Rumbun Qaya hausa Novel Page 15

Rumbun Qaya hausa Novel Page 15

Rumbun Qaya hausa Novel Page 15

RQ

      Page 15


Hafsat Rano


••••••


A tsaye ta samu Kamal din yana kaiwa da komowa, jin ta shigo ya saka shi saurin kallon kofar. Kanta a k'asa sosai ta karaso ciki ta samu waje ta zauna. Kofar ya rufe sannan ya dawo ya zauna yana duban ta


"Ina key din?" Yace mata kai tsaye, shar-shar-shar hawaye ya shiga biyowa kuncin ta, tissue ya mika mata da sauri


"Yanzu ba lokacin kuka bane ba, yana ina key din?"


"Hajiya Zeenat ce tasa na dauko mata."


Kad'an ya rage be fado daga kujerar da yake kai ba, yadda yayi wata irin zabura saboda tsananin mamakin abinda tace. Fashewa ta sake yi da wani irin kuka, ya mike tsaye yana mata wani irin kallo, kafin ya nuna ta da hannun sa


"Dama kece spy din?"


Girgiza masa kai ta hau yi da sauri


"Wallahi yaudara ta tayi, bansan me yasa tayi amfani dani, amma wallahi bani da burin cutar da kowa."


Yadda take kuka sosai ya sakashi samun waje ya zauna, a kalla zai bata damar jin ta bakin ta kafin ya yanke mata hukunci, dan yasan wallahi in dai har Aryan ya gano tana da alaka da Hajiya Zeenat shikenan an gama, ba ita ba kuma, duk wani da yasan yayi wata alaka ko mu'amula da ita babu shi babu su.


"Sai kiyi min bayanin komai, sannan karki yi mun karya."


Bayan hannun ta, tasa ta goge hawayen da yaki tsayawa sannan a hankali ta soma bashi labarin haduwar su da Hajiya Zeenat da duk abinda ya faru, da fara aikin da tayi dasu har zuwa gidan Aryan din da tasa ta taje, da kuma sakata daukar key din duk a tunanin ta taimakon Aryan din zatayi.


"Bayan na bata key din ta shiga ciki, anan na gane amfani tayi dani, suna maganar sunyi poisoning tea dinsa..."


"Poison!!!" 


"Haka na gani an turo mata message, abinda ya saka ni tahowa a yanayin nan kenan, bansan abinda suke shiryawa ba kenan, wallahi ban sani ba."


Mikewa tsaye yayi dan zaman ma ya gagareshi, wajen kofar ya koma ya bud'e ya leka ya tabbatar babu kowa a wajen sannan ya maida ita ya rufe ya dawo ya tsaya yana zagaye a dakin 


"You have indeed dodged a bullet, da Aryan yasha shayin nan fa?" 


Yace da muryar sa da take nuna yanayin tashin hankalin da yake ciki da wannan labarin 


Girgiza kai tayi har lokacin hawayen yake tsayawa sam


"She used you Raihana, tayi amfani dake ta samu abinda take so, a karshe ta dora miki blame din kamar yadda tayi a baya, da ace Aryan yasha tea din nan, da ba maganar da ake yi yanzu ba kenan, saboda ba zaki taba fita ba, ba zaki fita ba sam."


"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, Allahuma ajirni fi musibati..."


"Kin gama magana Rayhan, tunda kika ambaci Allah. Sai dai akwai babbar matsala."


Kallon sa tayi da alamar tambaya ya dora


"Yadda na san Hajiya Zeenat, bata taba barin abinda ta saka a gaba, sannan kin riga kin shigo circle din, dole dole ki san me yake faruwa, sai dai, dole a yanzu ki cigaba da bin ta a yadda kuke da, karki kuskura ko da wasa ki nuna mata kinsan shirin ta. Hakan shine kadai kwanciyar hankalin ki, kuma hakan shine zai taimaka mana mu kara sanin duk wani shirin ta."


"Wayyo Allah nah, wallahi ni tsoro nake ji."


"Me kike so ayi?"


"Garin mu nake son komawa, bana son cigaba da zama anan, tsoro nake ji dan Allah."


"Service din fa?"


"Innalillahi." 


"We have to do this together Raihana, ki taimaki rayuwar Aryan, dan Allah ki taimaka mana..." Sai ya dora 


"Na chanja key din nan bayan na samu leakage na son daukar, amma bansan wa zata saka ya dauka mata ba, saboda yadda Aryan yake kaffa-kaffa dashi zai yi wuya a yi dauka, ashe tayi amfani dake ne, saboda bayan Ya Nabeela dani babu wani da Aryan yayi saurin trusting sama dake, bansan me yasa ba, amma ko ma menene kina da babban tasiri a gare shi, dole zaki taimaka muyi aikin nan tare in har kina son ceto rayuwar sa, labarin sa yana cika da abun tausayi da tashin hankali wanda idan kika ji ke da kanki zaki yarda da yana bukatar taimako."


Kukan ta ne ya rinjayi maganar da take son yi, bata son tashin hankali ko kad'an dan bata taso a cikin sa ba, bata taba sanin akwai irin wannan rayuwar ba sai yau, ta kan yi tunani sosai akan dalilin da ya saka Abbyn ta zaman prison amma kuma bata samun gamsashiyar amsa a wajen wanda ya kamata su sanar mata. Duk da tana da yakinin sharri akayi masa, dan ta tabbata Abbyn ta baya cikin mutane marasa kirki sai dai kaddara da ta riga fata. Sai dai a yau ta sake tabbatar da akwai tarin mutane masu bakar zuciya a doran kasar nan, masu halin Hajiya Zeenat wanda zasu iya yin komai akan cikar burin sa. Tun farkon haduwar ta shirya komai, ta dora ta akan tsarin ta da abinda take so, dalilin ta kenan na kawota aiki a wajen. Duk cikin plan din ta ne. Ya zatayi yanzu? A yanzu lokacin farin ciki ne a gare su na fitowar Abbyn su, ba zata so tayi wani abu ko tazo da wani abun da zai saka yan uwanta a tashin hankali ba, sun mata dukkan gata, sun fifita bukatar kansu akan tata, dole tayi kokarin ganin ta danne damuwar ta zuwa lokacin da Abbyn ta zai warware baki daya.

  Kiran wayarta da akayi ne ya katse mata tunanin da take, ta share hawayen sannan ta daidai ta muryar ta sannan ta d'aga


"Hamma na."


"Me ya faru? Baki da lafiya ne?" 


Yace mata dan duk yadda taso ta daidaita muryar ta sai ya gano ta


"Cikina ne yake ciwo." Tayi karya dan tasan idan tace mishi babu komai ba yarda zai yi ba


"Subhanallah, bari nazo na dauke ki, ki nemi excuse a wajen aikin dan Abby yace gobe tare zamu tafi dake, idan kikayi sati daya sai ki dawo."


Kallon Kamal tayi shima ita yake kallo kuma yana dan jiyo muryar Hydar din, gid'a mata kai yayi alamar eh


"Ok tam, sai kazo Hamma." Ta zare wayar 


"Yayanki ne?" 


"Eh." Tace a sanyaye


"Shikenan, ina ganin hakan zai taimaka miki ki samu hutu sosai, next week sai ki dawo idan Allah ya kaimu, zan ma Aryan magana."


"Nagode."


"Ba komai, kiyi kokarin boye damuwar kar ki yarda ta gane."


"I will try."


"Yawwa, Adam yazo neman ki dazu, abinda ya faru kenan har kika ga Aryan a cikin yanayin da yake ciki, muna cikin neman key din ya shigo yana neman ki, abinda ya bata ran Aryan kenan har suka dan samu matsala. Akwai wata alaka tsakanin ki da Adam din ne?"


"A ah, babu komai."


"Ok ki kula sosai."


"In sha Allah."


***Duk da kasancewar mukullin a hannun sa amma ya kasa nutsuwa da abinda ya faru a dan lokacin, ya akayi ma key din ya fada kasan table din sa bayan tunda yazo be ciro shi ba. Menene matsalar ta da har zata zo tana rusa musu kuka haka bayan babu wanda yasan dalilin fitar ta daga office din cikin gaggawa. Tun ranar da ta sanar dashi mahaifiyar ta, ta rasu yaji tausayin ta ya tsarga masa, ya hasaso kalar rayuwar da 'ya mace zatayi ba tare da uwa wadda ta kasance jigo ba. Tabbas akwai abinda yake damun ta, dan har tayi yunkurin sanar dashi sai Kamal ya katse ta, ta hanyar maganar key din. Ya kamata su nemi ba'asin dalilin kukan nata wanda yayi kama da na wanda ya shiga mummunan tashin hankali. Da farko ya dauka akan key din ne wanda tashin farko ita ya zarga dan yana dubawa da yaga babu ya tuna sanda ya ganta a tsaye a gaban rigar sa, sai kuma ya aika a kirata aka ce masa bata nan, dalilin da ya daga hankalin sa kenan, sai kuma zuwan Adam da ya sake dagula masa lissafi baki daya.


Drawer ya bud'e a jikin table dinsa ya ajiye key din, sannan ya rufe. Ya tashi ya fita zuwa wajen Kamal domin akwai abubuwan da yake da bukatar sani. Tana kokarin fitowa daga office din yana shigowa, saura kiris tayi karo dashi tayi saurin yin baya. Tsayawa yayi ya toge a jikin kofar yana kallon ta, kanta a k'asa saboda tsabar nauyi da kunyar sa da take ji. Kamal ne ya tako zuwa wajen yace


"Ina ganin ya kamata mu fara shiryawa meeting din ganin saura lokaci kad'an."


"I'm not attending, kayi representing dina."


"Why?" Ya saka masa ido


"Fita zan yi, zanje naga Dr Ma'aruf."


"Ok ok"  Sai ya juya wajen Rayhana


"Sai next week kenan?"


Kamal yace ganin duk ta takura gashi Aryan din ya babbake kofar kuma ba zata iya bud'e baki tace masa ya matsa ba 


"Next week?" Aryan ya tambaya


"Yes zata dan je gida ne, bata jin dadi so ta nemi permission nace ta huta this week."


"Me yake damunki?" 

  Yayi directing tambayar kanta, duburburcewa tayi dan a tsorace take gani take zai gano abinda tayi ko kuma ma ya sani. 


"Let her go please Aryan, Raihana jeki Allah ya kara sauki."


Kallon sa yayi kamar zai magana, sai kuma ya fasa ya dan matsa mata daga hanyar tayi saurin wucewa. Tabe baki yayi ya juya ya bar Kamal din a tsaye, be san yaushe ya fara damuwa da abubuwan da basu shafe shi ba har ya bada kulawar sa kamar haka. Key din kawai ya dauka da jacket dinsa, ya jawo office din ya koma ya bawa Kamal mukullin sannan ya tafi. 


***Tunda ta fito daga office din Aryan din zuwa fitowar ta daga na Kamal ta lura da wani irin kallo da yan office din suke mata, ita kanta tasan tayi abun a kalleta sai kuma yanzu take tuno a yadda ta shigo wajen dole ta zama abun kallo kuma topic of discussion. Tazo daidai wajen da Zainab suke zaune tare da wata Cynthia sai kuwa Zainab din ta taso ta tare ta


"Menene matsalar ki ne wai ke?"


"Attention seeker ce kawai." 

   

Cynthia tace itama tana tasowa. Kurar dake kan Raihana tafi karfin ta bata lokaci wajen kula su dan ta lura so suke su kular da ita. Kin maganar da tayi musu ne ya sake tunzura su, suka shiga fada mata maganganu tayi biris kamar bata ji ba, ta wuce office dinsu ta dauki abinda zata dauka ta fito lokacin Hamma Haydar ya karaso yana chan gate dan haka ne ma ta sake banza dasu kar su sake bata mata lokaci har Aryan ya san abinda ya faru.

   Jiki a sanyaye ta isa wajen motar ta bud'e ta shiga tana sauke ajiyar zuciya. Cike da kulawa yake duban ta kafin ya sa hannu a saman kanta ya taba. 


"Tun yaushe ne baki da lafiya? Gashi har jikin ki yayi zafi."


"Dazu ne Hamma, muje inaso na kwanta."


"Asibiti zamu wuce ai, ba gida ba."


"Asibitin da Abby yake?"


"Eh nan zamu."


"Ok." Tace. Matsowa yayi ya kwantar mata da kujerar yadda zata ji dadi ya gyara mata kanta sosai sannan ya tada motar suka bar wajen.


*

*RUMBUN QAYA🔥


*DAUDAR GORA*🔥


*IDON NERA*🔥


*A RUBUCE TAKE*🔥


*KI KULANI*🔥


*_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊


*Nasan zakuce ya da murmushi haka?*


*Wanda bai shigo ba bazai gane ba*


*Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️


*KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU*


*KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?*


*KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?*


Littafi daya---400

Biyu---600

Uku----800

Hudu-----1k

Biyar din duka----1200


*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥


0022419171

Maryam sani

Access bank


*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*


09166221261


🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪

*Ina yan uwa 'yan nijer?*

*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*


+227 90 16 59 91


Littafi daya---450CFA

biyu---650CFA

uku----850CFA

hudu----1050 CFA

Biyar----1250CFA


*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*


*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*


*Thanks for choosing us*🔥

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post