Wata Sakayya Hausa Novels page 25 - Novels Elite

Wata Sakayya Hausa Novels page 25 - Novels Elite

Wata Sakayya Hausa Novels page 25 - Novels Elite

 *(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*


Kokarin azawa akan tafarki,shi ne abu mafi muhimmanci da yakamata marubuta su kware akai,mu proficient writers association za mu yada wannan manufa.


https://www.facebook.com/profile.php?id=100086156706062


https://t.me/+R7IGS941_bg3NDI0


  https://chat.whatsapp.com/GK9uG1er0mUFsuS1s5JE9K


BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM.


👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽  

😭😭😭😭😭😭 


 *WATA SAKAYYAR*

        (Sai a Lahira)


👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽


By

            *Nusaiba Alkamawa*

         

 _Free page 25_ 

*****

______Haka aka cigaba da samo masa wadan da zasu kula dashi amma ko wanne aka kawo baya wuce kwana uku zai kore sa, wai basu iya aiki ba, tun Muhseen na biye masa yana samo masa masu kula dashi harya gaji. 


"Mommy kuwa dama zura masa ido kawai tayi ta rasa mai zatace masa. 


yanzu haka itace takeyi masa komai domin babu mai kula dashi yanzu .Domin kanwar sa tayi tafiya sai su biyu ne kawai a gidan. 


 *Jiddah* 


_____Jidda ce kadai a cikin falon tana shara sharanma ba wani iya ta tayiba sosai, saiga Al'amin ya fito hannun sa dauke da kayan wanki, watsa mata su yayi yace "gashi nan maza _maza kibar abinda kikeyi kije ki wanke min su, kuma wllh idan basu fita ba sai jikin ki ya gaya maki" yana gama fadin haka ya barta tsaye da tulin kayan wanki a gabanta, wasu zafafan hawaye ne suka zubo mata tun da ta dawo daga asibiti sukaga ta samu lafiyar kafafuwa tun daga lokacin ta zama jakar su har wata yar rama tayi tsabar aikin da takesha a gidan sai kace wata jaka,ga kuma rashin sabo, haka ta bar sharar ta dibe kayan wankin ta fito nan gaban gidan inda fanfo yake ta fara wankin ba ita ta gama wankin ba sai karfe sha biyun rana saboda tsabar yawan kayan, tana gama shanya kayan ta nufi falo domin taje ta karasa sharar data fara dazu, tana saka kafar ta a falon ta taka kwalba ihu ta saki saboda zafin shigar kwalbar, dariya su Hassan suka saka suna nunata harda rike ciki dama sune suka fasa kwalbar danta taka saboda sun hango lokacin da take tahowa,tana tunanin, jini ne ya fara zuba a jikin kafar zama tayi a kasa ta zare kwalbar tana hawaye ga jinin da yake zuba, Hassana ce ta sauko daga sama saboda ihun dataji turus taja ta tsaya ganin har zuwa lokacin ba'a karasa sharar falon ba, tace "kee dan ubanki shine har yanzu baki karasa sharar ba, kuma ihun uban mai kikewa mutane?" duk kuwa da taga jinin da kafar jidda takeyi amma sai bata damu ba, "su Hassan ne suka fasa kwalba ni kuma ban sani ba na taka, tafa da da ya ran kura me  ","shine kuma kika zauna kinawa mutane kuka" ta fada tana duma mata dundu, "maza ki tashi ki karasa min sharar falo kafin na dawo wajan nan naci uban ki" rushewa da kuka Jidda ta kuma yi saboda zafin dundun da Hassana tayi mata, Shamsiya ce kawar Hassana ta shigo falon tana karkada mukullin mota a hannunta, "ita kuma wannan jakar gidan naku kukan mai takeyi","rabuda shegiya mana wai danta taka kwalba shine take wannan kukan" tsaki Shamsiya ta saki tana kara hanbare Jidda da kafa sannan ta wuce suka haye sama itada Hassana, da kallo Jidda ta bisu tana hawaye.


_____Suna shiga daki suka zauna suna dan taba hira Hassana sai tsinewa Jidda takeyi, "kece kika yarda ai na fada maki kawai ki kawar da ita da doran kasa ki huta kemah","Shamsiya kenan nifa na gaya maki duk tantiranci na bazan iya yin kisan kai ba gara dai nida yarana muyi ta gallaza mata a xaba ","Allah ko, to bari kiji na gaya maki kina zaune wani attajirin zaizo yayi wuf da ita wanda yafi mijin ki arziki da komai da komi, kina ganin wani azababban kyau da take karawa gashi yanzu har tafiya take iyayi","wllhi na rasa yadda zanyi da yarinyar nan na tsane ta wllhi shiyasa ma fa yanzu duk aikin gidan nan ya dawo kanta kuma nake saka yarana suna azabtar da ita","ni kuwa akwai wata yar uwar makociyata dattijuwa ce to yaranta bashi da lfy shine suke naiman mai kula dashi, kuma wllhi cewa sukayi ko nawa ne indai yaron ya yarda da aikinta zasu biyata, kinga in kika aika Jidda a matsayin wacce zata kula dashi ko duk wata dubu dari biyu suke biyan ki mai kika manta","wai da gaske kike","wllhi da gaske yanzu ma inkin amince saimu tafi da ita ta fara aikin","wllhi na amince ni dama  tsani na bude ido naga wannan shegiyar yarinyar","kinga kuwa yanzu inta tafi gidan da zata rika musu aiki shikkenan  sai dai intazo da yawo ne" haka suka sheke da dariya, saukowa Hassana tayi tana kwalawa Jidda kira, zuwa Jidda tayi tana sunkuyar da kanta kasa, kije ki hado kayan ki yanzu zaku tafi da Shamsiya zaki rika kula da wani marar lfy ana biyanki duk wata amma ki sani bake za'a rika bawa kudin ba nice wacce za'a rika bawa, kuma wllhi duk abinda yace kiyi masa to kiyi masa koda jikin ki yace yanaso ki bada wllhi muddin kika bari aka koro ki to wllhi sai zaman gidan nan ya gagare ki"

Share fisabilillah.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post