Tsintacciya Hausa Novel Page 11-17

Tsintacciya Hausa Novel Page 11-17

Tsintacciya Hausa Novel Page 11-17

 🌈TSINTACCIYA🌈

 

FITATTU HUƊU🔥

 

http://wa.me/+2348119237616

 

 

    Special thanks to *_Hawwa'u My Real Smasher_*

 

 

EPISODE1️1️-1️2️

Dafe kanta Jikinta ya shiga mahaukacin rawa jijiyoyin kanta suka mimmiƙewa, wasu abubuwa suka fara gilmawa ta cikin idanunta a hankali kuma take lumshe idanunta cikin nutsuwa bakinta yake motsawa a hankali take furta _“Ya hayyu ya ƙayyumu”_ shine kawai abinda yake faɗa drivern ne ya ɗan tsaya da gudun da yake tare da juyawa ya kalli Meema cikin girmamawa da bata matsayinta yace "Madam is everything okay?" Jinjina masa kai kawai tayi a hankali tai baya tana kwanciya a jikin kujerar motar da sauri kuma ta ɗauki wayar ta tura ta cikin hand bag ɗinta.

Ganin sauyin yanayinta yasa Driven ya fara da ita a hankali har suka isa clinic ɗin fitowa yay da gansa sosai mamaki ya kamasa ganin bacci take hankalinta kwance babu abinda ya dame ta, ya daɗe tsaye a kanta yama rasa mene zai mata, a hankali ya fara buga kujerar da take kai yana faɗin "Madam! Madam!" Idanunta ta buɗe tana ya motsa fuskarta ba tare data kallesa ba ta fito daga cikin motar kai tsaye cikin haɗaɗɗan Clinic ɗin Wanda Manyan likitoci suke ciki tana shiga Dr dake kula da mutumin ya fito Murmushi Yay mata yace "wlcm Madam Meema Ahmed Adil" Murmushi tayi masa wanda ya sanya yay ƙasa da kansa domin kwarjini gareta sosai ga shirme da manta abubuwa gaba ɗaya kanta bashi da saiti "how can i help you?" Taji Dr ɗin ya faɗa cikin ƙasa da murya tace "please ina son nai magana dakai prvtly firstly kuma ina son ganin sa please kaji?" Jinjina mata kai yay kafin yace "follow me"  bayansa tabi tana sakin murmushi a cikin wani haɗaɗɗan room mai masifar kyau ba zaka taɓa cewa mara lafiya bane a ciki waje ya bata ta shige ciki idanunta na kansa, yana kwance flat gaba ɗaya an sanya masa wasu na'ura a jikinsa fuskar nan nashi manne da bandeji kansa ma haka, baƙi ne his Elegant black skin ɗin nan nashi sai ƙyalli yake, babu abu mai haske a Jikinsa irin foot ɗin sa da tafin hannunsa a hankali kuma Numfashinsa ke sauka, he's dark-skinned yet handsome zai iya shekaru 29 to 30 kujera taja ta zauna kusa dashi a hankali ta kama hannunsa idanunta na kawo ruwa cikin ƙasa da Murya tace "you're my brother as frm today, I'll take good care of you kaji babu abinda zai sameka, i love You irin so na ƴan uwa in sha Allah zaka tashi you'll be fine ji nake kamar na sanka tun can baya" Shiru tayi kafin ta ƙara riƙe hannunsa tace "Nima zaka zaka kula dani ko? I'm scared ina jin tsoran mutane, kaga nan nima wai babba ce fa kullum Dad sai yace na zama babba classes lady zaka kuya min komai ai ko? Zaka dinga zuwa mall mall dani da park za muna hira ko?" Ta faɗa hawaye na sakko mata, mamaki ne ya kama Dr domin yaji ana faɗin Meema bata da wani cikakken hankali shiyasa mahaifin nata baya fita da ita amma the she's talking yanzu zaka ɗauka mai cikakken hankali ce Allah Al-hakkamu kenan.

Murmushi ta saki jin ya riƙe hannunta dake cikin nasa, juyawa tayi ta kalli Dr hawaye da dariya na kwance mata tace "You see ba? I'm lucky wallahi he loves me I'm so happy" ta faɗa kuka na ƙwance mata kamar wacce ta tuna wani abu kuma ta miƙe tsaye tana kallon Dr kafin tace "let's go" fita yay tana biye dashi a baya har office ɗinsa zama yay kana ta zauna tana faɗin "i need your help Dr but kada Dad yaji please" jinjina mata yay kafin yace "what the you want?" Shiru tayi tana tunani sai kuma tace "Ina son a sawa wannan mara lafiyar fuskar wani" idanunsa ya ware yace "fuskar wa kikeso asa masa to?" Ya faɗa cikin harshen turanci "bani da photon sa amma dai ina da photon a idanuna da zuciyata" Wayarsa ya ɗauka yace "ok bari na kira arteries muga" tana zaune yay waya not too long wani mutum ya shigo ɗauke da kayan drawing ajjiye komai yay a hankali Meema take masa bayanin komai tana faɗa yana zanawa Murmushi tayi tana jin wani mugun daɗi na ratsa Zuciyarta ta sauri Dr ya miƙe tsaye idanunsa akan zanan cikin ɗaga murya yace "wannan ai photon tsuhun ɗan majalisa ne (Members federal house of Representatives) Hon Bukar Bello..

 

A hankali yake sakkowa daga strains ɗin benen yana sanye da wata ɗanyar shadda fara dal da ita ɗinkin babbar riga da jamper, ya ɗura wata half jaddara a saman sumar kansa wacce tayi kwance lubb da ita, ƙafarsa sanye cikin wani Black half shoe na Gucci mai tsananin kyau.

Yana tafe yana maƙala Rolex ɗinsa na A.lange & Sòhne yay wani irin mahaukacin kyau idan kaga Akeem zaka ɗauka wani Balarabe ne fuskarsa tai wani fresh ga wata haiba da zallar nutsuwa fuskar nan babu yabo babu fallasa as usual yana tafe yana lumshe idanunsa tare da motsa bakinsa.

Abbu dake downstairs yace "Akeem yau dai ka makara kamar ka manta yau Friday" caraf Didi ta amshe zan can tana faɗin "yoooo Allah na tuba zuciya ce babu alkairi, mugun abu yay masa yawa faɗa yake nema dani saboda an faɗa masa ni sallamammiya ce irinsa to ba'a gantale nake ba, wallahi Bukari ina faɗa maka kaji tsoran ka nemawa ɗan ka magani gani kuke ina wasa amma billahi wannan yaron ba lafiya ce dashi ba" Murmushi Abbu yay yace "Didi kunfi kusa da mijin naki fa" wani zaro ido tayi tace "wa ɗin? To wallahi li'ilafi ƙurash banda a ido aka haifi Audil wallahi da cewa zanyi ba jinin ka bane, saboda tsabar maita ka kalli yadda yake jajir dashi kamar wannan yaron na yama sunan Film ɗin..." Ta faɗa tana kallon Afaf wacce ta fito daga part ɗinsu da sauri Afaf tace "Shuria khana, na Film ɗin maheyk" tafa hannu Didi tayi tace "Yawwa Shimam irin albarka shifa kai Muhammadur Rasulullah s.a.w wlh mugun halinsu ɗaya" A hankali Akeem ya gama sakkowa tsittt wajan ya ɗauka sai muryar Didi ta fara faɗin "Astagafirullah satali saboda Annabi albarkacin juma'a" Murmushi kawai Abbu yay a hankali yay gaba Akeem ya fara masa baya kamar wasu abokai kai tsaye mota suka nufa gaba ɗaya kuma back seat suka shiga driver yaja sun ɗan fara tafiya Abbu ya kalli Akeem yace "Ina son sanya Akeela makaranta what's your opinion?" Taɓe baki yay ba tare da yace komai ba ganin hakan yasa Abbu faɗin "Abdul-hakeem" marai-raice fuska yay kamar zai kuka yace "for God sake Abbu mene nawa ni" da mamaki Abbu yace "Akeem! what wrong with you? Ƴar uwar taka jikinka itace Meye ruwanka cikin lamuranta Are You at of your sense?" Haɗe fuska Akeem yay ba tare da yace komai ba a yanzu haushin yadda Abbu yake son fifita shi da village gal ɗin nan ya keji cikin damuwa Abbu yace "ashe zaka iya wulaƙanta jinin ɗan uwana jinin Baffanka har haka Abdul-hakeem? Akeela is your sister kamar Aleema da Afaf mene yasa kake haka ne?" Ɓata rai yay yana sauke numfashi kafin yace "Abbu ni kawai i hate her ne" wani sassanyan numfashi Abbu ya sauke yana mai jin daɗin hakan a ransa shi kaɗai yasan mene zuciyarsa ke faɗa masa a haka suka ƙarasa babban masallacin juma'a dake nan nasarawa gra.

 

A can gida kuwa su Akeem na fita Akeela ta fito a sanyaye kamar wata munafuka tana sanye da wata haɗaɗɗiyar open abaya blue black ta ɗura wata hula mai gashi a kanta, cikin nutsuwa ta ƙarasa shigowa ciki ganinta yasa Ummi faɗin "Daughter kin fito?" Ƙasa tayi da kanta tana wasa da yatsun hannunta Miƙewa Mami tayi tare da barin main Parlo ɗin gaba ɗaya taɓe baki Didi tayi tace "to ita dai rayuwar guda nawa take? Ban dai gantalewa da son zuciya irin na mutum, idan ka riƙe ɗan wani baka san wazai kula da naka ba fisabilillahi mugun abu ƙarara" Murmushi Ummi tayi tace "have a sit daughter" Afaf ce ta kama hannunta tana faɗin "Ummi wallahi tsoran Hamma Akeem take kamar ranta" taɓe baki Aleema tayi tace "ba dole ba, mutum sai faɗa da miskilanci wallahi gabana har faɗuwa yake idan na jisa kai wallahi munyi missed Hamma Adnan Allah ya dube mu" Ummi dake Miƙewa domin haɗa lunch tace "Za kuyi bayani bari yazo" da sauri Didi tace "Tsila (Akeela) ke dai babu ruwanki da shiga tsabgar wannan mutumin kada kuma ki biyewa su Shimam wallahi shawara nake baki bani da mugun abu ko kaɗan" ita dai Akeela da idanu kawai take kallonsu kafin tai magana taji ƙamshin turarensa da kuma zazzaƙar muryarsa yay sallama cikin parlon Abbu na bayansa da sauri ta kulle idanunta ƙirjinta na wani irin bugawa, babu wanda ya kalla cikin parlon part ɗin Mami ya nufa tana zaune a Parlon ta watching TV Akeem yay sallama Murmushi tayi tace "wlcm Hero" shigowa yay tare da zama saman sofa yana ɗan lumshe idanunsa kafin a hankali yace " Ma'ul khair Mami" Murmushi tayi tace "yawwa yaya aiki?" Yana lumshe idanunsa yace "Allahamdulillah Mami" kafin Mami tayi magana Amani ta shigo tare da faɗawa jikinsa tana faɗin "Abbie na" satar kallon Mami yay yaga basu take kallo ba da sauri ya rungume Amani yana bata peak a goshinta yace "little na" dariya tayi tace "Abbie na kayi kyau kamar new Aunty" ware idanunsa yay irin bai gane ba ɗin nan tace "Abbie Anuty Akeela tana da kyau" haɗe fuska yay yace "لاأريدالشوشرة" (ban son surutu). Shiru tayi masa domin tasan halin Abbien nata miƙewa yay Mami tace "Uba da ƴar duk babu kunya ka daure dai kayi wani Auran a samu more children's" shafa fuskarsa yay tare da ɗaukan Amani ya fita, ita kaɗai ce a parlon duk sun tafi taya Ummi shirya Lunch can nesa da ita ya zauna domin yunwa ya keji shiyasa ba zai iya komawa part ɗinsa ba, buɗe ido tayi a hankali tare da sauke ganinta a kan ƙwantaccen sajansa wanda yay mata masifar kyau bata taɓa ganinsa da manyan kaya ba kenan sai Friday Friday yake sawa? Ta tambaya a ranta, wani irin sahihin kyau yay kamar Balarabe Amani dake jikinsa ta zame tace "Abbie ka ganta tana da dimples irin nawa da naka Allah" Murya can ƙasa dai-dai kunan Amani yace ،أنت" إجلس معتزلا"  Wato _Ke! Zauna dai-dai_ jin abinda yace tayi shiru tare da komawa ta zauna tana jan gemunsa.

Fitowa Abbu daga part ɗinsa idanunsa akan Akeela ganin Akeem zaune a parlo abinda bai taɓa ba kenan yasa kawai ya nufi  dinning room gently Akeem ya miƙe da sauri Amani ta zame hannunta ta nufi wajan Akeela ogan kuwa tunda ya zauna bai kalleta ba, tana jin Ummi na kiranta kasa tashi tayi domin jinta take wani uncontactable a cikin su.

Bayan sun kammala yin lunch ɗin Akeem ya haura sama Abbu kamar yay ihu ya keji domin tun safe bai samu damar yin magana da Akeela ba bare yaga ƴar shagwaɓar data saba yi masa.

Da daddare bayan sallar Isshā duk suna zaune a parlo iya yaran Aleema, Afaf da kuma Akeela Amani tuni tayi bacci ya jima da shigowa amma gaba ɗaya basu san ya shigo ba hankalinsu na kan film ɗin This is fate da ake na karan da firita, gyaran murya yay yana zuba hannayensa a cikin hannun jallabiyar jikinsa da sauri gaba ɗaya suka juya tare da kallonsa a kusan tare da Afaf da Aleema suka shiga faɗin "lailatan Sa ida" wato barka da dare haɗe fuska Akeem yay cikin wata tsawa yace "duk Shegiyar dana ƙara gani da Wannan kayan uhm" ya faɗa yana duban ƙananun kayan dake jikinsu bakin Aleema na rawa tace "Ayyah Hero banmu ƙara sawa" wata tsawa ya daka mata yace "ku ɓace min da gani" Akeela tafi kuwa firgita jikinta na wani irin ɓari ta miƙe zata gudu da wani irin sauri yasa hannunsa ya riƙe wist ɗinta tare da wani irin juyo da ita ya haɗata da.....

 

 

 

😂 nifa na rasa gane kan bawan Allan nan Akeem what de you nufinka eh? Remain 1 page free pages ya ƙare 🤷🏾‍♀️.

 

 

 

 

*TSINTACCIYA*

NRML GRP ₦300

VIP: 500 SAFE YAMMA POSTING

0116886423 SULAIMAN NA'IMA S UNION BANK EVEDANCE OF PAYMENT 08119237616

 

*NOTE*

NRML GRP POSTING BA KULLUM BA🤷🏾‍♀️ IDAN ZAKI SAI BOOK ƊINA DOMIN KI FITAR NA YAFE NA FAƊA MAKU ZALLAR SOYAYYA NE A WANNAN BOOK ƊIN MAI TSAYAWA A ZUCIYA.

 

 

*FITATTU HUƊU🔥*

 

BAƘAR FATA

AutaR ManyA

 

DATTIJON ARZIƘI

Real ladingo

 

SULTAAN

Mss flower

 

gaba ɗaya ₦800

Via 6850917335 Na'ima Shu'aibu sulaiman fidelity bank masu tura kati 08167888934 ga ƴan uwa na Niger +22796515805 zaku tura Evedance of payment a nan 08142105218

 

 

 

  *SARAUTAR MARUBUTA*

*🌈TSINTACCIYA🌈*

 

FITATTU HUƊU🔥

 

   _Will Akeem ever fall for Akeela? The way she has fallen for him??_

 

http://wa.me/+2348119237616

 

EPISODE1️3️

Jikin bango da sauri kuma ya saketa jin foot steps alamar wani zaizo,  kama hannunta yayi ba tare daya kalli fuskarta ba ya fara janta zuwa upstairs Akeela tsoran da yay mata yawa ne yasa ko magana ta kasa,

Jikinta ya ɗauki ɓari sanin bata da wani mataimakin sai Allah yasa tabi bayansa babu gardama amma tuni hawaye ya fara bin kyakykyawar fuskarta,

Da wani irin ƙarfi cike da Zallar mugunta yake janta zuwa samansa, suna isa bakin ƙofa ya sanya fararan hannunsa masu ɗauke da wasu kwantaccen gashin dogwaye luff dasu,  cikin nutsuwa ya murɗa handle ɗin ƙofar tare da turawa tsayawa yay bakin ƙofar still bakinsa na motsawa alamar tasbihi yake, idanunsa ya buɗe sosai tare da saukewa a saman laɓɓanta wanda suke jajirrr dasu sunyi pink yirrrr dasu, da sauri kuma ya ɗauke idanunsa yana taɓe fuskarsa shiga cikin parlon nasa yayi, Akeela kanta a ƙasa ta riƙe bakin  buhhh ɗinta wacce ta tsaya mata iya cinyoyinta gaba ɗaya fararan dogayen ƙafafu wanta ana ganinsu, wani ajjiyar zuciya ta sauke tana ƙara ƙamƙame Jikinta bakinta na rawa sosai, ba tare da tunanin komai ba taji ya sanya hannunsa tare da fisgarta zuwa cikin parlon nasa, maida ƙofar yay ya rufe binta yay da kallo from head to toe kafin a hankali ya shige zuwa ciki,

Kai tsaye wajan fridge ɗinsa ya nufa a hankali ya durƙusa tare da sanya hannunsa ya buɗe fridge ɗin power horse ya ɗauka tare da ice cream da cake wanda cinsu ya zame masa kamar masifa.

Saman doguwar kujera yaje ya zauna tare da zube kayan hannunsa a kan center table, cikin nutsuwa ya sanya hannunsa ya zame jallabiyar jikinsa nan da nan murɗaɗɗan jikinsa ya bayyana, ko ina na jikinsa a murɗe yake Musamman Physique chest ɗinsa ga wasu manyan nonuwa da yake dasu nipples ɗin nan sunyi yirrr dasu, tsakiyar ƙirjinsa duk gashi ne wanda sukai masa kyau matiƙa.

Cake ɗin ya ɓare a hankali yay Bismillahi tare da buɗe bakinsa ya sanya, zaƙi da kuma daɗin cake ɗin ya haddasa masa lumshewar idanunsa yana sauke ajjiyar zuciya, baya yay tare da jingina da jikin sofar gently kuma ya miƙa hannunsa ya ɗauki remote ya kunna channel ɗin N.c.c ya fara kallon Labarai gyara zama yay sosai ganin an nuna zaman majalisa wanda ake a babban zauren Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin New York a ƙasar Amurka KENA BETANCUR POOL/AFP.

Idanunsa ya buɗe sosai ya zubawa zauran idanu wanda ake taron cikinsa wato United Nations.

Shugaban zauran Akeem ya kalla mai suna Abdul-ƙhadir Azeem (Chief of Staff) fuskar mutumin babu walwala kana kallonsa kasan ba kirki zai ba, a hankali kuma aka nuno shugaban lafiya wanda yake faɗin.

"June 19th was officially designated as World Sickle Cell Awareness Day,The international awareness day is observed annually with the goal to increase public knowledge and an understanding of sickle cell disease, and the challenges experienced by patients and their families and caregivers, kowa ya san cewa wannan rana a ita ake Wannan taron kuma ake tattaunawa da masu ciwon skila tare da family nasu, while mun ware manyan likitoci guda mace ɗaya namiji ɗaya wanda za suyi muhimman bayani akan wannan ciwo na sikila, mutum na farko shine Dr Abdul-hakeem Bukar Bello, sai kuma Dr Meema Ahmed Adil President's daughter, wanda za'ai taron ne a babban asibitin dake Nigeria a garin Kano wata Asibitin Murtala Muhammad, Wannan zaure na United Nations ya ware adadin kuɗaɗen kimanin 100.25m domin taimakawa masu wannan ciwon" shiru yay saboda tafin da aka ɗauka.

A hankali Akeela ta buɗe idanunta tare da sauke idanunta akan cineme ta kalli mutumin dake bayani, she's was shock da taji labarin domin kaf Duniyar nan ta ɗauka cewa ita ɗaya kawai take da wannan wahalalliyar ciwon.

Samun kanta tayi da son jin ragowar zan can, ana August gashi ance june kenan da sauran lokaci sai wata shekarar ma, cos already time ya shige.

A hankali Akeem ya ɗauki ice cream ɗin ya fara sha, a ransa yana ta tunanin Wacece Dr Meema ganin irin wannan sabgar bai damesa ba yasa kawai ya cire tunanin hakan a ransa.

Shi ya riga daya mance da itama gaba ɗaya a ɗakin, hakan yasa yaci gaba dayin abinda ya shafe sa, a lokacin kuma tunanin ƙauyen ne a ransu ya ɗauki niyyar a wannan weekend ɗin zai je yaga Meke going.

 

A can downstairs kuwa Abbu ne kwance a bedroom ɗinsa Mami na gefensa tayi shiru tunani fal a ranta, abu biyu ne ya shige mata ga rashin Adnan ga kuma matsalar mijinta, a koda yaushe suka zo kwanciya 5mins yay masa yawa wajan kawowa, tana da ishasshiyyar lafiya a lokacin da shi burinsa ya cika ya samu gamsuwa a lokacin ne ita kuma masifar sha'awar ta zata motsa, ta rasa da waye zatai sharing damuwar ta, ita kaɗai take fuskantar Wannan problems ɗin na rashin gamsuwa ko hadda sauran mata kamar ta.

Kuka ta fashe da shi da sauri Abbu ya buɗe idanunsa tare da miƙewa yace "Mami" bata kallesa ba kuma batai shiru ba ganin hakan yasa yace "please dan Allah stop cry Meke damun ki? What happened to you Khadijertou?" Cikin kuka tace "what should i do? Eh? Jina nake kamar zan mutu You older than me, buƙatarka na biya shikenan, You doesn't care about me ya nake I'm ok ko mene, na samu nutsuwa ko yaya? Kullum cikin ciwo nake me kake so nayi eh?"

Kallonta yay yama kasa Magana daman yasan wannan zan can ne baki ya buɗe zai magana tace "look! Abbu baka sona is Okey, amma kana son nabi maza ne? Abinda banyi da ƙuruciya ta ba sai yanzu, idan problem ɗin daga nine I'm ready to accept it kuma na gyara na nemi magani, amma zama haka ba zai yiwu ba, I'm so horny bana iya bacci wallahi billahi ni da ace ka raɓeni gwamma na zauna hakan nayi managing kai na hakan nan, amma ace 2mint da kwanciya mutum ya samu gamsuwa ni kuma ko ohhho! wacce kalar azalce haka ta hauni" kuka ta fashe dashi sosai tana riƙe cikinta dake matsananci ciwo zuwa Mararta.

Kasa magana yay sai miƙewa yay kawai tare kama hannunta ya jawota tare da bata side hug.

 

 

Akeelah

Hawaye ne ya sakko daga cikin idanunta zuwa saman fuskarta cikin tausayin kanta ta ƙara ware idanunta akan t.v tana jin bayanin da ake, a hankali shugaban lafiyar yace "zamu sakko da wannan taron wanda zamu gabatar soon, saboda yawan mace mace da kuma tarin masu sikila da muke dasu yasa dole a gabatar cikin wata mai kamawa in sha Allah period zamu sanar da mouth, day, time"

Jiki a sanyaye ta miƙe a hankali kuma ta zare hular kanta tare da wani irin baza gashin kanta ya sakko har waist ɗinta ta zama kamar wata ƴar India she look like Maheyk.

Jikinta yana wani irin Kaɗawa ta ƙanƙame Jikinta waje guda walking slowly ta nufi inda Akeem yake zaune ya shagala da shan ice cream ɗinsa yana danna system ɗinsa hankali kwance ba zato ba tsammani yaji Akeela tayi wani irin..

 

 

 

Dan Allah dan Annabi, dan darajar iyayenki da kimar da suke dashi a wajanki kiji tsoran Allah idan kin siyi littafi na kada ki fitar, kuɗin karantawa kika biya bana mallaka ba, idan taimako kike sonyi zaki iya biya ba ya zama mallakin ki a sakarwa kowa as free ki samu lada😍👏🏻 haƙƙin mutum masifa ne sosai wallahi.

 

 

 

 

*TSINTACCIYA*

NRML GRP ₦300

VIP: 500 SAFE YAMMA POSTING

0116886423 SULAIMAN NA'IMA S UNION BANK EVEDANCE OF PAYMENT 08119237616

 

*NOTE*

NRML GRP POSTING BA KULLUM BA🤷🏾‍♀️ IDAN ZAKI SAI BOOK ƊINA DOMIN KI FITAR NA YAFE NA FAƊA MAKU ZALLAR SOYAYYA NE A WANNAN BOOK ƊIN MAI TSAYAWA A ZUCIYA.

 

 

*FITATTU HUƊU🔥*

 

BAƘAR FATA

AutaR ManyA

 

DATTIJON ARZIƘI

Real ladingo

 

SULTAAN

Mss flower

 

gaba ɗaya ₦800

Via 6850917335 Na'ima Shu'aibu sulaiman fidelity bank masu tura kati 08167888934 ga ƴan uwa na Niger +22796515805 zaku tura Evedance of payment a nan 08142105218

 

 

 

  *SARAUTAR MARUBUTA*

*🌈TSINTACCIYA🌈*

 

FITATTU HUƊU🔥

 

http://wa.me/+2348119237616

 

EPISODE1️4️-1️5️

Faɗawa jikinsa tare da sakin wata gigitacciyyar ƙara wacce ta sanya Akeem saurin ware narkakkun idanunsa tare da sauke ganinsa a kanta, wani irin murɗewa jikinta yake tamkar ba mutum ba, ga wani rawa haɗi da kyarma da ɓari da naman jikinta ya shigayi kana ganin Akeela kasan she's not on her right sense, irin something is fishy ɗin nan.

Gajiyayyun idanunsa kawai ya sauke akanta yayinda zuciyarsa ta shiga wani irin masifafan harbawa fuskarsa babu walwala ko kaɗan, baƙin ciki da haushin yadda ta faɗa masa jiki yafi masa komai ciwo, cikin ɓacin rai bai ba duba condition ɗin da take ciki ba ya wani irin Miƙewa tsaye da sauri tare da sanya hannunsa ya fisgota haɗi da mannata jikin bangon parlon nasa, idanunsa na wani irin ruwan zallar bala'i ya mannata da jikin bangon tare da sanya hannunsa a wuyanta ya shaƙeta yadda Jikinta ke rawa haka nasa ke rawa, yama kasa magana saboda tsananin ɓacin rai, cikin tsananin ɓacin rai ya buɗe bakinsa cikin wata kakkausar murya yace "you're mad jakaness, jikina sa'anki? Eh? I'll killed you village gal" ya faɗa jijiyoyin kansa sun fito sunyi raɗa raɗa idanunsa yay Wani mahaukacin jaaa gaba ɗaya ya fita a hayyacinsa ba zaka ɗauka mai hankali bane saboda yadda yake huci kamar kumurcin Maciji.

Cikin wata iriyar Murya mai tsanani taushi da kuma amsa kowa Akeela ta buɗe bakinta tare da faɗin "mune zaka kashe ko ita? Duk abinda zakai a yanzu mu zakaiwa domin ita ɗin bata da wani laifi mune ne muka ziyarce ka" wani irin kallo yay mata har zuwa lokacin idanunta a lumshe suke suna zubar da ƙwalla, girgiza kai yay yana wani irin taune bakinsa cikin ransa yake faɗin "za'a rina gayyar aljanu kawai" ɗago idanunta yay wanda sukai wani irin bala'in jaaa kafin a hankali Murya babu wasa yace "open your eyes" girgiza masa kai tayi zaka ɗauka tasan abinda ta keyi kafin tace "i can't" cije baki yay yana wani ƙara shaƙe mata wuya cikin ɗaga murya yace "Open your eyes" da sauri itama ta sake girgiza masa kai tace "ban mu iyawa" kafin Akeem yay magana Didi wacce ta shigo tayi saurin faɗin "tsinannu gantalallu, to ubanwa kuka ajjiyewa a Jikinta? Wallahi Ii''ilafi ƙurash, tub! tub! tub! To basai kuci kanku ba Allah kurwarta ɗaci gareta" ta faɗa tana riƙe zani dake neman faɗuwa a hankali Abbu ya shigo sai Mami kana Ummi ta shigo sanye da hijab idanunta akan Akeem kasa magana tayi dan she can't believe ace wai Akeem yayma Akeela haka.

Cikin ɓacin rai Abbu yace "Well-done Abdul-hakeem Bukar Bello, Well-done" ya faɗa yana ƙarasawa wajan da sauri Akeem ya saki wuyan Akeela tayi wani luuu zata faɗi cikin zafin nama Abbu ya rungome ta a jikinsa yana ƙara kwantar da ita cike da ɓacin rai a kuma karon farko na rayuwarsa ya kalli Akeem yace "what nonsense! Eh? Kasheta zakai eh Dr nace mekai mata da harta suma haka eh?" Shiru Akeem yay kansa a ƙasa idanunsa a lumshe wani irin baƙin ciki da kuma tarin tsanar Akeela ya ƙara nunkuwa cikin zuciyarsa, a karo na farko na rayuwarsa ta dalilinta a yanzu ta sanya mahaifinsa yana ɗaga masa murya a all his life har kawo yanzu bari wannan bata haɗa shi da Abbu ba amma yanzu da girmansa da komai har ƴar ajjiye akan Wannan yarinyar mai kama da TSINTACCIYA a idanunsa  mahaifin zai masa faɗa,

Ummi dake tsaye tace "Akeem" a hankali ya ɗaga idanunsa wanda sukai jajirr ya kalleta kamar bazai magana ba sai kuma yace "Ummi..," wata tsawa ta daka mai wacce tunda yake bata taɓa yi masa irinta ba kafin tace "shut up! Akeem this is not how I train you ƴar Uwarka jininka? Eh Akeem? Where is your heart da har zaka sanya hannunka ka shaƙe wuyan yarinya nan, U hate her is your problem amma baka da ikon da zaka sanya hannunka a kanta idan har ba kuskure ta aikata ba, ko dan ciwonta ai ka daga mata haba, bata zo nan daka a wulaƙanta ta ba, baka san Wacece ita ba ko Do you know what gal has been through? Ka ban mamaki baici ace kayiwa jinin Baffa haka ba, da kasan waye Baffa da bakaiwa abinda ya haifa haka ba wallahi zan baka mamaki" Mami wacce ke tsaye ranta duk ya ɓaci domin har cikin ranta take jin faɗan da akewa Akeem wai kuma akan wannan Yarinyar cikin jin haushi tace "haba Ummi it was a mistake wanda kowa nayi kunsan Akeem ba mai shiga sabgar mata bane, inside of ku tambayi dalilin zuwan ta part ɗinsa sai ku hau yaro da faɗa" da sauri Didi tace "A toh! Yau ni naga ruwan masifa ai she daman indo ba ƙaunar yaron nan kike ba? Kai ma da laifinka wallahi idan nace ka kaf faɗin gidan nan nine kawai ke sonka to daman idan bani ba wazai so ka ai nice dolenka" Kai Akeem ya ɗaga tare da kallon Abbu a hankali kuma ya kalli Ummi da sauri kuma ya nufi saman sofa ya ɗauki car key ɗinsa ya nufi fita waje, cikin sauri Ummi tace "Akeem where are you going ina ne zaka nine kayiwa zuciya?" Ko tsayawa bai ba bare ta sanya ran cewa zai dawo, hankalin Abbu ne ya tashi domin yana masifar son Akeem kamar ransa, ya rasa Adnan bazai saken da zai rasa Akeem ba salati Didi ta fasa tace "Huuuu! Jama'a mun shiga uku wanne irin gantalallan Bukari ya samu ne? Anya ba'a sauya maka shi a asibiti ba wannan baƙar zuciya har ina, to wallahi sai dai kaci kanka tass"  wani irin Miƙa Akeela tayi a jikin Abbu bakinta na motsawa a hankali kuma tace "Abbu Hamma Akeemmm kada ya fita" da sauri Didi tazo tana dungure mata kai tace "Annamimiyya mai zubin munafukan farko ashe kina ji kikai shiru waike salammiya" yanayin Akeela yasa Ummi saurin cewa "Abbu anya ba mutanan ɓoye bane kuwa?" Kafin Abbu yay magana Akeela ta fasa wata gigitacciyyar ƙara tare da zabura ta nufi waje da gudu, cikin sauri Abbu ya mara mata baya yana faɗin "Akeela! Akeela!!" Ganin yadda take gudun kamar barewa Abbu bai san lokacin da yace "Babyna, Babyn Abbunta Stop" daga Ummi har Mami babu wanda yasan me yake nufi, cikin zafin nama kuma Akeela tai waje gaba ɗaya kasancewar ƙofar a buɗe take saboda ficewar Akeem daga cikin gidan.

Kai tsaye gate ta nufa shima yana buɗe gaba ɗaya ta fice daga cikin estate ɗin tana sharara uban gudu, daga ita sai Nightgown gashinta duk a zube tamkar mahaukaciya a haka ta nausa kan titi babu ko slippers.

Fitowa Abbu yay zuwa complete ɗin yana faɗin "Bala, Isa, Rabi'u" ya shiga kiran driver da gatekeeper da mai shukar Flowers, amma gaba ɗaya babu ko wanne bacci duk suke, jin shiru yasa Abbu komawa da gudu cikin gidan dai-dai lokacin kuma su Afaf suka fara daga baccin da suka fara domin duk da wuri suke bacci.

Car key ya ɗauka ya fito da sauri Mami tace "Ina zaka at this time?" Bai ko kalleta ba ya nufi wajan ɗaya daga cikin motocin sa ya shiga key yay mata ya fita da gudu tare da barin estate ɗin, kuka Didi tace "Bukari ka kawo masifar duniya gidanka" cikin damuwa Ummi tace  "Didi Aljanu ne da Yarinyar wallahi kuma sune suka tashi" wani zaro ido waje Didi tayi tace "Muhammadur Rasulullah s.a.w shine ke kuwa kikai min shiru itana da surutu yau na shiga wallahi gidan zan bari" juyawa Mami tayi ta shige ciki Ummi ba haka da gudu Didi tabi bayansu har zaninta na faɗuwa.

 

Akeem kuwa yana fitowa kai tsaye motarsa ya nufa idanunsa a Lumshe ko ganin gabansa ba yayi, wani irin zafi da tafasa zcuiyarsa ke masa, yana shiga motar ya jata da gudu bayan ya danna wani hargitsastsan horn da dauri Isa ya tashi daga baccin da yake ya buɗe masa gate fita yay da motar yana ƙara gudun motar tafiya yay mai nisan gaske har yabar gaba ɗaya cikin Rail way ɗin kafin ya nemi hanya yay parking motar, kansa ya kifa akan string motar yana sauke wani zazzafan numfashi jikinsa duk rawa yake amma har kawo lokacin fuskarsa bata nuna damuwar da yake ciki ba sai idanunsa kawai da suka sauya kala.

Akeela kam gudu kawai take tana bin sahun motar Akeem tun tana gudu kaɗan har ta fara mai yawa, kasancewa gudun ba nata bane na Iskane yasa itama ta fice daga cikin Rail way ɗin,

Akeem na zaune cikin motar yana sauke numfashi a hankali ya ɗaga kansa dai-dai lokacin da Akeela tazo ta gaban motarsu ta shige, bayanta yabi da kallo yana ganin yadda take gudu tamkar mahaukaciya tun yana iya ganinta har ta ɓace masa da gani, taɓe bakinsa yay a hankali yay baya tare da kwanciya a jikin kujerar motar yana maida numfashi tare da dafe kansa wanda matsanancin harba masa.

Duk inda Abbu yake tunanin ganin Akeela ya duba amma babu ita tashin hankalin mara misaltuwa ya sauka akan fuskarsa, yasan Akeem tun inda yake sai kula da kansa Amma Akeela waye ta sani a wannan garin? Musamman Wannan hargitsastsiyar unguwar tasu, jiki babu ƙauri ya koma gida har wayewar gari basu runtsa ba,Didi data rufe idanunta zata buɗe da sauri tana faɗin "Muhammadur Rasulullah s.a.w" washe gari wajan ƙarfe 8 na safe lokacin tuni Abbu ya gama bada cigiyar Akeela both side t.v Redio, a hankali motar Akeem take shigowa cikin estate kai tsaye kuma gate ɗin gidan su ya nufa yana zuwa Isa ya buɗe mata gate ya shiga tun kafin ya fito daga motar cikin ɓacin rai da kuma tashin hankali Abbu ya nufi kan Akeem gadan gadan domin rashin Akeela dai-dai yake da rasa rayuwarsa....

 

 

 

Hhhhh Akeem you're too selfish baka da kirki ko kaɗan😒

 

 

 

*TSINTACCIYA*

NRML GRP ₦300

VIP: 500 SAFE YAMMA POSTING

0116886423 SULAIMAN NA'IMA S UNION BANK EVEDANCE OF PAYMENT 08119237616

 

*NOTE*

NRML GRP POSTING BA KULLUM BA🤷🏾‍♀️ IDAN ZAKI SAI BOOK ƊINA DOMIN KI FITAR NA YAFE NA FAƊA MAKU ZALLAR SOYAYYA NE A WANNAN BOOK ƊIN MAI TSAYAWA A ZUCIYA.

 

 

*FITATTU HUƊU🔥*

 

BAƘAR FATA

AutaR ManyA

 

DATTIJON ARZIƘI

Real ladingo

 

SULTAAN

Mss flower

 

gaba ɗaya ₦800

Via 6850917335 Na'ima Shu'aibu sulaiman fidelity bank masu tura kati 08167888934 ga ƴan uwa na Niger +22796515805 zaku tura Evedance of payment a nan 08142105218

 

 

 

  *SARAUTAR MARUBUTA*

*🌈TSINTACCIYA🌈*

 

NIMCYLUV

FITATTU HUƊU🔥

 

Writer of

Abu Maleek

Sirrin mu

Uncle ne

Kwaila ce

The new emir

Jidda

Juyayi

Izzar so

Moon

Lamrat

Raino ne sila

Ranar Aure na

Ƙaddarar mace

Ashe ƴar babata ce

TSINTACCIYA

 

 

http://wa.me/+2348119237616

MASU SIYA SUYI MGN👆🏾

 

EPISODE1️6️-1️7️

Yana zuwa bakin ƙofar ya tsaya yana jiran fitowar Akeem, gently ya buɗe ƙofar ya fito idanunsa a lumshe ga yadda jijiyoyin kansa suke a mimmiƙewa fuskarsa tayi jajirrr da ita alamun har yanzu yana cikin ɓacin rai.

Ganin Akeem cikin wannan halin wanda bai taɓa ganinsa a ciki ba yay saurin faɗin "Dr" idanuna da suke a Lumshe ya buɗe tare da sauke ganinsa akan fuskar Abbu,wani irin bugawa zuciyar Abbu tayi saboda wani irin jaaa da idanun Akeem sukai har wani ruwa suke fitarwa. Muryar sa na rawa yace "what... what happened to Akeem?" Lumshe idanunsa yay kana ya buɗe kamar wanda baya son yin magana ya buɗe baki da ƙyar yace "noting" yana faɗin hakan ya nufi shiga cikin gidan da idanu kawai Abbu ya bisa yana mamakin baƙar zuciya irinta Akeem. Girgiza kai kawai yay tare da nufar cikin gidan kai tsaye part ɗinsa ya nufa, Akeem na shiga Amani na ganinsa ta miƙe tana faɗin "Abbie na" bai ko kalli inda take ba sai hannu daya sanya yama ture ta kai tsaye upstairs ya nufa yana dafe kansa yana jin yadda Amani ke kuka amma yau banza da ita, Didi dake zaune tayi saurin faɗin "Au! Yarinya ba sai dai kiyi tayiwa Ubanki istigifari ba, daɗin abin ko kashe ki yay shine ya haifa a toh" Aleema ce ta kama hannunta tana rarrashinta kasancewar weekend ne duk suna gida. Akeem na shiga side ɗinsa rest room ya nufa cire farar jallabiyar jikinsa yay tare da saƙale ta a hanger, fure fresh skin ɗinsa ta bayyana wani irin ƙwantaccen baƙin gashi ne a saman mararsa mai matuƙar ɗaukan hankali jikinsa a sanyaye ya nufi cikin tube tare da shigewa ciki, wani irin sauke numfashi yay a hankali kuma ya ƙara nutsewa cikin ruwan dake cike har bakin tube ɗin, zafin da zuciyarsa ke masa ya sanya gaba ɗaya yama mance a cikin ruwa yake, idan ya tuna irin faɗan da Ummi da Abbu sukai masa sai yaji wani abu ya tsaya masa a ƙirjin, cikin ficewar hayyaci da kuma zallar damuwar dake ransa ya ƙara nutsa kansa cikin ruwan a hankali kuma ruwan ya fara shige masa cikin baki da hanci.

 

A hankali wata baƙar mota mai ƙirar Audi RS5 ta fara shigowa ciki Nasarawa daga farko farkon Nasarawa harya gifta sai kuma ya dawo baya a hankali yana zare baƙin glasses ɗin dake idanunsa,  saurayi ne ɗan kimanin shekaru 27 yana sanye da wani farin voyal wanda yay masa kyau sosai kasancewar sa farin bafulatani kana ganinsa Kasan cewar kuɗi sun zauna masa, a hankali yake tafiya da motar zuwa baya kasancewar shike driving ɗin ganin hakan yasa wanda ke kusa dashi yace "Ajmal me kake haka ne?"shiru Ajmal ɗin yay domin baya jin akwai abinda zai iya faɗa, a hankali ya gama tsayar da motar  tare da buɗe murfin motar ya fito ganin hakan yasa Karim yay saurin fitowa yana faɗin "wallahi kaifa ba hankali gare ka ba, kana ganin aikin dake gabanmu dole ne a wannan satin mu samu mu shawo hankali duk raguwar jama'ar" ina Ajmal baya gane yaran domin tuni idanunsa suka sauka akan fuskar Akeela dake kwance a ƙasan wata bishiya wallahi wallahi a wannan lokacin duk wanda yaga Akeela dole zuciyarsa ta buga domin ba zaka taɓa cewa ƴar hausawa bace, tana kwance kanta na zubda jini saboda wata muguwar faɗuwa da tayi gaba ɗaya kayan baccin dake jikinta sunyi wani bala'in yin datti gashinta ya wargatse yay ɗai ɗai, tsaye Ajmal yay akan Akeela yana jin zuciyarsa na bugawa, a hankali kuma ya tsuguna a gabanta dai-dai lokacin da Karim yake ƙarasuwa wajan cikin sauri yace "wai Ajmal meke damunka ne? Baka tsoran abin cutarwa ne? Kilama ba mutum bace Aljana ce, ina ka taɓa ganin mace mai gashin wannan?" Banza Ajmal yay masa domin yadda idanunsa suka sauka akan fuskarta yasa baya fahimtar komai dukkan wani abu na kansa sai da ya kunce, hannunsa ya miƙa tare da tattare sumar data rufe mata fuska cikin sauri ya rufe idanunsa yana faɗin "Ohh God"  Karim yay saurin faɗin "is she died?" Girgiza masa kai kawai Ajmal yay yana ƙoƙarin sanya hannunsa ya ɗauke ta Abbu dake ƙarasuwa wajan yace "Akeela! Allahamdulillah"

Da sauri ya sanya hannunsa ya ɗauke ta tare da kallon Ajmal yace "thank you son, wallahi tun jiya mukai missed nata yanzu na ƙara fitowa ne, kamar daga sama na hangeka ji nai kawai ina son ganin Meke faruwa cikin ikon Allah kuma naga Akeela thank you" jinjina kai kawai Ajmal yay yana shafa wuyansa sosai ya gane Abbu amma shi Abbu sam bai gane waye Ajmal ba, kamar bazai magana ba sai kuma yace "Dad! A nan kuke ne?" Kallon Ajmal Abbu yay yana karantarsa sai kuma yace "eh cikin Railway quarters no 112" idanunsa akan fuskar Akeela yace "ok Thank you" yana faɗin hakan ya nufi cikin motar tare da zama wajan driving ba ganin hakan yasa Karim shima ya shiga cikin motar da gudu Ajmal yaja suka bar wajan, mai makon yaje inda zashi sai kawai ya juya kan motar ya nufi hanyar gida da Mamaki Karim yace "wai Ajmal Meke damun ka ne?" Cikin ɓacin rai Ajmal yace "ban sani ba, banza shege munafuki kawai haba" ya faɗa cikin ɓacin rai yana ƙara sharara gudu.

Abbu shima cikin farin ciki ya nufi motarsa bai yadda ya ajjiye ta a back seat ba a nan saman jikinsa ya barta key yaywa motar ya juya zuwa gida tun a hanya ya kira number Ummi da sauri tai picking call ɗin tana faɗin "Something news?" Cikin ƙasa da murya yace "I've seen her Ummi on my way yanzu" Murmushi tayi tace "Allahamdulillah"

 

A wahala Akeem ya ɗago kansa daga cikin ruwan yana sauke wahalallan numfashi a hankali kuma ya buɗe idanunsa da sukai wani mahaukacin ja, ya jima cikin ruwan kafin ya fito ya ɗauki  bathrobe ya sanya a jikinsa, ruwa na zuba a jikinsa ya fito kai tsaye ya nufi cikin wani special bedroom ɗinsa Yana zuwa ya rufe ƙofar da key, derect bed ya nufa yana zuwa ya faɗa tare da jan duvet ya rufe jikinsa tass domin wani mugun bacci ya keji, kamar yadda ya saba haka yanzu ma ya jawo pillow ya rungome a tsakanin ƙirjinsa yana sauke numfashi a haka bacci ya ɗauke sa da tunanin yadda zai rama abinda akai masa akan wannan yarinyar.

 

Ummi da Didi ne suka miƙe lokacin da Abbu ya shigo da Akeela a hannunsa, kai tsaye part ɗin su Aleema ya nufa da ita, Ummi na biye da shi Mami ko motsawa ba tayi ba idanunta akan cineme,  yana zuwa su Afaf suka miƙe fuskarsu ɗauke da farin ciki, kwantar da ita yay cikin nutsuwa Ummi tace "bari na duba ta" gefe Abbu ya koma yana jin kamar ya kori kowa ya jata jikinsa ya rungome ya lallasheta da kansa amma no way ahlinsa na wajan dole yaja da baya da yaga yana neman zama wani uncontrol sai kawai ya fice daga part ɗin, a hankali Ummi ta zauna idanunta akan Akeela tace "Afaf jeki kawon warm water a bowl with towel" "ok Ummi" bathroom tayi ta shiga haɗa ruwan zafin kana ta fito ɗauke da towel ɗin "drop it and leave and you too Aleema" ficewa duk sukai gently Ummi ta zamewa Akeela rigar jikinta babu ko bra a jikinta cikin tausayin ta Ummi ta shiga goge mata Jikinta da ruwan zafin, sosai ta kasa mata Jikinta ta shafe ta da robe kana ta sauya mata kaya zuwa Sleeve Bodycon mai sauƙin nauyi saboda zafi ake da alama akwai ƙaramin hadari a ƙasa, kwantar da ita tayi ta rufe da duvet gudun a.c ta ƙaro mata ba mai cutarwa, fuskarta tabi da kallo ganin yadda take sauke ajjiyar zuciya a jajjere, fita tayi daga bedroom ɗin a Parlo ta samu su Afaf ɗin suna buga game ficewa tayi daga part ɗin nasu baki ɗaya.

Ummi na fita Akeela tai wani irin juyi tare da buɗe idanunta abinda basu sani ba idanunta biyu kawai har yanzu mutanan na kanta ne irin aljanun nan ne masu mugun abu wanda sai ansha wahala kafin suyi magana ma. Parlo Ummi ta dawo kusa da Mami ta zauna ba tare da tace komai ba, a hankali Abbu yake tafiya cikin tafkeken bedroom ɗinsa hannunsa goye a bayansa sai numfashi yake fitarwa, gaba ɗaya yama rasa yaya zai yi baya jin daɗin komai burinsa kawai yaga fuskar Akeela, wani murmushi yay yana jin daɗi domin sai yanzu ya tuna da Ƙofar dake bedroom ɗinsa wacce kai tsaye hanyar tayi har parlon su Aleema, jikinsa na rawa ya buɗe ƙofar tare da fita su Afaf na tsaka da buga game su kaga Abbu kamar daga sama kallonsu yay yace "bari na mata magani" jinjina kai kawai sukai, bedroom ɗinsu ya nufa jikinsa har wani tsuma yake tana zaune ta tura kanta cikin tsakiyar cinyoyinta, ƙarasawa yay tare da faɗin "Babyn Abbunta zo nan gani nazo rarrashin ki" shiru bata motsa ba hakan yasa ya ƙarasa inda take yana zuwa ya jawota jikinsa yana shafa kanta tare da faɗin "Babyna" jajayen idanunta ta ɗaga ta kallesa cikin wata kakkausar murya tace "Abbu Akeem" zuciyar Abbu ce ta buga da ƙarfi cikin damuwa yace "me Akeem zai maki" kuka ta sanya masa ko kuma aljanun suka sanya masa cikin wata iriyar Murya mara daɗin saurara tace "Akeem muke son gani Abbu" sai a lokacin Abbu ya fahimci ba ita take Maganar ba, shafa kanta kawai yay yana faɗin "sorry Babyna kina shan wahala ko? Dana aureki zan bar ƙasar dake" wani irin kallo tayi masa tace "kai ma baka da lafiya Abbu Meye Wannan a jikinka?" Bai tsaye jin zan canta ba ya ɗura bakinsa a kunnanta ya shiga yi mata addu'a, miƙa ta fara yi kafin kuma a hankali jikinta ya saki bacci mai nauyi ya ɗauke ta, Murmushi Yay yace "Babyna zaki sanya zuciyata bugawa idan kina kiran sunan Akeem, Tabbas ni kaɗai zaki so nasan Akeem bai taɓa cewa yana sonki amma yadda kike da mugun kyan nan masu kawo maki hari suna da yawa, ni kawai zaki so zaki zauna dashi, zan koyar dake zallar so da kuma ƙauna ta Akeem kuma duk yadda za'ai a watan nan sai na tura shi Germany zai nesa dake sai yay Shekaru masu yawa lokacin tuni kin zama tawa zai dawo" ya faɗa yana shafa kanta a hankali ya sumbaci goshinta..

 

 

*Singapore*

Khoo Teck Puat Hospital

A hankali motar tai parking Meema ce a gaba sai mahaifinta President Ahmad Adil yana Cikin Wata dakakkiyar shadda dark blue mai kyau sai sheƙi yake, yayinda ita kuma take cikin wata milk ɗin abaya da red ɗin Stones tayi rolling kanta da vail tayi kyau sosai, hannunta riƙe da waya ga wasu manyan guards  kai tsaye cikin female sugical world suka nufa shiru asibitin saboda asibiti ne na masu kuɗi babu hayaniya ko kaɗan, cikin sauri Meema ta buɗe ƙofar office ɗin Dr ɗin ba tare dako permission ba, yana zaune yana duba wasu files Meema ta shiga tana faɗin "Dr what happened i saw your miss call" Murmushi yay yace "Na kira na faɗa maki yau za'a buɗe fuskar ƙaninki" wani daɗi taji da sauri ta rungome Dad tace "Dad bana faɗa maka ba" hannunta ya riƙe yace "ok be careful" Miƙewa Dr yay cikin so much respect ya shiga gaisar da Dad kafin yace "follow me" binsa sukai a baya har suka nufi wani room 11 buɗe ƙofar akai Dr na gaba Meema na baya sai Dad, cikin sauri ta zame hannunta ta nufi inda yake a kwance da kayan marasa lafiya Murmushi tayi tana riƙe hannunsa, ɗumin hannunta daya ratsa tafin hannunsa yasa yay sauri riƙe hannunta domin yau gaba ɗaya ba tazo hospital ɗin ba kamar yadda ta saba, kayan aiki Dr ya ɗauko Meema jikinta har rawa yake domin ta matso ta ganshi, cikin nutsuwa Dr ya fara ware masa bandejin fuskarsa yana cirewa, bakinsa ne ya fara bayyana mai ɗauke da jajayen laɓɓa, sai kuma hancinsa a haka har aka gama buɗe masa fuskar, idanunsa a rufe ruff fuskar Abbu kwance a saman nashi fuskar Dr ne yace "Congratulations now open your eyes" slowly ya shiga buɗe idanunsa kai tsaye ya sauke ganinsa akan fuskar Meema babu ko kifta idanu, cikin farin ciki Meema tace "Bro na" shiru yay mata bai ce mata komai ba ganin hakan yasa ta kwaɓe fuska tace "why baya magana?" "Ai sai ya koyi komai ba, kinga aiki ya sameki" Dad kam tunda aka buɗe fuskarsa yaji gabansa ya faɗi sosai ya san me fuskar amma mene haɗin Meema da wannan gske har ta sanya aka sawa wani ita? hannunsa Meema ta kama tace "I'm your sister" cikin kwaikwayon Abinda ta faɗa yace "I'm your sister" wani irin Murmushi Meema tayi tace "A'a ba haka za kace ba" kallon Dad tayi tace "Dad his name please" buɗe baki Abbu yay yace "Asheer" "Wow! Nice name" Meema ta faɗa tana faɗin "as from today sunanka Asheer amma zanna ce maka Bro ni kuma kace Sister" dry Dr yay yace "tab kina nufin a yanzu duk zaki koya masa komai? Mudai nan kafin ku tafi zamu kuya masa wanka,Sallah, cin abinci komai" Asheer kuwa tunda ya ɗura idanunsa akan Meema yaƙi ɗaukewa domin tsoran kallon mutanan wajan ma yake, miƙewa tayi zata ɗauko masa mirror da sauri ya riƙe hannunta yana juya idanunsa, da ƙyar dai ya sake ta lokacin da yaga kansa a madubi kansa ne yay wani irin sarawa da sauri ya saki madubin a ƙasa ji kake tasssss ya fashe a ƙasa cikin sauri kuma cike da tsoran abinda yayi ya ɓoye fuskarsa a bayan Meema..

 

 

Today is Monday yau Akeem ya tashi da azumin Litinin da Alhamis kamar yadda ya saba, rabonsa da ganin Akeela wajan sati guda kenan, domin ko zama yanzu ba yayi a Parlo, a hankali ya fito daga motarsa lokacin ana ta kiran sallar magrib kai tsaye pampo ya nufa tare da ɗaura alwala, ko cikin gida bai shiga ba ya nufi cikin masjid ɗin, lokacin daya isa ana jiran zuwan liman amma Shiru ganin an rasa wanda zai ja sallar sai kawai yay gaba tare da tada kabbara, nutsuwa kowa yay a hankali cikin zazzaƙar muryarsa mai daɗin gaske ya fara fidda kira'a yana fidda makarijil huruf, a can gida kuma Akeela na zaune domin ita sosai azumin ya wahalar da ita kuma ta saba tana yinsa ne, idanunta ta buɗe jin sautin Muryarsa ya daki kunanta rabon da taji Muryarsa haka harta mance, Miƙewa tayi saboda wani sanyi da jikinta yay a hankali ta nufi bathroom ta ɗaura alwala kana ta dawo tayi sallah ji tayi jikinta babu daɗi sai kawai ta zame hijab ɗin ta nufi bathroom, cikin sanyin jikinta ta buɗe ƙofar ba tare data rufe ba ta fara kwaɓe kayan jikinta ruwan zafi ta sakarwa kanta tana sauke ajjiyar zuciya.

Bayan an idar da sallah Akeem ya fito Abbu na bayansa a haka suka nufi gida babu kowa Parlo duk Sallah suke, part ɗinsa ya nufa Akeem kuma ji yayi yau babu abinda ya keso sama da zuma yasan kuma Didi kawai ke Shanta, part ɗin ta ya nufa a hankali ya shiga lokacin tana Sallah, wani daɗi yaji domin baya son masifar ta a yanzu, fridge ɗinta ya nufa gaba ɗaya robar zumar ya ɗauko Didi kam banda zare ido babu abinda take da taga abin bana wasa bane sai ta fara "ehem! ehem!" Ko Kallonta bai ba ya nufi waje ai da sauri tace "Assalamu alaikum" miƙewa tayi tana faɗin "Muhammadur Rasulullah s.a.w Audil sata ƙiri ƙiri Ubangiji dai yau ya nuna min ɓarawon zumata" jin tana kiran sunansa kuma ya tabbatar part ɗinsa zata bisa cikin rashin makamar yi kawai ya faɗa part ɗin su Aleema ga mamakinsa sai yaji tana faɗin "Munafikin ai na ganka" da sauri ya juya yana duban inda zai ɓoye ganin ƙofar bathroom a buɗe ya wani faɗa ciki da sauri yana murzawa ƙofar key.....

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post