Rumbun Qaya hausa Novel Page 17

Rumbun Qaya hausa Novel Page 17

Rumbun Qaya hausa Novel Page 17

RQ

      Page 17

Hafsat Rano

••••••


"Me kake fada min Salihu? Yaushe ya fito? Yaushe akayi haka duk ban sani ba."


Karbe wayar Daddy yayi


"Kana jina Salihu? Yi min bayani dalla-dallah ina sauraron ka."


"Har yanzu ban samu dalilin fitar sa ba, amma tabbas ya fito, na kuma yi kokarin ganin na binciki lamarin sai dai ban samu dama ba, idan kuma na cigaba da kokarin bincikawa Zan samu matsala da Oga, dan da alama umarni ne daga chan sama."


"Daga sama? Gwamna ko shugaban kasa?Wa ya damu dashi har haka da zai fitar dashi, waye wannan ya shammace mu? Waye shi?  Hajiya Zeenat tace


"Ban sani ba Hajiya, bari na koma bakin aiki kar oga ya lura bana nan."


  Jefar da wayar tayi bayan daddy ya miko mata. Ta cigaba da zagaye tana son figuring ainhin abinda yake faruwa.


  Babu wanda ya iya zama a tsakanin su saboda rud'ewa, dukkansu sun yi matukar shiga tashin hankali da gigita, shi Daddy har ya kusan d'ara Hajiya Zeenat a shiga yanayin tsoro da firgici ya dinga kai wa da komowa yana kokarin kiraye kiraye waye sai dai duk in da ya kira sai ya samu same labarin da Salihu ya bashi. Shugaban prison din baki daya ya yanke shawarar kira dan shima yaron sa ne kuma be kamata ace an yi irin wannan abun ya kasa sanar masa ba sai dai wayar sa ma a kashe. 

   Daidai lokacin waani abu ya taso ya daki gefen kirjin Daddyn ya rike shi yana yin kasa rike da kirjin . Hajiya Zeenat da take ta waya ta lura da halin da Daddyn ya shiga amma tayi kamar bata gani ba dan ba tashi take ba dan haka ne ma ta cigaba da kokarin ganin ta samu information akan case din ko ya ya ne, domin tabbas an mata shigar sauri kuma ko waye yana da kusanci sosai da ita da har ya san duk moves din ta. 

   Wayar da ta kira ta karshe ce ta tabbatar mata da komai zai soma budewa ne a wannan gabar, duk wani kulli da suka haka rami suke binne zai zama an tono shi ne. Duk kokarin ta na ganin ta batar da duk wani shaida a doran ya tashi a banza.


"An chanja shugaban wajen ne."


 Shine abinda wayar da tayi a karshe ya tabbatar mata.

   Iska ta shak'a me zafin gaske ta fezar, ta rik'e kanta tana kokarin saka bayanin a mazaunin tunani. A dan takin da be wuce sati biyu ba, ta shiga prison din kuma ta samu tabbacin komai normal. Babu yadda za'a yi har a chanja shugaban wajen a wannan dan lokacin kuma ya aiwatar da wannan babban aikin da zai zama babban dalilin da zai tarwatse koman da ta gina. Dole wani yaci amanar ta


"Ina ba zai yiwu ba!"  Ta furta da karfi 


"Zeenatu. Zeenatu." 


Daddy ya shiga kwala mata kira jin abun na neman fin karfin sa, hannun sa na dafe da kirjin sa, matsowa tayi ta tsaya daga kansa a tsaye tana masa wani mugun kallo


"Me kika bani nasha?" Yace da k'yar muryar sa na sarkewa ganin yadda take kallon sa


"Abinda ya dace da kai." 


Tari ya soma yi da karfi, ta dauki wayarta tayi kira, minti kad'an wasu kartin maza suka shigo dauke da wata katuwar jaka, lokacin ganin Daddyn ya soma disashewa, takardun dukkan kadarorin sa suka fito dasu, ta karba ta ajiye a gaban Daddyn, daya daga ciki ya kama hannun sa, ya danna akan paper bayan ya dora shi akan stamp, sannan suka tilasta masa yayi signing wasu daga cikin takardun amma wasu ya kasa, zuwa lokacin abinda yake ji ya riga ya rinjaye shi har idanun sa sun rufe ruf. Kafarta tasa ta bugi kujerar cikin tsananin bacin rai. Ta riga ta shirya wannan plan din sai kuma labarin fitowar MATAWALLE ya rusa mata kusan rabin plan din, gashi bata samu ya gama saka hannu a dukka takardun ba, wanda suka kasance mallakin Aryan da Nabeela 


"Ku haura min dashi dakin sama."


Tace tana kallon takardun ranta a bace. Ciccibar sa sukayi suka haura dashi zuwa dakin sa, suka kwantar dashi sannan suke rufe shi da blanket suka kashe wutar dakin suka fito. Sakowa sukayi ta basu umarni sannan suka fita. Sune sababbin masu kula da gidan daga yanzu, bata kuma yarda su bar kowa ya shigo gidan ba. 

  Dakin ta, ta shiga rike da takardun ta daga wajen da ta ajiye na Aryan din da ko bude su batayi ba ta hade su, su kadai zata rike yanzu a matsayin makami, sannan samun da tayi wa disk din nan shine a yanzu garkuwar ta, dan ta tabbata Matawalle bashi da wani copy dan haka ne ma tasan bashi da wani abu da zai rike hujja akan ta. Shiryawa tayi cikin rantsatsiyar shiga, ta bulbula designer perfumes masu matukar tsada da kamshi sannan ta yafa dan mayafi a gefen kafadarta ta fito, a daren nan zata yi maganin Matawalle dan ko da ace ya fito va zata taba bashi damar da zai iya tabuka komai ba. Na farko yanzu girma ya kamashi, haka bashi da wani matsayi a hukumance dan a gabanta aka kwace license dinsa tun a wanchan lokacin. Ba ma wannan ba, yar sa mafi soyuwa a gareshi tana a tafin hannun ta ne, dan haka kome ma yake shiryawa da wanda ya saka aka fitar dashi daidai take dasu.

   Sai da ta shiga mota ta zauna sosai sannan ta kira shi a waya, dama yasan da plan din haduwar su a daren yau din amma kuma tana so kafin ta karaso ya nemo mata in da Matawalle yake da abinda yake yi a lokacin. Tamkar babu wani abu da ya faru, haka ta nuna dan a tunanin ta, tafi karfin dukkansu musamman da tasan ta kama abubuwa masu muhimmaci a garesu. 




  ***Yau baki daya baya jin dadin jikin sa, tun da ya gama da wajen Dr Ma'aruf ya wuce gidan Ya Nabeela daga nan yayi kwanciyar sa dan ko ta kan wayar sa be bi ba shiyasa ma be ga kiran Kamal ba. Tun da akayi bikin Ya Nabeela bayan an dan kwana biyu ya tattaro ya dawo gidan dan kusan rabin rayuwar sa ta baya a tsakanin gidan ta da gidan su yayi ta, tun suna tsohon gida har suka dawo wannan da suke ciki mijinta yayi masa daki a gidan shikenan ya samu lasisin zama musamman duk sanda rashin lafiyar sa zata tashi dole tana kusa dashi tana kula dashi. Alwala ya shiga yayi a toilet din dakin da ya zama yanzu na baki  idan sun zo sai kuma shi idan yaji bukatar zuwan. Lokacin la'asar ta dan gota yazo yayi sallar sannan ya shiga ciki. Suna zaune ita da Mijinta Dr Farouk lecturer ne a Federal University dake Dutse suna hira Aryan din ya shigo bayan yayi musu sallama daga kofar sun amsa.


"Ka tashi kenan."


  Ya Nabeela tace tana kallon sa, 


"Eh bansan ya akayi nayi bacci haka ba."


"Maganin ne." 


"Barka da warhaka Yaya Farouk." 


Hannu ya mika masa suka gaisa


"Barka dai Aryan, ashe kana ciki."


"Eh na shigo dazu."


"Toh ya jikin?"


"Alhamdulillah, ciwon kan ne dai yake dan takura min amma Alhamdulillah."


"Toh Allah ya kara sauki, ka kula sosai ka kuma dinga ragewa kanka wasu abubuwan ba komai ake cewa dole dole sai an yi ba."


"In sha Allah."


"Gwara dai ka gaya masa zai fi ji, kuma kayi masa maganar aure dan zaman a haka ba zai yiwu ba."


Ta wuce kitchen bayan ta gama maganar. Murmushi Dr Farouk yayi dan yasan yadda Aryan din yake idan aka dauko maganar aure 


"Rabu da yayar nan taka bata son zaman lafiya."


Murmushi yayi kad'an ta fito rike da flask ta ajiye a saman dinning sannan tace ya taso yaci abinci. Tashi yayi yaje ya zauna ya zuba abincin kad'an ya dan chachakala ya tashi, nan ma sai da tayi maganar baya son cin abinci shi dai be ce mata komai ba, yayi musu sallama ya tafi.

  Har ya tafi ya tuna be dau wayar sa ba, ya dawo ya dauka anan yaga missed calls din Kamal rututu kamar ruwa, mamakin dalilin kiran ya tsaya yi sai kuma ya bi kiran yana rage gudun motar.


"Ina ka shiga man?"


"Ina gidan Ya Nabeela wallahi, bacci nayi bayan nasha magani."


"Ok yanzu kana ina?"


"Gani a hanya."


"Ok kazo gida please, akwai magana."


"Ok,i'm on my way." 


 Ajiye wayar sukayi ya juya akalar motar zuwa gidan Kamal din. A kofar gida ya hange shi tsaye da alama shi yake tsaiwar jira. Parking yayi suka shiga ciki.


"Madam fa?" Yace jin gidan shiru


"Taje gidan su, da magriba sai mu je ka rakani na dauko su."


"Ok." Yace ya zauna, ruwa da lemo Kamal yaje ya kawo masa sannan ya dauko jakar nan ya zauna yana dora ta a saman centre table


"Wannan fa?"


"Documents din nan ne, na cikin safe."


"Anan?"


"Eh, Hajiya Zeenat ta kai musu ziyara dazu."


  Ajiye ruwan hannun sa yayi da yayi niyyar sha, ya jawo jakar da sauri ya hau budewa. Sai da ya fito da komai ya tabbatar komai daidai sannan ya sauke nannauyar ajiyar zuciya


"Me ya faru? Ya akayi suka je gidan?"


"A coincidence, kasan mun yi zanje har ka bani key din, ina shiga sai gasu."


"Lallai tana da gut, da ranar Allah?"



"Kana mamaki? Kafi kowa sanin wacece ita, da abinda zata iya aikatawa"


"Then sai akayi yaya?"


"I changed everything, na bar musu fake papers and the disk too."


Zura masa ido Aryan yayi cikin rashin gamsuwa da bayanin sai dai ya yabawa kokarin Kamal din amma kuma be ji cewa ya gamsu coincidence bane, taya yayi planning komai within short time haka?


"Are you sure?" Ya tambaya yana kara jawo papers din ya duba


"Yes, it was a narrow escape."


"Amma...it looks like a plan or something!."


"How?"


"Da farko dalilin zuwan su, ba zata taba samun gut din zuwa ba idan bata rike wani abu ba, na biyu yadda kayi saurin chanja komai a dan lokacin."


Kallon sa Kamal din yayi, yana yabawa kaifin basirar Aryan din da saurin gano abu, amma dai dole a hakan zai barshi, dan ba zai iya fada masa abinda ya faru ba saboda Raihana, ba zai tona mata asiri ba dan yasan waye Aryan akan rashin yardar sa. Murmushi yayi ya dafa kafadar sa


"Chill bro, koma menene mu gode Allah tunda bata samu nasara ba, she's after cd din nan while empty ne bata san komai yana kan flash ba, secondly Barrister Matawalle ya fito, wannan ba start bane me kyau ba?"


"Oh yes!"


"Yawwa, don't think hard akai, koma menene dai in sha Allah zamuyi nasara."


"In sha Allah." 


Yace a sanyaye ya dan jingana da kujerar yana hasaso daga wannan sai wannan baki daya rayuwar. Daga sanda Hajiya Zeenat ta gane fake CD ne daga lokacin komai zai fara.


"Kana bukatar driver Aryan."


"Driver?"


"Eh, saboda tsaro ba dan tsoro ba."


"Bani da say ai, duk abinda ka tsara shi za'ayi dan yanzu kai ne ogan."


Dariya Kamal ya kwashe da, shima Aryan din sai yayi murmushi dan ya sake tabbatar da babu wani a yanzu sama da Kamal din a gareshi. Tashi Kamal din yayi ya shiga ciki, ya sauya shigar sa zuwa ta fita. Tunanin Raihana ne ya fadowa Aryan wanda a dazu baccin ranar da yayi hadda mafarkin sanda tana kukan nan yayi, sosai kukan nata ya tsaya masa a rai be kuma san dalili ba, ya dai ji kawai yana tausayin ta ne sosai. Da kallo yabi Kamal bayan ya fito yana tunanin ya tambaye shi ne ko ya share? Yanke shawarar tambayar tasa kawai yayi ya dan mike zaune daga kishingidar da yayi yace


"Yarinyar nan dazu ta fada maka matsalar ta?"


"Wa fa?" Kamal yace kamar be gane wa yake nufi ba


"Corper."


"Oh Rayhan, Allah sarki bata jin dadi ne."


"Ok."


"I'm impressed." Kamal yace yana murmushi


"With what?"


"Wannan ne karo na biyu da naga ka damu sosai da abinda ya shafi wani, na farkon ma akanta ne, ga na biyu, did you have any feel..."


 Ai da sauri Aryan ya kai masa bugu abinda yasa maganar ta katse 


"Don't even start."


Yace yana yin kicin kicin da fuska


"Baka barni na dire magana ta ba ai."


"Bana son ji, kuma ba zan sake tambayar ka ba, kawai dama naga yarinya ce, plus tace min ta rasa mamanta tun tana karama, and I know how it feels ka rasa iyayenka at younger age, shine kawai nothing more, shima ba zan sake tambaya ba."


"Ikon Alalh." Kamal yace yana dariya


"Why all this explanation? Daga magana? Ni na dade ban ji kayi irin wannan long sentence din ba wallahi, menene a ciki toh? Kai ma fa mutum ne me jini a jika, handsome guy son kowa kin wadda ta rasa."


"Sai kayi, zaka je daukar Madam din ne ko na wuce gida?"


"Zanje mana, an gaya maka zan iya kwana ni kadai a gidan nan? Nah ba zan iya ba, sai na rungume matata tsam tsam sannan."


"Dan iska" Aryan yace ya fice ya barshi yana kyal kyala masa dariya 






*RUMBUN QAYA*🔥


*DAUDAR GORA*🔥


*IDON NERA*🔥


*A RUBUCE TAKE*🔥


*KI KULANI*🔥


*_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊


*Nasan zakuce ya da murmushi haka?*


*Wanda bai shigo ba bazai gane ba*


*Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️


*KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU*


*KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?*


*KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?*


Littafi daya---400

Biyu---600

Uku----800

Hudu-----1k

Biyar din duka----1200


*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥


0022419171

Maryam sani

Access bank


*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*


09166221261


🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪

*Ina yan uwa 'yan nijer?*

*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*


+227 90 16 59 91


Littafi daya---450CFA

biyu---650CFA

uku----850CFA

hudu----1050 CFA

Biyar----1250CFA


*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*


*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*


*Thanks for choosing us*🔥

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post