Rumbun Qaya hausa Novel Page 4

Rumbun Qaya hausa Novel Page 4

 

Rumbun Qaya hausa Novel Page 4

*RUMBUN QAYA*


  

           Free Page 4


©️®️ *_Hafsat Rano_*


ZAFAFA 2023🔥🔥🔥🔥🔥


_____________


_*MAAB LUXURY HOME!!* Sabuwar duniyar hamshakan mata da ƴaƴan gata.💞_


_*GIDAN* ƙawa da ƙawata gidajen da suka cika gida._ 


_*SABUWAR DUNIYAR* Amare da uwargidan data amsa sunanta ƴar gaban goshi._


_*MAAB LUXURY HOME* wata duniya ce ta ƙawa da ƙawata gidajenmu da kayan ƙyale-kyale na burgewa da ɗaukar hankalin duk wani mai kallo_. 


_*SUNYI FICE* Fice irin na ɗaya a cikin tsara, sune na farkon fari, a farin da za'a kira fari a kowace irin duniya._


_*A GAREMU* ba sitturu na alfarma da kawa ne kawai ke tabbatar da mu hamshakai ba. Sai mun haɗa da ƙawata gidajenmu da kayan MAAB LUXURY HOME zamu kasance cikakkun ƴan gata ababen kallo da nunawa sa'a koda a cikin dubun da sukafi dubu._


_*MAAB LUXURY HOME* sun takaita mana dukkan wahalar nema ko order a kasashen ketare ta hanyar wadatamu da galla-gallan kayayyakin adon gidajenmu_


_*MAAB LUXURY HOME.* Duniyar kayan Kitchen da decoration din gida na keta raini._ 


_*INA UWARGIDA INA AMARYA!!?* Ku ziyarci shagon mu dake No 22 Ahmadu Bello Way, Kano state. Ko kuyi order daga shafin mu na Instagram @maabluxuryhome. Ko Facebook @maabluxuryhome. Ko Ku nememu a lambar waya *08034631010*._


*_Mai azama shi za'a kira dana farkon fari😉. Bara nai sauri nawa suzo hannuna kafin a kwashe😁⛹🏼‍♀️⛹🏼‍♀️⛹🏼‍♀️._*.•••••••


    Daga kansa yayi ya kalli kofar da akayi knocking kafin yace


“Yes!”  Turowa yayi ya shigo fuskar sa ba yabo ba fallasa,yanayin sa Aryan ya kalla kafin yace 


“Akwai matsala ne?” Girgiza masa kai yayi kafin ya zauna, sannan yace 


“A ah, maganar da na saba dai kullum ita ta kawo ni yanzu ma, dan Allah ka rage zafi Aryan."


Bata fuska yayi yana duban Kamal din yace


"Me kuma nayi?"


"Yadda kayi ma yarinyar nan dazu, ba dadi."


"Ni ba abinda nayi mata, iya gaskiya ta kawai na fada corpers din nan basa da wani amfani."


"But ai be kamata ka fada a fuskar ta ba."


"Toh naji, wai ka santa ne?"


"A ah me ka gani?"


"Yadda kazo ka titse ni mana akan ta."


"Ni dai kawai ka yarda bakayi daidai ba, mata suna da rauni sosai, hakan zai iya effecting dinta."


"I don't believe you, they are very cunning, sun iya shedding crocodile tears."


"Banda Raihana." Yace yana murmushi


"Raihana?""Yes! Baka ga sunan ta a jikin takardar ta ba?"


"Ban karanta ba ai."


"Amma kayi signing?"


"Ina da wani option ne?"


"You are not nice wallahi, ai shikenan. Nace ta fara zuwa gobe sai ta dinga zuwa sau uku a sati,ta zauna a cash office muga abinda zata iya."


"Cash office? Why not reception? Ko su zauna dasu Zainab."


"A ah, karatun ta ya wuce haka nan, taje dai cash office din su yi aiki tare da su abdulhakeem."


Mikewa yayi ya dauki rigar sa da ya sakale a jikin kujerar da yake zaune ya dora ta a saman t-shirt din dake jikin sa, ya kwashi wayoyin sa ya zuba su a aljihu sannan ya kalli Kamal din da ya mike tsaye shima yana daukar wani file a saman desk din Aryan din yace


"Zan je naga Ya Nabeela."


"Kaga da ba dan wannan aikin da yake gaba na ba, da munje dan na kwana biyu ban shiga ba, nayi missing daddad'an girkin ta


"Muje mana, ba dadewa zan ba nima muna da meeting da shareholders da karfe biyu, so har ma dawo ma."


"Ok toh bari na dauko wayata a office."


"Ka sameni a parking lot." Yace yana yin gaba, suka fito a jere shi yayi k'asa shi kuma Kamal ya koma office dinsa ya dauko wayar sa ya rufo.


   A harabar wajen ya same shi tare da Malam Musa suna magana akan sabbin motocin da suka siyo na mai wanda zasu iso anjima, gobe yake saka ran dawowar Daddy shiyasa ma zai yi duk kokarin sa wajen ganin ya kammala duk ayyukan da ya tafi ya bari. Hango Adam yayi ya fito daga dayan block din da yake kallon nasa, ya nufo su ya sakashi katse maganar da yake niyyar yi ta hanyar cewa


"Bari na dawo Malam Musa zamuyi magana."


Ya nufi motar sa, Kamal da ya fuskanci dalilin da ya sashi barin wajen yayi saurin bin bayan sa ya shiga motar, yaja suka bar wajen.


"Malam Musa biyo ni office."


Adam yace ya juya ganin sun watse ba tare da sun bari ma ya karaso ba, bin bayan sa Malam Musa yayi ciki yana ayyana abinda Adam din zai tambaye shi wanda ya saba tambaya a duk sanda ya gansu tare da Muhammadun suna wata magana.

   

***Wayar sa ya dago da tayi kara ya daga ganin Ya Nabila ce, sukayi magana ya ajiye yana maida hankalin sa akan tukin da yake yi. Kamal ne ya karya shirun da yayi ta hanyar sako maganar Adam


"Menene matsalar sa wai?"


 Yace yana duban Aryan din da kansa yake kallon titi cikin yanayin da zai yi wuya ka iya tantance abinda yake ransa


"Matsalar sa ta wuce ni?"


"Allah ya kyauta, yaushe Daddy zai dawo?"


"Gobe in sha Allah, bansan ko daga goben zan sake shigowa office din ba a cikin week din, dan nima inaso na danyi wani aiki a office dina."


"Ka daure dai ka shigo please, shi kansa Daddy yanzu baya iya dadewa a company dole dai kai ne kasan dai ba za'a sakar ma Adam komai ba ko?"


"Kana mamakin hakan? Daddy yana ta shirye-shiryen bashi share me tsoka a company din."


"Are you serious?"


Dage kafadarsa yayi irin I don't care din nan sannan yace


"I'm serious, abinda suke ta planning kenan."


"Then me ka shirya?"


"Ban shirya komai ba, na gaji ma baki daya ta zuwa company wallahi, na matsu ayi a gama na cike wa'adin da daddy ya daukar min nayi gaba, be damen ba wajen nan ko kad'an, buri na daya ne kuma ka sanshi, so bana bukatar wata dukiya ko wani fame, su suke ta wahalar da kansu I'm willing to give everything in dai zan samu cikar buri na."


Murza saman goshin sa Kamal yayi cikin yanayin damuwa yace


"Nasan yadda kake ji, ka sani kowanne tsanani yana tare da sauki, in sha Allah komai zai wuce kamar baa yi ba, zaka dawo rayuwar ka tamkar yadda kake a baya, in sha Allah."


"In sha Allah, amma bana tunanin hakan Kamal,karka manta ina fama da PTSD (Post Traumatic Stress Disorder )."


"Na sani, amma zaka samu sauki in sha Allah, mu cigaba da addu'a sannan ka cigaba da ganin therapist dinka kana shan dukkan magungunan ka, zai wuce."


"In sha Allah!" Yace daidai lokacin suka karaso gidan, yayi horn megadi ya bud'e musu suka shiga ciki.


  Amna ce a gaba Amaani na bayan ta cikin rige-rigen zuwa yi masa oyoyo, sune kananan yaran Ya Nabeela sai yayyane su biyu Affan da Hadiyya. Daga su yayi sama a tare cikin tsananin kaunar su, ya rungume su a jikin sa yana dariyar da ba zaka taba ganin yayi ta ba in dai ba yana tare da su ba. Sai da ya gama daga su sama sannan Kamal ya dauki Amaani shi kuma ya dauki Amna suka shiga ciki suna musu surutu.

  Hadiyya da Affan na zaune sun saka Ya Nabeelan a tsakiya suka shigo, tashi sukayi su ma suka zo wajen su suka yi hugging dinsa sannan suka zauna duk suka mamuke masa.


"Ku barshi ya zauna mana sosai Affan, kun bi kun dabaibaye shi kamar yau kuka fara ganin sa, sannun ku da zuwa kanina."


Ta karashe tana kallon Kamal


"Sannu da gida Babbar Yaya."


"Sannu Kamal, ya gida ya aiki?"


"Alhamdulillah wallahi."


"Masha Allah."


"Small mom ina wuni?"


"A ah gama da yaranka, sai mu gaisa." Tace cikin sigar tsokana, murmushi yayi ya gyara zaman sa sosai yana daidai ta su suma sannan ya gaishe ta, ta amsa tana masa murmushi me dauke da kaunar da tausayi a lokaci daya, murmushin shima yake ta tashi ta kawo musu abinci sannan ta kora su Amna dakin su ta saka musu kallo ta dawo suka sake gaisawa sosai suka dan taba hira, ta dauko wasu takardu na maman su ta bashi ya bud'e ya dudduba sannan ya mikawa Kamal shima ya duba. Daga nan suka tashi sukayi mata sallama yaran suka rakosu har mota tare da ita, ya dauko musu chocolates dinsu a baya da ya manta da ita ya basu sannan suka koma office dan lokacin meeting din nasa ya kusa dan sai da suka kara sauri idan ba haka ba da ya makara.***Tana fesa turare ta gama shiryawa Amina ta shigo, ta zauna tana kallon yadda tayi kyau cikin shigar riga da skirt na atamfa orange and mint green ta yafa orange veil wanda yayi matukar haska ta kasancewar ta fara sosai, tana son gayu a rayuwar ta duk da komai nata very simple ne amma tasan marching colours sosai shiyasa Amina take jinjina mata dan da gaske yar gayu ce ta bugawa a jarida, koman ta very unique and classy haka take yin sa. Tafa mata hannu tayi a saman fuskarta


"Meena wannan kallon fa?"


"Kin ganki kuwa Adda Raiha? Wallahi kayan sun miki kyau sosai, kar kije office kisa guys su dinga karo fa."


"Look at you, me wannan shigar yayi da har za'a yi karo, ni tsoron zuwa ma nake wallahi, boss din bashi da kirki ko kad'an, irin masu wulakancin nan ne kinsan masu kudi dangin mala'u."


"Allah? Wulakanci sukayi miki?"


"Bari kawai, dan tsabar wulakanci wai fa a gaban ido na yace wai ayi rejecting dina, hadda cewa wai corpers basu da wani amfani."


Dariya Amina ta fashe da ita ganin yadda Raihanan take tsuke fuska tana bada labarin


"Kice kin hadu da mara m, toh ya akayi kuma suka karbe ki?"


"Oga Kamal ne yaje ya same shi a office ko me suka ce oho, sai gashi ya dawo da takardar tawa anyi signing da stamp a jiki."


"Ok Allah sarki, shi me kirki ne Kamal din."


"A ah sosai wallahi, baki ga yadda ya dinga bani hakuri ba wallahi, har fa kuka nayi saboda takaici."


"Ai da haushi wallahi, sai kiyi takatsantsan dashi sosai, Allah ma yasa ba shine zai dinga baki monthly clearance ba."


"Da na kad'e har ganye na wallahi."


"Allah ma yasa dai ba shi din bane ba, dan ma dai an ce ba ma wani zuwa PPA din mutane suka ba."


"Ameen, idan ka hadu da supervisor me kirki ba, bari kiga na tafi yau farko kar nayi late nayi laifi."


"Sai kin dawo, ni sai rana nake da lectures ba ma lallai naje ba gaskiya."


"Ok." Tace ta zura takalmin ta suka fito a tare, taje tayi ma Adda Maimuna sallama sannan ta tafi.


   Kasancewar safiya ce bata wani sha wahalar abun hawa ba, nan da nan sai gasu a gaban wajen, ta sauka ta biya ta shiga takawa zuwa ciki. Gaisawa sukayi da masu gadin wajen dan sun gane ta zuwan da tayi, ta wuce ciki kanta tsaye. Babu cikar ababen hawa a harabar wajen hakan ya tabbatar mata da ba'a gama zuwa ba ko kuma ma dai tana cikin farkon wanda suka fara zuwa a yau din. Cikin reception din ta shiga ta tarar da wani namiji shi kadai yana zaune gaban computer, matsawa tayi suka gaisa tayi introducing kanta yace ta hau sama ta jira zuwan Oga Kamal, saman ta hau babu kowa sai Zainab tana gyara tarkacen da yake kan desk dinta. Itama gaisawa sukayi ta bata wajen zama tana dan satar kallon ta dan jiya da tazo bata nan sun fita da su Samuel.

  Tana nan zaune har aka dinga zuwa da kad'an kad'an, sai gashi wajen ya cika still dai tana zaune tana bin kowa da kallo tana jiran zuwan Kamal wanda take ganin kamar ba zai zo ba.


"Sir Aryan is here." Taji Zainab din ta fada daidai lokacin ta wani kamshin turare me sanyi da dadin kamshi a mamaye ilahirin wajen da suke. Takun tafiyar sa ce ta fara isowa in da suke bayan kamshin sa da ya gama karade wajen baki daya. Manyan kaya ne a jikin sa sabanin jiya da yake sanye da suit ash grey colour. Fuskar sa dinke kamar yadda yake a kullum sai dai shi hakan ya riga ya zame masa wani shashen na daga cikin shashen rayuwar sa, idan ya saki jiki yana walwala sai abinda ya faru a baya ya shiga dawowa yana masa yawo a tsakanin zuciya da kunnuwan sa.


"Welcome sir." Kawai kake ji tana tashi a wajen kusan dukkan su sun mike tsaye cikin girmamawa. Kallon sa take yi tun daga shigowar sa, har sanda ya tsaya gaban wani desk yayi signing jikin wata na'ura da ke daukar finger print din duk wanda ya shigo office a ranar da time din da ya shigo. Baki daya ya hada ya amsa gaisuwar da suke masa ya wuce kansa tsaye zuwa office dinsa dake daga dan wani corridor da ya hada da wani babban falon saukar baki.

  Ajiyar zuciya ta sauke bayan wucewar sa. Tashi tayi ta sake matsawa wajen Zainab ta tambaye ta yaushe Sir Kamal zai zo? Tana rufe bakin sa sai gashi ya shigo da saurin sa, da ita suka fara hada ido ya sakar mata murmushi ya karasa wajen attendance din yayi suka gaggaisa da kowa sannan ya karaso wajen da take a tsaye dan bata koma ta zauna ba kuma.


"Goodmorning sir." 


"Morning corper, follow me." Yayi hanyar office din da oga at the top din yayi, bin sa tayi a baya kamar munafuka suka isa kofar ya fara yin knocking kad'an sannan ya murd'a ya shiga sannan yace ta shigo.

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*


*DAUDAR GORA Billyn abdul*


*KI KULANI hafsat xoxo*


*A RUBUCE TAKE Huguma*


*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*


*IDON NERA Mamuh ghee*


_LITTAFI DAYA: 400_

_LITTAFI BIYU: 600_

_LITTAFI UKU: 800_

_LITTAFI HUDU :1000_

_LITTAFI BIYAR: 1200_


_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_


_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_


_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_


_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_


_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_


_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_


ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN


MARYAM SANI

ACCESS BANK

0022419171


SAI A TURA SHAIDAR BIYAN 


09033181070


IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA


09166221261


*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*


+22799643131


Books biyar  1250CFA

Books hudu  1050CFA

Books uku  850CFA

Books biyu  650CFA

Bookk daya  450CFA


KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.


MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post