Rumbun Qaya hausa Novel Page 14

Rumbun Qaya hausa Novel Page 14

Rumbun Qaya hausa Novel Page 14

RQ


      Page 14


Hafsat Rano


   Da duku-duku suka tashi ita da Amina suka shirya breakfast din da za'a kaiwa Abby a asibiti, daga nan sai ta wuce wajen aiki ta dau excuse ta dawo asibitin dan tana son zama kusa da Abbyn ta. 

  Wajen karfe bakwai suka fita tare da Muhammad ya sauke ta ya dawo gida ita kuma ta shiga asibitin ta tarar da Abbyn nata yana bacci Hamma Hydar ne kawai a dakin Lamido yaje jigawa wani aiki da Abbyn yayi masa, Dadah da Babbo Sadeeq sun koma Adamawa saboda aikin da ya taso masa.

   Tana zaune har lokacin tafiyar ta yayi sai ga Lamido ya shigo rike da wata jaka ya ajiye a gefen gadon daidai lokacin da Abbyn ya farka dan tunda yayi sallar asubah yake bacci. Ganin Raihanan a zaune ya sakashi jin dadi, Hamma Haydar ya taimaka masa yayi brush ita kuma ta bashi abinci sannan tace zata je ta dawo. Tare suka fito da Hamman Haydar din ya kaita har office din sannan ya wuce gida ya shirya. Gobe suke san wucewa Adamawa dan Abbyn yace baya son cigaba da zama a Kanon har sun siya ticket din jirgi dan ba zai iya doguwar tafiya ba, amma basu sanar wa Raihanan ba dan sun san dole za'a yi rikici da ita.

   

 Attendance ta dauka ta zauna bayan sun gaisa da mutanen dake reception din banda Zainab da ta daina mata magana tun ranar da abin nan ya faru, ita ta manta ma shaf da anyi haka wallahi, sai data ga tayi mata magana taki amsawa ta tuna. Tun daga ranar ta fita sabgar ta itama zatayi mata sallama dai ruwan ta, ta amsa ruwan ta, taki amsawa wannan duk be shafe ta ba.

  Kira ne ya shigo wayar ta, tana kokarin clearing kan table dinta, tabi wayar da kallo da mamakin dalilin kiran nata a wannan lokacin, hada ido sukayi da Abdulhakeem sai kawai ta d'aga.


"Ina kwana Anty?"


"Lafiya lou Raihana, kina lafiya?"


"Lafiya Lou."


"Har kinzo office din ne?"


"Eh nazo ban dade ba."


"Yawwa, Masha Allah , Aryan ya shigo?"


"Ban sani ba wallahi..."


"Oga Aryan ya shigo?" Ta dan janye wayar ta tambayi Abdulhakeem, girgiza mata kai yayi alamar a ah


"Be shigo ba wai."


"Toh shikenan, naji alamar kina cikin mutane, ko zaki dan matsa gefe?"


"Toh." Tace tayi hanyar fita daga office din nasu, ta nufi kitchen din dan tasan nan ne kadai za'a samu ba kowa.


"Yawwa kina jina? Akan matsalar nan ta Aryan ce, kinsan nace miki muna zargin duk magungunan sa baya sha ko? Toh shine likitan sa yazo kin ganshi zaune ma, da zaki taimaka ki samo min key din gidan nan nashi, akwai in da yake ajiye su tabbas kuma a gidan ne, dole mu san halin da yake ciki dan ciwon idan yayi worst har haukacewa anayi Raihana."


Sai ta fashe da kuka sosai, kukan da ya sake karyar mata da zuciya cike da tausayawa tace


"Aina key din yake?"


"Aljihun suit dinsa, yau ita zai saka saboda yana da meeting da shareholders, anan zaki samu idan kin dauko ki zarto gidan kawai ki kawo min da sauri, karki bari ya san bakya nan dan zai iya zargin komai."


"Ok,zan kawo in sha Allah."


"Tunda kin shigo sai ki karasa ladan ki, ki dafa mana shayi."


Kamal yace yana daga kofar kitchen din, zare wayar tayi daga kunnen ta, sannan ta gaishe shi.


"Lafiya lou, naje office dinku ai Abdul yace kin fito, ashe ma kina dayan office din naki"


Murmushi tayi kawai, ya ja mata kofar ita kuma ta shiga fiddo da kayan da zata bukata.

     A makare ya shigo office din dan haka yana zuwa akan aiki ya dira, ya shiga duba abubuwan da yayi ragowa kafin meeting din nasu da yake karfe biyu. Tunowa yayi da wani aiki da be karasa ba, sai ya jawo landline din dake saman desk din nasa ya shiga kiran office din su. Abdulhakeem ne ya daga ya tambaye shi ko tazo,tana kitchen yace masa sai yace shi yazo, ya ajiye wayar ya dauko takardar daidai lokacin Abdulhakeem din ya shigo ya bashi takardar yace ya kai mata yana son result in less than an hour. Karba yayi ya fita shi kuma ya cigaba da abinda yake yi.

   


***Tana tsaye gaban coat din sa dake rataye a jikin hanger da yake makaleta kullum yazo office din, waige-wage take tana son yin sauri ta dauki key din, sai da ta tabbatar da babu motsin kowa tayi saurin saka hannu a aljihun rigar ta jawo key din ta damke a hannun ta.


"What are you doing..." Ya fada yana tsaye daga bayan ta


Saura kiris glasses din idon ta ya fadi kasa, tayi saurin tare shi da dayan hannun ta juyo tana kallon sa. Takowa ya shiga yi har zuwa gabanta yana kare mata kallo tun daga sama har k'asa, kafin ya maida kallon sa zuwa wajen coat din tashi dake sakale.


"Me kike yi anan?"


Yace muryar sa a d'an shake yana kallon fuskarta, kanta ta sunkuyar kasa sosai ya cigaba da kallon ta a nutse kafin yace


"Are you trying to steal something?"


Zaro idanun ta, tayi da sauri ta hau girgiza kai


"Then tell me, me kike min a wajen rigana?"


"Am..am... Dama nazo na kawo maka wanchan report din da na hada ne, so sai na tarar kana restroom shine na ajiye a saman table shine sai naga kamar wani abu a saman rigar shine nazo zan duba na cire maka."


Dan jim yayi yana kallon ta, kafin ya ja siririn tsaki ya nufi wajen zaman sa ya zauna.


"Show it to me."


Yace yana jan mouse ya dora hannun sa akai. Fakar idon sa tayi ta tura key din a cikin aljihun jacket din dake jikin ta sannan ta karaso ta dauki report din ta bud'e ta fara masa bayani. Danne dannen sa yake har ta gama sai da yaji tayi shiru sannan ya dago ya dan kalle ta


"Ina jinki." 


"That's all." Tace 


"Shikenan abinda kika iya samu?" 


Gid'a kanta tayi kad'an


"Come here." 


Yace yana maida kansa ya cigaba da abinda yake, gefen sa ta matsa ta tsaya daga dan baya


"Result din nake son gani, show it to me."


"Ok!" Tace ta dan runkwafo kad'an ta shiga nuna masa. Kamshin turaren ta ne ya shige masa chan cikin hancin sa ya haifar masa da mixed feeling, dan muskuta jikin sa yayi yadda ba zata gane ba amma still yana jin kamar sake matso shi tayi.


"It's ok!" Yace da dan karfi


"Just go, ki tura min ta email zan duba anjima."


"Ok...Thank you" 


Tace dauki report din zata fita


"Wait..."  Yace ta juyo ta tsaya


"Ki bawa Kamal shayi na ya kawo min."


"Ok sir."


"Sannan...karki kara saka turare me karfi idan zaki zo aiki."


"Na'am?" 


"You heard me right! You may leave."


"Ok."  Tace da saurin ta, ta fice hadda dan gudun ta

  

Tana fita ya saka hannu ya hau janye necktie din wuyan sa yana mikewa tsaye, ya isa gaban dan madaidacin fridge din sa ya dauki ruwa me sanyi ya hau sha


"May I come in?"


  Ya turo kansa ya rike kofar ba tare da ya shigo ba


"Kana da matsala, kayi ta tsaiwa a wajen." 


Yace yana dire robar ruwan ya shiga takawa zuwa seat din sa ya zauna. Shigowa yayi ya rufe kofar ya samu waje ya zauna shima yana murmushi


"Ya akayi?"  Yace yana duban sa 


"Akwai babban labari..."


"Kamar na me fa?"


"Barrister Nasir Matawalle is out!"


"What!!!? Ya fada yana mikewa 


"Da gaske ko da wasa?"


"Allah kuwa, naji labari daga majiya me karfi ya fito last week ending, but zancen dai be fito sosai ba dan kamar yaran sa ne basa so a sani saboda suna so ya samu kulawa ta musamman ne."


"Alhamdulillah!" 


Ya fada a hankali yana maida kansa baya ya jingina da jikin kujerar yana lumshe idon sa. 


"Me ya kamata ayi yanzu?" Kamal yace ganin yayi shiru, bud'e idanun sa yayi ya zauna sosai yace


"Time zamu samu muje mu ganshi, inaso na ganshi dan shi kadai yasan abinda ya samu Mom, shi ne kawai zai taimaka min na cika buri na."


"Kana ganin bud'e case din ba zai zama matsala ba? Kasan fa Daddy baya so, sannan sau nawa kana zuwa prison dan ganin sa amma yaki, kana ganin zai saurare ka yanzu bayan da be saurare ka ba?."


"I don't know... "


Yace yana tuna jelar zuwa prison din da ya dinga yi dan duk ya samu ganin shi amma fafur yaki yarda su yi wata doguwar magana.


"Toh yanzu dai menene abun yi?" 


"Zuwa zamuyi mu ganshi din, ba kuma zamu hakura ba har sai ya hakura ya ganmu munyi magana, he's my only hope."


Shiru ya danyi sai ya dora


"Gaba daya rayuwata na yi ta ne akan jiran wannan ranar, that's what keeps me going, ba zan taba hutawa ba har sai na san abinda ya samu Mommy, wannan alkawari na ne, sai na bi kadin mahaifiyata, ko da hakan na nufin..."


"Shikenan, shikenan.  You have my support, Allah ya bayyana mana gaskiya."


"Amin! Thank you."


Yace yana hasaso abinda zai faru kuma, ajiyar zuciya ya sauke ya sake tashi da nufin dauko key din nan ya bawa Kamal.


***Tana fita daga office din nasa ta dauki handbag dinta akan table ta zare rigar saman ta ajiye ta fita da saurin ta, a titi ta tsaya ta kira wayar tana kokarin tsaida me napep


"Hello..." Tace tana fadawa cikin napep din bayan ya tsaya


"Eh na dauko, ina hanya ma."


Magana akayi daga dayan bangaren tace;


"Ok tam.."


ta kashe wayar tana sake duba key din ta tabbatar yana ciki. Tafiya kad'an suka isa unguwar, ta bashi kudin sa ta sauko ta karasa gidan a kafa.

  Ciki ta shiga bayan an bud'e mata kofar tangamemen gidan da kaf unguwar babu me girman sa, yau ne karo na biyu da ta zo gidan amma sai take ganin kamar yau ne karon farko. A hankali take tafiya tana karewa gidan kallo har ta isa main part din. Tana zuwa daidai kofar ta bud'e da kanta, ta saka kanta ciki bakin ta dauke da sallama. 

   Tana hakimce a saman daya daga cikin kujerun falon rike da door remote din dan ita ta bud'e mata kofar dan ta hango ta tun sanda ta shigo gidan. 


"Rayhana..." 


Ta kira sunan ta tana sakar mata murmushi, murmushin ta maida mata itama ta gaishe ta a nutse sannan ta sa hannu ta ciro key din ta mika mata


"Good! Kin taimaka min sosai kamar yadda nima na taimake ki, kin saka alkhairi da alkhairi nagode sosai."


"Ba komai Aunty!" Tace tana murmushin jin dadi


"Me zaki sha a kawo miki?"


"Ba komai, komawa zan kar ya gane na fita."


"Ok! Zan kiraki kinji?"


"Ok." Ta mike tana rataya jakarta tayi hanyar fita


"Kin ga jirani mu fita dake dan nima wajen hanyar taku zanyi."


"Ok nagode."


Tace ta koma ta zauna ita kuma ta tashi ta shiga ciki bayan ta dora wayarta a saman hannun kujerar da Batul din ke zaune. Tana zaune wayar tayi yar kara alamun shigowar sako, kallon wayar tayi sai ta dauke kanta kawai tana cigaba da more kallon dankararren falon. Wani sakon ne ya sake shigowa a wannan karon sai ta kasa dauke idon ta akai ta shiga karanta sakon da yake yawo a saman wayar


_"An gama hajjaju, an zuba poison din, wuyarta Aryan yasha tea din nan, sai dai wani ba dai shi ba, tunda mun samu key din sai kiyi kokarin kwashe duk wani abu da ya tanada as evidence, ita kuma yarinyar ita za'a kama da case din poison din, kinga shikenan mun jefi tsuntsu biyu da dutse daya!!"_


Wani irin sarawa kanta yayi cikin yanayin tashin hankali ta mike tsaye


"_Na shiga uku!"_


Ta furta tana dafe kirjin ta.


_" Amfani dani tayi kenan? Karya tayi min tasa na dauko mata key din? Duk abinda ta fada min akan sa kenan karya take?."_  


"Shayi? Wayyo innalillahi." Ta fada gabanta na faduwa


_"Ya Allah!!!"_


     Da sauri ta juya har da dan gudu-gudu ta fice daga falon. Tana fita Hajiya Zeenat ta fito, mamakin rashin ganin ta ya kamata ta shiga kiran sunan ta, waya ta dauka ta kira gate ta tambaya aka ce mata yanzu ta fito ta fita 


"Ok... Ta huta" Ta dauki wayoyin nata ta watsa su a handbag dinta ta shiga kwalawa mai aikinta Harira kira


  ****Yadda take gudu zaka dauka mahaukaciya ce sabuwar kamu, kamar zata fada duk napep din da tazo haka ta dinga bin su idan ta tsaida su basu tsaya ba, a karshe ta samu wani ta fada tana haki. Suna isa ta ciro kudi bata duba ko nawa bane ta cilla masa ta shiga building din a guje. Bata san in da take jefa kafarta ba har ta isa reception din, baki daya ma'aikatan wajen duk suna tsaitsaye sun yi cirko-cirko, kallon ta suka shiga yi irin kallon tuhumar nan, jikinta ne ya hau rawa tayi saurin haurawa sama zuwa office din sa. Kofar sa a bud'e take sabanin yadda take a rufe a kowanne lokaci, maganganu ne ke fitowa daga ciki wanda ta gaza fuskantar daya daga ciki, ji tayi kamar an dode mata jin ta, burin ta kawai ta isa ciki ta tabbatar da be sha shayin nan ba, kowa yasan Aryan da masifar son hadin shayi me na'a na'a da sauran nau'ikan kayan kamshi. Duk da rashin yardar sa da kowa amma ya kan sha shayin wanda ya yarda ta hada masa ita kadai, shi ma sai da Kamal ya tabbatar masa da babu wata matsala sannan ya amince. Idanun ta ne suka sauka akan Kamal dake dauke da tsantsar tashin hankali shinfide a saman fuskar shi, ji tayi tamkar an sassare mata guiwowin ta, ta zube a wajen tana fashewa da kuka.


"Na shiga uku."


Kawai bakin ta ke furtawa. Ji tayi an saka hannu an tura kofar office din, shiru ya biyo bayan hakan sai shashekar kukan ta dake tashi hade da garar A.C da aka kureta sosai har take fitar da sound me dan karfi.


Durkusawa yayi a gabanta ya toge hannun akan cinyar sa. Kamshin turaren sa ne ya doki kofofin hancin ta, tayi saurin dago jajaye idanun ta da suka yi matukar rinewa saboda kuka. Ganin sa a durkushe a gaban ta ya sakata zabura.


"Me ya faru?" 


Yace yana zuba mata ido muryar sa a matukar dashe saboda tsabar bacin ran da yake ciki. 


Mikewa tayi tsaye, ya saka hannu ya jawo ta da dan karfi har sai da tayi yar kara, ya kalli hannun nata ya dauke kansa yana girgiza mata kai.


"Menene?" 


Ya sake maimaitawa har lokacin idanun sa dake matukar shanye na kanta ya zuba mata su. Girgiza kai ta hau yi da sauri da sauri, zatayi magana kenan Kamal yayi saurin katse ta


"Ga key din Aryan, ashe nan ya fada."


Dago idanun sa yayi, ya kalli hannun Kamal din da yake rike da key din da suke ta nema tun bayan fitar ta, mikewa yayi daga durkuson da yayi ya karbi key din yana kallo, sai kuma ya damke shi sosai yana sauke ajiyar zuciya


"Jeki Raihana, jeki jirani a office dina."


Kamal yace yana takowa gabanta, kasa mikewa tayi sai kukan da take yi har da shasheka. Sake maimaitawa yayi ta dafa da k'yar ta tashi, ta bud'e kofar ta fito ta nufi kitchen din da sauri dan a chan ta bar shayin tun bayan ta gama, ta kuma tuna da yace ta bawa Kamal ya kawo mishi bata bashi ba dan hankalin ta yayi gaba. A ajiye ta ganshi sai dai ba yadda ta barshi ba, tana kalla ta san an taba. Sauri sauri ta juye shi a sink ta wanke kayan.


    A tsaye ta samu Kamal din yana kaiwa da komowa, jin ta shigo ya saka shi saurin kallon kofar. Kanta a k'asa sosai ta karaso ciki ta samu waje ta zauna. Kofar ya rufe sannan ya dawo ya zauna yana duban ta


"Ina key din?" Yace mata kai tsaye, shar-shar-shar hawaye ya shiga biyowa kuncin ta, tissue ya mika mata da sauri


"Yanzu ba lokacin kuka bane ba, yana ina key din?"


"Hajiya Zeenat ce tasa na dauko mata."


Kad'an ya rage be fado daga kujerar da yake kai ba, yadda yayi wata irin zabura saboda tsananin mamakin abinda tace.


*RUMBUN QAYA🔥


*DAUDAR GORA*🔥


*IDON NERA*🔥


*A RUBUCE TAKE*🔥


*KI KULANI*🔥


*_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊


*Nasan zakuce ya da murmushi haka?*


*Wanda bai shigo ba bazai gane ba*


*Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️


*KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU*


*KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?*


*KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?*


Littafi daya---400

Biyu---600

Uku----800

Hudu-----1k

Biyar din duka----1200


*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥


0022419171

Maryam sani

Access bank


*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*


09166221261


🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪

*Ina yan uwa 'yan nijer?*

*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*


+227 90 16 59 91


Littafi daya---450CFA

biyu---650CFA

uku----850CFA

hudu----1050 CFA

Biyar----1250CFA


*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*


*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*


*Thanks for choosing us*🔥

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post