Rumbun Qaya hausa Novel Page 18


Health College

Rumbun Qaya hausa Novel Page 18

Rumbun Qaya hausa Novel Page 18

RQ

      Page 18


Hafsat Rano


••••••Kokarin motsa ko da karamin dan yatsan sa Daddy yake amma ya gaza, gashi yana jin duk wani motsi amma ya kasa juya jikin sa. Kenan tsawon wannan lokacin Hajiya Zeenat ba san shi take ba? Ko kuma a yanzu ne ta sauya? Baki daya ya kasa tunanin abinda yake faruwa a dan gajeran lokacin. 


_"Tunda har ka iya biyewa mace ka bata da duk wani makusancin ka, toh tabbas dama irin wannan ranar ta nadama ta na nan zuwa."_ 


  Wata murya daga chan bayan kansa tayi kokarin tunasar dashi abinda ya faru a lokacin baya. Hawaye ne ya shiga sakkowa yana biyowa ta gefen kuncin sa, bayan ya gama tabbatar da shikenan tasa ta kare, watakila haka zai karasa rayuwar sa har mutuwa tazo ta riskeshi. Kaico! Rayuwar cin amana bata dauke da komai sa tsantsar tashin hankali. Yinkurin ya cigaba da yi har ma da na kokarin yin magana Amma sam muryar sa taki fitowa kwata-kwata, so yake ma ko ihu ne yayi ko wani zai jiyo shi, ko yayi sa'a Aryan ya shigo yazo ya taimake shi. Wayar sa ya hanga ta gefen idon sa tana haske alamar shigowar kira amma ba zai iya kaiwa gareta ba, ballantana ya iya dauka.


  A gajiya Aryan ya shigo gidan dan sun dade a gidan Kaamal bayan sun dauko matar sa, sai suka zauna zaman tattaunawa abubuwan da suke tunkaro su, basu ankara da dare yaja haka ba sosai sai da Khadija tayi wa Kamal flashing sannan suke duba lokaci yayi saurin yi masa sallama amma maimakon ya barshi ya taho shi kadai sai yace Khadijan ta dauko Hijab dinta aka shigo da motar Aryan din ciki sannan suka kaishi har gida a motar Kamal din. Sam be yarda da tafiyar a sa lokacin nan ba dan yana tsoron abinda Hajiya Zeenat zata aikata tunda har ta kai ga batun poison duk da ba wai yau ne karo na farko da tayi attempting hakan ba, Allah ne dai be bata sa'a ba. Amma dai duk tsiyar ta ba zata taba yi masa komai a cikin gidan ba sai dai a waje yadda ba zata taba zama abar zargi ba. 

   Stairs din ya kama ya soma hawa cikin yanayin kasala rike da suit din sa, duhu gidan yayi masa sosai duk da dama duk an kashe kwayayen dake bada haske a ilahirin falon zuwa saman an maida shi me dan gaske kad'an amma duk da haka sai yaga kamar ko ina baki ne kirin, ga wani irin shiru da ya dade be ji gidan ya dauka ba. Cigaba da hawa yayi zuciyar sa ta kasa nutsuwa da yanayin da yake jin sa, tabbas akwai abinda ya faru ko yake shirin faruwa, abinda ya dauka kenan dan a duk sanda yaji irin wannan toh yasan tabbas akwai wani abu da Hajiya Zeenat take kullawa. Dafe kirjin sa yayi da hannu daya jin yayi masa nauyi, ya shiga karanta la'ila ha illah anta subhanaka inni kuntu minazzalumin har ya kai kofar dakin sa, ya saka key din sa da yake tafiya da shi ko ina ya bud'e ya shiga sannan ya saka key din ya sake rufewa ya kunna hasken dakin. Ko ina a gyara yake tsaf tsaf kamar dakin mace, da kansa yake gyara komai dan yana da komai na gyara a ciki be yarda kowa ya shigar masa ba duk kuwa da ba wani abun amfani yake ajiyewa a dakin ba. Wajen shoe rack dinsa ya nufa ya dan duka ya hau zare takalmin kafarsa hade da socks din ya ajiye takalmin a ma'adanar sa sannan ya wuce wajen dan madaidacin laundry basket ya jefa socks din sannan ya fada saman gado yana sauke tagwayen ajiyar zuciya.




****Duk yadda suka bincika sun kasa samun bayanin komai akan fitowar MATAWALLE, da kuma whereabout dinsa, kanta ya soma daukar zafi amma duk da haka ba zata ka raya ba, a wannan karon ya shirya mata sosai amma abinda be sani ba shine itama a shirye take. Da wani mugun bacci ta shigo gidan dan haka ne ma bedroom ta wuce kai tsaye ta fada sai bacci. Su kuwa dama sallar asubah kawai sukayi, suka hau shiryawa kafin takwas sun isa airport takwas da wasu yan mintoci suka d'aga daga garin Kano da niyyar dawowa a cikin babban shirin da zai rusa Hajiya Zeenat har ma da Alhaji Mukaddas a cewaar Aby dan har shi babu wanda zai ragawa, duk wani ma da ya zama tsatso ko dan uwan Daddyn babu sassauci ko kyautawawa a tsakanin su.

  Bacci bilhaki Hajiya Zeenat take kamar wadda tasha wani abu dan sai da rana ta daga sosai sannan ta tashi tana mika. Wanka ta farayi dan a rayuwar ta bata wasa da kula da kanta da jikinta wanda tun a zamanin baya ya kasance jari da tsanin da ta kai har wannan matakin. Ta kan yi wasa da sallah har ma tayi mirsisi wani lokacin taki yi amma bata taba wasa da gyara kanta da fatarta. A shirye ta fito da nufin zuwa dakin Daddy sai ta tarar da Adam ya kwance yana bacci akan kujerar falon,matsawa tayi ta taba shi ya farka a rikice idanun sa sun yi wani irin ja sosai.


"Adam?" Tace tana dan ja baya saboda bud'e bakin sa da yayi wani irin wari ya bige ta 


"Giya Adam?" Tace tana waro ido, dan luu yayi da ya yi kokarin mikewa jiri ya kwashe shi ya koma jagaf yayi baya.


"Wanne irin iskanci ne wannan? Yaushe ka fara shan giya ban sani? Yaushe?"


"Maaa... Bafa giya bace."


"Uban kace, tunda an gaya maka bansan warin ta ba." Tace da karfi tana tura shi baya 


"Please stop shouting! ki daina bana so kina min ihu da sanyin safiyar nan."


"Adam!!!" 


"Sai kuma kiyi." 


Sai ya kama hannun kujerar ya mike yana cigaba da tangadi, yayi hanyar dakin Aryan kamar zai murd'a sai kuma ya fasa ya nufi nasa ya shige gami da banko kofar.


"Na shiga uku, sai dai komai yazo karshe wannan masifun zasu fara kunno kai?"


Bud'e kofar dakin Aryan din da taji anyi ya sakata kallon wajen da sauri, a shirye yake tsaf cikin shigar kamala kufta da hula sai kamshin turare ke tashi me matukar dadin kamshi, be ko kalli shashen da take ba kamar dai yadda ita take masa kallo me cike da tsana, tana kokarin hada yanayin nutsuwar sa da ta Adam wanda dama tun a zamanin kuruciya ba ma yanayin su daya ba.


"ARYAN!" 


Ta kwala kiran sa ganin yana neman barin falon. Chak ya tsaya sai dai be juyo ba dan idan akwai abinda ya tsana ya biyo bayan kallon fuskar ta.


"Daddyn ku yayi tafiya a daren jiya, zai kuma dan kwana biyu, ya bar sakon duk wani abu da ya shafi office ka sanar wa dan uwanka..."


Wani irin juyowa yayi da shi kansa be san yayi ba, ya wurga mata wani banzan kallo kafin ya kad'a kansa ya soma kokarin barin wajen, sai da ya kai kofar fita sannan yace


"Karki kara kokarin tsaida ni ki bata min lokaci akan shirmen ki."


Dariya ta kwashe da, ya girgiza kansa kawai ya karasa ficewa. 


"Lallai wuyan ka yayi kauri."


Tace tana bubbuga hannun ta da yake cike da bangles na zallar gold. Fasa zuwa duba Daddyn tayi dan tana bukatar sanin in da aka kwana da maganar Matawalle sannan kuma ta magance matsalar Adam da yake shirin bata mata komai bayan da take kokarin maida duk wani business akan sunan sa. Bayan Aryan din tabi suka hadu a compound din gidan yana tsaye jikin motar Daddyn suna magana da Kamal yayi kamar be san ta fito ba, ta girgiza kai ta shige motar ta suka fice daga gidan. 

   Wayar ya tura a aljihun gaban rigar sa ya taka zuwa gate din, ya samu maigadi a zaune jigum. Zama yayi a gefen sa yayi saurin mikewa cike da girmamawa ya gaida Aryan din, hannu ya mika masa suka yi musabiha sannan yace ya dawo ya zauna.


"Waye ya kawo wadanchan mutanen?"


Ya nuna manyan securities din dake kaiwa da komowa a harabar gidan rike da bindigu kowannen su fuskar sa a tamke zaka rantse basu taba dariya ba


"Hajiya ce ta kawo su."


"Aikin me suke?"


"Kula da shige da ficen gidan, kamar dai hakan ne."


Tabe baki Aryan yayi yana cigaba da kallon su, suna ta safa da marwa tamkar mayunwatan zakuna.


"Ok thank you" Yace ya mike ya isa wajen su, suka zubo masa ido kamar zasu cinye shi.


"Ku gaya wa wadda ta ajiye ku, ko irin ku dubu zata ajiye kewaye da ita sai ta sha k'asa."


"Ok sir!" Suka hada baki wajen fada, tsaki yaja ya juya ya barsu a tsaye suka bishi da kallo.


Kamal ne ya karaso tare da wani da ya jawo motar Aryan din, a waje suka parker ya fice yana duba agogon dake daure a tsintsiyar hannun sa


"Idan kace 5min toh sai ya zama 20min, sam baka abu a exact time din." 



Aryan yace yana mikawa Kamal din hannu, dariya yayi ya juya wajen matashin da yake tsaye rike da key din motar Aryan din yace


"Aryan ga Habeeb, sabon driver ka."


Kallon wanda aka kira da driver Aryan yayi, ya ganshi tsaf dashi babu wata wahala a tattare dashi sai ma yanayin yan boko.


"Amma be yi kama da driver ba."


"Gaskiya ne, be yi kama ba saboda dai dan makaranta ne, ya samu matsala da karantun sa ne har akayi withdrawing dinsa, so kasan yanayin rayuwar dole sai an rayu, plus shi yake kula da mahaifiyar sa, ga aiki yayi wuya shine na kirashi a daren jiya ya kuma tabbatar min zai iya, nasan shi nasan gidan su kuma na yaba dashi shiyasa ma na nemo shi."


"Allah sarki."


"Karka damu, yaro ne me hankali."


"Ok



RUMBUN QAYA*🔥


*DAUDAR GORA*🔥


*IDON NERA*🔥


*A RUBUCE TAKE*🔥


*KI KULANI*🔥


*_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊


*Nasan zakuce ya da murmushi haka?*


*Wanda bai shigo ba bazai gane ba*


*Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️


*KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU*


*KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?*


*KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?*


Littafi daya---400

Biyu---600

Uku----800

Hudu-----1k

Biyar din duka----1200


*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥


0022419171

Maryam sani

Access bank


*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*


09166221261


🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪

*Ina yan uwa 'yan nijer?*

*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*


+227 90 16 59 91


Littafi daya---450CFA

biyu---650CFA

uku----850CFA

hudu----1050 CFA

Biyar----1250CFA


*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*


*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*


*Thanks for choosing us*🔥

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post