Rumbun Qaya hausa Novel Page 20

Rumbun Qaya hausa Novel Page 20

Rumbun Qaya hausa Novel Page 20

RQ

      Page 20


****A gurguje Adam ya watsa ruwa ya fito ya tarar da Hajiya Zeenat a zaune tare da wata mata, wuce su yayi bayan ya gaishe ta a gajarce suka bishi da kallo Hajiya Zeenat na cike da mamakin in da kuma ya nufa. Office ya wuce kai tsaye ya duba parking lot yaga motar Aryan sai yayi murmushi ya wuce bangaren sa kawai yana sake nanata abinda yake shiryawa a cikin kansa. 

   Aryan na zaune a office ya gama duba wasu takardu Kamal ya shigo kamar yadda ya saba ya fara zuro kansa sannan ya shigo yana dariya. 


"Wai ina kaje?" 


"Sabuwar budurwar da nayi ce ta kirani, shine fa na amsa kira kar tayi fushi dani."


"Sabuwar budurwa kuma?"


"Eh karaye zan je, kai ba ka tsaye wasa ba, ta biyu nake shirin yi ka zauna dai."


"Lallai wahala bata ishe ka ba,mace daya ma ya aka kare bare har biyu? Akan me yasa ma zaka kara aure."


"Sunna."


"Yen yen, dama haka kuke fakewa ai, ku tara matan suyi ta neman ranku."


"Hahaha, ko su dinga yar rige-rigen kyautata mana ba."


"Ba wani nan."


"Yanzu kai kenan mijin mace daya ne."


"Ko rabi ba,dayar ma ba dani ba, kai ni bana son wannan zancen please, akwai tarin ayyuka masu yawa suna jiran ka."


"Yanzu zan hau kansu ai."


"Yauwa jeka toh."


"A ah ai yau a office din ka zanyi aikin, bari na kwaso komai na dawo."


Kallon sa Aryan yayi, yana fita ya tashi yasa key a kofar ya dawo ya zauna yana murmushi.


   Baki daya yan office din sun dauka Raihana ta tafi kenan, ganin kwana biyu bata zo ba tun ma ranar dai da abin nan ya faru, sosai hakan yayi wa Zainab dadi dan a kwana biyun nan ko yaushe ita Aryan yake kira kamar dai da kafin zuwan Raihanan.    Ta fito zata tafi gida kenan Adam ya tsaida ta, ta tsaya tana dan waige-wage, kafin ta dan matsa sosai yadda ba za'a gano ta ba.


"Me yasa Raihana bata zuwa?"


"Ya tambaya dan yana ta lura da shige da ficen wajen amma be ga wucewarta ba ko kad'an


"Inaga ta chanja wani wajen, tun ranar da abin nan ya faru bata sake zuwa ba."


"Damn it!" Ya bugi gefen gini sannan yace taje.



***Zaman Raihana a gidan su ya kara sata sakankancewa sosai har ta manta da sabgar Hajiya Zeenat da kowa ma, sosai Abbyn ta yake samun kulawa ta musamman dan bayan masu zuwa jaje sun zo sun gama wani sabon gida suka tattara suka koma me dauke da part hudu wanda Hamman ta suka dade suna ginawa dan sun yi alkawarin a tare zasu zauna gida daya har Abby. Bata san dalilin komawar su gidan a wannan lokacin ba dan ba'a gama ma sauran part din ba nasun dai kawai akayi sauri aka karasa. Ko yaushe Abby yana falon sa a zaune yana kallon news ko kuma ka same shi yana karatun alqur'ani me girma.  Ko yaushe suna tare da Tafeeda dan shine yake kula da Abbyn da koman sa musamman da ya kasance su Hamma Haydar da Babbo Sadeeq suna fita aiki kuma suna kai yamma likis kafin su dawo wani lokacin har dare ma.

   Da sallamar ta, ta shiga falon bayan an amsa mata an bata izinin shigowa. Lamido ne zaune a gefen Abbyn sai wata jaka a gefen shi wadda ta nuna da alama lokacin aka rufe ta.


"Uwata ce?" Abby yace yana dan mikewa daga kishingidar da yayi, 


"Eh." Ta gid'a kanta tana zama a daidai saitin kafarsa.


"Abby barka da gida."


"Barka dai, ya gidan?"


"Lafiya lou Abby, gobe zan koma Kano."


"Jibi, jibin nan?"


"Umm."


"Kaji Lamido, ba za'a yi wani abun ba akai?"


"Anyi Abby, shine ma har aka samu kanon."


"Toh ka tabbatar babu wata matsala ko?"


"Babu in sha Allah, ko akwai kanwata?" Ya kalle ta


"Babu Hamma." Tace tana murmushi


"Shikenan, Allah yayi muku albarka, sai ka shirya mata tafiyar Lamido."


"In sha Allah."


"Ki kula sosai kinji? Dan Allah Raihana karki wasa da rayuwarki da tarbiyyar da kika samu, karki ga babu idon mu akanki, muna sane da komai."


Shiru tayi kanta a k'asa, har ya gama mata nasihar, tayi godiya ta tashi ta fita wajen Dadah.


    ***Tafiyar rana zatayi dan haka ne ma ta karasa shiryawa a tsanake, bata son komawa har ga Allah amma kuma ya zatayi? Haka ta karasa hada abinda zata bukata sannan tayi wanka ta shirya. Babbo Sadeeq ne ya kaita airport dan Abby dama yace ya haramta mata tafiyar mota. A boye ta share hawayenta ba kamar wacchan tafiyar da take cike da dauki ba.


***Saukar ta a Kano yayi daidai da shigowar kiran Hajiya Zeenat, ta kikkirata a chan amma duk sanda tazo missed calls dinta take gani kawai kuma bata bi dan bata gama nutsuwa da abinda Kamal yake son tayi ba gashi be kirata ba kwata-kwata bare ta gaya masa abinda yake faruwa. Daga baya kuma kawai sai ta kashe wayar ta tura ta a drawer bata kuma sake kunna ta ba sai yau da zata taho shima dan tasan dole Dadah zata kira kafin su tashi sannan ta kira ta bayan sun sauka. Tsoron da take ji ne taji gaba daya ya dawo mata sabo. Kin dagawa tayi har ta katse sai tayi saurin kiran Kamal din tasan abinda ya kamata tayi.

   A lokacin suna tare da a gidan Aryan din kiran ya shigo, yayi murmured kad'an sannan ya daga yana mikawa Aryan din takardar hannun sa


"Raihanatu."


Dagowa Aryan yayi da dan sauri jin sunan da ya kira, Kamal na ankare dashi kawai sai ya bar wajen yayi hanyar fita baya yana amsa gaisuwar da take masa.


"Na dawo yanzu." 


"Masha Allah , ya hanya?"


"Alhamdulillah, lafiya lou."


"Good, kin baro kowa lafiya dai ko."


"Eh lafiya Lou."


"Toh madallah."


"Hajiya Zeenat ce take ta kirana a waya, bansan me zan ce mata ba."


"Dagawa zaki kamar babu abinda ya faru".


"Zan iya?"


"Sosai, ki daga kafin ta fara saka shakku akanki."


"Idan kuma ta sani wani abun fa?"


"Karki damu, yadda kuka fara a baya haka zaku dora, kina jina? You have to be strong babu abinda zai faru nayi miki alkawari, trust me."


"Ok." Tace a sanyaye


"Yawwa, call her back karki ji komai, kawai dai duk yadda taso kuyi maganar family dinki karki bata fuska."


"Ok." Ta sake cewa a sanyaye.


  Katse kiran yayi hango Aryan yana nufo wajen ta cikin glass, hannun sa rike da ball yazo ya wuce Kamal din ya bud'e kofar da zata kaika bayan gidan. Short ne a jikin sa da rigar sa da alama zai motsa jikin sa ne. Bin bayan sa Kamal yayi yana tattare hannun long sleeve din rigar sa


"Raihana ta dawo."


Yace masa yana durkushe yana gyara igiyar takalmin kafarsa. Be dago ba kawai yace ok ya daga ball din suka soma buga basketball.


***Bata bi kiran ba sai da ta karasa gida ta zauna bayan sun gaisa da Adda Maimuna sannan ta kira Hajiya Zeenat din gabanta na dukan uku uku. Rejecting kiran tayi ta biyo kiran nan take.


"Idon ki kenan Raihana?" 


"Kiyi hakuri Aunty, na danyi rashin lafiya ne."


"Ashsh, amma shine babu labari, ranar daga shiga in fito sai na neme ki na rasa ba wani bayani, ko akwai wani abu da ya faru ne?"


"A ah, kira na oga Aryan yayi ya gane bana office din shine nayi saurin komawa."


"Ok, toh ya jikin naki? Kin warware dai ko?"


"Alhamdulillah, na samu sauki gobe zan koma aiki ma in sha Allahu."


"Toh madallah, Allah ya kara sauki."


"Amin ya Allah, nagode."


"Zaki iya zuwa gobe? Ina son ganin ki."


"Na'am?"


"Eh ko akwai in da zaki je?"


"Eh amma zan gani idan na dawo da wuri."


"Toh ba damuwa,sai ki kirani."


"Ok tam."


    Baya tayi ta kwanta ta ajiye wayar a gefen ta, anya? Anya ba zata sanarwa ko Hamma Haydar bane ba? Zata fara dai tuntubar Kamal ya gaya mata gaskiyar komai kar ya sakata a matsala da karancin shekarun ta.


     

***Da sassafe Habib ya iso gidan ya tsaye a waje har sai da Aryan din ya gama shiryawa ya fito sannan ya ganshi zaune tare da Baba me gadi, tashi yayi da sauri ya gaida shi ya karbi jakar hannun sa ya saka a mota ya bud'e masa bayan motar amma sai yaki ya wuce ya zauna a gaba yana kin kallon sa. Rufe kofar yayi ya zagayo ya zauna sannan yace


"Sir da ka daure ka zauna a bayan"


"Anan nake son zama Habeeb."


"Please sir, bana so oga Kamal yaga kamar bana aiki na yadda ya kamata."


"Menene aikin naka?" Ya tambaye shi


"Driver."


Dan shiru Aryan din yayi kamar ba zai koma ba, sai kuma ya bud'e kofar ya koma bayan ya shiga ya rufe ba tare da ya sake cewa komai ba. 

  Gidan Ya Nabeela suka fara zuwa, tun daren jiya ta kira shi akan maganar daddy, hankalin ta ya kasa kwanciya dan duk wanda tasan suna harkar tafiye tafiye da Daddyn suna gari babu inda suka je, sannan duk rashin shirin da yake dasu musamman ma Aryan baya taba yin wata tafiya be sanar dasu ba, sannan wayar sa a kashe kuma maigadi yace be ga fitar sa ba dan tazo jiyan gidan lokacin Hajiya Zeenat tana sama sai wasu mutane da bata nutsu dasu ba da ta gani a gidan dan har ita kanta sai da suka tsaida ita da tambayar wajen wanda zata. Ko baccin kirki bata samu tayi jiyan nan ba kwata-kwata, shiyasa ta kira Aryan din shine yace mata zaizo da safe. 

   A zaune ya sameta tayi jigum tana zaune ko kayan baccin jikinta bata cire ba sai Hijab data dora akai ta sallami yan makaranta ta dawo ta zauna a falon tana cigaba da gwada kiran wayar Daddyn ko zata samu ta shiga. Tasowa tayi da sauri ta tare shi


"Aryan daddy ba kalou ba wallahi, ni ban yarda da matar nan ba,jiya da naje yanayin yadda take kaffa-kaffa da saman Daddyn na ji ban amince ba, dan Allah kayi wani abu akai, kar taje ta cutar da shi."


Hannun ta ya kama ya rike suka zauna ya zama tamkar shine wan itace kanwar saboda yadda duk ta rikice.


"Ya Nabeela, me yasa zaki damu kanki haka? Bayan kinfi kowa sanin Daddy ya zabi matar chan akan mu, duk abinda ya faru a yanzu be kamata ki damu ba, dan hakki ne ya fara bibiyar su idan ma wani abun ne ya same shi."


"Aryan! Kasan me kake fada kuwa? Daddy fa akace mahaifin mu."


"Na sani, ki kwantar da hankalin ki dan Allah, damuwarki matsala ce a gareni fiye da duk abinda zai same shi, amma zan bincika saboda ke, zan gano menene matsalar, amma saboda ke."


"Naji, ka shiga dakin sa ka dubo da kanka, ban yadda da ita ba wallahi, she's hiding something matar nan bata tsoron ALLAH."


"Zanyi, amma sai na gama da office"


"Na yarda, ina jiranka dan Allah."


"Ok, ki kwantar da hankalin ki, babu komai in sha Allah."


"Tohm shikenan."


"Bari naje, zamuyi waya anjima."


"Ok."


   Maganganun Ya Nabeelan ya dinga tattaunawa da zuciyar sa har suka iso company, yana zuro kafarsa suka hada ido da Adam a tsaye cikin fence yana kallon saitin sa, tahowa yayi wajen sa kai tsaye ya ganshi sarai anma sai yayi kamar be ganshi ba ya shiga barin wajen yayi hanyar nasu building din. Daga kafa yayi ganin zai shige ya cimmasa ya tsaida shi.


"Aryan please dan tsaye, tambayar ka zan,."


"Menene?"


"Dan Allah Raihana ta daina zuwa ne?"


Kamar wanda ya sokawa mashi haka yaji, yayi masa wani kallon lallai ma ka raina mun hankali sannan yayi shigewar sa. Tsaki Adam yaja ya juya yana kunkuni.

   Kanshi tsaye ya wuce office dinsu ko wajen yin attendance be je ba, ya samu desk dinta empty ba kowa,juyawa yayi ya wuce office din sa kawai ransa a bace dan idan akwai abinda yaki jini shine Adam ya tsaida shi da shirmen sa, musamman yanzu da maganar wata daban take hada su ba abinda ya saba hada su a baya ba. Haka kurum a duk sanda irin haka ta faru yake kasa controling fushin sa, ya kasa zama sam a office din ya fito ya leka office din Kamal shima be zo ba, agogon hannun sa ya kalla yaga karfe tara har da rabi ta dan gota ma. Tasowa Zainab tayi daga wajen zaman ta cikin yauki da yanga tazo ta tsaya a gabansa tana murmushi


"Akwai abinda kake bukata ne sir?"


"Babu komai, idan corper din nan tazo kice tazo ta sameni a office."  Sai ya juya ya koma office din ya barta a tsaye mamakin sa na neman kai ta kasa, akan Raihanan ya kasa nutsuwa tunda ya shigo haka ko kuma wani abun tayi da ya kasa hakura ya jira ta shigo. A sanyaye ta koma wajen zaman ta, ta zauna tana ko zama sai ga Raihanan ta shigo sanye da black abaya tayi rolling da mayafi mustard colour wanda yayi masifar karbar farar fatar ta. Wani kululun abu ne ya tokare Zainab a makogwaro ta yi saurin dauke kanta ganin tana bi suna gaisawa da mutane, ko da tazo kanta tayi mata sallama kamar yadda ta saba ta wuce office dinsu ta bar Zainab da wani irin sanyayyan kamshin ta da ya cika mata hanci. Tana sane taki fada mata sakon Aryan din dan zuciyar ta zata iya bugawa idan ta cigaba da ganin Aryan din yana kula Raihanan.

  Bayan mintuna kamar ashirin da zuwan ta, tana zaune kawai dan bata san aikin da zatayi ba Kamal kuma har lokacin be shigo ba bare ta tambaya shi, Aryan kuwa ko giyar wake tasha ba zata tunkare shi ba dan a dar dar take dashi gani take kamar zai gano abinda tayi. Kanta ta dora a saman desk din kawai ta kulle idon ta, ta kunna suratul bakara ta makala earpiece dan ta gaji da kallon wayar.

   A kanta ya tsaya yana nakaltar yanayin ta, amma sam bata san ya shigo ba, dan ko alamun an tsaya a kanta bata ji ba, a hankali kad'an kad'an take motsa bakin ta, tana bin kira'ar shuraim kuma har lokacin bata bud'e idon ta ba. Dan rankwafowa yayi a daidai saman kanta ya sa hannu ya zare earpiece din daga jikin wayar ta dago da sauri idanun su suka sarke da juna. Diriricewa tayi dan bata tsammaci ganin sa a wajen ba dan ba kasafai yake shigowa ba, waigawa tayi taga babu kowa ashe a office din su abdulhakeem duk sun fita sai ita kadai sai shi da yake tsaye a gabanta rike da earpiece din. Ji tayi baki daya office din yayi mata wani irin fadi da girman gaske, daidaita nutsuwar ta tayi ganin ko gezau be ba yana kallon ta kamar be san me yake ba.


"Ina kwana?" Ta tattaro jarumta ta gaishe shi ganin yaki cewa komai 


"Follow me." Yace kawai ya juya ya fice daga office din rike da earpiece din nata a hannun shi.






_ZAFAFA BIYAR 2023_*🔥🔥🔥

_*Sabuwar shekara sabon salo sabon taku,*_

_*Makaranta littafan hausa kuma masoya marubutan zafafa kuzo ga sabuwar tafiya zazzafa tazo karku bari ayi babuku *_


_*Zafafan alkaluman haziqan maruban zafafa biyar kowa yasan na daban ne,wannan karon ma sunzo da sababbin salo me kama zuciya.*_

_*ZAFAFAN MARUBUTAN SUNZO DA SABABBIN LITATTAFANSU NA 2023 Kamar haka,*_


1  _*IDON NERA*_

    Mamuhgee


2  _*DAUDAR GORA*_ ciki ka shata 

    Billyn Abdul


3  _*RUMBUN QAYA*_

     Hafsat Rano


4  _*KI KULANI*_ mallakin zuciyata

    Hafsat Miss Xoxo


5   _*A RUBUCE TAKE*_ qaddarata

    Safiya Huguma


_DUKA GUDA BIYAR DIN ZAKA SAMESU A FARASHIN 1200_


Guda 5 1200

Guda 4 1000

Guda 3 800

Guda 2 600

Guda 1 400


_*zaku saka kudin a wannan account din👇*_


_*0022419171 Access Bank Maryam sani*_


Saiku tura shedar ta👇


_*09033181070*_


Idan kuma katin Waya ne zaku tura katin MTN ta wannan layin👇


09166221261



TEAM ZAFAFA BIYAR🔥🔥

MUNGODE🙏🙏❤️

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post