Rumbun Qaya hausa Novel Page 19

Rumbun Qaya hausa Novel Page 19

Rumbun Qaya hausa Novel Page 19

RQ

      Page 19

Hafsat Rano

https://arewabooks.com/u/hafsatrano

*****Gaba ya bud'e ya fada ba tare da yace komai ba, dan tsaye Kamal yayi kamar zai ce masa ya koma baya amma sai ya kyale dan kar ya matsa sosai yasan halin Aryan sarai zai iya saka wani abu a ransa. Motar sa ya koma ya shiga, ya fara jira Habeeb din ya fara wucewa gaba sannan ya bisu a baya. A gate din company ya tsaya dan yana da dan wajen da zai je kafin ya shigo, wayar sa ya dauka ya kira Aryan din yace masa zai dan je ya dawo sannan ya juya ya bar wajen.

  Titin babu kowa dan ko motsin tsuntsaye babu saboda tsabar shirun shi, wajen ya kasance baya biyuwa saboda tsabar tsaron da yake wajen. Tun daga farkon titin suke tsayawa suna maida duk wani da yazo giftawa ta wajen tun mutane basu gane ba har suka gane kowa ya daina bi saboda tsoro. Sai kayi tafiya me nisa a kan titin sannan zaka iso gate din wajen, wanda shima yake zagaye da matakan tsaro. A guje wani rike da wata irin mahaukaciyar  bindiga ya taso, yazo ya hau bud'e masa gate din da saurin gaske. Ciki ya shiga bayan ya dan daga masa hannu ya samu wajen yayi parking ya fito da sassarfa. Gari guda ne a cikin wajen domin kuwa waje ne me girman gaske, sannan ga matasa maza da mata wanda a kalla shekarun su ba zasu haura ishirin da biyar ba suna kaiwa da komowa a cikin wajen da ya kasance a kebence dan ba zaka taba tunanin wajen yana existing ba. Kowannen su rike yake da bindigu manyan gaske sai dai suna ta walwala a tsakanin su tamkar babu wani abu da yake faruwa

  Kai tsaye office dinsa ya wuce wanda aka rubuta daga saman office din da babban baki LIEUTENANT KAMAL HASSAN SARKI (DSS)  Sergeants ne a kofar office din sukayi saurin bud'e masa, ya shiga ya zauna akan kujerar sa sannan ya fito da takardun Aryan din dukka ya baje su akan table din ya hau dubawa a tsanake. Knocking aka fara yi kad'an kafin ya bada izinin shigowa. Captain Mausul ne 


"Welcome sir." Yace yana sara masa.


"Thank you, ya ake ciki?"


"Ni da team dina mun samu nasarar kama wannan kasurgumin kidnapper din da ya addabi mutanen Batsari da kewayenta, mun yi ta bibiyar sa tun daga jos har zuwa sanda ya shigo Kano, but sai muka rasa shi kuma, jiya da safe ina kokarin shiga wanka na samu kira daga wajen Lawal, an samu signal na wayar sa a tasha, we quickly set-up a team muka bishi daga Kano har Katsina,anan ne mukayi arresting dinsa yana kokarin shiga garin na Katsina da tarin bullets."


Dagowa yayi ya bar abinda yake yi ya dube shi


"Well-done!" Ya hau tafa masa


"You did a good job!" Ya daga masa hannu alamar jinjinawa


"Thank you sir." Yace yana murmushi 


"Yanzu yana ina?"


"Yana cell sir, ga duk bayanin abinda muka samu a gidansa da muka je."


"Ka ajiye min, zan shigo da daddare sai mu duba komai, kwana goma na basu suyi duk binciken da zasuyi su gama, mu tur."


"Ok sir."


"Yanzu ina sauri ne, abubuwan sun fara sauya salo dan haka ne ma nake ganin kai ne zaka jagoranci wannan tafiyar a matsayin team captain din, dan na tabbatar zaka iya."


"Ok sir!"


"Ga record din komai, name, address and phone number, da duk finding dina yana ciki."


"An gama sir."


"Yawwa, thank you."


Fita yayi ya barshi a ciki, ya karasa abinda zai yi sannan ya fito ya nufi office din ogan sa, ya dan dade a ciki kafin ya fito ya tafi ba tare da ya koma office din nasa ba.


   A mota ya bar wayar sa da yake amfani da ita a gari dan dama ka'idar aikin kenan dan a kashe ma take sai da ya fito gaba daya daga lungun sannan ya kunna ta. Kamar Aryan yana jira sai ga kiran sa ya shigo


"Wai kana ina ne?"


"Gani nan na taho."


"Me ya samu wayarka a kashe?"


"A aljihu na turata, ashe na danne power button din ban sani ba."


"Ok sai ka karaso."


 Yace ya kashe wayar. Ajiye wayar yayi ya jawo dashboard dinsa ya d'aga wasu tarkace ya tura I'd card din sa.***Kamar wadda ta shekara rabon ta da gida haka taji, wato dai da gaske kowa ya bar gida, gida ya barsh. Ji tayi baki daya ta tsani Kano da duk mutanen da suke cikin ta. Dama zata koma baya da sai ta goge haduwar su da Hajiya Zeenat shikenan da bata shiga wannan masifar ba, da kuma bata hadu da Aryan da Kamal ba. Baki ne suka dinga tuttulowa gidan nasu zuwa yiwa Abby barka da fitowa dan haka sai gidan ya zama ya cika sosai. Dakin ta, ta gudu taje ta kwanta dan har lokacin jikinta be gama yi mata daidai ba, gashi da ta zauna sai tunanin abinda ya faru ya shiga dawo mata. Dadah ce ta biyo ta dakin ganin ta baro falon kuma duk sai taga bata yarda da yanayin Raihanan ba. Zama tayi a gefen gadon tana duban ta.


"Lafiya?" Tace mata dan fuskarta ta nuna ba lafiyar ba.


"Zazzabi nake yi,Amma nasha magani."


"Tun yaushe? Ko dai akwai wata damuwar bayan ta zazzabin Raihana?"


Girgiza mata kai tayi, dan bata san ta in da zata fara yi mata bayanin abinda ya faru ba, musamman a yanzu da duk suke cikin farin ciki mara misaltuwa.


"Ba komai Dadah na, da na sake hutawa shikenan."


"Kayya, babu karyar da zaki yi min na yarda dake Raihanatu, ki sanar dani damuwar ki, na sanki kamar yunwar cikina dan haka kar nake kallon ki."


Zamewa tayi daga kwanciyar da tayi da nufin zama sosai sai wayar ta, ta hau ringing, kurawa number dake kira ido tayi dan bata taba kawo kiran nasa ba.


"Ko dai sabon saurayi kikayi a Kanon Raihana?" 


Dadah tace tana rike baki, da sauri tace


" A ah wallahi, ni banyi komai ba."


"Toh waye yake kiranki? Kika zubawa waya ido kuma baki dauka ba? Ko fada kukayi da saurayin?"


"Kai Dadah kinji ki, ni wallahi ba wani saurayi, kawata ce ma take kira na."


"Kawa? Yaushe kikayi kawar bamu da labari."


"Shikenan bani da kawa a duniyar nan Dadah?"


"Baki da ita gaskia, sai abokan arziki."


"Ni me aka maida ni a gidan nan ne? Dole ma nayi sabuwar kawa."


"Oho, kamar gaske. Idan kin gama wayar ki fito cikin mutane bana son kina darere kanki ke kadai."


"Tohm." Tace ta rakata da ido har ta fice. Wayar ta riga ta katse, haka kawai sai taji babu dadin rashin dagawar da batayi ba. Jujjuya wayar ta dinga yi a tunanin ta zai sake kira amma shiru, yunkurawa tayi ta tashi tayi hanyar fita sai ga kiran ya sake shigowa, da sauri ta dawo baya ta rufe kofar kar Dadah ta dawo tayi wata maganar da zai ji, sannan ta daga tayi sallama a hankali chan kasa. Maimakon ya amsa sallamar sai yayi shiru ya fara tunanin dalilin da yasa shi kiran ta


"Ya jikin naki?" Ya tattaro kalmar da k'yar ya fada yana ciccijewa


"Ina wuni?" Ta gaishe shi a maimakon amsa tambayar da yayi mata


"Lafiya, sai anjima."


Kit ya kashe wayar, saroro tayi da waya a hannu cike da madaukakin mamakin sa, wannan wacce irin waya ce? Dariya abin ma yaso bata ganin yadda yayi maganar kamar wanda aka saka a gaba akayi masa dole ya kirata, saukin ta ma shine ya kira da ita ta kira yayi mata haka da tasha dan banzan kunya. Samun kanta tayi da dariya sosai daga karshe da ta gama tunanin abun, sam bata taba ganin irin sa ba, wai sai anjima, shikenan? Ta dauka ma wani abun ya rasa a office ya kira ta, bata ga amfanin kiran nata ba gaba daya. Toh ko dai kira yayi kawai ya duba ta tunda har yace mata ya jiki a farko. Ajiye wayar tayi kawai a dakin ta fice dan idan ta zauna tunanin son gano dalilin kiran nasa zata iya kaiwa dare a dakin bata fito ba.


****Dukkan wani kokari da Yaron Hajiya Zeenat zai yi mata akan Matawalle ya gaza, tun tana ganin abun wasa ne sai kuma jikinta ya fara bata lallai ya shirya mata, shirin da kuma ta gaza gane in da ya dosa, tasan shirun sa ba alkhairi bane a gareta, dan a sanin da tayi masa tasan tabbas da tuni ya neme ta ya kirata ya tabbatar mata da fitowar sa, dan ko a karshen zuwa ganin sa da tayi a prison ta lura da wata halayya daban da ta Matawallen da ta sani dan har ta dinga tunanin dalilin shi na share ta da kin yarda ya biye mata ba kamar a baya ba, idan taje ganin sa ya kan jaddada mata sai ya kaita k'asa in dai yana numfashi a doran k'asa. 

   Raihana ce ta fado mata, tabbas ita kadai ce a yanzu zata zame mata garkuwa da kuma tsani wajen samun lagon mahaifin ta, da ita zatayi amfani ta sake kaishi kasa wanda zai fi masa ciwo fiye da kaiwar da tayi masa a shekarun baya dan wannan sai yafi jin zafin ace yar cikin sa ce zata aikata masa hakan.

   Wannan tunanin ya dan bata hope har ta kara samun kwarin guiwa sosai duk kuwa da chan kasan zuciyar ta, tana cike da tsoron abinda zai biyo baya idan komai a fallasa, amma duk da hakan ba zata karaya ba, dan ita din ba raguwar mace bace ba, tun zamanin kuruciya kuwa ballantana yanzu da ta kai matakin kuloluwa a matakan nasarar da ta tsarawa kanta cimmawa a tsawon rayuwarta. Gida ta koma kawai dan tun fitar safen da tayi bata komo ba, sai dai tayi matukar tsurewa ganin Adam har lokacin yana gidan a dakin sa yana ta sharar baccin asara. Wani wawan duka ta kai masa a gadon baya wanda hatta takalmin kafarsa be samu cirewa ba dashi ya kwanta ruf da ciki ya dage kafafun sama. Dabiar da ya fara kenan chan baya ta shiga ta fita ta samu nasarar hanashi tun Daddyn be farga ba, sai yanzu da kusan komai yazo hannu shine zai dawo ruwa kenan, ya barta da komai ta ina zata fara bayan ba aikin ta bane ba, wa zai cigaba da kula da komai kenan? Idan haka ne karshe fa kenan sai dai komai ya dawo karkashin Aryan abinda ba kuma zata taba amincewa ba dan duk wata dukiya da Daddyn ya tara kusan tare da ita aka tarata dan ita ta taimaka masa matuka har ya kawo wannan matakin da yake kai shine kuma dan rashin alkawari har ya maida komai da sunan yaransa biyu ita da Adam sun tashi a tutar babu. Bata da plan din yiwa daddy komai dan ta gama sakankancewa zai damka wa Adam kusan komai, rana daya ta ji shi yana waya da lauyan sa, daga ranar komai ya chanja ta shiga neman rayuwar sa tun kafin ya nemi ta ta.

   Soshe soshe Adam din ya hau yi wajen da ta dake shi, ya tashi yana kumbura fuska ya wuce toilet ya wanko fuskar sa da bakin sa ya dawo ya tarar da ita a tsaye tana jiran sa


"Yanzu tun da na fita kake baccin asara Adam? Ina chan ina kokarin gina maka rayuwa amma shine zaka zo ka kwanta office din ma ka daina zuwa kenan Aryan ya mallake komai."


"Ni bana son komai idan har ba zan samu Raihana ba."


"Raihana kuma? Wai dama wannan maganar bata mutu ba?"


"Wallahi bata mutu ba, kuma son ta nake auren ta zan."


"Tirkashi, akan hakan kake son maida kanka wani na daban?"


"Lallai baka da hankali ma wallahi, idan ma zaka hakura tun wuri gwara ka hakura, mahaifin ta ko mutuwa zakayi ka dawo ba zai baka yarsa ba wallahi,."


"Akan me yasa ba zai bani ba?*


"Saboda baka san waye uban nata ba ai shiyasa zaka tsaya tambaya, toh yar Barrister Matawalle ce, ina fatan yanzu zaka saita hankalin ka waje daya ka dawo hayyacin ka, kasan in da yake maka ciwo."


Fuuu ta fice tana bambamin fada. Shiru yayi bayan ya fita, tabbas ya san waye Matawalle a wajen mahaifiyar sa, sannan yasan duk wata harkalla da ta ke tsakanin su, babban abinda yake damuwan sa shine yadda yaga Aryan ya damu matuka da al'amarin yarinyar, tunda ko last akan ta sukayi fada sosai ya kuma hangi wani abu a chan cikin idon Aryan din.


"Ba zai yiwu ba, sai dai dukkan mu, muyi biyu babu wallahi." Yace yana yin hanyar barin dakin. Dakin Hajiya Zeenat ya nufa ya tarar bata ciki sai wayar ta, dama abinda yazo nema kenan, da sauri ya bud'e wayar ya shiga wajen audios din dukkan wayar da sukayi da Raihana, yayi copying komai akan wayarsa sannan ya ajiye mata wayar ya juya ya bar dakin. Da wannan zai yi amfani yasa Aryan ya tsane ta, tsanar ta har abadah, shikenan kowa ya rasa dan zuciyar sa ba zata iya daukar nasarar Aryan din ba.***Daddy na kwance har ya bata jikin sa da fitsari dan gaba daya ranar babu wanda ya leko shi, motsin bud'e kofar yaji sai kuma haske ya gauraye dakin. Takowa tayi zuwa gaban sa tana toshe hancin ta da hannun ta.


"Menene haka?" 


Tace tana ja baya ganin kayan jikin sa a jike jagwab, hawaye ne ya biyo gefen fuskar sa tana kallo, ya motsa idon sa.


"Ni zaka ci amana Alhaji? Ni Zeenatu da na sadaukar da rayuwata da komai na akan ka ni kayi tunanin yaudara ko? Har kasa a fito da Matawalle ba tare da sani na ba, saboda kana son farantawa wanda ba zai taba yafe maka ba, duk da abinda kayi yanzu Matawalle ba zai taba yafewa mutum irin ka ba, macuci maha'inci irin ka, da kayi hakuri mun cigaba da yadda muka faro, domin nice daidai da kai, amma sai ka ci amanata bayan ka manta wacece Zeenatu, ba'a taba cin amaanata a zauna lafiya, dan haka sai ka cigaba da zama a haka har zuwa sanda na gama cika buri na,idan zuwa lokacin ka karasa kuma shikenan."


Kokarin motsawa yayi amma ya kasa, gashi yana so yayi mata magana amma sam bakin sa ya kasa, be san me tayi masa haka ba, amma ko ma menene Yana bukatar taimakon gaggawa, dan wani irin nauyi da jikin nasa yayi masa ga wani irin ciwo da idanun sa suke masa tamkar zasu daina gani. A yau yayi nadamar biye wa mace irin Zeenat, ta raba shi da yayansa masu so da kaunar sa, ta nisantasu dashi ya zama na basa iya neman sa face shi ya neme su, da kansa kuma ya kafa musu wannan sharadin a lokacin da yake jin su tamkar wasu nauyi a gareshi. Da ace be hana su, yasan da tuni sun neme shi tun a jiyan, yanzu be san ranar fitar sa daga nan ba,watakila haka zai karasa RAYUWAR sa a wajen ba tare da ya nemi yafiya da afuwar su ba, musamman ARYAN!
Ignore all the typos, I'm super busy wallahi. *_ZAFAFA BIYAR COMPLETE DOCUMENTS_**ZAFAFA BIYAR BACTH A*1.. _WUTSIYAR RAƘUMI_ 350

 *(Bilyn Abdul)*2.. _KAI MIN HALACCI_ 350

*(Miss xoxo)*3.. _BURI DAYA_ 350

 *(Mamu gee)*


4... _DAURIN BOYE_ 350

*(Huguma)*


5... _SAUYIN KADDARA_ 350

*(Hafsat Rano)*


_Duka biyar 1500_


*___________________________*

    


*_ZAFAFA BIYAR BATCH B_*1... _DAURIN GORO_ 350

*(Hafsat Rano)*


2... _ALKAWARIN ALLAH_ 350

*(Huguma)*


3... _QAUNAR MU_ 350

*(Mamu gee)*


4... _IGIYAR ZATO_ 350 

*(Miss xoxo)*


5... _GUDU DA WAIWAYE_ 350

*(Bilyn Abdull)*_Duk biyar 1500_


*_____________________________*


*_ZAFAFA BIYAR BATCH C_*


1... _MIN QALB_ 350

*(Mamu gee)*


2... _SARAN ƁOYE_ 350

*(Bilyn Abdull)*


3... _KIBIYAR AJALI_. 350

*(Miss xoxo)*


4... _ABINDA KE CIKIN ZUCIYA_ 350

*(Hafsat Rano)*


5... _SIRADIN RAYUWAR BILKISU_ 350

*(Huguma)*


_Duk biyar 1500_


*____________________________**_ZAFAFA BIYAR BACTH D_*


1... _ALKIBLA_ 350

*(Huguma)*


2... _DALAAL_  350

*(Miss xoxo)*


3... _UBAYD MALEEK_ 350

*(Mamu gee)*


4... _MABUDIN ZUCIYA_ 350

*(Hafsat Rano)*


5... _MAKAUNIYAR KADDARA_ 350

*(Bilyn Abdull)*_Duk biyar 1500_


*____________________________*


*_ZAFAFA BIYAR BATCH E_*


1... _SO DA ZUCIYA_ 350

*(Mss xoxo)*


2... _TAKUN SAAKA_ 350

*(Bilyn Abdull)*


3... _HALIN GIRMA_ 350

*(Hafsat Rano)*


4... _DAB'IZAR ZUCIYA_ 350

*(Huguma)*


5... _DEEN MARSHALL_ 350

*(Mamu gee)*_Duk biyar 1500_


*______________________________**_ZAFAFA BIYAR BACTH F_*


1... _BAKAR INUWA_ 350

   *(Bilyn Abdull)*


2... _RAYUWAR MACE_ 350

    *(Hafsat Rano)*


3... _NOOR ALB_ 350

     *(Mamu gee)* 


4... _MASARAUTA_ 350

    *(Mss xoxo)*


5... _KUFAN WUTA_ 350

    *(Huguma)*


_Duk biyar 1500_


*_____________________________*


*_ZAFAFA BIYAR BATCH G (COMPLETED)_*


1... _FARHATAL QALB_

*(mss xoxo)* 400


2... _GURBIN IDO_

*(Huguma)* 400


3... _SANADIN LABARINA_

*(Hafsat Rano)* 400


4... _INAYAH_

*(Mamu gee)* 400


5... _BABU SO_

*(Bilyn Abdull)* 400


_Kuɗinsu a yanzu 2K duk biyar_

*_ZAFAFA BIYAR 2023_*🔥🔥🔥

_*Sabuwar shekara sabon salo sabon taku,*_

_*Makaranta littafan hausa kuma masoya marubutan zafafa kuzo ga sabuwar tafiya zazzafa tazo karku bari ayi babuku *_


_*Zafafan alkaluman haziqan maruban zafafa biyar kowa yasan na daban ne,wannan karon ma sunzo da sababbin salo me kama zuciya.*_

_*ZAFAFAN MARUBUTAN SUNZO DA SABABBIN LITATTAFANSU NA 2023 Kamar haka,*_


1  _*IDON NERA*_

    Mamuhgee


2  _*DAUDAR GORA*_ ciki ka shata 

    Billyn Abdul


3  _*RUMBUN QAYA*_

     Hafsat Rano


4  _*KI KULANI*_ mallakin zuciyata

    Hafsat Miss Xoxo


5   _*A RUBUCE TAKE*_ qaddarata

    Safiya Huguma_DUKA GUDA BIYAR DIN ZAKA SAMESU A FARASHIN 1200_


Guda 5 1200

Guda 4 1000

Guda 3 800

Guda 2 600

Guda 1 400


_*zaku saka kudin a wannan account din👇*_


_*0022419171 Access Bank Maryam sani*_


Saiku tura shedar ta👇


_*09033181070*_


Idan kuma katin Waya ne zaku tura katin MTN ta wannan layin👇


09166221261

TEAM ZAFAFA BIYAR🔥🔥

MUNGODE🙏🙏❤️

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post