Rumbun Qaya hausa Novel Page 16
Health College

Rumbun Qaya hausa Novel Page 16

Rumbun Qaya hausa Novel Page 16

RQ

    16

Hafsat Rano

***Duba lokaci Kamal yayi ya tuna karfe biyu suke da meeting din, akwai sauran kusa awa daya. Yana bukatar yayi abinda zai yi kafin lokacin. Computer ya jawo ya shiga ya tura musu da email na shifting time din meeting din zuwa karfe uku. A gurguje yayi komai be jira reply din su ba, ya kashe computer din ya dauki key din ya fita da sauri. Fitar su dukka a lokaci kusan daya ya sake saka su Zainab a kundin tunanin abinda yake faruwa. Da farko Aryan sai kuma Raihana yanzu kuma Kamal kuma dukkan su basa cikin yanayi me dadi. Maganganun suke cigaba da tattaunawa har zuwa lunch time sannan kowa ya tashi don neman abinda zai sakawa cikin sa, masu sallah kuma suka tafi yin sallah kafin cin abincin.


   Da hannu daya yake driver dayan kuma yana kokarin kiran Aryan din ya tabbatar da in da abinda yake da wajen da yake a lokacin, be d'aga ba dan haka ne ma ya cigaba da kiran nasa har ya iso kofar gidan, amma ta baya. Ajiye motar yayi a wajen sannan ya zagayo gate din yana katse kiran ya tura wayar a aljihu kawai ya kwankwasa. Baba maigadi ne ya taso yazo ya bud'e yana ganin shine ya fadada fara'ar fuskar sa suka gaisa ya shiga ciki sannan yace



"Zakuyi baki anjima kad'an Baba, ku dan je kauye na kwana biyu zan kira ka a waya sai ku dawo, ga kudin mota da na dan abinda za'a bukata."


 Ya ciro kudi ya mika masa


"Lafiya dai ko?"


"Lafiyar za'a ce Baba, amma dai kuyi tafiyar ku dan idan suka zo suka nemi abinda suke nema basu samu ba, zasu iya huce haushin akanku."


"Toh Allah ya rufa asiri, ku kula dan Allah Kamalu, ku kula sosai da kanku dan Allah."


"In sha Allahu Baba,ku taya mu da addu'a."


"In sha Allahu."


"Yawwa Baba, ku hanzarta dan Allah, karku bata lokaci dan nasan daf suke da zuwa."


Da sauri ya juya ciki ya samu Hajara na wanki,ajiyewa tayi suka dau dan abinda zasu dauka suka fito.


    Direct chan cikin bedroom din Aryan din ya shiga ta hanyar amfani da key din, wajen Safe din ya nufa da dan saurin sa, ya bud'e ta hanyar saka security code din ya tattaro dukka abin da yake ciki ya fito dasu hade da wani dan karamin flash ya tura shi a cikin wandon sa sannan ya ajiye wani empty disk hade da wasu tarin takardu yayi sealing dinsu a wata babbar envelope ya maida ya rufe ba tare da ya rufe ruf ba. Jakar da ya shigo da ita ya zuge ya saka komai sannan ya goya ta ya nufi kitchen dan samun ruwa duk yanayin komai a gurguje ne yana amfani da lokaci.  Ledar dake saman island din kitchen din ce ta dauki hankalin sa, ya bud'e ganin Apple a ciki sai ya girgiza kansa dan da alama ya kwana biyu a wajen Aryan din ma ya manta dashi, jawo jedar yayi, ya kwashe su daga ciki ya zuba a wata container sannan ya saka a fridge ya rufe ya dauki pack din da niyyar sakawa a dustbin sai yaji kamar abu a jiki. Hannu yasa ya taba sai yaji dan karamin abu, dubawa yayi sai ga wata yar karamar camera a jiki an saka ta daga chan kasan yadda ba zaka taba gane akwai ta ba, ba ma kowa be zai san camera bace ba ,shima dan aikin sa ne, aikin da ko Aryan be san shi da shi ba, aikin da ya dau tsawon lokaci yana yin sa duk dan cimma wata manufa. Cire ta yayi daga jiki yana girgiza kansa, tabbas Hajiya Zeenat ce ta saka, kuma tabbas Raihana ce tazo da ita dan babu wani mahaluki da ya shigo gidan bayan Aryan, sannan apple baya cikin fruits din da Aryan din yake so balle har ya siya. Tambarin da yake jikin dan kwalin ya zubawa ido, sai ya ciro wayar sa ya dauka a hoto sannan ya shiga dudduba ko ina a gidan ko akwai wasu cameras din sai dai be gani ba. Ko ruwan da yayi niyyar sha be sha ba,dan ya sake bata lokaci sosai dan delay din da ya samu. 

   Karar mota yaji da karfi sai kuma yaji alamun ana kokarin shigowa gate din gidan, kofar baya da take a cikin kitchen din bayan wata babbar drawer wadda zaka rantse kawai drawer ce a wajen amma kana bud'e ta zaka ga kofa a wajen ya nufa, ya bud'e ya shiga sannan ya rufe daidai lokacin da suka shigo falon. Suna da kowanne key na gidan dama, na dakin sa ne kawai basu dashi samun sa a yanzu shi ya basu kwarin guiwar shigowa a lokacin. Sun riga sun san lokacin da Aryan yake zuwa gidan shiyasa suka zo a wannan lokacin. Su hudu ne karti majiya karfi, a zahiri Kamal zai iya kiranyan sanda a yanzu ganin sun shigo gidan amma kuma sanin wacece Hajiya Zeenat ya hanashi dan ita din me karfin fada aji ce, waya kawai zatayi a fitar dasu, shiyasa gwara su bi komai a hankali suyi mata kamun da ko ubanta ne shugaban kasa ba zai iya fitar da ita ba. Agogon hannun sa ya taba wanda ya kasance smart watch sannan ya karasa ficewa daga gidan.

 

   Suna zaune a harabar gidan akan fararen kujerun nan,hannun ta rike da glass cup fuskar cike da annuri dan tana da yakinin zuwa yanzu Aryan ya gama, kuma ta samu abinda yake tunkaho yake mata barazana dashi. Faifan CD da yake dauke da komai, wanda tayi tunanin ta shafe shi daga doron kasa, ta hanyar batar da shi da kuma batar da mamallakin sa. Bata san yadda akayi Aryan din yake da shi ba, dan iya binciken ta bata samu amsar ba.

  Dagowa yayi daga dukufa da yayi akan system din ya juyo mata gabanta yana pointing hannun sa akai


"Waye wannan?"


Kallon screen din tayi kad'an kafin tace


"Kamal ne." 


Wani abu ne ya fado mata, ta sake juyo da system din da sauri ta zubawa video din ido


"Me yake yi a gidan?"


"Ya cire camera din Hajiya."


"Oh shit! Me yasa yaron nan yake shiga gona ta ne???" 


Tace tana dire cup din hannun ta 


"Kyale shi kikayi Hajiya."


"Ba tashi nake ba yanzu, ka rabu dashi zan dawo kansa ne, ta uban gidan sa nake yi kuma ina jiran kyakkyawan labari."


"Amma shirun yayi yawa, da wani abu ya faru da tuni kin karbi wayoyi ba ma waya ba."


"Eh toh! Hakan ne kuma. Bari..."


Ta dauki wayar ta, ta shiga call log tayi dialing number.


"Ya naji shiru?" Tace yana dagawa


"An samu matsala!"


"Whaaat! Matsala? Ban santa ba, ban taba samun ta ba tunda nazo duniya, ban gane me kake nufi ba."


"Kiyi hakuri Hajiya, Aryan be sha tea din nan ba, Oga Adam ne yazo ya dagula komai."


"Adam! Adam? Ban gane ba."


"Zuwa yayi a daidai lokacin da ya kamata ace ya nemi tea din, yazo ya hargitsa komai suka dan samo sabani da oga."


"Ina ita Raihanan?"


"Ta tafi, dan sanda naga oga Adam ya shigo har an fara samun sabani sai na fice, yanzu na dawo ba oga Kamal, ba oga Aryan itama kuma bata nan."


Kit ta kashe wayar tana mikewa tsaye, ya za'a yi mata haka? Yaushe ta fara shirya abu yana watsewa haka?


"Me ya faru?"


"Babu nasara."


Murmushi yayi ya maida kansa ya cigaba da abinda yake yi. Tana tsaye bacin rai ya cikata wata wayar ta sake shigo mata, a sukwane ta dauka dan idan aka samu wata matsalar yanzu kuma shikenan.


"Ya akayi Gaza?"


"Mun dauko kayan nan Hajjaju."


Wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke ta zauna sharaf tana sharce gumi.


    ***Abby na zaune ya jingina bayan sa da pillow, Lamido na ta wajen kafarsa ya dora kafar Abbyn akan tasa kafar yana matsa masa a hankali. Rayhana na kwance a carpet bayan tasha magani ta lulluba har kusan kanta dan a tsorace take sosai da abinda ya faru wanda yayi effecting dinta har ya saukar mata da zazzabi me zafin gaske. 


"Uwata?" Abby ya kira ta ganin ta juyar da bayan ta, tana rufe idon ta. Juyowa tayi ta dan yaye rufar ta sama tana marairace fuskar ta 


"Kasan nan akwai sanyi gashi kina zazzabi, tashi Haydar ku tafi, sai ku fito da wuri idan Allah ya kaimu."


"Abby anan zan kwana." Tace kamar zatayi kuka


"A ah uwata, kije dai gida ki huta kiyi wanka da ruwan zafi kinji."


"Bata fa ci abinci ba ma kamar Abby." Lamido yace yana kallon ta


"Hamma fa naci."


"Kad'an ba, kuje Hydar ka samar mata abinda take so ko a hanya ne, sannan ka tabbata taci idan ba haka ba kuka zo gobe sai dai su yi mata alluran gaskiya."


"Gaskiya dai kuwa." Abby yace shima. Tashi tayi da k'yar kamar zatayi kuka, ta saka Hijab dinta suka fito tana jin kamar iska zata dauke ta saboda rashin kuzari.

   Suna fita Lamido ya mike ya dauko jakar da ya shigo da ita da safe ya zaro abubuwan da suke ciki ya mikawa Abby


"Sun cika komai Abby."


"Masha Allah." Ya karba ya duba, sannan yace


"Ya kukayi da Salihu?"


"Be sanar da ita ba tukunna, dama jiran abinda zaka ce muke, ya dai barta a matsayin bamu ma samu ganin ka ba, yadda ba zata bibiyi kowa ba."


"Sai ya sanar da ita yanzu ai, ina son haduwa da wanda ya taimaka fitowa ta duk da sun ki fada min saboda ya hana, amma ko waye yana cikin harkallar wanchan lokacin, zan dawo dawowa ta musamman, ba kuma zan yi bacci ba har sai na tabbatar da na tura Zeenatu gidan kaso!"


"Abby kana bukata hutu sosai yanzu."


" Kai yarone Lamido, ba zaka gane rayuwakan mutanen da suka shiga masifa ta dalilin ta ba, ba zaka gane komai ba, abinda na sanar maka kawai ka sani baka san komai ba."


"Ni zan daukar maka fansa Abby, ka kwantar da hankalin ka da kaina zan daure Hajiya Zeenat har sai an rasa igiya a garin nan!"


"Nasan zaka iya, dan ban haifi rago ba, sai dai nine kadai nasan lagon ta, ni kadai take tsoro a duk duniyar nan, dan haka a yanzu ne zata fara girbi!"

     

"Kira Salihun!"


Wayar ya ciro ya shiga kiran sa, ya saka wayar a handfree


"Hello!"


"Hello sir, barka da wannan lokacin."


"Barka dai Salihu, lokaci yayi na cikar aikin mu tare, sai ka sanar da ita."


"Ok an gama sir."


Yana kashe wayar ya yi dialing number Hajiya Zeenat, a lokacin tana zaune kusa da Daddy tana murza masa hannun sa a hankali yana shan mixed fruit. Kamar ba zata dauki wayar ba saboda bata san abinda zai katse ta, sai kuma ta dauka din dan tana da abubuwan da bata son missing. Ganin Salihu ne yake kira ya sakata saurin janye hannun ta daga na cikin Daddyn ya kalle ta.


"Lafiya?" Yace yana kokarin kallon wayar.


"Salihu ne." Tace tana daga wayar sannan ta sakata a handfree


"Hajiya akwai babbar matsala."


"Hanzarta fada min."


Kasa yayi da muryar sa sosai, kamar me rada sannan yace


"Yau Barrister MATAWALLE ya shaki iskar yanci!"


Cup din dake hannun Daddy ne yayi wata irin faduwa ya tarwatse a wajen, kafin ya mike tsaye cikin tashin hankali suka hada baki shi da Hajiya Zeenat din wajen cewa 


"WHATTTT!!!!"






*RUMBUN QAYA


*DAUDAR GORA*🔥


*IDON NERA*🔥777


*A RUBUCE TAKE*🔥


*KI KULANI*🔥


*_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊


*Nasan zakuce ya da murmushi haka?*


*Wanda bai shigo ba bazai gane ba*


*Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️


*KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU*


*KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?*


*KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?*


Littafi daya---400

Biyu---600

Uku----800

Hudu-----1k

Biyar din duka----1200


*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥


0022419171

Maryam sani

Access bank


*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*


09166221261


🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪

*Ina yan uwa 'yan nijer?*

*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*


+227 90 16 59 91


Littafi daya---450CFA

biyu---650CFA

uku----850CFA

hudu----1050 CFA

Biyar----1250CFA


*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*


*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*


*Thanks for choosing us*🔥

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post