yiwa Wannan stupid gal ɗin magana yay mata wata iriyar muguwar tsana wacce bai taɓa yiwa kuwa ba.

Yana daga tsaye ya ajjiye injection ɗin a gefensa cikin wani ɓacin rai ya sanya hannunsa tare fisgota daga kan gadon har sai da ƙashin ta yay ƙara.

Cije bakinta tayi bata son yin wani motsi saboda ciwon da jikinta yake mata, Nightgown ɗin tabi jikinta ta wani manne dukkan Jikinta ana gani ga fure fresh skin ɗinta sai glowing take.

Hannunsa ya miƙa dai-dai lokacin daya ɗauko allurar ta buɗe shanyayyun idanunsa wani irin zare ido tayi domin ba'a taɓa yi mata allura ba wata mugun jin tsoran allura take.

A sanyaye a hankali kuma ta shiga girgiza kanta har lokacin kuma bata kalli fuskarsa ba, jikinta na rawa ta ɗaga ƙafarta zata gudu da wani saurin ya sanya hannunsa ya fisgota ta zuwa jikinsa....




Free pages sun kusa kammala🤗 kada ki siyi littafi na idan kin san zaki fitar banwa kuwa dole ba please.



*TSINTACCIYA*  

NRML GRP: ₦300

VIP :500 SAFE YAMMA POSTING.

0116886423 SULAIMAN NA'IMA S UNION BANK EVEDANCE OF PAYMENT 08119237616



*🔥FITATTU HUƊU🔥*

      

BAƘAR FATA

Autar manya


SULTAN

mss flower


DATTIJON ARZIƘI

Real ladingo


Gaba ɗaya 800

Via 6850917335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman Fidelity Bank, masu tura kati 08167888934 ga ƴan uwa na Niger +22796515805 za ku tuntuɓa. To show evidence of payment 08142105218



 *AUTHOR NOTE*

_muhimman pages da romantic page suna cikin paid Page's kawai wannan matakin labari ne Wannan😁And wanda suka biya NRML GRP wallahi Azeem posting ba kullum ba, today posting tommorow babu😉kada kuce ban faɗa ba, Vip ko kakkaɓe zani za kusha karatu😍🤷🏾‍♀️_





   

   *SARAUTAR MARUBUTA*


*🌈TSINTACCIYA🌈*



FITATTU HUƊU🔥


Http://wa.me/+2348119237616


EPISODE7️⃣

Idanunta tayi saurin kullewa tana jin yadda haɗaɗɗan Baccarat rouge (Maison Francis) parfume ɗin sa ya wani daki hancinta, al'amarin daya haddasa mata lumshewar idanunta, jikinta na wani irin rawa domin this is the best time a tsayin rayuwata da  wani ya riƙe ta har ya sanyata a jikinsa so close to him, abin sai ya zama wani Extraordinary to her.

Ajjiyar zuciya ta sauke a hankali ta ɗaga hannunta da suka sauka a saman ƙirjinsa tana wani motsawa saboda zafi da zugin da ƙafarta ke mata yasa sam ba zata iya jure tsaiwar ba, a hankali ta fara yin ƙasa zata zille naman jikinta na wani irin motsi gaba ɗaya jijiyoyin ƙafarta har bawa suke saboda tsananin ciwo..

A karo na biyu Akeem ya ƙara ware gajiyayyun Maraitattun idanunsa tare da sauke su akan Akeela, wani irin lumshe idanunsa yay yana taune bakinsa ji yake kamar ya shaƙe ta ya wuta dama ganinta baki ɗaya a gidan.

Buɗe idanunsa yay yana jan wani mugun tsaki shi dai Abbunsa ya gama dashi, ganin yadda take ƙoƙarin zillewa daga jikinsa ya gently ya gyara tsaiwarsa, tare da ɗaga left hand ɗinsa ya wani manna shi a saman waist ɗinta slowly kuma ya haɗa ta da lafiyayyan jikinsa a hakan yana jin yadda naman jikinta ke rawa na tsananin azaba, cikin nutsuwa kuma ya fara murza Nightgown ɗin dake jikinta da sauri ta buɗe lumshasshun idanunta for the frist time ta sauke idanunta akan kamilalliyar fuskarsa.

Wani irin ƙyakƙyawan bugawa Zuciyarta tayi, zata iya cewa bata taɓa ganin Mutum mai mugun kyau kamar Abdul-hakeem Bukar Bello ba,  ƙwayar idanunsa kaɗai zata zautar da mace dalilin daya sanya koshi karan kansa ba kowa yake kalla da idanunsa ba, fuskar nan kamar tai tsartuwar jini saboda wani irin fari da yake da shi, ga wani haɗaɗɗan kewayayyan ƙwantaccen sajansa wanda ya taho da sumar kansa ya ke waye fuskarsa dashi da wani gashin baki amma akwai gemu da saje mai ɗaukan hankali.

Ga bakinsa kamar na mace Ƙarami laɓɓansa masu kauri jajaye wani yirrrrr dasu very cute and softness.

Da sauri ta rufe idanunta domin ba zata iya ci gaba da kallonsa ba wani mugun tsoransa ta keji, laɓɓanta ne suka shiga rawa gaba ɗaya suka jiƙe da yawo a karo na farko ta fisgi kalmar "Uhm..dan Allah kada kayi min zan mutu uhm" ta faɗa tana runtse idanunta sosai bugun Zuciyarta na ƙaruwa.

Taɓe bakinsa yay irin ko a jikinsa ɗin nan kima mutu waye yay asara, gumi ne ya shiga tsastsafo mata a tsakiyar goshinta tsakaninta da Allah take gudun allura, jin yaci gaba da murza rigar jikinta yana son fito da ass ɗinta waje yasa ta matse jikinta domin bata taɓa ganin sabon iskanci irin haka ba sai yanzu ko hannu ba'a taɓa riƙe mata ba, da sauri ta sanya tattausan tafin hannunta wanda ya jiƙe da gumi ga wani irin ɗumi da yake da shi ta riƙe hannunsa tana girgiza masa kanta kamar wacce take shirin shiɗewa tace.

"Dan Allah banso, kaji...uhm kada ka kalli jikina"

Wani zaro idanu waje yay wato saboda jikinta take wannan abin jikinta ɗin banza yay uwar me dashi, village gal like her ma harta san wani ɓoye jiki.

Wani cije lips ɗinsa yay yana ƙara haɗata ta  da jikinsa domin bai zo nan dan kallan wani part of her body ba, banda ɗoyi Meye ma jikin yake yanzu ma sai yaje yay wanka ysin.

Wata Ɓoyayyiyar Ajjiyar zuciya ta sauke tare da ware dukkan hannayenta ta wani zura su ta tsakanin hammatar sa ta wani irin ƙanƙamesa sosai lokacin daya caka mata allurar cike da zallar mugunta.

Cije bakinta tayi jikinta na rawa kafin ta wani fashe da maraitaccen kuka mai ratsa zuciya tare da kifa kanta a ƙirjinsa, ba taɓa sanin akwai mugunta irin haka ba, ana faɗin zafin allura bata taɓa sanin haka allura keda mafifaffan zafi ba sai yanzu, ji tayi ta ƙara jin haushinsa bata sanshi ba amma daga jiya zuwa yanzu yay mata abinda ko maƙiyinta ba lallai yay mata shi ba.

Ajjiye emtyn injection ɗin yay tare da sauke fuskarsa a tsakanin wuyanta cikin wata kasalalliyyar murya mai ratsa zuciya yace.

 _“I would rather waltz with the devil of loneliness than tango with a devil like you. I hate you.”_ ya faɗa yana wani jan numfashi tare ƙara sauke kansa a wuyanta cikin wata husky voice idanunsa na wani ruwa ruwa yace.

_“Do you know the real meaning of the world Selfish? Take a look into the mirror and you will find out. I hate you_, ke selfish ce kin kashe min ƙani ke gaki nan You still alive kina shaƙar iskar duniya, _You killed my brother_ wallahi na tsane ki bana son ko buɗe idanu na ganki _I hate you.. I hate you, I hate you! You stupid gal witch!!!_

Ya faɗa yana wani cilli da ita tare da hankaɗata baya Allah yasa da bed kusa da ita gaba ɗaya tai bed ɗin ta faɗa saman sa "Auchhhiiii!!" Ta faɗa tana tura ƙaramin bakinta gaba saboda zafin burgewar da tayi, abinda bai sani ba tunda yay mata allurar bacci yay gaba da ita, gyara kwanciya tayi wani nauyayyan bacci ya ɗauke ta.



Cike da zallar ɓacin rai yake taka ƙafafuwansa a nan Parlo ya samu Abbu da Ummi da Mami harda Didi wacce bacci ya ɗauke ta a saman carpet bakinta ɗauke da ƙashi tana tsotsa.

Kai tsaye upstairs yay yana wani irin fitinannan taku kamar wani ɗawisu,  kai tsaye bathroom yay tare da  zame jallabiyar jikinsa akan wannan Village girl ɗin yay late a wajan aiki.

Wanka yay ya fito ɗaure da towel kafin yay ɗauki handrayer ya fara gyara sumar kansa, lotion mai ƙamshi ya shafa a saman fatarsa kana ya ɗauki body spray ya fesa, nan da nan sumar kansa ta kwanta luff har wuya jan laɓɓan nan suka ƙara yin yirrrrr dasu.

Wajan closet ɗinsa ya nufa ya ɗauki Sunset Suit Nevy blue ya sanya kana ya ɗura jacket a sama kafin ya sanya white necktie.

Wani half cover shoe ya sanya black kafin ya ɗauki briefcase ɗin sa, wayoyinsa ya ɗauka ya sanya a aljihu gently ya fita daga part ɗin yana tafe yana duba Rolex ɗinsa na Companyn Patek philippe.

Lokacin daya fita bai samu kowa ba sai Didi wacce take bacci kai tsaye fita waje yay dai-dai lokacin da P.a ya shigo bai tsaya amsa gaisuwar P.a yau da kansa ya buɗe ƙofa ya shiga back seat ganin hakan yasa P.a yiwa motar key ya fita da gudu.

Kai tsaye Audi baƙo way suka nufa inda *AKEEM BETTER FARMING INSTITUTE A.B.F.I* Babban waje ne babba  babu mai iya ganin girmansa domin makaranta ce guda ta kuyar da aikin noma, da kuma taimakon mutane, kai tsaye sashin ma'aikata yay tun daga reception aka fara gyarawa ga Hero nan, ga Hero nan hannu kawai yake ɗaga masu har ya isa Elevator yana tsaye kafin ta buɗe ya shiga lift ɗin ya danna 8floor a dai-dai 8floor ɗin ta tsaya ya fito ta office ɗin Md Adnan ya fara shigewa yana wani irin runtse idanunsa sosai.

Kafin ya nufi office ɗinsa wanda aka rubuta Ceo haɗaɗɗan office ne mai kyau da tsari domin hadda ƙaramar cineme da deep frizer ga wasu a.c masu kyau.

Kujera yaja ya zauna a hankali ya buɗe System ya fara aiki.

Ya jima yana dannawa kafin ya ɗauki telephone line ya danna wasu Numbers ɗagawa akai cikin girmamawa akace.

"Mun ɗaga kira daga sashin karɓar ƙorafi Tayaya zamu iya taimakawa maka Dr Abdul-hakeem Bukar Bello Ceo? Lumshe idanunsa yay yana sauke numfashi kamar bazai magana ba sai kuma yace "Uhm Something new?" Cikin nutsuwa matar tace "Yes sir! Mun ƙara samun takardar ƙorafi daga Ƙauyen Wudil  akan matsalar ƙwace masu gona, zuwa yanzu Mutanan sun fara yi masu ta ƙarfi"

Tsayawa yay daga danna keyboard ɗin ɗin tare da sauke hannunsa a fuska yana shafa gemunsa cikin ƙasa da Murya yace.

"Uhm! Su waye ne?" "Binciken da mukai ya tabbatar da cewa wasu Manyan shugabannin ƙasa ne suke sun yin kwacan Wannan gonakin domin su kafa wani company kuma an tabbatar da cewa Wannan company na magani za suyi kuma irin haramtattun Drugs ɗin nan masu kashe mutane, suna son yi a Wudil saboda ruwan dake wajan zai hana aji wari da kuma shaƙar hayaƙin maganin"

Miƙewa yay tsaye ba tare da yace komai ba ya kashe wayar baki ɗaya.

Daga 8floor ya sakko zuwa reception a nan ya samu p.a fita yay daga cikin sashin gaba ɗaya ya nufi ɓangaren koyar da ilimin noman.

Tafiya yay mai ɗan nisa kafin yazo ƙarshen wajan wani ƙaton fili ne a ƙalla za'a iya gida sama da ashirin ga wasu ƙanan kurayen ganye sun fara fitowa alamar shukar ta fara huda.

ga yara a wajan da manya hadda ƴan primary school, cikin nutsuwa ya zare takalman ƙafarsa tare da naɗe hannun rigarsa cikin gonar ya shiga tare da ɗaukan Adda ya fara yanke ciyawar da tai tsayi ganin hakan yasa gaba ɗaya yaran suka fara yin aikin da yake.


**********************  ⬇ **************************

**********    Ai Hausa Novels  ****************

*************************⬆ **********************


DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.


Visit > https://www.aihausanovels.com.ng


Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

 

Email > aihausabooks@gmail.com


******* FOLLOW US ******


Facebook: Ai Hausa Novels


Twitter: Ai Hausa Novels


Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels




Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.


**********************  ⬇ **************************

***************   Ai Hausa Novels   ****************

**********************  ⬆ **************************


  *_littafi na paid book ne, 500 for vip 300 for nrml grp idan zaki siya dan ki fitar na yafe😂🤷🏾‍♀️_*


Http://wa.me/+2348119237616


A can gida kuwa Didi ce ta fito daga cikin gidan zuwan compound da sauri Bala driver ya ƙarasu tana ganinsa tace "Bala maza buɗe min mota" buɗe bayan motar yayta shiga kafin ya tayar da motar gatekeeper ya buɗe masu da sauri suka fita suna fita motar Abbu na shigowa.

A hankali Driven sa yay parking ajjiye jaridar daily trust ɗin hannunsa yay ya fito yana gyara zaman babbar rigarsa kai tsaye cikin babban parlo ya shiga da sauri Amani dake zaune ta riga da wando tana shan chocolate da ice cream ta miƙe tana faɗin "Oyoyo Grandfa"

Ɗaukan ta yay yana faɗin "eyee matar mai kama da Hero" Murmushi tai masa kafin yace "how was your school?" Tana sauka jikinsa tace "Allahamdulillah Grandfa" ganin babu kowa a Parlo ya san kuma su Aleema basu dawo ba kai tsaye ya nufi part ɗin yaran nasa yana sakin wani irin Murmushi domin ya azabtu da rashin ganin Akeela sosai.


Didi na cikin motar Bala driver yace "Hajiya Didi ina zan kaiki?" Kyaɓe fuska tayi tace "ofishin hisba" jinjina kai yay babu jimawa suka ƙarasa da sauri har tana ƙoƙarin faɗuwa ta shiga ciki tana shiga wajan mutane uku suka miƙe da sauri tace "A'a yaya..nace yaya haka kamar dai ana yaƙi bana son gantali babu ruwana wajan ogan ku nazo" ɗaya daga cikin su yace "Hajiya gani" wani kallo tai masa tace "Malam ogan ku nace yaya zakai min tsaye kamar sandar rake" wani ne yace "shine ogan" haɓa ta riƙe tace "Muhammadur Rasulullah S.a.w a'a babu ruwana akace hisbar malamai ne anya Wannan ya iya fataha ma, Tuf astagafirullah ai karatu kuma dai azuci yake Malam ƙara na kawo" Kallonta yay sosai kafin yace "ok Hajiya tame" fashewa tayi da kuka tace "Ubangiji dai ya haɗani da gantalallan jika abin yay masa yawa ga sata ga maita"

Cikin nutsuwa Abbu ya tura ƙofar ɗakin tun daga door way ya fara jiyo sautin shassheƙar kukan ta, da sauri ya rufe ƙofar tare da shiga ciki.

Tana zaune tayi wanka sanye take da Black Silk short robe sai wata Halter top data ɗura a sama, ta rufke gashin kan nan nata da ribbon ya sauka har baya sai ƙamshi take, wani irin harbawa zuciyar Abbu tayi kamar wanda ake ja da mayan ƙarfe haka ya nufi inda take ba tare da zato ba Akeela ta jita akan....



Me Abbu yake nufi ne😂😂 na kusa gama free pages tabbas daɗi na neman yi maku yawa.



*TSINTACCIYA*

NRML GRP ₦300

VIP: 500 SAFE YAMMA POSTING

0116886423 SULAIMAN NA'IMA S UNION BANK EVEDANCE OF PAYMENT 08119237616


*NOTE*

NRML GRP POSTING BA KULLUM BA🤷🏾‍♀️ IDAN ZAKI SAI BOOK ƊINA DOMIN KI FITAR NA YAFE NA FAƊA MAKU ZALLAR SOYAYYA NE A WANNAN BOOK ƊIN MAI TSAYAWA A ZUCIYA.



*FITATTU HUƊU🔥*


BAƘAR FATA

AutaR ManyA


DATTIJON ARZIƘI

Real ladingo


SULTAAN

Mss flower


gaba ɗaya ₦800

Via 6850917335 Na'ima Shu'aibu sulaiman fidelity bank masu tura kati 08167888934 ga ƴan uwa na Niger +22796515805 zaku tura Evedance of payment a nan 08142105218




  *SARAUTAR MARUBUTA*

*🌈TSINTACCIYA🌈*


FITATTU HUƊU🔥


Http://wa.me/+2348119237616


EPISODE8️⃣

Cinyarsa! Wata ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya mai sanyi Abbu ya sauke yana lumshe idanunsa, da sauri Akeela ta ɗaga jiƙaƙƙun eyes lashes ɗinta zuwa sama kafin a hankali ta buɗe idanunta tare da sauke Kallonta a fuskarsa Abbu wacce take dab da tashi.

Wani sassanyan Murmushi ya sakar a hankali kuma cikin sakin fuska yace..

"Babyna Daughter na"

Ƙuri tayi masa da idanu, saboda kamarsa da Mutumin ɗazo, she's a cleaver gal amma muguwar taɓararriyar mai saurin kuka, ko dan yawan ciwonta ya sanyata kuka ohhhu?!

Tana da ilimi sosai musamman na addini bata wasa da sallah sam komai tana da tsari.

Murmushi Abbu ya sakar mata yana shafa sumar kanta dai-dai fuskarta yace.

"You're wake up Babyn Abbunta how do you feel now? Ya jikin?" Ya faɗa yana manna mata kiss a goshinta a hankali ta zame jikinta daga kan cinyarsa tana ɗan marai-raice fuska kamar zatai kuka da sauri tace "no don't cry kinji" kai ta ɗaga masa tana lumshe idanunta can kuma ta buɗe murya can ƙasa kamar bata son yin magana tace "uhm who are you?" Shafa cikinsa yay kafin ya gyara zamansa tare kama fararan hannunta wanda suke da mugun taushi kamar auduga yace.

"Ok let me introduce myself to you" shiru yay yana kallon tana jin wani irin masifafan yanayi a kanta kafin ya numfasa yace.

"I'm Abubakar Bello, but some of people knowm me as Bukar, I'm the second born Of my parents, ina da big bro but he's passed away wajan shekaru masu yawa, babban yaya ne shine your father, Isma'il Bello kenan, we lost our father good 30yrs kenan, ina tare da my mother we called her Didi zaki ganta kamar su ɗaya da Aleema, seriously i love her irin sosai ɗin nan more than anything dake nan duniya, bayan ita ina da yara 4 my first son ɗina yafi komai muhimmacin a rayuwarta his name is Abdul-hakeem Bukar Bello zaki iya cewa Yaya, ko hero ko Hamma like yadda Fulani suke faɗa, sai Adnan we lost him shima amma komai ya faru it was a destiny, sa kuma Aleema sai auta Afaf amma yanzu bani da wata Auta sai ke Babyn Abbunta" ya faɗa yana jan hancinta, ɗan Murmushi tayi wanda yasa numfashin Abbu kusan ɗauke wa, domin wannan Shine karo na farko da tayi Murmushi wanda ya haddasa lomawar dimples ɗinta tare da teeths gave ɗinta wacce take siririya sosai,  numfashi ya sauke yace.

"Ina da mata guda biyu ta  farko sunanta Ayusher we called her Ummi, sai Khadijertou muna ce mata Mami, Nayi karatu mai yawan gaske, ni mai kuɗi ne the richer old man, ada nayi siyasa sosai amma yanzu na sauka, yanzu ina business ne ina da Manyan companies a nan 9ja da kuma ƙasashen waje, ina da manyan contact, ƙwangila kala-kala Allahamdulillah ina duba na ƙasa na ina taimako samuna bai tashi a banza ba, and duk da hakan komai na gidan nan Akeem ke yinsa baya using Kwabo nawa tashi yay ya nema duk yawan dukiyarsa shi ya nema da kansa babu sa hannu na, yana da faɗin rai koni sai nayi da gaske nake juya sa dan yana mugun suna ne yana da biyayya yana da ilimin addini fiye da tunanin mutum I'm so proud of him Wannan shine kawai"

Kallonsa tayi ba tare da tace komai ba shi dai yaji daɗi yana da kirki amma wannan ɗan nashi bashi da mutunci ko kaɗan, har yanzu ta kasa mance abinda yay mata har yanzu kuma tana jin ƙamshin turarensa a jikinta kamar zai zautar da ita.

Bata san mene yasa ba sai kawai ji tayi kuka ya kwace mata, da Sauri Abbu yace "Subuhanallah what happened ina ke maki ciwo" girgiza masa kai tayi tana kwaɓe fuska tare da tura baki gaba "Okey tell me mene ne?" Cikin shassheƙar kuka tace "Baffa na bai so na, he doesn't care about me zai haɗani da wani mai fitsarin ƙwance and ƴarni ɗin nan zaiwa Aure uhm" ta faɗa tana ƙara fashewa da kuka ita tana ganin ai kamar abin kunya ne a gareta mutane suji za'ai mata Aure wata muguwar kunya ta keji kamar me.

Bakinsa ya buɗe yace.

"No one's forcing you to get you marriage Babyn Abbu Autata Ohyyyah come here" ya faɗa yana jawota jikinsa tare da fara rarrashinta wani sabon sonta ya ratsa mata zuciya.

Akeela kam ganinsa take tamkar Baffanta Musamman da taji yace shi ƙanin Baffan tane.


Gyara zama Didi tayi tana kallon mutumin tace "Shikenan lashe baki yana tsotse laɓɓansa dan Allah Wannan ai sai ya jamin abin faɗa ko ba haka ba?  Mugun hali kuwa bai bar kuwa ba ranar nan balango nace ya siyo min yaƙi to dan Allah ina imani a nan? Taimako nefa abin ma da dukiyar tasa babu san tayaya akai ya rata ta ba, ai ba kayi magana ba ace Hassada bace ba" ta ƙare maganar tana goge hancinta gaba ɗaya mutanan wajan Murmushi suke domin sun fahimci kawai rikicin tsofa ne murmushi mutumin yay kafin yace "In sha Allah Hajiya babba zamu kirasa" da sauri tace "kuce Ubanwa ya faɗa maku a'a babu ruwan ai assurru ma'al sirri koba gaskiya ba, kawai ai faɗa masa ko dan tsire da kaza mai zafi ce yana kawo min" jinjina kai yay yace "to shkknan yadda kikace haka za'ai" tashi tayi Bala driver yana biye da ita a haka suka nufi mota tana shiga ya jata zuwa gida.


A wajan 6 na yamma motar Akeem tayi parking a parking space, P.a ne ya fito tare da buɗe masa ƙofa, gently ya fito da ƙafarsa yana wani lumshe idanunsa tare da sauke ajjiyar zuciya a hankali yake motsa bakinsa yana tasbihi a ransa, ya gaji sosai domin rabin aikin a hospital yay ga program ɗin da zai fara a M.hausa  channel, a hankali ya wani ya motsa fuska yana cije bakinsa wani siririn tsaki yaja ganin kallon da P.a ke masa dariya p.a yay kafin yace "Sorry sir" banza yay masa yana shigewa cikin gidan, juyawa p.a yay zuwa gida.

Lokaci daya shiga Afaf ce a Parlo da Aleema sai Akeela dake kwance saman duguwar sofa tana bacci gashinta duk ya rufe mata fuskarta, ga  wani ƙaramin Teyana wide-leg trousers dake jikinta sai Applique logo detail t.shirt jikin nan nata sai glowing yake.

Wani series film suke kalla mai suna My perfect husband a zee world.

Da sauri Afaf tace "Wlcm Hero" harara ya watsa mata cikin sauri ta ɗauki remote tare da kashe kallon.

Ɗauke kai yay ya nufi upstairs, yana shigewa Akeela ta sauke ajjiyar zuciya yana dafe ƙirji dariya Aleema tayi tace "Laa! so you're pretending kenan ai kam zan faɗa masa" kwaɓe fuska tayi tana langwaɓar da kanta gefe alamar "No" ba tare da tace komai ba kuma.

Wanka yay ya sauya kaya zuwa Racing jersey da tracksuit trousers, a hankali yake sakkowa daga steps ɗin benen idanunsa a lumshe yunwa ya keji sosai sai baza ƙamshi yake yana tafiya kamar so, kai tsaye kitchen ya nufa domin samun mayen nasa Coffee da ice cream domin ya duba gaba ɗaya ya shanye ice cream part ɗinsa, yana shiga ya rufe ƙofar kitchen ɗin tare da jingina da jikin ƙofar ya harɗe hannayensa a ƙirjinsa.

Tana tsaye a kitchen ɗin tana haɗa tea sai zabga madara take a mug ga kyawawan ƙafafuwan ta a waje ƙafarta sanye cikin wani slippers ga laft tummy ɗinta a lafe ya ƙara fidda shape ɗinta, a sanyaye take komai kamar bata so tana gamawa ta ɗauki mug ɗin tana juyawa idanunta ya sauka a kansa tsananin tsoro da gigicewar da tayi yasa gaba ɗaya ta saki mug ɗin cikin rashin Sa'a gaba ɗaya tea ɗin yay masa ka! Nan da nan fuskarsa tai ja idanunsa ya ƙanƙance ya wani haɗe fuska ta mau a hankali kuma ya fara takawa zuwa inda take tsaye....




*TSINTACCIYA*

NRML GRP ₦300

VIP: 500 SAFE YAMMA POSTING

0116886423 SULAIMAN NA'IMA S UNION BANK EVEDANCE OF PAYMENT 08119237616


*NOTE*

NRML GRP POSTING BA KULLUM BA🤷🏾‍♀️ IDAN ZAKI SAI BOOK ƊINA DOMIN KI FITAR NA YAFE NA FAƊA MAKU ZALLAR SOYAYYA NE A WANNAN BOOK ƊIN MAI TSAYAWA A ZUCIYA.



*FITATTU HUƊU🔥*


BAƘAR FATA

AutaR ManyA


DATTIJON ARZIƘI

Real ladingo


SULTAAN

Mss flower


gaba ɗaya ₦800

Via 6850917335 Na'ima Shu'aibu sulaiman fidelity bank masu tura kati 08167888934 ga ƴan uwa na Niger +22796515805 zaku tura Evedance of payment a nan 08142105218




  *SARAUTAR MARUBUTA*

*🌈TSINTACCIYA🌈*



FITATTU HUƊU🔥


Http://wa.me/+2348119237616


EPISODE9️⃣

Jikin Akeela na wani irin ɓari tayi baya tare da manne bayanta a jikin canter ɗin kitchen ɗin ta wani matse idanunta, laɓɓanta na wani irin Kaɗawa tana taune su gaba ɗaya ta jiƙasu da yawo, rawar da jikinta yake ya ƙaro.

A hankali Akeem yake takuwa zuwa inda take fuskarsa a haɗe tamau babu walwala sai ƙwantaccen sajansa dake ta sheƙi tsaye yay a gabanta yana ƙare mata kallo, ƙara matsawa yay kusa da ita very close to her har tana jin yadda Numfashinsa ke fita ga mayataccen ƙamshin turarensa dake dakar mata hanci.

Kamar zai matseta haka ya tsaya a gabanta kafin a hankali ya ɗaga ƙafarsa tare da sauke ta a saman ƙafarta ya wani irin murzawa.

Innalillahi wani irin azaba ta ratsa mata jiki har tana jin yadda ƙashin yatsunta yay ƙara baki ta buɗe zata kuka yay saurin sanya hannunsa tare fisgota jikinsa ya haɗata da Physique chest ɗinsa ya matse ta sosai cikin wata lallausar Muryar mai amsa kowa da sanya mutum zullumi da tarin fargaba yace.

"Shittt!!! Kul Kimin kuka" wani irin matse idanunta tayi  wani kalan tsoran Akeem take kamar mutuwa haka take jin tsoransa komai nasa da banne look what he did to her amma yana cewa kada tayi kuka gashi still ƙara murje yatsun ƙafarta yake.

Hannunsa guda ya ɗura akan waist ɗinta ya ƙara holding jikinta a nasa very tight. Ɗaya hannunsa kuma yana kan laɓɓansa daya nuna mata alamar tayi shiru ɗib tai shiru kamar ruwa ya cinyeta amma jikinta yana wani irin vibration, ga wani masifafan ƙamshin turarensa wanda yake sanyata jin bacci zuciyarta na wani irin bugu beating fast fast har Akeem na iya jin yadda ƙirjinta ke ɗagawa, ko da wasa ko baiyi tunanin kallon wajan ba domin babu haka a ransa..

Ƙara murje yatsun yay da sauri ta buɗe idanunta tare da buɗe baki tace "Auchhhiiii wayyooo Baffana" ta faɗa tana girgiza kanta tare da motsawa zata gudu daga jikinsa yadda kake tsoransa zaka ɗauka ma'aikatan ɗaukan rai ta gani.

Hannunsa dake saman lip's ɗinsa ya zame tare da sanya hannun ya tallafo haɓarta zuwa wajan fuskarsa fuskar nata yay so cute a hannunsa musamman eyes lashes ɗinta masu mugun tsayi da yawa.

Cikin wata husky kamar wanda akai forcing nasa dole yay maganar yace "kee!!" Da sauri ta buɗe idanunta  tare da sauke Kallonta a gashin ƙirjinsa dake kwance fuska ya ƙara haɗewa kamar zai fashe yace "look at into my eyes witch" girgiza kanta tayi tana ƙoƙarin sakar masa kuka cikin wata ƙaramar tsawa yace "heeey!!" Muryarta na rawa tana ƙanƙanme jikinta waje guda tace "Am sorry but I can't do this" lumshe idanunsa yay sosai yana jin wani abu mai kama da mugunta na taso masa a hankali kuma ya buɗe idanunsa tare da sakar mata wata gigitacciyyar tsawa haɗi da faɗin "keee" Innalillahi tsawar da tayi mata yawa ne da kuma rashin sabo da tayi da ita haɗi da gigicewar da tayi yasa kawai ta faɗa jikinsa ta wani ƙanƙamesa tana sakin maraitaccen kuka haɗi da faɗin "am sorry ha....ban sakewa Hamma Akeemmm!!" Ta jaa! Sunan nashi ta rufe fuskarta a tsakiyar ƙirjinsa gaba ɗaya jikinta rawa yake sosai.

Gaba ɗaya ta firgita da tsawar da yay mata domin tunda take a rayuwa babu wanda ya taɓa yi mata something like this to wama ta sani gaba ɗaya even friends Wannan bata dasu ita ɗaya take rayuwarta ita kam da zama a wajan mutum irin Akeem gwamma ta koma inda ta fito.

Sauke numfashi yay tare da jan wata iska zuwa cikin hancinsa, yadda Jikinta ke rawa yasa gaba ɗaya take neman yarda su a ƙasa, taƙi yarda ta buɗe idanunta balle ga kallesa sai tura fuskarta take cikin ƙirjinsa.

Wani irin taɓe baki yay kafin yay baya kaɗan tare da jingina da canter cikin wata kasalalliyyar murya can ƙasa yace "Uhm hold me tight kafin na ɓallaki" jin haka yasa ta ƙara tura hannunta in between his hammata tana ƙanƙamesa sosai kamar zata koma cikinsa, ganin yadda ta rungomesa irin rungumar nan ta neman tsira da rai rungumar da babu wanda ya taɓa yi masa ita sai Amani yasa ya wani shafa sumar kansa kamar bazai magana ba sai kuma yace.

"Duk abinda nace kice You are" da sauri ta ɗaga masa tana ƙoƙarin zame Jikinta daga nasa yace "don't ever try" dole ta koma tare da kwantar da kanta a ƙirjinsa tana sauke numfashi a wahalarce.

Gyara tsaiwarsa yay Muryar nan nashi kamar ana buda algaita yace "witch" bakinta na rawa tace "i am" tsaki yaja yana ƙara murje yatsun ƙafarta yace "pairy, mumu jakaness, emty head" wani runtse idanunta tayi sharrrr kuma hawaye suka zubo mata muryarta na rawa tana son fashewa da kuka tace "i am" shafa lafiyayyiyan gemunsa yay yace "aljanar ruwa, Kidnapper mai cin naman mutane ƴar yankan kai" kuka na kwance mata tace "i am" wani shu'umin Murmushi Yay Wanda ya jima bai irinsa ba kafin yace "Uhmm mai warin hammata" wani raunataccen kuka ta fashe da shi tama kasa magana hannunsa yasa ya zareta daga jikinsa harya juya sai kuma ya dawo ya ɗauki mug ya fara haɗa coffee ko inda take bai ƙara kalla ba, yanzu haka sai yay wanka domin shi da gaske warin take masa sbd rashin tsoran Allah irin na Abdul-hakeem Bukar Bello.

Ya gama haɗa coffee ya nufi wajan ƙofa tafiyarsa ma kaɗai abar kallo ce har zai fita sai kuma ya tsaya cikin wata kakkauran murya yace "ki faɗawa wani kiga sai na bawa karnuka sun cinye namanki" yana faɗin hakan ya fita.

Zubewa tayi a wajan tana sakin wani sabon kukan gaba ɗaya taji ta fara tsanar zaman gidan saboda shi.

Yana fitowa idanunsa ya sauka akan Didi tana zaune saman kujera an ɗura ƙafa ɗaya kan ɗaya tana ganin ta washe baki "kaga irin albarka, kai dai kaji daɗin ka tausayinta kaɗai yasa a soka baka da ƙyashi ko kaɗan shiyasa nace babu wanda zan faɗawa zaka siyo min nama, ato kaf Duniyar nan wa kake dashi mai sonka da sanya maka albarka ai sani ɗin dana zame maka dole na haifi gantalallan Ubanka" banza yay mata yana zaman kan sofa a hankali yake sipping coffee ɗin a bakinsa, Ummi ta fito daga part ɗin Abbu yana biye dashi da alama alwala yay idanunsa ya juya ganin babu Mami yasa ya nufi part ɗin ta.

A can cikin bedroom ya sameta zaune ta zabga tagumi idanunta yay jajir a gefenta ya zauna yana Kallonta a hankali itama ta kallesa kafin kuma kuka ya kwance mata bakinsa ya buɗe yace "come here" da sauri ta ƙara jikinsa tana fashewa da kuka sosai, bai hanata ba sai da tayi mai isarta kafin yace "Mami nasan dole kiji zafi domin ke ɗin uwa ce, duk yadda zanji ciwon abin ba kamar ke ba, amma wallahi bana baccin kirki kullum da damuwa nake kwana, ya Adnan yake? Wanne hali yake ciki? Yana raye? Baya raye? No one's know, amma dukkan abinda ya samu bawa rubutacce ne daga Rabbil izzati mai kowa da komai, ko da ba'a ce ruwa ya faɗa ba Tabbas zamu nemesa mu rasa, amma har yanzu jikina yana bani Adnan yana raye koma zai dawo garemu in sha Allah, so kiyi hqr kiyi accepting Wannan destiny ɗin you're muslim a musulmi should trust ƙaddara good or bad ok!" 

Kallonsa tayi kamar yadda yake kallonta kafin tace "Abbu ina jin babu daɗi ƙwarai rashin ɗa ba ƙaramin abu bane, kullum ina addu'ar Ubangiji ya kare min Adnan aduk inda yake,amma idan na kalli wannan Yarinyar zuciyata zafi take inside of kai punishing ɗinta akan dalilinta muka rasa Adnan amma ka ɗauke ta ka sanyata cikin yaranka me kake expecting idan wani abu ya samu ɗayan su?" Tunda ta fara magana yake kallonta kafin yace "jinina kike son na wulaƙanta Khadijertou? Ɗiyar yayana Baffa zan ci zarafi, ko bayan raina nasan Baffa zai kula da komai na iyali na mene yasa kike son ni naci zarafin tasa ƴar ƙwaya ɗaya tilo? Please bana so ki barni da masifar da take shirin kunno mini please" shiru tayi masa tana sauke ajjiyar zuciya, Miƙewa yay da ita kafin yasa hannu ya share mata hawayen cikin damuwa yace "Ni Ubane kuma mijine mai adalci, amma hakan ba zai sanya naƙi bin abinda zuciyata keso ke muradi ba" da rashin fahimta Mami tace "Me kake muradi Abbu" hancinta yaja yace "time zaizo Ohyyyah go and pray"  "bana yi" zare ido yay yana faɗin "eyee baƙin ciki ido biyu Allah ya Bukar Bello ba'a ɗakin Mami yake ba dana shige" ya faɗa yana ficewa.

A hankali Akeem ya miƙe kai tsaye suka nufi Masjid suna fita Akeela ta fito da sauri idanunta duk yay jaa sosai ga lip's ɗin nan yay wani pink yirrrrr dashi.

Didi ce ta tafka satali tace "Innahu sulaimanu wa Innahu Bismillahi Meye haka kamar wata munafuka kuma jama'a na shiga uku ke zonan" kwasa Akeela tayi da gudu tana nufar part ɗinsu dan Didi ta iya bala'i da surutan tsofa.



ABUJA

*Aso Rock Presidential Villa*

A hankali ya murɗa handle ɗin ƙofar ya shiga cikin wani makeken bedroom kusan dai gidan Shugaban ƙasa wasting time ne tsayawa description nasa just imagine.

Tsayawa yay yana ƙare mata kallo kafin a hankali yace "Meema" shiru tayi kanta a ƙasa ta tura hannunta a tsakanin cinyoyinta sai sauke Ajjiyar zuciya take..

Wata macace zatai sa'ar Akeem shekarunta kusan 32 amma idan ka ganta zaka ɗauka bata shige 25 ko 26 ba tana da kyau sosai fara tass da ita gashinta ya sauka sosai..

Ganin yadda tai masa shiru yasa ya girgiza kai tare da faɗin "ohh Rabbi ka kawo min ɗauki" ya faɗa a hankali ya gyara zaman babbar rigar jikinsa babban mutum ne shekara wajan 65 to 67 fari ne kamar Balarabe wajanta ya ƙarasa yana zuwa ta ɗaga kanta a tsoro ce domin kullum cikin firgita take kwaɓe fuska tayi har zatai shiru sai kuma tace "Dad" gashinta ya tattare tsaf kafin ya sanya ribbon ya haɗe mata su yace "oyaa stand up" tashi tayi a hankali har yanzu idanunta a ƙasa yace "Your Mom told me har yanzu baki breakfast ba what exactly wrong with my darling eh?" Kwaɓe fuska tayi kafin tace "Dad how is he?" Dafe kai yay yace "Ya rabbi Wannan mutumin ba kuwa asiri yay maki ba Meema? Mun tsinci Mutum a hospital daga zuwa zaga marasa lafiya kince dole dole a ɗauke shi na ɗauke sa gashi can ana kula dashi amma dole sai an fita dashi waje" kamar zatai kuka tace "Dad why?" Shafa kanta yay yace "come with me"  Kallon Mahaifin nata tayi PRESIDENT AHMED ADIL  kenan.

Kama hannunta yay kai tsaye ratsawa yay ta haɗaɗɗan parlon yarinyar tasa kafin ya nufi wani corridor a nan zaka samu main Parlo iya kar haɗuwa ya haɗu wata mata ce zaune tana kallon Aljazeera zatai shekara 54  tana sanye da wata haɗaɗɗiyar shadda ko'ina na jikinta sheƙi yake ga wasu gold a hannunta murmushi tayi tace.

"Ok dake kaine ta kulaka ko yayi" Murmushi Dad yay mata kafin yace "Meema kullum jin kanta take wata ƴar baby look da aure tayi da wajan yara biyu uku har huɗu gareta" dariya Mom tayi tace "aifa" hannunta yaja yace "bari na karata wajan mutumin ɗan yanzu bazan ƙara barinta fita ba"

"Adawo Lfy Ur Excellency" fita yay kafin ya shiga Elevator kai tsaye kuma da shiga ya dannawa lift ɗin 1floor, tana kusa dashi sai Ajjiyar zuciya take saukewa a haka suka sauka jama'a kuzo kuga haukan securities sai ku ɗauka yaƙin duniya ake, da sauri aka buɗe masu ƙofar wata lafiyayyiyar mota, kai tsaye wani Aso Rock Clinic Gulps suka nufa motar guards na biye dasu.

Sun ɗan jima suna tafiya a cikin gidan kafin su ƙarasa gaba ɗaya guards ɗin sukai masu rumfa Meema dai sai ɓoyewa take domin tsoran mutane take sosai.

A haka suka isa wani Dr ya tarɓesu bayan President Ahmad Adil ya zauna ya dubi Dr yace "Yaya jikin nasa?" Ajjiyar zuciya Dr yay kafin yace "To da sauƙi amma he's in critical condition sosai" gaban Meema ne ya faɗi da sauri ta riƙe Dad kafin Dr ya ɗura da faɗin "He lost his memory and fuskarsa ma ta lalace baki ɗaya.....



_Ki guji haƙƙin wani domin bala'i ne wallahi sosai fa, idan kina son this book ki siya akan 500 ko nrml grp 300 nidai bazan yafewa dukkan wanda zai karanta bai biya ba haka kukai min akan ABU MALEEK_




*TSINTACCIYA*

NRML GRP ₦300

VIP: 500 SAFE YAMMA POSTING

0116886423 SULAIMAN NA'IMA S UNION BANK EVEDANCE OF PAYMENT 08119237616


*NOTE*

NRML GRP POSTING BA KULLUM BA🤷🏾‍♀️ IDAN ZAKI SAI BOOK ƊINA DOMIN KI FITAR NA YAFE NA FAƊA MAKU ZALLAR SOYAYYA NE A WANNAN BOOK ƊIN MAI TSAYAWA A ZUCIYA.



*FITATTU HUƊU🔥*


BAƘAR FATA

AutaR ManyA


DATTIJON ARZIƘI

Real ladingo


SULTAAN

Mss flower


gaba ɗaya ₦800

Via 6850917335 Na'ima Shu'aibu sulaiman fidelity bank masu tura kati 08167888934 ga ƴan uwa na Niger +22796515805 zaku tura Evedance of payment a nan 08142105218




  *SARAUTAR MARUBUTA*

*🌈TSINTACCIYA🌈*



FITATTU HUƊU🔥


Http://wa.me/+2348119237616


EPISODE 1⃣0⃣



            Kuka Meema ta sanya wanda ya ƙara tayar da hankalin President Ahmad Adil,cikin damuwa yace "he looses his memory? I understand,but problem ɗin fuskar fa? How long zai kasance cikin rashin sanin wane ne shi?"  Kafin Dr yay magana Meema tace "i don't understand Dad,loosing memory kamar ya?" Cikin nutsuwa Dr ɗin ya kalleta kafin yace "everyone forgets things atimes,how often have you misplaced your car keys or forgotten the name of a person you just met,some degree of memory problems as well as a modest decline in other thinking skills,is a fairly common part of ageing,there's a difference,however between nrml changes in memory and memory loss associated with alzheimer's disease and related disorders,and some memory problems are result of treatable condition Madam Meema Ahmed Adil" shiru tayi idanunta yay rau rau zai kawo ruwa kafin a hankali tace "kenan bazai iya tuna waye shi ba? Balle ya tuna abinda ya faru dashi,more explanation please" farin glass ɗinsa ya ɗauka tare da sanyawa cikin nutsuwa yace da Meema "he looses his memory,he can't remember anything about his life,and normal age-related kin gane ba? Memory loose doesn't prevent you from living a full productive life for example,you might occasionally forget a person's name,but recall it later in the day,amma tunawa lokaci guda it's difficult,you might misplace your glasses sometimes,or maybe you need to make lists more often than in the past to remember appointment or tasks. These changes in memory are generally manageable and don't disrupt your ability to work,live independently or maintain a social life" Dr ya ƙare maganar yana sauke numfashi baya jin hausa ko kaɗan hakan yasa dukkan wani bayani da zai yi dole sai dai yay da yaran nasara Ingilishi kenan.

Kasa magana Meema tayi bata san mene yasa ba amma wani mugun jin tausayin mutumin take kafin a hankali tace "alright yanzu dole sai the same abinda ya faru da shi ya sake faruwa zai iya tuna waye shi?" Ta faɗa abinda Dr ɗin ya faɗa,jinjina kai yay kafin yace "sure" miƙewa President Ahmad Adil yay yana kama hannun Meema kafin yace "Dr ka shirya komai na tafiyar cikin week ɗin nan za'a fita dashi" ya faɗa yana jan Meema zuwa waje,kallonsa tayi tana kwaɓe fuska kafin tace "Dad" ba tare da ya kalleta ba yace "what again Meema?" Idanunta na kawo ruwa tace "Dad i want see him please! Please Dad" tsayawa yay yana kallonta kafin yace "Look Meema wannan ba age ɗin soyayya dashi bane,infact kin girme masa respect yourself ok?" Ƙasa tayi da idanunta tana jin ranta babu daɗi kafin tace "Dad ni fa ba?" Tsareta yay da idanu kafin yace "kefa mene? Uhm gayan naji" girgiza masa kai tayi kafin tace "nothing" kama hannunta yay tare da shiga cikin mota securities suka rufa masu baya.

  Can cikin gidansa suka nufa bayan sun ƙarasa Meema ta fito da sauri ba tare data tsaya Dad ɗinta ba,murmushi kawai Dad yay domin hakan da tayi yasan fushi tayi.

  A bakin shiga lift ya sameta tana ganinsa tai saurin shigewa tana danna 3rd floor,rabuwa yay da ita ya nufi wata daban yana shiga ya danna shima,a parlor ya sameta tana maƙale jikin Mom tana surutai wanda ita kaɗai ta san mene take cewa,kallon juna sukai shi da matarsa kafin Mom tace "yanzu kuka fita lafiya amma ji har abin ya motsa" cike da so da ƙaunar ƴar tashi ya kalli Meema wacce zufa ke yanko mata sai surutu take ita ɗaya murmushi yay kafin ya ƙarasa tare da kama hannunta yace "Allah sarki Mamana,Ubangiji yana sane dake kinji nothing will happened to you again,ina nan kinji i'm always be by your side kinji" ya faɗa yana yin gaba da ita tare da nufar side ɗinta,suna zuwa ya zaunar da ita bakin bed kafin ya fara bin bedroom ɗin da kallo,a hankali ya ɗauki wayarta tare da kunnawa yace "ke ƴar gidan shugaba ce,President's daughter,ya kike son maida kanki middle class ne eh? U have to be classes lady irin manyan matan nan,ni da na keso ki fara fita kina rage min wasu manyan ayyukan tunda kinga ba ni da wanda zai taimake ni ba ni da wani babban ɗa,soon zaki fara fita zuwa wasu Company,wai ke nan sunan babbar likita,a haka zaki zama babbar baƙuwa a wajan taron sickler day ɗin,haaaa! Taɓ su Meema ƴan ƙasa na gari a nan tare dasu I.d card voters card anya kin taɓa voted na Dad ɗinki ma?" Murmushi tayi masa tana ƙwace jakarta bai kulata ba,a hankali ya zauna a gefe ganin wayar nata empty ba komai gata sabuwa dal iphone 13pro max,transfer kati yay mata na 50k kana ya sai mata data cikin sauri ya shiga play store tare dayi mata download na I.G whatsapp,twitter sai wattpad da okoda books tare da games da app na qur'an da azkar,buɗe mata komai yay da wani special name Meema_ President's daughter,wayarsa ya ɗauka tare da yi mata sending na picture ɗinta,ɗora mata shi yay saman profile kana ya bata yana faɗin "yanzu kika fito Mamana,oyah tashi ki fara duba wayanki gashi nan ki yi abinda kike so na tura maki 500k a acct naki" dariya ta masa tace "thank you Dad i love you" Murmushi yay mata yana miƙewa yace "love you too Meema,kinfa girma good 32 to 33 yrs amma abu ya saki gaba kamar yaƙi please ki yita addu'a,ki samu kiyi aure kamar ko wacce mace i don't know what wrong with your mother bata damu ba sam,ina cikin mutane hankalina na kanki ki taya ni kula da kanki,ahha! Ba na son facebook domin zaki iya gani ana zagin Dad ɗinki ranki ya ɓaci,ina yin abinda naga zan iya,amma kin san halin mulki,mai makon jama'a su tayamu da addu'a sai su bimu da zagi,bayan bama da laifi domin na saman su ke take komai,ki kula da kanki akwai guards naki guda ashirin duk inda zaki,make sure tare kuke,ok?" Jin shiru yasa ya juya,ashe tuni bacci ya ɗauke ta shi kaɗai yake abinsa,girgiza kai yay tare da ƙarasawa wajanta ya gyara mata kwanciya,a hankali ya shafa kanta tare da sumbatar goshinta,fita yay yana rufe mata ƙofar bedroom ɗin.

  Washe gari Dad da wuri ya fita zuwa wajan meeting wanda zai zauna da ƴan majalisu na dokoki wato _(National assembly)_ na ƙasa baki ɗaya,akan lafiya musamman ciwon sikila wanda ya zama kamar Annoba.

   A hankali Meema ta fito sanye da  silhouette da VGOLD palazzo trousers wanda yake da faɗi sosai daga ƙasa kamar skirt daga waist ɗinta kuma ya ɗame ta irin sosai ɗin nan ba zaka taɓa cewa tayi shekaru har 33 ba,tayi rolling kanta da wani haɗaɗɗan vail,a hankali take tafiya kamar wata ɓarauniya tazo dai-dai parlor taji ance "mrng mai satar hanya" ajiyar zuciya ta sauke tare da faɗin "Mom" sai kuma ta juya tana murmushi,zama tayi tace "mrng Mom?" "Mrng how are you? Ina zaki haka ko breakfast baki ba?" Shiru tayi sai kuma tace "kamar nayi ko? A'a banyi ba,kai na yi" girgiza kai Mom tayi tana ajiye system ɗin gabanta,wato al'amarin Meema kullum ɓaci yake kamar da sauƙi sai kuma ta ƙara komawa ruwa "bama ki tabbar kinyi ba kenan ko,eh?" Taɓe baki tayi domin Mom faɗa gareta yanzu zata hargitsa ta,miƙewa tayi ta fice daga cikin gidan baki ɗaya.

  A can waje kuwa wata mota ta shiga cikin sauri guards suka nufota,da sauri ta ɗaga masu hannu driver yaja da gudu tana faɗin "aso rock clinic gulps za kai dropping nawa"  ta faɗi hakan tana buɗe network ɗin wayarta,kai tsaye wattpad ta shiga ta fara dube dube domin tun sanda Dad yay mata settings ɗin komai bata taɓa wayar ba sai yanzu,har ta shige wani book sai kuma ta dawo baya taga ansa _Our secret_ (Sirrin mu) shiga tayi tana zaune ta karanta Episode 1 to 5 lokacin da tazo wajan da Airah ta kewa Sheikh kiss kanta yay wani mahaukacin sarawa a firgice kuma tai wani irin....


Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post